Hakkoki a Musulunci

Hakkoki a Musulunci0%

Hakkoki a Musulunci Mawallafi:
Gungu: Kala-kala
Shafuka: 4

Hakkoki a Musulunci

Mawallafi: Hafiz Muhammad Sa'id
Gungu:

Shafuka: 4
Budawa: 1672
Gurzawa: 542

Bayanai:

Bincike Cikin Littafi
  • Farawa
  • Na Baya
  • 4 /
  • Na Gaba
  • Karewa
  •  
  • Budawa: 1672 / Gurzawa: 542
Girma Girma Girma
Hakkoki a Musulunci

Hakkoki a Musulunci

Mawallafi:
Hausa
HAKKOKI A MUSULUNCI HAKKOKI A MUSULUNCIHafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
Kur'ani Mai Daraja: Kuma sama ya daukaka ta, kuma ya sanya sikeli. Kuma ku daidaita awo da adalci, kada ku rage sikelin. Kuma kasa ya sanya ta domin talikai ne.[1].

Gabatarwar Mawallafi Muna godiya ga Allah da ya ba ni damar rubuta wannnan Littafi game da hakkokin zamantakewar al'umma. Wannan littafin an wallafa shi ne da nufin isar da sakon gyara da sanin ya kamata tsakanin juna a zamantakewa a matsayin al'umma daya, da kuma sanin hakkin Allah (S.W.T) da na mutum a kan dan'uwansa mutum da kokarin ganin kiyaye hakan.
Sanin hakkokin Allah da halittarsa da suke kanmu wani abu ne wanda yake mafi muhimmanci a rayuwarmu, domin da shi ne zamu iya tasra rayuwarmu ta duniya da lahira. Tun asali ma ba komai ne kasancewar al'umma mai kamala da sanin ya kamata ba sai kasancewarta ma'abociyar kiyaye dokoki da hakkokin da yake kanta na mahaliccinta da na sauran halittu da suka hada da mutane da dabbobi da sauran samammu, wannan kuwa a matsayinta na daidaiku ne ko a matsayinta na jama'a.
Mun yi amfani da misalai masu yawa a littafin domin ya zama kusa da cimma abin da muke so na fahimtarsa, don cimma buri na kawo gyara ga al'umma da yanayin da kowa zai iya karantawa ya kuma fahimci sakon da ake son isarwa.
Ina rokon Allah ya bayar da ladan rubuta wannan littafi ga Ahlul Bait (A.S) kuma ya karbi wannan dan kokari namu ya taimake mu a kan hidimar addininsa.
Hafiz Muhammad Sa'id Rabi'ul Awwl 1424. H.K Khurdad 1382 H.SH Mayu 2003. M
Hakkokin Allah Madaukaki A Kanmu[2] Hakkin Allah (S.W.T) shi ne kadaita shi ba tare da yin shirka da shi ba, kuma da bin umarninsa da nisantar haninsa, da bauta masa ba tare da shirka ba, da yin Salla, da Zakka[3], da Azumi, da hajji, da son abin da yake so, da kin abin da yake ki, da tsayawa kan iyakar da ya gindaya mana. Amma akwai magana kan cewa tun da kadaita Allah ba ya yiwuwa sai da saninsa shin zai yiwu a yi koyi[4] a akida? wato imani da Allah da kadaita shi ya kasance a bisa dogaro da biyayya ga fatawar malami ko kuwa hakan ba ya inganta?
Sanannen abu shi ne bai halatta ba a dogara da fatawa a kan imani da samuwar Allah ko kadaita shi[5], wajibi ne a akida a yi imani da hakan a zuciya tare da gasgatawa da hakan bisa dalili na hankali, wannan kuwa ba ya dogara bisa fatawar malami. Misali a kan haka; da wani malami zai ce da kai: Ka yi sallar Jumma'a da Azahar tare wajibi ne, wato Juma'a ba ta isarwa sai ka hada da Azahar, wannan Malami kuma da shi kake koyi sai ya mutu ko kuma ka gano wani wanda ya fi shi ilimi ya ce: Ai Azahar kawai ta isa ko Jumma'a kawai ta isa yaya zaka yi? Amsa ita ce, sai ka koma wa fatawar Malami na biyu domin nan furu'a ce kuma tana kama da aikin likita ne a Asibiti da kake komawa wanda ya fi kwarewa domin magani ko tiyata.
Amma a Akida da wani malami zai ce da kai: Ai ya gano Allah biyu ne ko sama da hakan yaya zaka yi? Sai ka bi shi? A'a. A nan sai ka ce: Malam nan dai rike Akidarka ko ka kawo wani dalili karbabbe na hankali domin ba a yi wa kowa koyi a kan Akida, haka ma da zai ce: Ya gano shi ya yi ka ba Allah ne ya halicce ka ba.
Hakkokin Allah (S.W.T) a kan 'yan Adam suna da yawa kuma aiki jajir yana kanmu, sai a mike domin a san su a kuma aikata su. Rashin sanin hakkokin Allah ya sanya jahiltarsa, jahiltarsa kuwa daidai take da jahiltar kawuka kamar yadda ya zo a wasu ruwayoyi, don haka ne jahiltarsa ta sanya rashin sanin kawukanmu[6], rashin sanin kawukanmu kuwa ya kai mu ga rashin girmama junanmu. Wannan ne ya sanya ba mai girmama ra'ayin dan'uwansa har a siyasar duniya, duba ka ga yadda aka dauki al'amarin addini kansa cikin jahilci ana jifan juna da kafirci, ana kafirta juna alhalin babu wani dalili na shari'a da zai hana ma'abota mazhabobi mabambanta su yi komai are.
Kuma yana da kyau malamai su kafa wata majalisa da zata hada kowane bangare domin kusanto da ra'ayin juna domin tattaunawa da fahimtar juna don amfanar al'umma gaba daya har ma a koyi yadda ake haura katangun mazhabar juna domin wanda ya ga wata mazhaba a wurinsa ita ta fi sai ya haura ya ketara zuwa gareta. Haka nan ya kamata katangun su zama gajeru daidai yadda za su yi dadin haurawa ga mai son haurawa, kuma wannan shi ne yake iya sanya a san abin da kowa yake a kai da fahimtarsa.
Rashin sanin Allah ya sanya ana iya yi wa mutane fashin tunani wanda ya fi fashin kaya da rayuka muni da hadari, har al'umma ta koma jayayya kan abin da bai kamata ya kai ga sabani ba. Duba ka ga rikici kan NEPU da NPC da na PRP da NPN da sauransu, har ma cikin Addini kamar sabani da rikicin 'yan kabalu da 'yan sadalu wanda har ya kai ga sakin aure, da kuma rikicin shin Annabi ya san gaibi ko bai sani ba? Kuma da zaka tambayi masu rikicin menene ma'anar gaibi da ka samu cewa babu wanda ya sani, amma ana iya kashe juna a kan irin wadannan. Nisantar tunani ingantacce mai kyau ya kai ga yin fada a kan Bushanci da Sadamanci har da kashe juna a lokacin Yakin Gabas Ta Tsakiya Na Biyu.
Haka nan a wannan lokaci a kan canja wa wasu rikice-rikicen riga sukan fito da sababbun riguna kamar ba su ba ne, sai dai babu mai iya gane su sai mai idon basira da Ilimi da tunani, misalinsa a yau shi ne batun 'yan Shi'a da Ahlussunna.
Bambancin fahimta ba matasla ba ne matukar Allah daya, manzo daya, Littafi daya, in dai ba neman fitina ba, kasancewar wannan mabiyin Ahlul Bait (A.S) ne, wancan kuma mabiyin hanafiyya ne ko shafi'iyya ko malikiyya, ko kuma wancan Sufi ne ko Arifi bai kamata ba ya cutar ko ya jawo rigima da fitina. Ba ma tsakanin musulmi ba, har ma tsakaninsu da wasunsu bai kamata ba a samu sabani da rigima!.

Tsarin Allah Madaukaki Allah ya saukar da tsarinsa mai cike da hikima wanda ya saba da tsari irin na Kwaminisanci da Demokradiyya, Tsari ne wanda aka jahilce shi a duniya wanda da an san hakikaninsa da hatta wanda ba musulmi ba, ba zai nemi wani tsari ba sai shi. Akwai wasu tsarurruka a Duniya amma ko kadan ba a iya kwatanta su da tsarin Musulunci, Kwaminis ya kafu ne bisa Fomular Hegel da Marks ya dauka ya yi amfani da ita, Hegel ya yi amfani da nazarinsa ne a kafa dalili da ilimin tunanin dan Adam, amma su Marks sun yi amfani da ita a nazari na tarihi ne da kuma juyi na al'umma don neman hada fada tsakanin masu jari da ma'aikata da kuma yakar dabi'ar halittar mutu ta ikon mallaka. Tsari ne mai yakar 'yan jari-hujja da abokan hamayya, amma ta hanyar zalunci da yakar dabi'ar halittar dan Adam da kisan kare dangi, tsari ne da bai san akwai Allah ba.
Amma Demokradiyya Ita tana dauke da jari-hujja ne da ya sanya mutum a matasyin Ubangiji da yake da iko sakakke, yana da ikon ya bautar, ya tatse, ya shanye jinin talaka, sannan ya wurgar da kashin, tsari ne mai tsotse talaka har kashinsa ya mayar da shi kamar kwarangwal.
Amma duba Musulunci ka ga ni, koma ka san Allah ka ga tsari da mulki wanda ya shimfida da yadda aka sanya dokoki aka ba wa kowane mutum hakkinsa da ya hada mace, namiji, mai kudi, talaka, mai mulki, da wanda ake mulka, da yaro, da babba. Ba zalunci, ba zalunta, ba take hakkin juna, babu yakar dabi'ar halittar dan Adam, ba bambanci ko fifiko sai da takawa.
Musulunci tsari ne cikakke bai zo da tsari irin na Demokradiyya ba, ya zo ne da AsalatusShura[7], Musulunci tsari ne mazhabi[8], amma Demokradiyya tsari ne Ilmi[9].

