• Farawa
  • Na Baya
  • 36 /
  • Na Gaba
  • Karewa
  •  
  • Gurzawa HTML
  • Gurzawa Word
  • Gurzawa PDF
  • Budawa: 7632 / Gurzawa: 2597
Girma Girma Girma
Hakkoki a Musulunci

Hakkoki a Musulunci

Mawallafi:
Hausa

Dukkan hakkokina cibiyar Muassasar alhasanain (a.s) ne, kuma yada rubuce-rubucen tare da ambaton inda aka dauko su ba shi da matsala. Muassasar alhasanain (a.s)

Hakkoki A Musulunci

Mawallafi: Hafiz Muhammad Sa'id

hfazah@yahoo.com

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Kur'ani Mai Daraja: Kumasama ya daukaka ta, kuma ya sanya sikeli.Kuma ku daidaita awo da adalci, kada ku rage sikelin. Kuma kasa ya sanya ta domin talikai ne.[ 1].

Gabatarwar Mawallafi

Muna godiya ga Allah da ya bani damar rubuta wannnan Littafi game da hakkokin zamantakewar al'umma. Wannan littafin an wallafa shi ne da nufin isar da sakon gyara da sanin ya kamata tsakanin juna a zamantakewa a matsayin al'umma daya, da kuma sanin hakkin Allah (S.W.T) dana mutum a kan dan'uwansa mutum da kokarin ganin kiyaye hakan.

Sanin hakkokin Allah da halittarsa da suke kanmu wani abu newanda yake mafi muhimmanci a rayuwarmu, domin da shi ne zamu iya tasra rayuwarmu ta duniya da lahira. Tun asali ma ba komai ne kasancewar al'umma mai kamala da sanin ya kamata ba sai kasancewarta ma'abociyar kiyaye dokoki da hakkokin da yake kantana mahaliccinta da na sauran halittu da suka hada da mutane da dabbobi da sauran samammu, wannan kuwa a matsayinta na daidaiku ne ko a matsayinta na jama'a.

Mun yi amfani da misalai masu yawa a littafin domin yazama kusa da cimma abin da muke so na fahimtarsa, don cimma buri na kawo gyara ga al'umma da yanayin da kowa zai iya karantawa ya kuma fahimci sakon da ake son isarwa.

Ina rokon Allah yabayar da ladan rubuta wannan littafi ga Ahlul Bait (A.S) kuma ya karbi wannan dan kokari namu ya taimake mu a kan hidimar addininsa.

Hafiz Muhammad Sa'id

Rabi'ul Awwl 1424. H.K

Khurdad 1382 H.SH

Mayu 2003. M

Hakkokin Allah Madaukaki AKanmu[ 2]

Hakkin Allah (S.W.T) shi ne kadaita shi ba tare da yin shirka da shi ba, kuma da bin umarninsa da nisantar haninsa, da bauta masa ba tare da shirka ba, da yin Salla, da Zakka[3], da Azumi, da hajji, da son abin da yake so, da kin abin da yake ki, da tsayawa kan iyakar da ya gindaya mana. Amma akwai magana kan cewa tun da kadaita Allah ba ya yiwuwa sai da saninsa shin zai yiwu a yikoyi[ 4] a akida?wato imani da Allah da kadaita shi ya kasance a bisa dogaro da biyayya ga fatawar malami ko kuwa hakan ba ya inganta?

Sanannen abu shi ne bai halatta ba a dogara da fatawa a kan imani da samuwar Allah ko kadaita shi[5], wajibi ne a akida a yi imani da hakan azuciya tare da gasgatawa da hakan bisa dalili na hankali, wannan kuwa ba ya dogara bisa fatawar malami. Misali a kan haka; da wani malami zai ce da kai: Ka yi sallar Jumma'a da Azahar tare wajibi ne, wato Juma'a ba ta isarwa sai ka hada da Azahar, wannan Malami kuma da shi kake koyi sai ya mutu ko kuma ka gano wani wanda ya fi shi ilimi ya ce: Ai Azahar kawai ta isa ko Jumma'a kawai ta isa yaya zaka yi? Amsa ita ce, sai ka koma wa fatawar Malami na biyu domin nan furu'a ce kuma tana kama da aikin likita ne a Asibiti da kake komawa wanda ya fi kwarewa domin magani ko tiyata.

Amma a Akida da wani malami zaice da kai: Ai ya gano Allah biyu ne ko sama da hakan yaya zaka yi?Sai ka bi shi? A'a. A nan sai ka ce: Malam nan dai rike Akidarka ko ka kawo wani dalili karbabbe na hankali domin ba a yi wa kowa koyi a kan Akida, haka ma da zai ce: Ya gano shi ya yi ka ba Allah ne ya halicce ka ba.

Hakkokin Allah (S.W.T) akan 'yan Adam suna da yawa kuma aiki jajir yana kanmu, sai a mike domin a san su a kuma aikata su. Rashin sanin hakkokin Allah ya sanya jahiltarsa, jahiltarsa kuwa daidai take da jahiltar kawuka kamar yadda ya zo a wasu ruwayoyi, don haka ne jahiltarsa ta sanya rashin saninkawukanmu[ 6], rashin sanin kawukanmu kuwa ya kai mu ga rashin girmama junanmu. Wannan ne ya sanya ba mai girmama ra'ayin dan'uwansa har a siyasar duniya, duba ka ga yadda aka dauki al'amarin addinikansa cikin jahilci ana jifan juna da kafirci, ana kafirta juna alhalin babu wani dalili na shari'a da zai hana ma'abota mazhabobi mabambanta su yi komai are.

Kuma yana da kyau malamai su kafa wata majalisa da zata hada kowane bangare domin kusanto da ra'ayin juna domin tattaunawa da fahimtar juna don amfanar al'umma gaba daya har ma a koyi yadda ake haura katangun mazhabar juna domin wanda ya ga wata mazhaba a wurinsa ita ta fi sai ya haura ya ketara zuwa gareta. Hakanan ya kamata katangun su zama gajeru daidai yadda za su yi dadin haurawa ga mai son haurawa, kuma wannan shi ne yake iya sanya a san abin da kowa yake a kai da fahimtarsa.

Rashin sanin Allah ya sanya ana iya yiwa mutane fashin tunani wanda ya fi fashin kaya da rayuka muni da hadari, har al'umma ta koma jayayya kan abin da bai kamata ya kai ga sabani ba. Duba ka ga rikicikan NEPU da NPC da na PRP da NPN da sauransu, har ma cikin Addini kamar sabani da rikicin 'yan kabalu da 'yan sadalu wanda har ya kai ga sakin aure, da kuma rikicin shin Annabi ya san gaibi ko bai sani ba? Kuma da zaka tambayi masu rikicin menene ma'anar gaibi da ka samu cewa babuwanda ya sani, amma ana iya kashe juna a kan irin wadannan. Nisantar tunani ingantacce mai kyau ya kai ga yin fada akan Bushanci da Sadamanci har da kashe juna a lokacin Yakin Gabas Ta Tsakiya Na Biyu.

