• Farawa
  • Na Baya
  • 43 /
  • Na Gaba
  • Karewa
  •  
  • Gurzawa HTML
  • Gurzawa Word
  • Gurzawa PDF
  • Budawa: 3497 / Gurzawa: 937
Girma Girma Girma
Shi'anci da Shi'a A Duniya

Shi'anci da Shi'a A Duniya

Mawallafi:
Hausa

SHI'ANCI DA SHI'A A DUNIYA

Wallafar: Sheikh Ja'afar al-Hadi

Fassarar: Hafiz Muhammad Sa’id

Ahlul Baiti a Kur’ani da Hadisai :

“Kawai Allahyana son ya tafiyar da dauda daga gareku ne Ahlul Baiti kuma ya tsarkake ku tsarkakewa [1]”.

“Lallaini mai bar muku nauyaya biyu ne; Littafin Allah da Ahlin gidana, ba zaku taba bata ba bayana har abada matukar kun yi riko da su [2]”.

Bukatar Sanayya

"Muka sanya ku jama'u da kabilu domin ku san juna...". Musulunci ya zo alhalin jama'u suna rarrabe masukyamar juna, masu fada da yake-yake, amma sai ya gaggauta domin warware wannan ya mayar da sanayya mahallin kiyayya da kyama, ya sanya taimakekeniya mahallin jayayya da husuma, ya sanya sadarwa tsakanin juna a mahallin yankewa, wannan kuwa duk da albarkacin koyarwa musulunci ta tauhidi da kadaita Allah ne. sai a sakamkon haka aka samu bayyanar wata al'umma mai girma da wayewa da ci gaba mai girma, kamar yadda ta kare al'ummunta daga zaluncin dukkan wani azzalumi mai danniya, wannan al'umma ta zamanto mai kwarjini da ban tsoro a idanun duk wani azzalumi mai dagawa. Wannan kuwa duk bai samu ba sai da albarkacin hadinkai da sadarwa tsakanin jama'u wadanda suka taru karkashin inuwar musulunci guda daya, duk da kuwa nau'o'in jinsinsu, da sabanin ijtihadodinsu, da yawaitar kabilunsu da sabanin al'adunsu, don haduwaa asasi da asali da farillai da wajibai ya ishesu, don haka hadin kai karfi ne, amma rarraba rauni ce.

Al'amarin ya cigaba da haka har sai da aka sake mayar da wannan soyayya ta koma kiyayya, fahimtar juna ta koma kyamar juna, sashensu suka kafirta sashe, aka yi doke-doke tsakanin juna. Sai wannan girma da izza suka kawu daga cikinsu, azzalumai suka sake yi musu hawan kawara, suka kutsa cikin gidajensu kwararo-kwararo, suka daidaice, suka warwatse, aka wawashe arzikinsu, aka wulakanta huruminsu, aka keta mutuncinsu karkashin fajirai, suka rika yin kasa-kasakullum, da rushewa da take bin su faduwa bayan faduwa. Dashan kashi a hannu a Andulus, da bukhara, da samrakand, da Daskand, da Bagdad, a da can, da kuma a yau a palasdin daAfganistan.

Idan ta yi kira baa amsa mata, idan ta nemitaimkao ba a taimaka mata, yaya kuwa haka zata faru alhalin cutarta wani abu nedaban, maganinta wani abu daban ake ba ta. Alhalin Allah ba zai yarda ba, saidai al'amurasu tafi daidai gwargwadon sababinsu, kuma karshen wannan al'umma ba zai gyaru ba sai da abin da farkonta ya gyaru da shi. A yau da muke ganin al'umma tana cikin mafimunin harin makiya a kan samuwarta da akidarta, kuma hadin kanta yana cikin mafi munin harin makiya, ta hanyar samar da matsala a rayuwarta ta addini da mazhaba da ijtihadi, kuma ga wannan harin yana kusan kai wa ga gaci. Shin bayana kan ita al'ummar ba ta yi kokarin ganin hada sawunta da karfafa alakarta. Duk da kuwa nau'in rarraba ta mazhabobi da takeda ita, amma ta yi tarayya a littafi da Sunna a matsayin madogara, kuma ta yi tarayya a tauhidi, da annabta, da imani da lahira, da salla, da azumi, da hajji, da zakka, da jihadi, da halal, da haram, da kuma son ahlin gidan Annabi (s.a.w) da kuma kin makiyansu, duk da wasu sun fi wasu. Sassabawar tana kasance ne kamar sassababawar'ya'yan yatsu na hannu daya da dukkaninsu suna tukewa ne zuwa ga gaba daya duk da kuwa tsakaninsu sun sassaba a tsayi da fadi da shakalin kira, wannan al'umma kamar gabubuwa ne na jiki da suka sassaba amma dukkaninsu sun yi tarayya wajen tafiyar da jiki domin hada samuwar dan Adam ta wata fuska tare da kuwa sabanin shakalolinta. Kuma kamanta wannan al'umma da hannu dayako kuma jiki daya nuni ne zuwa ga wannan hakika din.

Tun da can malamai ma'abota mazhabobi mabambantasun kasance suna rayuwa da jun a tare ba tare da wani jayayya ba ko taho mu gama, saudayawa sukan yi taimakekeniya tsakaninsu, har ma wani ya yi sharhin littafin wani na fikihu ne ko na akida, kuma daliban wasu suka yi karatu wajen wasu, kuma wasu su karfafi ra'ayin wasu, wasu kuma su ba wa wasu izinin ruwaya ga wasu, wasu kuma suna bayar da izinin ruwaitowa daga littafin mazhabinsa dajama'arsa ga wasu. Kuma suka yi salla bayan juna, suka yi kykkyawar sheda ga juna, suka yarda da juna, kuma suna rayuwa tare waje daya, har ma ta bayyana cewa kamar babu wani sabani tsakaninsu, duk da kuwa wani lokaci akan samu raddi na ladabi tsakaninsu, raddi na ilimi da dalili. Da yawa aka samu dalilai na tarihi mai yawa gameda wannan al'amari da taimakekeniya mai zurfi tsakaninsu, kuma malaman musulunci sun cika wayewarsa da kayan tarihi na rubuce-rubuce, kamar yadda da wannan aiki nasu suka bayar da kyakkyawan misali mai girma game da 'yancin mazhabanci, hada da cewa sun iya janyo hankalin duniya zuwa ga himmantuwa da su, kuma suka kiyaye girmansu. Mu sani ba wani abu ne mai wahala ba malamanwannan al'umma su hadu cikin sauki da nutsuwa su tattauna da ikhlasi da gaskiyar niyya game da abin da aka sassaba a cikinsa da kuma sanin dalilankowace al'umma da kuma hujjar da take daita . Kamar yadda yana da kyau kuma abu ne na hanklaikowace al'umma da jama'a ta bijiro da akidunta, da matsayin ta na tunani da fikihu a cikin 'yanci a fili, domin rashin ingancin abin da ake jifanta na tuhumomi da shubuhohi ya bayyana a fili, kuma kowa ya san bambance-bambancen da yake tsakaninsa da waninsa, kuma su san cewa abin da ya hada kan musulmi ya fi abinda yake rarraba su yawa. Wannan dan littafi mataki ne zuwa ga kaiwa gawannan gaci, kuma domin gaskiya ta bayyana ta fito a fili kowa ya san ta kamar yadda take, Allah ya sa mu dace.