Daraja Da Sakamako Gwargwadon Sani Ne Mu sani kamalar hankali yana cikin sanin Allah ne, kuma Allah yana saka wa mutane da ladan aiki gwargwadon saninsu ne. Duba ka gani mana Annabi Nuhu (A.S) duk da ya dade yana shan wahala an ce tun yana shekara arba'in yake kira ga Allah (S.W.T) kuma ya rayu kusan shekara 2500 amma bai kai darajar Annabi Muhammad ba, ba domin komai ba sai domin cewa annabi Muhammad (S.A.W) ya fi shi sanin Allah (S.W.T), shi kuma Allah yana sakawa daidai gwargwadon saninsa ne ga masu aiki na gari na daga bayinsa.
Wata rana wani Mala'ika ya yi mamakin karancin ladan wani mutum mai yawan bauta ga Allah, sai yake cewa da Ubangiji: Ya Ubangiji yaya wannan bawa yana bauta mai yawa amma ladansa kadan ne? Sai Allah ya ce da shi: Ina sakawa gwargawdon sanina ne amma tafi wajansa ka gani, sai Mala'ika ya tafi wajansa, da safiya ta yi suna maganar ciyawa da take fitowa lokacin damuna ta mutu lokacin rani sai mai bauta ya ce da Mala'ika: Ai da Ubangijinka yana da jaki da ciyawan nan ba ta lalace a banza ba da yana da jaki da mun kiwata shi. Haka nan Mala'ika ya ga karancin hankalin wanann bawan shi ya jawo masa karancin lada: Haka nan abin yake wanda yafi sanin Allah ibadarsa ta rana daya tafi ta jahili na shekaru da yawa.
Ga kissar kamar yadda take a ruwaya: Wata rana wani Mala'ika yana yawo sai ya wuce wani tsibiri da wani mai bauta yake rayuwa a ciki sai ya tambayi Allah ya nuna masa ladan wannan mai bauta, sai Allah ya nuna masa, sai Mala'ika ya karanta ladansa, sai Allah ya ce da shi: Ka zama tare da shi, sai Mala'ika ya zo masa a surar mutum, sai ya tambayi Mala'ika: Wanene kai? Sai Mala'ika ya ce: Ni wani mai bautar Allah ne na ji labarinka ne da ibadarka sai na zo don in kasance tare da kai, sai ya zauna da mai bauta wuni daya, da safiya sai Mala'ika ya ce: Wannan wuri yana da shuke-shuke bai dace da komai ba sai ibada. Sai mai bauta ya ce: Ai wurin yana da aibi. Mala'ika ya ce: Menene aibin? Sai ya ce: Ubangijinmu ba shi da dabbobi, da Ubangijinmu yana da jaki da mun kiwata shi a nan, ga ciyawa nan tana lalacewa a banza. Sai Mala'ika ya ce: Shin Ubangijinka ba shi da jaki ne? Sai ya ce: Ai da yana da jaki da wannan ciyawa ba ta lalace ba! Sai Allah ya yi wa Mala'ika wahayi da cewa ni ina saka masa daidai gwargwadon hankalinsa ne[10].
Ko mutane haka suke yi a ayyukansu domin a bisa dabi'ar dan Adam ilimi shi ne yake bayar da kima da daukaka, kuma sabawa dabi'ar haka tana nufin rushewar dan Adam. Wannan al'amari na saba wa dabi'ar dan Adam shi ne ya sanya rushewar tsarin gurguzu, shi tsari ne da ya shahara da yakar dabi'ar dan Adam musamman a abin da ya shafi mallaka.
Misali; A tattalin arziki, lokacin da su Lenin suka so kafa Gurguzu (Kwaminisanci) da suka ga ba zai yiwu ba sai suka kafa Gurguzu mai sauki (Soshiyalizm): A nazarinsu aiki shi ne yake bayar da kima ko mallaka. Saboda haka a misali mai kaya idan ya kai zinarensa wajan makeri don ya yi masa dan kunne da shi, idan ya kera ba zai ba shi dankunne ba sai ya ba shi kudin zinarinsa, domin aikin kira da ya yi shi ne yake bayar da kima da mallaka. Wannan kuwa al'amari ne da ya saba wa dabi'ar dan Adam, a sakamakon haka ne ba su je ko'ina ba suka rushe. Yanzu ta kai ga cewa hatta Akidun da suka dasa na rashin samuwar mahallicci sun rushe, har a ranar 1 ga Disamba 2002 Gidan Rediyo/Telebijin na IRNA ya shelanta cewa: A yanzu kashi sittin cikin dari na mutanen Rasha sun yarda akwai Allah, al'amarin da su Lenen suke ganin haka a matsayin rashin hankali ne sakamakon maye na banju da Duniyar dan Adam ta sha ta fada cikin dimuwa.
Kwatanta aikin Lebura da Purincipal, haka nan kwatanta aikin Manajan banki da na Masinja, da na Saje da Janar, Me ya sa albashin aikin na sama na rana daya ya fi albashin aikin dayan da tazara mai yawa, wannan ba domin komai ba ne sai bambancin sani da tunani da na sama yake amfani da shi fiye da na kasa. Haka nan ne yake wajan Allah tunani da sani su suke bayar da kima ba kawai aiki ba. Amma kada mu manta cewa sanin da ba a aiki da shi mummunan abu ne maras amfani.

Masu Hana Sanin Allah Da Hakkokinsa Sannan kuma ba a bari Annabawa (A.S) sun kafa Daular Allah ba, kai hatta da lokacin Manzo (S.A.W) ya sha matsala da munafukai, amma duk da haka annabawa (A.S) sun kafa ci gaban da ba kamarsa a Duniya.
Kasar Farisa ta fi kowace kasa aikata Addinin Musulunci a hukumance da a siyasance, amma su ma ba su kai kashi hamsin cikin dari ba sakamakon yanayi. Ya zo a ruwayoyi cewa; Imam Mahadi (A.S) ne kawai Allah zai ba shi ikon kafa hukuma ta Allah mai aiki da cikakkiyar shari'a[11], shi kuwa zai samu wannan ne saboda Allah zai ba shi damar hukunci da hakikanin yadda abu yake ne ba da zahiri kawai ba[12]. Imam Sadik (A.S) yana cewa: Idan imam Mahadi (A.S) ya shugabanci mutane zai yi hukunci tsakanin mutane da hukuncin Dawud (A.S), ba ya bukatar sheda ko rantsuwa, a kowane hukunci Allah yana yi masa ilhamar hakikanin abin da ya wakana, kuma da dogaro da wannan ilimin nasa ne zai yi hukunci[13].
Sai ga wasu wadanda suke kiran kansu musulmi ba sa son a bi Allah a kasashenmu na musulmi, suna kokarin ganin hana sanin Allah ta kowane hali, da kokarin toshe duk wani kokarin fahimtar addininsa da hakkokinsa a kanmu. Sai ga Addini ana wasa da shi kowa ya fiye bangaranci da mazhabanci sai ga rarraba, sai ga jifan juna da kafirci, sai ga …
Da mutane sun san Allah hakikanin sani kuma suka bi umarninsa, da sun ci arzikinsa ta sama da ta kasa. Rashin saninsa[14] ya sabbaba rashin sanin yadda za a bauta masa ko a gode masa. Domin su malam tsutsa sun shiga cikin goro sun hana shi sakat, don haka aka kasa aiwatar da abin da Allah ya zo da shi ta hannun Annabawansa. Don haka ne ya bar wasiyyan Annabi su ci gaba da shiryar da mutane bayansa (A.S), amma duka an kashe su ne daya bayan daya[15].
Ba kawai sanin Allah (S.W.T) mahalicci ba har ma furu'a kamar siyasa, da hukunce-hukunce, da zamantakewar dan Adam, da dokoki, da tsarin musulunci duk an jahilci da yawansu a yankunanmu da sauran kasashen musulmi.
Amma nau'in matsalar yammacin Duniya ta bambanta da ta sauran kasashen musulmi ta wani banbare ne, domin su wannan hasken da yake hannunmu da ba a aiki da shi, su ba su da shi, babban misali muna iya duba al'amura kamar a Ilimin zamantakewar dan Adam, su sun sanya mutum ne a matsayin Ubangijin kansa, shi ne mai sanya doka da shar'antawa a bayan kasa amma a Musulunci ba haka ba ne, wannan yana daga abin da ya nesanta su daga sanin Allah.

Hatta Musulmi Sun Jahilci Addini Kamar yadda yake game da kuskuren da Turai suka yi na mummunar fahimta da kuma jahiltarsu game da musulunci, haka su kansu musulmi suka yi masa mummunar fahimta kuma suka jahilce shi. Babban misali a kasashenmu shi ne: Da zaka ambaci kalmar shari'a sai mutane su yi tunanin irin fille kai, da jefewa, da gutsure hannaye da kafafu.
Misali da zaka tambayi wanda ba musulmi ba a sabanin da makiyan kasarmu na ciki ko na waje suka haifar kan batun shari'a a Arewa me yake nufi da ba shari'a? Zai ce: Ba gutsure hannu da makamantan wannan, haka nan amsar da musulmi zai iya ba ka kenan idan yana maganar shari'a. wato wannan shi kenan shi ne musulunci.
Saboda haka dole ne a tashi don kawar da jahilci da miyagun hannayensa masu guba da suke tafiyar da tunanin mutane game da musulunci har aka kai ga fadawa cikin irin wannan dimuwa. Musulunci yana da fadi ba babi daya ba ne, ya kamata a nemi saninsa daga masanansa na ainihi, ba kowa ne ya san shi ba don ba gado ba ne kuma ba al'ada ba ce.

Ba A Karanta Akidu Da Tarihi Babbar matsala a cikin al'ummarmu ita ce kauracewa Ilimin sanin Allah da shagaltuwa da furu'a kawai, wannan kuwa ya tauye tunanin mutane game da saninsa (S.W.T). Ash'arawa sukan takaita a kan Littafin Kawa'idi ne da mafi yawa ba sa ma fahimtarsa, wanda ya yi zurfi shi ne wanda ya kai ga Sharhi Ummul Barahin, da kyar zaka sami wanda ya wuce hakan sai daidaiku. Ba a ma san Al'makalat da Al'ibana na Al'ash'ari shi kansa mai Mazhabar Ash'ariyya ba, yawanci ba a san wanda ake bi a Mazhaba ko Akida ba.
Haka sanin Allah ya yi nesa da mutane suka yi nisa da shi, haka ma al'amarin tarihin musulunci da ba a karanta shi wai akwai rigima a ciki da ba a so a sani, wai idan aka yi fada da uwa da uba Shin ka so ka sani?
Sai na ce da mai wannan tunani: Da bambanci, domin na su baba bai shafi makomarka ta Lahira ba, kuma ba ka son sanin waye Manzo (S.A.W) ya bari tsakaninsu wanda bin sa ya zama hujja a kanka. Amma na tarihin musulunci ya shafe ka, domin zai gaya maka makomarka ne, da abin da Manzo (S.A.W) ya bar maka a matsayin tsiranka a duniya da lahira.
Na biyu, ana bukatar ma'aunin waye maganarsa ta fi zama hujja don ka yi aiki da ita, wannan duk ya shafi makomarka ne.
Haka aka haramta wa al'ummarmu sanin Akidu da ilimomi har ka san menene gasakiya ka bi, menene a ganinka ba daidai ba ne ka bari. Duba ka ga ni mana Shehu Dan Fodia (R.A) yana ganin daga cikin bala'in da ya game kasashenmu na Hausa shi ne koyi a Usuluddin amma har zuwa yanzu abin da Shehu ya so a kawar na koyi a Usuluddin ya ci gaba. Koda yake wasu malamai sun tafi a kan cewa; wanda ya fadaka, ya yarda har a zuciyarsa, ya yi imani da samuwar Allah da kadaita shi a bisa sahihiyar Akidar musulunci, duk da tun yana yaro ya yi koyi da malamai ne ko iyaye, amma irin wannan imanin yana isarwa gare shi.

Hakkin Da Yake Kan Annabawan Allah Annabawa (A.S) sun zo ne domin motsa hankali[16] ya yi tunani ya yi imani a Akidar samuwar Allah da kadaita shi a ibada da zatinsa da siffofinsa da ayyukansa, da kuma yarda da annabawan da ya aiko da riko da sakonnin da suka zo da su. Annabawa ba su ce a bi su ido rufe ba dalili ba, wannan al'amari ne ya sanya Allah yake ba su mu'ujiza da take dalili ce na hankali a kan cewa sakon da suke dauke da shi daga gareshi ne, wannan kuwa zai samar da nutsuwa a zukata har su karbi sakonsa.
Amma hukuncin furu'a (hukunce-hukunce) su an sanya su bisa biyayya da maslaha ne wacce ba kasafai aka santa ba sai dai a bi umarnin Allah a ciki, don haka ne Allah yake sanya wa kowane Annabi (A.S) wasiyyi da zai yi wa mutane bayanin abin da sakon ya kunsa bayan wafatinsa, kamar yadda annabin rahama (S.A.W) ya yi wasiyya ga wannan al'umma da imam Ali (A.S) da goma sha daya daga 'ya'yansa a bayansa.
Matsalolin da wasiyyan Annabi suka fuskanta na kawar da su daga fagen jagorancin al'umma a hukumanci da kisa sun sanya Allah (S.W.T) ya boye na karshensu imam Mahadi (A.S) domin kada a kashe shi domin ya zo a karshen duniya ya cika ta da adalci bayan an cika ta da zalunci. Shi kuma imam Mahadi (A.S) kafin ya boyu ya yi wasiyya da riko da malamai na gari. Saboda haka duk wanda ya kai matakin Ijtihadi wato ya daukaka kan sauran mutanen duniya gaba daya a ilimi, da takawa, da adalci, da kamala, da tsentseni kuma ya kasance dan halal ne, to ya zama dole ne a bi shi[17].