Haka nan a wannan lokaci a kan canja wa wasu rikice-rikicen riga sukan fito da sababbun riguna kamar ba su ba ne, sai dai babu mai iya gane su sai mai idon basira da Ilimi da tunani, misalinsa a yau shi ne batun 'yan Shi'a da Ahlussunna.

Bambancin fahimta ba matasla ba ne matukar Allah daya, manzo daya, Littafi daya, in dai ba neman fitina ba, kasancewar wannan mabiyin Ahlul Bait (A.S) ne, wancan kuma mabiyin hanafiyya ne ko shafi'iyya ko malikiyya, ko kuma wancan Sufi ne ko Arifi bai kamata ba ya cutar ko ya jawo rigima da fitina. Ba ma tsakanin musulmi ba, har ma tsakaninsu da wasunsu bai kamata ba a samu sabani da rigima!.

Tsarin Allah Madaukaki

Allah ya saukar da tsarinsa mai cike da hikimawanda ya saba da tsari irin na Kwaminisanci da Demokradiyya, Tsari ne wanda aka jahilce shi a duniya wanda da an san hakikaninsa da hatta wanda ba musulmi ba, ba zai nemi wani tsari ba sai shi. Akwai wasu tsarurruka a Duniya amma ko kadan ba a iya kwatanta su da tsarin Musulunci, Kwaminis ya kafu ne bisa Fomular Hegel da Marks ya dauka ya yi amfani da ita, Hegel ya yi amfani da nazarinsa ne a kafa dalili da ilimin tunanin dan Adam, amma su Marks sun yi amfani da ita a nazari na tarihi ne da kuma juyi na al'umma don neman hada fada tsakanin masu jari da ma'aikata da kuma yakar dabi'ar halittar mutu ta ikon mallaka.Tsari ne mai yakar 'yan jari-hujja da abokan hamayya, amma ta hanyar zalunci da yakar dabi'ar halittar dan Adam da kisan kare dangi, tsari ne da bai san akwai Allah ba.

Amma Demokradiyya Ita tana dauke da jari-hujja ne da ya sanya mutum a matasyin Ubangiji da yake da iko sakakke,yana da ikon ya bautar, ya tatse, ya shanye jinin talaka, sannan ya wurgar da kashin, tsari ne mai tsotse talaka har kashinsa ya mayar da shi kamar kwarangwal.

Amma duba Musulunci ka gani , koma ka san Allah ka ga tsari da mulki wanda ya shimfida da yadda aka sanya dokoki aka ba wa kowane mutum hakkinsa da ya hada mace, namiji, mai kudi, talaka, mai mulki, da wanda ake mulka, da yaro, da babba. Ba zalunci, ba zalunta, ba take hakkin juna, babu yakar dabi'ar halittar dan Adam, ba bambanciko fifiko sai da takawa.

Musulunci tsari ne cikakke bai zo da tsari irin na Demokradiyya ba, ya zo ne daAsalatusShura[ 7], Musulunci tsari ne mazhabi[8], amma Demokradiyya tsari ne Ilmi[9].

Daraja Da Sakamako Gwargwadon Sani Ne

Mu sani kamalar hankali yana cikin sanin Allah ne, kuma Allah yana saka wa mutane da ladan aiki gwargwadon saninsu ne. Duba ka gani mana Annabi Nuhu (A.S) duk da ya dade yana shan wahala an ce tun yana shekara arba'in yake kira ga Allah (S.W.T) kuma ya rayu kusan shekara 2500 amma bai kai darajar Annabi Muhammad ba, ba domin komai ba sai domin cewa annabi Muhammad (S.A.W) ya fi shi sanin Allah (S.W.T), shi kuma Allah yana sakawa daidai gwargwadon saninsa ne ga masu aiki na gari na daga bayinsa.

Wata rana wani Mala'ika ya yi mamakin karancin ladan wani mutum mai yawan bauta ga Allah, sai yake cewa da Ubangiji: Ya Ubangiji yaya wannan bawayana bauta mai yawa amma ladansa kadan ne? Sai Allah ya ce da shi: Ina sakawa gwargawdon sanina ne amma tafi wajansa ka gani, sai Mala'ika ya tafi wajansa, da safiya ta yi suna maganar ciyawa da take fitowa lokacin damuna ta mutu lokacin rani sai mai bauta ya ce da Mala'ika: Ai da Ubangijinka yana da jaki da ciyawan nan ba ta lalace a banza ba da yana da jaki da mun kiwata shi. Hakanan Mala'ika ya ga karancin hankalin wanann bawan shi ya jawo masa karancin lada: Haka nan abin yake wanda yafi sanin Allah ibadarsa ta rana daya tafi ta jahili na shekaru da yawa.

Ga kissar kamar yadda take a ruwaya: Wata rana wani Mala'ika yana yawo sai ya wuce wani tsibiri da wani mai bauta yake rayuwa a ciki sai ya tambayi Allah ya nuna masa ladan wannan mai bauta, sai Allah ya nuna masa, sai Mala'ika ya karanta ladansa, sai Allah ya ce da shi: Ka zama tare da shi, sai Mala'ika ya zo masa a surar mutum, sai ya tambayi Mala'ika: Wanene kai? Sai Mala'ika yace : Ni wani mai bautar Allah ne na ji labarinka ne da ibadarka sai na zo don in kasance tare da kai, sai ya zauna da mai bauta wuni daya, da safiya sai Mala'ika ya ce: Wannan wuri yana da shuke-shuke bai dace da komai ba sai ibada. Sai mai bauta yace : Ai wurin yana da aibi. Mala'ika yace : Menene aibin? Sai yace : Ubangijinmu ba shi da dabbobi, da Ubangijinmu yana da jaki da mun kiwata shi a nan, ga ciyawa nan tana lalacewa a banza. Sai Mala'ika yace : Shin Ubangijinka ba shi da jaki ne? Sai yace : Ai da yana da jaki da wannan ciyawa ba ta lalace ba! Sai Allah ya yi wa Mala'ika wahayi da cewa ni ina saka masa daidai gwargwadon hankalinsane[ 10].

Ko mutane haka suke yi a ayyukansu domin a bisa dabi'ar dan Adam ilimi shi ne yake bayar da kima da daukaka, kuma sabawa dabi'ar haka tana nufin rushewar dan Adam. Wannan al'amarina saba wa dabi'ar dan Adam shi ne ya sanya rushewar tsarin gurguzu, shi tsari ne da ya shahara da yakar dabi'ar dan Adam musamman a abin da ya shafi mallaka.

