• Farawa
  • Na Baya
  • 18 /
  • Na Gaba
  • Karewa
  •  
  • Gurzawa HTML
  • Gurzawa Word
  • Gurzawa PDF
  • Budawa: 2358 / Gurzawa: 1705
Girma Girma Girma
Tafarki Zuwa Gadir

Tafarki Zuwa Gadir

Mawallafi:
Hausa

TAFARKIN ZUWA GADIR

Wallafar: Kamal Assayyid

Fassarar: Hafiz Muhammad Sa’id

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Kura'ni Da Hadisi Suna Cewa : “Kawai Allah yana son ya tafiyar da dauda daga gareku Ahlul Baiti kuma ya tsarkake ku tsarkakewa[1]

“Ni na bar muku nauyaya biyu; Littafin Allah da Ahlin gidana, ba zaku taba bata ba bayana har abada matukar kun yi riko da su[2]

Gabatarwar Mafassari

Musulunci shi ne addinin Allah dawwamamme da yake kunshe cikin Kur’ani da Sunna, kuma Allah da manzonsa sun sani cewa al’umma zata yi sabani kamar al’ummun da suka gabace ta, don haka ne Kur’ani mai girma ya sanya wa al’umma makoma da zasu dogara da ita bayan wafatin manzo (S.A.W), wacce take haskaka musu abin da suka takaita ga fahimtarsa da tafsirinsa, wannan kuwa su ne; Ahlul Baiti (A.S).

Su tsarkaka ne daga dukkan dauda da kuma kazanta wadanda Kur’ani ya sauka ga kakansu Mustapha (S.A.W), suna karbarsa suna karanta shi suna hankaltarsa da kiyayewa, sai Allah ya ba su abin da bai ba waninsu ba, kuma manzo ya yi wasiyya da su a matsayin makoma ta gaba daya a hadisin sakalain mash’huri, wannan al’amari an gina tushensa tun ranar Gadir bisa umarnin Allah ga manzonsa da ya kafa dan amminsa imam Ali (A.S) a matsayin halifansa na farko, wanda ya sanya shi haske da wannan al’umma take shiriya da shi.

Wannan littafin yana son ya yi bincike ne game al’amarin Gadir ne kamar yadda zamu karanta cikin bayanan da shi Kamal Assayyid ya kawo, amma domin tabarruki sai ya fadada bayanin da kawo kissar Gadir kamar yadda ta zo a cikin littattafan tarihi da hadisai.

Daga karshen muna neman Allah ya gafarta mana zunubanmu domin albarkacin wannan rana mai albarka ta Gadir, ya samu cikin masu riko da wilayar imam Ali (A.S) da sauran imamai (A.S). Kuma ya bayar da ladan wannan fassara ga iyayena, ya tsawaita rayuwarsu da albarka a cikinta.

Hafiz Muhammad Sa'id

hfazah@yahoo.com

Khurdad 1381 H.Sh, Mayu 2002 M

Gabatarwar Mawallafi

A tarihin Musulunci akwai abubuwan da suka damfara da bayanin sunaye madaukaka a tarihi, sunayen mazaje ne gwaraza da suka cika wa Allah alkawarin da suka dauka da kuma mataye muminai. Da sunayen wuraren da ke can kasar wahayi da duk wani wuri da Annabi ya tsaya a wurin, kamar kogon Hira wanda ya ga hudowar haske, hasken ruhi mai tsarki. Zuwa Zazar Abi Dalib, zuwa gidan Arkam, zuwa kogon Sauru, zuwa idaniyar ruwa ta Badar, zuwa dutsen Uhud da bishiyar Ridwan, zuwa Hudaibiyya da Fadak zuwa… Gadir Khum.

A cikin wannan waje, a inda idanun Gadir ke kwarara, inda Annabi (S.A.W) ya tsaya yana mai isar da sakon Ubangijinsa a sakon karshe na sama. Na’am wannan waje, waje ne mai tsarki, inda Jibril (A.S) ya sauka dauke da sakon sama “Ya kai wannan Manzo ka isar da sakon da aka saukar gare ka daga ubangijinka! Idan ba ka yi haka ba, to ba ka isar da sakonsa ba!” Annabi ya tsaya, tawagar alhazai ta tsaya, sannan ya shelanta a cikin wannan taron jama’a “Duk wanda nake Shugabansa, to wannan Ali Shugabansa ne”.

A wannan lokaci na tarihi a zamani an sami bayyanar abubuwa na farin ciki domin su dawwamar da wannan rana ta goma ga Zulhajji, shekara ta goma da hijira domin ya zama idi mai tarihi. Wannan gabatarwa mun kawo ta ne domin ta share fagen bayanin Gadir a tarihin rayuwar musulunci bayan haskakawar tarihinmu mai girma.

Kamal Assayyid

Tafarki Zuwa Gadir Khum

A tsakanin hanyar Makka mai girma abar girmamawa da Madina mai haske abar haskakawa, a kusa da Juhufa, akwai wani yanki wai shi Gadir Khum. Gadir ya kasance a hanyar matafiya ne, Manzon Allah (S.A.W) ya taba wucewa ta nan a lokacin hijirarsa mai tarihi a watan Rabi’ul Awwal shekarar 622 miladiyya, kamar yadda ya tsaya a 18 Zul hajji shekara ta goma hijira a lokacin dawowarsa daga hajjin bankwana. Ta haka ne wannan wuri ya shiga cikin tarihin Musulunci mai girma.

Hanyar Gadir tana da nisa daga babban titi a wannan zamani, saboda rairayin da ya mamaye hanyar karauka a lokutan baya da suka gabata, kamar yadda a yanzu ake ce wa wannan yanki Algurba. Har yanzu akwai wata idaniyar ruwa da take bubbugo da ruwanta daga cikin duwatsu a wani waje mai yalwa.

Saboda samuwar wannan idanwar ruwa ne itacen dabino da itacen arak suka fito a duk wurin, wanda ya bar garin Jidda a kan hanyar nan ta gefen kogin maliya zai isa mararrabar nan ta Juhfa a kusa da garin Rabig daidai da tashar jirgin saman cikin gida na Saudiyya a daman hanya. Daga mararrabar zuwa masallacin mikati wanda aka sabunta gina shi a gefen kusa da kufan wani masallaci dadadde rusasshe zai kai kilomita goma. Daga masallacin mikati zai yiwu a fuskanci Kasrul ulya ta wata hanya wacce take cike da rairayi daidai inda alamomin kufan tsohuwar hanyar hijira suke.

Shi kuma Kasrul Ulya yana kusa da alkaryar nan ta Juhufa ta fuskar hanyar nan da ta yi Madina da garin Rabig. Shi kuma masallacin mikati yana fuskacin hanyar da za ta kai zuwa Makka. Nisan da yake tsakanin masallacin mikati da Kasrul ulya ya kai kilomita biyar, kwararar ruwa da iska duk sun yayimo malalar rairayi da suka yi shingaye na rairayi tsakanin yankunan guda biyu. A wannan yanki akwai tsaunuka na duwatsu da suka iyakance hanyar nan da takan kai zuwa wani wuri mai yalwa inda hanyoyi suka rarraba.