1
HAKKOKI A MUSULUNCI Hakkin Imami (Shugaban Zamani) A Kannu Sanin Imamin lokacinmu yana daga cikin hakkokin Allah a kanmu, domin duk wanda ya mutu bai san Imamin zamaninsa ba ya yi mutuwar Jahiliyya[18], haka nan ya zo a Kur'ani mai girma cewa a Ranar Lahira kowace al'umma za a kira ta tare da imaminta ne[19]. Wadannan imamai Allah bai bar mu mun zabe su da kanmu ba sai da ya shelanta su ta hannun Manzonsa (S.A.W)[20] wanda ya sanar da mu cewa su goma sha biyu ne: Na farkonsu Ali (A.S) na karshensu Mahadi (A.S) wanda yake shi ne imamin wannan zamanin.
Sanin Imam ba wai kawai sanin sunansa ba ne, saninsa ya hada da binsa kuma da koyi da abin da ya bari na wasiyyarsa kuma da bin koyarwarsa da malaman da suke shiryarwa zuwa ga abin da ya bari da kin makiyansa[21]. Al'amarin ba wasa ba ne kamar yadda wasu suke dauka domin ko Salla da Azumi da duk wata ibada idan babu mika wuya ga Imami Allah ba ya karba. Manzon tsira (S.A.W) ya ce: "Wanda ya mutu bai san Imaminsa ba ya yi mutuwar Jahiliyya"[22]. Domin zai tashi a Ranar Lahira kamar wanda ya yi zamani kafin a aiko Annabi ba shi da komai da Allah (S.W.T) ya karba daga gare shi.

Hakkokin Littafin Allah A Kanmu Karanta littafin Allah da saninsa suna daga cikin hakkokinsa a kanmu, amma sanin littafin ba yana nufin mu san sunansa ba kawai domin hakan ko kadan ba shi da wata ma'ana, amma abin nufi shi ne ya zama mun siffantu da Kur'anin a aikace. Idan ba haka ba a ranar lahira akwai kara da zai shigar a kotun Allah[23] wacce ba a zalunci a nan kuma ba a iya boye gaskiya. Kuma dole a bi shi kamar yadda Manzo da wasiyyansa goma sha biyu daga Alayensa suka fassara domin su ne ya ce: "Idan an yi riko da su ba za a taba bata ba har abada". kuma "Da Su da Littafin Allah ba sa rabuwa har sai sun riske shi a tafki"[24].
Haka nan al'amarin yake a matsayin al'umma, dole ne Littafin Allah ya yi iko da rayuwarmu a matsayin al'umma, in ba haka ba, ba mu sauke nauyin da yake kanmu ba. Kuma dole ne mu siffantu da shi, in ba haka ba, yana da hakkin karar cewa musulmi sun bijire masa.

Hakkokin Addini A Kanmu Addinin Musulunci yana da hakki na kare shi a kan kowane musulmi da bakinsa da basirar da Allah ya ba shi, da wajabcin saninsa da taimakawa wajan yada shi a aikace[25] da baki da kyawawan dabi'u, da kokarin hada kan mabiyansa, da raddi cikin hikima ga masu gaba da shi, da girmama fahimtar ma'abotansa don ba ka sani ba ta yiwu shi mai waccan fahimtar da ta saba da taka shi ne yake a kan daidai.
Kada mutumin da bai fahimta ba ko bai sani ba ya tsoma baki da jayayya a kan mas'alolin Addini[26] wannan na malamai ne, kamar yadda shehu Usman dan fodiyo (R.A) ya yi nuni da haka yayin da yake nuni da bidi'oin da aka farar cikin Addini da cewa: Shi malami kada ya sa mutane cikin rikicin Addini haka ma maras Ilimi kada ya sanya kansa cikin rikicin Addini, bayyana ra'ayi kan mas'aloli abu ne na malamai.

Hakkokin Garuruwa Ne A Tsaftace Su Rashin kula da tsafta daga bangaren gwamnati da kuma al'umma yana daga cikin mummunan al'amari da addabi birane da kauyuka, ta yadda zaka ga duk ko'ina ana iya zuba shara[27]. Ga mummunan tsarin da garuruwa suke fama da shi, sai a sayar da hanyoyi har da hanyar ruwa ta yadda damina da kwararar ruwa zasu wahalar da talaka, ga karancin manyan hanyoyi da matsattsun kananan lunguna[28]. Idan kuwa damina ta zo talakawa suna fargaba ne, ga miyagun lunguna da kududdufai marasa hanya, amma ba za a rushe gidaje a fadada hanyoyin ruwa da na motoci da yin kwatami don samar da magudanar ruwa ba.
Mafi girman abin takaici shi ne abin da na gani a Jami'ar Bayaro da na dade ban ga irinsa ba, sai na ga takardu a ko'ina a kasa, matattakala duk da tabo ta yi bakin kirin, muna tsaye muna hira sai wani ya watso ruwa daga sama duk ya kusa bata mu, idan kuwa ka wuce wasu wurare wari yana tashi. Sai na fara tunanin Jam'iar Tehran da wuri ne kodayaushe kamar ka sanya abincinka a kasa ka ci, na rika tunanin cewa a yanzu da wani zai zo daga abokanmu daga Jami'ar ya ga wurin kwanan dalibai kawai da an ji kunya. Kuma da zaka tambaya a kan me aka gina imani? Daya daga mafi muhimmancinsu ita ce tsafta: Hatta ma wasu hukunce-hukuncen Allah yakan sanya su ne domin kai wa ga cimma samuwar tsafta a cikin al'umma.
Ba ma jami'a ba, a irin wadannan kasashe a cikin gari duk wani yanki a kowane dare yana da motoci na musamman wadanda da dare sukan wanke titinan yankin. Amma wani abin takaici a kasarmu ba ma kawai tsaftar gari ba, kana iya ganin yanki da miliyoyin mutane suke rayuwa ba tare da wani isasshen ruwan sha ba.

Hakkokin Da Suke Tsakanin Mutane Kowane mutum yana da hakkoki masu yawa a kan dan'uwansa mutum musamman abokin zamantakewa na kasa ko gari, ko makaranta, da duk wani waje da alaka ta kan hada juna kamar wajan aiki. Babban ma'auni na hakkin junanmu a kanmu shi ne wanda ya zo a cikin Hadisai na cewa: "Mu duba duk abin da muke so a yi mana sai mu yi wa mutane shi, mu kuma duba duk abin da muke ki a yi mana shi sai mu guji yi wa mutane shi"[29]. Misali kana kin a wulakanta ka, kuma kana son a girmamaka, to a nan sai ka ki wulakanta mutane kuma ka girmama su.
Wannan hadisi da za a yi aiki da shi, da Duniya gaba daya ta zauna cikin aminci, da ta juya ta zama kamar aljanna, da so ya game tsakanin mai kudi da talaka, da mai ilimi da maras ilimi, da miji da mata, da 'ya'ya da iyaye, da malami da dalibi, da mai mulki da wanda ake mulka, da dukkanin nau'i na mutane gaba daya.
Wannan hakkoki kuwa sun hada nisantar cutar da waninmu ta kowace hanya kamar duka ko da kuwa dalibinmu ne, amma a kasashenmu duka wani abu ne mai sauki. Kai a makarantun Furamare da na Allo har yakan yi muni kwarai; mai dukan ba ya neman izinin Shugaban musulmi, ko uban da, sai a yi ta jibga ko mai kankantar abu.
Duka ba ya halatta koda kuwa uwa ce ga danta sai da izinin uba[30], ko dukan uba ga dansa ko wanda Shugaban musulmi ya ba wa izini. Shi ma uban a matsayin tarbiyyantarwa da ya zama sai ta hakan, kuma ba mai cutarwa ba. Ko kuma miji ga mace mai nushuzi[31], shi ma a mataki na uku na karshe[32] kuma ba mai cutarwa ba, sai kuma Shugaban musulmi ga mai laifi kamar a haddi ko ladabtarwa.
Daga cikin hakkin mutum a kan waninsa shi ne ya shiryar da shi abin da zai amfanar da shi, kamar hakkin mutane a kan likita na ya nuna musu hanyar tsafta da kare lafiya, da yadda zasu tsara abinci da abin sha mai sanya lafiya, da magunguna, musamman ta hanyar Gidan Radio da Talabijin; Da maras lafiya zai tafi wajan likita sai ya cutar da shi to dole ne ya biya shi diyya, amma idan da gangan ne sai a yi masa kisasi.
Kamar yadda yake wajibi ne a kan malami ya shiryar da al'umma kuma ya ilmantar da ita, mai kudi kuwa ya yi odar abin da yake tattalin rayuwa na al'umma kuma ya sanya farashi da talaka zai iya saya cikin sauki, haka ma injiniya ya kyautata mota ta yadda ba zata zama hadari ga mai hawanta ba, mai gini kuwa ya kyautata shi.
Haka nan yana kan mai sayan kaya ya girmama mai sayarwa shi ma mai sayarwa ya mutunta mai saya, likita da marasa lafiya, mai kudi da talaka, malami da marasa sani, mai haya da dan haya, mai aiki da shugaba. Bai kamata ba shugaba a ma'aikata ya rika kallon masinja kallon wulakanci, hakki ne a kansa ya girmama masinja, ya tuna shi ma dan kasa ne kamarsa kuma ma'aikaci da bai fi shi da komai ba a wajan Allah sai dai idan ya fi shi takawa domin ita ce ma'aunin fifiko. Haka ma dan hayar mota kamar Taksi da Bos (hayis) kada ya zama idan ya ga fasinja yana ganin naira goma ne ko biyar ko ishirin, hakki ne a kansa ya ga mutum yake kallo kafin ya ga Naira ishirin, kuma ya yi mu'amala da shi ta mutunci da girmamawa tsakanin juna.
Haka nan alakar na kan mota da na kan jaki, da na jirgin sama da na kasa[33], duka daya ne a wajan Allah kuma ba mai fifiko sai da takawa, rashin kiyaye wannan da mantawa da Allah ya sanya rashin kiyaye hakkin juna.
Wani misali a kan haka shi ne; wata rana wani mai kudi shahararre ya taba kade wani almajiri da mota a kan titi, maimakon mutane su nemi ya bayar da kudin magani a kai almajirin kyamist tun da shi ba shi da mutuntaka domin ba ya ganin almajirin mutum ne kamarsa don ko taba shi bai yi ba, sai suka zo suna ba shi hakuri. Har da cewa: Ai da ma haka almajirai suke ba sa jin magana. Haka mutakabbirin ya hau mota ya wuce! Shi kuwa bawan Allah yana ta nishi har ya samu da kyar ya taka. Su kuwa mutanen ba mai ji a jikinsa cewa an ji wa wani mutum daga cikin mutane masu hakki kamar kowa ciwo! Wallahi da dabba ce aka kade da sun fi ba ta muhimmanci!.
Daga cikin hakkin mutun a kan dan'uwansa mutum taya shi bakin ciki idan wani abu ya same shi musamman ma dan'uwa na jini ko na Addini da makwabci, kamar idan an yi masa mutuwa to ya kamata ne bisa koyarwa ta Manzo (S.A.W) a yi abinci kwana uku daga makwabta ana kai musu kamar yadda ya koya mana kyawawan dabi'u da fadinsa: "Ku yi wa iyalan Ja'afar abinci hakika wani al'amari da ya shagaltar da su ya same su"[34]. Amma abin sai ya zama bisa akasi, maimakon a kai gidan mutuwa, sai ya zama su ne kuma za a shagaltar da su da ciyar da masu taruwa.
Idan muka waiwayi alakar mai kudi da yaronsa al'amarin ya kai ga ana iya samun yaron Alhaji da rashin lafiyarsa bai fi a kashe kudi kankani a kansa ba ya warke amma yana iya mutuwa alhali Alhajin da ya yi wa hidima a gida, da shago, da kanti, shekaru masu yawa yana gani sai dai ya mutu. Wani kuma yana aiki karkashin uban gidansa amma canja riga mai tsada yana iya tayar da mugunyar tsatsar nan ta hassada a zuciyar uban gidan, sai ya ce da shi: Ka tattara naka ka yi gaba kuma ka bar min shagona.
Akwai wata kabila da galibinsu ba ma musulmi ba ne amma har bikin yaye yaron shagonsu suke da shi. Idan kuwa ka duba bangaren kere-kere to a nan sun yi nisa, sannan wasu abubuwan idan kana nemansu ranar lahadi to lallai ka wahala domin sun kulle shaguna. Don haka idan ana son mafita da ci gaba ya zama dole ne a siffantu da siffa ta gari a bar hassada da kyashi, a cire duk wata dauda daga zuciya. Idan wani ya ci gaba ta hanyarmu sai mu gode wa Allah, amma rashin kishin kai da son ci gaban juna, da rashin kyawawa dabi'un musulunci ya sanya ana danne hakkin juna, kuma mu sani cewa dukkan ayyukanmu suna da hisabi a Lahira.