Misali; A tattalin arziki, lokacin da su Lenin suka so kafa Gurguzu (Kwaminisanci) da suka ga ba zai yiwu ba sai suka kafa Gurguzu mai sauki (Soshiyalizm): A nazarinsu aiki shi ne yakebayar da kima ko mallaka. Saboda haka a misali mai kaya idan ya kai zinarensa wajan makeri don ya yi masa dan kunne da shi, idan ya kera ba zai ba shi dankunne ba sai ya ba shi kudin zinarinsa, domin aikin kira da ya yi shi ne yakebayar da kima da mallaka. Wannan kuwa al'amari ne da yasaba wa dabi'ar dan Adam, a sakamakon haka ne ba su je ko'ina ba suka rushe. Yanzu ta kai ga cewa hatta Akidun da suka dasa na rashin samuwar mahallicci sun rushe, har a ranar 1 ga Disamba 2002 Gidan Rediyo/Telebijin na IRNA ya shelanta cewa: A yanzu kashi sittin cikin dari na mutanen Rasha sun yarda akwai Allah, al'amarin da su Lenen suke ganin haka a matsayin rashin hankali ne sakamakon maye na banju da Duniyar dan Adam ta sha ta fada cikin dimuwa.

Kwatanta aikin Lebura da Purincipal, haka nan kwatanta aikin Manajan banki da na Masinja, da na Saje da Janar, Me ya sa albashin aikin na sama na rana daya ya fi albashin aikin dayan da tazara mai yawa, wannan ba domin komai ba ne sai bambancin sani da tunani da na sama yake amfani da shi fiye da na kasa. Hakanan ne yake wajan Allah tunani da sani su suke bayar da kima ba kawai aiki ba. Amma kada mu manta cewa sanin da baa aiki da shi mummunan abu ne maras amfani.

Masu Hana Sanin Allah Da Hakkokinsa

Sannan kuma ba a bari Annabawa (A.S) sun kafa Daular Allah ba, kai hatta da lokacin Manzo (S.A.W) ya sha matsala da munafukai, amma duk da haka annabawa (A.S) sun kafa ci gaban da ba kamarsa a Duniya.

Kasar Farisa ta fi kowace kasa aikata Addinin Musulunci a hukumance da a siyasance, amma su ma ba su kai kashi hamsin cikin dari ba sakamakon yanayi. Ya zo a ruwayoyi cewa; Imam Mahadi (A.S) ne kawai Allah zai ba shi ikon kafa hukuma ta Allah mai aiki da cikakkiyarshari'a[ 11], shi kuwa zai samu wannan ne saboda Allah zai ba shi damar hukunci da hakikanin yadda abu yake ne ba da zahiri kawai ba[12]. Imam Sadik (A.S) yana cewa: Idan imam Mahadi (A.S) ya shugabanci mutane zai yi hukunci tsakanin mutane da hukuncin Dawud (A.S), ba ya bukatar sheda ko rantsuwa, a kowane hukunci Allah yana yi masa ilhamar hakikanin abin da ya wakana, kuma da dogaro da wannan ilimin nasa ne zai yihukunci[ 13].

Sai ga wasu wadanda suke kirankansu musulmi ba sa son a bi Allah a kasashenmu na musulmi, suna kokarin ganin hana sanin Allah ta kowane hali, da kokarin toshe duk wani kokarin fahimtar addininsa da hakkokinsa a kanmu. Sai ga Addini ana wasa da shi kowa ya fiye bangaranci da mazhabanci sai ga rarraba, sai ga jifan juna da kafirci, sai ga …

Da mutane sun san Allah hakikanin sani kuma suka bi umarninsa, da sun ci arzikinsa tasama da ta kasa. Rashinsaninsa[ 14] ya sabbaba rashin sanin yadda za a bauta masa ko a gode masa. Domin su malam tsutsa sun shiga cikin goro sun hana shi sakat, don haka aka kasa aiwatar da abin da Allah ya zo da shi ta hannun Annabawansa. Don haka ne ya bar wasiyyan Annabi su ci gaba da shiryar da mutane bayansa (A.S), amma duka an kashe su ne daya bayandaya[ 15].

Ba kawai sanin Allah (S.W.T) mahalicci ba har ma furu'a kamar siyasa, da hukunce-hukunce, da zamantakewar dan Adam, da dokoki, da tsarin musulunci duk an jahilci da yawansu a yankunanmu da sauran kasashen musulmi.

Amma nau'in matsalar yammacin Duniya ta bambanta da ta sauran kasashen musulmi ta wani banbare ne, domin su wannan hasken da yake hannunmu da ba a aiki da shi, su ba su da shi, babban misali muna iya duba al'amura kamar a Ilimin zamantakewar dan Adam, su sun sanya mutum ne a matsayin Ubangijin kansa, shi ne mai sanya doka da shar'antawa a bayan kasa amma a Musulunci ba haka ba ne, wannan yana daga abin da ya nesanta su daga sanin Allah.

Hatta Musulmi Sun Jahilci Addini

Kamar yadda yake game da kuskuren da Turai suka yina mummunar fahimta da kuma jahiltarsu game da musulunci, haka su kansu musulmi suka yi masa mummunar fahimta kuma suka jahilce shi. Babban misali a kasashenmu shi ne: Da zaka ambacikalmar shari'a sai mutane su yi tunanin irin fille kai, da jefewa, da gutsure hannaye da kafafu.

Misali da zaka tambayiwanda ba musulmi ba a sabanin da makiyan kasarmu na ciki ko na waje suka haifar kan batun shari'a a Arewa me yake nufi da ba shari'a? Zaice : Ba gutsure hannu da makamantan wannan, haka nan amsar da musulmi zai iya ba ka kenan idan yana maganar shari'a.wato wannan shi kenan shi ne musulunci.

Saboda haka dole ne a tashi don kawar da jahilci da miyagun hannayensa masu guba da suke tafiyar da tunanin mutane game da musulunci har aka kai ga fadawa cikin irin wannan dimuwa. Musulunciyana da fadi ba babi daya ba ne, ya kamata a nemi saninsa daga masanansa na ainihi, ba kowa ne ya san shi ba don ba gado ba ne kuma ba al'ada ba ce.

