Jagorancin Imam Sadik

Jagorancin Imam Sadik0%

Jagorancin Imam Sadik Mawallafi:
Gungu: Imam Sadik
Shafuka: 5

Jagorancin Imam Sadik

Mawallafi: Sayyid Khamna'i
Gungu:

Shafuka: 5
Budawa: 1653
Gurzawa: 308

Bayanai:

Bincike Cikin Littafi
  • Farawa
  • Na Baya
  • 5 /
  • Na Gaba
  • Karewa
  •  
  • Budawa: 1653 / Gurzawa: 308
Girma Girma Girma
Jagorancin Imam Sadik

Jagorancin Imam Sadik

Mawallafi:
Hausa
JAGORANCIN IMAM SADIK (a.s) JAGORANCIN IMAM SADIK (a.s)Ayatullahi Uzma Sayyid Ali Alkhamena'i Fassarar: Malam Umar Kumo Dubawa: Hafiz Muhammad Sa’id
Gabatarwar Cibiyar Ahlul-bait (a.s) Rayuwar Ahlulbaiti (a.s) ta banbanta da ta waninsu domin ita wata silsila ce kwakkwara, mara yankewa, sai dai yanayin zangon tarihin da kowane imami yake rayuwa a cikinsa, ya kan sa ya dauki wani matsayi wanda a zahiri ka ce yana sabawa da wanda imamin da ya gabace shi ko ya biyo bayan sa ya dauka, sabani mai tsanani. Muna iya ganin wannan a matsayin da Imam Hassan (a.s) da Imam Hussain (a.s) suka dauka. Amma bisa hakika wannan ba sabani ba ne, aiki ne daidai da abin da yanayi ya nema, ta yanda matsayin kowane daya daga cikinsu yana cikata aikin imamin da ya gabata ne ko ya yi shimfida ga aikin da wanda zai gaje shi zai gudanar.
Sakamakon rashin fayyacewar nazari a tattare da sashen masu bahasi kan rayuwar imamai, an sami nazariyya da ra’ayoyi daban-daban wajen kokarin bayyana yanayin aikin da wani Imami ya zartar.wanda sun kasance bisa kuskure, bincike-bincike kuwa ba a zurfafa mahangarsu ba kuma ba su dogara kan tushe na imamanci da isma ba domin ba su ginu kan ingantacciyar fahimta mai iya riskar hakikanin yanayin ba.
Asalin wadannan nazarce-nazarce mara tushe ne mai cin karo, ta kowace fuska da imani da ma’asumin jagoranci wanda kowane imami yake tafiya a kai bisa abin da ya fahimta daga yanayi ko kuma dabai’ar zangon da ya sami kansa a ciki, da kuma kasancewar matsayinsa ba matsayi ne wanda son rai ko amfanin kai ko mai da martani a makance suke rinjaya ba. Matsayi ne wanda yake tattare da hikima da hangen nesa da dacewa da taimako daga ludufin ubangiji.
Irin wancan karkatacciyar fassara ta shafi rayuwar dukkan imamai. Sai ka ga wani lokaci ana sifanta su da daukar matakin dauki ba dadi, kamar matakin juyin juya halin da Imam Hussain(a.s) ya dauka, ko kuma a ce sun karkata zuwa rayuwar tsanaki da nisantar fagen siyasa kamar yanda Imam Sajjad (a.s) ya yi. Ko kuma a buga masu tambarin masu daidatawa da azzaluman mahukunta kamar matsayin Imam Sadik (a.s).
Wannan littafin da ke gabanmu ya kunshi wata laccar da mai girma shugaban musulmi Sayyid Ali Khamene’i (Allah ya ja zamaninsa) ya yi kafin juyin Islama mai albarka da aka aiwatar a kasar Iran. A cikinta ya bijiro da wadancan karkatattun nazarce-nazarce tare da rusa su ta hanyar karfafan hujjojin ilmi da tarihi.
Daga bisani, Sayyid ya gabatar da ingantaccen nazari mai fassara matsayin da kowane imami ya ba da himma a kan shi domin ya yi shimfida ga imamin da zai biyo bayan shi, har al’amari ya iso hannun imam Sadik (a.s). jagorancin wannan imami bai kasance mai mika wuya ga son rai ko amfanin kai ko kuma tsoron azzalumai ba. Wannan jagorancin wani ma’sumin matsayi ne mai bin ka’idar da Allah subhanahu wa ta’ala ya bayyana, ma’asuman gabanin Imam (a.s) kuma suka shimfida masa. Imam Sadik a nasa bangaren aiwatar da wannan tafarkin ne ya yi, yana mai amfani da kwarewarsa ta siyasa da saninda Allah (s.w.t) ya karfafa shi da shi, domin ya jagoranci jirgin musulunci zuwa gabar tsira da aminci, domin kuma ya tsare wa musulmi addininsu da akidarsu bisa dacewa da ingantaccen asalinsu wanda Annabi Muhammadu (s.a.w) ya kawo, tushen da azzalumai suka yi kokarin shafe almominsa da bice haskensa, tsawon tarihi.
Cibiyar Ahlulbaiti (a.s) ta kasa da kasa, saboda sauke nauyin da ya rataya a wuyarta, ta dauki nauyin buga wannan littafi tare da watsa shi don ya kasance wata haskakawa ce kan tunanin musulunci da ingantaccen tarihi, domin kuma ya bayyana wa masu bincike kan Ahlubaiti fuska mafi tsabta da za’a fahimci hanyarsu mai albarka. Cibiyar Ahlulbaiti (A.S) Ta Kasa Da Kasa

Gabatarwar Mai Tarjama Wani dan labari dangane da wannan lacca:- Wannan labari yana nuna abinda rayuwa a kasar Iran gabanin Juyin Islama take tattare da shi, na aiyukan tabbatar da musulunci da kuma kalubale da karfen kafa daga bangaren masu adawa da kiran .
Wata rana cikin watan Shawwal shekara ta 1394 H. kararrawar tarho ta buga a gidan malami mai laccan a birnin Mashhad, mai magana a wayar shi ne Shahid Dokta Muhammad Mufattih daga Tehran.
Bayan gaisuwa, Sheikh Mufattih sai ya nemi Sidi da ya taho Tehran.ran 25 ga Shawwal (watau ranar wafatin Imam Jaafar bin Muhammad Assadik (a.s) domin ya gabatar da wata lacca kan Imam Sadik .
Halin da ma’abocin laccar yake ciki ya kasance mai kunci a wancan lokacin saboda yawan aiyuka da karantarwa da yawan jama’a masu zuwa daga nahiyoyi daban-daban na Iran. Yana ba da laccoci a masallacin Imam Hassan da masallacin Alkarama a Mashhad, birnin da ke gabashin Iran, sannan ya tafi yammacin kasar domin gabatar da lacca a Hamadan da Kermanshah. A cikin Mashhad din kansa yana koyar da tafsiri da Nahjul balaga da hadisi ga kuma darusan kwarewa a fikihu da usulu.
Duk wadannan aiyuka Sidi yana gabatar da su ne a cikin wani hali mai tsananin matsi, ga wahalar rashin kudi ga ta kuntatawar yanayin siyasa. Ya kasance yana rayuwa cikin matsanancin talauci ba tare kowa ya sani ba. Sannan masu mulki suna matsa masa lamba suna sa ido ainun bisa duk abin da yake yi. A wannan shekaran ne suka rufe Masallacin Alkarama, abin da ya sanya Sidi ya takaita da karamin masallacinsa, watau masallacin Imam Hassan ya ci gaba da aiyukansa. A cikin hunturun wanna shekarar ne masu mulki suka sake kama shi, abin da ya kai shi kurkuku a karo na biyar ke nan.
To a cikin irin wannan yanayin ne Sheikh Mufattih ya bukaci Sidi Khamene’i da ya gabatar da lacca a kan Imam Sadik (a.s) a Tehran a Masallacin Javid inda shi Sheikh Mufattih yake ba da salla. Ma’abocin laccar sai ya ba da hanzari saboda dalilan da muka ambata da kuma saninsa cewa akwai malaman da za su cike gurbinsa a can Tehran, kamar su Sheikh Mufattih kansa. Amma Sheikh ya matsa, saboda haka malamin ya yarda. Bayan kwanaki Sheikh Mufattih sai ya sake buga waya yana cewa:-
“Yan sanda sun hana taron laccar” Sidi ya yi ajiyar zuciya, yana mai jin ya huta da wannan nauyin, ya kuma yi hamdala. Ba’a dade ba sai ga Sheikh ya sake bugo waya yana mai cewa:- “ Alhamdu lillahi an dauke hanin. Muna nan muna sauraronka a ranar da muka ajiye”.
Sidi ya yi iya kokarinsa domin a karbi uzurinsa amma ina Sheikh Mufattih bai gamsu ba, sai ya amsa da cewa:- “Mun riga da mun sanar da batun laccan nan cikin jami’o’ i” Sidi ya ba da dalilin cewa samun tikitin jirgi yana da wahala. Amma Sheikh sai ya ce a shirye yake ya saya masa tikitin, saboda haka ba makawa ga halartar Sidi!
A ranar laccar ya baro Mashhad ya kuma iso Tehran yan sa’ o’ i kafin lokacin farawa, sai ya wuce zuwa masallacin kai tsaye. Yayin da mai masaukinsa ya gan shi, ya yi farin ciki matuka, a lokacin kuwa yana tare da matasa kamar dari biyu suna jiran a ta da salla. Ana cikin salla matasa sai zuwa suke yi har adadinsu ya kai dururuwa da dama. Bayan’yan mintoci sai ga dalibai gungu gungu suna ta shigowa, wannan bayan an tashi daga darasi a jami ‘o’ i kenan.
Masallacin da farfajiyarsa da loko-lokon da ke daura dashi duk suka cika makil da mutane. Sidi ya fara lacca yana rike da takardu guda arba’in wadanda suke kunshe da muhimman batutuwa kan laccar. Ya ci gaba da bayani wanda ya dauki hankalin masu sauraro, kai ka ce tsuntsaye ke bisa kawukansu saboda tsananin natsuwa. Laccar ta dauki tsawon sa’a uku amma sashen takardun nan kawai Sidi ya sami damar sharhinsu. Da ya zo rufewa sai ya daga wadancan takardu arba’in yana mai ishara da cewa lokaci bai ba shi damar gabatar da dukkanin abin da ya yi niyya ba.
Bayan wannan zama ba a dade ba sai aka kama Sheikh Mufattih aka hana shi salla a masallacin Javid. Bayan an sako shi sai ya koma masallacin Kuba. A nan, ya zama wajibi mu yi nuni da wani muhimmin al’amari, shi ne : Sidi Khamene’i (Allah ya kiyaye shi ) ya gabatar da laccan nan ne shekara ashirin da suka wuce. Kuma babu shakka ya yi nazari da bincike mai yawa kan rayuwar Imaman Ahlulbaiti (a.s) saboda haka ta yiwu yana da wadansu sababbin ra’ayoyi ko kuma ya canja ra’ayi, kan wata mas’ala daga cikin mas’alolin da ya gabatar cikin jawabin. Hakika mun so mu san ra’ayinsa kan wadannan mas’aloli domin mu cimma ra’ayoyinsa na baya-bayan nan kafin mu soma tarjamar wannan jawabin zuwa harshen larabci. Amma nauye-nauye da tarin ayyuka da cushewarsu ya hana hakan. Saboda haka za mu gabatar da ita kamar yanda take. A cikinta akwai sabon ilmi mai yawa da kuma gadon tunane-tunanen musulunci kamar yanda ake tattauna shi a Iran gabanin nasarar Juyin Islama, abubuwanda suke da muhinmanci ga duk wani mai bincike.
Ana iya lura da cewa Sidi ya yi fito-na-fito da ra’ayoyi guda biyu wadanda yake yawan sukar su a laccocinsa da darussansa. Wadannan kuwa su ne: Ra’ayin gurguzu mai sukan musulunci da alamominsa, yana sifanta mazajen musulunci da cewa ba su tabuka komai ba wajen kare hakkin matalauta da wadanda aka zalunta, dadin dadawa ma sun kasance madogarar azzalumai da masu hanu da shuni! Na biyunsu shi ne ra’ayin wanda suka yarda an rinjaye su. Saboda rinjayarsu da aka yi sai suka kasance ba su da katabus, kokari suke su sami abin da wai zai zame musu hujjar rashin motsawa, a cikin tarihin rayuwar Imaman musulunci. Wadannan ra’ayoyi sun yi tasiri a kasar Iran kafin habakar Juyin Islama, sun kuma zamo karfen kafa ga masu kiran al’umma zuwa hanyar musulunci. Dokta Muhammad Ali Azarshab

Ubangiji Madaukaki yana Cewa: Daga muminai akwai wandansu mazaje da suka gaskata abin da suka yi wa Allah Alkawari a kansa, sa'annan a cikinsu, akwai wanda ya biya bukatarsa, kuma basu musanya ba, musanyawa. Ahzab 23
Kuma muka sanya su shugabanni suna shiryarwa da umurninmu. Kuma muka yi wahayi zuwa gare su da ayyukan alheri da tsayar da sallah da bayar da zakka. Kuma sun kasance masu bauta garemu. Anbiya 73.

Dubi Biyu Karkatattu Godiya tabatta ga Allah, tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzon Allah da alayesa da wadanda suka yi koyi da shiriyarsu.
Akwai karkatattun dubi guda biyu kan al’amrin Imam Sadik (a.s) wadanda suka samo asali daga nau’i biyu na tunani. Abin mamaki a nan shi ne duk da sabawarsu da juna suna da kusaci wajen kamanni da abin da suka kunsa da kuma tushe, kai ana ma iya cewa wadannan dubi biyu suna da cikakkar tarayya a sashen ginshikansu.

Dubi Na Farko Ra’ayi ko kuma kallo irin na masu karewa watau masoya, wannan ra’ayin wasu masu zaton su mabiyan Imam Sadik (a.s) ne amma shi’arsa ne da fatar baki kawai banda aiki. Ra’ayin a takaice shi ne:-
Cewa Imam Sadik (a.s) ya sami yanayin da imaman da suka gabace shi ko suka biyo bayan shi basu samu ba, yanayin da ya ba shi damar yada hukunce-hukuncen addini da kuma bude wa dalibai kofofin majlisinsa. Ya zauna gidansa yana karbar masu zuwa, ya rungumi karantarwa da yada ilmomi, duk dalibi ko mai bidar gaskiyan da ya zake masa yana kashe kishinsa na ilmi. Mutum dubu hudu suka yi karatu a gabansa, kuma ta hanyar wadannan dalibai ilmomin Imam Sadik sun watsu a ko ina. Daga cikinsu akwai ilmomin addini kamar su fikihu da hadisi da tafsiri, akwai kuma ilmomin dan’adamtaka kamar su tarihi da kyawawan dabi’u da ilmin zamantakewar al’umma.
Imamu ya yi mukabala da ma’abota sababbin ra’ayoyi, ya yi raddi kan zindikai da yan maddiyya da mulhidai, ko dai kai tsaye ko kuma ta hanyar dalibansa. Ya yi yaki da mazowa karkatattun addinai matuka. A ko wani fagen addini Imam ya tarbiyantar da wasu fitattun dalibai da kwararru.
Ma’abota wannan mahanga suna karawa da cewa: domin burin Imam a kan ci gaban wannan gagarumin aikin ilmantarwa, dole ta sa ya guji sa baki cikin al’amuran siyasa, saboda haka bai gabatar da kowani aikin siyasa ba, bugu da kari ya ma zabi hanyar daidaitawa da irin siyasar halifofin zamaninsa domin dadada musu da nisantar duk wata rikitarwa da ka iya kusantar aikinsa. Don haka bai yi fito-na-fito da halifofin ba, ya kuma hana kowa yin hakan. Wani zubin ma yanayi yana sawa Imam ya je gaisuwa ya kuma sami kyaututtuka da goyon bayansu. Idan shugaba ya yi masa mummunan zato sakamakon faruwar wata harkar tawaye ko kuma tsegunta masa wata tuhuma, Imam ya kan je gaban shugaban domin ba da baki.
Ma’abotan wannan dubin su kan jero hujjojin tarihi domin karfafa ra’ayinsu. Hujjojin sun hada da riwayar Rabi’u Alhajib da makamantansa, wadanda suke siffanta Imam da baiyana kuskure da nadamarsa a gaban Halifa Mansur. Wannan riwaya tana dangantawa Imam kalmomin yabon Mansur, wanda ko shaka babu karya ce a ce sun fito daga Imam Sadik (a.s.) dangane da azzalumai irinsu Mansur. Wadannan kalmomin suna sifanta Mansur cewa kamar Yusuf da Sulaiman da Ayyuba ya ke, suna neman ya dauki hakuri kan munana masa da Imam ko ‘ya’yan Hassan suke masa: “Hakika an baiwa Sulaiman (mulki) kuma ya yi godiya, an jarrabi Ayyuba, ya yi hakuri, kuma an zalunci Yusufu, ya yi gafara, kai kuma irinsu ne……”[2]
Wannan ra’ayi yana sifanta Imam da cewa shi masani ne mai bincike, Abu Hanifa da malik sun sha daga kogin ilminsa, sai dai ya yi matukar nisantar yaki da zaluntar addini da masu mulki ke yi, ya kuma nisanci bukatun umurni da kyakkyawan aiki da hana munkari yayin da sarki ya zama ja’iri. Imam ba shi da wata dangantaka da masu tawaye wa zalunci ire-iren su Zaid ibn Ali da Muhammad bn Abdullah da Hassan bn Ali shahidin Fakh ko kuma rundunonin wadannan mutane. Bai kasance yana mai da martani kan abin da yake aukawa jama’ar musulmi, ko nuna damuwa kan dimbin dukiyar da Mansur yake tarawa, ko yunwar da ‘ya’yan Annabi (s.a.w.a) suke fama da ita a cikin tsaunukan Tabaristan da Mazandaran da garuruwan Irak da Iran ba, ta yanda basu da abinda zasu sa a baka ko abinda zai rufe musu al’aura idan suna son salla a jam’i !! Kuma ba ruwansa da kisa da azabtarwa da tarwatsa mabiyansa alhali suna hannu rabbana basu samun ko da kwatankwancin abin da marasa galihun wancan lokaci suke mora!!!
A zaton ma’abota wannan dubin Imam Sadik sam bai nuna wata damuwa kan wannan yanayi ba, a maimakon hakan ya gamsu da yin mukabala da ire-iren su Ibn Abi Awja, ya rufe masa baki da hujjoji ya kuma rinjaye shi duk da cewa ba zai ba da gaskiya ba. Wannan shi ne siffanta Imam Sadik da mazowa ra’ayin farko sukayi.