To daga nan zai yiwu a dauki hanyar Guraba wacce da wahala a gane ta saboda yawan mamalelen rairayi. Amma yankin Gadir yana yankin Harra, wanda wuri ne da yake cike da bakaken duwatsu wadanda ba sa karbar shuka, a karshen Harra akwai wannan wuri mai yalwa da fadi, inda idanun ruwan Gadir yake. A wannan wurin Annabi (S.A.W), ya tsaya domin ya isar wa tawagar alhazai da al’ummar musulmi sakon sama na karshe. Wurin mai yalwa yana tsakanin jerarrun duwatsun arewa da na kudu. Idanun ruwan Gadir yana bubbuga daga kusa da gindin duwatsun bangaren kudu, wanda sun fi na Arewa girma sosai,

A daidai kwararon wuraren ne itacen dabino suka tsuro, akwai tsammanin kwarai cewa wadannan itacen sun tsuro ne sakamakon jefar da kwallon dabino da matafiya suka yi a wurin. Yalwar fadin wurin da ruwan Gadir suna jan hankalin matafiya zuwa ga neman hutawa da shan gahawa a wurin.

A kusa da magangaran wajen a bangaren yamma akwai fadama inda ruwa yake bubbuga ya haifar da wata magudana, saboda tsananin kwararar ruwan ne a lokutan ruwan sama ya sanya yanayin yankin yakan canza akai-akai. Wanda yake so ya samu albarkacin wannan wuri inda karshen Annabawa ya tsaya zai yiwu ya iya bi ta hanya biyu ta Juhufa da Rabig.

Hanyar farko tana farawa daga mararrabar hanyar Juhufa daidai filin jirgin saman Rabig inda hanyar matafiya take mai tsayin kilomita tara zuwa alkaryar Juhufa, a wajen akwai wani babban masallaci. Daga Alkaryar hanyar tana karkata dama da nisan kilomita biyu, tana cike da yashi, kuma yanki ne mai cike da duwatsu, to daga karshenta ne filin Gadir yake farawa. Amma hanyar ta biyu tana farawa daga mararrabar hanyar Makka da Madina ta hanyar Rabig. Bayan tafiyar kilomita goma hanyar da take kaiwa zuwa Gadir take yankewa, Daga Rabig zuwa Gadir zai kai kusan kilomita ashirin da shida.

An gina masallacin a wannan wuri mai tsarki, amma yanzu ya rushe kuma ba wata alamarsa sakamakon gudanar ruwa da iska. Ta yiwu masallacin ya kai kusan wannan lokuta zuwa farkon karni na takwas, lokacin da ya rushe ba abin da ya rage sai katangunsa. Dalilin da ya sa aka gano haka shi ne littattafan fikihu da tarihi da abin da ya zo na mustahabbancin yin wasu ayyuka kamar addu’a da salla a cikinsa.

Kuma akwai alamomin da suka zo game da wajen da Annabi ya tsaya a cikinsa, inda ya shelanta wilayar Imam Ali (A.S) a cikin taron al’ummar musulmi, Bakari yana cewa: Wurin yana tsakanin Gadir da idaniyar ruwan, kamar yadda Hamawi ya fadi a cikin Mu’ujamul Buldan, ya kuma iyakanta wurin masallacin. Haka nan an ambace shi a littafin Jawahir, kuma ya yi nuni zuwa ga ragowar kufan garunsa rusassun tare da dogaro da abin da ya zo a Durus na Shahidul Awwal Muhammad bn Makki, amma Ibn Batuta ya yi nuni zuwa ga wucewarsa ta yankin da garuruwan kusa da Juhufa suke ne a tafiyarsa zuwa ga hajjin dakin Allah mai alfarma.

A Musulunci an mustahabbantar da tsayuwa a Gadir Khum da salla a cikinsa da addu’a. Hakika daya daga cikin sahabban Imam Sadik (A.S), an ruwaito daga gare shi cewa ya tafi tare da shi daga Madina zuwa Makka. Yayin da suka isa masallacin, sai ya ce, “Nan ne wurin sawun tafin Manzon Allah (S.A.W) yayin da ya ce “Duk wanda nake Shugabansa, to wannan Ali Shugabansa ne. Ya Ubangiji ka taimaki wanda ya taimaki wanda ya taimake shi, ka ki wanda ya yi gaba da shi, ka tabar da wanda ya ki riko da shugabancinsa”.

Hakika mustahabbancin salla a masallacin Gadir ya zo a da yawa daga littafan fikihu, kuma Annabi (S.A.W) ya tsaya a yankin Gadir bayan saukar wahayi, “Ya kai wannan Manzo ka isar da abin da aka saukar daga Ubangijinka, kuma idan ba ka aikata ba, to ba ka isar da sakon sa ba, Allah ne yake kare ka daga mutane”.

Littattafan tarihin sun ambaci cewa hakika Manzon Allah (S.A.W) ya yi umurni da a tsai da karauka domin ya yi huduba mai girma a rana mai tsananin zafi, al’amarin da ya sanya musulmi suna tambayar musabbabin tsayawa a wannan wurin mai tsananin zafi, kuma ya yi huduba yana mai cewa: “Godiya ta tabbata ga Allah, Muna neman taimakonsa, muna imani da shi, muna dogaro da shi, muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu, wanda ba mai shiryarwa ga wanda ya batar. Ba mai batarwa ga wanda ya shiryar, ina shaidawa babu abin bautawa sai Allah kuma Muhammad bawansa ne, Manzonsa ne.

Bayan haka, ya ku mutane! Hakika Mai tausayi, Mai sani (S.W.T) ya ba ni labari cewa ba wani Annabi da aka rayar sai kwatankwacin rabin rayuwar wanda yake gabaninsa, kuma ni an kusa kirana in amsa, ni abin tambaya ne, ku ma haka. Me za ku ce?”

Sai suka ce: “Mun shaida ka isar da sako, ka yi nasiha, ka yi kokari, Allah ya saka maka da alheri”.

Sai ya ce: “Shin ba ku shaida ba abin bautawa da gaskiya, sai Allah ba, kuma hakika Muhammad bawansa ne kuma manzonsa ne ba, aljannarsa gaskiya ce, wutarsa gaskiya ce, mutuwa gaskiya ce, kuma tashin alkiyama mai zuwa ne ba kokwanto a cikinta, kuma Allah (S.W.T) yana tashin na cikin kaburbura”?.

Suka ce, “E, mun shaida da haka”.

Sannan ya ce: “Allah ka shaida” kuma ya ce: “Ya ku mutane! Shin kuna ji na”?.

Suka ce, “E”.

Sai ya ce: “Ni zan gabace ku tafki (alkausar), kuma ku zaku zo min a wajen tafkin, fadinsa ya kai tsakanin Sana’a da Busra, a cikinsa akwai kofuna adadin taurari, ku duba ku gani, yaya za ku maye (bi) nauyaya biyu, wato littafin Allah da Ahlin gidana bayana”!.

Sai wani ya yi kira da murya madaukakiya, “menene nauyaya biyu ya Manzon Allah?”.