Ba A Karanta Akidu Da Tarihi

Babbar matsala a cikin al'ummarmuita ce kauracewa Ilimin sanin Allah da shagaltuwa da furu'a kawai, wannan kuwa ya tauye tunanin mutane game da saninsa (S.W.T). Ash'arawa sukan takaita akan Littafin Kawa'idi ne da mafi yawa ba sa ma fahimtarsa, wanda ya yi zurfi shi ne wanda ya kai ga Sharhi Ummul Barahin, da kyar zaka sami wanda ya wuce hakan sai daidaiku. Ba a ma san Al'makalat da Al'ibanana Al'ash'ari shi kansa mai Mazhabar Ash'ariyya ba, yawanci ba a san wanda ake bi a Mazhaba ko Akida ba.

Haka sanin Allah ya yi nesa da mutane suka yi nisa da shi, haka ma al'amarin tarihin musulunci da ba a karanta shi wai akwai rigima a ciki da ba a so a sani, wai idan aka yi fada da uwa da uba Shin ka so ka sani?

Saina ce da mai wannan tunani: Da bambanci, domin na su baba bai shafi makomarka ta Lahira ba, kuma ba ka son sanin waye Manzo (S.A.W) ya bari tsakaninsu wanda bin sa ya zama hujja a kanka. Ammana tarihin musulunci ya shafe ka, domin zai gaya maka makomarka ne, da abin da Manzo (S.A.W) ya bar maka a matsayin tsiranka a duniya da lahira.

Na biyu, ana bukatar ma'aunin waye maganarsa ta fizama hujja don ka yi aiki da ita, wannan duk ya shafi makomarka ne.

Haka aka haramtawa al'ummarmu sanin Akidu da ilimomi har ka san menene gasakiya ka bi, menene a ganinka ba daidai ba ne ka bari. Duba ka gani mana Shehu Dan Fodia (R.A) yana ganin daga cikin bala'in da ya game kasashenmu na Hausa shi ne koyi a Usuluddin amma har zuwa yanzu abin da Shehu ya so a kawar na koyi a Usuluddin ya ci gaba. Koda yake wasu malamai sun tafi akan cewa; wanda ya fadaka, ya yarda har a zuciyarsa, ya yi imani da samuwar Allah da kadaita shi a bisa sahihiyar Akidar musulunci, duk da tun yana yaro ya yi koyi da malamai ne ko iyaye, amma irin wannan imanin yana isarwa gare shi.

Hakkin Da Yake Kan Annabawan Allah

Annabawa (A.S) sun zo ne domin motsahankali[ 16] ya yi tunani ya yi imani a Akidar samuwar Allah da kadaita shi a ibada da zatinsa da siffofinsa da ayyukansa, da kuma yarda da annabawan da ya aiko da riko da sakonnin da suka zo da su. Annabawa ba suce a bi su ido rufe ba dalili ba, wannan al'amari ne ya sanya Allah yake ba su mu'ujiza da take dalili ce na hankali a kan cewa sakon da suke dauke da shi daga gareshi ne, wannan kuwa zai samar da nutsuwa a zukata har su karbi sakonsa.

Amma hukuncin furu'a (hukunce-hukunce) su an sanya su bisa biyayya da maslaha ne wacce ba kasafai aka santa ba sai dai a bi umarnin Allah a ciki, don haka ne Allah yake sanya wa kowane Annabi (A.S) wasiyyi da zai yi wa mutane bayanin abin da sakon ya kunsa bayan wafatinsa, kamar yadda annabin rahama (S.A.W) ya yi wasiyya ga wannan al'umma da imam Ali (A.S) da goma sha daya daga 'ya'yansa a bayansa.

Matsalolin da wasiyyan Annabi suka fuskantana kawar da su daga fagen jagorancin al'umma a hukumanci da kisa sun sanya Allah (S.W.T) ya boye na karshensu imam Mahadi (A.S) domin kada a kashe shi domin ya zo a karshen duniya ya cika ta da adalci bayan an cika ta da zalunci. Shi kuma imam Mahadi (A.S) kafin ya boyu ya yi wasiyya da riko da malamaina gari. Saboda haka duk wanda ya kai matakin Ijtihadi wato ya daukaka kan sauran mutanen duniya gaba daya a ilimi, da takawa, da adalci, da kamala, da tsentseni kuma ya kasance dan halal ne, to ya zama dole ne a bishi[ 17].

Hakkin Imami (Shugaban Zamani) A Kan mu

Sanin Imamin lokacinmu yana daga cikin hakkokin Allah a kanmu, domin duk wanda ya mutu bai san Imamin zamaninsa ba ya yi mutuwarJahiliyya[ 18], haka nan ya zo a Kur'ani mai girma cewa a Ranar Lahira kowace al'umma za a kira ta tare da imaminta ne[19]. Wadannan imamai Allah bai bar mu mun zabe su da kanmu ba sai da ya shelanta su ta hannun Manzonsa (S.A.W)[ 20] wanda ya sanar da mu cewa su goma sha biyu ne: Na farkonsu Ali (A.S) na karshensu Mahadi (A.S) wanda yake shi ne imamin wannan zamanin.

Sanin Imam ba wai kawai sanin sunansa ba ne, saninsa ya hada da binsa kuma da koyi da abin da ya bari na wasiyyarsa kuma da bin koyarwarsa da malaman da suke shiryarwa zuwa ga abin da ya bari da kinmakiyansa[ 21]. Al'amarin ba wasa ba ne kamar yadda wasu suke dauka domin ko Salla da Azumi da duk wata ibada idan babu mika wuya ga Imami Allah ba ya karba. Manzon tsira (S.A.W) yace : "Wanda ya mutu bai san Imaminsa ba ya yi mutuwar Jahiliyya"[22]. Domin zai tashi a Ranar Lahira kamarwanda ya yi zamani kafin a aiko Annabi ba shi da komai da Allah (S.W.T) ya karba daga gare shi.

Hakkokin Littafin Allah A Kanmu

Karanta littafin Allah da saninsa suna daga cikin hakkokinsa a kanmu,amma sanin littafin ba yana nufin mu san sunansa ba kawai domin hakan ko kadan ba shi da wata ma'ana, amma abin nufi shi ne ya zama mun siffantu da Kur'anin a aikace. Idan ba haka ba a ranar lahira akwai kara da zai shigar a kotunAllah[ 23] wacce ba a zalunci a nan kuma ba a iya boye gaskiya. Kuma dole a bi shi kamar yadda Manzo da wasiyyansa goma sha biyu daga Alayensa suka fassara domin su ne yace : "Idan an yi riko da su ba za a taba bata ba har abada".kuma "Da Su da Littafin Allah ba sa rabuwa har sai sun riske shi a tafki"[24].

Hakanan al'amarin yake a matsayin al'umma, dole ne Littafin Allah ya yi iko da rayuwarmu a matsayin al'umma, in ba haka ba, ba mu sauke nauyin da yake kanmu ba. Kuma dole ne mu siffantu da shi, in ba haka ba,yana da hakkin karar cewa musulmi sun bijire masa.