Dubi Na Biyu Masu dauke da irin wannan dubin ba su yarda da imamancin Imam Sadik ba. Ita wannan mahanga tana ganin cewa ya nuna halin ko oho bisa zaluncin da yake aukawa al’umma. A zamamaninsa al’umma na kukan zaluncin yanayin zaman jama’a mai hawa-hawa da dagawar siyasa da babakere kan dukiyoyin jama’a [3] da hadarin da ya shafi rayuka da mutuncinsu. Dadin dadawa sarauta ta rinjayi hankula da rayuka da tunani da kuma zukatan mutane. Lamarin ya kai ga al’umma ta rasa mafi kankantan hakkokin bil Adama wanda ya hada da ikon zabe. A gefe guda kuma azzalumai suna ta wasa da makomar mutane yanda suka so, suna gina katafaran soraye kamar soron Al-hamra wanda ke makwabtaka da dubban kangwayen da matalautan al’umma ke zaune a ciki. Cikin wannan jama’ar da take dandana nau’i daban-daban na rashin adalci da danniya wai Imam Sadik ba abin da ya yi sai fuskantar bahasinsa da bincike da tarbiyyar dalibai, yana karkata dukkan kokarinsa kan samarda fukaha’u da masana ilmul kalam!!
Hakika dukkan mahanga biyun nan sun bi son zuciya wajen hukunci kuma basu ginu kan wani tushe ba, basu kuma dogara kan wani dalili na gaskiya ba. Sai dai ra’ayin farko ya fi tsanani wajen bin son zuciya da zaluntar Imam Sadik (a.s) tun da yake ya fito ne daga masu da’awar wai su shi’arsa ne kuma mabiyansa.
A nan ban yi niyar daukan salon bahasin ilmin nan da aka saba bi wajen bincike-bincike, wanda a kan bijiro da dukkanin nassoshin da suka yi magana kan rayuwar Imam Sadik (a.s) sannan a auna wannan da wancan wajen matani da isnadi har a fitar da sakamako ba. Abin da nake nufi shi ne gabatar da nazari na uku wanda ya sha bam-bam da wadancan biyun. Sannan in auna shi da hujjojin da zan tsamo daga littattafan da suke hannunku’ domin, a matsayinku na alkalai ‘yan ba-ruwan mu, ku iya hango fuskar Imam ta hakika.
Kafin in shiga cikin bahasin ya zama wajibi in yi nuni da cewa dukkanin nazariyyan na biyu basu dogara kan sahihin tushe abin amincewa ba. Kamar yanda na ambata, ra’ayin farko yana dogara kan wasu riwayoyi(na bayyana yanayin isnadinsu a kasa). Wadannan riwayoyi bisa dabi’a sun dace da bukatar masu neman hutu da gudun tsangwama suna fakewa da su a matsayin yankakken hujja.Lallai kam sun isa hujja ga raunanan zukata masu saukin girgizuwa!
Wadannan riwayoyi sun sifanta Imam da cewa yana mai lallamin Mansur domin kare rayuwarsa duk da cewa yana iya magance yanayin da ya sami kansa ta hanyar hikima. Idan dai haka jagora yake, me zaton ka da mabiyi? Mun yi imani cewa yanayin nassin wanna riwaya ya wadatar wajen tabbatar da cewa kirkirarta aka yi. Ai Imam yana da damar tunkude sharrin Mansur ta wadansu hanyoyin daban kamar yanda amintattun riwayoyi suka nakalto abin da ya faru a wurare mayaiwata. Ashe babu dalilin da zai sa Imam ya koma wa lalama mara tushe ko yabon da ba na gaskiya ba, har ma ya baiwa Mansur halayen da ba shi da su da matsayin da bai cancance shi ba. Babu shakka matsayin imamanci ya daukaka sama da wannan, daukaka mai girma, darajarsa kuwa ta wuce irin wannan kaskanci ya gurbata ta.
Ta bangaren isnadi kuwa, idan aka zurfafa bin diddigin masu ruwaya abubuwa da yawa za su baiyana a gare mu. Isnadin wasu daga cikinsu yana karewa ne kan Rabi’u Alhajib sarkin kofa.Sarkin kofan Mansur! Wannan kuwa akwai adali! Littattafai sun nuna cewa Rabi’u ya fi kowa kusanci da Mansur, ya fi kowa fada. Mansur ya yi masa waziri a shekara ta dari da hamsin da uku hijiraya watau shekaru biyar bayan wafatin Imam Sadik. Hakika Rab’u ya sami daukaka a matsayin ladan karairayin da ya kirkira ya kuma danganta su ga Imam.
Irin wannan mutum wanda kusancinsa da alkawarinsa ga halifa ya tabbata ba abin mamaki ba ne ya kirkiri karairayi ya kuma jingina wa Imam Sadik lalama ko ya sake kalami mai zafi da Imam ya yi furuci da shi, ya mai da shi na kankan da kai da lallami. Wannan ba bakon abu ba ne wajen irin wannan bafaje, amma abin al’ajabin shi ne yanda mai hankali zai gaskata abokin sirrin halifa a kan abin da ya shafi abokan gabarsa, har ma a ce wai shi ma shi’a ne. Wannan kaulin shi ma wani yanki ne daga kule-kullen da kaskanci ne musabbabinsu.
Shi ma ra’ayi na biyun fonko ne kwatankwacin na farkon, kuma bai kafu bisa ilmi ba. Ra’ayin yana kama da irin hukuncin da mustashrikai suke yi wanda ya samo asali daga jahilci da kulli, da kuma ruhi irin na tsagwarar maddiyya wacce ba ta tafiya daidai da dabi’ar abin da yake gudana a musulunci. Mun ga irin wancan hukunci na rasar kunya da bashi da kanshin gaskiya wanda sashen mustashrikai suke yanke wa musulunci da Imaman Ahlulbaiti (a.s). Ga abin da daya daga cikin su [4] ya fada kan Imam Hassan Mujtaba: cewa ya sai da halifanci ya karbi kudi! Ya gama rayuwarsa tare da turare da mata da walwala. Wani [5] kuma ya ce: Musulunci ya cirato al’umma daga matakin bauta zuwa na tsarin akda’(watau tsarinda talakawa basa mallakar filayen noma sai dai su yi aiki a filayen masu iko kana su raba amfanin)! Mahanga ta biyun tana tarayya da zantuttukan wadannan mustashrikai wajen biri-boko da garaje da kuma madogara ta maddiyya. Abin sha’awa a nan shi ne hujjojin da ma’abota ra‘ayi na biyu, watau ra’ayin ‘yan gurguzu, suka dogara da su ba komai ba ne face hukunce-hukuncen da ma’abota ra’ayin farko suka kirkiro!

Sahihin Dubi: Na Uku Bari mu fara bayanin mahanga ta uku kan lamarin Imam Sadik, ra’ayi da ko wani kaifin basira yana iya tsinkayar shi idan ya koma ga littafan riwaya. Wannan hukuncin ba ya takaita da rayuwar Imam Sadik kadai, a’a yana game dukkan Imaman Ahlulbaiti, bambancin kawai shi ne abin da aikin kowannensu ya kebanta da shi gwargwadon abin da yanayin zamani da wuri ya hukunta. Wannan sabawar kebantattun sifofin aikin ba ta cin karo da haduwar ruhin aiki da hakikaninsa ko kuma haduwar manufa da hanya.
Idan muna son fahimtar yanayin rayuwar Imamai ya wajaba da farko mu fahimci falsafar Imamanci. Tafiyar da aka san ta a mazhabar Ahlulbaiti da sunan Imamanci, wacce ginshikanta mutum goma sha biyu ne daya na bin daya kuma ta dauki kusan tsawon karni biyu da rabi, bisa hakika ci gaban aikin annabci ne. Shi annabi, Allah (s.w.t) yana aiko shi ne da wata sabuwar manhajar rayuwa, da sabuwar akida da wani sabon shirin alakokin dan Adam da kuma sako wanda aka dora masa, gwargwadon shekarun da aka ba shi a wannan takaitacciyar rayuwa.
Wajibi ne kira ta ci gaba a bayan Annabi domin sakon ya cimma mafi daukakan matsayin da ake bukata wajen tabbatar da manufofinsa. Kazalika dole ne mutumin da ya fi kusaci da ma’abocin sakon ta dukkanin fuskoki ya dauki nauye-nauyen ci gaba da kira, domin sakon ya kai amintaccen matsayi, ya sami turke mai karfi, tabbatacce mara yankewa. Wannan aiki, babu shakka yana bukatar amintattun mutane. Wadannan sune Imamai, wasiyyan Annabi. Kuma dukkanin Imamai madaukaka kuma ma’abota sako suna da wasiyyai da halifofi. Ba za mu san nauyin al’amarin Imamai ba sai mun san na Annanbi, wanda Alkur,ani mai girma ya bayyana da cewa: “Hakika, lalle, mun aiko manzanninmu da hujjoji bayyanannu, kuma muka saukar da littafi da sikeli tare da su domin mutane su tsayu da adalci……..” [6] Wannan daya daga cikin ayoyi masu baiyana dalilin aiko annabawa da kuma nauyin da aka dora masu ne. An aiko su ne saboda gina wata sabuwar al’umma da tuge ginshikan fasadi da sanarwa kan aiwatar da sauyi ga jahiliyyar zamaninsu da kuma sake wa al’ummarsa fasali. Wannan shiri na kawo sauyi Imam Ali (a.s) ya bayyana shi a farkon karbar ragamar shugabancinsa da cewa :-. “ …..har sai na kasanku sun zamo su ne a sama na samanku kuwa sun zamo su ne a kasa….”[7] Wannan aiki ne na gina al’umma bisa asasin tauhidi da adalcin zamamtakewa da martaba dan Adam da yanta shi da tabbatar da daidaiton hakkoki da dokoki a tsakanin jama’u da dai-daiku da yarfar da kangi da zalunci da boye kayan masarufi; da bude kofa ga karfi da kokarin dan Adam; da kwadaitarwa kan neman ilmi, da ba da shi, da kwadaitarwa kan tunani da sauransu. Shi aiki ne na kafa wata jama’a wacce a cikinta, ake habaka ilahirin hanyoyin daukakar dan Adam ta dukkanin muhimman fuskoki da kuma zaburar da shi don ya fuskanci tafiyan nan ta neman kamala a tsawon tarihinsa.
Saboda wannan nauyin ne Allah ya aiko annabawa.A matsayin Imamanci na ci gaba da daukar nauye-nauyen annabci, muna iya cewa yana daukar wadancan aiyuka. Da a ce Manzon Allah (s.a.w.a) ya rayu shekara 250 da wadanne ayyuka zai gabatar? Yanda ya aikata wajen kira haka nan Imamai suka aikata. Manufar Imamanci ita ce ta annabci hanyar daya ce watau samar da al’umma ta musulunci adila da kokarin kare ingantaccer tafarkin musulunci. Sai dai abin da zamani yake hukuntawa yana bambanta, kuma gwargwadon wannan bambancin dabaru da solon aiki na sabawa. Annabi (s.a.w.a)da kansa ya yi aiki da wani salo a farkon kira wajen tabbatar da manufofinsa bayan an kai wani zango kuma ya yi amfani da wani salon dabam.
Yayin da kirar take farkonta, tana kewaye da barazana da kalubale tana bukatar wani shiri na musamman domin gudanar da aikin ida sako. Yayin da kuma ginshikan tsarin musulunci suka kafu, musulunci ya sami kafuwa a Tsibirin Larabawa sai dabaru da salo suka sake.Tabbataccen al’amari na dindindin shi ne madaukakiyar manufar da sakon ya sauko saboda ita. Shi ne kuma kokarin samar da al’ummar da a cikinta dan Adam yake iya tafiyarsa ta bidan kamala ta dukkanin fuskoki, a ciki ne kuma kwazo da karfin da ke boye cikin halittar dan Adam za su bubbugo. A nan fa kariyar wannan al’umma da tsarinta na musulunci suke.
Imaman shi’a, kamar yanda Annabi ya yi, suna faskantar ainihin wannan manufar ne watau kafa adalin tsari na musulunci mai wadannan sifofi kuma bisa wannan tafarki. A dai dai lokacin da ake kafa wannan tsarin ana kuma ba da karfi wajen kariya da tabbatar da dogewarsa.
Me kafa tsarin zaman jama’a da ci gaban gudanarsa yake bukata?. Da farko yana bukatar wata manufa ko akida (aidiyolojiyya) mai shiryarwa wacce daga gare ta ne wancan tsarin yake bubbugowa kuma ita take zayyana shi. Na biyu yana bukatar karfin zartarwa mai iya kutsawa cikin wahalhalu da matsaloli da kangiya domin tabbatar da manufar tsarin. Mun san cewa aidiyolojiyyar (ko kuma akida) Imamai ita ce musulunci. Shi kuwa musulunci sako ne madawwami ga dan Adam, watau sakon da ke tattare da sinadarin wanzuwa da tabbatarsa.[8]
Idan muka lura da wadannan mas’aloli, cikin sauki za mu iya fahimtar manhajar Imamai na Ahlulbaiti kuma wasiyyan Annabin rahama (s.a.w.a). Wannan manhajar tana da sassa biyu malizimta juna: na farkon yana dangantaka da akida, na biyun kuma yana da alaka da samar da karfin zartarwa da zamantakewa. A sashen farko, Imaman suna fuskantarda kokarinsu da himomminsu ne wajen yada manufofin sako da kafa su, da tono duk wani kaucewa gaskiya da karkata wadanda masu bin son rai suke sabbabawa; da bayyana ra’ayin musulunci kan sababbin mas’aloli da raya alamomi wadanda suka rushe, sakamakon karo da amfanin ma’abota iko da masu fada a ji; da faiyace abin da ya boyu wa hankula na daga littafin Allah mai girma da sunnar Ma’aiki. Ana iya takaita zance kan nauyin sashen farko da cewa kare rayayyen sakon musulunci ne mai ginuwa, tsawon zamani.
A sashen na biyu kuwa gwargwadon abin da yanayin siyasa da zamantakewar al’ummar musulunci suke hukuntawa, suna kokarin samar da shimfida da ake bukata wajen karbar ragamar shugabancin al’umma da kansu a kusa, ko kuma shimfida domin imamin da zai ci gaba da tafiyar tasu a nan gaba ya kuma karbi shugabanci bayan zango mai tsawo.
Wannan a takaice shi ne manufar rayuwar tsarkakan Imamai, kuma wadannan su ne tsarin manufofinsu a game, saboda su suka rayu kuma dominsu suka yi shahada. Idan tarihin rayuwar Imamai wanda ya zo mana ba ya tabbatar da ra’ayin da muka tafi a kai, to akidarmu kan Imamai ta isa ta sauwara mana rayuwarsu ta wannan fuskar kadai. Mene ne zatonka idan tarihi yana ba da shaida da take gamsar da ko wane mai bincike cewa rayuwar Imaman Ahlulbaiti tana kan wannan mafuskantar?.

Zango-zango na Tafiyar Imamanci Tafiyar Imamanci ta fara ranar da Manzon Allah (s.a.w.a) ya bar duniya cikin watan Safar, shekara ta goma sha daya bayan hijira har zuwa wafatin Imam Hassan Askari (a.s) a watan Rabi’ul Awwal, shekara ta dari biyu da sittin bayan hijira. Cikin wadannan shekaru, tafiyar Imamaci ta ci zango hudu, wanda a kowanne Imamai sun dauki matsayi fitacce gaba ga mahukuntan al’ummar musulmi.

Zango na Farko Wannan ya kunshi matakin kame baki ko mu ce matakin taimakawa mahukunta. A wannan zango jinjirar al’ummar musulunci ta yi fama da hadarin magabta wanda ya yi mata kawanya. Yayin da wadannan magabta suka ji barazanar da sakon musulunci yake masu, sai suka dana tarkon su daga wajen daular musulunci suna dakon wata dama domin su aukawa wannan sabuwar al’umma. A wani janibin kuwa akwai adadi mai yawa na sabon-shiga musulunci wadanda hankalinsu ba zai iya daukar halin rarraba cikin al’ummar musulunci ba, saboda haka duk wata tsagar da ka iya faruwa za ta zama barazana ga tushen al’ummar da ma samuwarta. Na uku, karkatar da ta sami al’umma ba ta yi tsananin da har mutum kamar Amirul Muminina Aliyu ibn Abi Talib(a.s) wanda ya fi kowa kaunar kubutar sakon musulunci da al’ummarsa, ba zai iya jure mata ba. La’alla wanna halin da ya sami jama’ar musulmi shi ne abin da Manzon tsira Muhammadu (s.a.w.a) ya yi ishara da shi lokacin da ya yi wasici ga wannan dalibinsa wanda yake farda, da ya yi juriya idan ya auku.
Wannan zangon ya dauki tsawon rayuwar Imam Ali (a.s) fara daga wafatin Manzon Allah ( s.a.w.a) har zuwa karbarsa halifanci. Imam ya yi sharhin matsayin da ya dauka cikin takardar da ya rubuta wa mutanen kasar Masar yayin da ya nada masu Malik Ashtar hakimi. Ya ce:- “Sai na kame hannuna yayin da na ga masu juyawa sun juyawa musulunci baya, suna kira zuwa shafe addinin Muhamamdu (s.a.w.a). Sai na ji tsoron idan ban taimaka wa musulunci da ahlinsa ba, zan ga tsagewa da rugujewa tattare da shi. Da haka zai faru, to da musibar da za ta sami musulunci ta fi tsanani a gare ni bisa ga kubucewar shugabancin ku.……sai na bayar da gudumowata a abubuwan da suka faru”(1)
Yayin da shugabanci ya kauce masa sai ya hakura domin musulunci, lokacin da al’umma ta fuskanci hadura masu girma sai ya mike domin kare musulunci da al’ummarsa, yana mai shiryarwa da aiki a fagagen siyasa da soji da zamantakewa. Cikin Nahjul Balaga da sirar Imam Ali, akwai bayanai masu tabbatar da irin nau’in kokarinsa a zamanin shugabancinsa.


1
JAGORANCIN IMAM SADIK (a.s) Zango Na Biyu Zangon rike ragamar shugabanci. Wannan zangon ya dauki shekaru hudu da wata tara na halifancin Amirul Muminina Ali (a.s) da kuma wasu watanni na halifancin dansa Hassan (a.s). Duk da wahalhalu da matsaloli da damuwa da tsanani da yake tattare da wannan zangon, kamar yadda duk wata hukuma mai ra’ayin juyi take fuskanta, mafi haske da ban sha’awan shafuffukan tarihi ne suka kunshi bayanin aikace-aikacesa, kamar su mu’amala mai cikakkiyar dan Adamtaka da adalci da tsananin lizimtar hukunce-hukuncen musulunci ta fuskoki dabam-dabam wajen gudanar da al’ummar musulunci da kuma rikon magana daya da fayyacewa da jaruntaka wajen aiwatarwa da kuma daukan matsayi.
Wannan zango na tarihin imamanci ya zama abin koyi wanda Imaman Ahlulbaiti (a.s) suka yi kira domin aiwatar da shi a rayuwar siyasa da zamantakewa, tsawon karni biyu. Mabiya Ahlulbaiti suna kankame da son wancan yanki na tarihin musulunci, suna neman dawo da shi, suna kuma auna tsare-tsaren da suke rayuwa cikinsu da wancan zamani mai ban sha’awa. Da wannan ma’aunin ne suke tuhumar tsare-tsaren da suka baude wa turbar musulunci. Mai ra’ayin sauyi a al’ummar wacce da bidi’a da baudiya suka addaba. Wannan halin da al’umma take cikinsa ya dorawa Imaman da suka biyo baya nauyi mai tsanani da mas’uliya mai girma.

Zango Na Uku Shi ne wanda ya dauki shekara ashirin,tsankanin sulhun Imam Hassan (a.s) a shekara ta 41 H zuwa shahadar Imam Hussain (a.s) a shekara ta 61 H. Bayan sulhun Imam Hassan (a.s) an soma wani nau’in aiki mai kama da sirri wanda kuma manufarsa ita ce maido da jagorancin musulunci wa ma’abotansa na gaskiya tun da lamarin yana bukatar dako har sai mulkin Mu’awiya ya kare. Cikin wannan gajeran lokaci an fuskantar da kokarin kyautata yanayi wajen yin shimfida ga zango na gaba.

Zango Na Hudu A nan ya kamata mu yi bayani mai dan dama, tun da wannan zangon shi ya shafi laccarmu domin a ciki Imam Sadik (a.s) ya rayu. Cikin wannan zangon da ya dauki kusan karni biyu, tafiyar Imamanci ta ci gaba kan wani dogon layi domin canja al’umma har ta dace da ra’ayin musulunci a dukkanin fagage wadanda suka hada da jagorancin siyasa. Tafiyar sashe ta yi galaba sashe kuma ta gamu da ci baya; tana tattare da nasara mai girma a fagen tunani da akida, tana cudanye da salo daban daban na dabarun gudanar da kira, abin adonta kuwa shi ne ikhlasi da sadaukarwa da fana’i da girman dan adamtaka a idon musulunci, halayen da suka kai kololuwa da kuma matukar kyau.Wannan marhala ko zango ya fara daga watan Muharam shekara ta 61 bayan hijira, bayan shahadar Imam Hussain bin Ali (a.s). Kamar yanda muka ambata, cikin wannan zangon, al’umma ta kara motsawa kwarai da gaske a fagen manufa (watau aidiyolojiyya) da tinkarar baude-baude ba jirkice-jirkice, wadanda matattarar iko da kuma kwakwalen jahiliyya suka wanzar. Waccar motsawa manufarta gudanar da aiyuka tsawo lokaci domin kafa hukumar musulunci mai tafiya bisa turbar Alkur’ani da sunnar Ma’aiki (s.a.w.a) kamar yanda Imam Ali (a.s) ya misalta.
A sarari yake cewa zartarda manhajar sauyi ‘yar asali a cikin al’ummar da ta sami shekaru da dama cikin karkacewar tunani da aiki yana bukatar kwararan dabaru da shiri mai tushe. A wancan lokacin, al’ummar Annabi ta rayu karkashin hukumar Mu’awiya mai cike da karkata gaskiya da musanya ta da wata fuska ta jabu, halin da ya jefa jama’a cikin wani barci mai nauyi tare da nisanta tunanin mutane daga ruhin jagoranci mai bin ka’ida. Wannan baudewa ta kai har lamarin ya janyo kashe badadin Manzon Allah (s.a.w.a) a Karbala, al hali wannan al’umma tana ji tana gani, al’ummar da take fama da halin fargaba da rauni da fatattaka a hannun razanarwar banu Umayya.
Saboda haka sai an yi aiki tukuru kafin a iya maido wa wannan al’umma ruhinta rasashshe da mutuntakarta wanda aka tattake, hakika aiki ne mai girma wanda al’umma take bukatarsa domin sake cancantar daukar sakon Islama da kama yunkurin ciccibar nauyin rike shi. Ba makawa ga wani sauyi tamkar wanda Manzon Allah (s.a.w.a) ya fuskanci al’ummar jahiliyya da shi, sannan daga bisani a karbi jagorancin jama’a.
Babu shakka dawo da rayuwa irin ta sauyi da sabonta ta aiki ne wanda bai kasa samar da ita tun farko wajen tsauri da muhimmanci ba. Tajdidi irin na juyi yana bukatar imani mai karfi da azama tabbatatta da hankali mai tsarawa da tunani farkakke, wayayye mai motsawa. To wane ne mai daukar wannan nauyin?! Waccar jama’ar da ta kasa tafiya tareda Imam Hassan (a.s) ta kuma kasa kai matsayin taimakawa Imam Hussain (a.s) lallai ba ta iya wannan aikin raya al’ummar musuluncin. Saboda haka dogaro ga wanna jama’ar babu abin da zai haifar illa cin tura da tabewa. Hakika motsin da Tawwabin suka jarraba da tawayen Mukhtar da Ibrahim bin Malik hujja ce babba kan abin da muka fadi.