Jama'ar Ja'afariyya imamiyya

1- Wannan jama'ar ita ce aka fi sani da Shi'a imamiyya ja'afariyya, jama'a ce mai yawa a wannan zamani namu, kuma ana kaddara adadinisu da kusan kwata na yawan al'ummar musulmi gaba daya, kuma asalinsu a tarihi ya taso ne daga ranar saukar fadin Allah madaukaki a surar bayyina: wadannan da suka yi imani kuma da aiki na gari, wadannan su ne mafifitanal'umma[ 3]. Sai Manzo (S.A.W) yadora hannunsa a kan kafadar Ali dan Abi Dalib (A.S) kuma sahabbai suna wajen, ya ce: Ya Ali kai da shi'arka ku ne mafifitan al'umma. (Ana iya duba misali: a tafirin dabari –jami'ul bayan- da durrul Mansurna suyudi bashafi'e, da tafsirul ma'ani na Alusi bagdadi bashafi'e game da tafsirin wannan aya). Daganan ne aka kira wannan al'umma da Shi'awacce ake danganta ta zuwa ga imam Ja'afar assadik (A.S) saboda suna bin fikihunsa.

Bayani Na Biyu

2- Ana samun wannan jama'a da yawa a kasashe kamar Iran da Irak, da Pakistan, da Afganistan, da Indiya, kuma sun yadu da yawa a kasashen Kogin farisa, da Turkiyya, da Siriya, da Labanon, da Rasha da kasashen da suka rabe daga gare ta. Kuma suna yaduwa a kasashen turai kamar Ingila, da Jamane, da Paransa, da Amurka, da Yankin Afrika, da kasashen Asiya ta gabas, suna da masallatai da cibiyoyin ilimi da wayewa ta zamantakewar al'umma.

Bayani Na Uku

3- Su jama'a ce daga jinsina daban-daban daluggogi, da launuka, kuma suna rayuwa tare da 'yan'uwansu sauran musulmi daga sauran jama'u na sauran mazhabobi cikin aminci da soyayya, da taimakekeniya a dukkan fagagen rayuwa da gaskiya da ikhlasi, dogaro da fadin ubangiji madaukaki: Hakika muminai 'yan'uwan juna ne[4]. Da fadinsa: Ku yi taimakekeniya a kan biyayya datakawa[ 5]. Da kuma riko da fadinsa mai girma (S.A.W): Musulmi hannu daya ne a kanwaninsu[ 6]. Da fadinsa: Muminai kamar jiki dayane[ 7].

Bayani Na Hudu

4- Suna da ayyuka muhimmai da suka yi a tarihimasu girma na kariya ga musulunci, da kuma al'ummar musulmi, kamar yadda sun yi dauloli da hukumomi da suka yi hidima ga ci gaban musulunci, da kuma malamai masu ilimi da suka bayar da gudummuwa wajen wadatar da littattafan musulunci da wallafe-wallafe masu yawa da suka kai daruruwan dubunnai kanana da manya a fagagen tafsirin Kur'ani, da hadisi, da akida, da fikihu, da usul, da akhlak, da rijal, da palsafa, da wa'azi, da siyasa, da zamantakewa, da lugga, da magani, da adabi, da pizik, da kimiyya, da lissafi, da ilimin falaki, da sauran ilimomi na rayuwa. Kuma suna da muhimmiyar rawar da suka taka ta asasi wajen assasa ilimomi daban-daban: (A duba, littattafan: Ta'asisus Shi'a li ulumil Islam, da zari'aila tasanifis Shi'a na Aga buzurg mai mujalladi 29, da kashaful zunun na Afande, da mu'ujamul mu'allfin na Kahala, da A'ayanus Shi'ana sayyid muhsir amin amuli da sauransu).

Bayani Na Biyar

5- Sun yi imani da Allah daya makadaiciwanda bai haifa ba, kuma ba a haife shi ba, kuma wani bai kasance tamka da tsara gareshi ba.Suna korewa Allah jiki da jiha, da wuri, da zamani, da canjawa, da motsi, da hawa da sauka, da dukkan abin da bai dace da ubangiji ba madaukaki. Kuma suna yin imani da cewa babu wani abin bautasai shi, kuma hukunci da shar'antawa duka suna hannunsa ne shi kadai ba tare da waninsa ba, kuma shirka da dukkan nau'o'inta karamace ko babba, ta boye ko ta sarari duka zalunci ne mai girma kuma zunubi ne da ba a yafewa.Kuma dukkan wannan sun dogara ne da hankali maihujja da aka karfafe ta da littafin Allah mai girma, da Sunna madaukakiya. Basa karbar hadisan isra'ilanci (na attaura dainjila) da majusanci da suka dauka Allah yana da jiki, kuma suke kamanta shi dabayinsa.Ko kuma suke danganta zalunci zuwa ga Allah madaukaki.Ko kuma suke danganta aikata mummuna zuwa ga annabawa tsarkaka ma'asumai.

Bayani Na Shida

6-Sun yi imani cewa Allah adali mai hikima, yahalicci halittarsa da adalci da hikima, bai yi halittar wani abu don wasa ba, sandararre ne, ko tsiro, dabba ne ko mutum, sama yake ko kasa, domin wasa ya koru ga Allah wanda yake mai dukkan kamala korarre daga dukkan tawaya da aibi.

Bayani Na Bakwai

7- Sun yi imani cewa Allah ya aiko manzanni daadalcinsa da hikimarsa zuwa ga mutane gaba daya, tun daga farkon rayuwarsu a duniya, annabawa da manzanni da suka siffantu da isma da ilimi mai yalwa, da Allah ya yi musu baiwarsa ta hanyar wahayi, don shiryar da dan Adam da kuma taimaka masa domin kaiwa zuwa ga kamalar da aka zana musu. Da kuma shiryar da su zuwa ga biyayya da zata kai su zuwa ga aljanna, take kumasamar musu da dacewa zuwa ga rahamar Allah da yardarsa. Mafi shaharar wadannan sun hada da annabawa da manzanni kamar: Adam, da Nuhu, da Ibrahim, da Isa, da Musa, da sauran wadannda aka ambaci sunansu da halayensu a cikin Kur'ani mai girma da Sunna madaukakiya.

Bayani Na Takwas

8- Sun yi imani da cewawanda ya bi Allah yagudanar da umarninsa, ya tafiyar da dokokinsa a fagagen rayuwa to ya tsira ya rabauta, ya kuma cancanci yabo da lada, koda kuwa bawa ne baki. Kuma dukkanwanda ya saba wa Allah (S.W.T) ya yi kunnen uwar shegu da umarninsa to ya tabe ya halaka ya kuma cancanci zargi da azaba koda kuwa bakuraishe ne sharifi kamaryadda ya zo a hadisin Annabi madaukaki. Kuma sun yi imani da cewa inda za a yi sakamakoda ladako azaba a ranar lahira ne wanda a cikinta akwai hisabi, da ma'auni, da aljanna, da wuta, wannan kuwa bayan wucewar kabari da barzahu. Amma tanasuhiwanda masu musun ranar kiyama suka tafi a kansa, to Shi'a suna musunsa domin ya lizimta kayarta Kur'ani mai girma da Sunna madaukakiya.