Hakkokin Addini A Kanmu

Addinin Musulunci yana da hakki na kare shi a kan kowane musulmi da bakinsa da basirar da Allah ya ba shi, da wajabcin saninsa da taimakawa wajan yada shi aaikace[ 25] da baki da kyawawan dabi'u, da kokarin hada kan mabiyansa, da raddi cikin hikima ga masu gaba da shi, da girmama fahimtar ma'abotansa don ba ka sani ba ta yiwu shi mai waccan fahimtar da ta saba da taka shi ne yake a kan daidai.

Kada mutumin da bai fahimta ba ko bai sani ba ya tsoma baki da jayayya a kan mas'alolinAddini[ 26] wannan na malamai ne, kamar yadda shehu Usman dan fodiyo (R.A) ya yi nuni da haka yayin da yake nuni da bidi'oin da aka farar cikin Addini da cewa: Shi malami kada ya sa mutane cikin rikicin Addini haka ma maras Ilimi kada ya sanya kansa cikin rikicin Addini, bayyana ra'ayi kan mas'aloli abu ne na malamai.

Hakkokin Garuruwa Ne A Tsaftace Su

Rashin kula da tsafta daga bangaren gwamnati da kuma al'umma yana daga cikin mummunan al'amari da addabi birane da kauyuka, ta yadda zaka ga duk ko'ina ana iya zubashara[ 27]. Ga mummunan tsarin da garuruwa suke fama da shi, sai a sayar da hanyoyi har da hanyar ruwa ta yadda damina da kwararar ruwa zasu wahalar da talaka, ga karancin manyan hanyoyi da matsattsun kanananlunguna[ 28]. Idan kuwa damina ta zo talakawa suna fargaba ne, ga miyagun lunguna da kududdufai marasa hanya, amma ba za a rushe gidaje a fadada hanyoyin ruwa dana motoci da yin kwatami don samar da magudanar ruwa ba.

Mafi girman abin takaici shi ne abin da na gani a Jami'ar Bayaro da na dade ban ga irinsa ba, sai na ga takardu a ko'ina a kasa, matattakala duk da tabo ta yi bakin kirin, muna tsaye muna hira sai wani ya watso ruwa daga sama duk ya kusa bata mu, idan kuwa ka wuce wasu wurare wari yana tashi. Saina fara tunanin Jam'iar Tehran da wuri ne kodayaushe kamar ka sanya abincinka a kasa ka ci, na rika tunanin cewa a yanzu da wani zai zo daga abokanmu daga Jami'ar ya ga wurin kwanan dalibai kawai da an ji kunya. Kuma da zaka tambaya akan me aka gina imani? Daya daga mafi muhimmancinsuita ce tsafta: Hatta ma wasu hukunce-hukuncen Allah yakan sanya su ne domin kai wa ga cimma samuwar tsafta a cikin al'umma.

Ba ma jami'a ba,a irin wadannan kasashe a cikin gari duk wani yanki a kowane dare yana da motoci na musamman wadanda da dare sukan wanke titinan yankin.Amma wani abin takaici a kasarmu ba ma kawai tsaftar gari ba, kana iya ganin yanki da miliyoyin mutane suke rayuwa ba tare da wani isasshen ruwan sha ba.

Hakkokin Da Suke Tsakanin Mutane

Kowane mutumyana da hakkoki masu yawa a kan dan'uwansa mutum musamman abokin zamantakewa na kasa ko gari, ko makaranta, da duk wani waje da alaka ta kan hada juna kamar wajan aiki. Babban ma'aunina hakkin junanmu a kanmu shi ne wanda ya zo a cikin Hadisai na cewa: "Mu duba duk abin da muke so a yi mana sai mu yi wa mutane shi, mu kuma duba duk abin da muke ki a yi mana shi sai mu guji yi wa mutane shi"[29]. Misali kana kin a wulakanta ka, kuma kana son a girmamaka, to anan sai ka ki wulakanta mutane kuma ka girmama su.

Wannan hadisi da za a yi aiki da shi, da Duniya gaba daya ta zauna cikin aminci, da ta juya ta zama kamar aljanna, da so ya game tsakanin mai kudi da talaka, da mai ilimi da maras ilimi, da miji da mata, da 'ya'ya da iyaye, da malami da dalibi, da mai mulki da wanda ake mulka, da dukkanin nau'i na mutane gaba daya.

Wannan hakkoki kuwa sun hada nisantar cutar da waninmu ta kowace hanya kamar dukako da kuwa dalibinmu ne, amma a kasashenmu duka wani abu ne mai sauki. Kai a makarantun Furamare dana Allo har yakan yi muni kwarai; mai dukan ba ya neman izinin Shugaban musulmi, ko uban da, sai a yi ta jibga ko mai kankantar abu.

Duka ba ya halatta koda kuwa uwa ce ga danta sai da izininuba[ 30], ko dukan uba ga dansa ko wanda Shugaban musulmi ya ba wa izini. Shi ma uban a matsayin tarbiyyantarwa da yazama sai ta hakan, kuma ba mai cutarwa ba. Ko kuma miji ga mace mainushuzi[ 31], shi ma a mataki na uku na karshe[32] kuma ba mai cutarwa ba, sai kuma Shugaban musulmi ga mai laifi kamar a haddi ko ladabtarwa.

Daga cikin hakkin mutum a kan waninsa shi ne ya shiryar da shi abin da zai amfanar da shi, kamar hakkin mutane a kan likita na ya nuna musu hanyar tsafta da kare lafiya, da yadda zasu tsara abinci da abin sha mai sanya lafiya, da magunguna, musamman ta hanyar Gidan Radio da Talabijin; Da maras lafiya zai tafi wajan likita sai ya cutar da shi to dole ne ya biya shi diyya, amma idan da gangan ne sai a yi masa kisasi.

Kamar yadda yake wajibi ne a kan malami ya shiryar da al'umma kuma ya ilmantar da ita, mai kudi kuwa ya yi odar abin da yake tattalin rayuwa na al'umma kuma ya sanya farashi da talaka zai iya saya cikin sauki, haka ma injiniya ya kyautata mota ta yadda ba zata zama hadari ga mai hawanta ba, mai gini kuwa ya kyautata shi.