Matsayin Imam Sajjad (a.s) Bayan waki’ar Ashura Imam Zainul Abidin Ali bin Hussain (a.s) yana da zabi biyu,su ne:- Imma dai ya sa sahabbansa shiga wata harka sakamakon motsawar rai da tausayi ya jefa su cikin wani garaje wanda wutarsa ba badewa ruruwarta zai yi sanyi, ya bice (saboda ba su da sifofin masu jihadi), sannan daga bisani a bar wa Banu Umayya filin ci gaba da danniya da babakere kan makomar al’umma wajen tunani da siyasa, ko kuma ya rinjayi tausayi da biri---bokon fushi da tunzura, kana ya tanadi share fage wa wani babban aiki wanda zai kai ga dawo da rayuwa irin ta musulunci. Bukatun share fagen su ne tunani mai jagorantan aiki da samar da wata salihar jama’a domin ta zama iri ga juyi da sauyi nan gaba, ya kuma nisanci idanun Banu Umayya, ya ci gaba da aiki haikan wanda manufarsa ita ce gina tunani da kuma dai-daikun matane. Da haka ne zai yi tafiya mai yawa kan manufar kira, Imamin da zai gaje shi kuwa zai zama ya kara kusanto cimma manufar.
To wani zabi ko hanya zai fifita? Ko shaka babu, hanyar farko ita ce ta sadaukarwa da daukar fansa, sai dai jagoran da yake shiri saboda harakar tarihi da kuma zamanin da tsawonsa ya zarce tsawon rayuwar Imam nesa ba kusa ba, sadaukar da rayuwarsa kawai ba ta isa. Dole ne ya zama mai zurfin tunani, mai yalwar zuciya, mai hangen nesa mai dabara da hikima cikin al’amuransa. Wadannan sharrudda sun wajabtawa Imam zabar hanya ta biyun.
Imam Ali bin Hussain (a.s) ya zabi ta biyun duk da dauriya da wahal-halu da juriya da kuncin da ke tattare da wannan hanya. Ya ba da rayuwarsa kan wannan tafarki (a shekara ta 95 bayan hijira).
Imam Sadik (a.s) ya sifanta mana yanayin da imami na hudu ya rayu a kai da kuma rawar da ya taka ta jagaba, ya ce:-“Bayan Imam Hussain (a.s) mutane sun juya baya banda mutum uku, Khalid Alkabuli da Yahya ibn Ummi Dawil da Jubair bin Mud’im. Daga bisani sai mutane suka dawo suka yawaita. Yahaya Ibn Ummi Dawil ya kan shiga masallacin Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce:- “Mun fita batunku kuma kiyayya da jiyewa juna sun bayyana a tsakaninmu …..”(Mumtahina aya 4.)
Wannan riwaya tana nuna halin da al’ummar musulmi take ciki bayanan kashe Imam Hussaini (a.s). yanayi ne mai ban tsoro, na fatattaka da raunin zuciya wanda ya game al’ummar musulunci a lokacin da waccan waki’ar ta faru, abin takaicinda ya auku a Karbala al’ummar har ma shi’ar Ahlulbaiti, ya fadi warwas. Wadannan ‘yan shi’an da suka gamsu da alaka da Imamai a zuci kawai amma a aikace sun karkata wa duniya da jin dadinta da kelkelinta. Irin wadannan suna nan tsawon tarihi hatta a zamanin nan namu, ba kuma kadan suke ba.
Daga cikin dubban masu da’awar shi’a a zamanin Imam Sajjad (a.s) mutum uku kadai suka rage bisa tafarki, mutum uku ne razanarwar Ummayawa da kamun da hukuma ke yiwa mutane bai sa su firgita ba, kuma son kubuta daga neman zaman lafiya bai girgiza azamarsu ba. Sun ci gaba da amsa kira da fama bisa wannan tafarki da cikakkiyar azama da tabbata. Guguwar da ta kwashi al’umma tamkar wasu zauna gari-banza suka kuma bi manufar azzalumar hukuma, ba ta kwashi wadannan mutanen ba. Dayansu watau Yahya ibn Ummi Dawil ya kan mike a masallacin Madina ya yi huduba wa masu da’awar wilaya ga Ahlulbaiti yana mai baiyana bara’a gare su, kamar yanda ya gabata, yana kafa hujja da abin da Annabi Ibrahim (a.s) da mabiyansa suka fada wa masu bijirewan zamaninsa “ Mun fita batunku kuma kiyayya da jiyewa juna sun bayyana a tsakaninmu.” Ibn Ummi Dawil ya karanta wannan aya mai girma gaba ga masu da’awar wilaya ga Ahlulbaiti ne domin ya baiyana cikakken rabewa tsakanin sassan guda biyu:sashen ma’abota sako masu lizimta da kuma sashen masu zaman dirshan da sassautowa zuwa burace-buracen da basu taka kara sun karya ba da kuma rudi da abin duniya mara kima. Wannan rabewa tana tare da dukkanin kiraye-kirayen addini. Imam Sadik ya sifanta wannan rabewa na sassan biyu da cewa:- (Wanda ba ya tare da mu, to yana adawa da mu). Watau wanda duk ba ya sashen tauhidi to yana bangaren dagutu, babu wata ma’ana ga zama dan ba ruwanmu domin kuwa ba wani yankin tsaka-tsaki.
Wannan musulmi mai wilayar gaskiya ga Ahlulbaitin Manzon Allah (s.a.w.a) watau Yahaya bn Ummi Dawil, da wannan kiran nasa ya baiyana rabewa tsakanin masu gamsuwa da wilayar da ta takaita ga motsin rai alhali suna kwanto cikin abubuwan amfanin kansu, suna nitse cikin dattin kuntataccen zatinsu,da masu lizimtar Imam a tunani da kuma aiki. Bisa dabi’a wannan rabewa tana nufin wuce gaban cewa batattun masu rinjaye su janye mutum, amma ba tana nufin watsi da batattun ba. Da wannan fikira ne wannan salihar jama’a ta fuskanci aikin tsamar da duk wani mai iya ‘yantuwa daga wahala da kangi. Sannu a hankali, sai wannan jama’a mai jihadi da dauriya ta yawaita, kuma da wannan ne Imam Sadik (a.s) yake ishara yayin da ya ce: “…… daga bisani sai mutane suka dawo suka yi yawa” Ta haka ne Imam Sajjad ya ci gaba da ba da himma kan aikinsa. Wannan aikin da wadansu matsayin da Imam ya dauka, wadanda za mu ambato nan gaba yana daga cikin abubuwan da suka janyo shahadarsa da ta wasu daga mukarrabansa.
Ban ga wani bayyanannen sa-in-sa da hukuma a rayuwar Imam Sajjad (a.s) ba. Kamar yanda muka ambata, hakan shi ne abin da ya dace da hikima. Domin da ya dauki irin matsayin da muke gani a rayuwar Imam Musa ibn Ja’afar (a.s) da imaman da suka biyo bayansa dangane da mahukuntan zamaninsa da bai iya ciyar da aikin sauyi gaba har ya samar wa Imam Baqir (a.s) damar mayalwacin aiki ba. Da yayi haka da an hallaka shi da salihar jama’ar da take tare da shi.
Ba mu iya tsinkayar ra’ayin Imam na hakika dangane da masu iko illa nadiran, ko a nan ma bai kai matsayin fito-na fito ba. Iyaka dai yana tabbatar da wani matsayi wa tahiri yana kuma fadakar da jama’ar da take kusa da shi kan abin da ya shafi aikinsa da harakarsa gwargwado. Irin wadancan matsayi sun hada da takardar suka mai tsanani da Imam da aikewa wani malami mai alakar kut-da-kut da Banu Umayya watau Muhammad bin Shihab Azzuhri. Muna iya fahimta a takardar cewa Imam yana magana ne da tsararraki masu zuwa tsawon zamani, ba da Azzuhri ba saboda Azzuhri ba mutumin da zai iya yantuwa daga kangin liyafar Banu Umayya da wasanninsu da mukamansu da al’farmarsu ba ne.Tahiri ya tabbatar da hakan, domin kuwa Azzuhri ya gama rayuwarsa ne cikinsa hidimarsu tare da rubuta littafi da kuma kirkirar hadisai saboda neman kusanci da su [9]
Saboda haka takardar Imam tana bayyana matsayinsa kan yanayin zamaninsa ne. Nassin wannan wasika yana nan cikin littafin Tuhaful Ukul.[10]
Akwai kuma wasikar da Imam ya aikewa Abdulmalik ibn Marwan a matsayin jawabi kan wata wasikarsa wacce take dauke da aibantawa ga Imam saboda ya auri wata baiwar da ya yanta. Abin da Abdulmalik yake son baiyanawa Imam (a.s.) shi ne yana sane da duk abin da yake aikatarwa hatta al’amuran da suka kebance shi. Kazalika yana nufin tunatar da Imam (a.s) da dangantakarsa da shi da zimmar jan hankalinsa.
A jawabin da ya rubuta, Imam ya baiyana ra’ayin musulunci a kan wannan mas’ala yana mai takidin cewa fifikon imani da musulunci ya kore kowani fifiko. Sannan ta hanyar kinaya, mai gwanin kyau, imam yayi ishara da hali rin na jahiliyya wanda iyayen halifa suka rayu a kai, la’alla ya hada har da rayuwar halifan shi kan shi. Ya ce: “ Babu karanta ga musulmi, karantar jahiliyya ce kawai karanta”.
Da halifa ya karanta kalmomin Imam (a.s) ya fahimci ma’narsu,cikakkiyar famta,kamar yanda dansa Sulaiman ya tsinkayi ma’anar yayin da ya ce da mahaifinsa: “Ya Shugaban Muminai alfaharin da Ali bn Hussaini ya yi hakika ya yi tsanani!” Saboda gogewarsa ta siyasa,halifa sai ya amsa wa dansa da abin da zai nuna masa cewa ya fi shi sanin abin da karo da imamin shi’a zai hafar. Ya ce da shi: “Da na kada ka fadi haka,domin wadannan harsunan Bani Hashim ne masu tsaga dutse, masu kamfata daga teku. Da ma ai Ali ibn Hussaini yana bayyana daukakarsa a yanayin da sauran mutane suke fankamar mika wuya.”
Wani misali mai nuna matsayin da Imam ya dauka shi ne yin watsi da wata bukatar Abdulmalik bin Marwan. Abdulmalik ya sami labarin cewa akwai takwabin Manzon Allah (s.a.w.a) wurin Imam sai ya aiko yana neman ya ba shi kyautarsa ya kuma yi barazanar yanke abin da ake baiwa Imam daga baitul mali.Sai Imam (a.s) ya rubuto masa:-
((Bayan haka, Lallai Allah ya lamunce wa masu tsoronsa mafita ta inda suke ki, da arziki ta inda basu tsammani. Mai girman ambato ya ce (Lallai Allah ba ya son duk wani mai tsananin ha’inci mai yawan kafirci), sai ka duba ka gani wane ne daga cikinmu ya dace da wannan aya?[11]))
A wasu wurare muna ganin Imam Sajjad (a.s) yana motsawa cikin natsuwa da kuma garkuwa da tarbiyar dai-daiku da gina mutumtaka ta musulunci bisa karantarwar mazhabin Ahlulbaiti da yaki da baude-baude da sauransu. Da wannan aikin ne bisa hakika, ya dauki matakin asasi na farko a kan tafarkin tabbatar da manufar mazhabin Ahlulbaiti wanda ita ce kafa jama’ar musulunci karkashin inuwar salihar hukumar musulunci bisa misalin hukumar Manzon Allah (s.a.w.a) da Ali bin Abi Talib (a.s). Kuma kamar yanda muka ambata Imam (a.s) da mabiyansa basu nemi daidaitawa da hukuma mai kamu da azabtarwa ba duk da cewa sun bi hanyar da a zahiri tana daidaitawa da hukuma.
Daga cikin mabiyansa akwai wadanda aka kashe ta kazamar hanya, wasu an daure wasu kuwa an kore su nesa da mutanensu da gidajensu. Imam da kansa a kalla sau daya an tusa keyarsa a cikin kangi a cikin halin torartawa da wahala daga Madina zuwa Sham, sau da yawa kuma ya fada cikin nau ‘o’ in cutarwa da azabatarwa. Daga karshe halifan banu Umayya, Walid bin Abdulmalik ya ciyar da shi guba. Imam (a.s) ya yi shahada a shekara ta 95 bayan hijira.