Hakkokin Mai Mulki Da Wanda Ake Mulka Wannan yana iya bayyana ne ta hanyar sanin wanene shugaba da siffofinsa, domin idan mun san siffofin mai mulki to muna iya gane wannan alaka ta hakkokin mai mulki da wanda ake mulka: Daga cikin siffofin shugaba su ne; ya zama mai karfin tafiyar da mulki da Iliminsa da basirarsa, mai karfin zartarwa, kuma amintacce, wanda ba ya cin amanar al'ummar kasarsa.
Mai neman maslaha ga al'ummarsa, mai daukarsu a matsayin 'yanuwansa, maras tsanantawa a kan mutanensa. Kuma mai sakin fuska, mai hankali, da ilimi, da adalci, mai karbar shawara daga mutanensa wajan gudanar da al'amuranta, mai daidaitawa tsakanin mabiyansa ba tare da son kai ba ko fifita wasu kan wasu.
Haka nan ya kasance mai kwarjini, mai kyawawan dabi'u da son gyara, mai hidima ga mutanensa, masanin siyasar Duniya da al'amarin tafiyar da al'umma, mai karbar nasiha daga talakawansa ko wakilansu, mai saukin hali. Ya kasance ba ya daukar fansa kan abokan hamayya, kuma mai kyauta ba marowaci ba, mai kaifin basira da yakan iya mayar da makiyi masoyi saboda kyawawan halaye da basirarsa, mai tausasawa ba mai tsanantawa ba.
Duba wasikar da Imam Ali (A.S) ya rubuta wa Malik Ashtar yana cewa da shi: "Ka nisanci fushin al'ummarka domin fushinsu yana tare da fushin Allah"[35]. Mu sani cewa idan shugaba zai kalli kansa ne to lallai zai fada cikin fushin al'umma domin su ba su da abin da yake da shi, wasu shugabannin sukan kara kudin kaya ba ruwansu da talaka, sai ka ga al'ummar ta koma tana kinsa ba ta ganinsa daya daga cikinta, da zai wuce tana iya jifansa.
Amma a tsari na adalci dole ne shugaba ya ji cewa shi daya ne daga cikin 'ya'yan al'ummarsa, wannan zan sanya idan ta gan shi ta nuna shaukinta da kaunarta gareshi, idan ya mutu tana nuna bakin cikinta kamar yadda a wannan zamani namu ya faru ga Imam khomaini da mutane sama da miliyan ishirin suka zo jana'izarsa, mutanen kasarsa suka yi kwanaki suna kuka, kasar gaba dayanta ta shelanta zaman makoki na kwanaki. Ta haka ne a kan gane waye ya yi wa al'ummarsa adalci? Waye kuma ya zalunce ta?
Akwai wanda ya taba rike babban mukami a kasar nan amma da ya mutu mutane da yawa sun yi bukukuwan murnar mutuwarsa, aka hole aka yi annashuwa, a kan titina. Akwai kuma wadanda suka mutu amma har yanzu al'umma tana bakin cikin rashinsu, wannan kuwa ya isa wa'azi ga na yanzu rayayyu.

Hakkin Shugaba A Kan Al'umma Daga cikin hakkokin shugaba su ne; a yi masa biyayya ga abin da bai saba wa Allah (S.W.T) ba. Kuma wasu bayanai sun zo game da cewa; yana daga hakkin shugaba a kan al'umma a ba shi shawara da nasiha, idan kuwa zai kauce hanya sai a tuna masa, sannan a taimaka masa domin ci gaban addini da al'umma gaba daya[36].
Dan kasa na gari shi ne wanda yake kiyaye doka koda kuwa ta kan titin mota ce. Wani malamin Ilimin tafiyar da al'amuran al'umma ya taba ba mu labari cewa: Wata rana ya dauko wani dalibinsa suna tafiya, sai suka isa wata danja ba mota ko daya amma bangarensu ba a bayar da hannu ba sai ya wuce. Sai dalibinsa ya ce: Amma da an kiyaye. Sai ya ce da shi: Ai ba mota. Sai dalibin ya ce: Amma da ka girmama dokar da kuma wadanda suka sanya dokar, don sun yi tunani kafin kafa ta, kuma don maslahar kanka da ta sauran 'yan kasa ne. Ya ce: Sai ya yi kwana ya koma ya sake jira sannan ya wuce. Tun ran nan ya amfana da nasihar dalibinsa kuma ya yi masa godiya.

Hakkokin Dan Kasa A Kan Shugaba Yana daga cikin hakkokin dan kasa a samar masa da aminci, da kariya, da lafiya, da ilimi, da hakkin fadin ra'ayinsa, da hakkin zamantakewa, da na walwala, da dukkan abin da ya shafi ci gaban rayuwarsa ta Duniya da Lahira. Haka nan yana da hakki kan masu tsaron kasa, amma wani abin haushi shi ne; samun tazara mai yawa tsakanin masu tsaron kasa da al'umma, ta yadda al'umma ba ta ganinsu wani bangare nata. Wannan kuwa yana faruwa ne sakamakon ba sa ji ko kadan cewa suna aiki don al'ummarsu ne kamar suna aiki don shugaba ne.
Wannan mummunan kuskure ya sanya masu kare doka sai su yi zalunci babu tausayi, har ma takan kai ga lahantawa ko salwantar da rai, kuma ga karbar cin hanci da ya zama ruwan dare. Koda yake a ciki akwai mutane masu hankali da kula da aiki da son taimakon al'umma kuma ba sa karbar cin hanci, irinsu ne suke iya mutuwa wajan kare mutanensu, amma da yawa ba haka suke ba sai dai kokari wajan neman na aljihunsu kawai sun manta da manufarsu. Wani lokaci kamar suna cike da jin haushin mutane ne, ta yadda da sun kama mai laifi sai duka da azabtarwa, alhali shi mai laifi koda kuwa barawo ne da makamancinsa mai kare doka ba shi da hakkin yi masa wani abu sai dai ya kai shi kotu ta yanke masa hukunci.
Ban taba sanin cewa al'umma tana da tazara mai yawa da 'yan doka ba sai ranar da na samu nawa rabon, har ma wani yana jinginamu da wata kasa kai ka ce su ba mutane ba ne. Wani daga cikinsu ya ce: Irin wannan ku rika guduwa tun da ku ba ma su laifi ba ne! Kai ka ce su makafi ne da ba sa ganin mai laifi!. A ofishinsu ne na ga wani ana ta dukansa wai ya yi taurin kai a shiga mota, ana buga kansa da kasa, shi kuwa yana ta la'antar duk wani uba ko uwa na dan sanda.
Kuma a nan ne na yi mamakin yadda wani tsararre yake la'antar uwar ma da ta haifi dan sanda, har ma ya ce: Babansa ya taba cewa da shi tun da ya rasa aiki ya yi aikin dan doka. Sai ya ce: Ai baba gwara ka tsine mini in san ni tsinanne ne da in yi wannan aiki, ya kara da cewa: Wallahi in gawa ta kai dubu to shi zai iya gano ta dan sanda a ciki don fuskarsa ba ta cikawa da imani.
A lokacin ne na san cewa lallai akwai tazara mai yawa sosai tsakanin 'yan sanda da al'umma, amma ra'ayin mutane da yawa ya tafi a kan cewa: Zafin zalunci da take hakkin dan Adam shi ya jawo haka, ta yadda mai tsaron kasa yake ganin yana yi wa shugaba aiki ne ba al'ummarsa ba, kuma yana ganin hadafinsa shi ne ya huce haushinsa kan al'ummarsa, sai ya cire wa al'umma jin cewa shi daga cikinta yake.
Haka al'amarin yake game da soja, kamar yadda dan sanda yake da hakkin kare cikin kasa da samar da aminci, haka ya zama wajibi a kansa ya kare kasa daga waje kada wani ya kai farmaki kanta. Amma wani abin takaici al'umma ba ta jin su nata ne haka su ma ba sa jin al'umma ta su ce. A misali da za a yi rigima tsakanin wani dan kasa da soja, da zaran sojoji sun isa wurin ba sa tambaya, a wurinsu mai gaskiya shi ne mai kaki na soja. Wannan rashin ganin juna a matsayin abu daya ya shafi har matsayin auratayya, domin na sha jin soja (ladani ne) yana nasiha a masallacin Barikin Bukabu da yake Kano yana cewa: Me ya sa ba a zuwa daga gari a auri 'ya'yansu? Ko su ba kamar sauran mutane suke ba. Haka nan aka jahilci hakkin juna tsakanin mai tsaro da wanda ake tsaro har ya zama kamar al'umma daban-daban ce a cikin al'umma daya.
Duba ka ga me Imam Ali (A.S) yake cewa game da mai tsaron kasa: "Runduna: Ita ce kariyar al'umma da izinin Allah, kuma adon shugabanni, izzar Addini, hanyoyin aminci, al'ummar kasa ba ta tsayuwa daram sai da su"[37]. A wani wurin yana cewa: "Ka sanya wa rundunarka jagora wanda ya fi su nutsuwa da biyayya ga Allah da Manzonsa a ganinka. Wanda ya fi sirri na gari (wato mai dabi'u masu kyau), wanda ya fi su hakuri, da ilimi, da sanin tafiyar da al'amuran al'umma, da rashin saurin fushi, kuma da karbar uzurin mutane. Mai tausayawa talakawa, maras bayar da dama ga masu karfi. Wanda takurawa ba ta harzuka shi, rauni (karayar zuci) ba ya dunkufar da shi[38]. A cikin wannan akwai nuni da cewa: Cin hanci shi ne abin da yake kawo ba wa mai karfi dama ya taka doka. Kuma akwai nuni da cewa: Bin hakkin dan kasa wajibi ne a kan hukuma a ko'ina ne yake, al'amarin da ya yi karanci a kasashenmu ko ma ba a san da shi ba.
Yana daga cikin hakkin dan kasa a samar masa da wurin shakatawa da walwala da wuraren hutawa da na wasanni da shi da iyalinsa da yaransa. Wani abin takaici irin wadannan filayen da ake warewa unguwanni domin wasanni saudayawa maciya amanar al'umma suka sayar da su al'umma tana gani, mafi ban haushi da muni shi ne mafi yawa ba su san ma cewa wannan hakkinsu ba ne.


2
HAKKOKI A MUSULUNCI Hakkokin Mutane Game Da Arzikin Kasa Haka nan talaka ba ya ganin ma yana da hakki a arzikin kasa, in banda 'yan kwanakin nan da wasu 'yan kadan suka san hakan, al'amarin har ya kai ga wasu daga masu tafiyar da al'amarin al'umma suna neman jahiltar hakan. Saudayawa mai mulki ba ya kiyaye hakkin wanda yake mulka game da arziki da albarkatun kasa, idan kuwa ka ce zaka yi magana kan sauran kayan rayuwa a nan kam sai dai ka mutu da bakin ciki. Duba ka ga wutar lantarki, da ruwan famfo, da man fetur da kasar nan take ita ce ta biyar a duniya a yau. Kuma duba ka ga wasu kasashe da mun fi su karfin tattalin arziki amma ba su da wata matsalar irin wadannan abubuwan rayuwa, man fetur kuwa a wajensu kusan mafarki ne wani ya ce ya ga dogon layi ko babu, kuma a gidaje akwai wuyarin na wutar lantarki da fayef na famfo da na Gas, wannan kuwa duk sun yi shi ne cikin shekaru kadan. Kuma mutanensu suna biyan kudi kankani ne domin duk talaka yana iya biyan kudin. Haka ma a gidaje akwai kayan sanyaya gida a lokacin zafi kuma da abin dumama daki lokacin sanyi, amma wadannan abubuwan a kasarmu a gun talaka wani kayan masu jin dadi ne.
Wani abin kunya da dan Nijeriya yake sha a duniya shi ne; ga shi kasar a waje tana da kima saboda suna jin labarin tana da arziki, amma hatta da gasar kwallon kafar da aka yi a kasar sai ana yi ana dauke wuta. Irin wannan al'amarin ya faru wata rana yayin da muka isa tashar jiragen sama ta Kano, ga fankokin kansu suna bayar da zafi ne amma duk wannan bai isa ba sai aka dauke wuta, wani mutum (ba dan Nijeriya ba ne) ina ji ya ce: Kai ka ga Air port sai ka ce kango. Haka nan ake tara wa 'yan kasar abin kunya a kasashen waje kai ka ce masu mulki ba sa zuwa wasu kasashe suna ganin abin da yake faruwa.