Sai ya ce, “sako mafi nauyi littafin Allah, gefensa a hannun Allah, gefe a hannunku, dayan karamin shi ne zuriyata. Hakika Ubangiji Mai tausayi, Masani, ya ba ni labari cewa su ba zasu taba rabuwa ba har abada har sai sun riske ni a tafki. Sai na roka musu wannan a wajen Ubangijina. To kada ku shiga gabansu, sai ku halaka, kada ku tsaya can bayansu, sai ku halaka”.

Sannan ya riki hannun Ali (A.S) har sai da aka hango farin hammatarsa, mutane suka gan shi gaba daya, sannan ya ce: “Ya ku mutane, wanene ya fi wa muminai kawukansu?”.

Suka ce: “Allah da Manzonsa sune mafi sani”.

Sai ya ce: “Hakika Allah Shugabana ne, ni kuma Shugaban mutane. Kuma ni ne na fi wa muminai kawukansu. To duk wanda nake Shugabansa, wannan Ali Shugabansa ne!”. ya maimaita sau uku, a ruwayar Ahmad ya maimaita sau hudu.

Sannan ya ce: “Ka jibanci lamarin wanda ya mika masa wuya, ka ki wanda ya ki shi, ka so wanda ya so shi, ka taimaki wanda ya taimake shi, ka tabar da wanda ya ki taimakon sa, ka juya gaskiya tare da shi duk inda ya juya. Ku saurara! Wanda yake nan ya isar wa wanda ba ya nan”.

A wannan lokaci mawakin Manzon Allah, Hasan bn Sabit ya shiga waka don ya koda wannan al’amari da ya zama idi ga musulmi. Yana cewa: Annabinsu yana kiran su a ranar Gadir A Khum an ji Annabi yana mai kira Yana cewa wanene Shugabanku Mahaliccinku Suka ce ba tare da musun da ya bayyana ba Ubangiji Mahaliccinmu, kai kuma Shugabanmu Ba a ga wani a cikinmu mai sabawa cikin wilaya ba Sai ya ce tashi ya Ali hakika cewa ni na yarda Da kai bayana Imami kuma mai shiryarwa A nan ne ya yi addu’ar Allah ka taimaki wanda ya bi shi ka kuma zama makiyi ga wanda ya zama makiyin Ali

Abubuwan Da Suka Faru A Tarihin Hijira

Abu Na Farko

Hijira ta kasance abin da ya ta’allaka da tarihin rayuwar dan Adam tun farkon bayyanar tarihi har zuwa yau. Haka nan kuma ba za ta gushe al’amari na zamantakewar dan Adam ba tana mai kunshe da abubuwa da suka zama mafitarsu ta doru a kanta ne. Idan abin ya zama gwagwarmaya da dauki-ba-dadi tsakanin zalunci, to abin yakan zama abu mai girma na tarihi, kuma farkon shafi na rayuwar wata al’umma ko dan Adam mai hijira.

Zalunci ya yi kamari a Makka har ya zama ba malumfasa, rayuwar mutanen da suka yi imani da sakon sama ta zama abu mai wahalar jurewa. Manzon Allah (S.A.W) ya kasance yana so ya gina rayuwa mafificiya ga mabiyansa. Hijira zuwa Habasha ta zama warwara ga wahalhalu na wani dan lokaci har zuwa lokacin da haduwar Akaba ta wakana.

A cikin duhun dare ne haduwar ta wakana, Akaba wuri ne kusa da Makka. Hanyar tsira da kubuta ta bude, Annabi (S.A.W) ya dawo alkaryarsa yana yi wa mabiyansa albishir da cewa: “Allah ya ba ku ’yan uwa da garin da zaku zauna ku debe kewa a cikinsa”.

Haka nan sabon shafin rayuwar Musulunci ya fara a wadannan kwanaki masu cike da wahalhalu da firgici da tsoro da buri. An ga mutane suna gudu suna barin garinsu da aka haife su suka taso a ciki.

Kuraishu da tsaurin kanta ta kasa gamawa da wannan al’amari mai hadari a gun ta. Al’ummar Makka ta fara girgiza ana barin gumaka, maslaharta tana raurawa.

Makirci

Abu Jahal, da Abu Sufyan, da Umayya, da dukkan manyan Kuraishawa suka ga mafificiyar hanyar mafita shi ne gamawa da Manzo da hutawa daga gare shi. Tunda rabe-raben kabilu da kuma matsayin Bani Hashim a al’umma da kare Manzo da suke yi tsayin shekaru daga kisa. To idan kabilu da yawa suka yi tarayya a kashe shi, wannan zai sanya Bani Hashim su kasa daukar fansa, su yarda da diyya. Haka nan ran Abu Jahal ta kitsa masa don makirci.

Makirci ya kai hadarin da sai da Jibril (A.S) ya sauka daga sama da wannan aya. “Kuma yayin da kafirai suke kulla makirci a gareka domin su tsare ka ko su kashe ka ko su kore ka, suna makirci, Allah shi ne fiyayyen mai (raddi ga) kulla makirci”.

Dare ya yi a Makka, taurari sun bayyana, dare na cike da zukata masu boye gaba ga Manzon Allah (S.A.W) daga nesa. Abu Jahal na sanye da abayarsa, yana mai takama da tunaninsa, yana ganin cewa Makka za ta karfafa da tunaninsa, ya zama mutumin tarihinta (Gwarzo), dabararsa ta zama mafita kuma abin fada.

Fansa

A cikin wannan lokaci mai tashin hankali kuma ana dab da zartar da shirin da aka kulla, sai gwarzon saurayin nan na Musulunci a tarihi, a daya daga cikin irin sadaukarwarsa ya fanshi Manzo (S.A.W) da ransa. Wannan saurayi shi ne Imam Ali (A.S), hakika yana daga jarumtaka mazaje su shiga fagen fama suna yaki har mutuwa, amma mutum ya kutsa wa mutuwa karkashin sukan takubba da masu da zabinsa, wannan abu ne wanda alkalami duk yadda ya kai bayani da zurfi wajen bayyanawa bai isa ya iya kawo hakikanin wannan jaruntaka ba.

Ali ya sunkuya yana sauraron maganar mutumin da ya rayu da shi sama da shekara ashirin. Ya ce: Shin za ka tsira ya Manzon Allah idan na fanshe ka da raina? Sai ya ce, “E mana, haka Ubangijina ya yi min alkawari”. Ali, da ya kasance mai bakin ciki, amma da jin haka, sai zuciyarsa ta yi fari.

Makka ta kasance gari ne wanda mutanenta azzalumai ne da suka yi shirin kashe mutumin da sama ta aiko domin tseratar da duniya. Sai dai Ali, da jin wannan amsar (cewa Manzo zai tsira), sai bakin cikinsa ya koma farin ciki.

Saurayi (A.S) ya tafi cikin nutsuwa zuwa shimfidar Annabi (S.A.W) ya lulluba da bargonsa yana sauraron takubba su yayyaga namansa, su zubar da jininsa mai tsarki. Ali (A.S) ya yi barci a shimfidar Annabi, yayin da shi kuma (Annabi) ya fuskanci hanyar gudu daga mutanensa ta hanyar Madina.