Bayani Na Tara

9-Sun yi imani da cewa karshen annabawa da manznnai kuma cikamakonsu mafificinsu, shi ne Muhammad manzon Allah (S.A.W) dan Abdullah, dan Abdul Mudallibi (A.S) wannan da Allah ya kare shi daga sabo da kurakurai. Ya kuma kare shi daga manyan sabo da kananansu, kafin annabta da bayanta,a al'amuran isar da sako ko a waninsu. Ya kuma saukar masa da Kur'ani mai girma domin ya kasance littafin tsarin dokoki ga rayuwar dan Adam har abada, sai Manzo (S.A.W) ya isar da sako, yabayar da amana da gaskiya daikhlasi, ya kuma sadaukar da komai. Shi'a suna da gomomin littattafai da suka wallafa game da tarihin rayuwar Annabi (S.A.W) da halayensa da mu'ujizozinsa. Komawa littafin Irshad na Sheikh Mufid, da kuma A'alamul wara, da a'alamul huda na Dabrasi, da kuma biharul anwar na Majlisi, da kuma littafin arrasulul Musdapha na sayyid Muhsin khatami.

Bayani Na Goma

10- Shi'a sun yi imani da cewa Kur'ani mai girmada Allah ya saukar ga annabinsa Muhammad (S.A.W) ta hanyar jibrilu (A.S) kuma wasu daga sahabbai masu girma suka rubuta shi, wanda imam Ali (A.S) yana gabansu a lokacin Annabi (S.A.W) kuma a karkashin kulawar Annabi da lurarsa garesu, da shiryarwarsa da kuma hardace shi a zuciya (da ka), da kuma kiyaye rubuta haruffansa da kalmominsa da ayoyinsa da surorinsa da kare su da kiyaye su, wanda suka nakalto shi kakanni da iyaye har zuwa yau, wanda shi ne musulmi suke karantawa gaba dayansu a cikin dare da rana, ba tare da wani dadi ba ko ragi, ko canji ko jirkita. Kuma Shi'a sun yi rubuce-rubuce masu yawa game da wannan al'amari, sai ka komawa littattafansu matsawaita da magajerta. (Komawa littafin al'Kur'ani na Zanjani, da tamhidul Kur'ani na Hadi ma'arifa da wasunsu).

Bayani Na Sha Daya

11- Shi'a sun yi imani cewa Muhammad (S.A.W)Manzon Allah ne kuma bawansa ne, wanda yayin da ajalinsa ya kusanto ya sanya Ali (A.S) halifansa a bayansa, kuma jagoran musulmi gaba daya bayansa domin ya jagorance su a siyasance, kuma ya shiryar da su a tunani, ya waraware matsalolinsu, ya ci gaba da tarbiyantar da su, da tsarkake su, wannan kuwa duk da umarnin Allah ne (S.W.T) a wani wuri da ake kira Ghadir Khum, a karshen shekarun rayuwarsa kuma a hajjinsa na karshe, a cikin jama'ar musulmi masu yawa wadanda suka yi hajji tare da shi, wadanda a wasu ruwayoyi ya zo cewa adadinsuya kai kusan mutum dubu dari. Kuma ayoyi masu yawa sun sauka game da wannanal'mari mai girma. Kamar yadda Annabi ya nemi mutane su yi mubaya'aga imam Ali (A.S) su sanya hannuwansu akan hannunsa, sai suka yi masa bai'a kuma na gaba-gabansu su ne manyan sahabbai mutanen Makka da madina da shahararrunsu. (Duba littafin Ghadirna allama Amini, da ya cicciro daga littattafai daban-daban na tafsiri da tarihi)

Bayani Na Sha Biyu

Bayani Na 12- Shi'a suna imani da cewa imami (jagora) bayan Manzo (S.A.W) tun da shi ma dukkan abin da ya wajaba ga Annabi (S.A.W) shi ma ya wajaba akansa (A.S) kamar al'amarin jagorancin al'umma da shiryar da ita, da tarbiyynantarwa da bayanin hukunce-hukunce, da warware matsalolin tunani masu wahalar warwara, da kuma maganin mas'alolin zamantakewa masu muhimmanci. Don haka dole ne ya kasance mutum ne da mutane suke samun nutsuwa da shi, domin ya jagoranci al'umma zuwa ga tudun tsira, kuma yana tarayya da Annabi a siffofinsa kamar isma, da ilimi, domin yana tarayya da shi a dukkan abin da ya shafi cancanta da daukar nauyi, in ban da annabta ka karbar wahayi, domin annabci an cika shi da cikamakon annabawa Muhammad (S.A.W), wanda yake cikonannabawa da manzanni (A.S). Kuma addininsa shi ne cikamakon dukkan addininAllah (S.W.T), shari'arsaita ce karshen shari'o'i, littafinsa karshen littattafai, kuma babu wani Annabi bayansa, kuma babu wani addini bayan nasa, babu wata shari'a bayan shari'arsa.(Shi'a suna da wallafe-wallafe a wannan fage masu yawan gaske).

Bayani Na Sha uku

13- Shi'a sun yi imani da cewa bukatuwar al'ummazuwa ga mai jagoranci mai shiryarwa kuma shugaba ma'asumi ta sanya kada al'amarin ya tsayu da kafa imam Ali (A.S) halifansa kawai, dole ne al'amarin ya ci gaba har zuwa mudda mai tsawo har a samu kafuwar musulunci kafuwa mai karfi kuma a kiyaye asasin shari'a, kuma da kare dokokinta daga abubuwan hadari da suke kawo mata hari, kuma suke barazana gareta kamar yadda ta yi barazana ga dukkan wata akida da imani da Allah da dukkan tsarin ubangiji madaukaki. Kuma domin wadannan jagororina Allah su tsayu da matsayin bayar da kyawawan misalai a lokuta mabambanta game da ayyukansu a halaye mabambanta da suka dace dadukkan halayen da al'ummar musulmi zata shige su a nan gaba.

