Sakon Hakkoki

Sakon Hakkoki0%

Sakon Hakkoki Mawallafi:
: Imam Aliyyu Assajjad a.s
: Shekh Hafiz Muhammad Sa'id
Gungu: Litattafan Halaye

  • Farawa
  • Na Baya
  • 11 /
  • Na Gaba
  • Karewa
  •  
  • Gurzawa HTML
  • Gurzawa Word
  • Gurzawa PDF
  • Budawa: 4992 / Gurzawa: 1633
Girma Girma Girma
Sakon Hakkoki

Sakon Hakkoki

Mawallafi:
Hausa

Dukkan hakkokina cibiyar Muassasar alhasanain (a.s) ne, kuma yada rubuce-rubucen tare da ambaton inda aka dauko su ba shi da matsala 2012. Muassasar alhasanain (a.s)

Sakon Hakkoki

Mawallafi: Imam Aliyyu Assajjad (a.s)

Imam Aliyyu Zainul-abidin (a.s)

Tarjamar: Hafiz Muhammad Sa'id

Laburare ›

Halaye Da Addu ›

Litattafan Halaye

Hausa 2011-07-30 08:29:38

Sakon Hakkoki (Risalatul Hukuk) Sakon Hakkoki (Risalatul Hukuk)

Da Sunan Allah Mai Rtahama Mai Jin Kai

Kur'ani Mai Daraja : Kumasama ya daukaka ta, kuma ya sanya sikeli.Kuma ku daidaita awo da adalci, kada ku rage sikelin. Kuma kasa ya sanya ta domin talikai ne.[ 1].

Gabatarwar Mafassari

Kamalar dan Adam wani abu ne mai wahalar isa zuwa gareshi domin hanyoyin suna da surkukiya mai wahalar gaske, saidai akwai ma'aunai da suke nuna cewa mutum yana samun ci gaba. Wadannan ma'aunan suna iya kasancewa na tunani ko na aiki, ta yadda kyawawan halayen mutum su ne suke iya nuna cewa shi salihi ne ko fasidi ba yawan ibadojinsa ba, sau da yawa wani yake bauta amma babu inda take zuwa, imma dai don bai riki imamin zamaninsa ba, ko ya riki masoya Allah makiya, ko halayensa sun munana, don haka a cikin kyawawan halaye ne masu rige zasu yi rige domin kai wa ga kamala.

A cikin littafin alKafi na sheikh Kulaini ya zo daga gareshi daga Usman dan Isa, daga Ishak dan Ammar da waninsu, daga Abu Abdullah Imam Ja'afar Sadik (a.s) ya ce: Kada ku rudu da sallarsu, ko da azuminsu, domin sau da yawa ta yiwu mutum ya riki yin salla da azumi ta yadda da ya bar su sai ya samu jin babu dadi, amma ku jarraba su gun gaskiyar magana, da bayar daamana .

A wata ruwayar Imam Ja'afar Sadik yana cewa ne: Duk wanda harshensa ya gaskata, to aikinsa zaitsarkaka .

Lamarin kiyaye hakkin mutane ya kai ga hatta cikin abin da ya shafi mutum ya haukansa ya kiyaye hakkin mutane a cikinsa. Lamarin ya kai ga manzon Allah (s.a.w)yana la'anar mai cin guzurinsa (a tafiya) shi kadai ya bar sauran mutane.

Jarabawar da take gaban mutum tana da girma da wahala matuka, kuma kowacce ana son ya kiyaye cikinta don ya kasance mutum mai kamala wurin Allah madaukaki. Muna iya duba wannan ruwaya don muga santsin wannan hanya kamar haka:

Daga littafin Ihtijaj na dabarasi, Mansur Ahmad dan Abi dalibAddabrasi , da sanadinsa zuwa Imam Hasan al'Askari (a.s) daga Imam Ridha (a.s) ya ce: Aliyyu dan Husain (a.s) ya ce:

(Yaudara da nuna Salihanci) Idan kuka ga mutum yanayinsa da basirarsa sun kyautata, yana kaikaice maganarsa, da nuna kaskantar da motsinsa, to ku yi a hankali kada ya rude ku, sau da yawa a kan samu wanda samun duniya da hawa kan haram yake yi masa wahala saboda raunin niyyarsa, da wulakantuwarsa da tsoron zuciyarsa, sai ya nuna addini a matsayin tarkonsa, shi ba ya gushewa yana yaudarar mutane da zahirinsa, idan kuma ya samu damar aikata yin haram sai ya fada masa.