Hanya Zuwa Yasrib

Matakin Annabi (S.A.W) shi ne ya fuskanta zuwa kudu zuwa Kogon Sauru domin ya buya a can wasu kwanaki, ta yiwu a yi tattalin kayan hawa da tafiya, Kuraishu ta yanke kauna daga kama shi, kamar yadda kwanan Ali (A.S) a kan shimfidarsa ya ba da gudummuwa sosai wajen batar da kama da jinkirta ganewar masu kaidi ga labarin hijirarsa.

A yanayi na sirri kwarai Ali (A.S) ya sayi rakuma biyu ga Annabi (S.A.W) da sahabinsa Abubakar, kamar yadda yarjejeniya ta cika da dan jagoran nan na sahara, wato Abdullah dan Uraikidi. Duk da mutum ne da ya wanzu kan shirkarsa, amma hakika ya kasance mutum ne amintacce da Annabi (S.A.W) ya dogara da shi. Kuraishawa sun fadaka suka dauki matakai masu tsauri, mahaya suka fantsama neman Annabi (S.A.W), aka kuma sanya kyauta mai yawa ga wanda ya kamo shi, ko ya nuna wata alama da za ta sanya kama shi, amma duk da sun samu wasu mutane suna da shaidu masu girma, amma suka samu rashin sa’a wajen samun su.

Hakika Kuraishawa sun natsu cewa lallai zasu kama Muhammad (S.A.W), har ma sun samu labari na wani yanki da ake kokwantonsa. Kai har ma sun kai Kogon Sauru, inda Annabi (S.A.W) da Sahibinsa suka buya, sai ikon Allah ya shiga tsakani don kare Annabin karshe (S.A.W). Dayansu ya hau kan kogo don ya ga abin da yake ciki da wanda ke ciki. Nan da nan sai ya dawo zuwa ’yan uwan tafiyarsa.

“Menene a nan? (Suka ce)

(Ya ce): “Ba komai”.

“Kogo fa?”

“Na ga sakar gizo-gizo a bakinsa, ina ganin ya saka ta tun kafin haihuwar Muhammad (S.A.W). Na ga shekar akwai tattabara biyu a cikinsa da kuma rassan itaciya, sun shiga juna ta yadda ba yadda za a yi wani mutum ya shiga kogon sai ya kawar da ita”.

(Suka ce): “Ke nan ba wanda ya shige shi?”

(Ya ce): “E, ba wani mutum da ya zo masa”.

Manzon Allah (S.A.W) ya kasance yana sauraron tattaunawar, sai ya fadi a cikin zuciyarsa: “Alhamdu lillah”. Nutsuwa ta mamaye zuciyarsa.

Tafiya

A lokacin da aka ayyana (zuwan Jagoran hanya), sai ya zo yana janye da rakuma biyu, bayan kwanaki uku da Manzo (S.A.W) ya yi a kogon.

Yasrib (Madina) tana arewa da Makka, amma duk da haka Manzo (S.A.W) ya yi kudu wajen kogon Sauru domin boye tafiya da cikakken sirri: Dan jagora ya yi hanyar kogin maliya, ya kama hanya mafi nisa daga karauka. Tafiyar ta kasance mai wahala, ta dauki kwana bakwai. Annabi yana ratsa mamaleliyar Saharar Tahama a zafi mai kuna, a hanya mai tsanani, hakika ya ketare hadarin, Kuraishu ta kasa komai.

A 12 ga Rabi’ul Awwal ya kai alkaryar Kuba’a a nahiyar yankin Yasrib (Madina) A Kuba’a Annabi (S.A.W) ya yi kwana hudu yana jiran zuwan dan Amminsa, Ali bn Abi Dalib (A.S). Yayin da ranar Juma’a ta zo, Manzo (S.A.W) ya fuskantar da fuskarsa nahiyar Madina, ya kasance dubunnan mazaunan Madina suna sauraron zuwansa.

A wannan lokacin mai ban tsoro, yayin nan ne garuruwa suke canza sunayensu, a 16 ga Rabi’ul Awwal da ya yi daidai da ga watan Yuli 622 miladiyya, Annabi (S.A.W) ya isa Yasrib a lokaci mai dawwamammen tarihi, mutanen Madina kaf sun mike don tarbar karshen Annabawa a tahiri.

’Yan matan Madina suka fito suna wakar farin ciki, suna kallon abin hawan mai hijira (Annabi) yana keta Saniyyatul Wada’a, a wannan lokuta masu cike da buri da farin ciki ne tarihin hijira ya fara, aka kafa tsuron al’ummar Musulunci.

Al’amari Na Biyu

Mutuwa da rayuwa sun zama ala-kakai a rayuwar mutum. dan hakin da aka raina zai tsone ido fa. Ga wanda ke son rayuwa, wace hanya zai bi? Hanyar rayuwa ko mutuwa? duba mana ku ga gida mai girma a Makka ya yi shekara goma sha uku da saukar Jibril (A.S) a kogon Hira.

Mushrikan Makka suka ga akwai hadari, suna ganin ’ya’yan Makka suna gudu da addininsu, suna gudu arewa zuwa Madina, Allah ya tashi mutane don taimakon sakon sama. Hijira ta yawaita har ta washe unguwa gaba dayanta, Kuraishu suka ga matakinsu bai kai ga nasara ba, kullum hadari yana karuwa. Abu Jahal ya motsa don ya sanya mataki na jahannamanci don gamawa da Muhammad (S.A.W) har abada.

Jibril (A.S) ya sauka yana mai kunyata da bata matakin Shedan na bice hasken da ya haskaka a dutsen Hira zai haskaka duniya gaba daya. “(Tuna) Yayin da wadanda suka kafirta suke makirci don su tsare ka ko su kashe ka ko su fitar da kai, suna makirci, Allah yana makirci, Allah shi ne fiyayyen masu iya (sakamakon) makirci”.

A wannan lokaci ne mai tarihi daya daga mafi girman fansar da kai ta faru a tarihin dan Adam. Duk irin tunanin mutum ba zai iya suranta yanayi na wannan saurayi dan shekara ashirin da uku, yana shiga gaba don rungumar mutuwa ba. Abubuwa suka faru akai-akai, Kuraishu ta saka mafi girman makircinta kamar yadda gizo-gizo yake saka gidan da yake shi ne mafi raunin gidaje. Annabi (S.A.W) ya kira dan Amminsa, masoyi, ya nuna masa kaidinsu, ya zama abin da yake so daga Ali (A.S) shi ne ya kwana a shimfidar Annabi (S.A.W), amma abin da ya zama burin Ali dan Abi Dalib shi ne ciran Manzo don haka ya tambaya, “Shin za ka kubuta ya Manzon Allah in na fanshe ka da raina?”

“E, haka Allah ya yi mini alkawari”. Sai ga farin ciki yana bayyana a fuskar Ali (A.S). Ya gabata wajen shimfidar Annabi (S.A.W) don ya kwanta ya yi barci da aminci da natsuwa. Yayin da idanun miyagun (mutane) arba’in suna sauraro a cikin duhu (don kashe Manzo), lokaci ya ja Manzon Allah (S.A.W) ya sulale wajen gida ya fuskanci kudu zuwa kogon Saura.