Hakanan yana kan mai sayan kaya ya girmama mai sayarwa shi ma mai sayarwa ya mutunta mai saya, likita da marasa lafiya, mai kudi da talaka, malami da marasa sani, mai haya da dan haya, mai aiki da shugaba. Bai kamata ba shugaba a ma'aikata ya rika kallon masinja kallon wulakanci, hakki ne akansa ya girmama masinja, ya tuna shi ma dan kasa ne kamarsa kuma ma'aikaci da bai fi shi da komai ba a wajan Allah sai dai idan ya fi shi takawa domin ita ce ma'aunin fifiko. Haka ma dan hayar mota kamar Taksi da Bos (hayis) kada yazama idan ya ga fasinja yana ganin naira goma ne ko biyar ko ishirin, hakki ne a kansa ya ga mutum yake kallo kafin ya ga Naira ishirin, kuma ya yi mu'amala da shi ta mutunci da girmamawa tsakanin juna.

Haka nan alakar na kan mota da na kan jaki, da na jirgin sama da na kasa[33], duka daya ne a wajan Allah kuma ba mai fifiko sai da takawa, rashin kiyaye wannan da mantawa da Allah ya sanya rashin kiyaye hakkin juna.

Wani misali a kan haka shi ne; wata rana wani mai kudi shahararre ya taba kade wani almajiri da mota a kan titi, maimakon mutane su nemi ya bayar da kudin magani a kai almajirin kyamist tun da shi ba shi da mutuntaka domin ba ya ganin almajirin mutum ne kamarsa don ko taba shi bai yi ba, sai suka zo suna ba shi hakuri. Har da cewa: Ai da ma haka almajirai suke basa jin magana. Haka mutakabbirin ya hau mota ya wuce! Shi kuwa bawan Allahyana ta nishi har ya samu da kyar ya taka. Su kuwa mutanen ba mai ji a jikinsa cewa an jiwa wani mutum daga cikin mutane masu hakki kamar kowa ciwo! Wallahi da dabba ce aka kade da sun fi ba ta muhimmanci!.

Daga cikin hakkin mutun a kan dan'uwansa mutum taya shi bakin ciki idan wani abu ya same shi musamman ma dan'uwa na jini ko na Addini da makwabci, kamar idan an yi masa mutuwa to ya kamata ne bisa koyarwa ta Manzo (S.A.W) a yi abinci kwana uku daga makwabta ana kai musu kamar yadda ya koya mana kyawawan dabi'u da fadinsa: "Ku yi wa iyalan Ja'afar abinci hakika wani al'amari da ya shagaltar da su ya same su"[34]. Amma abin sai yazama bisa akasi, maimakon a kai gidan mutuwa, sai ya zama su ne kuma za a shagaltar da su da ciyar da masu taruwa.

Idan muka waiwayi alakar mai kudi da yaronsa al'amarin ya kai ga ana iya samunyaron Alhaji da rashin lafiyarsa bai fi a kashe kudi kankani a kansa ba ya warke amma yana iya mutuwa alhali Alhajin da ya yi wa hidima a gida, da shago, da kanti, shekaru masu yawa yana gani sai dai ya mutu. Wani kumayana aiki karkashin uban gidansa amma canja riga mai tsada yana iya tayar da mugunyar tsatsar nan ta hassada a zuciyar uban gidan, sai ya ce da shi: Ka tattara naka ka yi gaba kuma ka bar min shagona.

Akwai wata kabila da galibinsu ba ma musulmi ba ne amma har bikin yayeyaron shagonsu suke da shi. Idan kuwa ka duba bangaren kere-kere to anan sun yi nisa, sannan wasu abubuwan idan kana nemansu ranar lahadi to lallai ka wahala domin sun kulle shaguna. Don haka idan ana son mafita da cigaba ya zama dole ne a siffantu da siffa ta gari a bar hassada da kyashi, a cire duk wata dauda daga zuciya. Idan wani ya cigaba ta hanyarmu sai mu gode wa Allah, amma rashin kishin kai da son ci gaban juna, da rashin kyawawa dabi'un musulunci ya sanya ana danne hakkin juna, kuma mu sani cewa dukkan ayyukanmu suna da hisabi a Lahira.

Hakkokin Mai Mulki Da Wanda Ake Mulka

Wannan yana iya bayyana ne ta hanyar sanin wanene shugaba da siffofinsa, domin idan mun san siffofin mai mulki to muna iya gane wannan alaka ta hakkokin mai mulki da wanda ake mulka: Daga cikin siffofin shugaba su ne; ya zama mai karfin tafiyar da mulki da Iliminsa da basirarsa, mai karfin zartarwa, kuma amintacce, wanda ba ya cin amanar al'ummar kasarsa.

Maineman maslaha ga al'ummarsa, mai daukarsu a matsayin 'yanuwansa, maras tsanantawa a kan mutanensa. Kuma mai sakin fuska, mai hankali, da ilimi, da adalci, mai karbar shawara daga mutanensa wajan gudanar da al'amuranta, mai daidaitawa tsakanin mabiyansa ba tare da son kai bako fifita wasu kan wasu.

Hakanan ya kasance mai kwarjini, mai kyawawan dabi'u da son gyara, mai hidima ga mutanensa, masanin siyasar Duniya da al'amarin tafiyar da al'umma, mai karbar nasiha daga talakawansa ko wakilansu, mai saukin hali. Ya kasance ba ya daukar fansakan abokan hamayya, kuma mai kyauta ba marowaci ba, mai kaifin basira da yakan iya mayar da makiyi masoyi saboda kyawawan halaye da basirarsa, mai tausasawa ba mai tsanantawa ba.

Duba wasikar da Imam Ali (A.S) ya rubutawa Malik Ashtar yana cewa da shi: "Ka nisanci fushin al'ummarka domin fushinsu yana tare da fushin Allah"[35]. Mu sani cewa idan shugaba zai kallikansa ne to lallai zai fada cikin fushin al'umma domin su ba su da abin da yake da shi, wasu shugabannin sukan kara kudin kaya ba ruwansu da talaka, sai ka ga al'ummar ta koma tana kinsa ba ta ganinsa daya daga cikinta, da zai wuce tana iya jifansa.

Amma a tsari na adalci dole ne shugaba ya ji cewa shi daya ne daga cikin 'ya'yan al'ummarsa, wannan zan sanya idan ta gan shi ta nuna shaukinta da kaunarta gareshi, idan ya mutu tana nuna bakin cikinta kamar yadda a wannan zamani namu ya faru ga Imam khomaini da mutane sama da miliyan ishirin suka zo jana'izarsa, mutanen kasarsa suka yi kwanaki suna kuka, kasar gaba dayanta ta shelanta zaman makoki na kwanaki. Ta haka ne akan gane waye ya yi wa al'ummarsa adalci?Waye kuma ya zalunce ta?

Akwaiwanda ya taba rike babban mukami a kasar nan amma da ya mutu mutane da yawa sun yi bukukuwan murnar mutuwarsa, aka hole aka yi annashuwa, a kan titina. Akwai kuma wadanda suka mutu amma har yanzu al'umma tana bakin cikin rashinsu, wannan kuwa ya isa wa'azi gana yanzu rayayyu.