(Dukiya da Mata) Idan kuwa kuka same shi yana kamewa daga haram to (har yanzu dai) ku yi a hankali kada ya rude ku, domin lallai sha'awowin halittu suna sassabawa, sau da yawa wani wanda yake nisantar dukiyar haram komai yawanta, (amma) kuma (da zai samu dama, da) ya dora kansa (ya hau) kan wata mummunar mata mai muni (duk muninta) sai ya aikata haram (na zina) tare da ita.

(Samuwar Hankali) Idan kuwa kuka same shi yana kamewa daga wannan (zina) to (har yanzu dai) ku yi hankali da shi kada ya yaudare ku har sai kun duba hankalinsa, sau da yawa wani ya bar wannan duka amma ba shi da wani hankali mai karfi, sai ya kasance abin da yake batawa da jahilcinsa ya fi abin da yake gyarawa da hankalinsa.

(Son Zuciya) Amma idan kuka sami hankalinsa mai karfi ne, to (har yanzu dai ku yi hattara da shi) ku yi hattara dai kada ya yaudare ku har sai kun ga shin yana tare da son ransa a kan (watsi da) hankalinsa, ko kuma yana tare da hankalinsa ne a kan (watsi da) son ransa.

(Son Shugabanci batacce) Sannan yaya sonsa yake ga shugabancina barna da nisantarsa gareshi. Hakika a cikin mutane akwai wanda ya rasa duniya da lahira, yana barin duniya don duniya, yana ganin dadin jagorancin barna ya fi dadin dukiyoyi da ni'imar halal da aka halatta, sai ya bar wannan duka don neman jagoranci har sai idan aka gaya masa cewa ka ji tsoron Allah, sai girman kai ya kwashe shi da barna, to wutar jahannama ta wadatar masa, kuma tir damakoma .

Yana mai gangara kawararo gaba gadi, farkon barna tana jansa zuwa ga mafi nisan matukar tabewa, kuma ubangijinsa yana mai barinsa da kansa bayan nemansa ga abin da ba zai iya masa ba a cikin taurin kansa, shi yana mai halatta abin da Allah ya haramta, yana mai haramta abin da Allah ya halatta, ba ruwansa da abin da ya kubuce masa na addininsa idan dai shugabancin da ya tabe saboda shi ya kubuta, wadannan su ne wadanda Allah ya yi fushi da su ya la'ance su kuma ya tanadar musu da azaba mai wulakanci .

(Mutumin kwarai) Saidai cikakken mutum, madalla da mutumin da yake sanya son ransa kan biyayya ga umarnin Allah madaukaki, kuma karfinsa ya kasance ya bayar da shi cikin yardar Allah, yana ganin kaskanci tare da gaskiya shi ya fi kusanci zuwa ga daukakar har abada a kan daukaka cikin barna.

Kuma ya san cewa mafi karancin abin da zai iya jurewa na cutuwarta (duniya) zai kai shi ga dawwamar ni'ima ne a gidan da ba ya rasuwa ba ya karewa(lahira), kuma mafi yawan abin da yake samun sa na farin cikinta (duniya) idan ya bi son ransa zai kai shi ga azabar da babu yankewa gareshi babu gushewa (a lahira), to wannan mutumin madalla da shi (ya cika) mutum, da shi ne zaku yi riko, kuma ku yi koyi da sunnarsa (aikinsa), kuma ku yi tawassali da shi zuwa ga ubangijinku, domin shi ba a mayar masa da addu'a, kuma ba a hana shi abin da ya nema.

Littafin da yake gabanka mai karatu shi ne Littafin "Sakon Hakkoki"na Imam Aliyyu Zainul-abidin wanda aka san shi da asSajjad, ko "Sayyidus Sajidin". Shi bayani ne mai kima matuka da ya ishi mutun rayuwar duniya gaba daya, wanda da al'umma ta kiyaye shi, da ba a samu sabani tsakanin mutane biyu ba, da duniya ta koma kamar aljanna saboda zaman lafiya, da yalwa da arziki, da kauna da so sun maye gurbin kiyayya da gaba, da sulhu da zaman lafiya sun maye gurbin yaki da kashe-kashe!.