Bayani Na Sha Hudu

14- Shi'a suna imani da cewa Muhammad danAbdullah (S.A.W) don wannan dalili ne da kuma hikima madaukakiya ya kafa imamai goma sha daya bayan imam Ali (A.S) a matsayin jagorori a bayansa. Wadanda su ne imamai goma sha biyu har da imam Ali (A.S) da aka yi nuni da su da kabilarsu ta kuraish a sahihul Buhari da Muslim da lafuzza mabambanta: Yayin da suka ruwaito daga manzon Allah (S.A.W) cewa: Wannan addini ba zai gushe ba yana mai tsayuwa da kafafunsa yana mai daukaka da buwaya har sai an samu shugabanni/halifofi goma sha biyu daga cikinku dukkaninsu daga kuraishawa (Ko bani hashim, kamar yanda ya zo a wasu ruwayoyin wasu littattafai, domin kuwa sunayensu sun zo a wasu littattafan a babin falaloli da darajoji da wakoki daAdabobi).Hadisan cikin Buhari da musulim duk da su ba su kunshi sunayensu ba, amma sun yi daidai da adadin imaman Shi'a goma sha biyu, wato Ali (A.S) da sha daya daga zuriyarsa kamar yadda Shi'a suka yi imani da hakan. Kuma ba yadda zaa iya fassara wannan hadisi sai da abin da ya yi daidai da zancen da Shi'a suka tafi a kai. (Komawa littafin khulafa'unnabi, na ha'iri bahrani).

Bayani Na Sha Biyar

15- Shi'a ja'afariyya sun yi imani da cewa imamai kuma halifofin manzon Allah da Allah ya yi umarni da binsu guda goma shabiyu ne, wadanda su ne: Adadi AI- kunya Suna Lakabi haihuwa Rasuwa 1 Abul Hasan Aliyyu Murtadha 23 K.H 40 H 2 Abu Muhammad Hasan Mujtaba 2 H 50 H 3 Abu Abdullah Husain Shahid 3 H 61 H 4 Abul Hasan Ali Sajjad 38 H 95 H 5 Abu Ja'afar Muhammad Bakir 57 H 114 H 6 Abu Abdullah Ja'afar Sadik 83 H 148 H 7 Abul Hasan Musa Kazim 128 H 183 H 8 Abul Hasan Ali Ridha 148 H 203 H 9 Abu Ja'afar Muhammad Jawad 195 H 220 H 10 Abul Hasan Ali Hadi 212 H 254 H 11 Abu Muhammad Hasan Askari 232 H 260 H 12 Abul Kasim Muhammad Mahadi 256 H Araye

Kuma wadannan su ne Ahlul Baiti da Manzo Muhammad (S.A.W) ya kafa su da umarnin Allah a matsayin jagororin al'ummar musulmi saboda ismarsu da tsarkinsu daga sabo da zunubi, da kuma iliminsu mai fadi wanda suka gaje shi daga kakansu, kuma Allah ya yi umarni da sonsu da biyayya garesu yayin da yake cewa, "Ka ce: Ba na tambayarku wani lada a kansa sai dai soyayya ga makusanta"[8]. Kuma yace : "Ya ku wadanda kuka yi imani ku ji tsoron Allah ku kasance tare da masu gaskiya"[9]. (Ka komawa littattafan hadisai da tafsirai da falaloli da darajajin manyan mutane kamar Ahlul Baiti (A.S) da sahabbai daga littattafan Sunna da Shi'a).

Bayani Na Sha Shida

16-Shi'a sun yi imani da cewa wadannan imamai tsarkakatarihi bai taba kawo musu wani zamewa ba ta dugadugai, ko wani sabo ko saudaya a zance ko a aiki, kuma sun yi hidima mai girma ga al'ummar musulmi da iliminsu, suka cika ta da sani mai zurfi, da sahihiyar mahanga ta akida, da shari'a da kyawana halaye, da ladubba, da tafsiri, da tarihi. Kamar yadda suka tarbiyyantar da jama'a mai yawa mata da maza gwaraza zababbuna musamman wadanda kowa ya yi furuci da falalarsu da iliminsu, da kyawawan dabi'unsu. Kuma Shi'a suna ganin cewa duk da an nesantar da su wadannan imamai daga fagen siyasa da jagoranci saidai su sun bayar da gudummuwarsu da sauke nauyinsu na bayar da ilimi da fikira da nazari ingantacce, yayin da suka kare akidar musulunci da shari'arsa daga hadari. Da al'ummar musulmi ta ba su dama sun tafiyar da al'amuransu na siyasa da Allah (S.W.T) da Manzo (S.A.W) suka ba su, da al'umma ta samu sa'adarta da daukakarta, da girmanta cikakke, da ta wanzu mai hadin kai mai karfi daya da ba ta da rarraba, babu sabani, babu jayayya, ba fada, ba kashe-kashe, babu daukar kaskanci. (Duba littafinnan na imam S adik (A.S) da mazhabobi huduna Haidar mai mujalladi uku).

Bayani Na Sha Bakwai

17- Shi'a sun yi imani da cewa saboda wadannan dalilai na hankali da ruwya masu yawa da aka ambata a littattafan akida, ya zama waji bi a yi biyayya ga Ahlul Baiti (A.S) da kuma lizimtar tafarkinsu domin ita ce hanyar da manzon Allah (S.A.W) ya zana wa al'umma, kuma ya yi wasiyya da bin ta da lizimtar ta a cikin hadisin sakalain, yayin da yake cewa: "Ni na bar muku nauyaya biyu: littafin Allah da ahliln gidana, matukar kun yi riko da su, ba zaku taba bata ba har abada", Kamar yadda Muslim a littafin da kuma gomomin masu ruwaya sun rawaito wannan hadisi. "(Ka komawa littafin Risalatuns sakalain na Bash'nawi, wacce jami'ar azhar ta gaskata da ita shekarakusan talatin da suka gabata). Kuma sanya halifa da yin wasiyya al'amari ne da ya shahara acikin rayuwar annabawa (A.S) da suka rigaya, (Ka duba isbatul wasiyyana mas'udi, da littattafan hadisai, da tarihi, da tafsiri na jama'a biyu).

Bayani Na Sha Takwas

18- Shi'a sun yi imani da cewa abin da ya haukan al'umma shi ne ta zauna ta duba wadannan al'amura da idon basira ta hanyar tattaunawa da juna, tare da nisantar duk wani zagi da cin mutunci da tuhuma da kage a kan juna. Kuma abin da ya hau kan malamai da masu tunanin al'umma na kowace jama'a da mazhaba da kungiya ta musulmi shi ne; su taru da kulla tarurruka su yi bincikenwannan al'amari da tsarkin zuciya da ikhlasi, da 'yan'uwantaka bisa dalili da sanin menene 'yan'uwansu Shi'a suke cewa, kuma menene dalilinsu a littafinKur'ani da sunnar Annabi (S.A.W), da kuma hankli da tarihi da siyasa da zamantakewa da suka gabata tun lokacin Annabi (S.A.W).