Rayuwar Imam Bakir (a.s) Zarcewar Irin Rayuwar Imam Sajjad An wayi gari mabiya Ahlulbaiti sun zama wata jama’a fitacciya mai dogaro da kai, kirar Ahlulbhaiti kuwa wacce ta dan tsaya ta kuma boye bayan shamaki mai kauri a dalilin waki’ar Karbala da waki’o’in da aka zubar da jini da suka biyo bayanta kamar waki’ar Harra da tawayen Tawwabun wadanda fir’aunancin Umayyawa ya haifar ta zama samamma ce mai yaduwa ta kuma bayyana cikin da yawa daga yankunan daular musulunci, musamman a Iraki da Hijaz da Kurasan. Tare da wannan samuwa, ta haifar da tsari na tunani da kuma aiki. Kwanakin da Imam Sajjad (a.s) ya sifanta da cewa : “ mabiyansa ba su wuce ashirin ba” sun kau sai ga Imam Bakir (a.s) yana shigo masallacin Ma’aiki (s.a.w.) a Madina jama’a mai yawa daga mutanen Kurasan da sauran lardunan duniyar musulmi suna kewaye shi, suna tambayarsa hukuncin musulunci kan al’amuran rayuwa dabam-dabam. Mutane kamarsu Dawus Yamani da Katada ibn Da’ama da Abu Hanifa da wadansu daga shugabannin mazhabobin fikihu suna tahowa domin su sha daga ilmin Imam ko kuma su yi jayayya da shi kan al’amura dabam-dabam.
A wannan zamanin an sami mawaka masu kare mazhabin Ahlulbaiti da bayyana manufofinsa. Daga cikinsu akwai Kumait wanda ya sauwara mafi kyan surar da kwararru ke zaiyanawa a kan wilaya ta tunani da kauna ga mutanen gidan Manzon Allah (s.a.w.a) cikin kasidarsa mai suna hashimiyya. Hakika harsuna basu gushe ba suna nakaltar wadannan gwalagwalan wake yayin da zukata suke kiyaye su.
Ta wata fuska kuwa halifofin Banu Marwana cikin wannan dan lokacin, sun sami wata natsuwa da tabbatar mulki bayan Abdulimalik ibn Marwan (m.86H) cikin shekara ashirin da ya yi mulki, ya murkushe dukkan masu ja da mulkinsu, kuma yiwuwa cewa sansancewar aminci da natsuwa da halifofin Marwaniyawa na wannan lokacin ya samo asali ne daga kasancewar sun sami mulki tamkar wata ganima, sabanin magabatansu wadanda suka yi jan aiki kafin su kai ga mulki. Wannan natsuwa ta sa halifofin baya shagaltuwa da wasanni da jin dadin duniya, tadodin da galibi suke tare da mai jin iko da alfarma da kuma girma. Ko mene ne ma dai, damuwar halifofin Banu Marwan da lamarin mazhabin Ahlulbaiti ta ragu a wancan lokacin, sai ga Imam da mabiyansa suna rayuwa kusan a ce cikin aminci daga farautar hukuma. Bisa dabi’a, Imam zai ci tafiya mai yawa kan tafarkin tabbatar da manufofin mazhabin Ahlulbaiti a irin wannan yanayi ya kuma kai shi’anci wani sabon zango. Wannan kuwa shi ne ya bambanta rayuwar Imam Bakir (a.s) da ta saura. Ana iya takaita abin da rayuwar Imam, cikin shekaru goma sha tara na imamancinsa (95-144H) ta kunsa kamar haka:-
Yayin da mahaifinsa Imam Sajjad (a.s) ya zo cikawa ya yi wasici da cewa dansa Muhammadu ya zama Imami bayansa, gaba ga sauran ‘ya’yansa da danginsa, ya kuma ba shi wani akwati. Riwayoyi sun ce akwatin cike yake da ilmi, sun kuma ce akwai makamin Manzon Allah (s.a.w.a) a ciki. Imam Sajjad (a.s) ya ce:- “Ya kai Muhammadu wannana akwati ka tafi da shi gidanka” Sannan ya ce:- “Hakika babu dinari ko dirhami a ciki, sai dai cike yake da ilmi”[12]
La’alla wannan akwati wata alama ce mai muna cewa Imam Sajjad ya mikawa dansa jagorancin tunani da ilmi (tunda yana cike da ilmi) ya kuma mika masa nauyin jagorancin juyi (tun da yana kunshe da makamin Annabi (s.a.w.a)).
Gami da farawar Imam da mabiyansa faffadan aikinsu na yada koyarwar Ahlubaiti (a.s) farfajiyar yaduwar kiran ta kara fadi, ta sami sababbin fuskoki wadanda suka zarce fagenta daya gabata a Madina da Kufa. Sai ga ta tana yaduwa cikin larduna manisanta daga cibiyar mulkin Umayyawa. Lardin Kurasan na daga cikin wadancan wurare kamar yanda riwayoyin tahiri suka nuna.[13]
Yanayin tunani da zamantakewa mai kaskanta mutane ya zaburar da Imam da mabiyansa wajen haraka mai dorewa ba tare da gajiya ko kosawa ba domin sauya wannan mummunan yanayi da tabbatar da abinda Ubangiji ya wajabta na kawar da wannan baudiyar.
Suna ganin mafiya yawan mutane sun rusna wa gurbatanccen yanayin da Banu Umayya suka yada, suka nitse cikin kazantar abin duniya iya wuya har suka wayi gari tamkar mahukuntan nasu,basu fahimtar zance, kunnensu bai jin nasiha. “Idan mum kira su ba sa amsa mana”.[14]
Ta wata fuska kuwa, Imam da jama’arsa suna ganin bincike-binciken fikihu da ilmul kalam da hadisi da tafsiri na karkata ne wajen dadada wa fir’aunancin Umayyawa da bin sonransu. Saboda haka duk hanyoyin dawowar jama’a kan katari da sun toshe, ba don zaburar mazhabin Ahlulbaiti wajen bayar da wajibinsa ba idan kuwa muka kyale su ba za su shiriya ta hanyar waninmu ba[15]
Mazhabin Ahlulbaiti ya yi Allah wadai da malamai da mawaka da suka sayarda kansu. An yi wannan sukan ne saboda kokarin farkarda zukatan wadancan malaman ko kuma zukatan mabiyansu. Imam yana fadawa Kumait, sha’irin Ahlulbaiti, da lafazin suka:- yabon Abdulmalik kayi?
Ya ce:- Ban ce da shi ‘ya shugaban shiriya’ ba, abin da na ce shi ne ‘ya zaki’ zaki kuma kare ne, ‘ya rana’ rana kuwa jamadatu ce, ‘ya kogi’ kogi kuwa mataccen abu ne, ‘ya maciji’ maciji kuwa kwaro ne mai wari, ‘ya tsauni’ tsauni kuwa kurman dutse ne. Sai Imam ya yi murmushi. Kumait sai ya rera wannan baitin gaban Imam:- Zuciyar da so ya tsare ya aure? Ban da yaranta tasa har da guri, Wannan mimiyar ta kafa mararraba tsakanin alkiblar Alawiyya da ta Umawiyya a daraja da kuma halaye ta hanyar dawwamammar zaiyanawa mai kyan gaske.
Wata rana Ikrima almajirin ibn Abbas wanda yake sananne ne, mai matsayin ilmi a cikin al’ummar wancan zamanin ya je yin mukabala da Imam sai haibarsa da natsuwarsa da ruhinsa da tunaninsa suka kama Ikrima. Abin da kadai ya iya fada shi ne:- “Ya dan Manzon Allah hakika na zauna gaban Ibn Abbas da waninsa sau da yawa amma irin abin da ya same ni yanzu bai taba samu na ba”. Sai Imam ya amsa masa da cewa:- “(Kai kana gaba ga gidaje wadanda Allah ya yi wa daukaka kuma ake ambaton sunansa a cikinsu)[16]
Ta wandansu fuskoki daban na ayyukan mazhabin Ahlulbaiti a wannan zangon kuwa, akwai jerin zalunci da fir’aunanci da kisa da azabtarwa da kora, da suka kewaye Ahlulbaitin Manzon Allah da mabiyansu ba don komai ba sai domin kokarin da suke yi na iza matacciyar zuciyar mutane da girgiza rayukansu wadanda suka yi sanyi da zaburar da kwantacciyar azamarsu da shiryar da su zuwa harakar juyi.
Alminhal bin Umar ya ruwaito cewa:- “Na kasance ina zaune tare da Muhammad bn Ali Albakir (a.s) sai wani mutum ya taho ya ce da shi: Yaya kuke? Sai Imam Bakir(a.s) ya ce:- “Lokaci bai yi ba da za ku san yanda muke? Misalinmu a wannan al’umma tamkar Bani Isr’a’ila ne a da,ana yanka ‘ya‘ya maza ana barin (raya )mata. Ka saurara! Lallai wadannan suna yanka ‘ya‘yanmu maza suna barin ‘ya ‘yanmu mata. Larabawa sun yi da’awar fifiko bisa baibayi. Sai baibayin suka ce: ‘Mene ne dalilin haka?’ Sai suka ce: “Muhammadu balarare ne daga gare mu” Sai suka ce da su: “Kun yi gaskiya.” Kuraishawa kuwa suka yi da’awar cewa suna da wani fifiko bisa sauran larabawa. Sai sauran larabawa suka ce “Mene ne dalili?” Sai suka amsa da cewa: ‘Muhammadu bakuraishe ne’. Suka ce da su: ‘Kun yi gaskiya’. Idan mutanen nan sun yi gaskiya, to muna da fifiko bisa mutane domin mu zuriyar Muhammadu ne, mutanen gidansa kuma makusantansa masu kebanta da shi, waninmu ba ya tarayya da mu a wannan” Sai mutumin ya ce da Imam; “Wallahi ni ina son ku, ku Ahlulbait”. Sai ya ce da shi: “To ka dauki bala’i a matsayin riga, domin kuwa wallahi shi (bala’i) ya fi kusa da mu da kuma shi’armu bisa ga gudanar igiyar ruwa a cikin kwari. Da mu bala’i zai fara sanan ku”[17]
Da ganin alamar cewa mutumin ya girgiza saboda zaburarwar da ya ji sai Imam ya yi maza ya zana masa tafarkin kiran, ya fayyace.Shi dai tafarki ne wanda aka shimfida shi da jini da kwalla, Imam kuwa shi ne madugun tafiyar, bala’i yana samunsa da farko kafin ya kai ga shia’rsa.
A tsakanin shi’arsa alakar Imam tana da wadansu sifofi kebantattu. Za ka gan shi cikin mabiyansa tamkar yanda kwakwalwa take a tsakanin gabban jiki yana ciyar da ruhinsu yana karfafa masu haraka da himma ba tare da yankewa ba. Akwai hujjoji a hannunmu wadanda suke bayyana wannan alaka mai ba wa mabiya manufofi da karantarwa mabayyana da kuma tsara al’amuransu bisa tafarki hadadde, lasaftacce.
Misali; A farkon haduwar Jabir Alju’fi da Imam Bakir(a.s) sai ya masa wasiyya da kada ya fada wa kowa cewa daga Kufa yake ya kuma yi fita irin ta mutanen Madina .Da wannan Imam yake koyar da darasin rike sirri ga wannan sabon dalibi wanda ya ga alamun iya rike sirri tattare da shi. Wannan dalibi mai cancanta sai ya zama ma’abocin sirrin Imam. Tsakaninsa da hukuma kuwa lamarin ya kai ga abin da Nu’man bin Bashir ya ce:-
“Ina mai lizimtar Jabir bin Yazid Alju’fi yayin da muke Madina sai ya shiga wurin Abu’far (a.s) ya yi masa bankwana ya fito yana farin ciki. (Muka kama hanya) har muka isa Al’ukairaja, daga kewayen Madina, a ranar Juma’a. Muka yi salla. Mun kama tafiya kenan sai ga wani mutum dogo mai duhun fatar jiki da wasika a hannunsa. Sai Jabir ya karbe ta ya sunbace ta yasanya ta kan idanunsa. Sai ga shi a rubuce(( Daga Muhammad bin Ali ( Bakir) zuwa ga Jabir bin Yazid)), ga kuma danyen bakin yumbu a kanta. Sai ya ce da shi: ‘Yaushe rabonka da shugabana?’ Sai mutumin ya ce: ‘Dazun nan; sai ya ce: ‘kafin salla, ko bayan salla? Sai ya ce : ‘Bayan salla.’ Sai ya warware hatimin ya ci gaba da karantawa, yana daure fuska har ya kai karshenta, sannan ya nade ta. Daga nan ban sake ganinsa yana dariya ko farin ciki ba har muka isa Kufa”.
Numan ya ci gaba da cewa: “Mun isa kufa cikin dare, kashegari sai na tafi wajen Jabir Alju’fi saboda girmama shi, sai gashi ya fito bisa dokin kara yana rataye da wadansu kulle-kulle, tamkar yanda mahaukata ke yi, yana rerawa kamar haka: ‘Na san Mansur mutumin mutane; Mai umurni ba’a umurtansa’ da wasu baitoci irin wannan. Sai ya kalli fuskata na kalli tasa amma bai ce da ni komai ba, ni ma ban ce masa komai ba. Sai na juya ina kuka saboda abin da na gani. Sai jama’a, babba da yaro, suka kewaye mu. Sai ya tafo har ya shigo dandali, ya kama zagawa tare da yara mutane na cewa Jabir bin Yazid ya haukace. Wallahi bayan ‘yan kwanaki sai ga takardar Hisham Ibn Abdulmalik an aiko ta gare ni kan batun shi. Tana cewa: ‘Ka binciki wani mutun mai suna Ja’bir Ibn Yazid Alju’fi ?’sai mutane suka ce: ‘Allah ya kiyaye ka’. Da mutun ne mai ilmi da daraja da sanin hadisi, ya yi aikin haji sai ya haukace. Shi ne wancan a dandali bisa dokin kara yana wasa da yara. Sai na ce: “Godiya ta tabbatar ga Allah wanda ya hutar da ni kisansa’.[18]
Wannan misali ne na alaka tsakanin Imam da mabiyansa na kusa. Yana bayyana tsananin tsari sa alaka kazalika yana nuna wani misali na matsayin hukuma kan mabiyan Imam. Wannan yana tabbatar mana cewa, masu iko ba cikin cikakkiyar gafala dangane da alakar Imam da mabiyansa na kusa suke ba, a’a, suna sa ido kan wadannan alakoki, suna kokarin gano su da kuma yin fito-na-fito da su.[19]
Sannu a hankali bangaren fito-na fito a rayuwar Imam Bakir (a.s) da ta shi’a yana tabbatar da wani fasali na rayuwar Ahlulbaiti (a.s).
Nassoshin tarihi da riwayoyin hadisi wadanda suke hannunmu basu faiyace samuwar wata matsananciyar harakar fama a siyasance wacce Imam yake aiwatarwa ba. Wannan rashin bayyanannar fama yana da dalilai, kamar su wanzuwar wani yanayi na jabberanci da azabtarwa mai mamaye da rayuwar al’umma, abin da ya tisalta wa mabiyan Imam wadanda su kadai ne masu masaniya kan rayuwarsa ta fuskar siyasa da su yi riko da takkiya. Sai dai martani matsananci wanda magabta (hukuma) suke mayarwa yana nuni da aikin jihadi mai zurfin tasiri da ake yi. Yayin da karfin mulki iri na Abdulmalik Ibn Marwan,wanda ake daukarsa a matsayin mafi karfin sarakunan Umayyawa, yayin da yake daukar mafi tsanani da tsaurin mataki kan Imam Bakir, ba wata tantama, wannan yana nuna cewa halifan yana jin tsoron hadarin da harakar da Imam da mabiyansa ke gudanarwa take tattare da shi ne. Da a ce Imam ya shagaltu ne da aiyukan ilmantarwa kadai ba tare da ya ba da himma kan gina tunani da tsare-tsare ba, to da sai mu ce ba maslaha ce ga masu mulki ba su matsawa Imam din lamba domin wannan mataki yana iya sa wa shi da mabiyansa su dauki matsayin fushi matsananci tamkar wanda mai tawayen nan ba’alawe Shahidin Fakh, watau Hussain bin Ali ya dauka.
A takaice, ana iya fahimtar matsanancin matsayin da hukuma ta dauka dangane da Imam Bakir (a.s) ta fuskar mayar da martanin da take yi kan aiyukan Imam masu sabawa da ra’ayin masu iko.
Daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a karshen rayuwar Imam Bakir (a.s) akwai kiransa da aka yi zuwa hedkwatar halifancin Umayyawa watau Sham (Dimashka). Halifofin Umayyawa sun yi niyyar bincikar matsayin Imam kan hukuma. Wannan ya sa suka yi umurni da kama shi da kuma kai shi Sham cikin cikakken tsaro. A wasu riwayoyi an ce wannan umurni ya hada har da dansa matashi watau Ja’far Sadik.
An kawo Imam fadar halifa. Kafin haka Hisham ya yi wa jama’arsa shiftar yanda za su fuskanci Imam yayin da yake shiga. Abin da ya shirya shi ne, shi halifa zai fara bijiro da tuhumce-tuhumce kan Imam sannan jama’a su ci gaba.
Abubuwa biyu yake da niyyar cimmawa: na farko shi ne raunana azamar Imam da sanya masa rashin yarda da kai. Na biyu: Kokarin sukar Imam a cikin taron da ya hada jagaban jama’ar halifanci da kuma na Imamanci a waje guda, sannan daga bisani a yada wannan cin zarfin ta hanyar kakakin fada kamar masu jawabi da masu wa’azin sarki da kuma ‘yan laken asiri, kuma da haka ne Hisham yake fatar samawa kansa nasara kan abokin hamayyarsa.
Da Imam ya shigo fadar halifa, sabanin yanda masu shigowa suka saba da yin gaisuwa ga halifa da sunan shugaban muminai, sai ya fuskanci dukkan mahalarta yana mai nuni ga ilahirinsu, ya ce: assalamu alaikum. Sannan ba tare da jiran izinin zama ba sai ya yi zamansa.
Wannan abin da Imam ya aikata ya cinna wutar hasada da kufe a zuciyar Hisham. Nan take sai ya fara jefa muggan maganganu yana cewa: ‘ Ya Muhammad Ibn Ali ba’a gushe ba wani daga cikinku yana rarraba kan musulmi, yana kiran mutane da su bi shi, yana kuma da’awar shi ne Imami (shugaba ) saboda wauta da karancin sani ………[20]Ya dai ci gaba da sukar sa.


2
JAGORANCIN IMAM SADIK (a.s) Bayan Hisham ya gama sai jama’a suka karba, suka ci gaba da maimata wadannan tuhumce-tuhumce da soke-soke. A tsawon wannan lokaci Imam uffan bai ce ba, yana sunkuye da kai cikin natsuwa, yana jiran damar ba da amsa. Yayin da mutanen nan suka kare duk abin da ke gare su, wuri ya yi tsit, sai Imam ya mike ya fuskanci jama’a, ya yi yabo ga Ubangiji ya yi salati ga Manzonsa (s.a.w.a) kana ya yi jawabi.
Wannan jawabin ya kunshi kalmomi ne matakaita masu kwankwasa tare da bayyana rauni da kuma sakar akala tamkar kumaki wanda wadancan ‘yan amshin Shatan suka yi. Kazalika ya nuna matsayi da daukaka da Ahlulbaiti suke da shi, kamar yanda ma’aunan musulunci suka tabbatar, ya kuma wulakanta duk abin da halifa da jama’arsa suka mallaka na kazamar dukiya da kuma iko. Ya ce:- ‘Ya ku mutane ina kuke tafe ne? Ina aka nufa da ku? Da mu Allah ya shiryi na farkonku kuma da mu ne zai cikata (shiryar da) na karshenku. Idan abin gaggautawa na mulki naku ne to (ku sani cewa ) abin da aka jinkirtar na mulki namu ne sannan kuma babu wani mulki bayan namu saboda mu ne ma’abota kyankkyawan karshe. Allah mai girma da daukaka yana cewa: “Kuma kyakkyawan karshe ya tabbata ga masu takawa”[21].
Wadannan kalmomi matakaita wadanda suka kunshi wawaitarwa da kokowa da zalunci, da albishiri da bazarana, da tabbatarwa da kuma raddi duk a lokaci guda, ba shakka masu girgizawa ne tare da sa mai sauraro yin imani da cewa mai fadarsu shi ne ma’abocin hakki. Sakamakon haka, Hisham sai ya ga babu abin da zai yi face umarni da a jefa Imam kurkuku. Imam Bakir ( a.s ) ya ci gaba da aikinsa na gyara hatta a cikin gidan kaso, al’amarin da ya yi tasiri matuka kan fursunoni. Da labari ya kai ga Hisham,sai ya ji tsoron cewa irin wannan farkawa za ta faru a hedkwatarsa wacce aka kiyaye daga tasirin Alawiyyawa. Sai ya yi umarni da fitar da wannan fursunan (Imam Bakir) tare da wadanda suka dauki ra’ayinsa da kuma aika su da daggawa zuwa Madina wanda shi ne mazaunninsa. Umarnin ya hada da cewa idan sun kama hanya kada kowa ya yi wata hulda da wannan ayari wanda halifa yake fushi da shi. Kada a ba su guzurin abinci ko ruwan sha.
Bayan kwana uku ana tafiya ba kakkautawa abinci da ruwan da yake tare da su sai ya kare, a wani birni da ake kira Madin. Saboda umarnin Hisham, mutanen sun kulle kofifin birnin suka kuma ki sayarwa wadannan bayin Allah da komai. Yunwa da kishi suka yi wa mabiya Imam tsanani. Sai Imam ya haura kan wani tudu wanda daga bisan shi ana iya hangar cikin birnin ya daga murya da kyau ya ce:- “Ya ku mutan garin da mutanensa suka yi zalunci! Ni ne falalar Allah mai wanzuwa Allah yana cewa”:- Falalar Allah mai wanzuwa (bakiyyatul lahi ) ita ce mafi alheri a gare ku idan kun kasance muminai, kuma ni ba mai tsaro ne a kanku ba”.
Mai riwaya ya ci gaba da cewa: Akwai wani tsoho tukuf a wannan birni, wanda ya ce da su: ‘Mutanena, wallahi wannan kira ne irin na Annabi Shu’aibu ( a.s). Na rantse da Allah idan ba ku fita kuka sayar wa wannan mutumin (abin da yake bukata) ba za’a kama ku daga birbishinku da kuma karkashinku. To lallai ku gaskata ni kuma ku bi maganta, domin ni mai nasiha ne a gare ku’.
Mutanen garin sai suka amsa kiran dattijon nan, suka fita da gaggawa suka sayar wa Abu Ja’afar (Imam Bakir (a.s)) da sahabbansa da abin da suke bukata.[22]
Karshen wannan ruwaya yana nuna mana irin dirar da halifan Abbasiyawa yake yi kan mutane da kuma jabberancinsa. Bayan mutanen birnin sun budewa Imam da sahabbansa kofofin gari sai aka rubuta dukkan abin da ya faru aka aike wa Hisham. Sai ya aiko da takarda zuwa hakimin Madin da umarnin cewa ya kama wancan dattijon ya kashe. Allah ya ji kansa da rahama![23]
Tare da wannan hali, Imam yana nisantar duk wani matsanancin fito-na-fito da yin gaba da masu mulki. Ba ya daukar takobi ba ya kuma yardarwa masu garaje zare tokobi, yana dai shiryar da su ta hanyar hikima. Takobin harshe ma Imam ba ya zarewa idan ba aikinsa na gyara da sauyi daga tushe ya bukaci hakan ba. Kuma bai yardar wa dan uwansa Zaid, wanda fushi da motsin rai ya kai masa iya wuya, yin tawaye ba. A ‘a, shi dai aikinsa yana ba da karfi ne wajen shiryarwar da wayar da kai da tunani, hakan kuma gina tushen manufa (aidiyoloji) ne tare da kula da takiyya a siyasance.
Sai dai wannan salon bai hana Imam ya bayyana wa mabiyansa “harakar imamanci” ba, kamar dai yanda muka yi nuni da shi, bai kuma hana shi karfafa musu babban burin shi’an nan na kafa sahihin tsarin siyasa mai bin tafakarkin Imam Ali (a.s) ba. Wani lokaci ma yana tunzura zukatansu gwargwadon bukata saboda raya wannan burin.
Daya daga hanyoyin da Imam Bakir (a.s) yake kwadaitar da mabiyansa ita ce ishara ga zamanin mai haske wanda zai zo nan gaba. Wannan kuma yana nuna yanda Imam (a.s) ya kwatanta zangon da yake raye a harakar imamanci. Hakam ibn Uyaina yana cewa: wata rana ina tare da Abu Ja’far (a.s) alhali gidan na cike makil da mutanen gidansa sai ga wani dattijo ya tafo yana tokarawa da mashinsa har ya tsaya bakin kofa ya ce:
Aminci da rahamar Allah da albarkarsa su tabbatar gare ka ya dan Manzon Allah (watau ya yi sallama). Sannan ya yi shiru. Sai Abu Ja’far ya amsa masa: Aminci ya tabbata gare ka da rahamar Allah da albarkarsa. Sai dattijo ya fuskanci mutanen gidan ya ce: assalam alaikum, sannan ya saurara har jama’a suka amsa sallama gaba dayansu. Sai ya fuskanci Imam ya ce: “Ya dan Manzon Allah ka kusantar da ni gareka, Allah Ya sanya ni fansarka. Wallahi ni ina kaunarku, ina kuma kaunar mai kaunarku. Kuma wallahi ba na son ku tare da son mai son ku saboda kwadayin abin duniya. Kuma ni ina kin mai gaba da ku ina kubuta (bara’a) daga gare shi. Kuma wallahi ba na kin shi ina kubuta daga gare shi domin wata kullalliya da ke tsakaninmu. Wallahi ni ina halatta abin da kuka halatta shi, ina haramta abin da kuka haramta shi ina sauraron umarninku. To shin kana mini tsammanin (alheri ),Allah ya sanya ni fansar ka? Sai Imam ya ce: “ Taho nan, taho nan” ya zaunar da shi gangarsa sannan yace:-
‘Dattijo! Lallai wani mutum ya zo wa babana Ali bin Hussain (a.s) ya tambaye shi tamkar abin da ka tambaye ni sai babana (a.s) ya ce da shi:- Idan ka mutu za ka zo ga Manzon Allah (s.a.w.a) da Ali da Hassan da Hussain da Ali ibn Hussaini, kuma za’a sanyaya zuciyarka, za ka ga farin ciki, za’a tarbe ka da hutawa da kyakkyawan abinci tare da Masu daraja, Marubuta ( kiramun katibuna ). Idan kuma ka rayu za ka ga abin farun cikin da Allah zai sanya ka ciki za ka kasance tare da mu cikin kololuwar daukaka”.
Cikin gigicewa saboda girman wannan albishiri,dattijo sai ya ce:`Ta yaya,ya kai Abu ja’far? Sai Imam ya maimaita masa maganar da ya yi. Sai tsohon nan ya ce:Allahu akbar! Ya Abu Ja’far idan na mutu zan zo wa Manzon Allah (s.a.w.a) da Ali da Hassan da Hussain da Ali ibn Hussaini, kuma zan ga abin farin ciki, a kuma sanyaya min zunciya, a tarbe ni da hutawa da kyakkyawan abinci tare da Masu daraja, Marubuta idan na cika? Idan kuma na rayu zan ga abin da zai faranta mini rai, kuma in zama tare da ku a kokoluwar daukaka?” Sai tsoho ya kama kuka sai da ya kai kasa. Yayin da mutanen gidan Imam suka ga yanayin da dattijon nan ya shiga sai su ma suka kama kuka. Sai dattijo ya daga kai ya nemi Imam ya mika masa hannunsa. Sai ya sumbanci hannun ya sanya shi kan idanu da kumatunsa sanan ya yi ban kwana ya fita. Imam yana kallonsa yana cewa:- Wanda ya so ganin wani mutum daga mutanen aljanna to ya dubi wannan (mutumin).[24]
Irin wannan fayyacewa tana karfafa ruhin buri a zukatan da suke rayuwa cikin yanayin zalunci da danniya, ta kan wanzar da tunkudawa zuwa ga manufar da ake bida wacce ita ce kafa adalin tsari na musulunci.
Shekara goma sha tara na imamanci Imam Bakir (a.s) aka yi aiki na gudana bisa wannan mikakken layi mabayyani. Shekara goma sha tara na koyarwa kan manufar gini da dabarun kare kai da tsare-tsare da kare haraka da takiyya da karfafa ruhin sa-rai da sauransu.
Shekara goma sha tara ana gudanar da wannan tafiya mai tattare da kaya da munin hanya wanda yake bukatar kokari da ijtihadi mai yawa. Lokacin da wadannan shekaru suka kawo karshe, ranar rayuwarsa mai albarka ta zo faduwa, sai abokan gabansa suka yi ajiyar zuciya domin a zatonsu idan wannan jagora mai shiryarwa ya tafi za su huta da tushen farkarwa da izawa wanda ya dade yana hana su hutu da barci.
Amma hakan bai yiwu ba domin Imam ya tabar da burinsu ya kuma sa wannan dama ta kubuce musu saboda ya sanya wafatinsa ya zama tushen shiryarwa, musabbabin farkawa sannan kuma hanyar wayar da kai mai dorewa. Imam ya umarci dan sa Sadik(a.s) a karshen rayuwarsa, ya umarce shi da wani aiki wanda samfuri ne mai gwanin ban sha’awa daga samfur-samfur na takiyya da kuma salon kira wadanda Imam Bakir (a.s) ya yi amfani da su a zangon zamani wanda ya kebance shi . A cikin ruwaya daga Abu Abdillah Sadik (a.s) ya ce: ‘Babana ya ce da ni: Ka ware abu kaza daga dukiyata saboda a mini zaman makoki na tsawon shekara goma a Mina a ranakun Minan”.[25] ..Ita wannan ruwaya , wadanda suka yi bincike kan rayuwar Imam Bakir basu dube ta da kyau ba kuma sun gafala ga barin ma`anoni masu girma wadanda ta kunsa. Imam ya rasu ya bar dirhami dari takwas, yayi umarni da aware wani abu daga ciki a baiwa masu kukan mutuwarsa a Mina. Yin kukan rasuwar Imam a Mina ya kunshi ma`ana mai girma .Lallai shi aiki ne na raya tushen nan da ya kasance a ko yaushe yana watsa hasken wayar da kai da farkarwa da kuma sanya ruhin kamuji da gwagwarmaya.
Zaben Mina kuwa yana nufin wanzar da aikin a tsakiyar taron jama`a masu tahowa daga dukkanin sassan duniyar musulunci a dai dai lokaci guda daya tak da ake zaune wuri guda yayin aikin haji. Saboda dukkan ayyukan haji ana gabatar da su ne cikin halin motsawa ba tare da sararawa ba idan ba a Mina ba, inda ake kwana biyu ko uku, saboda haka alhazai suna samun isashshen lokaci domin sauraro da ganin kukan rasuwar Imam a wannan wuri zai kuma sa a yi tambaya kan ko wane ne wannan mamacin? Za’a kuma sami jawabi wajen mutanen Madina wadanda suka yi zamani da shi. Za su ce shi daya daga ‘ya’yan Manzon Allah ne, kuma shi ne malamin fukaha`u da masana hadisi. Za’a kuma tambayi dalilin da ya sa ake makokinsa a wannan guri, shin mutuwarsa ta bambanta da ta saura ne? To wane ne ya kashe shi ko ya sanya masa guba? Shin ya kasance wata barazana ga mulkin Umayyawa ne? Da dai sauran su. Gomonin tambayoyi aka yi ta jefowa yayin da ake kukan rasuwar Imam a wannan wuri, sannan masu tambaya suna samun amsa. Kuma labarin ya yi ta watsuwa cikin garuruwa, sako sako, bayan komawar alhazai kasashensu. Akwai kuma masu zuwa daga Kufa da Madina takanas saboda amsa wadannan tambayoyi da yada ruhin shi’a suna daukar damar taron musulmi, damar da ba’a samun tamkar ta a wancan lokacin.
Haka Imam ya rayu, haka kuma ya tsara al’amura domin abin da zai zo bayan wafatinsa. Tsira ta tabbata gare shi ranar da aka haife shi da ranar da ya yi jihadi da ranar da ya yi shahada a tafarkin Allah da kuma ranar da za’a tashe shi rayayye.
Imam Bakir (a.s) ya rasu yana da shekara hamsin da bakwai a duniya, a zamanin Hisham bin Abdulmalik, wanda yake daya ne daga sarakunan Banu Umayya wadanda suka fi iko. Duk da matsaloli da wahalhalun da suka addabi sarautar Banu Umayya a wancan zamanin wannan bai hana su aikata makida ga zuciyar shi’an nan mai bugawa, watau Imam Bakir, ba. Hisham ya yi ishara ga barorinsa cewa su sanya wa Imam guba, da haka ne kuma ya cimma burinsa na hallaka mafi hadarin abokan gabansa.