Imam Ali asSajjad shi ne Imamina Hudu cikin jerin wasiyyan annabi (s.a.w) wadanda su ne ruwayoyi suka ambace su da Ahlul-baiti da suka hada sayyida Zahara (s.a) da kuma goma sha biyu tsarkaka da manzon Allah (s.a.w) ya yi umarni da riko da su bayan wafatinsa kamar yadda ya zo a manyan littattafan ruwayoyi na hadisai. Saidai kauce wa wannan wasiyya ta manzon Allah (s.a.w) ya sanya al'umma fadawa cikin rudani da bambance-bambance har zuwa wannan zamanin.

Allah (s.w.t) yana fada cewa: "Kawai Allah yana son ya tafiyar da daud'a daga gareku ne Ahlul-baiti kuma ya tsarkake ku tsarkakewa" .

Wasiyyar manzon Allah (s.a.w) ga al'ummarsa: "Lallai ni mai bar muku nauyayan (alkawura) biyu ne; Littafin Allah da Ahlin gidana, ba zaku taba bata ba bayana har abada matukar kun yi riko da su" .

Hadisai sun yi nuni da su a littattafai daban-daban, kamar yadda Shehu Usman dan Fodio Allah yakara masa yarda ya kawo sunansu a cikin Nasihatu Ahluzzaman a yayin da yake kawo salsalar Imam Mahadi (a.s) wanda zai zo a karshen duniya. Da al'umma ta fuskanci koyarwarsu da ba ta samu kanta cikin wannan faganniya da rudani ba, saidai abin da ya faru ya riga ya wakana.

Domin tubarraki zamu so kawo sunyensu kamar haka: Imam sayyidi Ali (a.s), sai Imam Hasan (a.s), sai Imam Husain (a.s), sai Imam Aliyyu Zainul-abidin (a.s) wanda shiryarwarsa take kunshe cikin wannan littafin, sai Imam Muhammad al'Bakir (a.s), sai Imam Ja'afar asSadik (a.s), sai Imam Musa alKazim (a.s), sai Imam Ali arRidha (a.s), sai Imam Muhammad al'Jawad (a.s), sai Imam Ali al'Hadi (a.s), sai Imam Hasan al'Askari (a.s), sai Imam Muhammad al'Mahadi (a.s).

Da yake ruwayoyi biyu ne, don haka mun kawo su da maimaicin da suka zo da shi a ruwayoyi mabambanta saboda sabanin da yake tsakaninsu, sai dai mun sanya ruwayar da tafi fa'idoji masu yawa, ita kuwa ruwayar da ta fi sanadi mai karfi mun sanya ta a kasa.

Muna rokon Allah ya sanya Imam Khoamain (k.s) cikin ladan wannan rubutun sakamakon yau ta yi daidai da ranar juyayin wafatinsa.

Hafiz Muhammad Sa'id

hfazah@yahoo.com

www.hikima.org

Saturday, June 04, 2011

Imam Aliyyu Zainul-abidin (a.s)

Ali Dan Husain Assajjad (a.s), sunansa da Nasabarsa: Aliyyu dan Husaini dan Ali dan Abi Dalib (a.s). Babarsa;ita ce Shahzinan 'yar Yazdajir dan Shahribar dan Kisra, an ce sunanta Shahri Banu. Alkunyarsa: Abu Muhammad, Abul Hasan, Abul-Husaini, Abul Kasim. Lakabobinsa: Zainul Abidin, Sayyidul-abidin, Assajjad, Zussafanat, Imamul Muminin, Almujtahid, Azzahid, Al'amin, Azzakiyyi. Haihuwarsa: 5 Sha'aban 38 H, a wata ruwaya 15 Jimada Akhir. Matansa:An rawaito cewa ya auri mata bakwai, Ta farko ita ce: Ummu Abdullahi, amma sauran duk Kuyangi ne. 'Ya'yansa: 1-Imam Bakir (a.s) 2-Abdullahi 3-Al-Hasan 4-Al-Husaini 5-Zaid 6-Umar 7-Al-Husainil Asgar 8-Abdurrahman 9-Sulaiman 10-Ali 11-Muhammad Asgar 12-Khadija 13-Fadima 14-Aliyya 15-Ummu Kulsum. Tambarin zobensa: Wama taufiki illa bil-Lahi. Littattafansa: Sahifatus sajjadiyya da Risalatul hukuk. Tsawon rayuwarsa: shekara 57. Tsawon Imamancinsa: Shekara 35. Sarakunan zamaninsa: Mu'awiya da Yazidu dan Mu'awiya, da Mu'awiya dan Yazidu dan Abi Sufyan, da Marwan dan Hakam, da Abdulmalik dan Marwan, da Walid dan Abdulmalik. Tarihin shahadarsa: An yi sabani a kan hakan amma an ce 12 Muharram ko 18 ko 25 ga Muharram, haka nan shekara an ce 94 ko 95 H. Inda ya yi shahada: Madina. Dalilin shahadarsa: Guba da aka ba shi a lokacin halifancin Walid dan Abdulmalik. Kabarinsa: Makabartar Bakiyya Madina.

