• Farawa
  • Na Baya
  • 15 /
  • Na Gaba
  • Karewa
  •  
  • Gurzawa HTML
  • Gurzawa Word
  • Gurzawa PDF
  • Budawa: 8133 / Gurzawa: 2005
Girma Girma Girma
Gudummawar Mace

Gudummawar Mace

Mawallafi:
Hausa

Mace a Rayuwar Annabawa (A.S)

Hakika mace ta kasance tana da babban kashi hayyananne a tafiyar kira zuwa ga Allah da yunkurin Annabawa da Manzanni (a.s.). Hakika mace ta taka muhimmiyar rawa wajen yakin tunani da siyasa, ta kuma sha azaba, kisa, hijira da dukkan nau'o'in wahalhalu da ta'addancin tunani, siyasa da fin karfi. ta kuma mike ta bayyana ra'ayinta bisa 'yanci, ta shiga cikin kira zuwa ga Allah, duk kuwa da abin da ya same ta na hasarar mulki, matsayi da dukiya; da abubuwan da ta hadu da su na kora, kisa da ta'addanci.

Misali akan haka ita ce Maryam Uwar Annabi Isa (a.s.), wadda AlKur'ani ya girmamata kamar yadda Annabin Musulunci (s.a.w.a.) ya girmamata. Hakika Alkur'ani,a ayoyi masu yawa, ya yabi wannan mace abin koyi, ya kuma kaddamar da ita a mastsayin wata abin koyi ga maza, kamar kuma yadda ya gabatar da ita abin koyi ga mata don su yi koyi da dabi'unta da daidaiton tunaninta da mutuntakarta.

Dukwanda ke karanta tarihin mace cikin da'awar Allah, zai same ta ana magana da ita kamar yadda ake yi da namiji, ba tare da maganar Allah ta nuna wani bambanci tsakaninsu ba saboda kasancewa namiji ko mace.

Ta hanyar nazari tarihin rayuwar mata cikin tafiyar kira zuwa ga Allah, za mu iya fahimtar matsayina ja-goranci da tasiri da mace ta samu a rayuwar Annabawa da kiraye-kirayensu, da haka kuma kimar mace a cikin al'ummar Musulmi da shigar ta cikin harkokin siyasa, da hakkokinta na mutuntaka da doka, za su bayyana. Za mu ga irin wannan tarayya mai fadi idan muka karanta kissar gwagwarmayar uban Annabawa Ibrahim (a.s .) da mutanensa a Babil da ke kasar Iraki, da fito-na-fitonsa da Namarudu, fito-na-fiton nan da ta kare da tsirar Annabi Ibrahim (a.s.) daga wuta ta hanyar mu'ujizar Allah wadda tafi karfin tunanin hankali na zahiri.kumaal'amarin da ya sa shi (Annabi Ibrahim) yin hijira zuwa garin Sham. Matarsa Saratu wadda ta yi imani da kiransa ta kasance abokiyar jihadinsa.wadda ta kasance tare da shi a lokacin hijirarsa zuwa Sham.daganan zuwa Masar.kuma ya sake dawowa Sham ya zauna a can.inda wani babban zango daga zangogin tarihin dan Adam ya fara a hannun Annabi Ibrahim (a.s.) alhali matarsa Saratu na tare da shi, tana tsaye a gefensa cikin jihadinsa, wahalhalunsa da hijirarsa.

Alkur'ani mai girmana magana game da kissar hijira da rayuwar wannan iyali, kamar yadda yake magana game da gudummawar matar Ibrahim (a.s.) ta biyu, da shigar ta wajen rubuta littafin wannan zango mai haske a tarihin mutum a kasar Hijaz, a garin Makka mai girma wanda ya iso shi yayin da ya baro Masar.

Hakika kissar wannan matana daga mafi shaharar kissoshin tarihi kuma wadanda suka fi ban mamaki kuma suka fi girman gwagwarmaya da hakuri. domin ta ta'allaka a saman tarihi ta hanyar renon dan Annabi Isma'ila (a.s.) a wani kwari da baya shukuwa a wajen Daki mai alfarma, don ya zama uba ga mafi girman Annabawa a tarihin bil Adama, wannan shi ne Muhammadu (s.a.w.a.); Alkur'ani na bayyana wannan al'amari da cewa:­

"Ya Ubangijinmu, hakika ni na zaunar da wasu daga zuriyyata a wani kwari wanda ba a shuka a cikinsa a wajen DakinKa mai alfarma.." Surar Ibrahim, 14:37.

Haka nan AlKur'ani na magana game da mahaifiyar Annabi Musa (a.s.) da yadda ta karbi fuskantarwar Allah da aka jefa a zuciyarta don ta kare Annabi Musa (a.s.) daga zaluncin Fir'auna, da yadda aka karrama ta ta hanyar dawo mata da shi, inda ta zama mahaifiyar Annabi mai ceto, wanda da taimakon Allah ya wargaza mafi girman dagutu a tarihin dan Adam.Alkur'ani na bayyana ta a matsayin tsaikon asali na faruwar wadannan al'amurra.

Sannan kuma yana magana game da matar Fir'auna Asiya, da Maryam mahaifiyar Annabi Isa (a.s.), yana bijiro da su a matsayin mata madaukaka abin koyi ga zamunan dan Adam, inda ya ce:-­

"Allah Ya buga misali ga wadanda suka ba da gaskiya (na) matar Fir'auna, lokacin da ta ce: `Ya Ubangiji Ka gina min gida a wurinKa a Aljanna, kuma Ka tserar da ni daga Fir'auna da aikinsa, kuma Ka tserar da ni daga mutane azzalumai.(Wani misalin) kuma da Maryamu `yar Imrana wadda ta kiyaye farjinta, sai Muka yi busa a cikinsa daga RuhinMu, ta kuma gaskata ayoyin Ubangijinta da IittattafanSa, ta kuma kasance cikin masu bautar Allah". Surar Tahrim, 66:11-12.