Bayani Na Sha Tara

19- Shi'a sun yi imani da cewa sahabbai da dukkan wadandasuke tare da Annabi sun bayar da tasu gudummuwa mai girma mazansu da matansu, kuma sun yi hidima ga musulunci, sun sadaukar da komai wajen ganin yada shi, kuma musulmi dole ne su girmama su, su nema musu yardar Allah da gafararsa. Sai dai dukkansu ba daidai suke ba, akwai wadanda ayyukansu na gari ne wasu kuma ba na gari ba wadanda ba su fi karfin kawo su gaban nakadi da musanta su ba, wannan kuwa domin su mutane ne kamar saura da suke iya yin daidai ko kuma su saba, kuma tarihi ya ambaci cewa wasunsu sun kaucewa hanyar manzon Allah (S.A.W) hatta a zamaninsa, kai Kur'ani mai girma ya furta hakan ma a wasu daga surorinsa kamar surar munafikun da ahzab da hujurat, da tahrim dafath, da Muhammad, da tauba. Sukan wasu munanan ayyuka na wasunsu ba yana nufin kafirtasu ba, domin ma'aunin imani da kafirci sananne ne bayyananne, domin ma'aunin hakan shi ne kore tauhidi da sakon manzon rahama (S.A.W) ko yarda da su, ko kuma kore wani al'amari na larurar addini kamar wajebcin salla, da azumi dahajji, da zakka, da haramcin giya da caca, da sauransu. Sai dai, wajibi ne kame harshe ga zagi ko cin mutuncin wanimusulmi wannan kuwa ba bambanci ko sahabi ne ko ba shi ba, haka nan kuma kare alkalami daga hakan, domin zagi ba ya daga cikin sunnar ma'aiki cikamakon annabawa Muhammad (S.A.W). Kuma tare da hakan zamu ga cewa mafi yawan sahabbai salihan bayin Allah ne, masu gyara da suka cancanci girmamawa da jajintawa. Mu sanineman sanin halayensu domin sanin adili amintacce dawanda ba hakan yake ba, al'amari da ya faru domin sanin waye hadisansa za a karba waye kuma ba za a karba daga gareshi ba. Wannan kuwa ba domin komai ba sai domin kare sunnar Annabi daga cakuda tsakanin karya da gaskiya ko sanin kage da aka yi wa Manzo (S.A.W) wanda tun a zamaninsa wasu daga cikinsu suka fara yi masa karya da kage har ya tsawatar kan hakan. Tare da sanin cewa yi masa karyazai dadu ya yawaita bayan rayuwarsa. Don haka ne ma malamai masu yawa kamar suyudi da ibn jauzida sauransuna malaman duka jama'u biyu suka yi ta'lifin littattafai domin gano hadisan da suke tabbas daga Annabi (S.A.W) suke da kuma wanda kage aka yi masa.

Bayani Na Ashirin

20-Shi'a sun yi imani da cewa akwai imami mahadi (A.S)wanda ake sauraronsa daga zuriyar Fadima (A.S) saboda ruwayoyi masu yawa daga Annabi (S.A.W). Kuma shina tara ne daga jeren salsalar 'ya'yan imam Husaini (A.S). Kuma tunda na takwas shi ne imam Hasan Askari (A.S) wanda yarasu a shekarar hijira 260, kuma ba shi da wani da sai dansa mai suna Muhammad wanda ake yi wa kinaya da Abul kasim (A.S) kuma da yawa daga amintattun mutane sun gan shi, suka kuma bayar da labari game da haihuwarsa da siffofinsa da jagorancinsa da kuma wasiyya da shi ta bangaren babansa, kuma ya buya daga ganin idanuwa kusan shekaru biyar daga haihuwarsa yayin da makiya suka so kashe shi. Don haka ne Allah ya boye shi saboda yazama ajiya domin kafa hukumar adalici ta musulunci mai game dukkan duniya a karshe zamani, domin tsarkake kasadaga zalunci da fasadi, bayan ta cika da su. Ba mamaki ga tsawon rayuwarsa, domin Kur'ani mai girma yaambaci Isa Masihu (A.S) cewa rayayye ne har yanzu duk da kuwa ya wuce shekaru 2004, kuma Nuhu (A.S) ya rayu a cikin mutanensa shekaru dubu daya ba hamsinyana kiran su zuwa ga Allah, ga kuma Khidr (A.S)yana raye har yanzu. Allah mai iko ne a kan komai, kuma nufin mai zartuwa ba maiiya hana shi ko tsayar da shi, shin ubangiji mai daukaka bai fadi ba game da Annabi Yunus (A.S) yana mai cewa: "Ba domin ya kasance cikin masu tasbihi ba * Da ya zauna a cikinsa har ranar tashin kiyama"[10]. Kuma da yawa daga malaman ahlussunna sun yi furuci dasamuwar imam mahadi (A.S) a raye, suka ambaci sunan iyayensa (A.S) kamar:

a- Abdul Mumin Shablanji, Bashafi'e a littafinsana Nurulabsar.

b- Ibn Hajar Alhaisami Almakki, Bashafi'e a litafinsa naSawa'ikul muhrika, yayin da ya ambace shi da Abul kasim, kuma babansa ya rasuyana da shekaru biyar, sai dai Allah ya ba shi hikima, kuma ana kiransa da Al'ka'imAl'muntazar.

c- Al'kanduzi Bahanife, Albalkhi, a littafinsana Yanabi'ulmawadda tun wanda aka buga a Turkiyya lokacin halifancin usmaniyya.

d - Assayyid Muhamma Sadik Hasan Alkanuji Albukhari, alittafinsa na Al'iza'a limakana wamayakunu baina yadai assa'a.

Da sauran malamai magabata kamar: Dakta Mustapaha Rafi'i, alittafinsa islamuna, ya yi maganar haihuwarsa a ciki dalla-dalla.

Bayani Na Ashirin Da Daya

21- Shi'a suna salla, suna azumi, suna zakka, suna bayar dahumusin dukiyarsu, suna yin hajji, a Makka, suna yin ayyukan umra da hajji na farkon a matsayin sauke wajibi, amma sama da hakan mustahabbi ne, suna umarni da kyakkyawa suna hani daga mummuna, suna bin masoyan Allah (S.W.T) da manzonsa (S.A.W), suna kin makiyansu, suna jihadi a tafarkin Allah ga dukkan mai yakarsu, ko kuma mai zagon kasa ga al'ummar musulmi gaba daya, suna aiwatar da dukkan ayyukansu daidai da hukuncin shari'a kamar: cinikayya, da haya, da aure, dasaki, da gado, da shayarwa, da hijabi, da tarbiyya. Suna masu rikon wadannan hukunce-hukunce daga ijtihadi, da malamai suke yinsa daga littafin Allah (S.W.T) da sunnar manzonsa (S.A.W), da hankali, da haduwar malamai.

Bayani Na Ashirin Da Biyu

22- Shi'a suna ganin dukkan farilla ta kullum mai lokaciayyananne guda biyarce wato: (asuba, azahar, la'asar, magariba, issah). Kuma suna ganin abin da ya fi shi ne a yi kowace sallah a lokacin da ya kebanta daita wato lokuta guda biyar. Sai dai suna hada azahar da la'asar, da kuma magariba da issha, domin Manzo (S.A.W) ya hada shi ma ba tare da wani uzuri ba kamar na ruwan sama, ko rashin lafiya, ko safara, kamar yadda ya zo a littattafai kamar sahih Muslim, ba domin komai ba sai don ya saukaka kan al'ummarsa, wannan kuwa al'amari ne na yau da kullum a wannan zamani namu.