A cikin tsawon lokacin imamancinsa ya ga rashin imani da kekashewar zuciya mai tsanani daga matsantawar da gwamnatin Umayyawa ta yi masa. Sun saka masa tsaro mai takurawa, kuma sun ajiye masa 'yan leken asiri domin kada ya cigaba da harkar da'awar Musulunci wacce mahaifinsa Imam Husain (a.s) ya ciyar da ita gaba ta hanyar sadaukar da ransa da ya yi a ranar Karbala. Saidai cewa gaba dayan abubuwan da suka aiwatar, da riga kafin Umayyawa a game da Imam Ali dan Husain (a.s) bai iya hana shi ci gaba da harkar da'awar musuluncin ba. Yariga ya dauki wasiyyoyi da kira a matsayin wata hanya ta yada Musulunci da yakar Umayyawa.An tattara da yawa daga cikin addu'o'insa a cikin littafi guda daya aka kira shi da suna "Assahifa Assajjadiyya".

Assahifa Assajjadiyya: Shi littafi ne da ya kunshi addu'o'i guda 54 daga addu'o'in Imam Ali dan Husain (a.s),an tattara shi aka wallafa shi a zamanin Imam Ali dan Husain (a.s), kuma an rubuta shi guda biyu. Imam Muhammad al-Bakir ne ya ajiye guda dayawanda sauran imamai suka gaje shi, daya kuwa shi ne wanda Zaidu dan Aliyyu Zainul-abidin ya ajiye wurinsa, 'ya'yansa suka gaje shi.

Assahifayana da babban muhimmanci a wurin musulmai, sun kula da shi babbar kulawa, kuma ba zai gushe ba abin kulawa da muhimmanci. Muhimmancinsayana bayyana a cikin abubuwa masu zuwa:

1. Saboda shiyana kunshe da addu'a ne, addu'a kuwa tana daga cikin mustahabbai mafi muhimmanci na Musulunci.

2. Daukar Littafin a matsayin abin dogaro (da ake komawa gare shi) a cikin ilimomin harshen larabci da adabobinsa.

3. Daukar sa a matsayin abin dogaro (da ake komawa gare shi) a cikin ilimomin Akidar Musulunci.

4. Daukar sa a matsayin madogara (da ake komawa gare shi) a cikin ilimin kyawawan halaye.

5. Daukar sa a matsayin madogara (da ake komawa gare shi) a cikin wasu Ilimomi

Risalatul Hukuk: Shi ne wannan littafin da yake gaban mai karatu, shidai wani tari ne na bayanai daga koyarwar Imam Ali dan Husain (a.s) da yake kunshe da hakkokin dan Adam daban-daban. Yana kunshe ne da hakkoki guda hamsinna koyarwar Musulunci da Imam Ali Sajjad dan Husain (a.s) ya yi bayani a kai. Ya hada da hakkin Allah (s.w.t), dana mutum a kansa, da iyali, da jama'a, da na daula.