Mu karanta wadannan ayoyi biyu kuma lura da abubuwan da suka kunsa natunane-tunane masu kyau wadanda ke magana akan matsayin mace da girmamawa da mutuntawa, babu wata wayewa da abin duniya na zahiri

da ta ba ta irin shi. Hakika AlKur'ani, aaikace, ya gabatar da managarciyar mace akan maza da mata, ya kuma bukace su da yin koyi da ita cikin fadarsa:

"Allah Ya buga misali ga wadanda suka ba da gaskiya" Surar Tahrim, 66:11. domin kalmar: "Allah Ya buga misali" da "ga wadanda suka ba da gaskiya...", kamar yadda yake bayyane, suna nuna wata wayewa ta imani makadaiciya a duniyar tunani, da wata wayewa da ta kebanta ga managarciyar mace; hakika an sanya ta babbar abar koyi ga maza kamar yadda take abin koyi ga mata cikin akida da matsayin siyasa; sai ya bijiro da wasu misalai biyu na daukakar mutuntakar mace Mumina da matsayinta a tunanin Musulunci, sai ya bijiro da matar Fir'auna sarauniyar Masar, matar gidan mulki da siyasa da babbar daula a waccan duniyar, wadda ta kalubalanci babbar daula; da Maryamu 'yar Imrana wadda ta kalubalanci manyan Bani Isra'ila da makirce-makircensu da mummunan yakinsu a kanta.

Kamar yadda mace ta kasance tana da gudummawarta a rayuwar Ibrahim, Musa, Isa (a.s .); haka nan za mu same ta tana da bayyananniyar gudummawa mai girma a rayuwar Annabi Muhammadu (s.a.w.a.) da da'awarsa. Hakika wannan zangona akida makadaici ya shaida Khadija bint Khuwalid Bakuraishiya (r.a.), wadda ta kasance mace mai babban matsayi a cikin al'ummar garin Makka, mai dukiya da kasuwanci da ra'ayi. Ta kasance farkon wadda Annabi (s.a.w.a.) ya fara magana da ita da kiranshi -bayan Ali (a.s.)­kuma ta yi imani da shi ta gaskata shi, ta bayar da dukiyarta

masu yawa don taimakon kiran shi, ta fuskanci nau'o'in cutarwa da wahalhalu tare da shi na tsawon shekaru goma daga rayuwarta; ta shiga shigifar nan tare da shi, ta jure wahalhalun takunkumin nan da ya ci gaba har na tsawon shekaru uku, sai ta zama cikin mutane mafi girma a tarihin Musulunci; don haka ne ma Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kira shekarar da ta rasu a ciki da shekarar bakin ciki. Musulmina matukar girmama wannan mata, kuma suna koyi da halayensa da irin wadancan matsayai na ta masu girma.

A wata muhawara da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi da matarsa A'isha (r.a.), a wani martani da ya mayar ga wata maganarta, ya ce

"Wallahi Allah bai sauya min ita da wadda ta fi ta ba, ta kasance uwar iyali, mai tarbiyyar gida, ta yi imani da ni lokacin da mutane suka karyata ni, ta taimaka min da dukiyarta lokacin da mutane suka hana ni, kuma an azurta ni da `ya'ya ta hanyarta aka hana ni da wasunta".[ 12] A wani lokaci ya kasance yana magana game da ita da cewa:­ "Lalle ni ina son mai son ta".[13]

Kuma kamar yadda ya yi magana a kan matsayinta a ranshi da yunkurin da'awarshi da tafiyar sakonshi, haka nan ya yi magana a kan `yarsa Fadimatu al-Zahara (a.s.), inda ya ce:­ "Fadimatu wata tsoka ce daga gare ni, abin da ke cutar da ita yana cutar da ni.[14]

Haka an taba tambayarsa cewa: Ya manzon Allah,wa ya fi soyuwa gare ka cikin iyalinka?sai ya ce: "Fadimatu 'yar Muhammadu.[15] Daga madannan nassosi za mu fahimci matsayin mace da mutuncinta a rayuwar Annabi (s.a.w.a.) da da'awarsa, kuma wannan matsayina Annabci yana misalta tunanin Musulunci na mafi girman daga matsayin mace na mutuntaka da girmama ta. Watakila ta hanyar wannan takaitaccen bayani na Alkur'ani da tarihi za mu gane cewa mace a fahimtar AlKur'ani da sakon Allah, ita ce mai renon manyan Annabawa (a.s.), wadda ke dawainyar kare su da lura da su da tsayuwa a gefensu; wannan na bayyana karara a rayuwar Annabi Ibrahim, Musa, Isma'il, Isa da Muhammadu (Amincin Allah ya tabbata gare su baki daya), manyan Annabawa da Manzanni (a.s.), jagororin tunani, kawo gyara da wayarwa a doron kasa.

Hakika AlKur'ani ya zana mana gudummawar mace a rayuwar Annabi (s.a.w.a.) da kiransa, da shigar ta cikin hijira da jihadi, kafada kafada da gudummawar namiji, a lokacin da yake magana game da hijira, mubaya'a, mika wilaya, cancantar lada da babban matsayi, alakar namiji da mace da wasun su, a cikin daruruwan ayoyi na bayanai da maganganunsa a kan wadannan al'amurra, kamar fadarSa Madaukaki

"Muminai maza da muminai mata kuwa, masoya juna ne; suna umurni da aikata alheri kuma suna hani da daga mummunan aiki..."Surar Taubati, 9:71.

"Ya Ubangiji, Ka gafarta minni da mahaifana da kuma wadanda suka shigo gidana suna masu imani, da kuma (sauran) Muminai maza da mata, kuma ka da Ka kari kafirai da komai face halaka". Surar Nuhu, 71:28. "Ranar da za ka ga Muminai maza da muminai mata haskensu na tafiya a tsakaninsu.." Surar Hadidi, 5'l:l ?.

A wadannan ayoyi AIKur'ani ya daga mace zuwa mafi girman matsayi da mutun zai iya kai wa a duniya da lahira, shi yana mu'amala da ita da dan'uwanta namiji daidai wa daida; ita da namiji a fahimtar sakon Musulunci masoya juna ne da soyayya ta akida, suna aikin gyara al'umma, da yaki da barna, laifuka da lalacewa, suna daukar sakon alheri da zaman lafiya da gina fcasa.

A aya ta biyu Annabi Nuhu (a.s .) ya fuskanci Ubangijinsa da addu'a ga Muminai mata kamar yadda ya fuskance Shi da addu'a ga Muminai maza; daga abin da wannan ganawa (da Ubangiji) ta kunsa; asasan karimci, kauna da girmama mace na fitowa, wannan kuwa saboda yin addu'a ga wani dauke da dukkan wadannan ma'anoni.