Hakkokin Mutane A Kotuna Idan kuwa ka waiwaya kotu abin ya yi muni sosai, amma akwai ma'auni na gane kotun zalunci da kotun adalci, Idan ka ga kotu mai kudi da sarki suna jin tsoronta to ana adalci ne kuma ana bin gaskiya ne, amma idan ka ga talaka kawai ne yake tsoron kotu to ka sani ana zalunci ne. Wani lokaci akan ja shari'a da ya kamata a yanke ta a sati ko awowi kadan amma sai ta yi watanni da shekaru har ma mai hakki ya ce ya yafe, ko ya gaji ya bari don kansa. Wani lokaci hakkin yana rutsawa da kudin marayu ne amma sai ka ga kotu ta ajiye a banki tana samun kudin ruwan, wani lokaci ma ba ya isa sai an diba daga hakkin maraya an sa a aljihu. Wani lokaci kuma akan iya mirgide gaskiya ko jifa da hauka ga wani don wani ya kubuta, da haka ne hakkoki masu yawa na mutane suke salwanta.

Hakkin Malami A Kan Dalibi Malami yana da hakki a kan dalibi, a takaice muna iya cewa: a girmama shi, da sauraronsa idan yana magana, da barinsa ya amsa tambayar da wani ya yi masa, da kaskantar da kai a gare shi, da kare shi daga mai sukansa, da rufa asirinsa ko aibinsa, da yada kyawawansa da alherinsa, kada ka zauna da makiyinsa, kada ka yi gaba da masoyinsa.

Hakkin Dalibi A Kan Malami Malami ya tausaya wa dalibai kuma ya san cewa su 'ya'yansa ne don haka yana neman tsiransu ne, kada kuma ya taba yi musu gori ko kausasa musu hali. Kuma ya rika yi musu nasiha, ya nisantar da su daga miyagun halaye, kada ya muzanta musu wani ilimi da ba a wajansa suke koyonsa ba, kamar idan shi malamin nahawu ne to kada ya rika kushe musu Ilimin mandik, ya rika yi musu magana daidai fahimta da kwakwalwarsu, kada ya yi musu rowa ta Ilimi.

Hakkin Mace A Kan Mijinta Daga cikin hakkin mace a kan mijinta shi ne ya girmamata, kuma ya tausaya mata da tausasawa, ya ciyar da ita, idan ta yi laifi ya yafe mata, kada ya la'ance ta ko ya zage ta ko ya doke ta, kada ya muzanta ta ko ya kunyata ta ko ya daidaita mata asiri.
Haka nan akwai hadisai da dama da suka zo game da falalar mutumen da yake taya matarsa aikin gida, don haka bai kamata ba al'ada ta rinjayi Addini, don wasu sukan ki hakan saboda wani dalili maras ma'ana na al'ada.
Dole ne miji ya yi adalci ga matarsa da tsakanin 'ya'yansa da matansa, kamar yadda yake wajibi a kansa ya nuna mata soyayyarsa, kuma ya nuna mata wannan a fili ta yadda zata zama abokiyarsa a komai. Kuma ya rika yi mata maganganu irin na soyayya da nuna kauna ga juna, bai isa ba ya ba ta kudi kawai don yana da shi, wannan ba ya isa ga bukatun mace. Shi ya sa Allah (S.W.T) ya fada a cikin littafinsa cewa: "Ya sanya soyayya (kauna) da tausayi (rahama) a tsakaninku"[39].
Haka nan ba shi da kyau ga miji ya munana zato ga matarsa, ko ba komai munana zato ga musulmi haramun ne, idan mace ta san mijinta yana munana mata zato alhalin tana mai kame kanta wannan yana iya rusa alakar soyayya da girmama juna da ke tsakaninsu har ya kai su ga rabuwa.

Hakkin Miji A Kan Matarsa Daga cikin hakkin miji a kan matarsa shi ne: Kada ta ki shimfidarsa in ya neme ta, kada ta bayar da izinin shiga gidansa ga wanda ba ya son shigarsu, kada ta yada sirrinsa ko ta yi masa barnar dukiya, ta kula da yaransa da kuma ayyukansa na gida da suka shafeta, kada ta kausasa masa harshe, ta yi kokarin faranta masa rai. Sannan ta rika ba shi uzuri a kan wasu al'amuran, kada ta yi abin da zai sa shi ya ji baya son zama da ita a gida ko abin da zai sanya shi nisantar hira da ita ko kaurace mata.
Wasu ruwayoyi sun kawo hakkin miji kan matarsa kamar haka: Yayin da wani sahabi ya ba wa Manzon Allah (S.A.W) labari cewa: Yana da mata da idan ya kalle ta sai ta faranta masa rai, idan ya shiga gida da bakin ciki sai ta yaye masa shi, idan kuwa ba ya nan tana kare shimfidarsa ba ta ha'intarsa, kuma ta kare dukiyarsa da kula da tarbiyyar 'ya'yansa. Sai Manzon Rahama (S.A.W) ya ba shi amsa da cewa: "Allah yana da ma'aikata, kuma wannan matar tana daga cikin masu aikin Allah, kuma tana da rabin ladan shahidi"[40]. Haka nan wata ruwaya ta nuna cewa: "Mace mai aiki a gidan miji daidai take da wanda yake Jihadi a tafarkin Allah"[41].
Haka nan dole ne ta yi biyayya a gare shi[42] domin shi shugaba ne a gida babu kuma yadda mutane biyu zasu hadu a wuri ba tare da shugaba ba, ta sani rashin biyayya a gare shi yana rusa masa ruhinsa da karya masa zuciya, sai ya fara tunanin daukar fansa sai gaba ta faru, kuma zamansu ya gurbace, ko kuma wannan fushin ya tura shi ga miyagun halaye da kuma yawan fusata da fada.
Kada wata mata ta rika gasa da wasu mata ta ce: An saya wa kawata kaza kai ma sai ka yi min kaza wannan ko kadan ba shi da kyau. Yana da kyau mata su dauki samfurin rayuwar zamantakewa daga Imam Ali (A.S) da sayyida Zahara (A.S), ga wani misali daga irin wannan; Wata rana Imam Ali (A.S) ya shiga wajan Fadima (A.S) sai ya tambaye ta ko tana da wani abu sai ta ce: "Wallahi kwana uku ke nan ya Dan Ammina ba mu da komai". Sai ya ce: "Me ya sa ba ki gaya min ba" Sai ta ce: "Manzon Allah ya hana ta tambayarsa, ya gaya mata cewa: Kada ki tambayi Dan Amminki (Imam Ali) komai, idan ya kawo, in ba haka ba, kada ki tambaye shi".[43]
Duba ki ga irin wannan rayuwa ta gidan Ahlul Bait (A.S) wacce hatta abin da yake wajibi a kan miji ba ta tambaya sai idan ya kawo, saboda haka yana da kyau mata su kamanta daidai gwargwado, kamar yadda maza su kuma su kiyaye ba kwauro ba barna.

Hakkokin Iyaye A Kan 'Yaya A nan saboda girma da muhimmancin hakkin iyaye a kan 'ya'yansu babu wani abu da zamu ce sai dai; duk abin da kasan zaka yi in dai bai saba wa shari'a ba don faranta masu rai to wannan abin ka yi shi, idan kana da da zaka iya gano sirrin haka, duba ka ga danka da wahalar da kake sha a kansa, wannan kuwa bai kebanta da mai da ba domin hankali yana iya fahimtar wahalar rayuwa da iyaye suke sha a kan 'ya'ya.
Akwai hadisai masu yawa da suka zo game da girmama iyaye da kuma biyayya a gare su kamar haka;
1-Wanda ya yi kallo zuwa ga iyayensa kallo na rahama Allah zai rubuta masa ladan aikin Hajji[44].
2- Wanda ya kalli iyayensa kallo na wulakanci Allah ba zai karbi sallarsa ba koda kuwa sun kasance suna masu zaluntarsa ne[45].
3- Umarnin iyaye ana gabartar da shi a kan wajibi kifa'i[46].
4- Kada a daga sauti kan sautin iyaye ko gabata gaba gare su[47].

Hakkokin 'Ya'ya A Kan Iyaye Daga nasihohi tattararru da suke cikin wasu hadisai su ne; Kada ka fusata danka ba tare da hakkin shari'a ba, wannan yana iya sanya masa jin haushi, da son barna, da daukar fansa, da nisantar gida ta hanyar kusantar mutanen banza. Haka nan an yi wa uba da yake tura dansa cikin biyayyar iyaye saboda kyawawan dabi'unsa rahama [48]. Game da tausasawa cikin mu'amala wannan ya zo cewa, sauki shi ne yake kawata komai[49], tsanantawa ita ce take bata komai, haka nan mata da 'ya'ya ana son a biyar da su daidai yadda zasu iya da gwargwadon karfinsu, kuma a yarda da dan kadan da zasu iya ba kausasawa ko tsanantawa. Game da girmama 'ya'ya a mu'amala ya zo cewa; Manzon Rahama (S.A.W) idan Fadima (A.S) ta shigo Gidan yakan tashi daga wajansa, ya kama hannunta, ya sumbance ta, ya zaunar da ita kan shimfidarsa[50].
A daidaita tsakanin 'ya'ya hatta a kallo: Da uba zai rika yi wa wannan kallon wulakanci ba dalili, amma wancan kuma ana lallashinsa to ba abin da wannan zai haifar sai kaiwa ga tarwatsawa da rarraba tsakanin 'ya'yan[51]. Annabi Ya'akub (A.S) ya kasance a aikace ba ya rabawa tsakanin 'ya'yansa, ba ya fifita wani a kan wani a aiki da mu'amala, amma ya kasance yana nuna wa Yusuf (A.S) soyayya domin Allah ya zabe shi, Sannan shi ne salihi a cikinsu da shi da dan'uwansa, kuma shi ne karami yana da hakkin soyayya da akan nuna wa yara. Amma da yake 'yanuwansa mujrimai ne sai wannan ya sanya haushi ya rike su suka nemi kashe Annabin Allah su huta saboda soyayyar da yake da ita ta musamman wajan Annabin Allah Ya'akub (A.S), Sannan suka zo suka yi karya da kyarkeci don cimma mugun kaidinsu. Wannan mun kawo shi ne domin kare Annabi Ya'akub (A.S) da barrantar da shi daga zunubi ko laifi da wasu suke jinginawa gareshi.
Kyautata sunan 'ya'ya da sanya musu sunan Annabawa da wasiyyansu; kamar Muhammad da Ibrahim da Ali, ko kuma sunan da aka danganta zuwa ga Allah kamar Abdullahi da AbdurRahman, ko sunan salihan bayi kamar Fadima da Maryam da Khadija ko Lukman. Haka nan tarbiyyar 'ya'ya tana daga wajibi na farko a kan iyaye kamar yadda ya zo a Hadisai.