Sanadin Ruwaya

Aliyyu bn Ahmad dan Musa ya karbo daga Muhammad al'Asadi, daga Ja'afar dan Malik alFazari, daga Khairan dan Dahir, daga Ahmad dan Ali dan Sulaiman alJabali, daga babansa, daga Muhammad dan Ali, daga muhamamd dan Fudhail, daga Abi Hamza asSumali yace :

Wannanita ce Risalar Ali dan Husain (a.s) zuwa ga wasu daga sahabbansa:

Ka sani Allah madaukaki yana da hakkoki da suka kewaye ka a cikin duk wani motsi da kake yi, ko wani nutsuwa da kake yi, ko wani hali da kake da shi, ko wani masauki da kake sauka, ko wata gaba da ka juya ta, ko wani abu da ka sarrafa.

Kuma mafi girman hakkin Allah a kanka shi newanda ya wajabta maka ga kansa daga hakkinsa wanda shi ne asalin hakkoki, sannan sai kuma abin da ya wajabta maka ga kanka tun daga samanka kanka har zuwa tafin kafarka, a bisa sassabawar gabobinka.

Sai ya sanya wa harshenka wani hakki a kanka, kuma jinka yana da wani hakki a kanka, ganinka yana da wani hakki a kanka, hannunka yana da wani hakki a kanka, kafarka tana da wani hakki a kanka, cikinka yana da wani hakki a kanka, farjinka yana da wani hakki a kanka, to wadannan su ne gabobi bakwai wadanda da su ne ake yin ayyuka.

Sannan sai madaukaki ya sanya wa ayyukan hakkoi a kanka, sai ya sanya wa sallarka tana da hakki a kanka, haka azuminka yana da hakki a kanka, sadakarka tana da hakki a kanka, kyautarka tana da hakki a kanka, kuma ayyukanka suna da hakkoki a kanka.

Sannan sai ya fitar da hakkoki a kanka zuwa ga waninka daga ma'abota hakkoki a kanka, sai ya wajabta su a kanka; hakkoki jagororinka, sannan sai hakkokin al'ummarka, sannan sai hakkokin danginka; wadannan su ne hakkokin da sauran hakkoki suke rassantuwa daga garesu.

To hakkokin jagororinka guda uku ne da ya wajabta su a kanka: hakkin mai jagorantarka da mulki, da hakkin mai jagorantakarka da ilimi, da hakkin mai jagorantakarka da mallaka.

Kuma hakkokin al'ummarka da ya wajbta a kanka guda uku ne: Hakkin al'ummarka da mulki, sai hakkin al'ummarka da ilimi domin jahili nauyin al'umma nekan malami, sannan sai hakkin al'umma da mallaka kamar hakkin mata da abin da ka mallaka na kuyangi.

Kuma hakkokin dangi da aka wajabta a kanka suna da yawa daidai gwargwadon kusancin dangantaka: Hakkin babarka, sannan sai hakkin babanka, sai hakkin danka, sai hakkin dan'uwanka, sai hakkin nakusa sannan sai mai biye masa a kusanci, sai hakkinwanda ya fi cancanta sai kuma mai biye masa.

Sannan sai hakkin ubangijinka mai ni'imta maka, sai hakkin ubangidanka wanda yake ni'imta maka, sannan sai hakkin masu kyautata maka, sai hakkin mai yi maka kiran salla, sai hakkin limaminka a sallarka, sai hakkin abokin zaman wuri daya, sai hakkin makocinka, sai hakkin abokinka, sai hakkin wanda kuka hada hannu, sai hakkin dukiyarka, sai hakkin wanda kake bin sa bashi, sai hakkin wanda yake bin ka bashi, sai hakkin wanda kuke cudanya da shi, sai hakkin wanda kuke gaba da rigima da ya kai ka kara kotu, sai hakkin wanda kuke gaba da rigima da ka kai shi kara kotu. Sannan sai hakkin wanda ka nemi shawararsa, sai hakkin wanda yake ba ka shawara, sai hakkin wanda ya nemi ka yi masa nasiha, sai hakkin mai yi maka nasiha, sai hakkin wanda ya grime ka, sai hakkin wanda ka girma, sai hakkin mai tambayarka (rokonka), sai hakkin wanda ka tambaya (ka roka), sai hakkin wanda ya munana maka da wata magana ko wani aiki da gangan ne ya yi maka ko ba da gangan ba, sai kuma hakkin jama'arka a kanka, sai hakkin ma'abota zaman amana, sai kuma hakkokin da suke kanka daidai gwargwadon dalilan halaye, da sabuban da suka wakana.