Matsayin macena kara haske da tartsatsi mai tsarki a shafukan Alkur'ani ta hanyar surantawarsa ga Muminai maza da Muminai mata a wani sarari na haske, ranar haduwa da Ubangiji, sa'ar cancantar sakamakon da ayyana makomar mutum ta hanyar ayyukansa da tafiyarsa a rayuwa.

Haka muke fahimtar cewa AlKur'ani ya ba managarciyar mace kauna da soyayya, ya kuma yi mata addu'a da gafara, afuwa da rahama; ya kuma kewaye ta da sararina haske; misalinta ita ce Asiya matar Fir'auna, Maryamu mahaifiyar AlMasihu, Khadija matar Manzon Allah (s.a.w.a.) da Fadimatu 'yar Muhammadu (s.a.w.a.). Za mu riski girman mace a sakon Musulunci da rayuwar Manzon Allah (s.a.w.a.) ta hanyar da ta daukaka mutuntakarta, ya yabe ta da girmamawa; idan muka san cewa farkonwanda ya yi shahada a Musulunci ita ce Sumayya, mahaifiyar babban Sahabin nan Ammar bin Yasir, jagoran shirka Abu Sufyan ne ya kashe ta. Hakika tabayar da rayuwarta ga asasan sakon Musulunci, a lokacin da fito-na-fito ya fara tsakanin 'yan ta'adda da dagutai (a wani bangare), da Muahammadu (s.a.w.a.) da wadanda aka raunana da bayi, wadanda suka sami sakon Musulunci mai kwato hakkin dan Adam, mai 'yanto mutane daga jahilci da danniyar mutum ga dan'uwansa mutum (a daya bangaren).

Hakanan da yawa daga matan da aka raunana sun yi gaggawa wajen gaskata Annabi (s.a.w.a.) a farkon kiransa, sun jure cutarwa, azabtarwa da wahalhalu.sun yi hijira zuwa Habasha da zuwa Madina, sun taimaki Allah da ManzonSa (s.a.w.a.) da duk karfin da suke da shi. Mutuntakar managarciyar mace za ta kara kyautata lokacin da muka shiga sararin nan da ke cike da Shahidai ta hanyar surantawar AIkur'ani da labarinsa da ya bayar da cewa

"Kuma kasa ta haskaka da hasken Ubangijinta, aka kuma ajiye takardu (na ayyuka), kuma aka zo da Annabawa da Shahidai, aka yi hukunci a tsakaninsu da gaskiya, alhali su ba za a zalunce su ba". Surar Zumari, 39:69.

Lalle mace Musulma ba ta gano matsayinta na hakika a Musulunci ba tukuna, haka nan namiji Musulmi bai san matsayin mace a Musulunci a bisa hakikanin shi ba tukuna; don haka ma'aunin mu'amala da alaka suka gurbace, irin wanda ba ya tabbata sai an dawo zuwa ka'idojin Alkur'ani don kowane daga cikinsu ya san hakkinsa da matsayinsa da nauyin da ya hau kansa a kan dayan, da alakarsa da shi. Macen da ke haniniya a bayan hohonnan na wayewar abin duniya na zahiri wanda babu abin da ke bayansa face mafada da wulakanci ga mace.da ta san abin da ke cikin Musulunci na kima da hakki, da ba ta kira komai ba in ba Musulunci ba.kuma da ta san cewa abin da zai ceto karamarta da hakkinta su ne ka'idojin Alkur'ani.

Tanadin Mace Don Cika Aikinta

Shiri da tarbiyyana da tasiri mai karfi wajen gini da hada mutum da aikinsa a cikin al'umma, da fuskantar da iyawarsa da kokarinsa zuwa mafuskanta ta gini mai kyau. A halin yin watsi da mutum da hana shi tarbiyya da fuskantarwa, da tanaji mai tsari kuwa, zai sa ya tashi sakakke, wanda yanayi da fare-fare ke galaba a kan shi, irin wad'anda a galibi suke musabbabin lalacewar mutum da tafiyar kokari da kwarewarsa da yi wa ci gaban zamantakewa tangarda; daga nan sai mutum ya zama mai rauni sukurkutacce, baya iya mu'amala da al'umma da fare-fare da matsaloli da damammaki da mu'amala mai nasara.

Surar nan ta misali a Musulunci wadda ya wajaba ta yi nazarin yanayin mace ta hanyar ta, ita ce surar mace a cikin AIKur'ani da sunna, wadda kuma ke tsaye a kan asasai masu yawa kamar haka

1-Kadaitar Nau'in dan Adam: Wadda ta ginu a kan asasin fadar Allah Madaukaki "Ya ku mutane, ku ji tsoron Ubangijinku, wanda Ya halicce ku daga rai guda daya (Adamu), Ya kuma halittar masa mata (Hauwa'u) daga gare shi, Ya kuma baza maza da mata masu yawa daga gare su.Ku ji tsoron Allah Wanda kuke tambayar (taimakon junanku) da Shi, kuma (ku ji tsoron hakkokin) zumunta. Hakika Allah Ya kasance Mai kiwo ne a gare ku". Surar Nisa'i, 4:1.

Muna iya fahimtar cewa girman wannan aya ba kawai daga abin da ta kunsa na manyan ma'anoni ba ne, a'a har ma daga bude Surar Nisa'i, wadda ke magana game da sha'anonin mata, da wannan aya; wadda kuma take cikin manyan surori, da d'aukar wannan aya a mastayin asasi da mabubbugar tunani da shar'ancin Musulunci wadanda suka tsara alaka tsakanin namiji da mace, suka kuma iyakance matsayinta da gudummawarta a cikin al'umma.

2-Asasi na biyu da ya wajaba a yi nazarin shi a bisa asasin alaka tsakanin namiji da mace shi ne alakar so, kauna, tausayi, tabbaci da natsuwar zuci, wad'anda suka misaltu a fadar Allah Madaukaki

"Akwai daga ayoyinSaYa halittar muku mata daga kanku, don ku natsu zuwa gare ta, kuma Ya sanya kauna da tausayi a tsakaninku, lalle cikin wannan akwai ayoyi ga mutanen da ke tunani." Surar Rumu 30:21. 3- Daidaitawa cikin hakkoki da wajibai

"..kuma suna da hakkoki a kan mazajensu kamar (yadda mazajensu ke da hakkoki) a kansu da kyautatawa.." Surar Bakara, 2:228.