Hakkin Shugaba A Kan Al'umma

Daga cikin hakkokin shugaba su ne; a yi masa biyayya ga abin da baisaba wa Allah (S.W.T) ba. Kuma wasu bayanai sun zo game da cewa; yana daga hakkin shugaba a kan al'umma a ba shi shawara da nasiha, idan kuwa zai kauce hanya sai a tuna masa, sannan a taimaka masa domin ci gaban addini da al'umma gaba daya[36].

Dan kasana gari shi ne wanda yake kiyaye doka koda kuwa ta kan titin mota ce. Wani malamin Ilimin tafiyar da al'amuran al'umma ya taba ba mu labari cewa: Wata rana ya dauko wani dalibinsa suna tafiya, sai suka isa wata danja ba motako daya amma bangarensu ba a bayar da hannu ba sai ya wuce. Sai dalibinsa yace : Amma da an kiyaye. Sai yace da shi: Ai ba mota. Sai dalibin yace : Amma da ka girmama dokar da kuma wadanda suka sanya dokar, don sun yi tunani kafin kafa ta, kuma don maslahar kanka da ta sauran 'yan kasa ne. Ya ce: Sai ya yi kwana ya koma ya sake jira sannan ya wuce. Tun rannan ya amfana da nasihar dalibinsa kuma ya yi masa godiya.

Hakkokin Dan Kasa A Kan Shugaba

Yana daga cikin hakkokin dan kasa a samar masa da aminci, da kariya,da lafiya, da ilimi, da hakkin fadin ra'ayinsa, da hakkin zamantakewa, da na walwala, da dukkan abin da ya shafi ci gaban rayuwarsa ta Duniya da Lahira. Hakanan yana da hakki kan masu tsaron kasa, amma wani abin haushi shi ne; samun tazara mai yawa tsakanin masu tsaron kasa da al'umma, ta yadda al'umma ba ta ganinsu wani bangare nata. Wannan kuwayana faruwa ne sakamakon ba sa ji ko kadan cewa suna aiki don al'ummarsu ne kamar suna aiki don shugaba ne.

Wannan mummunan kuskure ya sanya masu kare doka sai su yi zalunci babu tausayi, har ma takan kai ga lahantawako salwantar da rai, kuma ga karbar cin hanci da ya zama ruwan dare. Koda yake a ciki akwai mutane masu hankali da kula da aiki da son taimakon al'umma kuma basa karbar cin hanci, irinsu ne suke iya mutuwa wajan kare mutanensu, amma da yawa ba haka suke ba sai dai kokari wajan neman na aljihunsu kawai sun manta da manufarsu. Wani lokaci kamar suna cike dajin haushin mutane ne, ta yadda da sun kama mai laifi sai duka da azabtarwa, alhali shi mai laifi koda kuwa barawo ne da makamancinsa mai kare doka ba shi da hakkin yi masa wani abu sai dai ya kai shi kotu ta yanke masa hukunci.

Ban taba sanin cewa al'umma tana da tazara mai yawa da 'yan doka ba sai ranar dana samu nawa rabon, har ma wani yana jinginamu da wata kasa kai ka ce su ba mutane ba ne. Wani daga cikinsu ya ce: Irin wannan ku rika guduwa tun da ku ba ma su laifi ba ne! Kai ka ce su makafi ne da ba sa ganin mai laifi!. A ofishinsu ne na ga wani ana ta dukansa wai ya yi taurin kai a shiga mota, ana buga kansa da kasa, shi kuwa yana ta la'antar duk wani uba ko uwa na dan sanda.

Kuma anan ne na yi mamakin yadda wani tsararre yake la'antar uwar ma da ta haifi dan sanda, har ma ya ce: Babansa ya taba cewa da shi tun da ya rasa aiki ya yi aikin dan doka. Sai yace : Ai baba gwara ka tsine mini in san ni tsinanne ne da in yi wannan aiki, ya kara da cewa: Wallahi in gawa ta kai dubu to shi zai iya gano ta dan sanda a ciki don fuskarsa ba ta cikawa da imani.

A lokacin ne na san cewa lallai akwai tazara mai yawa sosai tsakanin 'yan sanda da al'umma, amma ra'ayin mutane da yawa ya tafi a kan cewa: Zafin zalunci da take hakkin dan Adam shi ya jawo haka, ta yadda mai tsaron kasa yake ganin yana yi wa shugaba aiki ne ba al'ummarsa ba, kuma yana ganin hadafinsa shi ne ya huce haushinsa kan al'ummarsa, sai ya cire wa al'umma jin cewa shi daga cikinta yake.

Haka al'amarin yake game da soja, kamar yadda dan sanda yake da hakkin kare cikin kasa dasamar da aminci, haka ya zama wajibi a kansa ya kare kasa daga waje kada wani ya kai farmaki kanta. Amma wani abin takaici al'umma ba tajin su nata ne haka su ma ba sa jin al'umma ta su ce. A misali da za a yi rigima tsakanin wani dan kasa da soja, da zaran sojoji sun isa wurin basa tambaya, a wurinsu mai gaskiya shi ne mai kaki na soja. Wannan rashin ganin juna a matsayin abu daya ya shafi har matsayin auratayya, dominna sha jin soja (ladani ne) yana nasiha a masallacin Barikin Bukabu da yake Kano yana cewa: Me ya sa ba a zuwa daga gari a auri 'ya'yansu?Ko su ba kamar sauran mutane suke ba. Hakanan aka jahilci hakkin juna tsakanin mai tsaro da wanda ake tsaro har ya zama kamar al'umma daban-daban ce a cikin al'umma daya.

Duba ka ga me Imam Ali (A.S) yake cewa game da mai tsaron kasa: "Runduna:Ita ce kariyar al'umma da izinin Allah, kuma adon shugabanni, izzar Addini, hanyoyin aminci, al'ummar kasa ba ta tsayuwa daram sai da su"[37]. A wani wurinyana cewa: "Ka sanya wa rundunarka jagora wanda ya fi su nutsuwa da biyayya ga Allah da Manzonsa a ganinka. Wanda ya fi sirrina gari (wato mai dabi'u masu kyau), wanda ya fi su hakuri, da ilimi, da sanin tafiyar da al'amuran al'umma, da rashin saurin fushi, kuma da karbar uzurin mutane. Mai tausayawa talakawa, marasbayar da dama ga masu karfi. Wanda takurawa ba ta harzuka shi, rauni (karayar zuci) ba ya dunkufar dashi[ 38]. A cikin wannan akwai nuni da cewa: Cin hanci shi ne abin da yake kawo bawa mai karfi dama ya taka doka. Kuma akwai nuni da cewa: Bin hakkin dan kasa wajibi ne akan hukuma a ko'ina ne yake, al'amarin da ya yi karanci a kasashenmu ko ma ba a san da shi ba.