To farin cikiyana ga wanda Allah ya taimaka masa a kan yin abin da ya wajabta masa na hakkokinsa, kuma ya datar da shi ga wannan ya ba shi katari.

Matanin Bayanin Hakkoki Hakkokin Allah da Sassan Jiki Hakkin Allah :

"Amma hakkin Allah mafi girma, shi ne ka bauta masa, ba ka tarayya da shi da wani abu, idan ka yi haka da tsarkin niyya, to Allah ya daukar maka alkawari akansa cewa zai isar maka lamarin duniya da lahira".

Hakkin Rai: "Amma hakkin ranka a kanka shi ne ka sanya ta cikin biyayya ga Allah, sai ka ba wa harshenka hakkinsa, ka ba wa jinka hakkinsa, ka ba wa ganinka hakkinsa, ka ba wa hannunka hakkinsa, ka ba wa kafarka hakkinta, ka ba wa cikinka hakkinsa, sai ka ba farjinka hakkinsa, kuma sannan sai ka nemi taimakon Allah (s.w.t) a kan hakan.

Hakkin Harshe: "Kuma hakkin harshe; shi ne ka kare shi daga mummunar magana ta alfahasha, dasaba masa alheri, da barin shiga maganar da ba ta da wani amfani, da kyautata wa mutane, da kyautata zance game da su".

Hakkin Ji: "Amma hakkin ji shi ne a tsarkake shi daga giba -yi da wani-, da jin abin da bai halatta a ji ba, da tsarkake shi daga sanya shi hanyar zuwa ga zuciya, sai dai idan wata magana ce mai kima da zata farar da wani alheri a cikin zuciyarka, ko kuma zaka samu wata dabi'a mai daraja da girma da ita, domin shi ji shi ne kofar magana zuwa ga zuciya wanda yake kaiwa ga fahimtar abubuwa daban-daban na alheri da na sharri. Babukuma karfi sai da Allah".

Hakkin Gani:"Amma kuma hakkin gani shi ne ka rufe shi daga ganin abin da bai halatta ba, ka yi lura da gani da shi ".

Hakkin Kafa: "Amma kuma hakkin kafafuwanka, shi ne kada ka yi tafiya da su inda ba ya halatta gareka, akansu ne zaka tsaya kan siradi, ka duba domin kada su zamar da kai sai ka halaka cikin wuta".

Hakkin Hannu: "Amma hakkin hannunka shi ne kada ka shimfida takan abin da bai halatta gareka ba, sai ka samu azabar Allah a gobe -kiyama- da wannan shimfidawar da ka yi, ka kuma samu zargi daga mutane a gidan yau -duniya-. Sannan kada ka rike ta daga abin da Allah ya wajabta mata, sai dai ka kiyaye ta da rike ta daga mafi yawan abin da bai halatta gareta ba, da shimfida ta zuwa ga mafi yawan abin da bai zama wajibi a kanta ba, sai ta kasance ta yi hankali, ta daukaka a wannan gida -duniya-, sannan lada kyakkyawa ya wajaba gareta daga Allah a gidan gobe -lahira-".

Hakkin Ciki: "Kuma amma hakkin cikinka shi ne kada ka sanya shi salka -jaka- ga haram kadan ne ko mai yawa, (kuma kada ka kara a kan koshi) kuma ka nufi halal da shi, kada ka fitar da shi daga haddin karfafa zuwa haddin wulakanci da zubar da mutunci, domin koshi mai kai ma'abocinsa zuwa ga maye wanda wulakanta kai ne, da jahilci, da kuma zubar da mutunci".

Hakkin Farji: "Amma hakkin farjinka shi ne ka kare shi daga zina, kuma ka kiyaye kada a gan shi".

Hakkokin Ibadoji

Hakkin Salla: "Kuma hakkin salla shi ne ka san cewa ita halartowa ce zuwa ga Allah madaukaki, kuma kai mai tsayuwa ne a cikinta a gaban ubangiji mai girma da daukaka, to idan ka san haka, sai tsaya matsayin bawa mai kaskanci, wulakantacce; mai kwadayi, mai razana; mai kauna, mai jin tsoro; miskini, mai kaskan da kai. Mai girmamawa gawanda yake gabansa da nutsuwa da kawaici; Ka fuskanto ta da zuciyarka, ka tsayar da (kiyaye) iyakokinta (dokokinta), da hakkokinta".