Wannanyana nufin cewa kowane daya daga namiji da mace akwai hakki na wajibi da ya hau kanshi kuma ya zama wajibi ya aiwatar da abin da ya hau kanshi game da dayan da kyautatawa da zamantakewa mai kyau.Da wannan Musulunci ya auna kuma ya tsara a sasan alaka da wannan ka'ida ta shari'a da halayya makadaiciya, sai ya tabbatar da mafi daukakar ka'ida ga hakkin mace.

4-Amma alakar zamantakewa tsakanin namiji da mace, ita ce alakar kauna kamar yadda AIKur'ni mai girma ya fada: "Muminai maza da muminai mata kuwa, masoya juna ne.."

Alkur'ani na bayar da wannan kyakkyawar sura ta alakar namiji da mace a al'umma da cewa ita ce alakar kauna, wadda ta hada mafi girman so da girmamawa, kalmar (اولياء ) da ayar ta yi amfani da ita da larabci, tana nufin: mai taimako, masoyi da aboki, da wannan za mu fahimci kimar managarciyar mace, da ita da namiji daidai ne a wannan bayani na Alkur'ani.

Wani abuna zamantakewa da za a iya ganin shi a duniyarmu ta yau wadda ta kaskantar da kai ga mulkin mallaka, danniya da fin karfin dagutai, shi ne bayyanar danniya, fin karfi da mamaya, tasirin wadannan ya bayyana a cikin mu'amalar zamantakewa da tarbiyya a makarantu da gidaje da alakokin ayyuka da tsare-tsaren zamantakewa ta surori dabam-dabam.

Fakuwar 'yanci, kaskanta mutuntakar wasu da yi musu danniya da rashin mutunta bukatunsu, duk wasu abubuwa ne da ake raye tare da su a cikin duniyarmu ta yanzu; ba a yunkurin hamayya da rashin amincewa sai aiyakokin da ba su dace da wadancan halayya ba.

Abin da yasami mace a karkashin fitinun wadancan halaye ya fi tsananin kan abin da ya sami namiji, domin hakika kasashenmu sun gaji ci baya na al'adu da tunane-tunane na kauyanci wadanda ta hanyarsu aka yi mu'amala da mace da wulakanci ga mutuntakarta, iyawarta da `yan Adamtakarta; kai! a wasu yanayoyi masu yawa namiji ya yi mu'amala da ita a matsayin wata halitta da ba ta kai matsayin mutum namiji ba, sai wasu tunane-tunane, wadanda suka kawar da mace daga rayuwar zamantakewa na ci gaba, suka taso a tsakanin wasu kauyawa wadanda ke fuskantar fakuwar wayewa da rashin fahimtar Musulunci daga cikin Musulmi, wannan kuwa wani sakamako ne na dabi'a ga yanayin tunani, siyasa da zamantakewar da suka yadu. Saidai abin mamaki shi ne yadda wasu marubuta da masu kira zuwa ga tunane-tunanen abin duniya na zahiri, ke dangana wa Musulunci, wadannan tunane-tunane da abubuwan da mace ke dandanawa na tauye hakki da ture ta daga fagen zamantakewa.

A karkashin yaduwar yanayin jahilci da ci baya ne Musulumi suka kaskantar da kai ga yakin nan na tunanin abin duniya na zahiri da ya fito daga tafarkokin nan biyu na jahiliyyar gabashi da yammaci; ya zama daga manyan abubuwan da wannan yaki ya sa a gaba, akwai yakar tunane-tunanen Musulunci da mayar da hankali a kan yanayin mace a duniyar Musulmi; sai cibiyoyin al'adu da kafafan watsa labarai da ba na Musulumi ba da jam'iyyun da ba su yi imani da addini ba da masu kira zuwa ga abubuwan zahiri na duniya da kawo sauyi, duk suka himmatu wajen janye mace daga wannan yanayi da take raye a ciki a kasashen da suka ci baya, suka jefa ta a tsaikon sakewa da zubar da kimar mace da yin kasuwanci da al'amarinta na siyasa da wayewa; bayan ta bayyana gare su cewa lalata mace ta hanyar jima'i karkashin ikirarin 'yancin mace da hakkokin mace shi ne kawai hanyar lalata bangaren matasa maza da mata; wannan kuwa saboda mace ita ce tushen rudarwa da tayar da sha'awar jima'i. Hakan yada tunanin sakin akalar jima'i da suka kirkirarwa suna da hakkokin jima'i,yana daga mafi hadarin hanyoyin rushe iyali, watsa 'ya'ya da wargaza alakokin mutuntaka masu karfi da ke tsakanin namiji da mace. Haka shirin tarbiyya da tanajin mace ke fuskantar fuskoki uku kamar haka

1-Fuskar da yanayin kauyanci da al'adun da suka ci baya suka haifar da su:itace fuskar da ta ginu a kan asasan wulakanta mutuntakar mace, murkushe iyawarta da boye gudummawarta na zamantakewa da mutunka da ke kafada-da-kafada da na namiji. Wannan itace fuskar da aka gada daga al'adun da suka samo asali daga jahiltar Musulunci, yanayoyin danniya, fin karfin namiji da ci bayana tunani.

2- Fuskar abin duniyana zahiri: Wadda wayewar duniyanci na yammaci ke kira zuwa gare ta. Wannan itace fuskar da ke kira zuwa ga sakin akalar jima’i, abin da ke haifar da wargajewar iyali da mamayar danniya da zalunci akan mace amma ta wata hanya a karkashin yekuwar hakkokin mace da hakkokin jima'i da wasun wadannan, wanda ya sanya mace ta zama kan-mai-uwa-da-wabin fyade da cutukan zinace-zinace.

3-Fuskar Musulunci: Ita ce fuskar da ta yi imani da kadaicin nau'in dan Adam, ya kuma tsara alaka tsakanin namiji da mace a kan asasan girmamawa da taimakon juna wajen gina al'umma; da tsara alakar jima'i ba a kan asasin halattar jikin mace da jin dadi da shi (haka nan) ba, ko rushe asasan alakokin iyali, kamar yadda yake faruwa a halin yanzu a kasashen Turai, Amirka, Rasha, Sin, Japan da sauransu na daga kasashen da suka tasirantu da wayewar abin duniya na zahiri ba.maimakon haka, a kan asasin girmama mutuntakar mace da ba ta hakkokinta a matsayinta na mutum da ke da abubuwan da suka kebance ta da hakkoki da abubuwan da hakikaninta suka ginu a kai.