Yana daga cikin hakkin dan kasa asamar masa da wurin shakatawa da walwala da wuraren hutawa da na wasanni da shi da iyalinsa da yaransa.Wani abin takaici irin wadannan filayen da ake warewa unguwanni domin wasanni saudayawa maciya amanar al'umma suka sayar da su al'umma tana gani, mafi ban haushi da muni shi ne mafi yawa ba su san ma cewa wannan hakkinsu ba ne.

Hakkokin Mutane Game Da Arzikin Kasa

Hakanan talaka ba ya ganin ma yana da hakki a arzikin kasa, in banda 'yan kwanakin nan da wasu 'yan kadan suka san hakan, al'amarin har ya kai ga wasu daga masu tafiyar da al'amarin al'umma suna neman jahiltar hakan. Saudayawa mai mulki ba ya kiyaye hakkinwanda yake mulka game da arziki da albarkatun kasa, idan kuwa ka ce zaka yi magana kan sauran kayan rayuwa a nan kam sai dai ka mutu da bakin ciki. Duba ka ga wutar lantarki, da ruwan famfo, da man fetur da kasarnan take ita ce ta biyar a duniya a yau. Kuma duba ka ga wasu kasashe da mun fi su karfin tattalin arziki amma ba su da wata matsalar irin wadannan abubuwan rayuwa, man fetur kuwa a wajensu kusan mafarki ne wani ya ce ya ga dogon layi ko babu, kuma a gidaje akwai wuyarin na wutar lantarki da fayef na famfo da na Gas, wannan kuwa duk sun yi shi ne cikin shekaru kadan. Kuma mutanensu suna biyan kudi kankani ne domin duk talakayana iya biyan kudin. Haka ma a gidaje akwai kayan sanyaya gida a lokacin zafi kuma da abin dumama daki lokacin sanyi, amma wadannan abubuwan a kasarmu a gun talaka wani kayan masujin dadi ne.

Wani abin kunya da dan Nijeriya yake sha a duniya shi ne; ga shi kasar a waje tana da kima saboda sunajin labarin tana da arziki, amma hatta da gasar kwallon kafar da aka yi a kasar sai ana yi ana dauke wuta. Irin wannan al'amarin ya faru wata rana yayin da muka isa tashar jiragensama ta Kano, ga fankokin kansu suna bayar da zafi ne amma duk wannan bai isa ba sai aka dauke wuta, wani mutum (ba dan Nijeriya ba ne) ina ji ya ce: Kai ka ga Air port sai ka ce kango. Hakanan ake tara wa 'yan kasar abin kunya a kasashen waje kai ka ce masu mulki ba sa zuwa wasu kasashe suna ganin abin da yake faruwa.

Hakkokin Mutane A Kotuna

Idan kuwa ka waiwaya kotu abin ya yi muni sosai, amma akwai ma'auni na gane kotun zalunci da kotun adalci, Idan ka ga kotu mai kudi da sarki suna jin tsoronta to ana adalci ne kuma ana bin gaskiya ne, amma idan ka ga talaka kawai ne yake tsoron kotu to ka sani ana zalunci ne. Wani lokaci akan ja shari'a da ya kamata a yanke ta a sati ko awowi kadan amma sai ta yi watanni da shekaru har ma mai hakki ya ce ya yafe, ko ya gaji ya bari don kansa. Wani lokaci hakkinyana rutsawa da kudin marayu ne amma sai ka ga kotu ta ajiye a banki tana samun kudin ruwan, wani lokaci ma ba ya isa sai an diba daga hakkin maraya an sa a aljihu. Wani lokaci kumaakan iya mirgide gaskiya ko jifa da hauka ga wani don wani ya kubuta, da haka ne hakkoki masu yawa na mutane suke salwanta.

Hakkin Malami A Kan Dalibi

Malami yana da hakki a kan dalibi, a takaice muna iya cewa: a girmama shi, da sauraronsa idan yana magana, da barinsa ya amsa tambayar da wani ya yi masa, da kaskantar da kai a gare shi, da kare shi daga mai sukansa, da rufa asirinsa ko aibinsa, da yada kyawawansa da alherinsa, kada ka zauna da makiyinsa, kada ka yi gaba da masoyinsa.

Hakkin Dalibi A Kan Malami

Malami ya tausayawa dalibai kuma ya san cewa su 'ya'yansa ne don haka yana neman tsiransu ne, kada kuma ya taba yi musu gori ko kausasa musu hali.Kuma ya rika yi musu nasiha, ya nisantar da su daga miyagun halaye, kada ya muzanta musu wani ilimi da ba a wajansa suke koyonsa ba, kamar idan shi malamin nahawu ne to kada ya rika kushe musu Ilimin mandik, ya rika yi musu magana daidai fahimta da kwakwalwarsu, kada ya yi musu rowa ta Ilimi.

Hakkin Mace A Kan Mijinta

Daga cikin hakkin mace akan mijinta shi ne ya girmamata, kuma ya tausaya mata da tausasawa, ya ciyar da ita, idan ta yi laifi ya yafe mata, kada ya la'ance ta ko ya zage ta ko ya doke ta, kada ya muzanta ta ko ya kunyata ta ko ya daidaita mata asiri.

Haka nan akwai hadisai da dama da suka zo game da falalar mutumen da yake taya matarsa aikin gida, don haka bai kamata ba al'ada ta rinjayi Addini, don wasu sukan ki hakan saboda wani dalili maras ma'ana na al'ada.

Dole ne miji ya yi adalci ga matarsa da tsakanin 'ya'yansa da matansa, kamar yadda yake wajibi akansa ya nuna mata soyayyarsa, kuma ya nuna mata wannan a fili ta yadda zata zama abokiyarsa a komai. Kuma ya rika yi mata maganganu irinna soyayya da nuna kauna ga juna, bai isa ba ya ba ta kudi kawai don yana da shi, wannan ba ya isa ga bukatun mace. Shi yasa Allah (S.W.T) ya fada a cikin littafinsa cewa: "Ya sanya soyayya (kauna) da tausayi (rahama) a tsakaninku"[39].

Hakanan ba shi da kyau ga miji ya munana zato ga matarsa, ko ba komai munana zato ga musulmi haramun ne, idan mace ta san mijinta yana munana mata zato alhalin tana mai kame kanta wannan yana iya rusa alakar soyayya da girmama juna da ke tsakaninsu har ya kai su ga rabuwa.