Hakkin Hajji: "Kuma hakkin hajji shi ne ka san cewa shi zuwa ne ga ubangijinka, kuma gudu ne daga zunubanka zuwa gareshi, kuma da shi ne za a karbi tubanka, da sauke nauyin wajibi da Allah ya wajabata maka shi a kanka". (Hakkin Hajji bai zo ba cikin ruwayarsama , sai dai ya zo a ruwayar da muke kawowa nan kasa).

Hakkin Azumi: "Kuma hakkin azumi shi ne ka san cewa shi wani hijabi ne da Allah ya sanya shi a kan harshenka, da jinka, da ganinka, da cikinka, da farjinka, domin ya kare ka daga wuta da shi, idan kuwa ka bar azumi, to ka keta suturar (katangar) da Allah ya yi maka".

Hakkin Sadaka: "Kuma hakkin sadaka (zakka) shi ne ka san cewa ita ajiyarka ce gun ubangijinka, kuma ajiyarka ce wacce ba ka bukatar sanya sheda a kanta, idan ka san haka sai ka kasance mafi amintuwa da abin da ka ajiye shi a sirrance fiye da abin da ka bayar da ajiyarsa a fili, kuma ka sani cewa ita tana kare maka bala'o'i da cututtuka daga gareka a duniya, kuma tana kare maka wuta a lahira. Sannan kada ka yi wa wani gori da ita domin taka ce, idan kuwa ka yi gori ga wani da ita, to ba ka amintuwa ka kasance gareta kamar wulakanta kanka ne gareta da abin da ka yi gori da ita kan wani, domin wannan yana nuna cewa ba kanka kake nufi da ita ba, domin da kanka kake nufi da ba ka yi wa wani gori da ita ba".

Hakkin Hadaya: "Amma hakkin hadaya shi ne ka nufi Allah mai girma da daukaka da shi kawai (don Allah), ba ka nufin halittunsa da shi, kuma ba sa son komai da shi sai rahamar Allah da tsiran ranka ranar da zaka gamu da shi".

Hakkin Shugaba: "Amma hakkin jagora shi ne ka san cewa shi jarrabawa ce gareka, kuma shi abin jarraba ne game da kai saboda abin da aka sanya a hannunsa a kanka na iko, kuma kai kada ka jawo wa kanka fushinsa sai ka jefa kanka cikin halaka, sai ka zama wanda ya hada hannu da shi a kan duk abin da ya same ka na cutarwa".

Hakkin Ilimi: "Kuma hakkin mai tarbiyyantar da kai da ilimi shi ne ka girmama shi, ka kuma karrama majalisinsa da kyautata sauraronsa da fuskantowa zuwa gareshi, kuma kada ka daga masa muryarka, kada ka amsa wa wani mutum wani abu da yake amsa masa sai dai ya kasance shi ne wanda yake amsawa, kada ka yi wa wani magana a majalisinsa, kada ka yi gibarsa, kuma ka yi kariya gareshi idan aka ambace shi da mummuna, kuma ka suturta aibinsa ka bayyanar da darajojinsa, kada ka zauna da mikiyinsa, kuma kada ka yi gaba da masoyinsa. Idan ka yi haka, to mala'ikun Allah zasu yi maka sheda cewa ka nufe shi kuma ka san iliminsa saboda Allah madaukaki ne ba don mutane ba".

Hakkokin Al'umma Hakkin Jama'a:

"Amma hakkin jama'ar kasa da kake jagoranta shi ne ka sani cewa sun zama jama'arka ce saboda rauninsu da kuma karfinka, don haka wajibi ne ka yi adalci a cikinsu, ka zama garesu tamkar uba mai tausayi ne, ka yafe musu jahilcinsu, kada ka gaggauta musu da ukuba, kuma ka gode wa Allah a kan abin da ya ba ka na karfi kansu".