Jagorancin Imam Sadik (a.s) Imam Sadik (a.s) ya dauki nauyin ci gaba da wannan tafiya a cikin yanayi mai tsananin sarkakiya da wahala. Bore ya kunno kai a ko ina a daular musulunci, hakimai sun shagaltu da tara kazamar dukiya alhali ga annoba da fari sun aukawa yanki mai yawa wanda ya hada da Kurasan da Irak. Masu mulki kuwa suna tursasawa da zalunci ba tare da rahama ba ko kankani, da haka suke jefa mutane cikin halin kaskanci da mika wuya. Kuma galibi hadarin masu shagaltuwa da ilmomin musulunci kamar fikihu da hadisi da tafsiri bai kasa na ‘yan siyasa da mahukunta ba. Alhali kuwa su ake tsammanin zamansu mafaka ga mutane. Yawa yawan wadannan malamai na kawata fatawowi saboda dadada wa sarki da hakimansa. Da yawa daga cikinsu suna shagaltar da kansu da ma mutane da mas’alolin da basu taka kara sun karya ba, suna ta da jayayyar da ba bakin komai take ba cikin mas’alolin ilmul kalam kuma babu abin da ya danganta ta da musulunci ko wahalhalun da al’umma ke ciki.
Nauyin da ya rataya a wuyan Imam Sadik (a.s) a wannan yanayi mai duhu shi ne abin da muka ambata kan sha’anin nauyin imamanci.A takaice shi ne bijiro da ingantaccen tunanin musulunci, watau bayyana musulunci kamar yanda ya zo cikin Alkur’ani dasunnarMa’aiki(s.a.w.a) gami da yaki da dukkanin baude-baude da gurbatarwar jahiliyya mai bin son rai. Haka nan kuma da shirya dabarun kafa tsarin adalcin musulunci da kuma kare wannan tsarin yayin kafa shi.Duk wannan nauye-nauye guda biyu watau nauyin wanzar da tsarin tunani da nauyin tsarin siyasa suna matsayin wani hadari mai girma ne ga tsarin da yake mulki. Ba nauyin siyasa kadai yake tunzura fushin sarauta ba, a’a shi ma nauyin tsarin tunani wanda yake jifa da baudaddun tunane-tunane da manufofin da sarki da masu wa’azinsa ke gabatar wa al’umma da sunan addini, yana fusata ta. Wannan ya nuna cewa aikin kyautata tunani abin fifitawa ne domin yana kawar da karkatarwa da sunan addini wacce tsarin sarauta ke dogaro da ita wajen wanzarda zaluncin da yake yi wa jama’a. Ta wata fuska kuma yanayin da ake cikinsa a shirye yake ya saurari tunanin shi’a mai neman sauyi, domin yaki da talauci da danniya sabubba ne masu habaka ruhin sauyi, ga kuma share fage da ayyukan Imam Bakir (a.s) suka yi a yankuna dabam-dabam. Dabarar cimma manufar Imamanci a game ita ce yunkurin sauyin tauhidi irin na Imam Ali. Bukatunta su ne:-Na farko: Samarda wata jama’a wacce za ta dauki tunanin imamanci, ta yanda zai saje da ita, sannan ta zama mai begen aiwatar da shi.
Na biyu: Samar da wata jama’a tsararriya mai jihadi da sadaukarwa. Shi kansa cimma wadannan bukatu yana bukatar yada kiran gaskiya a sassan duniya da shirya zukata domin karbar tunanin musulunci mai ra’ayin sauyi a dukkanin wurare. Har ila yau yana bukatar wani kiran daban wanda zai tanadi daidaiku masu sadaukarwa da fana’i, wadanda za su zama mambobin shirin tsare-tsaren kiran na sirri.Wannan shi ne sirrin wahalar kira bisa tafarkin imamancin gaskiya. Saboda kira mai dauke da sako, mai zimmar kawar da dagutu da fir’aunanci da jabberanci da dagawa da zalunci a cikin al’umma tare da cewa tana riko da ma’aunan musulunci wajen ayyukanta dole ne ta yi dogaro da zabin (irada) talakawa da karfinsu da imaninsu da nunarsu. Sabanin kiraye-kirayen da suke dauke da taken yaki da masu dagawa alhali su ma suna aikata irin ayyukan dagutai da azzalumai, basu lura da dokokin kyawawan dabi’u da na halin zaman jama’a. Irin wadannan kiraye-kiraye basu fuskantar wahalhalun da kira mai dauke da sako, mai manufa, take fuskanta. Wannan shine sirrin rashin tabbatar manufofin harakar Imamanci cikin gaggawa, shi ne kuma sirrin samun nasara nan take na harakokin da suka yi hannun riga da harakar imamanci, kamar ta Banu Abbas.
Yanayin da ake ciki da shirin da ayyukan imamin da ya gabata (Imam Bakir) bai shafi takwabi ba. A’a shi yana tsayawa ne ta hanyar suka mai tsanani, sawa’un da salon aikin gyaran tunani ko na tsare-tsare ko kuma ta wata fuskar dabam, da nufin kwankwasar azzalumai da yakar su. A nan Imam Bakir (a.s) yana karfafawa kan ma’anar yukurin da Imam Sadik zai yi saboda aiwatar da babban nauyi wajen fuskantar mulki mai ci, kuma ba ya karfafawa kan sakamakon da ka iya biyowa baya. Kai a wata riwayar ma maganarsa kusan tana yanke kaunar samun nasarar harakar imamanci ne a cikin wannan yanayin siyasar da ake ciki.Daga cikin riwayoyin da a cikin su Imam Bakir (a.s) yake karfafawa kan rawar da Imam Sadik (a.s) zai taka akwai abin da Abu Sabah Alkinani ya ruwaito, ya ce: “Abu Ja’afar ya dubi dansa Abu Abdillah sai ya ce: ‘Kana ganin wannan? Wannan yana cikin wadanda Allah Ta’ala ya ce (game da su :Kuma muna nufin Mu yi falala ga wadanda aka raunanar a cikin kasa kuma Mu sanya su shugabanni, kuma Mu sanya su magada.[26]
La’alla wadannan fayyace-fayyacen Imam Bakir su ne suka yada tunanin yunkurin Imam Sadik (a.s) da halifancinsa a tsakanin ‘yan shi’a, ya kuma sanya sahabban Imam Bakir da Imam sadik(a.s) sauraron wata faraga daga lokaci zuwa lokaci. Akwai wata riwaya cikin Rijal na Shaikh Kashshi wacce a cikinta ana iya fahimtar wannan yanayi mai wanzuwa a tsakanin mabiya Ahlulbaiti a wancan lokacin. Ibn Miskan ya ruwaito daga Zurara cewa ya tambayi Abu Abdillah (a.s) batun wani mutum cikin abokanmu wanda yake buya saboda gudun tara. Ya ce: Allah ya kiyaye ka! Akwai wani mutum cikin abokanmu yana buya saboda gudun tara, idan wannan al’amari kusa yake zai hakura har ya fito tare da mai tsayawa, Idan kuma akwai jinkiri zai yi sulhu ( da mahukunta ) saboda gudun tara. Sai Abu Abdillah (a.s) ya ce: Zai kasance. Sai Zurara ya ce : Zai kasance nan da shekara? Sai Abu Abdillah ya ce: Zai kasance insha’allahu. Sai Zurara ya ce: Zai kasance nan da shekara biyu? Sai Abu abdillah ya ce: Zai kasance insha’allahu. Sai Zurara ya fita, sai ya kwallafa ransa kan cewa zai kasance nan da shekara biyu. Amma bai faru ba. Sai ya ce : Ban kasance ina ganin Jafar ba face ya fi haka sani.[27]
Kalamar ‘wannan al’amari’ a sanin mabiya Ahlulbaiti kinaya ce kan zamani mai zuwa wanda aka yi musu alkawarinsa, watau karbar ragamar mulki ko kuma tabbatar da abin da zai kusanta su da wannan, kamar juyin juya hali ta hanyar daukan makami. Kuma ‘Mai Tsayawa’ shi ne zai jagoranci wannan aikin.
A wata riwaya Hisham Ibn Salim wanda shi ma wani babba ne kuma sananne daga cikin shi’a, ya ambaci cewa Zurara ya ce da shi: “Ba zaka ga wani kan karagar shugabanci ba face Ja’afar.” Ya ce: Yayinda Abu Abdillah ya yi wafati sai na zo na ce masa (Zurara): Kana tuna labarin da ka bani? Na ambata masa shi, ina mai tsoron kada ya yi musun cewa ya fada mini. Sai ya ce: “Wallahi ni ban fadi waccar maganar ba face dama nawa ra’ayin ne(watau dama ba ya ruwaito maganar Imam ba ne)”.
Daga jumlar abin da ya gabata muna fahimtar cewa a ra’ayin babansa da na jama’a Imam Sadik (a.s) shi ne mai tabbatar da burin imamanci da shi’anci. Kuma silsilar imamanci ta riga ta yi tanadinsa domin tabbatarda kokarin Imam Sajjad da Imam Bakir(a.s) . Kamar dai shi ne ya wajaba a kansa ya dawo da ginin hukumar Alawiyya da tsari irin na tauhidi,watau ya wajaba ya aiwatar da wani sabon yunkurin musulunci. Imaman nan biyu da sauka gabata sun riga sun ci zango-zango masu wahala da kunci a kan wannan gwadabe, shi kuma sai ya ji da zangon karshe. Kamar yanda muka ambata, yanayi ya daidaita ga Imam kuma ya yi amfani da wannan dama wajen yukurin gabatar da sakonsa mai girma.
Tun lokacin da ya karbi nauyin shugabaci har zuwa wafatinsa, Imam ya dauki shekara talatin da uku yana jihadi maras yankewa. Cikin wadannan shekarun yanayi ya kasance yana sa kyakkyawar fata, wani lokacin kuma matsin lamba yana hawa da kuma sauka;wani zubi ya dace da maslahar mazhabin Ahlulbaiti, wani zubin kuwa yanayin ya juya akasin hakan. Wani lokaci halin yana sa kyakkyawar fata, wani lokacin kuma matsin lamba yana tsanani, har sahabban Imam su zaci cewa dukkan buri ya tarwatse. A duk wadannan halaye Imam Sadik(a.s) yana rike da ragamar jagoranci kyam tare da azama da jajircewa. Yana keta fagen nan mai rudani, mai tattare da tsammani da kuma yanke kauna, ba ya damuwa da komai sai tafiyar da ke gaba yana wanzar da kokari da karfin gwiwa da imani wa mabiyansa domin kaiwa ga tsira.
A nan ya zama wajibi mu yi nuni da wani al’amari mai ban takaici wanda dukkan masu bincike kan rayuwar Imam Sadik(a.s) suke fuskanta .
Wannan kuwa shi ne halin rashin tabbas wanda ya lullube shekarun farkon imamanci Sadik(a.s) wadanda suka yi muni daidai da karshen zamanin Banu Umayya. A lokacin rayuwa ba ta san natsuwa ba tana kuma cike da aukuwar manya-manyan al’amura,muna iya fahimtar alamunsu cikin daruruwan riwayoyi. Sai dai malaman tarihi da hadisi basu kawo mana labarin wannan lokacin a jere tare da sajewa da daganta wannan bayani da wancan ba. Saboda haka ya zama dole ga mai bincike ya yi dogaro da kuma lura da al’amura da suke baiyana cikin abinda yake karantawa (kara’in), ya lura da kungiyoyi da ra’ayoyi a game na wancan zamani sannan ya kwatanta ko wace riwaya da bayanan da ya riga ya sani domin ya ga abin fahimtar(mafhumi) abinda riwayar ta kunsa da rabe-raben ta.
La’alla daya daga dalilan wannan rikitarwa shi ne kasancewa harakar Imam da mabiyansa an yi ta cikin sirri, domin shiri na siri wanda ya kafu bisa ingantattun ginshikai dole ne bayanan da suka dangance shi su wanzu cikin sirri da boyewa, kuma wajibi ne kada wanda yake waje da wannan shiri ya tsinkaye su. Wadannan bayanai ba su watsuwa sai bayan tabbatar harakar da kuma nasararta. Saboda haka ne muke samun cikakkun bayanai dalla-dalla kan sadarwa ta sirri a harakar Abbasiyawa domin harakarsu ta yi nasara. Babu shakka da an kaddara wa harakar Ahlulbaiti kaiwa ga nasara da karbar ragamar mulki da a yau mun riski sirrin tsare-tsarenta masu fadi.
Akwai wani dalilin daban wanda zai iya janyo wannan rashin baiyana dangane da harakar Ahlulbaiti, cewa murubuta tarihi, bisa al’ada suna rubuta abin da yake dadada wa sarakuna ne. Domin haka muke ganin bayanai filla-filla kan rayuwar halifofi da wasanninsu da hirarrakinsu da wuraren holewarsu amma bamu ganin bayanan kirki kan masu neman juyi da wadanda aka zalunta da wadanda aka murkushe. Domin samun irin wadannan bayanan mai bin diddigi na bukatar dogon bincike da kirkado da tsananin biyawa. Amma rayuwar halifofi bayani ne tanadadde, tsuntsu daga sama gasashshe, yana kawo yardarsu da tarin kyaututtuka.
Marubuta tarihi masu rusnawa ga halifofin Abbasiyawa sun ci gaba da rubutu bisa wannan hanya na tsawon shekara dari biyar bayan rayuwar Imam Sadik (a.s). Saboda haka ba za mu yi tsammanin samun wani abin kirki na bayanai kan rayuwar Imam Sadik (a.s) ba, da ma na ko wani imamin shi’a cikin wadannan littafai.
Hanyar kadai da za ta iya shiryar da mu kan layin da rayuwar Imam Sadik ta duka ita ce gano muhimman alamu na rayuwar Imam ta hanyar ka’idoji, a game, na salon tunanin Imam da dabi’unsa. Kana mu yi bincike kan abubuwan tarihi da suka danganci wannan rayuwa da hujjojin tarihi da suke warwatse da kuma irin wadancan abubuwa masu dangantaka da rayuwar Imam wadanda ba na tarihi ba har mu kai ga rarrabewar al’amarin filla-filla.

Alamomi a Rayuwar Imam Sadik (a.s) Muhimman alamomi wadanda suke fitattu a rayuwar Imam Sadik (a.s) idan muka lura da mahangar bahasinmu, suna iya tattaruwa cikin wadannan:-
1. Bayyana sha’anin imamanci da kira zuwa gare shi.
2. Sharhi kan hukunce-hukunce da tafsirin Alkur’ani dai-dai da abin da mazhabin Ahlulbaiti ya gada daga Manzon Allah (s.a.w.a)
3. kafa tsari na sirri kan manufa da kuma siyasa.
Hanyar da bahasinmu zai dauka ita ce yin bincike kan kowani daya daga wadannan alamomi sannan daga karshe mu sanya wani jadawalin ayyukan Imam (a.s) Duk wannan zai kasance da salon masu tarihi ba na masu hadisi ba, gwargwadon iyawarmu.
1. Bayyana sha’anin imamanci da kuma yin kira zuwa gare shi.
Wannan maudu’i yana daukar masayin mafi bayyanan alamomin kiran imaman Ahlulbaiti (a.s) tun shekarun farko bayan kaurar Annabin rahama (s.a.w.a). Mas’alar tabbatar da imamancin Ahlulbaiti ita ce al’amari na kan gaba wajen kira a dukkan zamunnan imamanci. Muna iya ganin wannan mas’alar a yunkurin Imam Hussain ibn Ali (a.s) da kuma yunkurin ‘ya‘yan imaman Ahlulbaiti kamar Zaid ibn Ali. Kirar Imam Sadik ita ma ba ta fita daga wanna fagen ba.
Kafin mu bijiro da hujjoji kan wannan maudu’i ya zama wajibi tukun mu fara da bayanin ma’anar (imama) ‘imamanci’ a tunanin musulunci. Kuma mene ne kira zuwa ga imamanci? Kalmar imamanci a asalinta tana nufin jagoranci sake ba kaidi. A tunanin musulunci kuwa galibi ana amfani da ita ne a kebance. Wannan wurin kuwa shi ne jagoranci a sha’anin halin zaman jama’a walau wajen tsarin tunani ne ko kuwa tsarin siyasa.
Kalmomin da aka tsago daga ita kalmar ‘imama’kamar su ‘imam’ da ‘a’imma,’ duk inda suke a cikin Alkur’ani abin da ake nufi da su shi ne kebantaciyar ma’anarsu watau jagorancin al’umma. A wadansu wurare abin da ake nufi da ita shi ne jagorancin tunani a wadansu kuwa jagorancin siyasa ko kuma biyun gaba daya.
Bayan kaurar Ma’aiki da bayyanar rarrabuwar salon tunani da siyasa tsakanin jama’ar musulmi, kalmar imamanci, da imama, ta dauki wani kebantaccen masayi, saboda mas’alar jagorancin siyasa ita ce jigon sassabawar musulmi. Da farko, kalmar tana da manufar siyasa fiye da kowace manufa wacce ba ta siyasa ba. Daga bisani wadansu ma’anonin sun riske ta sannu a hankali, har aka wayi gari a karni na biyu mas’alar ‘imama’ ta zamo mas’ala mafi muhimmanci wajen makarantan ilmul kalam masu baiyana ra’ayoyinsu kan sha’anin sharuddan imam da sifofinsa, watau sharuddan mai hukunci a al’ummnar musulunci; wannan kuwa shi ne ma’anar imamanci a siyasance.