Gina Al'umma Ta Hanyar Alakokin Iyali

Ta bayyana gare mu cewa al'umma na tsayuwa ne a kan asasai uku kamar haka

1-Tasiri tsakanin halayyar nan ta mace da namiji da siffofin da kowannensu ke da shi na jiki da rai, da cewa jin dadin al'umma da amincinsa na rai da bunkasar zamantakewa da bukatun rayuwa da fadadar hanyoyin shiga da daidaiton halayyar su, duk suna da alaka mai nisa ta hanyar daidaitaccen tasirin da ake musaya tsakanin jinsosin biyu, wato jinsin namiji da jinsin mace.

2- Alakar tunani da wayewa da suka hadu a kai.

3-musayar amfanoni tsakanin daidaikun al'umma mazansu da matansu.

Akan asasai na daya da na uku ne ayyukan zamantakewa ga kowane daya daga daidaikun al'umma mazansu da matansu ya samo asali, kowanne da yadda ya dace da karfinsa na jiki da hankali da kuma inda ransa ya fi karkata.

Daganan ne mace ke motsawa don tarayya cikin aikin gina gida da al'umma, kuma mafi fadin fagagen wannan tarayya shi ne fagen iyali.

Hakika sakamakon darussan kan halayyar dan Adam sun isa zuwa ga abin da Alkur'ani mai girma ya bayyana, na cewa iyali shi ne ginshikin ginin al'umma, kuma tushe da asasi daga muhimman asasan da ake gina rayuwar al'umma a kan su; don haka AIkur'ani ya bayyana haka, ya kuma sanya ka'idojin alakar auratayya, ya bayyana hakkokin da wajiban da ke kan kowane daya daga namij da mace, don su iya aiki da gina rayuwar zamantakewa mai lafiya.

"Akwai daga ayoyinSaYa halittar muku mata daga kanku, don ku natsu zuwa gare ta, kuma Ya sanya kauna da tausayi a tsakaninku, lallai cikin wannan akwai ayoyi ga mutanen da ke tunani." Surar Rumu, 30:21. "Shi ne Wanda Ya halicce ku daga rai daya (wato Annabi Adamu), Ya kuma halicci matarsa daga jikinsa don ya sami natsuwa da ita.." Surar A'arafi, 7:189.

"Mazasama suke da mata saboda abin da Allah Ya fifita sashensu (da shi) a kan sashi, da kuma abin da suke ciyarwa daga dukiyoyinsu. Sannan matana gari masu biyayya ne (kuma) masu kiyaye asirin abin da ke boye wanda Allah Ya kiyaye..." Surar Nisa'i, 4:34.

"..kuma suna da hakkoki a kan mazajensu kamar (yadda mazajensu ke da hakkoki) a kansu da kyautatawa.." Surar Bakara, 2:228. "..Kuma ku zauna da su da kyautatawa.." Surar Nisa'i, 4:19.

"Kuma ma'abucin yalwa ya ciyar daga yalwarsa.." Surar Dalaki, 65:7. "Kuma ku taimaki juna da aikin alheri da tsoron Allah, kuma kar ku taimaki juna a kan yin sabo da ta'adda.." Surar Ma'ida, 5:2.

Hakanan kamar yadda AIkur'ani mai girma ya yimagana game da asasai da alakokin `yan Adamtaka da doka a iyali, haka nan ma hadisan Annabi suka yi magana a kan haka, za mu ambaci abin da aka ruwaito daga Manzon Allah (s.a.w.a.):­

"Dukkan ku masu kiwo ne kuma wadanda za a tambaya a kan kiwonsu; sarki da ke saman mutane mai kiwo ne kuma abin tambaya a kan abin da yake kiwo, namiji mai kiwo ne a kan iyalinsa kuma shi abin tambaya ne a kansu; mace mai kiwo ce a kan gidan mijinta da `ya'yanshi kuma ita abar tambaya ce a kansu, bawa mai kiwo ne a kan dukiyar ubangidansa kuma shi abin tambaya ne a kan shi.Ku saurara, dukkan ku masu kiwo ne, kuma kowannenku abin tambaya ne a kan abin da yake kiwo." [16]

Da abin da aka ruwaito daga Imam Sadik (a.s.) cewa "Daga cikin dabi'un Annabawa akwai son mata".

Da abin da aka ruwaito daga gare shi (a.s.) cewa "Bana tsammanin mutum na kara alheri a kan imani har sai ya kara so ga mata.[17]

Yana da kyau anan mu yi ishara da cewa ginin da mace ke yi a cikin al'umma a wasu lokuta ya kan zama aiki ne kai tsaye, a wasu kuma ya kan zama ta hanyar alakarta ta rai da halayya da miji da `ya'ya. Matar da ke samarda yanayin hutawa da kyakkyawan zamantakewa da miji, take kuma tabbatar da kauna, soyayya da kwanciyar hankali, kamar yadda ya kamataa alakokin da ke tsakaninsu, to irin wadannan yanayoyi na rai suna tasiri ga miji da alakarsa ta zamantakewa da wasu, da ikonsa na neman abinci da bayarwa.wannankuwa saboda yanayin rai ga mutum yana tasiri a daukacin harkokinsa da alakokinsa da wasu.

Amma lokacin da rayuwar aure ta cika da matsaloli da damuwa da tashe-tashen hankula, to wannanyana tasiri mara kyau ga miji, aikinsa, neman abinci da alakokinsa da wasu. Kamar yadda yanayoyin rai a cikin iyali ke tasiri ga miji, haka yake tasiri ga `ya'ya; domin yaron da ya tashi cikin yanayin kiyayya, rikice-rikce, matsaloli da mummunan mu'amala, da wuya ya zama daidaitaccen mutum cikin halayyarsa da alakokinsa da wasu, da fuskantar da iyawarsa ta tunani da jiki; domin so tari yaro, saboda yanayin mummunar tarbiyya, yakan sauya ya zama karkataccen mutum mai adawa, ko malalaci da ba ya amfanin komai, ko birkitacce mai kawo matsaloli da aikata laifuka. Alhali kyakkyawar tarbiyyana taimakawa wajen samar da mikakken mutum, ta yadda irin wannan tarbiyya ke tasiri a rayuwar gobe ta yaro ta ilimi, zamantakewa da tattalin arziki.