Bayani Na Ashirin Da Uku

23- Shi'a suna kiran salla kamar sauran musulmi sai daibayan hayya alal falah, suna kara hayya ala khairil amal, kamar yadda yake a lokacin Manzo, sai dai umar dan khaddabi ya cire ta, domin yana ganin fadin hakan zai sanya musulmi su bar zuwa jihadi su shagaltu da salla don haka ya cire ta. (Kamar yadda malam Kushji al'ash'ari ya kawo a littafinsa: sharhin tajridul I'itikad, haka ma kindi a littafinsa, da muttaki: a kanzul ummal, dasauransu). Kuma umar dan khaddabi yakara assalatu khairun minannaumi azamaninsa abin da babu shi a asalin kiran salla, (Duba littattafan hadisai da tarihi). Shi'a suna ganin tunda ibada dole ta kasance kamar yadda maishari'a ya zo da ita, don haka ne duk wani abu dole ya kasance kamar yadda ya zo da shi, kuma duk wani kari kan hakan, kari ne kuma bidi'a ce da za a mayar da ita ga mai ita… don haka ne ya kasance ba sa yarda da dadi ko ragi a ibadasai abin da mai shari'a ya zo da shi, ba ra'ayi na waninsa ba. Amma abin da Shi'a suke karawa na kiran salla da suke cewa:Ash'hadu anna aliyyan waliyyul Lah! Bayan sun kawo ash'hadu anna muhammadar rasulul Lah!, Wannan saboda wata ruwaya ce da suke da ita da take cewa babuwani waje da aka ambaci "Muhammadur rasululLah!"Ko kuma aka rubuta hakan a bakin kofar aljanna, sai an raba masa, "Aliyyun waliyyulLah". Wannan kuwayana nuna Shi'a ba sa furuci da annabtar imam Ali (A.S) balle kuma batun ubangijintakarsa, kamar yadda masu yi musu kage da sharri sukefada. Wal'iyazu bilLah!. Don haka ne Shi'a suke fadin wannan kalma domin ladan abinda ya zo a wannan ruwaya, amma ba domin tana wani bangare na kiran salla ba, domin idan wani ya fadi kalmar Ash'hadu anna aliyyan waliyyul Lah!a cikin kiran salla da nufin ita wani bangare ce ta kiran salla to ya zo da bidi'a, amma tunda ana fadarta ba da nufin ita wani bangare ce ta kiran salla ba, to ba bidi'a ba ce. Don haka, ba za a iya kiranta abin da ba shi da asali dagashari'a ba, kuma ba bidi'a bace .

Bayani Na Ashirin Da Hudu

24- Shi'a suna yin salla a kan turbaya ko fakon kasa ko kantabarmar kaba, ko wani dutse da dukkan abin da yake da asali daga kasa da tsurranta, banda shimfida da yadi da abin ci, da kayan ado, saboda ruwayoyimasu yawa da suka zo daga littattafan jama'a biyu cewa Manzo (S.A.W) ya kasance al'adarsa ita ce yin sujada a kan turbaya ko dandariyar kasa, kuma yana umartar amusulmi da hakan, don haka ne ma wata rana da Bilal ya yi salla a kan nadinrawaninsa domin gudun zafin rana mai kuna, sai Manzo (S.A.W) ya zo ya kawar da rawanin nasa daga goshinsa ya ce: Ka sanya goshinka a kasa Ya kai Bilal". Kuma ya fadawa Suhaib, da Rabah, irin hakan yayin da yakecewa: Ka sanya fuskarka a turbaya ya Suhaib, Ka sanya fuskarka a turbaya ya Rabah (Duba Buhari, Kanzul Ummal, Almusannaf, da Assujudu alal ard na KashifulGida'). Ya zo a cikin littafin Buhari Manzo (S.A.W) Yana cewa: "An sanya mini kasa wajen sujada, kuma tsarki". Kuma sujada akan turbaya da dora goshi kan kasagun sujada shi ya fi dacewa ga sujada a gaban Allah (S.W.T) (S.A.W) domin shi ya fi sanyawa ga tsoron Allah kuma ya fi kusa da kaskan da da kai gareshi abin bautarsa (S.W.T). Kuma a lokaci gudayana tuna wa mutum da makomarsa da asalinsa. Shin ubangiji madaukaki baice : "Daga gareta ne muka halitta ku kuma a cikinta ne zamu mayar da ku, kuma daga gareta ne zamu futar da ku wani lokacin ba"?![11]. Ku sani sujadayana nuna matukar kaskantar dakai ne, da ba zai iya tabbata ba a kan shimfida da zani, da sauran kayan ado masu tsada.Tana iya tabbata ne da sanya mafi darajar waje a jikin mutum wato goshinsa a mafi kaskancin abu wato kasa. (Duba littafin alyawakit wal jawahirna sha'arani al'ansari almisiri daga malaman karni na goma). Sai dai, ba makawa turbayar ta kasance maitsarki, shi ya sa Shi'a suke daukar wani guntu na turbaya, wanda yake an kwaba shi an mulmula shi domin su tabbatar da cewa suna sujada kan abu mai tsarki ne. Wani lokaci saudayawa kasar takan kasance an ciro ta ne daga wani waje mai tsarki kamar kasar karbala, wacce imam Husaini (A.S) jikan manzon Allah (S.A.W) ya yi shahada a cikinta, kamar yadda a wancan zamanin wasu sahabbai sun kasance suna daukar tsakuwowin kasar Makka domin su rika sujada a kanta a safararsu, domin neman albarka. (Duba littafin musannafna San'ani). Sai dai Shi'a ba su dage a kan haka ba, ba sulizimci hakan ba har abada, wani loaci suna sujada a kan kowa ce tsakuwa ce mai tsarki mai tsafta, kamar dakalin masallacin annabi da na masallacin ka'aba batare da wani kokwanto ba. Kamar yadda basa sanya hannunsu na dama a kanhagu yayin salla, domin annabi (S.A.W) bai aikta hakan ba. Kuma wannan bai tabbata ba da nassi sahihi, shi yasa ma malikiyya ba sa yin sa. (Duba Buhari, Muslim, sunan baihaki, da bidayatul mujtahidina Ibn Rushdi al'kurdabialmaliki).

Bayani Na Ashirin Da Biyar

25- Shi'a suna yin alwala ta hanyar wanke hannayensu daga gwiwar hannu zuwa 'yan yatsun hannu, kuma ba sa akasin hakan, domin sun dauki yadda ake yin alwala ne daga imamai jagororin Ahlul Baiti (A.S) wadanda su kuma sun koya daga manzon Allah ne (S.A.W) kuma su suka fi waninsu sanin me kakansu yake yi, kuma ya kasance yana yin haka ne. Kuma sun fassara kalmar "ila" da "tare da" ne[12], kamar yadda shafi'i assagirya kawo a littafinsa Nihayatul muhtaj. Hakanan suna shafa kafafunsu dakawukansu ba sa wanke wa saboda wannan dalilin da muka ambata, kuma dan Abbas yana cewa: Alwala wankewa biyu ne, da shafawa biyu, wato abin wanke wa biyu da abin shafawa biyu ne, (koma wa sunan da masanid, da tafsirin fakhrur razi, gun tafsirinsa ga ayar alwala).