Miyagu suka kewaye gidan Manzon Allah da takubba masu kyalli, a ketowar farko na alfijir fuj’atan ai Ali ne! ya tashi daga shimfidarsa: Manzo ya riga ya kubuta!. A lokacin safiyar farko Makka ta ga wani sabon yanayi mara dadi. Ashe Manzon da Allah ya aiko domin ya cika kasa da haske ya gudu, mahaya dawakai suna ta bincike kowane waje. Kuraishu ta sa kyauta mai yawa ga wanda ya zo da Muhammad (S.A.W) a raye ko a mace, ko ya bayar da wata alama da za ta sa a kama shi.

Ali (A.S) ya zauna a Makka kwanaki yana shelantawa a kwarin Makka cewa, “Duk wanda yake da wata amana a wajen Muhammad (S.A.W) ya zo mu ba shi kayansa”.

Wasika Daga Kuba’a

Manzo (S.A.W) ya isa Kuba’a ya sauke kayansa a can, daga nan ya aika da wasika zuwa ga dan Amminsa yana umurtar sa da ya zo. Abu Wakid Allaisi ya tafi Makka ya ba wa Ali (A.S) wasika. Wai menene ya sa wannan nacewar don sauraron zuwan Ali (A.S), bai shiga Madina ba har sai da Ali (A.S) ya zo?

Lallai tarihin hijira ya ba da labarin sauraron wannan lokaci mai zafi da tsanani don haduwar Muhammad da Ali (A.S), lallai a cikin ruhin Ali (A.S) akwai sirri mai ban mamaki, yayin da hakika take bayyana a zatin mutum, ta sanya duk abin da yake tattare da shi ya damfaru da haske wanda ba daga rana ko wata yake ba, sai dai haske ne wanda yake daga tsakatsakin sammai.

Haka nan imanin wannan saurayi yake, wanda bai san wani Shugaba ba banda Muhammad (S.A.W). Muhammad din da ya bude idanunsa a kan kofofin haske a tuddan duwatsun Hira. Tawaga ta kutsa cikin rairayi, yana tafiya sannu-sannu, a tare da shi akwai Fadimomi: Fadima ’yar Asad, da Fadima ’yar Muhammad, da Fadima ’yar Hamza, da Fadima ’yar Zubair.

A wani wuri “Ziduwa” ababen zalunta suka saurari zuwan Ali (A.S) don ya tseratar da su daga garin da al’ummarta suke azzalumai, suka keta hanyar kwarurruka da kwazazzabai da babu komai sai shudiyar sama da farin rairayi.

Ali (A.S) ya san abubuwa da yawa, tun kafin shekaru ashirin ne yake tare da zababben Allah (S.A.W), ba kawai yana tare da shi bane, sai dai ya narke a cikinsa ne narkewa. Shi ya sa shi ya san sirrin duniya (halitta). Abu guda ne Ali (A.S) bai san shi ba faufau, wato; tsoro, hakika mutum ya gajiya gaban surkukiyar mutuwa karshen rayuwa, shin shi ne karshe ko farko?

Amma Ali (A.S) ya gano makamar dawwama, ya rinjayi mutuwa ba sau daya ba, ba sau biyu ba, amma mutuwa tana gudunsa, tana guje masa duk sadda ya so rungumar ta. Ya lulluba a cikin bargon Annabi (S.A.W), ya runtse idanunsa a shimfidar da kanshin aljannar Firdausi ya mamaye shi, yana mai ba da ransa fansa ga karshen Annabawa a tarihin dan Adam.

Idan Isma’il ya mika wuya ga Allah, lallai ya san babansa zai yanka shi a sannu-sannu ne, sai dai Imam Ali (A.S) ya runtse idanunsa don ya bude su a kan gomomin takubba masu guba. Mala’iku sun so kansu wajen gogoriyon rayuwa, Jibril (A.S) bai fanshi Mika’ilu ba (A.S), kowannensu ya zabi rayuwar, amma sai ga shi wannan saurayi mai suna Ali da ubangiji mai iko ya kare shi, yana mai karya bangon mutuwa, ya zabi mutuwa dan’uwansa Manzon rahama ya rayu.

Tawaga tana tafiya har ta kai kusa da “Rajnan”, sai aka cim mata, sai ga mahaya doki takwas sun bijiro musu suna son su mayar da hannun agogo baya. A nan ne aka yi wa yankin nan na Larabawa bazata da “Zulfikar”. Takwas din nan suna son su mayar da tawagar zuwa Makka, zuwa alkaryar da mutanenta azzalumai ne, idanu suna cike da hikidu da mugun kulli. Wani mahayin doki cikinsu a lokacin ba a san waye Ali ba, ya ce:

“Kai mayaudari, kana tsammanin za ka tsira da mata? koma don gidanku!” Tir da wannan magana da ya gaya wa Ali.

Ali ya amsa da sabati kamar dutsen Hira, “In ban koma ba fa?”.

Suka ce: “Ko ka ki, ko ka so”.

Sai Junahu ya kawo wa taguwa hari, don ya mai da ita.

Sai Ali (A.S) ya tare shi.

Ya kawo sara, Ali (A.S) ya kare ta.

Ya kuma sare shi, sara mai tsage mutum, ya kuma gama da shi.

Saura suka ja da baya.

Lallai abin ya dimauta su, ba su taba ganin sara kamar haka ba a rayuwarsu. Dayansu ya daga murya, ya ga saurayi yana shiri don kawo hari: “Ka kame kanka daga barin mu, ya dan Abi Dalib”.

Ali (A.S) ya fada da karfi: “Ni mai tafiya ne wajen dan’uwana kuma dan Ammina Manzon Allah (S.A.W)”.

Tawaga ta tafi hanyar Yasrib, Manzon Allah bai gushe ba, yana sauraro a Kuba’a. A 16 ga Rabi’ul Auwal ne, wanda ya yi daidai da 20 ga Yuli 622 na miladiyya tawagar tarihin hijira ta isa garin Yasrib. Jama’ar musulmi ta cika a Saniyyatul Wada’ tana jiran isowar karshen Annabawa a tarihin dan Adam.

Al’amari Na Uku

Sama tana cike da taurari ababen damfarawa, tana walkiya daga nesa kamar lu’ulu’u abin yayyadawa, Muhajirun sun sauka a Rajnan, Ali (A.S) ya sunkuya yana magani ga kafafunsa, da saboda tafiyar daruruwan milamilai sun tsattsage. Taguwowi sun durkusa a kan yashi suna lumfasawa daidai suna jin kanshin gari nan kusa.

Idanun Fadima (A.S) suna yawo tsakanin taurari suna kallon sasannin sama inda babanta ya yi tafiyar isra’i da mi’iraji a kan Buraka. Idanun Fadima (A.S) ba su gushe ba suna kallon taurari, fuskarta tana haskakawa kamar tauraron da ya sauko kasa, wata ya bayyana a karshen dare. A lokacin Fadima (A.S) ta lumfasa tana munajati da Ubangijinta.