Don haka gudummawar mace ke da tasiri wajen ginin zamantakewa ta hanyar tarbiyya da tanajin ingantattun mutane ga al'umma; hakanan ta hanyar samar da yanayi mai kayu ga miji.

A cikin wadannan nassosi Akur'ani mai girma da hadisai masu tsarki sun iyakance asasai da ka'idojina dokokin, halayya, tarbiyya, tsari da gudanar da iyali; a kan wannan hanya kuma mace na taimakawa wajen ginin al'umma. Ginin al'umma kuwa ya ginu akan asasai kamar.Soyayya da kauna da jin kai da girmamawa tsakanin ma'aurata.

b-Mace na da hakkoki kamar yadda wajibobi suka hau kanta.

c-Maza ke rike da nauyin shugabanci da daukar dawainiyar gudanar da al'amurran gida.

d-Taimakekeniya cikin sha'anonin rayuwar aure.

e-Yin tsaka-tsaki wajen ciyarwa da kiyaye tattalin iyali.f-Kula da nauyi, wato kulawar miji da nauyin da ya hau kansa game da matarsa da sauran wadanda ke cikin iyali; da kulawar mata da nauyin da ya hau kanta game da mijinta, `ya'yanta da iyalin ta.Domin a kanta nauyin kulawa da gida da `ya'ya, tarayya wajen ba su ingantacciyar tarbiyya da yin mu'amala da su da kauna da tausayi da kulawa.

Mace Da Tattalin Arzikin Iyali

Daga cikin manyan matsalolin da suka addabi al'umma,akwai matsalar kudi da hanyoyin shiga ga mutane; da aunawa tsakanin abin da ke shigowa da wanda ake kashewa; hakan na faruwa a tattalin iyali da zarafinshi na kudi wajen ciyarwa da hada-hadar gida. Barnar abinci, abin sha, kayan kwalliya, sutura, mazauni da sauran hidimomi na daga mafi hadarin matsalolin dan Adam; domin akwai almabazzaranci da kashe kudi ba tare da basira ba da ke gurgunta tattalin arzikin iyali, al'umma da gwamnati, wadanda so tari ba sa dacewa da hanyoyin shigar iyali da abin da yake samu.

Saboda tsara ma'aunin tattalin arzikin al'umma ne Musulunci ya yi kira zuwa ga daidaito wajen ciyarwa, ya kuma haramta barna kamar yadda ya yi hani ga, matsolanci, kwauro da rowa.

Daya daga cikin manyan matsaloli wajen ciyarwaita ce matsalar biyan bukatun iyali da kasafin sa, wadanda mace ke da babban alhakin da ya hau kanta wajen tsara shi da iyakance dabi'arsa.

Hakika shari'ar Musulunci ta sanya gamammun asasai don tsara ciyarwa daga sakewarsa; kamar yadda ta tsara iyakoki na asasi wajen biyan bukatun iyali da kasafinsa a iyakance; daga irin wannan za mu ambaci abin da Allah Ya siffanta "Bayin Mai rahama° da shi a matsayin wani madaukakin abin koyo wajen tsari da lizimci, wanda kuma ya bayyana mikakken tafarkin wajen ciyarwa irin wanda aka yi kira ga mutane su yi riko da shi, Allah Madaukaki Yana cewa

"..Kuma wad'anda idan suka ciyar basa almubazzaranci kuma ba sa yin kwauro, sai dai ya kasance tsaka-tsaki ne". Surar Furkani, 2s:67.

A wani wuri kuma AIKur'anina hani da almubazzaranci kuma yana tsanantawa a kan haka da fad'arsa:­

"...kuma ku ci ku sha, amma kuma kada ku yi almubazzaranci, hakika shi Allah baYa son masu almubazzaranci". Surar A'arafi, 7:31. Da fadarsa

"Kuma ku baiwa makusanci hakkinsa, da miskini da matafiyi; kada ka batar (da dukiya) ta hanyar almubazzaranci. Hakika almubazarai dangin shedanu ne; shedan kuwa mai yawan kafircewa Ubangijinsa ne". Surar Isra'i, 17:26-27."Kuma kar ka kunkunce hannuwanka a wuyan ka (wato yin kwauro), kuma kar ka shimfida gaba daya (wato yin almubazzaranci), sai ka wayi gari abin zargi (saboda kwauro), mai nadama (saboda almubazzaranci)". Surar Isra'i, 17:29. "Kuma ku zaunar da su (mata) ainda kuka zauna daidai halinku, kuma kar ku cutar da su (da kwauro) don ku kuntata musu; idan kuwa sun kasance masu ciki ne, sai ku ciyar da su har sai sun sauke abin da ke cikinsu; sannan idan sun shayar muku (da `ya'yanku), sai ku ba su ladaddakinsu, kuma ku daidaita tsakaninku da kyautatawa; idan kuma abin ya gagara daidaitawa, sai wata (matar) ta shayar masa (da jaririn). Ma'abucin yalwa ya ciyar daga yalwarsa,wanda kuwa aka kuntace masa arzikinsa sai ya ciyar daga abin da Allah Ya ba shi, Allah ba Ya dora wa rai face abin da Ya ba ta, da sannu Allah Zai sanya sauki bayan matsi". Surar Dalaki, 65:6-7.

Haka gamammun asasan kasafin iyali da kashewa da ciyarwa ke iyakantuwa cikin tsaikoki biyuna doka, tarbiyya da fuskantarwar halayya; su ne tsaikon zamantakewa da tsaikon iyali.

Kuma gudummawar mace cikin gudanar da tattalin arzikin gidana bayyana wajen kiyayewarta ga kudaden iyali da lurar ta da daidaito wajen kashewa da kayayyakin kyale-kyale da (kiyayewa daga) nuna takama da son a sani wajen kashe kud'i.

Uwana iya bayar da wani kashi daga mashigar iyali ta ragewa namiji nauyin basussuka ta hanyar rage kashe kud'i da yin tasiri a kan yara, kai!a kan miji ma ta hanyar tsara siyasar ciyarwa madaidaici ga iyali, irin wanda ke daidai da bukatu da gwargwadon abin da ake kashewa.