Hakkokin Dan'uwa A Kan Dan'uwansa Da farko muna iya cewa musulmi duka 'yan'uwan musulmi ne saboda haka hakkin da yake hawa kan dan'uwa yana hawa tsakaninsu amma dan'uwa na jini yana da kari kan dan'uwa na musulunci da kamar wajabcin sadar da zumuncinsa. Daga cikin hakkokin dan'uwa a kan dan'uwansa su ne: Yi masa nasiha da kare shi daga wahalhalun da zaka iya taimaka masa wajan maganinsu kamar taimakonsa wajan sana'a, da samun magani, da kudin makaranta, da biyan bukatunsa, da kokarin kawar masa da talauci, da taimakonsa a kan makiyinsa.
Malam Muzaffar a Littafinsa yana cewa: Daga cikin mafi girma da kyawun abin da Musulunci ya yi kira zuwa gareshi shi ne 'yan'uwantaka tsakanin musulmi a kan duk sassabawarsu da martabobinsu da mukamansu. Kamar yadda mafi munin abin da musulmi suka yi a yau da kuma kafin yau shi ne, sakacinsu wajan riko da wannan 'yan'uwantaka ta musulunci.
Domin mafi karancin koyarwar wannan 'yanuwatakar ita ce "Ya so wa dan'uwansa musulmi abin da yake so wa kansa, kuma ya ki masa abin da yake ki wa kansa, kamar yadda zai zo a hadisin Imam Sadik (A.S).
Ka duba ka yi tunani a kan wannan dabi'a mai sauki a mahangar Ahlul Baiti (A.S), za ka samu cewa yana daga mafi wahalar abin da zaka iya samu wajan musulmi, da musulmi zasu yi wa kansu adalci su san addininsu sani na hakika, su yi riko da wannan dabi'a ta so wa dayansu dan'uwansa abin da yake so wa kansa, da ba a ga zalunci daga wani ba ko ketare iyaka, ko sata, ko karya, ko yi da wani, ko annamimanci, ko zargi da mummuna, ko suka da karya, ko wulakanci, ko girman kai.
Idan da musulmi sun tsaya sun fahimci mafi karancin ma'anar hakkin 'yan'uwantaka a tsakaninsu kuma suka yi aiki da ita, da zalunci da ketare iyaka sun kau daga bayan kasa, kuma da ka ga 'yan Adam sun zama 'yan'uwa suna masu haduwa da juna cikin farin ciki, kuma da mafi daukakar sa'adar zamantakewa ta cika garesu, kuma da mafarkin malaman falsafa na da na samar da mafificiyar hukuma ya tabbata, da sun kasance masu musayar soyayya a tsakaninsu, da ba su bukaci wasu hukumomi da kotuna ba, ko 'yan sanda, ko kurkuku, ko dokokin laifuffuka, da dokokin haddi da kisasi ba, kuma da ba su rusuna wa 'yan mulkin mallaka ba, kuma da dawagitai ba su bautar da su ba, kuma da kasa ta canja ta zama aljannar ni'ima kuma gidan sa'ada.
Bugu da karin cewa, da dokokin soyayya sun jagoranci rayuwar 'yan Adam kamar yadda Addini yake so na koyarwar 'yan'uwantaka, to da kalmar neman adalci ta bace daga harsunanmu da ma'anar cewa, ba za mu zamanto muna bukatar adalci da dokokinsa ba ballantana har mu bukaci amfani da kalmarsa, saboda dokokin soyayya sun isar mana wajen yada alheri, da aminci, da sa'ada, da murna, domin mutum ba zai bukaci amfani da adalci ko dokoki ba, sai idan ya rasa soyayya daga wanda ya wajaba ya yi masa adalci, amma a wajan wanda yake nuna masa kauna da soyayya, kamar da, da dan'uwa, sai dai ya kyautata musu ya hakura da dama daga abubuwan da yake so, duk wannan sakamakon so da kauna ne daga yardar zuciya, ba don adalci ko masalahar kansa ba.
Sirrin haka kuwa shi ne cewa mutum ba ya so sai kansa da kuma binda ya dace da kansa, kuma mustahili ne ya so wani abu ko wani mutum da yake wajen ransa, sai dai idan yana da alaka da shi, kuma ya shiga ransa. Kamar kuma yadda yake mustahili ne ya sadaukar da zabin kansa gareshi a cikin abin da yake so yake kuma kauna saboda wani mutum da ba ya sonsa, ba ya kuma kaunarsa, sai dai idan yana da wani imani mai karfi da ya fi karfin son ransa, kamar imani da kyawun adalci da kyautatawa, a yayin nan yana iya sadaukar da dayan abubuwan da yake so, ya yi fansa da shi saboda son wani.
Farkon madaukakan darajoji da suka wajaba musulmi ya siffantu da su, su ne; ya kasance yana jin hakkin 'yan'uwantaka ga sauran mutane, idan kuwa ya kasa wannan, to zai gaza aikata mafi yawa da haka saboda galabar son ransa, saboda haka yana wajaba a kansa ya cusa wa kansa akidar son adalci, da kyautata biyayya ga shiryarwar musulunci, idan kuwa ya gaza hakan to bai cancanci ya zama musulmi ba sai dai a suna, kuma ya fita daga soyayyar Allah (S.W.T), kuma Allah ba ya da wani buri a kansa kamar yadda zai zo a hadisi mai zuwa.
Saudayawa sha'awar mutum takan yi galaba a kansa, sai ya zamanto mafi wahalar abin da yake fama da shi, shi ne, ransa ta yarda da adalci, balle kuma ya samu imani cikakke da ya fi karfin sha'awarsa.
Saboda haka ne ma kiyaye hakkin 'yan'uwantaka ya zama daga mafi wahalar koyarwar addini idan babu imani na gaskiya game da 'yan'uwantaka. Don haka ne imam Abu Abdullah (A.S) ya ji tsoron yi wa sahabinsa "Almu'ula Bn Khunais" bayanin tambayarsa game da hakkin 'yan'uwantaka sama da abin da ya kamata ya bayyana masa, domin tsoron kada ya koyi a bin da ba zai iya aiki da shi ba.
Sai Mu'ula ya ce[52]: Menene hakkin musulmi a kan musulmi?
Sai Abu Abdullahi ya ce: yana da hakkoki bakwai wajibai, babu wani hakki daga cikinsu sai ya wajaba a kansa, idan ya tozarta daya daga ciki to ya fita daga soyayyar Allah da biyayyarsa, kuma Allah ba shi da wani buri a gareshi.
Sai na ce masa: A sanya ni fansa gareka! Mecece?
Sai ya ce: Ya Mu'ula ni ina mai tausasa wa gareka, ina tsoron ka tozarta ba zaka kiyaye ba, ko kuma ka sani ba za ka aikata ba.
Na ce: Babu karfi sai da Allah.
Yayin nan sai Imam (A.S) ya ambaci hakkoki bakwai, bayan ya fada game da na farkonsu cewa: "Mafi saukin hakki daga cikinsu shi ne ka so wa dan'uwanka kamar yadda kake so wa kanka, ka kuma ki masa abin da kake ki wa kanka".
SubhanalLahi! Wannan shi ne hakki mai kankanta, to yaya wannan hakkin mafi kankanta yake a garemu yau mu musulmi? Kaicon fuskokin da suke da'awar musulunci amma ba sa aiki da mafi kankantar abin da ya wajaba na daga hakkokinsa. Abu mafi ban mamaki kuma shi ne, a dangata wannan rashin ci gaban da ya samu musulmi ga musulunci, alhalin laifi ba na kowa ba ne sai na wadanda suke kiran kansu musulmi amma ba sa yin aiki da mafi karancin abin da ya wajabta musu da su yi aiki da shi na koyarwar addininsu.
Domin tarihi kawai, kuma don mu san kawukanmu da takaitawarta zamu ambaci wadannan hakkoki bakwai wadanda Imam (A.S) ya bayyana su:
l- Ka so wa dan'uwanka musulmi abin da kake so wa kanka, kuma ka ki masa abin da kake ki wa kanka.
2- Ka nisanci fushinsa, ka bi yardarsa, kuma ka bi umarninsa.
3- Ka taimake shi da kanka, da dukiyarka, da harshenka, da hannunka, da kafarka.
4- Ka zamanto idonsa, dan jagoransa, kuma madubinsa.
5- Kada ka koshi, shi kuma yana cikin yunwace, kada ka kashe kishirwarka shi kuma yana jin kishirwa, kada ka zama a suturce shi yana tsirara.
6- In kana da mai hidima shi kuma dan'uwanka ba shi da mai hidima, to wajibi ne ka tura mai hidimarka, sai ya wanke masa kaya, ya dafa masa abinci, ya gyara masa shimfida.
7- Ka kubutar da rantsuwarsa, ka amsa kiransa, ka gaishe da maras lafiyarsa, kuma ka halarci jana'izarsa. Idan kuwa ka san yana da wata bukata sai ka yi gaggawar biya masa ita, kada ka bari har sai ya tambaye ka, sai dai ka gaggauta masa.
Sannan ya rufe maganarsa da cewa: "Idan ka aikata haka to ka hada soyayyarka da soyayyarsa, kuma soyayyarsa da soyayyarka".
Akwai hadisai da yawa da suka kunshi ma'anar da ta zo a wannan hadisi daga imamanmu (A.S), wasunsu daga littafin Wasa'il a babobi daban-daban.
Tayiwu wasu su yi tsammanin cewa abin nufi da 'yanuwantaka a hadisin Ahlul Baiti (A.S) ya kebanci tsakanin musulmi ne wadanda suke daga mabiyansu a kebance, amma komawa ga ruwayoyinsu yana kawar da wannan zato, koda yake sun kasance ta wani bangare suna tsananta musantawa ga wanda ya sabawa tafarkinsu kuma ba ya riko da shiriyarsu. Ya wadatar ka karanta hadisin Mu'awiya Dan Wahab da ya ce[53]:
Na ce masa[54]: Yaya ya kamata gare mu mu yi tsakaninmu da mutanenmu, da kuma wadanda muke cudanya da su na daga mutane wadanda ba sa kan al'amarinmu".
Sai Ya ce: "Ku duba Imamanku wadanda kuke koyi da su ku yi yadda suke yi, na rantse da Allah! su suna gaishe da maras lafiyarsu, suna halartar jana'izarsu, suna ba da shaida garesu da kuma a kansu, kuma suna bayar da amana garesu".
Amma 'yan'uwantakar da Imamai suke son ta daga mabiyansu, tana saman wannan 'yan'uwantaka ta musulunci, Kuma ya isar ka karanta wannan muhawara tsakanin Abana Bn Taglib da Imam Sadik (A.S) daga hadisin[55] da Abana ya rawaito da kansa yana mai cewa: Na kasance ina dawafi tare da Abi Abdullah (A.S) sai wani mutumi daga cikin mutanenmu ya bujuro mini wanda ya riga ya tambaye ni in raka shi wata biyan bukatarsa, sai ya yi mini ishara, sai Abu Abdullahi (A.S) ya gan mu.
Sai ya ce: Ya Abana kai wannan yake nema?
Na ce: Na'am.
Ya ce: Shin yana kan abin da kake kai?
Na ce: Na'am.
Ya ce: Maza ka tafi zuwa gare shi ka yanke dawafin.
Na ce: Koda ya kasance dawafin wajibi?
Ya ce: Na'am.
Abana ya ce: Sai na tafi, bayan nan -wani lokaci- sai na shiga wajansa (A.S) na tambaye shi game da hakkin mumini. Sai ya ce: Bari kada ka kawo wannan! Ban gushe ba ina sake tambaya har sai da ya ce: Ya Abana ka raba masa rabin dukiyarka, sannan sai ya kalle ni ya ga abin da ya shige ni, sai ya ce: Ya Abana ashe ba ka san Allah ya riga ya ambaci masu fifita wasu a kan kansu ba?
Na ce: Haka ne!
Ya ce: "Idan ka ba shi rabin dukiyarka ba ka fifita shi ba, kana fifita shi ne kawai idan ka ba shi daya rabin!
Na ce[56]: hakika a yanayinmu mai ban kunya bai dace ba mu kira kanmu muminai na hakika. Mu muna wani waje ne, koyarwar Imamanmu (A.S) tana wani wajen. Kuma abin da ya Shigi zuciyar Abana zai Shigi zuciyar duk mai karanta wannan hadisin, sai dai ya juya fuskarsa kawai yana mai mantar da kansa shi kamar wani ake wa magana ba shi ba, kuma ba ya yi wa kansa hisabi irin na mutumin da yake abin tambaya.