“Kai ne mai wanzuwa, komai mai bacewa ne, taurari wata... Fararen rayuka suna fuskantar ka, ba ruwansu da kayoyin da ke kan hanya a sahara, koda kuwa ba su da takalma, kai kadai ne gaskiya. Ya Ubangiji kai ne hasken idanuna da farin cikin zuciyata, ka bar ni in kutsa wa malakutinka in yi tasbihi, in kewaya tare da taurari a gefen Al’arshinka, kai kadai ne hakika, waninka wahami ne. Kai kadai ne mabubbugar rayuwa, waninka sururi ne da mai jin kishirwa yake tsammanin ruwa ne”.

A Kuba’a Jibril (A.S) ya sauka yana dauke da kalmomin sama zuwa ga mutumin da ya gudu daga uwar alkaryu (Makka) yana ba shi labarin matafiya da ’yarsa, da matar da ta rene shi, da saurayin da ya rena a dakinsa, wanda yayin da ya girma ya tsaya a gefensa yana kare shi iyakar karfinsa.

A nan ne fa mafarkin nan na wahayi ya tabbata, farfajiyar Kuba’a ta yi yalwa, yayin da Annabi (S.A.W) ya gina masallacin farko a Musulunci. “Wadanda suke ambaton Allah a tsaye da kuma tunani a cikin halittar sammai da kasa (suna cewa): Ya Ubangijinmu ba ka halicci wannan don wasa ba, tsarki ya tabbata gare ka, ka kiyashe mu azabar wuta. Sai Ubangijinsu ya amsa musu cewa ni ba na tozarta ladan aikin mai aiki, namiji ko mace, sashenku daga sashe yake, wadanda suka yi hijira daga gidajensu aka cutar da su a tafarkina, suka yi yaki aka kashe su, zan shafe kurakuransu, kuma in shigar da su aljanna koramu suna gudana ta karkashinta, sakamako daga wajen Allah, Allah a wajansa akwai kyakkyawan sakamako”.

Annabi (S.A.W) ya kasance yana sauraron isowar tawagar matafiya da ’yarsa da mai renonsa suke ciki, kuma kalmomin da Jibril (A.S) ya gaya masa ba sa gushewa cikin tunaninsa, yana kallon nesa, amma ba komai sai yashi. Da an kaddarawa wani yana Kuba’a a wannan lokaci da (ya ga abin mamaki), ya ga wani mutum wanda ya kai shekara hamsin, shi ba dogo ba, ba gajere ba, matsakaici, (hakika an sanya alheri duk a cikin tsakaitawa), mai farin fuska, mai fari tas, an cakuda shi da jaja mai sauki (ta yiyu sakamakon rana ta doke shi ne), mai yawan gashi zai kai bayan kunnensa, ya kusa ya hau kafadunsa, mai yalwar goshi, mai lankwasassun gira kamar wata (jinjirin wata biyu), idanunsa masu haske ne, masu fadi, mai madaukakin karan hanci, hakoransa kamar lu’ulu’u ne da aka daddasa, idan yana tafiya yana tafiya da sauki, takunsa makusanta ne kamar kwale-kwale da ya yo gangara.

Annabi (S.A.W) ya tsaya yana tunanin sahara mai nisan gani yana sauraron masoyan da ya bar su a wani lokaci na dare, kurayen Makka sun kewaye shi. Dare ya mamaye sahara, Annabi (S.A.W) ya koma hayin Bani Saham, a fuskarsa akwai bakin ciki kamar bakin cikin annabi Adam ranar da yake binciken Hawwa a bayan kasa.

Matafiyan (masu hijira) sun isa da aminci, Uban (S.A.W) ya tattaka domin haduwa da tarbar ’yarsa abar tunawarsa daga Hadiza (A.S), Hadizar da ta tafi ta bar shi shi kadai. ‘Yar ta rungume Babanta, ta dulmiya cikin tunaninsa, idanunta cike da hawaye, hawayen farin ciki da rahma. Mamakin girman wahalar da Muhammad ya sha! Mamakin girman wahalar da Annabawa suka sha!

Ta yiwu ya ba da mamaki kwarai ga wasu mata su ga mutumin da ya haura shekara hamsin ya zama kwatankwacin misali na dan yaro a karkashin renon babarsa. Yana mai niyyar sanya haddi ga tambayoyi da zasu yadu cikin mutane, yana mai cewa da ita: “Fadima (A.S) Babar Babanta ce”. Fadimar da take a kan sha ukunta, amma sai ga ta ta koma Uwa ga mafi girman Annabawa (A.S). Da kuma fadinsa: “Fadima tsoka ce daga jikina”.

Muhammad (S.A.W) ya kalli idanun ’yarsa da suka zama suna binciken saurayin da ya sayar da ransa saboda Allah a cikinsu, amsar da ke idanunta shi ne: Ga shi can ya Baba, shi ne... wanda kafafunsa suka tsattsage, jini ya zubo ta cikinsu da sukan kaya da zafin rana da wahalar sahara, ba shi da taguwa ko rakumi. Idanun Annabi (S.A.W) suka amsa cewa: Ashe dan’uwana ne take so! Sai Muhammad (S.A.W) ya tafi don haduwa da dan’uwansa mai hijira, shi kuwa saurayi ya tashi domin haduwa da Manzon sama (S.A.W) yana mai mancewa da zoginsa da wahalhalunsa.

Annabi (S.A.W) ya sanya tafinsa mai kanshin Rahikul mahtum na Annabta ya shafa duga-dugan saurayi mai hijira kamar uwa tana shafa kan danta don ya lallasu ya yi barci.

Fararrun Abubuwa A Hanyar Hajjin Karshe Al’amari

Na Farko

A watan Zul ka’ada, a shekara ta goma hijira, Annabi (S.A.W) ya shelanta niyyar zuwa hajjin dakin Allah (S.W.T). Iskar sahara ta dauki labaran farin ciki. Sai ga kabilun Larabawa suna ta kwararowa zuwa Madina don su shiga karkashin tutar karshen Annabawa a tarihi, gomomin dubunnai suka tafi suna masu barin alkaryunsu da biranensu da hayoyin kabilunsu.

Ashirin da biyar ga wannan wata karaukoki suka nufi Makka (Wajen son kowa), Sahara ta ga taron farko mafi girma da ya kai mutum dubu dari suna masu tafiya cikin sauki zuwa ga dakin da Ibrahim da Isma’il (A.S) suka gina shi. A biyar ga Zulhajji mai alfarma, Annabi ya shiga Makka daga Babus Salam, ya yi dawafi gefen tsohon daki (Ka’aba) sau bakwai, sannan ya tafi Safa da Marwa, yana mai koyi da ayar Kur’ani “Lallai Safa da Marwa yana daga cikin alamomin (addinin) Allah”.

Ya yi sa’ayi tsakanin duwatsun biyu a motsi da yake tunatarwa game da babar Isma’il (A.S) yayin da take binciken digon ruwan sha ga danta Isma’il (A.S), ya hau dutsen Safa ya kalli Ka’aba mai girma, ya shelanta karewar bautar gunki.