3
JAGORANCIN IMAM SADIK (a.s) A kan imami kuma cewa ya yi:- “(Shi) tauraruwa mai shiryarwa ne, ruwan dadi ne, matsera daga halaka ne, girgije mai kawo ruwa ne, mafakar bayi a lokacin bala’i ne, amintaccen Allah kan halitarsa ne, hujjarsa bisa bayinsa ne, halifansa a kasashe ne, mai kira zuwa ga Allah, mai tsare hurumin Allah ne, daidaiton addini ne, daukakar musulmi ne, fushin munafukai ne, kuma halakan kafirai ne”[29]
Duk nauye-nauye da mas’uliyyar da Annabi ya gudanar, Ali (a.s) da imamai daga ‘ya’yansa suna daukarsu.[30]
A wata riwaya daga Imam Sadik (a.s) akwai ta’kidi kan biyayya ga ‘wasiyyai’. Riwayar ta fayyace cewa wasiyyan su ne wadanda Alkur’ani ya kira da lakabin ulul amri .[31]
Daruruwan riwayoyi da ke rarrabe cikin babi daban-daban suna fayyace mana cewa manufar imam da imamanci a tunanin shi’a ba komai ba ce face jagoranci da gudanarwa na al’amuran musulmar al’umma kuma imaman Ahlulabaiti (a.s) basu takaita wajen da’awar imamanci kan abin da ya shafi tunani da ma’nawiyya kadai ba, a’a suna kira da cewa hukuma ita ma tasu ce. Kiransu mai fadi kamar haka mai kuma tattara dukkan sassa hakika kira ce ta wata harakar siyasa da kuma soji wadda take da zimmar karbar shugabanci.
Wannan batu ya ci gaba da zama boyayye ga masu bincike a zamunnan da suka biyo baya amma a fahimtar sahabban imamai da wadanda suka yi zamani da su batun yana daga mafi bayyanannun al’amura. A cikin daya daga kasidunsa na Hashimiyyat, Kumait yana sifanta imaman Ahlulbaiti da cewa su ne shugabanni masu jagorantar mutane ta wata hanya wacce ta saba gaba daya da hanyar da azzaluman mahukunta suka bi, inda suke mu’amala da mutane tamkar dabbobi.[32]
Mu koma ga maudu’in asali cewa kashin baya a kiran Imam Sadik (a.s) da sauran imaman Ahlulbaiti (a.s) shi ne batun imamanci. A tare da mu akwai riwayoyi masu karfafa juna wadanda suke tabbatar da wannan batu na tarihi. Ana nakalto su a bayyane tare kuma da wannan fayyacewa daga Imam Sadik (a.s) inda ya yi da’awar imamanci. Za mu bayyana nan gaba cewa lokacin da Imam yake bayar da sanarwar wannan kiran nasa, yana ganin kansa cikin wani mataki na jihadi mai bukatar ya yi watsi da mahukuntan zamaninsa, ta hanya bayyananna kuma kai tsaye, sannan kuma ya sanar cewa shi ne ma’abocin hakki na hakika, ma’abocin shugabanci (wilaya) da kuma imamanci. Irin wannan fitowa, bisa al’ada, tana nufin an ketare sauran matakan jihadi wadanda suke gabatarta tare da nasara. Dole ne ya kasance farkawa a siyasance da yanayin zaman jama’a ta zama tuni ta sami goyon baya mai fadi, ana jin shirin mutane ya yi karfi a ko wani wuri, shimfida kan manufa ta kankama ga wani adadin mutane mai dama, sannan jama’a masu yawa sun yi imani da wajibcin kafa hukumar gaskiya da adalci, sannan daga karshe, jagoran ya zama ya riga ya dauki kuduri mai karfi akan wannan fito-na-fito mai tsanani. Idan wadannan sharuddan basu cika ba,sanarda imamancin wani mutum ayyananne da jagorancin sa na gaskiya ga al’umma abu ne mai tattare da ujula ba kuma cimma manufa tare da shi.
Wata mas’alar da ba makawa ga karfafawa game da ita a wannan bayanin ita ce, a wadansu lokutan Imam Sadik (a.s) ba ya takaita kan tabbatar da imamancinsa kadai, yana ma ambaton sunayen imaman gaskiya magabatansa tare da ambaton nasa sunan, watau, bisa hakika, yana gabatar da silsilar imaman Ahlulbaiti tare da sadarwa, daya bayan daya, ta yanda yayyankewa ko rarrabewa ba ya yiwu wa.
Wannna matsayin yana nuni da dangantakar da ke akwai tsakanin jihadin imaman Ahlulbaiti (a.s) da dorewarsa tun daga zamunnan da suka gabata har zuwa lokacin Imam Sadik (a.s). Imam Sadik (a.s) yana bada sanarwar imamancinsa a matsayin shi na wani sakamakon da ba makawa zai biyo bayan imamancin magabatansa, kuma da wannan yake bayyana tushen wanna kiran da zurfin kafuwarta a tarihin sakon musulunci, da dangantakarta da ma’abocin kiran, Manzon mai girma, mafificin tsira da aminci ya tabbata gare shi. Bari mu kawo wasu samfurin kiran Imam:-
Riwayar Amru ibn Abi Mikdam ita ce mafi ban-sha’awa a wannan babin, tana kuma sauwara wani yanayi mai ban mamaki.
A ranar tara ga watan Zulhijja, yayin da mahajjata suka taru a Arfa domin tsayuwa gashi sun riga sun hallara a wannan wuri daga ko ina: kamar daga karshen kasar Kurasan har zuwa gabar tekun Atlantika, a wannan wuri mai hadarin gaske, inda kira a cikinsa tana iya aika amon ta zuwa nisan duniyar musulunci. Imam ya hadu da wannan taron jama’u masu yawa saboda ya isar musu da kalmarsa. Mai ruwaya yace:- na ga Imam ya tsaya cikin jama’an nan, ya daga murya da kyau domin ya isa kunnuwar mahalarta sannan daga bisani ya kai ga kunnuwan talikai, yana kira kamar haka:-“Ya ku mutane ! Lallai Manzon Allah ya kasance shi ne shugaba (imam), sannan Ali ibn Abi Talib, sannan Hassan, sannan Hussaini, sannan Ali ibn Hussain, sannan Muhammad Ibn Ali, sannan ……..” Yana wannan kiran sau uku ga wadanda suke gabansa, da gefensa na dama, da gefensa na hagu da kuma bayansa, kira goma-sha biyu ke nan”[33]
A wata riwayar daga Abu Sabah Alkinani cewa Imam Sadik (a.s) ya sifanta kansa da kuma imaman shi’a da cewa ganima (anfal) da zababben dukiya tasu ce.
Daga Abi Sabah ya ce:- Abu Abdillah ( a.s) ya ce da ni: “Ya Aba Sabah, mu mutane ne wadanda Allah ya farlanta biyayya gare mu. Ganima tamu ce, zababben dukiya namu ne, mu ne matabbata cikin sani kuma mu ne wadanda aka yi wa hasada wadannan da Allah ya fade su cikin littafinsa”[34]
Safwul mali, zababbar dukiya, shi ne kayayyakin da suke da kima matuka daga cikin ganimar yaki. Da ba’a raba wa mayaka irin wadannan kayayyakin kamar yanda ake raba musu sauran dukiyar ganima saboda kada a fifita wani da zababben abu, gudun kada wannan ya zamewa wani wata daraja ta karya. Maimakon haka ana barin irin wadannan kayayyaki ne a hannun shugaban musulunci ya yi amfani da su wajen abin da zai tabbabtar da maslahar musulmi gaba daya. Azzaluman mahukunta su kan dauki irin wannan dukiya su kebanta da ita ta hanyar kwace(gasabi). Imam yana fayyacewa kan cewa zababbar dukiya, wajibi ta zama tasu, haka nan ganima. Wannan yana nufin cewa Imam yana bayyana kansa a sarari a matsayin shugaban musulmi a ganin shari’a, wanda nauyin jujjuya wadannan dukiyoyi dai-dai da abin da yake ganin zai tabbatar da maslahar al’umma a kansa yake.
A wani hadisin Imam Sadik (a.s) yana ambaton sunayen imamai magabatansa daya bayan daya, yana ba da shaidar imamancinsu da wajib cin biyayya gare su. Yayin da ya iso kan sunansa sai ya yi shiru, masu saurare kuma sun sani sarai cewa gadon ilmi da hikima bayan Imam Bakir (a.s) a wajen Imam Sadik (a.s) yake. Kuma da wannan Imam (a.s) yake bayyan hakkinsa na jagorantar al’umma, yana bayyana shi da wani salo mai danganta hakkin nasa da kakansa Ali ibn Abi Talib (a.s). Cikin wadansu babi-babi na littafin Alhujja cikin Alkafi da ma cikin juz’i na arba’in da bakwai na Biharul Anwar akwai irin wadannan hadisai da yawa, suna fayyacewa, wani zubin kuwa suna kinaya kan da’awar imamanci da kuma kira gare ta.
Domin tabbatar da wannan batu na tarihi, akwai hujjoji ko shaidu da suke tabbatar da samuwar wani tsararren shirin sadarwa da yake gudanar da kiran Imam (a.s) a ko ina cikin sassan duniyar musulunci. Mayawaitan hujjoji da ke akwai a kan wannan batu sun sa samuwar wannan shirin sadarwa wani al’amari ne yankakke ba wani shakka a kansa. Wadannan shaidun sun yi yawa da karfin da ana iya kafa hujja da su a kan wannan maudu’i namu, hujja tabbatatta, ko da ba’a sami sahihin hadisi ko guda ba kan wannan batu. Mu dubi wadannan tabbatattun al’amuran tarihin:-
1.Akwai wata tsararrar alaka ta tunani da ta abin da ya shafi dukiya tsakanin imamai (a.s) da mabiyansu, kuma an kasance ana daukar dukiyoyi daga sassa dabam dabam na duniya ana kaiwa Madina kazalika da tambayoyin addini mayawaita.
2.Fadadar fagen da ke wilaya ga mutanen gidan Manzo (s.a.w.a) musamman a yankunan duniyar musulunci wadanda suke masu saurin daukar dumi.
3.Tattaruwar jama’a masana hadisi da maruwaita Kurasanawa da Sistanawa da Kufawa da Basarawa da Yamanawa da Misrawa gaban Imam (a.s).
Shin wannan al’amari wanda sashensa yake munasaba da sajewa da sashe ya faru ne kwatsam ba tare da an shirya shi ba?
Wajibi ne mu yi kari da cewa wannan al’amari ya tabbata ne karkashin ikon siyasa wanda ya yi da gaske wajen watsi hatta da sunan Ali (a.s) kai da ma zagin Ali a kan mimbarori da wanzar da nau’o’in dira da razanarwa kan mabiyansa. To a irin wannan halin, yaya aka iya samar da mabiya mayawaita masu wilaya ga Ahlulbaiti daga cikin talakawa suna taka dubban milamilai saboda su kai kasar Hijaz da birnin Madina da zimmar daukar karatu gaban imaman Ahlulbaiti (a.s) da kuma koyon tunanin musulunci a kan rayuwar dai-daiku da ta jama’a da kuma tattaunawa da su kan batutuwa mayawaita da kuma mas’alolin tawaye wa yanayin barna da fasadi, ko kuma kamar yanda riwayoyi suke kiran al’amarin-mas’alolin ‘tsayawa’ da ‘ficewa’ daga da’a ga azzalumai )?!!
Idan da ace masu kiran Ahlulbaiti suna takaita bayanansu ne kan ilmin imamai (a.s) da zuhudunsu, to me ya sa tattaunawar wadannan mabiyan a kullum take kan batun tawaye ta hanyar daukar makami? Shin wannan baya nuni da samuwar wani tsararren shirin sadarwa saboda kira zuwa imamancin Ahlulbaiti (a.s) da cikakkiyar ma’anar imamanci, watau tsrin tunani da na siyasa?
A nan tambaya za ta zo kan cewa dalilin kawaicin tarihi dangane da samuwar irin wannan tsararren shirin sadarwa a kiran Ahlulbaiti (a.s). Shin mene ne ya sa tarihi bai ambaci komai kan wannan batu a fayyace ba? Amsa ita ce abin nan da muka yi nuni da shi a baya. Ta yiwu sahabban imamai sun lizimci ka’idar nan ta hikima wajen haraka wanda aka sani da takiyya, wanda take ba ta bada duk wani bare a tsarin imama damar kutsa kai. Haka kuma mai yiwuwa ne tarihi bai ce komai ba saboda rashin kaiwa harakar jihadi ta shi’a ga tabbatar da manufofinta da karbar ragamar mulki. Da a ce Banu Abbas basu hau karagar mulki ba da kuwa, ba shakka duk bayanen aikace-aikacensu na sirri da muhimman batutuwan kiransu mai dadi da mara dadi da ya takaita ga zukatansu kadai, ba tare da wani ya san su ba kuma da tarihi bai rubuta komai a kansu ba.
Duk da haka riwayoyin da suke fayyacewa gwargwado kan samuwar mayalwacin kira zuwa ga imamancin Ahlulbaiti (a.s) ba kadan suke ba. Za mu hakura da guda daya mai cewa:-
Wani mutum daga mutanen Kufa ya zo Kurasan, sai ya kira mutane zuwa wilayar Jafar ibn Muhammad (a.s). Wata jama’a sai ta bi shi ta amsa kiransa. wata kuma ta musa masa ta yi inkari wata kuma ta dakata ta yi tsantseni. Sannan riyawar ta ce: Sai mutum daya daga kowace jama’a ya tafo wa Imam Abu Abdillahi (a.s). Mai magana daga cikinsu shi ne wannan da ya dakata ya yi tsantsenin. Sai ya ce : Allah ya kiyaye ka, wani mutum ya zo mana daga mutanen Kufa ya kira mutane zuwa biyayya da wilaya gare ka sai wasu mutane suka amsa masa, wasu suka yi inkari wasu kuma suka ya tsantseni suka dakata. Imam (a.s) ya ce:- “Daga cikin ukun wacce kake ciki? “Ya ce:- Daga jama’ar da ta yi tsantseni ta dakata. Ya ce: To ina tsantsenin ka yake daren kaza da kaza? (sai ya tunatar da shi kasawarsa a wani hali na sha’awa) sai mutumin ya yi shakka. [35]
Kamar yanda ka ji, mai kiran daga mutane Kufa yake, kiran nasa kuwa zuwa imamancin Ja’afar ibn Muhammad Al Sadik (a.s) da wilayarsa da kuma biyayya gare shi ne.
Akwai wadansu hujjoji daban masu bayyana abin da kiran imaman Ahlulbaiti (a.s) da shi’arsu kan imamanci ya kunsa. Jayayya tsakaninsu da abokan hamayyarsu na siyasa (Umayyawa da Abbasiyawa) ta bijiro da shi. Wani lokaci ana wannan jayayya ne ta hanyar kafa hujja a fagen addini da ilmul kalam a wasu lokatan kuma tana daukar salon adabi mai zurfi ta hanyar wake. Duk jayayyar ana yin ta ne kan tabbatar da cancantar imamanci a siyasance da shugabanci ga imaman Ahlulbaiti (a.s) da gwagwarmaya da masu kankamewa kan karagar hukumar musulmi bisa zalunci da kwace. Saboda yin zamani daya da harakar Abbasiyawa da samun nasararta, lokacin Imam Sadik (a.s) ya kasance a cike yake da irin wannan jayayya da mujadala.
Mawakan Abbasiyawa suna kokarin tabbatar da cancantar shugabanci ga Abbasiyawa suna dogaro da hujjojinda, bisa al’ada, masu kwadayin mulki da kuma masu kankamo da karagar sarauta suke gabatarwa. Mawakan shi’a kuwa sukan fuskance su suna gugar wadancan hujjojin suna masu kafa hujja kan fandarar da mulkin Abbasiyawa ya yi daga mandikin musulunci ( dalilan da ya dogara a kansu ) wanda yana kafe ne bisa yarfar da zalunci da aikata laifi da ha’intar hakkokin al’ummar musulunci.
Mukabala ta hanyar wake tsakanin Abbasiyawa da Alawiyyawa tana da muhimmanci a nan saboda irin muhimmiyar rawar da wake ke takawa a wancan lokacin wajen bayyana abin da rai ya kunsa da tunane-tunane saboda kuma irin tsarin da yake da shi kan mabiya cikin talakawa. Ma’abocin littafin “Abbasiyawan Farko” yana ambatar rawar da adabi ya taka a karnin farko da na biyu. Ya ce:-
“Adabi ya kasance yana tasiri a zukata yana kokarin samun goyon bayan jama’a da karkatarsu ga wannan kungiya ko waccar, mawaka da masu jawabi matsayinsu irin wanda jaridu suke da shi ne a yau . Ko wannensu yana bayyana wani ra’ayin siyasa ne yana kuma kare wata kungiya ayyananna, yana bijiro da dalilin ingancikin kirar da yake yi daya bayan daya yana rushe ra’ayoyin abokan hamayya da magana maiu tasiri da salo mai fasaha”[36]
Mawakan fadar Abbasiyawa sun kasance suna kokarin tabbatar da cancantar Abbasiyawa ga halifanci da hujjar alakarsu da Annabi ta hanyar ‘ya’yan baffa, sun kafa hujja kan hakan da cewa gado ba ya riskar ‘ya’yan diya tare da samuwar baffanu. Saboda haka halifanci a bayan Annabi hakkin Abbas, baffan Annabi ne, a bayansa kuma, na ‘ya’yansa ne, watau yayan Abbas. Marwan ibn Abi Hafsa ya ce:- Kaka zai yiwu, ai bai yiwuwa, Gadon baffanu a hannun dan diya Abban ibn Abdilhamid Lahiki ya ce:- Ya’yan Abbas su ke da gado nai, Baffa ga dan baffa ai hijjabi ne Mabiya Ahlulabaiti sai suka zabura saboda ji a jika cewa wannan furuci zalunci ne, suka yi raddi kan wadancan hujjoji da irin tunanin (mandiki) da aka yi amfani da shi a wani lokaci, a wani zubin kuma su kan dauki wani mandikin dabam, daboda kafa hujja kan hakkin imaman Ahlulbaiti na imamanci. Daga wannan akwai kafa hujja da hadisin Gadir kummi kamar zancen Sayyid Himyari, inda ya ce:- Wanda nake a gare shi shugaba, Wannan tabbas a gare shi shugaba Amma sun ki yarda sun ki gamsuwa Muhammad ibn Yahya ibn Abi Murra Taglibi ya yi raddi kan hujjar mawakin Abbasiyawa wanda ya yi magana kan gadon baffanu, ya ce:- Me zai hana, kai hakika hakku ne, Rabon baffa a tattara shi wa dan diya Rabi daga dukiya na diyarsa ne, Shi baffa ya tai gida ba ko daya Kai sakakke me ya kai ka batunta ne? Ba don kisa ba bai ruku’i ko daya Du’bal yana ganin cewa duk ma masifun da suka auka wa Ahlulbaiti (a.s) ba don komai ba ne sai domin sun gaji Annabi, sai masu hadama suka yi rub da ciki kan wannan gadon kuma suka cutar da wanda shi ke da hakkin imamancin. Gadon Ma’aiki ya lahanta madaukaka, Mutuwa, tsoro wawasonsu suke Kurayen Umayya su kira su azazzala, Tuttudar kunci, da masifu kansu ne Banu Abbasin dinu su barnata, Ha’inci, zalunci, halinsu ne Wai shi Rashidu saboda shiriya tasa Mamun, Amin ka ga fa nasu ne Shiriya! Wanga bai tsare hakki ko daya Amincin biyun zagon ga Islama ne Ba abu ne mawuyaci ba ga mai bincike a kan farkon zamanin Abbasiyawa samun daruruwan misalai kan muhawarori da mukabalar siyasa wadanda suka kai yawan wake-waken da aka yi kan wannan batu. Mawakan shi’a da abokan hamayyarsu su kan kafa hujjoji ne kan kiran da kowannensu yake yi. Ba shi da muhimanci mu san ingancin hujjojin da ake kafawa a wannan jayayya, abin da yake da muhimmanci shi ne mu gane ginshikin jayayyar da ake yi da kuma hakkin da sassan biyun ke da’awarsa. Akwai wani hakkin da ko wani sashe yake da’awa wannan kuwa shi ne gadar Manzon Allah (s.w.a) wajen mulki da jagorancin musulmi.
Jayayyar tsakanin sashen Alawiyawa da na Abbasiyawa ba kan gadar tadodi da dabi’u na gari da ma’nawiyya ko tsarin tunani irin na Annabi (s.a.w.a) ba ne. Ba wai ana sassabawa kan wane ne ya cancanci gadon wata tada ba ne, domin wadannan tadodi ba wani hakki ne da bangare biyun za su yi sa-in-sa a kai ba. Jayayyar dai a kan wani hakki ne wanda sassan biyu suke da’awarsa. Kuma mun ji yanda mawaka a zamanin Imam Sadik (a.s) suke kare hakkin imami na jagorancin musulmar al’umman nan ma na mulkar jama’ar musulunci. Suna kuma kutsawa cikin yaki da wadanda basu da cancantar mulkar musulmi. Akwai shaidu masu yawa kan wannan batu a wake-waken karni na biyu bayan hijjira.
Kafin mu rufe wannan fasali ya dace mu yi nuni da wani salon kafa hujjan daban wanda kuwa shi ne salon wasika. Wadannan wasikun kafa hujja, a wani gefen, suna kunshe da bayanan manufofin kungiyoyi a sarari ba da wata rikitarwa ba. Ta wani gefen kuwa suna jan hankalin talakawa bayan yaduwar manufar bayanan. Kazalika ana samun tasiri mai karfi kan mataimaka da kuma abokan hamayya. Za mu ambaci wasikar da Muhammad ibn Abdillah ibn Hassan, Nafsi Zakiyya, ya aikewa Mansur sarkin Abbasiyawa. Wannan Ba’alawe mai neman juyi yana fayyacewa gaba gadi cewa yana fafutukar kwabe halifanci daga hannun abokin hamayyarsa domin ya kasanse a hannun ‘ya’yan Ali (a.s), ya ce:- “Lallai mahaifinmu Ali ya kasance shi ne wasiyyi kuma shi ne imami, to ta yaya kuka gaji shugabancinsa alhali ‘yayansa suna raye?”[37]
Ga alama Ba’alawen ya kawo wannan hujjan ne saboda raddi kan kafa hujja da Abbasiyawa suka yi kan gadar halifanci, domin banu Abbas ba su mallaki wata hujja ba face wannan da’awar gadon. Nafsi zakkiya ya yi haka ne domin ya toshe musu duk wata kafa da irin nasu mandikin (salon hujja).
Ana iya lura a kalmominsa yanda yake karfafawa kan imammanci kana ya karfafa kan yanayin kiran Gidan Ali wanda wannan mai neman juyin yake wakilta a wannan jayayya.
2. Sharhi kan hukunce-hukunce da tafsirin Alkur’ani dai-dai da abin da mazhabin Ahlulbaiti (a.s) ya gada daga Manzon Allah (s.a.w.a).
Wannan aikin shi ma ana iya ganinsa a rayuwar Imam Sadik (a.s) fiye da yanda ake iya ganin sa a rayuwar sauran imaman Ahlulbaiti (a.s) abin da ma ya sanya ake kiran fikihun shi’a da sunan Fikhun Ja’fari kenan. Hatta masu rintsa ido kan ayyukan Imam Sadik na siyasa sun hadu kan cewa Imam ya kasance yana gudanar da daya daga cikin mafi girman makarantun fikihu a zamaninsa, idan ma ba mafi girmansu ba. Abin da bai gushe ba yana lullube ga barin idanun mafi yawan masu bincike kan rayuwar Imam shi ne ma’ana ta siyasa da ta gwagwarmaya wadanda irin wadannan ayyukan Imam suke dauke da shi. Wannan shi za mu kawo a yanzu.
Da farko ya zama wajibi mu ambata cewa mukamin halifanci a musulunci yana da wadansu sifofin da suke sanya shugaba ya banbanta da shugabanni a wadansu tsare-tsaren shugabanci na daban. Shi halifanci ba wai tsarin siyasa ne kadai ba a’a, shi tsari ne na siyasa da addini a gwame. Baiwa shugaban musulunci lakabin halifa yana karkafa wannan batu: shi halifan Manzon Allah (s.a.w.a) ne a duk wani aikin da Manzo yake aiwatarwa ga jama’a wa lau nauyin da ya shafi addini ne ko kuwa na jagorancin siyasa.
Shi halifa a musulunci yanan dauke da mas’u’liyyar siyasa da ta addini gaba daya. Wannan tabbataccen al’amari ya sa halifofin da suka zo bayan na farko, wadanda rabonsu a cikin ilmomi addini ya yi karanci ainun, ko kuwa basu da wani rabo sam, ya sanya su rufe wannan nakasu ta hanyar malaman addini masu aikata musu abin da suke so. Sai suka baiwa fukaha’u da malaman tafsiri da na hadisi aiki a fada saboda tsarinsu na shugabanci ya tara sassan nan biyu: na addini da na siyasa.
Wata fa’idar samuwar masu wa’azin sarki a tsarin shugabanci, ita ce: azzalumin shugaba mai kama karya, a duk lokacin da ya so, yana iya canja wa hukunce-hukuncen addini fuska ko kuma ya musanya su dai-dai da bukatunsa. Wadancan ma’aikata, malaman fada, su suke aiwatar da wannan domin dadada wa masu azurta su. Suna yin haka ne karkashin rigar istinbadi da ijtihadi mai rudin jama’a.
Mawallafa da marubuta tarihi daga magabata sun ambato mana misalan da kare ba zai ci ba kan kirkirar hadisai da tafsiri da ra’ayi inda ake ganin hannun ikon siyasa a sarari. Za mu yi nuni da wani abu akai a nan gaba. Wannan al’amari wanda da farko(har zuwa karshen karnin farko bayan hijira) ya dauki salon kirkirar riwaya ko hadisi, sannu a hankali ya dauki matsayin fatawa. Daboda haka ne a karshen zamanin Banu Umayya da farkon na Banu Abbas muke ganin bayyanar fukaha’u masu yawa suna amfani da hanyoyin ka’idojin istinbadi masu rauni domin su kafa dokoki dai-dai da zabinsu wanda a kashin gaskiya zabin tsarin da yake shugabanci ne. A fagen tafsirin Alkur’an ma, dai-dai wannan aiki aka zartar. Tafsiri da ra’ayi, galibi, ya sa gaba wajen bayar da fahimce-fahimce wa musulunci, wadanda basu dogara da komai ba face zabin mai fassara da son ransa, wanda ba kome na ne illa son ran tsarin da yake shugabanci.
Wannan shi ne musabbabin rabuwar ilmomin musulunci: na fkihy da hadisi da tafsiri, tun zamunan na farko, zuwa ra’ayoyi biyu.
Ra’ayin Farko:- Ra’ayin da ke da alaka da tsarin azzulumar hukuma mai kwace. Yana bambata da dayan wajen sadaukar da gaskiya domin tabbatar da ‘maslaha’ wacee bisa hakika maslahar tsarin da ke shugabanci ne. Daga sifofin wannan ra’ayin har wala yau akwai baudar da hukunce-hukuncen Allah domin, ladan ‘yan dirhamomi.
Ra’ayin na Biyu:- Ra’ayi dan asali amintacce wanda ba ya ganin akwai wata maslaha mai daraja da daukaka da ta wuce bayyana ingantattun hukunce-hukuncen Ubangiji. Wannan ra’ayi ya kasance, ko an ki ko an so, yana cin karo da tsarin da yake shugabanci da kuma masu wa’azin fada, a duk wani taku da ya yi. Saboda haka tun farkon al’amari ya dauki mafuskanta irin ta talakawa tare da taka tsan- tsan da kiyayewa.
Fahimtar wannan zai sa mu gane da kyau cewa sabawan Fikihun Ja’afar da fukaha’un sarauta a zamanin Imam Sadik ba wai sabawa ce ta tunani da akida kadai ba, a’a ta hada har da abin da ya kunsa na hari irin wanda abokin hamayya yake yi.
Mafi muhimmanci daga kusurwowin wannan abin da ya kunsa shi ne tabbatar da cewa tsarin da ke shugabanci fanko ne kawai wanda ya rasa dukkan ma’anonin addini, ga kuma gajiyawarsa wajen gudanar da al’amuran tunani ga al’umma. Ko kuma mu ce rashin cancantarsa hawa mukamin “halifanci”. Wata kusurwa ita ce ayyana wuraren da aka baude cikin fikihun sarauta, wadannan baude-baude da aka gina kan tunanin “maslaha” wajen bayanin hukunce-hukuncen fikihu da sassautarwar malaman fikihu ga tsarin da ke shugabanci. Imam Sadik (a.s), da ayyukansa na karantarwa da kuma sabar nauyin bayyana hukunce-hukuncen fikihu da ilmomin musulunci da tafsirin Alkur’ani ta hanyar da ta saba da ta masu wa’azin fada, hakika, a’aikace, ya dauki matsayin hamayya da tsarin da ke mulki. Da wannan aikin, Imam ya iya watsi da duk tsarin sarauta a addini da fikihu wanda wani bangare ne na hukumar halifofi, ya kuma tube wa tsarin da ke mulki duk wata rigar addini.
Ba mu da wani tabbataceen isnadi mai bayyana lurar tsarin Umayyawa da wannan janibin hamayya, wanda Imam Sadik (a.s) ya aiwatar a fagen ilmi da fikihu. Sai dai abin da aka fi tsammani shi ne tsarin Abbasiyawa mai mulki-----musamman lokacin Mansur wanda yake mai wayo da gogewa da fahimtar halayyar duniya, abubuwan da ya koya a lokacin dambarwar siyasa mai tsawo sakaninsa da mulkin Umayyawa kafin shi kansa ya sami mulkin--wannan tsarin nasu yana kiyaye mas’alolin masu wuyar fahimta da ke tattare da ayyukan gidan Ali. Kuma tsarin Abbasiyawa mai mulki yana fahimtar muhimmiyar rawar da wancan aikin ulmi zai iya takawa ta bayan fage.
Barazana da kuntatawa da matsin lamba wadanda suke tattare da ayyukan Imam Sadik (a.s) na ilmantarwa wadanda kuma riwayoyi masu yawa na tarihi ke nakalto mana, sakamakon wannan luran ne da kasancewar mas’alar mai hadari ce. Kazalika muhimmancin da Mansur ya bayar wajen tara mashahuran fukaha’u daga Hijaz da Irak a helikwatarsa, kamar dai yanda nassoshin tarihi mayawaita suke nunawa, shi ma ya samo asali ne daga wancan lurar da ya yi.
A magarsa da koyarwarsa ga sahabbansa da mukarrabansa, Imam (a.s) yana kafa hujja da “yanayin holoko da jahilci na halifofi” kan cewa a ra’ayin musulunci basu cancantar shugabanci. Ana iya ganin wannan sigar suka kan tsari mai mulki a sarari da fayyacewa a darusansa na fikihu.
An ruwaito zancensa (a.s):- “Mu mutane ne wadanda Allah ua farlanta biyayya gare mu, kuma kuna koyi da wanda ba’a yi wa mutane hanzari saboda jahilcinsa”[38]
Abin nufi shi ne mutane sun baude saboda jahilcin mahukuntansu da shugabanninsu, sun dauki hata wanya bata Allah ba. Wadannan ba abin yi wa hanzari ba ne wajen Allah domin biyayyarsu ga wadannan mahukunta aiki ne na baudiya saboda haka ba zai wanke abin da ke biyo bayansa na abkawa cikin baude-baude ba.[39]
A koyarwar imamai ( a.s) kafin imam Sadik da bayansa kuna ganin karfafawa kan wajibcin gwama jagorancin siyasa da tunani da manufa (aidiyolojiyya). A wata riwaya daga Imam Ali ibn Musa Al Rida (a.s) daga kakansa Imam Muhammad Bakir (a.s) ya ce: Makami a gare mu tamkar akwati ne ga Bani Isra’ila, duk inda akwati ya juya, sai mulki ya juya, (ka yi tunani da kyau kan ma’ana irin ta alama (ramzu) da ke cikin maganar) duk kuwa inda makami ya juya a cikinmu ilmi can zai juya. A wata riwayar kuma duk inda makami ya juya a cikinmu, to can al’amarin (hukuncin) yake. [40] Sai mai riwaya ya tambayi Imam ya ce:- Shin makamin yana rabuwa da ilmi?
Imam ya ce:- A’a (watau jagorantar al’ummar musulmi wajibine ta zama a hannun wanda yake rike da makami da kuma ilmi gaba daya). Saboda haka Imam (a.s) yana ganin cewa ilmin addini da fahimtar Alkur’ani ingantacciyar fahimta daya daga sharudan imamanci ne. Ta wata fuska kuma ta hanyar aikinsa na ilmi da tara adadi mai yawa na masu kishirwa da begen ilmomin addini a gangarsa, da koyar da addini yanda ya saba cikakkiyar sabawa da hanyar da aka saba wajen malamai da masana hadisi da masana tafsiri masu alaka da tsarin halifanci. Wannan yana tabbatarwa, a aikace, da cewa janibin addini sifa ce ta asali a makarantarsa, da kuma cewa rigar addinin da tsarin halifanci da malaman fada masu daka rawarsu ke da shi ta boge ce. Da wannan hanyar hari mai tsanani mara yankewa kuma cikin tsanaki Imam yake baiwa jihadinsa wata sabuwar kusurwa.
Kamar yanda muka ambata a baya, mahukuntan Abbasiyawa na farko wandanda suka sami shekaru da dama kafin su karbi mulki, suna tare da jihadin Alawiyawa kuma mataimakansu suna da masaniya kan da yawa daga hanyoyi da sako-sakon kirar. Sun riski rawar da hari da fama da wannan aikin fikihu da hadisi da tafsiri ke takawa fiye da magabatansu, Umayawa. Hala wannan dalilin shi ya sanya Mansur, saboda tinkarar Imam Sadik (a.s) ya hana shi zama a halakar koyarwa na wani lokaci da hana mutane zuwa gare shi. Har Mufaddal ibn Umar yana cewa:- “ Hakika Mansur ya daura aniyar kashe Abu Abdillah ba ma sau daya ba ko yaushe ya aika a kira shi domin ya kashe shi, idan ya dube shi sai haibar Imam ta rufe shi kana ya bar shi-sai dai fa ya hana mutane zuwa gare shi, ya kuma hana shi zama saboda mutane, ya bincike shi bincike mai tsanani, har al’amar ya kai ga cewa waninsu zai bukaci samun haske a wata mas’alar addini kan batun aure ko shika ko wani abin daban, gashi basu da sanin ta, kuma basu iya isa gare shi. Sai mutum ya kaurace wa iyalinsa. Wannan abu ya kuntata wa shi’arsa ya kuma yi musu tsananin”[41]
3. Kafa tsari na sirri kan manufa da kuma siyasa
Ya gabata cewa Imam Sadik (a.s) a karshen zamanin Umayyawa ya jagoranci wani shirin sadarwa da sanarwa mai fadi wanda kuma manufarsa ita ce kira zuwa imamanci irin na Ali (a.s) da bayyana sha’anin imamanci a kan sahihiyar ma’anarsa. Wannan shirin sadarwa ya yi yunkurin tabbatar da aikin yada ma’anonin imamanci. Wannan yunkuri ya yi alfanu saboda irin tasirinsa a sassan duniyar musulunci masu nisa masamman a Irak da Kurasan.