Yawan kashe kud'i da almubazzaranci a iyali na barin tasirinsa ba kawai a cikin iyali ba, har ma a kan yanayin tattalin arzikin mutane da gwamnati, domin farashin kayayyakin masarufi za su hauhawa a kasuwa saboda hauhawar ciyarwa da kashe kud'i, wad'anda ke haifar da fad'uwar darajar kud'i da tashin kayayyki; da haka sai yawan talauci ya karu, iyalai su rika nutsuwa cikin basussuka da matsalolin zamantakewa; kamar yadda takardun kud'i za su yawaita, sai matsalolin siyasa, tsaro da d'abi'u su kunno kai a sakamakon tabarbarewar yanayin tattalin arziki a cikin al'umma.

Wayar da kan mace da kebance wasu darussa na masamman cikin tsare-tsaren karantarwa game da tattalin arzikin gida a Musulunci, da wayar da kan mace a kan daidaita wa wajen ciyarwa da tsara kasafin iyali, duk suna taimakawa wajen gina yanayin tattalin arziki da ceto shi daga matsaloli, masamman ma matsalar tsadar kayayyaki da rashi ga talakawa.

Da wannan macena bayar da gudummawa wajen ginin al'umma ta hanyar fuskantarwa da tsarin tattalin arzikin iyali, da daidaitawa wajen ciyarwa ta hanyar bin tsare-tsaren AIKur'ani da kiransa mai hikima. Kuma don mace ta sauke nauyin da ya hau kanta a matsayintana mai lura da gidan mijinta, kuma wadda za a tambaya a kan shi kamar yadda ya zo cikin bayanin Annabi mai girma (s.a.w.a.).

Yin Aiki a Shari'ar Musulunci

Hakika shari'ar Musulunci ta yi kira zuwa ga yin aiki, ta kuma karakwadaitarwa akan shi da abin da ba ya bukatar kari a cikin nassosi da karantarwa da matsayi na aikace. Daga cikin su akwai fadar Allah Madaukaki

" ( Allah) Shi ne Wanda Ya sanya kasa horarriya, saboda haka ku yi tafiya a cikin sassanta, kuma ku ci daga arzikinSa, kuma makoma zuwa gare Shi ne (kawai)". Surar Mulki, 67:15. Haka nan akwai fadarSa Madaukaki

"Sannan idan aka idar da Salla, sai ku bazu cikin kasa ku nemi falalar Allah, kuma ku ambaci Allah da yawa tsammaninku ku rabauta". Surar .Tuma'ati, 62:10

Haka nan akwai fadarSa "Kuma ka nemi gidan lahira ta hanyar abin da Allah Ya ba ka, kuma kar ka manta da rabonka na duniya..". Surar Kasasi, 28:77.

Kamar yadda shari'ar Musulunci ta yi kira zuwa ga yin aiki da neman kudi, haka ta yi bayani a kan bambamce-bambamcen karfi da iyawar dan Adam, da wajibcin samun kamala ta hanyar musayar amfanoni tsakanin daidaikun nau'in dan Adam; Allah Madaukaki Ya ce

"...kuma muka daukaka darajojin sashinsu a kan wani sashi don wani sashin ya riki wani mai yi mishi hldima." Surar Zukhrufi, 43:32.

Kamar yadda AIkur'ani ya kwadaitar a kan yin aiki,neman abinci da musayar amfanoni; Manzon Allah (s.a.w.a.) na daukar yin aiki da neman arziki a matsayin jihadi da ibada; hakika haka ya zo cikin abin da aka ruwaito daga gare shi (s.a.w.a.) cewa:­ "Mai wahalar neman kudi don iyali kamar mai jihadi ne a tafarkin Allah".[18]

"Ibada kashi bakwaice , mafificiyarsu neman halaliya".[19]

Hakika malaman furu'a (fikihu) sun yi kokari mai yawa wajen karance-karance da bin diddigin game da yin aiki da neman abinci, inda suka fitar da hukunce-hukuncen shari'a da matsayinta game da aikin sana'a da hidima, kuma suka kasa su kashi biyar ta fuskar shari'a kamar haka:­

1-Shari'ar Musuluncina daukar yin aiki don samun biyan bukatun rayuwa ga mutum ko ga wanda daukar dawainiyarsa ta zama dole a kan shi, a matsayin wajibi; kai!ta ma wajabta wa wanda ake bi bashi kuma yake da ikon yin aiki da ya yi aiki don biyan bashin da ke kansa.

2-Hakanan Shari'ar Musulunci na daukar yin aiki don yalwatawa cikin ciyarwa, samar da jin dadin rayuwa da ayyukan alheri; a matsayin mustahabbi da take kwadaitar da mutum a kan yin haka.

3-Shari'ar Musulunci ta haramta yin ayyukan da aka haramta, kamar sana'anta giya, miyagun kwayoyi, raye-raye, zina da wasun wadannan; kamar yadda ta haramta duk wani aiki da ke ja-gora zuwa aikata haram,ko da kuwa shi a kashin kanshi halal ne.

4-Shari'arna daukar wasu ayyuka a matsayin makaruhai a kashin kansu ko saboda wani abu dabam.

5-Koma bayan abubuwan da muka ambata a sama, asalin da shari'ar Musulunci ke tabbatarwa game da aiki shi ne halalci; da haka yin aiki don tara dukiya ko kara yin kudi wani al'amari ne na halal matukar yana gudana a kan hanyar da shari'a ta halalta.

Yayin nazari da bin diddigin ma'anonin ayoyi da nassosi, a cikinsu ba za mu samiabin da ya hana mace yin aiki ba,ko ya kebe halaccin haka ga namiji, duk kuwa da cewa kwadaitar da namiji da magana da shi sun zo cikin wasu nassosi.

Ayyukan Matar Aure: Shari'ar Musulunci ta iyakance wasu hukunce-hukunce da suka kebanci aikin matar aure da abubuwa kamar haka

1-Yana daga hakkin mace ta shardantawa miji cewa ba zai hana ta yin aiki ba a lokacin daura aure.