“Ba abin bauta sai Allah daya, Ba shi da abokin tarayya, Mulki da godiya sun tabbata a gare shi. Shi mai iko ne a kan komai, Ba abin bauta sai Allah, ya cika alkawarinsa, ya taimaki bawansa, ya rusa runduna shi kadai”.

A Arfa Annabi (S.A.W) ya tsaya yana mai huduba, ya yada al’adun Musulunci tsakanin musulmi, yana mai albishir da bankwana na aminci. Yana mai cewa: “Ya ku mutane! Ku ji daga gare ni, ta yiwu ba zan hadu da ku bayan wannan shekarar ba a wannan wuri nawa, lallai jininku da dukiyarku haramun ne har ku hadu da Ubangijinku kamar haramcin ranarku wannan”.

Sannan ya shelantar da wurgi da kabilanci da kuma wajabta girmama mutum: “Ya ku mutane! hakika Ubangijinku daya yake, kuma babanku daya ne, dukkanku daga Adam (A.S) kuke, shi kuwa Adam daga kasa yake, Kuma mafi girmanku a wajen Allah (S.W.T) shi ne mafi tsoron ku ga Allah, balarabe ba shi da wani fifiko a kan ba’ajame sai da takawa”.

Sannan ya wuce yana mai kafa sababbin dokoki da aminci da soyayya da kaunar juna zai zama a cikinsa. Ya ce: “Duk wanda yake da amana, to ya ba da ita zuwa ga wanda ya ba shi amana. Kuma ribar jahiliyya babu shi, kuma farkon riba da zan fara saryar da shi shi ne ribar Ammina Abbas dan Abdulmudallib, kan dukiyarku yana gare ku, ba ku zalunta ba, ba a zalunce ku ba. Kuma bin jinin jahiliyya babu shi, kuma farkon jinin da zan saryar shi ne jinin Amir dan Rabi’a dan Haris dan Abdulmudallib”, yana mai kare bayaninsa da cewa: “Na isar! Allah ka shaida!”

Annabi bai manta bayanin hakika mai girma ba ta hanyar da zasu bi bayansa (S.A.W). Ya ce “Ya ku mutane! Lallai muminai ’yan uwa ne, dukiyar dan’uwa musulmi ba ta halatta gun dan’uwansa musulmi sai da yardarsa. Kada ku koma kafirai bayana sashenku yana dukan (saran) wuyan sashe. Kuma hakika ni na bar muku abin da idan kun yi riko da shi ba za ku taba bata ba bayana har abada - littafin Allah da Ahlin gidana”.

Isar Da Sako Bayyananne

Kwanakin hajji mafi girma sun wuce, yanzu lokaci ya yi tawagar mahajjata su koma gidajensu, mutanen Makka suka zama suna kallon jama’a mai yawa cike da mamaki. Ga su suna barin kasa mai tsarki inda Jibril ya sauka yana dauke da sakon karshe na sama. Manzo (S.A.W) ya bar Makka ransa cike da natsuwa da yaduwar musuluncin da ya zama addinni farko a lokaci kankani a yanki mai fadi na duniya.

Runduna ta isa yankin Juhufa a mararrabar hanya. Rana ta take a sama, zafinta ya bugi sahara, ga rayirayi ya dauki zafi. A wannan wuri mai zafi na duniyar Allah, Jibril (A.S) ya sauka da sakon karshe. “Ya kai wannan Manzo! ka isar da sakon da aka saukar maka daga Ubangijinka, idan ba ka yi ba, to ba ka isar da sakon sa ba, kuma Allah ne yake kare ka daga mutane”.

Yana bayyana daga maganar nan ta Kur’ani, wacce ta dauki matakin gargadi cewa, lallai akwai wani babban al’amari da ya wajaba a kan Annabi (S.A.W) ya isar da shi zuwa ga al’ummar da aka fare ta kafin wasu ’yan shekaru. Sai kawai aka yi wa tawagar alhazai mufaja’a da kiran Annabi da cewa a tsaya a sararin nan mai tsandauri, mai wahala da zafi, babu wata bishiya da matafiyi zai sha inuwa, babu ruwa da mai kishi zai kashe kishinsa, aka sanya alamar tambaya da mamakin al’amarin Annabta!.

Mutum ba zai iya kore abin da Manzo ( S.A.W) yake ji ba na makomar musulunci bayan wafatinsa, musamman da ya zama yana ganin karshen rayuwarsa ya zo, ba abin da ya rage masa a duniya sai wani dan taki. Musulmi suka rika tsinkayo zuwa ga Annabi (S.A.W) yana hawa tuddai da wasu sahabbansa suka jera, ya tsaya a kai yana mai kallo zuwa ga gomomin dubunnai na wadanda suka yi imani da ya shi, suka karbi sakonsa, idanunsa suna yawo da tunanin al’amari mai zuwa da ba wanda ya san sirrinsu sai Allah. Ga jawabin da Manzo (S.A.W) ya yi:

“Lallai an kira ni na amsa, kuma ni mai barin nauyayan alkawura biyu a gare ku ne: Littafin Allah da Ahlin gidana. Ku duba ku gani me za ku yi bayana (game da al’amarinsu) domin su ba za su rabu ba har sai sun riske ni a tafki”. Ali dan Abi Dalib (A.S) ya kasance yana kusa da shi, sai ya kira shi ya yi riko da hannunsa ya gabatar da shi ga duniya gaba daya. “Shin ba nine waliyyin muminai ga kawunansu ba, kuma matana iyayensu ba?” Sai ga amsa da murya mai karfi ta ko’ina.

“Haka ne ya Manzon Allah!”.

Sai Annabi (S.A.W) ya daga murya, yana mai daga hannun Ali “Duk wanda nake Shugabansa, to wannan Ali Shugabansa ne. Ya Ubangiji (S.W.T) ka taimaki wanda ya bi shi, ka kuma ki wanda ya ki shi”, Manzo ya isar da sakonsa. Sai Jibril (A.S) ya sauka yana mai shelanta bishara daga sama: “A yau ne na kammala muku addininku, na cika ni’imata a gare ku, kuma na yardar muku da Musulunci shi ne addini”. Sai farin ciki ya yadu a wannan sahara mai tsananin zafi. Hasan dan Sabit ya mike don farin ciki, yana mai nanata wadannan baitoci, yana mai godiya da yabo:

Annabinsu (S.A.W) yana kiran su ranar Gadir a Khum Ya mamakin jin Annabi! yana mai shelantawa Yana mai cewa wanene Shugaba kuma Waliyyinku Suka fada ba tare da wani musu ba Ubangijinka Shugabanmu, kuma kai Shugabanmu Babu wanda ya saba daga cikinmu a wannan rana Sai ya ce da shi: Ya Ali (A.S) tashi lallai Ni na yarda da kai Shugaba mai shiryarwa a bayana Duk wanda nake Shugabansa, wannan Shugabansa ne Ku zama masu taimako na gaskiya gare shi A nan ne ya yi addu’ar Allah ka taimaki wanda ya bi shi Ka tabar da wanda ya ki shugabancinsa

Annabi (S.A.W) a cike da idanu masu hawaye don farin ciki, ya ce da Hasan, “Ba ka gushe ba da taimakon Ruhul Kuds matukar ka taimake mu da harshenka”.