4
JAGORANCIN IMAM SADIK (a.s) A nan za mu yi ishara ga kadan daga wannan al’amari. Sha’anin tsaren-tsaren sirri a rayuwar siyasa ta Imam Sadik (a.s) da sauran imamai yana daga cikin al’amura wadanda suka fi muhimmanci kuma suka fi tsanani ko hadari a lokaci guda kuma shi ya fi komai zama dishi-dishi da rashin bayyana a rayuwarsu. Kamar yanda muka ambata ba zai yiwu mu sami bayani wannani al’amari a fayyace ba tun da ba mu tsammanin Imam ko wani daga sahabbansa zai yi furuci da cewa akwai wadannan tsare-tsaren siyasa da tunani a fili.
Wannan abu ne wanda ba za’a iya gano shi ba. Abin da hankali zai kama shi ne Imam ya tabbatar da rashin samuwar irin wannan tsari na sirri, tare da musantawa mai tsanani, haka nan ma sahabbansa, kuma sun dauka wannan wata tuhuma ce da mugun zato da tsarin hukuma zai nemi su ba da bayani kan wannan lamari. Wannan ita ce sifar da aikin sirri ya kebanta da ita, kuma shi ma mai bincike yana da damar rashin gamsuwa da samuwar irin wanna tsarin idan ba da dalili mai gamsarwa ba. Idan haka ne to ya zama wajibi mu bincika da shaidu da abubuwan da suka auku wadanda ga alama ba bakin komai suke ba kuma basu daukar hankalin mai karatu mara lura, saboda mu yi binciken manuniyar da suke da ita a kan wannan batu. Da irin wannan bin diddigi a rayuwa imamai (a.s) cikin karni biyu da rabi, mai bincike zai iya natsuwa da samuwar irin wadannan tsare-tsare masu aiki karkashin jagorancin imamai (a.s).
Me ake nufi da tsari? Ba fa tsari a nan yana nufin wata jam’iyya tsararra bisa irin manufar da take da ita a yau ba. Ba kuma samuwar wasu dakaru tararru masu jagorantar larduna, masu dangantaka tamkar tsarin dala ba. Babu wannan, kuma bai yiwuwa a same shi. Abin nufi da tsari shi ne samuwar wata jama’a ta bil Adama mai tarayya kan wata manufa, masu aikace-aikace daban-daban wadanda cimma waccan manufa shi suka sa gaba, masu alaka da matattara daya da zuciya mai bugawa guda daya da kwakwalwa mai tunani guda daya, sannan daidaikunta suna tarayya a alakar soyayya.
Wannan jama’a, a zamanin Imam Ali (a.s) (watau cikin shekara ishirin da biyar tsakanin wafatin Manzon tsira da mubaya’ar Ali a matsayin halifa) ta kasance imani da hakkin Imam Ali na halifanci yana hada ta. Ta kan bayyana cika alkawarinta ga Imam ta hanyar tunani da ta siyasa, sai dai ita tana koyi da Imam Ali (a.s) kan rashin ta da abin da zai girgiza jaririyar al’ummar musulunci. Haka kuma suna yunkurawa kan abin da a wadancan shekaru Imam Ali yake yunkuri saboda shi kamar nauye-nauyen sako da zimmar kare musulunci da yada shi da kokarin takaita baude-baude. Saboda wilayar ta wannan jama’a ta dauki sunan ‘Shi’ar Ali’.
Wadanda suka shahara daga cikinsu akwai Salman da Ammar da Abu Zarri da Ubayy ibn Ka’ab da Mikdadi da Huzaifa da sauransu, daga manyan sahabbai.
Muna da shaidun tarihi masu tabbatar da cewa wadannan suna yada tananinsu kan al’amarin imamancin Ali (a.s) cikin mutane tare da hikima. Wannan aiki nasu ya zama gabatarwa ga dafifin da mutane suka yi kan Imam Ali (a.s) da kafa hukumarsa.
Bayan Imam Ali (a.s) ya karbi ragamar mulki shekara ta talatin da biyar bayan hijira mutane iri biyu suke tare da shi. Na farko sun san Imam da matsayinsa, sun fahimci ma’anar imamancin sun kuma gaskata shi. Wadannan su ne shi’arsa wadanda suka yi tarbiyya a gabansa ko dai kai tsaye ko kuma ta hanyar wadansu. Kashi na biyu ya kunshi jama’a baki daya wadanda suka rayu cikin yanayin tarbiyyar Imam da tafarkinsa amma basu da alaka ta tunani ko ta ruhi da jama’ar da Imam ya yi wa tarbiyya ta musamman.
Saboda haka ne za ka sami mabiya Imam iri biyu ne na mutane, tsakaninsu da fifiko mai yawa. Kashi guda ya hada da Ammar da Malik Ashtar da Hujr ibn Adiy da Sahl ibn Hunaif da Kais ibn Sa’ad da tamkarsu. Daya kashin kuwa ya hada da Abu Musa AlAsh’ari da Ziyad ibn Abih da ire-irensu.
Bayan sulhin Imam Hassan (a.s) muhimmin matakin da Imam ya dauka shi ne yada tunanin mazhabin Ahlulbaiti da daidaita tsakanin masu wilaya da wannan tunanin, tun da an sami faragar motsawa mafi yalwa sabili da danniyar mulkin Umayyawa. Da’iman haka al’amarin yake, danniya tana kawo hadin kan wadanda ake dannewa ya sa su sajewa da kafuwa a maimakon watsewa da rarraba. Dabarun Imam Hassan sun fuskanci tara karfi mai wilaya dan asali waje guda da kare shi daga rabkar tsarin Umayyawa, da kuma yada tunanin musulunci dan asali a tsakanin wata takaitacciyar kungiya, sai dai an zurfafa koyar da su wannan tunanin. Sauran ayyuka sun hada da neman masu shigowa safun wilaya da dakon damar da ta dace da yin tawaye wa tsarin zalunci: da yin bindiga da ginshikansa da kuma aza hukumar Alawiyya a gubinsa. Wannan dabarar aiki ita ta bar Imam Hassan (a.s) da zabi daya kadai, wanda shi ne sulhu.
Wannan shi ya sa muke ganin wani gungun ‘yan shi’a karkashin jagorancin Musayyib ibn Najiyya da Sulaiman ibn Sard Alkhuzai, ya tafo gurin Imam Hassan (a.s) a Madina bayan sulhu, yayin da ya dauki birnin ya zama sansanin aikinsa na tunani da siyasa bayan dawowarsa daga Kufa. Wadannan mutane suna gabatarwa Imam da shawarar sabonta karfinsu da tsare-tsarensu na soji da mamayar Kufa da yin tafo-mu-gama da rundunar Sham. Imam ya yi kiran wadannan mutane biyu daga cikin gungun, ya kebance da su, ya kuma tattauna da su kan abin da ba mu san me ya kunsa ba. Mutanen nan biyu sun fito a karshen wannan tattaunawa tare da cikakken gamsuwa da rashin alfanun daukar wannan mataki. Yayin da wadannan biyun suka koma ga wadanda suka zo tare da su sai suka fahimtar da su a takaice cewa an yi watsi da batun tawaye ta hanyar daukar makami, kuma dole ne a koma Kufa domin a sake sabon aiki a can.[42]
Wannan muhimmin al’amari ya kunshi ma’anoni masu girma wadanda suka sa sashen malaman tarihi na wannan zamani daukar wancan zama a matsayin tushen da aka kafa tsare-tsaren shi’a a kansa.
Hakikan al’amari shi ne idan dai matakin farko na tsare-tsaren shi’a an dauke shi ne a wancan zama tsakanin Imam Hassan (a.s) da mutane nan biyu wadanda suka tafi daga Irak to ai Imam Ali (a.s) ya yi wasici da irin wannan matakin a lokacin da ya yi wasici ga sahabbansa mukarrabai da cewa:- “Idan kun rasa ni lallai za ku ga a bayana abubuwan da dayanku zai yi burin mutuwa saboda zalunci da gaba da son kai da rikon sakainar kashi da za’a yi wa hakkin Allah da kuma tsoron abin da zai sami ransa. Idan haka ya faru :-
-Ku yi riko da igiyar Allah gaba dayanku, kuma kada ku rarraba…..
-Na hore ku da dauriya da kuma salla.
-Da kuma takiyya.
Kuma ku sani Allah Mai girma da daukaka yana kin bayinsa su zama masu fuska biyu. Kada ku gusa daga gaskiya da mutanenta domin duk wanda ya musanya mu da wani ya halaka, kuma duniya ta kubuce masa, zai kuma fita daga cikin ta yana mai sabo)[43]
Wannan nassi mai zana yanayin bala’i da ya wanzi a zamanin Umayyawa a fayyace, mai fuskantar da muminai kan wajibcin taimakekeniya da daidaitawa da sajewa da juna yana furuci da mafi hasken shaida kan shirin tsare-tsare a harkar Ahlulbaiti (a.s). Wannan shirin tsare-tsare ya fito fili da siffarsa ta aikace a zaman nan da Imam Hassan (a.s) ya yi da biyu daga cikin shi’arsa makusanta. Kuma babu shakka cewa ba duka mabiyan Ahlulbaiti suke da masaniya kan wannan shiri mai zurfi ba. La’alla wannan yana iya zama wani hanzari kan abin da yake fitowa daga sahabbansa wanda ya danganci suka. Masu sukan kuwa sun kasance suna fiskantar maganar Imam sa’ar da ya yi masu bayani. Ga abin da ta kunsa: “……wa ya sani, ko wannan jarrabawa ce a gare ku, kuma amfani mai gushewa ga abokan gabarku……” A cikin wannan amsa akwai wata ishara boyayya ga siyasa da tsare-tsaren Imam[44]
A tsawon shekaru ishirin wadanda Mu’awiya ya yi mulki, farfaganda mai tsanani wanda ake gudanarwa da zimmar muzanta gidan Ali, wanda ya kai ma ana tsine wa Amirul Muminina Ali bisa mimbarorin musulmi da kuma janyewar Imam Hassan da Imam Hussain (a.s) daga fagen bayyannanar haraka wacce ake iya ganinta a fili, wannan yanayi ya sa babu wani musabbabin yaduwar tunanin Ahlubaiti da fadadar farfajiyar shi’a a Hijaz da Irak da za’a iya gani face samuwar wannan shirin tsare-tsare. Bari mu leka mu ga yanayin da fagen tunani ya ke ciki a wadannan wurare shekar ishirin bayan sulhun Imam Hassan (a.s).
A Kufa za ka samu cewa mazajen shi’a suna daga cikin mashahuran mutane. A Makka da Madina, kai da ma larduna masu nisa za ka ga mabiuya Ahlulbaiti tamkar wata sarka, sashinta yana sane da abin da yake samun daya sashen.
Bayan wasu shekaru, da daya daga mazajen shi’a watau Hujr ibn Adiy ya yi shahada sai ka ji suka da nuna rashin yarda a wurare da dama na kasashen musulunci duk da razanarwar da aka kakaba a ko ina.
Bakin ciki da takaicin ya kai ma wani sanannen mutum a Kurasan ya mutu saboda tsananin bakin ciki bayan ya bayyana suka cikin fushi.[45]
Bayan mutuwar Mu’awiya dubban wasiku suka zo wa Imam Hussaini (a.s) suna kiran sa da ya taho Kufa ya jagoranci juyi. Bayan shahadar Imam gomomin dubbai suka shiga kungiyar “ Tawwabun” ko suka shiga safun rundunar Muktar da Ibrahim ibn Malik masu adawa da mulkin Umayyawa.
Wajibi ne mai binciken tarinin musulunci ya yi tambaya kan musabbabin yaduwar wilaya ga Ahlulbaiti (a.s). Shin yana yiyuwa hakan ta tabbata ba tare da samuwar wani aiki mai yawa da tsari, wanda aka auna shi, wanda kuma hadadde ne wajen tafarki da manufa ba?
Amsa a’a, bisa dabi’a wannan ba zai yiwu ba. Gagarumar farfa-gandar da mulkin Umayyawa suka dana ta hanyar daruruwan alkalai da hakimai da masu huduba ba za ta rushe kuma ta ci tura ba idan ba wani zayyanannar farfaganda mai hamayya da waccar, wacce wani tsari hadadde, daidaitacce, boyayye ya yunkura da ita ba. Dab da mutuwar Mu’awiya aikace-aikacen wanna shirin Alawiyyawan ya ci gaba, saurinsa kuma ya karu. Lamarin ya kai ga hakimin Madina ya rubuta wa Mu’awiya abin da ya kunshi wannan: “Bayan haka, Umar ibn Usman (dan leken asirin hakimin Madina wanda ya sa ido kan Imam Hussain (a.s)) ya ba mu labarni cewa wadansu mazaje daga Irak da sashen manyan mutanen Hijaz suna yawan zuwa wajen Hussain Ibn Ali, suna kuma tattauna batun daga tutar tawaye …….ku rubuto mana ra’ayin ku.”[46]
Bayan waki’ar Karbala da shahahar Imam Hussain (a.s) aikin tsare-tsare na shi’a a Iraki ya karu sakamakon girgizar da ta sami zukatansu saboda kisan Imam Hussain (a.s) inda wannan babban laifi wanda ya kwace musu daman shiga ayarin Hussain da mutanen gidansa a Karbala ya zo musu ba zata. Wannan motsawa tasu tana kewaye da jin zafi da tabewa da takaici.
Dabari ya ce : Mutanen ba su rabu da tara kayan yaki da shirya masa da kiran jama’ar shi’a da ma waninsu, a asirce, kan daukar fansar jinin Hussain ba. Mutane sun amsa kiransu jama’a na bin jama’a, birni na bin birni, ba su rabu da haka ba har Yazid ibn Mu’awiya ya mutu.[47] Abin da littafin Jihadu Shi’a yake fadi gaskiya ne, inda ya yi taliki wa zancen Dabari da cewa:-
“Bayan kashe Imam Hussaini, jama’ar shi’a ta bayyana a matsayin wata jama’a mai tsari, ra ayoyin addini da alakar siyasa suna dinke ta, tana gudanar da tarraki tana da shugabanni, kana tana da karfin soji. Jama’ar “Tawwabun” ita ce farkon mai bayyana dukkan wanna.
Bincike kan al’amuran da suka auku a tarihi da ra’ayin marubuta tarihin kan wancan zamani, ga alama, yana nuna cewa shi’a suna daukar nauyin jagoranci da shirye-shirye, sai dai farajiyar fusata da sukar Banu Umayya ta fi tsararriyar jama’ar shi’an nan fadi. Wannan farfajiyar tana haduwa da kowace haraka mai rinin shi’a .
Za mu gane cewa masu motsawa da hamayya kan Banu Umayya ko da sun yi amfani da taken shi’a ba dai dai ne mu dauka cewa dukkansu suna cikin adadin shi’a ba, watau adadin tsararren shirin nan na imaman Ahlulbaiti (a.s)
Bayan bayanin da ya gabata, ina son in yi ta’akidi kan cewa bayan shahadar imam Hussaini wadanda kadai ake kiransu shi’a su ne jama’ar nan da take da alaka mai karfi da imamin gaskiya, tamkar yanda lamarin yake a zamanin Amirul Muminina (a.s). Wannan jama’a ita ce bayan sulhun Imam Hassan (a.s) ta fuskanci kafa tsarin shi’a da umarnin Imam, kuma ita ce ta yi kokarin jawo mutane zuwa wannan tsarin da kuma kange mafiya yawa wadanda basu kai matuka a tunani ba kuma basu yi kwari a fagen aiki ba balle su kai matsayin shiga tsarin, wanda yake da zimmar samar da wata babbar harakar shi’a.
Riwayar da muka kawo a farkon wannan bahasi wacce aka rawaito daga Imam Sadik (a.s) mai cewa adadin muminai bayan waki’ar Ashura bai wuce uku ko biyar ba, abin da take nufi shi ne ‘yan wannan kebantacciyar jama’a. watau mutanen nan da suke iya rawar gani, a matsayinsu na madugu mai wayewar kai a kokarin kaiwa matuka cikin al’amarin juyin Alawiyyawa.
Sakamakon aikin da Imam Sajjad (a.s) ya yi a cikin sirri da tsanaki, turakun wannan ‘yar jama’a sun fadada kuma da wannan Imam Sadik (a.s) yake ishara a riwayar da muka ambata…… “sannan mutane suka risko su suka yawaita”. Za mu gani cewa zamanin Imam Sajjad da Imam Bakir da Imam Sadik ya ga motsawar wannan jama’a, wanda ta jefa tsoro da firgici a zukatan azzaluman mahukunta, al’amarin da ya sa du mai da martani mai tsanani.
A takaice, a karnin farko da na biyu bayan hijira da ma tsawon zamanin imamai (a.s) ba’a kiran wadanda suke kaunar Ahlubaiti da imani da hakkinsu da gaskiyar kiransu kadai ba tare da yin tarayya a tafiyar harakarsu ba da sunan shi’a. Su shi’a suna bambanta da saura ne ta hanyar wani tabbatanccen sharadi na tushe, wanda shi ne alaka da Imam wajen tunani da aiki da tarayya a aikin tunani da siyasa kai da ma ta fuskar aikin soji wanda yake jagoranta saboda dawo da hakki ga mai shi da kafa tsarin Alwawiyyawa na musulunci. Wannan alaka ita ake kira “wilaya” a kamus na shi’a.
Bisa hakika jama’ar shi’a suna ne wanda ake baiwa ‘yan jam’iyyar imamanci, jama’iyyar da take motsawa karkashin jagorancin Imam (a.s) take kuma daukar boyewa da takiyya a matsayin mafaka, tamkar duk wata jam’iyya ko shiri mai rayuwar cikin tsoro da danniya. Wannan shi ne takaitaceen bayani kan dubi na hakika kan rayuwar Imamai (a.s) musamman Imam Sadik (a.s) kuma kamar dai yanda muka ambata tun farko ba zai yiwu a sami hujjoji bayyanannu kan irin wannan al’amarin ba, tun da ba za mu yi tsammanin za’a kafa wa wani gidan sirri alama mai cewa: “wannan gidan sirri ne” ba! Kazalika ba zai yiwu mu natsu da sakamakon (bincike) ba, ba tare da samuwar wasu tabbatattun shaidun yanayi ba. Saboda haka ya kamata mu bi biddigin wadannan shaidu da isharori.
Daga cikin kalmomi masu zufafan ma’anoni wadanda suke jan hankalin mai bincike mai bin diddigi a riwayoyin da rayuwar imamai (a.s) ko kuwa wadanda ake kawowa a maganganun masu talifin karnin musulunci na farko akwai kalmomin “kofa” da “wakili” da “ma’a bocin sirri” wadannan kalmomi ne da ake kiran wasu sahabban imami da su. Alal misalim mashaurin malamin hadisi dan shi’a yana fada dangane da rayuwar Imam Sajjad (a.s) cewa :- “ Yahya ibn Ummu Dawil shi ne kofarsa” a kan ta Imam Bakir ( a.s) kuwa ya ce: “Jabir ibn Yazid Alju’fi shi ne kofarsa”, batun rayuwar Imam Sadik (a.s) kuwa ya ce:- “Muhammad Ibn Sinan shi ne kofarsa”. A cikin littafin “Rijalul Kashshi” ana kiran Zurara da Buraid da Muhammad ibn Muslim da Abu Basir da lakabin “ma’ajin sirri”. A cikin littafan hadisi ana ruwaito kalmar “wakili” daga Imam Sadik (a.s) a kan batun Mu’alla ibn Kunais. Ko wani daya daga cikin wadannan kalmomi imma dai ya fito ne daga Imam, wa imma sakamakon bincike ne mai yawa kan rayuwar imamai, wanda magabatan marubutan shi’a suka gudanar. Ko ma yaya ta kasance zabar wadannan kalmomi masu zurfafan ma’anoni ya samo asali ne daga wadansu fitattun alamomi a rayuwar Ahlulbaiti (a.s). Idan muka yi tunani da kyau kan wadannan kalmomi za mu tarar cewa ko wacce daga ciki tana nuni da cewa karkashin ayyukan zahiri wadanda imamayi (a.s) suke gudanarwa, akwai wani rayayyen shiri na boye.