Bayani Na Ashirin Da Shida

26-Shi'a suna tafiya akan cewa aurenmutu'a halal ne, saboda nassin Kur'ani mai girma da ya ce: "Abin da kuka ji na dadi daga garesu da shi, to ku ba su ladansu"[13]. Kuma saboda musulmi sun yi a lokacin manzon Allah (S.A.W) har zuwarabin lokacin halifancin umar. Kuma shi aure nena shari'a, da ya yi tarayya da aure na da'imi a:

a- mace ta kasance ba ta wani aure, kumata yi siga shi kuma mijin ya karba.

b-kuma wajibi ne a ba wa mace ladanta,kamar yadda Kur'ani yak ira shi da wannan sunan, abin da ake cewa da shi sadakia aure da'imi.

c-kuma dole ne mace ta yi idda bayanrabuwarsu da mijin.

d-kuma dole ne bayan wajebcin idda, daya zama na mijin ne idan an samu haihuwa, kuma dole mijin ya zama shi kadai ne,ba sama da hakan ba.

e-ana gado tsakanin uwayen da kumatsakanin yaron da iyayen nasa akasi da akasi.

Wannan aure ya bambanta da aure da'imi awajen cewa shiyana da mudda da aka ayyana karewarsa, da kuma rashin wajebcin ciyar da mace, da rashin wajebcin raba kwana tare, da rashin gado tsakanin ma'autan biyu, da rashin bukatar saki idan mudda ta kare. Domin karewar mudda shi kadai ya isa yazama yankewa da rabuwa, ko kuma idan mijin ya yafe mataragowar muddar. Hikimar shar'anta wanna aureita ce: domin biyan bukatun namiji da mace na sha'awa ga wanda ba zai iya daukar nauyin jigilar yin aure na da'imi ba, ko kuma wanda/wacce ya/ta rasa matarsa/mijinta, saboda wafati, ko wani dalilin, tare da nufin rayuwa cikin mutunci da daukakaba rayuwar zina ba. Mutu'a wani abu ne da yakena farko wajenwarware matsalar zamantakewa mai hadari da takan iya kai al'umma zuwa ga fasadi mai muni na zina, ko madigo, da fitar da mani ta hanyar haram. Ana amfani da wanna aure saboda nufinaure na shari'a da yaka iya hana kaiwa ga haram, da zina, ko istimna'i, ko amfani da wasu hanyoyi na haram domin kashe sha'awa, ga maras aure, ko kuma wanda ba ya iya hakura da mace daya, ko kuma ba zai iya aure ba sam, sakamakon kuncin rayuwa a lokaci guda kuma ba ya son fadawa cikin haram. Ta kowane hali dai, halaccin auren mutu'aya dogara da littafi da Sunna ne, kuma sahabbai sun yi aiki da shi, da ya ksance zina ne da ba abin da wannan yake nufi sai cewa Allah da Manzo da sahabbai sun halatta zina wal'iyazu bilLah!. Hada da cewa shafe shi bai zo dagalittafi da Sunna ba, kuma babu wani dalili akan hakan.

Shi'a duk da sun halatta wannan aure bisa dogaro da littafin Kur'ani da sunnar annabi sai dai sun fifita yin aure da'imi da tarbiyyar iyali domin samar da jama'a mai karfi, kada su karkata ga yin auren mutu'a haka nan duk da kuwa halal ne yinsa ga wanda ya so. Hakanan Shi'a a bisa dogaro da littafinAllah da sunnar annabinsa da kuma koyi da wasiyyoyin imamai masu daraja (A.S) suna girmama mace matukar girmamawa, suna ba ta kima kwarai da gaske. Suna da hukunce-hukunce masu kayatarwa game da matsayin mace da hakkokinta da kuma mu'amala da ita musamman a fagagen kyawawan halaye da mallaka, da aure, da saki, da reno, da shayarwa, da ibada, da mu'amala, hukunce-hukunce masu muhimmanci a ruwayoyin imamansu da kuma fikihunsu.

Bayani Na Ashirin Da Bakwai

27- Shi'a suna haramta: Zina, da luwadi,da riba, da kashe rai, da shan giya, da caca, da yaudara, da makirci, da algussu, da 'yar dubara, da boye kaya, da tauye ma'auni, da kwace, da sata, da ha'inci, da mugun nufi, da waka, da rawa, da kazafi, da tuhuma, da annamimanci, da fasadi, da cutar da mumini, da giba, da zagi, da alfahasha, da karya, da kire, da sauransu na manyan zunubai da kanana, kuma suna kokari matuka domin nisantar idan ake yinsu, suna kokari matuka domin hana su cikin al'umma ta hanyoyi daban-daban kamar rubutu da yada littattafai, da yin majalisosi, da hudubobi, da sauransu.

Bayani Na Ashirin Da Takwas

28- Shi'a suna himmantuwa da kyawawan halaye, da son wa'azi, da jinsu, kuma suna shirya su a masallatai, da dakunantaro da gidaje, da filaye. Kuma suna himmantuwa da addu'o'i da sukazo daga annabi (S.A.W) da Ahlul Baiti (A.S), kamar: addu'ar Kumail, da Abi Hamza, da simat, da jaushan, da makarimul akhlak, da iftitah, da ake yi a watan ramadan, kuma suna karanta su cikin nutsuwa da jin tsoron Allah, musamman tare da kuka da kaskan da kai, domin wannan yakan sanya tsarkake rayuka, da kusantazuwa ga Allah.

Bayani Na Ashirin Da Tara

29 Shi'a suna himmantuwa da ziyarar kabarin annabi da na alayensa da zuriyarsa da aka binne a Bakiyya a madina mai haske, kamar kabarin imam Hasan Mujtaba, da imam Zainul Abidin, da imam Muhammad Bakir,da Imam Ja'afar Sadik (A.S). A garin Najaf ma akwai kabarin imamAli( A.S) da kuma garin karbala akwai na imam Husaini (A.S). Dana 'yan'uwansa, da na 'ya'yansa, da na 'ya'yan 'yan'uwansa, da na sahabbansa da suka yi shahada tare da shi a ranar ashura. A garin samra'u akwai kabarin Imam Ali Alhadi, dana imam Hasan askari (A.S). A garin kazimiyya kuwa akwaina imam Musa Kazim dana Imam Jawad, wadannan duka a garuruwan Iraki ne.A garin Mash'had kuwa da yake Iran akwaikabarin imam Ali arridha (A.S). A garin Kum da Shiraz kuwa akwaina 'ya'yansu. Hakanan na Damashk da take Siriya akwai na sayyida Zainab Kubra (A.S). A birnin Alkahira akwaina sayyida Nafisadaya daga manyan zuriyar Ahlul Bait (A.S).