Sahabbai suka taso suna masu yi wa Ali (A.S) gaisuwa da barka suna cewa: “Barka! Barka! gare ka ya Ali. Ka zama Shugabanmu, Shugaban kuma dukkan mumini da mumina. Ranar 18 ga Zulhajji ta zama ranar idi da farin ciki, kuma hakika addini ya kammala, ni’ima ta cika”.

Al’amari Na Biyu

Manzon Allah (S.A.W) ya tsaya ranar suka a Hajjatul Wada yana mai huduba. “Amma bayan haka, ya ku mutane! Ku ji daga gare ni abin da zan bayyana muku. Ni ban sani ba ko ta yiwu in hadu da ku bayan wannan shekara tawa a matsayina wannan, lallai jininku da dukiyarku haramun ne a kanku har ku hadu da Ubangijinku kamar (haramcin) alfarmar ranarku wannan, a watanku wannan, a garinku wannan”.

“Ya ku mutane! lallai muminai ’yan uwan juna ne, bai halatta ba ga wani mutum ya ci dukiyar dan’uwansa sai da son ransa. Kada ku koma kafirai bayana, sashenku yana dukan sashe. Lallai ni na bar muku abin da in kun yi riko da shi ba za ku taba bata ba bayana har abada: Littafin Allah da Ahlin gidana…”

Aikin hajji ya kare, Annabi (S.A.W) ya koma Makka da wanda ke tare da shi, su dubu dari ko sama da haka. Kuma tarihi ya nuna cewa, ranar goma 18 ga zulhijja na shekara ta goma hijira ne.

Tawagar Alhazai tana keta fagage, rana ta take a sama, ta bude kamar tana huruwa da wuta. Tawaga na isa wani wuri kusa da Juhufa a mararrabar hanyoyi, sai ga sako ya zo wa Annabi (S.A.W) yana kan taguwarsa kuswa, Jibril (A.S) ya sauko yana mai dauke da sakon sama. Annabi ya tsaya yana mai sauraron sakon sama. “Ya kai wannan Annabi! ka isar da sakon da aka saukar maka daga Ubangijinka, in ba ka yi ba, to ba ka isar da sakonsa ba, kuma Allah ne yake kare ka daga mutane”.

Gomomin dubunnai sun tsaya suna tambayar sirrin tsayawar Annabi (S.A.W) a wannan wuri mai tsananin zafi. Sai wasu sashen sahabbai suka hanzarta suka yi wa Annabi (S.A.W) wani tudu, don yana da wasu sakonin da zai isar da ita ga gomomin dubunnan sahabbansa da al’ummu masu zuwa. Kalmomin godiya da yabo da suke fita daga bakin karshen Annabawa (S.A.W), Ali (A.S) ya kasance a tsaye kusa da mutumin da ya rene shi yana yaro, ya sanar da shi yadda zai rayu.

Annabi ya yi bayani, gomomin dubbunai suna tsinkayo a gare shi, ya ce: “Shin ba ni ne mafi cancantar muminai daga kawukansu ba”? Sai ga amsa daga gomomin dubunnan saututtuka: “E, ya Manzon Allah!!”

Ya riki hannun Ali (A.S) ya daga sama, yana mai cewa: “Duk wanda nake Shugabansa, Ali Shugabansa ne. Annabi ya daga hannunsa zuwa sama, ya ce: “Ya Ubangiji ka jibanci lamarin wanda ya taimake shi, ka tabar da wanda ya ki shi, ka taimaki wanda ya taimake shi, ka tozarta wanda ya ki taimakon sa”.

Sai Jibril (A.S) ya sauka yana mai albishir ga Muhammad (S.A.W) cewa; ya bayar da wajibinsa na isar da sako. Lokaci ya yi da zai huta, hakika addini ya cika, ni’ima ta kammala, kuma godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai. Goshinsa yana sheki, ga gumi… kwayoyin digon gumi suna zuba kamar dige-digen yayyafi, ga sakon wahayi na sama ya mamaye zukata da farin ciki maras misali, wanda ya cika duniya a tarihin dan Adam, “A yau na kammala muku addini, kuma na cika ni’imata a gare ku, na yardar muku Musulunci shi ne addini”.

Al’amari Na Uku

Kwana da kwanaki… Annabi (S.A.W) ya tafi hajji, sakon Allah ya zabi ya kasance a Gadir Khum, a kan hanyar komowa ne Jibril (A.S) ya sauka: “Ya kai wannan Manzo (S.A.W) ka isar da abin da aka saukar maka daga Ubangijinka, idan ba ka aikata ba, to ba ka isar da sakon sa ba”.

“Mutane fa”?

“Allah ne zai kare ka daga mutane”.

Ga rairayi yana kunkuna da zafin da ba za a iya daukewa ba, Annabi (S.A.W) ya tsaya, mutane dubu dari ko sama da haka suka tsaya tare da shi, ga alamomin tambaya suna bayyana a fusaku. Tarihi ya tsaya yana sauraron abin da karshen Annabawa zai ce. Ya ce: “Shin ba nine mafi cancantar musulmi fiye ga kawukansu ba? suka ce: E, ya Manzon Allah (S.A.W)”. Sai ya ce: “Duk wanda nake shugabansa, to wannan Ali (A.S) shugabansa ne… ya ku mutane za ku zo min wajen tafki, ni kuma zan tambaye ku game da nauyayan alkawura biyu”.

Suka ce:- “Menene nauyaya biyu, ya Annabin Allah (S.A.W)?”

Ya ce, “Littafin Allah da Ahlin gidana (A.S)”.

Tawagar alhazai na hajji mafi girma tana shirin komawa zuwa garuruwansu, ga mutane suna shiga addinin Allah, jama’a-jama’a, Jibril (A.S) ya sauka yana karanta wa Manzon Allah (S.A.W) ayar karshen sakon sama, “A yau ne na kammala muku addininku gare ku, na cika ni’imata a gare ku, na yardar muku da musulunci shi ne addini”. Annabi (S.A.W) ya san cewa aikinsa ya kare a bayan kasa, lokaci ya yi da zai huta sai dai…

____________________

Masdarorin Madogarar Wannan Littafin

Kur’ani mai girma

[1] - Surar Ahzab aya: 33

[2] - Sahihan Littattafai Da Masanid

Abin Da Littafin Ya Kunsa

Gabatarwar Mafassari 3

Gabatarwar Mawallafi 4

Tafarki Zuwa Gadir Khum 5

Abubuwan Da Suka Faru A Tarihin Hijira 8

Abu Na Farko 8

Makirci 9

Fansa 10

Hanya Zuwa Yasrib 11

Tafiya 12

Al’amari Na Biyu 13

Wasika Daga Kuba’a 14

Al’amari Na Uku 16

Fararrun Abubuwa A Hanyar Hajjin Karshe Al’amari 18

Na Farko 18

Isar Da Sako Bayyananne 20

Al’amari Na Biyu 22

Al’amari Na Uku 23