Ma'ajin Sirri Idan mutum ba shi da wani “sirri” to ba shi da ma’ajin sirri. To mene ne wannan sirrin a rayuwar imamai? Me ne abin da sahabban imami a game ba za su iya rikewa ba sai wata jama’a da bata wuce a kidaya ta ba take da dacewa da cancantar rike shi? Kuma da haka ta sami darajar “ ma’ajin sirri”?
Hankula na baya-bayan nan manisanta daga ainihin abubuwan da suka auku a tarihi da rarrabe su suna fassara wannan sirrin da cewa shi ne sirrorin gaibi da iko kan ababen da suka keta al’ada da kuma mu’jizoji.
Ni ina imani da ikon wannan sifa tsarkakka ta Ahlulbaiti wadanda Allah ya zabe su domin ci gaba da nauyin rungumar sako da iyar da shi bayan kaurar Manzon Allah, na yarda suna dauke da irin wannan iko da irin da wadannan ilmomi. Kamar yanda nake imani da cewa adon da suka yi da wannan karfin da kuma wadannan ilmomi ko kadan ba ya karo da dubin da musulunci ke yiwa bil Adama da ka’idojin dabi’a da kuma dabi’ar kaunu. Amma fa wanna kari da ilmomi ba su ne “ sirrin imam” ba. Ai irin wannan karfi da kuma ilmomi su ne mafi bayyanar dalilai mai tabbatar da imamanci da gaskiyar da’awar imani. To me zai sa imami ya boye wadannan al’amura ya kuma yi wasici ga sahabbansa da boyewa, a riwayoyi mayawaita, wadanda yawansu da karfafa juna ya kai littafan shi’a na hadisi suna kebe babi mai suna “babin boyewa”? Dole ne wannan sirri ya zama cewa idan ya yadu zai zame wa Imam da sahabbansa wani hadari mai girma, wannan kuma ba zai zama al’amuran gaibi da masu keta al’ada ba.
Shin sirrin shi ne ilmomi da ma’arifar Ahlubaiti? Shin shine irin ganinda mazhabin Ahlulbaiti yake yi wa musulunci da fikihunsa da kuma hukunce-hukunce sa? Ba mu musun cewa ilmomi Ahlulbaiti ana yada su a zamanin danniyar Umayyawa da Abbasiyawa ta hanyar hikima da dabara domin kada ko wani sususu da shashasha ya kutsa cikinsu, amma wadannan ilmomi ba zai yiwu a ce su ne sirrin Imam ba. Duk da kebantar da take tattare da wadannan ilmomin ana karantar su a daruruwan makarantin fikihu da hadisi a wadansu manyan biranen lardunan musulunci a wancan lokacin. ‘Yan shi’a sun kasance suna nakalta wa juna wadannan ilmomin tare da sharhinsu. Muna iya cewa wadannan ilmomi da ma’arifa kebantattu ne amma ba na sirri ba. Kebantuwarsu tana nufin cewa yaduwarsu ta takaita ga haular ‘yan shi’a, amma a halaye na musamma suna isa ga wadanda ba shi’a ba ma. Sam ba masu takaita da kadan daga sahabban imamai, boyayyu ga wanin su ba ne.
Gaskiyan al’amarin shi ne sirrorin su ne al’amuran da suke ta’allaka da bayanan da suka danganci shirin tsare-tsaren imami,……….shirin da yake kutsawa cikin filin daga a siyasance da zimmar cimma manufar juyi,…… ko wadanda suka danganci dabarun da shirin ya haifar, ko ayyukan da zai aiwatar, ko suka danganci sunaye da nauye-nauye mambobin shirin ko hanyoyin kudi ko labarai, da rahotannin da suka ta’allaka da muhimman ababen da suke faruwa. Wadannan da ire-irensu sirrori ne wadanda ba dama wani ya tsinkaya idan ba jagora ba ko mataimakan da suke rike da ayyuka daban daban. Tana yiwuwa a sami yanayin da ya dace da bayyana wadannan sirrori a kwaye lulubinsu, ko a kusa ko kuwa tare da jinkiri, sai dai kafin wannan lokaci ba dama wani ya sami masaniya kan wadannan sirrori face wanda aikinsu yake da dangantaka da su kai tsaye, su ne kuwa “ma’ajin sirri”. Duk wani zarcewarsu zuwa ga makiya (shi kuwa laifi ne mai girma wanda ba’a yafewa) laifi ne wanda ka iya janyo rushewar jihadi da ayyuka da kuma tsararrar jama’an nan. Wannan zai fahimtar da mu abin da Imam (a.s) yake nufi da cewa: “ Jidalin da mai gaba da mu (nasib) yake janyo mana baya wuce wanda mai baza sirrinmu zuwa wanda ba ahalinsa ba yake jawowa. Mai baza sirrinmu ba zai bar duniya ba sai makami ya ci shi”[48]

Kofa Da Wakili A alakar sirri tsakanin Imam (a.s) da shi’a ta yiwu a bukaci isar musu da wasu bayanai ta hanyar “ mai shiga tsakanin” ko kuma sila. Wannan kuwa dabara ce mai ma’ana, abin da aka saba bisa alada. Yan leken asiri masu lababawa da zimmar gane alakokin Imam (a.s) su kan faki zaman ganawarsa da mabiyansa a lokacin aikin haji a Makka da Madina yayin da ayarai daga nisan duniya suke zuwa. Fakon wadannan zama ya kan kai ga ganowa bakin zaren babban shirin tsare-tsaren Imam. Saboda haka kake ganin Imam (a.s) wani lokaci yana nisanta wasu mutane daga gare shi da kalami mai taushi, a wani lokacin kuma da lafazin suka. Alal misali Imam ya ce da Sufyan Sauri:- “Kai mutum ne abin nema, sarauta kuma tana da ‘yan leken asiri a kanmu, saboda haka ka fita amma ba korar ka aka yi ba”[49]
Wani lokaci sai ka ga Imam (a.s) yana rokon jinkai ga mutumin da ya yi kicibis da shi a kan hanya amma ya kau da kai kamar bai gan shi ba, a wani zubin kuwa yana laifanta wani wanda ya gan shi a makamancin wancan yanayin ya kuma yi wa Imam sallama tare da karramawa da girmamawa.[50]
Irin wadannan yanayi na bukatar samuwar wani mutum da zai zama sila taskanin Imam da mai neman bayanai masu iso shi daga wajen Imam, to wanna silan shi ne “kofa” kuma wajibi ne ya zama daya daga mafiya amincin mabiyan Imam, wadanda suka fi kusaci da shi, kuma suka fi wadatuwa wajen sanin bayanai da hanyoyin sadarwa. Dole ne ya zama tamkar kudan zuma wacce da muggan kwari za su san zumar da take dauke da ita da sun sassare ta sun kuma kai hari kan gidanta.[51] Ba banza ba muke ganin wadannan “kofofi” galibi ana farautarsu ana kamawa ana dira kansu da mafi munin nau’in azaba.
Yahya ibn Ummi Dawil, “Kofar” Imam Sajjad an kashe shi, mummunan kisa.[52] Jabir ibn Yazid Alju’fi kuwa dole ta sa ya sa rigar hauka kuma wannan labarin ya watsu ya zama dalilin tsirarsa daga kisan da halifa ya riga da ya bayar da umurninsa ‘yan kwanaki kadan kafin yaduwar labarin haukacewarsa. Muhammad ibn Sinan kuwa ‘kofar’ Imam Sadik (a.s) korarsa Imam ya yi, kora ta zahiri duk cewa Imam ya bayyana yardarsa gare shi da yabonsa a wasu wuraren. Ba don komai aka yi masa haka ba sai domin shigarsa irin wadannan hadura, kamar yanda sanarwar Imam cewa ba shi da wani sananne mashahurin marawaici wanda kuwa ya rabauta da sanarwar yarda daga Imam. Sau da dama yana ishara, bisa ra’ayi mai karfi, cewa dabara ce ta tsare-tsare.
Irin wannan makoma tana fuskantar “wakili” shi ma. “Wakili” shi ne mai nauyin tara dukiyoyin da suke da alaka da Imam da kuma rarraba su. Shi ma ya san sirrori masu yawa, alal akalla, sunayen masu bayar wa da na masu karba. Wadannan bayanan, makiya Imam basu raina su. Mafificin hujja kan haka shi ne makomar Mu’alla ibn Kunais, wakilin Imam Sadik (a.s) a Madina da kalmomin Imam game da Mufaddal ibn Umar, wakilinsa a kufa, wadanda ya fade su bisa takiyya.
Lakabin nan guda uku: kofa da wakili da ma’abocin sirri, wadanda muke samun cewa masu su wadansu wanyan mutane ne daga mazajen shi’a suna bayar da haske kan halin da shi’a ke ciki da alkarsu da Imam da kuma harakar tsare-tsare ta shi’a.
Da wannan dubi muna iya fahimtar cewa shi’a su ne jama’ar mutane masu sajewa da junansu, jama’a mai manufa, mai himma, mai matattara a kan wani ginshiki mai tsarki wanda yake watsa haske kan mataimakan sa ta hanyar umurce-umurce da shiriyarwarsa. Su kuma mataimakan suna da alaka da shi, suna kawo masa bayanai, suna kame motsin rai suna kuma fin kafin zuciyarsu albarkacin wasice-wasicensa na hikima. Suna kuma lizimtar salon sirri wajen aiki, kamar kiyaye sirrori da karancin magana da rashin shiga mutane da aikace –aikacen jama’a da kuma nisantar al’amuran kawo juyi.


5