3
HAKKOKI A MUSULUNCI Hakkokin Kawukanmu A Kanmu Kawukanmu da gabobinmu suna da nasu hakki a kanmu[57] saboda haka haramun ne mu cutar da kanmu cutarwa ta Lahira kamar mu yi sabo da su wanda zai jawo musu azaba, haka ma cutarwa ta Duniya kamar kin cin abinci da shan ruwa, da kin shiga inuwa, da shan guba. Don haka ne ma wasu malamai suka haramta shan taba don tana cutarwa. Kodayake malamanmu suna cewa: Ba ta zama haramun da farko amma in ta kai matsayin in mutum ya sha tana cutar da shi to a nan ta zama masa haramun[58].
Mafi munin zaluntar kai shi ne hana kai sanin Allah da manzanninsa da Ilimin aikace-aikace da suka shafi Sanin Duniya da Lahira na dan Adam, idan mutum bai san Allah ba sai ya kamanta shi da halittu sai ya bauta wa Allah (S.W.T) yana mai shirka da shi.
Masu hikima suna cewa: Sanin kawukanmu ya dogara kan amsar wadannan tambayoyi ne kamar haka: Ni wanene? Daga ina nake? A ina nake yanzu? Kuma Ina za ni?.
Rayinmu tana bukatar irin nata abincin da abin shan kamar yadda jiki yake bukata, mafi dadi a ciki shi ne sanin Allah da ganawa da shi ta hanyar addu'o'i da sauran ibadoji, amma babban asasi shi ne saninsa da farko, domin in ba sanisa yaya za a gana da shi?[59] Rashin sani ko wane iri ne yana daidai da sanya rai a kurkuku ne.
Haka nan ba ya halatta ga mutum ya halakar da ransa ta kowace hanya, kamar ta hanyar ganganci da mota ko babur da kowane irin abin hawa da zai iya kaiwa ga cutar da jiki, ko kin shan magani ga maras lafiya.
Haka nan ji da gani, da hannu, da ciki, da kafa, da farjinmu, duk suna da hakki a kanmu na kada mu yi sabo da su, kuma mu nemi Duniya da Lahira da su, kuma mu nemi Ilimi da su ta hanyar gani, da ji, da tafiya wajan neman Ilimi ko neman halal, haka nan kada mu taba haram ko daukarta ko kallonta da su. Wani lokaci ana zaluntar kai ne da zaman banza har ma kana iya ganin mutum ya shantake yana ta barci wai hutawa yake yi saboda lalacewa alhali bai yi aikin komai ba. Wani kuwa yana alfahari ne da cewa babansa yana da dukiya mai yawa, sai ya zalunci kansa ba zai je ya nemi abin da zai mutunta kansa ba.

Hakkin Kiyaye Harshenmu Ya zo a ruwayoyi cewa harshe mai dadi da kalma ta alheri sadaka ne[60], kuma ya zama wajibi a kare shi daga maganganu na karya, da hada husuma, da giba, da annamimanci. Kalma mai dadi da harshe mai hada sulhu tsakanin mutane[61] shi ne wanda Allah ya ke so. An karfafa yin hakan musamman tsakanin ma'aurata da abokan zamantakewa a matsayin al'umma.
Wani lokaci a kan samu wasu mata suna gaya wa mazajensu "Me ka taba yi mini" wato duk alherinsa maimakon godiya sai su kushe. Haka nan wasu matan idan suna magana da mazajensu kamar suna magana da wani azzalumi babu wata kalma ko magana mai dadi. Haka nan ta bangaren mazaje akwai irin wadannan mutane masu jahiltar rayuwa da manufa da hadafin yin aurensu.
Harshe ya fi komai hadari, saudayawa masu kin kasashen musulmi da masu ganin hada husuma tsakanin musulmi da 'yan'uwansu na zaman kasa daya sukan yi amfani da harshe da yada jita-jita don ganin sun kawo husuma da yaki. Kuma saudayawa irin wannan ya faru a kasashenmu da biranenmu kuma ya jawo kashe dubunnan mutane! mu sani babu wani abu da ya fi harshe santsi da hadari don haka sai a kiyaye shi.

Hakkin Kiyaye Jinmu Ya wajaba a kiyaye ji daga sauraron haram da jita-jita musamman ga mai maganar da an san ba ta da tushe, da yawa mutanen da aka saurare su maganarsu ta zama bala'i ga al'umma da kuma ga mai sauraron. Haka nan ana son sauraron magana mai amfani kamar ta Ilimi da sauraron karatun Kur'ani (musamman ga mai ciki), kuma mai magana da kai yana da hakkin ka saurare shi idan ya gama maganarsa sai ka yi taka.

Hakkin Kiyaye Ganinmu Ya wajaba a kiyaye gani daga haram[62] musamman kallon namiji ga mace, Musulunci ya hana kallo mai tayar da sha'awa ko kuma da nufin tayar da sha'awa, kamar yadda ya hana kallon jikin mace ajnabiyya in banda fuska da tafuka koda ba tare da nufin sha'awa ba. Haka nan yana hana mace kallon abin da maza bisa al'ada sukan rufe shi na daga jikinsu, amma in ba haka ba, ba ya zama haramun. Amma idan ya zama a matsayi na dole kamar a matsayi na magani da ba wani mai iyawa sai ajnabi to a bisa lalura ya halatta idan zai yiwu ta madubi ko ruwa, idan ba zai yiwu ba to a lokacin yana halatta da idanu[63].
Haka nan akwai abubuwan da ya halatta da wanda bai halatta ba a gani a telebijin da satalayet da bidiyo da hoto kamar tsaraici. Haka nan yana da kyau ga iyaye su kayyade wa yara lokacin kallonsu domin yakan hana su karatu, a wannan kwanaki an samu lissafi mai yawa a kasashen Yammacin duniya na kallon telebijin da ya sanya karatun yara ya yi rauni sosai.

Hakkin Yin Aiki Ga Dukkan Musulmi 1-Shari'ar Musulunci tana daukar yin aiki don samun biyan bukatun rayuwa ga mutum ko ga wanda daukar dawainiyarsa ta zama dole a kansa a matsayin wajibi, kuma ta wajabta wa wanda ake bi bashi kuma yake da ikon yin aiki da ya yi aiki don biyan bashin da yake kansa.
2-Haka nan Shari'ar Musulunci tana daukar yin aiki don yalwatawa cikin ciyarwa, samar da jin dadin rayuwa, da ayyukan alheri, a matsayin mustahabbi da take kwadaitar da mutum a kan yin su.
3-Shari'ar Musulunci ta haramta yin ayyukan da aka haramta, kamar sana'anta giya, miyagun kwayoyi, raye-raye, zina, caca, riba, da wasun wadannan, kamar yadda ta haramta duk wani aiki da yake jagora zuwa aikata haram ko da kuwa shi a kansa halal ne.
4-Shari'ar tana daukar wasu ayyuka a matsayin makaruhai a kashin kansu ko saboda wani abu daban, kamar sayar da likkafani.
5-Asalin da shari'ar musulunci take tabbatarwa game da aiki shi ne halacci, don haka yin aiki don tara dukiya ko kara kudi wani al'amari ne na halal matukar yana gudana a kan hanyar da shari'a ta halatta.
Yayin nazari da bin diddigin ma'anonin ayoyi da nassosi, a cikinsu ba zamu sami abin da ya hana mace yin aiki ba, ko ya kebe halaccin haka ga namiji, duk kuwa da cewa kwadaitar da namiji a kan aiki ya zo a cikin wasu nassosi.

Hakkin Yin Aiki Ga Matar Aure Shari'ar Musulunci ta tanadi wasu hukunce-hukunce da suka kebanci aikin matar aure kamar haka:­
1-Yana daga hakkin mace ta shardanta wa miji cewa ba zai hana ta yin aiki ba a lokacin daura aure.
2-Miji ya amince a kan aikin matarsa ta hanyar fahimtar juna tsakaninsu, wannan kuwa idan ta so yin aiki ba tare da wani sharadi da ya gabata ba kenan. Idan kuwa miji ya ki amincewa da matarsa ta yi aiki a irin wannan hali, ba yana nufin cewa shari'ar musulunci ce ta hana mace aiki ba.
3-Idan mace ta yi aure alhali ta riga ta yi yarjejeniyar aiki na wani ayyanannen lokaci da wasu to yarjejeniyar aikin ba ta baci ba koda kuwa ya sabawa hakkin miji.
4-Idan matar aure ta kulla yarjejeniyar aiki ba tare da izinin mijinta ba to ingancin wannan yarjejeniya ta dogara ne a kan yardar mijin idan aikin ya sabawa hakkokinsa, idan kuwa bai saba wa hakkokinsa ba, to yarjejeniyar tana zartuwa.
5-Hukuncin duk wata yarjejeniyar aiki da mace ta kulla tana gudana ta hanyar nazarin hukunce-hukuncen shari'a, ba zamu taba samun wani nassi da yake haramta yin aiki ga mace ba.
Masu haramta aikin mace suna bayar da dalili ne da kasancewarsa a wajen gida wanda fita yana bukatar izinin mijinta, wasu kuwa ba su amince da aikin mace cikin ma'aikatun da ake cakuda maza da mata ba saboda hakan yana haifar da fasadi da fadawa cikin abubuwan da aka haramta.
A nan ya kamata mu yi nuni da cewa aikin da yake haifar da aukawa cikin haram, haram ne ga dukkan jinsosin biyu namiji da mace, don haka matsayi na iya tilasta hana cudanyar da kuma kokarin sanya aiki a hannun jinsin namiji ko mace kamar yadda nau'in aikin yake bukata, ko samar da yanayin da zai hana kai wa ga haram. Sannan mu sani aikata haram ba ya kebanta da yin aiki idan masu aikata haram sun kasance fasikai ne.
Sa'annan ta hanyar wannan aya: "Kuma muka daukaka darajojin sashensu a kan wani sashe don wani sashen ya riki wani mai yi masa hidima.."[64]. muna iya gani cewa; bamabancin iyawa, kwarewa, da karfin aiki, yana sabawa daga wani mutum zuwa wani ba tare da la'akari da kasancewarsa namiji ko mace ba, kuma alkar musayar amfanoni da biyan bukatun rayuwa da hidima suna cika ne tsakanin daidaikun al'umma baki daya. Kuma kowane daya ba tare da la'akari da jinsinsa (namiji ko mace) ba, yana yin kokarinsa da abin da zai iya wajen biyan bukatun al'umma wanda da haka ne shi ma zai sami tashi biyan bukatar. Manomi yana gabatar da kayan noma, injiniya da masanin fanni suna sana'anta na'ura, likita yana bayar da magani, malami yana yin aikinsa na karantar da manyan gobe, dan kasuwa na samar da kayayyakin masarufi a kasuwa, soja yana kare kasa, mai gadi yana maganin barayi, da sauransu.
Darasi da nazarin hukunce-hukuncen Musulunci dukkansu zasu tabbatar mana da cewa musulunci bai haramta wani nau'i na aiki ko ilimi ga mace ba bayan ya halatta shi ga namiji, mace tana iya yin kowane irin aiki kamar noma, sana'a, likitanci, injiniyanci, gudanarwa, ayyukan siyasa, tela, tukin jirgin sama, da sauransu.
A Musulunci babu wani aiki na samar da wani abu ko hidima da aka halatta ga namiji amma aka haramta shi ga mace, kowa a shari'ar Musulunci daya ne. A kan haka bambancin kawai da yake tsakanin namiji da mace a wasu wajibai ne da aka kallafa wa namiji ko mace, ko wasu maslahohi da suka ginu a kan asasin ilimi da aka yi la'akari da yanayin halittar gabobi ga kowannensu, da kuma wajibcin tsara rayuwar zamantakewa da gudanar da ita.
Asali a shari'ar Musulunci shi ne halaccin aiki, ko wajibcinsa a wasu halaye, in banda abin da shari'a ta haramta, ko abin da yake haifar da fadawa cikin abin da aka haramta. Idan kuwa har akwai wani ra'ayin haramta aiki ga mace daga wajen wasu, to wannan yana bukatar dalili. A tsarin musulunci da abin da ya dora shi a kan musulmi na wajibai aini[65], ko kifa'i[66], ya wajabta su ne a kan maza da mata ba tare da iyakance jinsinsu ba, ya wajabta musu samar da bukatun al'umma gaba daya kamar likitanci, injiniyanci, karantarwa, noma, kasuwanci, sufuri, tsaro da sauransu na daga ayyukan da al'umma suke bukata. Kuma wajibin kifa'i yana iya sauyawa ya zama wajibi Aini a kan mutanen da ikon aiwatar da wannan wajibi ya kebanta da su ba tare da la'akari da jinsin namiji ko mace ba. Sai dai wani lokaci shari'a tana fuskantar da wajabci ga wani jinsi idan aikin ya shafe shi ne kamar aikin likita da ya kebanci haihuwa (unguwar zoma) da al'amuran da suka shafi mata.