2-Miji ya amince akan aikin matarsa ta hanyar fahimtar juna tsakaninsu; wannan idan ta so yin aiki ba tare da wani sharadi da ya gabata ba ke nan. Idan kuwa miji ya ki amincewa da matarsa ta yi aikia irin wannan hali, wannan ba ya nufin cewa shari'ar Musulunci ta hana mace aiki.maimakon haka wannan na komawa ne ga alakar miji da matarsa.

3-Idan mace ta yi aure alhali tariga ta yi yarjejeniyar aiki na wani ayyanannen lokaci da wasu.to yarjejeniyar aikin ba ta baci ba, ko da kuwa ya sabawa hakkin miji.

4-Idan matar aure ta kulla yarjejeniyar aiki ba tare da izinin mijinta ba.to ingancin wannan yarjejeniya ya tsayu ne a kan yardar mijin idan aikin na sabawa hakkokin miji.idan kuwa ba ya sabawa hakkokinsa, yana aiwatuwa.

5-Hukuncin macen da ta kulla duk wata yarjejeniyar aiki da mace ta kullayana gudana.

Ta hanyar nazarin hukunce-hukuncen shari'a ba za mu taba samun wani nassi da yake haramta yin aiki ga mace a matsayin ka'ida ta farko ba; maimakon haka masu haramta aikin mace suna bayar da dalili ne da kasancewarsa a wajen gida; wasu kuwa ba su amince da aikin mace cikin ma'aikatun da ake cakuda maza da mata ba, saboda hakan na haifar da fasadi da fadawa cikin abubuwan da aka haramta; ma'ana haramcin ya zo ne saboda abin da cudanyar maza da mata ke haifarwa a lokacin ayyuka na fadawa cikin abubuwan da aka haramta.

Don haka wannan haramci ne ta la'akari da ka'ida ta biyu ba ka'ida ta farko ba; da wata magana, wannan yana cikin babin haramcin mukaddamar haram da ake kira da "kawar da sabuaba" ko haramta halal din da ke haifar da fadawa cikin abin da aka haramta.

A nan ya kamata mu yi ishara da cewa aikin da ke haifar da aukawa cikin haram, haram ne ga dukkan jinsosin biyu, namiji da mace; don haka matsayin na tilasta hana cudanya, da yin amfani da irin jinsin da aikin ke bukata ba tare da la'akari da kasancewarsa namiji ko mace ba.

Ya bayyana gare mu ta hanyar ayar nan mai girma mai cewa: "...kuma muka daukaka darajojin sashinsu a kan wani sashi don wani sashin ya riki wani mai yi mishi hidima.." cewa bamabancin iyawa, kwarewa da karfin aiki na sabawa daga wani mutum zuwa wani, ba tare da la'akari da kasancewarsa namiji ko mace ba; da cewa musayar amfanoni da biyan bukatun rayuwa da hidima na cika ne tsakanin daidaikun al'umma baiki daya, kuma kowane daya, ba tare da la'akari da jinsinsa (namiji ko mace) ba, yana yin kokarinsa da abin da zai iya wajen biyan bukatun al'umma, don shi ma ya sami tashi biyan bukatar ta hanyar aikin musayar abin duniya da hidima a cikin al'umma. Manomi na gabatar da kayan noma, injiniya da masanin fanni suna sana'anta na'ura, likita na bayar da lafiya, malami na yin aikinsa na karantar da manyan gobe, dan kasuwa na samar da kayayyakin masarufi a kasuwa, soja na kare kasa, mai gadi na maganin barayi da dai sauransu.

Darasi da nazarin hukunce-hukuncen Musulunci dukkansu, za su tabbatar mana da cewa Musulunci bai haramta wani nau'ina aiki ko ilimi ga mace bayan ya halalta shi ga namiji ba; mace na iya yin kowane irin aiki, kamar noma, sana'a, likitanci, injiniyanci, gudanarwa, ayyukan siyasa, tela, tukin jirgin sama da sauransu.

A musulunci babu wani aiki na samar da wani abu ko hidima da aka halalta ga namiji alhali kuma an haramta shi ga mace; kowa a shari'ar Musulunci daya ne a kan haka; bambancin kawai da ke tsakanin namiji da mace a wasu wajibai ne da aka kallafa wa namiji ko mace ko wasu maslahohi da suka ginu a kan asasan ilimi da aka yi la'akari da yanayin halitta ta rai da ga66ai ga kowannen su, da wajibcin tsara rayuwar zamantakewa da gudanar da ita.

Abin da yake asali a shari'ar Musulunci shi ne halaccin aiki, kai!wajibcin shi ma a wasu halaye; in banda abin da shari'a ta haramta ko abin da ke haifar da fadawa cikin abin da aka haramta.

Idan kuwa har akwai wata hayaniyar haramta aiki ga mace daga wajen wasu, to wannanna bukatar dalili, babu kuwa dalili na shari'a a kan wannan haramci.

Lura na ilimi ga bin diddigin malamai game da wajibai, da kasa su zuwa wajibi na Aini (shi ne irin wajibin da ya hau kan kowane mutum, wani ba ya daukewa wani; kamar sallolin wajibi) da na Kifa'i (shi ne wajibin da ya hau kan mutane a matsayin su na jama'a, idan wasu suka yi shi ya fadi a kan sauran; kamar sallar gawa), za ta bayyana gare mu, ta hanyar nazarin wajibin Kifa'i, cewa tsarin Musulunci ya wajabta wa daidaiku, ba tare da iyakance jinsin mace ko namiji ba, ya wajabta musu samar da bukatun al'umma da duk kashe-kashensu; kamar likitanci, injiniyanci, karantarwa, noma, kasuwanci, sufuri, tsaro da wasunsu na daga ayyukan da al'umma ke bukata; kai!wajibin Kifa'i ma na sauyawa ya zama wajibi Aini a kan mutum ko wasu mutane da ikon aiwatar da wannan wajibi ya kebanta da su; ba kuwa tare da la'akari da jinsin namiji ko mace ba.

Daga wannan za mu fahimci cewa kasa ayyukan hidima cikin al'umma da aiwatar da su, ya ginu ne a bisa asasai biyu: na mutum shi kadai da na tarayya; kuma a cikin dukkan halayen biyu, Musulunci bai bambanta tsakanin namiji da mace ba, maimakon haka, a wasu fagagen wajibcin Kifa'i, kamar wajibcin aikin likita da ya kebanci mata da karantar da su, yana fuskantar da wajibcin ne zuwa ga jinsin mace.