Wannan kuwa duka domin girmamawa ne gamanzo (S.A.W) da ahlinsa, domin mutum ana kiyaye shi ta hanya kyautatawa zuriyarsa ne, kuma girmama su girmamawa ne gareshi. Kuma Kur'ani mai girma ya yabi Ali imarna, da Ali yasin, da Ali Ibrahim, da Ali ya'akub, ya kuma yaba su sosai, alhalin wasunsu ba ma annabawa bane . Yana cewa: "Zuriya ce sashenta daga sashe"[14]. Kuma Kur'ani mai girma bai hanawa wadanda suka riki kabari masallaci ba, yayin da suka ce: "Lallai sai mun riki (yin) wani masallaci a gunsu"[15]. Wato sai mun yi wani haramin ziyara a kaburburan as'habul Kahafi domin mu bauta Allah a wajen, kuma wannan aikin nasu ba a siffanta shi da shirka ba, domin musulmi mumini yana ruku'u da sujada ga Allah ne shi kadai, kuma yana zuwa kabari ne na wadannan waliyan bayi na Allah domin tsarkin wurin sakamakon albarkacinsu. Kamar yadda ya faru ga annabi Ibrahim (A.S), da fadinsa madaukaki: "Ku riki matsayar Ibrahim wajan yin salla"[16]. Wanda ya yi salla bayan makamu Ibrahim baya bauta wa makam ba ne, haka nan wanda ya yi ibada tsakanin safa da marwa shi ma ba bawan duwatsu ba ne guda biyu, amma Allah ya zabi wajen ne mai albarka da matsayi mai tsarki domin wajen yana dangantuwa zuwa ga Allah ne, domin kwanaki da wurare suna da tsarki da matsayi kamar ranar arfa, da kasar mina, da kasar arfa, saboda an danganta su zuwa ga Allah madaukaki.

Bayani Na Talatin

30- Saboda haka ne kamar sauran musulmi, Shi'a suke himmantuwa da sha'anin manzon Allah (S.A.W) da ahlin gidansa masu tsarki ta hanyar ziyarar kaburburansu, domin girmama wa garesu, da kuma sabunta musu alkawarin biyayya, da kokari a kan tafarkinsu wanda saboda shi ne suka yi shahada, domin ziyarar wadannan kaburbura nasu, yana tunatar da falalarsu da jihadinsu, da tsayar da sallarsu, da zakkarsu, da kuma juriyar da suka yi wajen shanye duk wata azaba da cutuwa a kan wannan tafarki, hada da cewa a cikin wannna akwai taya manzon rahama bakin ciki game da abin da ya samu ahlinsa(A.S) da aka zalunta.

Shin bai fada ba game da shahadar Hamza (A.S) "Sai dai Hamza ba shi da mai yi masa kuka"?!

Shin bai kasance ya yi kuka ba a mutuwarIbrahim (A.S) dansa abin sonsa?!

Shin bai kasanceyana zuwa Bakiyya bayana ziyartar kaburbura?!

Shin bai kasanceyana cewa: "Ku ziyarcikaburbura ba, domin itan tana tuna muku lahira ba?![17].

Haka ne, hakika ziyarar kaburburan imamanAhlul Baiti (A.S) da abin a ake fada na tarihinsu, da matsayinsu na jihadi tana tuna wa zuriya masu zuwa abin da wadannan masu girma suka yi saboda ci gaban musulunci da musulmi na sadaukarwa, kamar yadda kuma wannan yana karfafa su ta hanyar sanya musu ruhin sadaukarwa da sadaukantaka, da zabin wasu a kansu atafarkin Allah. Wannan al'amari aiki nena hankali da mutuntaka, mu sani al'ummu suna dawwamar da ambaton manyansu da suka kafa musu ci gabansu, suna kuma raya ambatonsu ta kowace hanya, domin wannan yana sanya musu alfahari da jin karfi, kuma yana dada musu janyo hankalin al'ummu zuwa gare su da kuma ci gabansu.Wannan shi ne abin da Kur'ani ya so mana yayin da yake karfafa mana matsayin annabawa da waliyyai da salihai da kuma ambaton kissoshinsu.

Bayani Na Talatin Da Daya

31- Shi'a suna neman ceton annabi da alayensa, kuma suna tawassuli da su (A.S) domin neman gafarar zunubansu, da biyan bukatunsu, da ceton marasa lafiyarsu, domin Kur'ani mai girma ya ba su damar haka, kuma ya yi kira zuwa ga hakan, yayin da yake cewa: "Da ma yayin da suka zalunci kawukansu sun zo maka, sai suka nemi gafarar Allah, sai manzu ya nema musu gafara, to da sun sami Allah mai yawan karbar tuba, mai yawanrahama[ 18]. Kuma yace : "Da sannu ubangijinkazai ba ka sai ka yarda"[19].Wannan kuwa shi ne matsayin ceto.

Yaya kuwa za a ce Allah ya ba waannabinsa matsayin ceton masu sabo sannan kuma ya ba shi matsayin wasila da biyan bukatar masu bukatu, sannan kuwa sai ya hana mutane neman wannan ceton,ko kuma annabi ya haramta neman hakan?! Shin Allah bai ba mu labarin 'ya'yanannabi Ya'akub (A.S) ba yayin da suka nemi ceton babansu sukace masa: "Ya babanmu ka nema mana gafarar zunubanmu, mu mun kasnace masu kuskure ne"[20]. Amma wannan annabi ma'asumi mai girma bai hana su ba, kuma ma yanema musu gafara yana cewa: "Da sannu zan nema muku gafarar ubangijina"[21]. Ba yadda za a yi wani ya yi da'awar cewaannabi da imamai (A.S) matattu ne, don hakaneman addu'a a wajensu ba ya amfani. Domin kuwa annabawa rayayyu ne musamman annabi da ubangiji madaukaki ya fada game da shi cewa: "Hakanan muka sanya ku al'umma madaidaiciya domin ku kasance sheda a kan mutane, kuma manzo (S.A.W) ya kasance sheda a kanku"[22]. Yace : "Kuma ka ce: Ku yi aiki, da sannu Allah da manzonsa da muminai za su ga ayyukanku"[23].

Wannan aya tana gudana kuma mai ci gabace har zuwa ranar kiyama kamar gudanar rana da wata, da ci gaban juyawar dare da rana.

Hakanan domin annabi da imami daga ahlin gidansa shahidai ne kuma shahidai rayayyu ne, kamar yadda Allah ya fada awurare masu yawa a littafinsa mai girma.

Bayani Na Talatin Da Daya

32- Shi'a suna mauludin annabi (S.A.W) daimamai daga ahlin gidansa (A.S) gaba daya, suna kuma yin bukukuwa da kuma zaman makokin wafatinsu da rasuwarsu, suna masu ambaton falalarsu da darajojinsu da matsayansu wadanda suka zo a littattafai kamar yadda Kur'ani ya kawo labaran darajojin annabawa da matsayinsu kuma ya shelanta hakan. Sai dai Shi'a suna nesantar abubuwanharamun a wadannan bukukuwa kamar cakuda maza da mata, da cin haram ko shansa, da shisshigi a yabo, da sauran abubuwan da suka haramta wadanda suka sabawa shari'ar musulunci, da kuma ketare haddi, ko sabawa wata aya ko wata ruwaya kowata doka ta littafi da Sunna.