Hakkin Harkokin Siyasa Ga Mace Daga cikin al'amura na asasi da aka sanya a teburin tattaunawa da muhawara na tunani da wayewa a karni na ishirin akwai al'amarin hakkokin mace, daga ciki kuwa har da shigarta cikin harkokin siyasa, abin da yake bayar da mamaki shi ne, cewa wadannan masu kira ga hakkokin mace na siyasa suna fuskantar da tuhumarsu ga tunanin musulunci da akidunsa, suna siffanta su da cewa akidu ne da suka haramta wa mace shiga cikin rayuwar siyasa, kuma suke hana ta aiwatar da ayyukan siyasa. Suna dogara da yanayin zamantakewa da siyasa wadanda suke gani a garuruwan musulmi ba tare da sun tantance musulunci a matsayinsa na tsarin shari'a da dokoki ba, da kuma masu bin musulunci da suka cakuda shi da al'adunsu a a siyasa da zamantakewa[67] ba.
Sun dauka abin da suke gani a kasashen musulmi shi ne ainihin musulunci alhalin ya saba wa yadda ya kamata ya kasance cikin al'ummar musulmi. Domin mace a wadannan kasashe na musulmi da yadda ake yin mu'amala da ita da kimarta a cikin al'ummar musulmi duk sun doru bisa al'adu ne a zamantakewa, da fagagen aiki, da siyasa, da alakarta tare da namiji.
A musulunci siyasa tana nufin lura da sha'anonin al'umma a dukkan fagagensu na rayuwa da jagorancin tafiyar da su ta hanyar Musulunci. Don haka ita wani nauyi ne na zamantakewa da aka dora wa musulmi baki daya, wannan nauyi an dora shi a kan dukkan musulmi ba tare da la'akari da kasancewarsu maza ko mata ba.
Misalin fadinsa Madaukaki: ­"… ku tsayar da Addini kuma kada ku rarraba". Surar Shura, 42:13. Da fadinsa Madaukaki:­ "Allah kuma ya yi wa wadanda suka bayar da gaskiya daga cikinku kuma suka yi aiki na gari alkawarin lallai zai sanya su masu mayewa a bayan kasa, kamar yadda ya sanya wadanda suka gabace su masu mayewa..." Surar Nuri, 24:55. Da fadinsa Madaukaki: ­"Ku bi Allah kuma ku bi Manzonsa kuma da majibanta al'amuranku (Imamai Ma'asumai)" Surar Nisa'i, 3:59.
Cikin dukkan wadannan ayoyin ana magana ne ga dukkan musulmi maza da mata, ashe kenan tsayar da Addini da Akidunsa da dukkan tsare-tsarensa na siyasa, zamantakewa, ibada da sauransu, nauyi ne a kan dukkan Musulmi, haka nan umarnin yin biyayya ga majibanta al'amura da ya zo a cikin wannan aya ya doru a kan dukkan baligai, kuma alkawarin mayewa ana fuskantar da shi ne ga dukkan wadanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka na gari maza da mata.
Fadinsa Madaukaki:­"Ya kai Annabi idan muminai mata suka zo maka suna mubaya'a gareka a kan ba zasu hada wani da Allah ba, ba zasu yi sata ba, ba za su yi zina ba, ba zasu kashe `ya'yansu ba, ba zasu zo da wata karya wadda zasu kage ta tsakanin hannayensu da kafafuwansu ba, kuma ba za su saba maka cikin wani kyakkyawa ba, to ka yi mubaya'a da su, kuma ka nema musu gafarar Allah, hakika Allah Mai yawan gafara ne Mai jinkai". Surar Mumtahannati, 60:12.
Wannan wani abu ne da ya faru a aikace, kuma dalili ne na Kur'ani da Manzon Allah (S.A.W) ya aikata shi cikin rayuwarsa ta isar da sako da siyasa game da karbar bai'ar mace, kuma mubaya'a a wannan aya tana nufin biyayya ga majibancin al'amari a kan lizimtar hukunce-hukuncen shari'a da dokokinta, da ikrari da shugabancinsa. Mubaya'a kuwa ita ce mafi girman hakkokin siyasa a cikin al'umma, kuma wannan dalili ne a kan gudummawar mace ta siyasa da hakkokinta na siyasa a Musulunci.
AyatulLahi Shahid Sayyid Bakir Sadar (R.A) ya kafa dalili da wannan aya a kan cewa mumini da mumina sun cancanci shugabancin siyasa, da cewa namiji da mace a kan wannan daya ne. Ya zo cikin nassin abin da ya fada cewa: "AI'umma tana taka rawarta wajen halifanci a tsayar da shari'a, da dalilin ka'idoji biyu na Kur'ani masu zuwa: "AI'amuransu shawara ne tsakaninsu" Surar shura: 38. da ayar "Muminai maza da muminai mata kuwa, majibanta al'amarin juna ne, suna umurni da aikata alheri kuma suna hani daga mummunan aiki...' Surar Tauba: 71.
Nassi na farko yana ba wa al'umma damar aiwatar da al'amuranta ta hanyar shawara ne matukar wani nassi na musamman bai zo da abin da ya saba da haka ba.
Nassi na biyu kuwa yana magana ne a kan jibintar al'amari da cewa kowane mumini majibancin al'amarin saura ne, saboda dalilin horo da aikin alheri da hani da mummuna da ya biyo baya. Wannan nassi dalili ne na zahiri a kan gudanar wannan jibantar al'amari tsakanin dukkan muminai maza da muminai mata daidai wa daida.
Daga nan za a iya fitar da ka'idar shawara da bin ra'ayin mafi yawa a yayin sabani." Musulma ta shiga fagen siyasa a zamanin Manzon Allah (S.A.W) kamar yadda ayar bai'a ta tabbatar da haka, sun shiga fagen siyasa sun kuma yi tarayya a rayuwar siyasa.
Haka nan mace Musulma ta shiga kuma ta bayyana ra'ayinta game da jagorancin siyasa da halifanci bayan rasuwar Manzon Allah (S.A.W), mafi girman dalili a kan haka shi ne matsayin Fadimatu 'yar Manzon Allah Muhammadu (S.A.W) kuma matar Imam Aliyyu dan Abi Dalibi (A.S) wacce ta shiga fagen siyasa bayan rasuwar mahaifinta, ta kasance a gefen Aliyyu cikin harkokinta da matsayinta na siyasa har wasu taron mutane daga Muhajirai da Ansar suka hadu tare da ita. Wannan ne ma ya samar da bangaren siyasa mai hamayya da bai'ar Halifa na farko ta Sakifa, kuma mai kira zuwa ga sake yin mubaya'a ga Imam Ali (A.S).
Ta kasance tana ganawa da Ansar (mutanen Madina) a gidajensu tana neman su da su yi mubaya'a ga Imam Ali (A.S), tana mai hamayya da bai'ar Sakifa. Ya zo a cikin tarihi cewa; Sai Aliyyu ya fita yana dauke da Fadima 'yar Manzon Allah (S.A.W) a kan dabba da daddare zuwa Ansar tana neman taimakonsu, su kuwa sun kasance suna cewa: Ya 'yar Manzon Allah hakika bai'armu ta gudana a kan wannan mutum, da mijinki kuma dan baffanki ya riga zuwa wurinmu kafin Abubakar da ba mu kauce daga gare shi ba.
Haka nan tarihi ya rubuta muhawarori da matsayin siyasa na hamayya da ya gudana tsakanin Fadima da halifa Abubakar da Umar Dan Khaddabi.
A musulunci fagen siyasa fage ne mai fadi da ya hada da horo da kyakkyawan aiki da hani daga mummunan aiki wadanda suka kunshi kira zuwa tsayar da tsarin musulunci, da kalubalantar azzaluman shugabanni, da karkatattun tsare-tsare na zalunci, kamar yadda suka kunshi shiga cikin gudanar da shugabanci, da tsarin siyasar al'umma, wayar da kan mutane a fagen siyasa, shawara da mubaya'a kamar zaben shugaba da wakilan al'umma, shiga cikin wakilcin al'umma a majalisu da muke kira da 'majalisun wakilai, wadanda suke aikin horo da kyakkyawa da hani daga mummuna ta fuskar siyasa.
Wannan yana nufin wajibcin shigar mace yadda ya kamata cikin jama'a da ayyukan siyasa, da kungiyoyi, da jam'iyyu, da cibiyoyin tunani, da kawo gyara, matukar aiwatar da wajibai kamar yadda ake bukata ya ta'azzara.
Daga wadannan asasai na Kur'ani zamu fahimci cewa rayuwar siyasa a musulunci a bude take ga mace kamar yadda take bude ga namiji a dukkan matsayinsu na wajibi Aini da Kifa'i, ko halaccin shiga cikin rayuwar siyasa da dukkanin al'amura na zamantakewar al'umma.
Godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai

Masdarorin Madogarar Wannan Littafin: Kur'ani mai girma
Sharhu risalatil hukuk
Tauhid, saduk
Al'intisar, amuli
Ma'asatuz Zahara, murtadha amuli
Alwilayatut takwiniyya alhakkud dabi'I lilma'asum, jalal sager
Nahajul balaga
Aka'idul imamiyya
Usulul kafi
Biharul anwar, Allama majlisi
Hudubar imam khomaini 15 sha'aban 1400
Mikyalul makarim, Muhammad taki al'asfahani
Namazijun min karamatil ayimma wa mu'ujizatihim, markazul musdapha
Ruzgare rahayi
Ba'adhu ma warada min siratil imam Hasan Askari (A.S)
Murkazul musdapha, min zulamatihim fi a'hdi banil Abbas
Asshabus sawakib, Muhammad Ali Abduljabbar
Nahajul imani, Ibn hajar
Masharikul yakin
Assiradul mustakim
Misbahul mutahajjid, shaikh Dusi
Minhajul karama, allama hilli
Muhadharatun fil ilahiyyat, bahasu fi as'ilatin haulal mahadi, subhani
Sharhu ihkakul hakk, mar'ashi najafi
Salim bn Kais
Sharhu Risalatil hukuk
Muniyyatus sa'il, almasa'ilul mutafarrika, sayyid Khu'I
Siradun najat, Mirza Jawad tabrizi
Masharikul anwaril yakin
Markazul musdapha, minal a'amalil lati tujibul janna wannari
Raudhatul wa'izin, al'fitalin naisaburi
Masnad Ahmad bn Hambal
Al'baharur ra'ik, ibn Najimul misri
Takmilatu hashiyati raddil mukhtar, Ibn Abidin (Ala'ud din)
Almabsud, shaikh Dusi
Al'mu'utabar, muhakkikul hilli
Al'wasa'il
Munyatut dalib, na'ini
Wilayatul fakih, musdapha khomaini
Nahajul balaga, ibn abil hadid
Tazkiratul fukaha', allama hilli
Fikihus Sunna, sayyid sabik
Al'majmu'u, nawawi
Sharhin akhbar, alkali Nu'uman almagribi
Al'amali, Shaikh Dusi
Raushatul wa'izin, al'fitalun naishaburi
Zubdatul bayan, muhakkikul ardabili
Al'hada'ikun nadhira, baharani
Kitabul hajj, sayyid Khu'I
Tafsirul kur'anil karim, sayyid musdapha
Samarud dani, Azhari
Al'intisar, sharif murtadha
Makatibur rasul, ahmadi miyanji
Markazur risalatil hukukul ijtima'iyya
Tafsirul Ayashi
Kanzul ummal
Hashiyatu majma'ul fawa'id wal burhan, bahbahani
Kitabuddahara, ansari
Jawahirul kalam, jawahiri
Mizanul hikima, Raishahari
Tahrirul wasila, imam khomaini
Raddi Kan Sukan Auren Mace Fiye Da Daya.


4