Hakkin Ilimin Jama'a: "Amma hakkin jama'arka na ilimi shi ne; Ka san cewa Allah mai girma da daukaka ya sanya ka ne mai daukarsu darasi da abin da ya ba ka na ilimin da ya bude maka shi na taskokinsa, to idan ka kyautata koyar da mutane, ba ka wulakanta su ba, ba ka kyare su ba, sai Allah ya dada maka daga falalarsa, amma idan ka hana mutane iliminka, ka wulakanta su yayin da suka nemi ilimi gunka, to Allah mai girma da daukaka yana da hakkin ya kwace maka ilimi da kwarjininsa, kuma ya zubar da matsayinka daga zukata.

Hakkokin Makusanta

Hakkin Matar Aure: "Amma hakkin mata shi ne ka san cewa Allah madaukaki ya sanya ta mazauni da wurin nutsuwa gareka, sai ka san cewa wannan ni'ima ce da Allah madaukaki ya yi maka ita, sai ka girmama ta, ka tausaya mata, duk da kuwa hakkinka a kanta ya fi wajaba, amma tana da hakki a kanka na ka tausaya mata domin ita ribacewarka ce, kuma ka ciyar da ita, ka tufatar da ita, sannan idan ta yi rashin sani da wauta sai ka yafe mata".

Hakkin Bawa: "Kuma hakkin wanda kake mallaka shi ne ka sani cewa shi halittar ubangijinka ne, kuma dan uwanka na uba da uwa, kuma tsokarka da jininka ne, ba ka mallake shi domin kai ne ka halicce shi ba Allah ba!, kuma ba ka halicci wani abu na daga gabobinsa ba, ba ka fitar masa da wani arziki ba. Saidai Allah madaukaki ne ya isar maka da wannan sannan ya hore shi gareka, ya sanya shi amana a hannunka, ya ba ka ajiyarsa, domin ya kiyaye maka abin da kake zo masa da shi na alheri. Don haka ka kyautata masa kamar yadda Allah ya kyautata maka, idan kuwa ka ki shi, to sai ka canja wani da shi, amma kada ka azabtar da halittar Allah madaukaki da buwaya, kuma (ka sani) babu karfi sai ga Allah".

Hakkin Mai Bawa: "Amma hakkin mai jagorantarka da mallaka, shi ne ka yi biyayya gareshi kada kasaba masa sai dai cikin abin da ya saba wa Allah mai girma da daukaka, to (ka sani) babu biyayya ga abin halitta cikin sabon mahallicci".

Hakkin Ubangida: (Amma hakkin mai mulki da kaiyana kama da na mai mulki da kai a jagoranci, sai dai wannan -jagora- ba ya mallakar abin da wancan -mai bawa- yake mallaka. Don haka haka biyayyarsa ta zama wajibi a kanka a cikin komai karami da babba, sai dai idan wani abu ne da zai fitar da kai daga biyayyar hakkin Allah, wanda zai hana ka biyan hakkinsa (ubangiji), da hakkokin sauran halittu, idan ka gama da hakkinsa (ubangiji) sannan sai ka shagaltu da hakkinsa (ubangida), kuma babu karfi sai da Allah).

Hakkin Uwa: "Ka sani hakkin babarka cewa ta dauki cikinka a inda babu wani mutum mai iya daukar wani, ta ciyar da kai daga cikin zuciyarta da abin da babu wani mutum mai ciyar da irinsa ga wani, ta zama lokacinka da dukkan gabobinta; ba ta damu ba ita ta ji yunwa, ta tufatar da kai ita kuwa ta tsaraita, ta kosar da kai, ta ji kishirwa ta shayar da kai, ta yi tsaraici ta tufatar da kai, ta ji rana ta inuwantar da kai, da rasa bacci saboda kai, ita ce lokacinka zafi da sanyi, don kawai ka zama nata, to kai ba zaka iya gode mata ba sai dai da taimakon Allah da dacewarsa.

Hakkin Uba: "Kuma hakkin babanka ka sani cewa shi ne asalinka, kuma ba don shi ba, da babu kai, kuma duk wani abu da kake gani gareka da yake kayatar da kai, to ka sani babanka ne mafarin wannan ni'imar gareka, sai ka gode wa Allah, ka gode masa gwargwadon wannan. Babukarfi sai da Allah".

Hakkin Da ('ya'ya): "Kuma hakkin danka shi ne ka san cewa shi daga gareka yake kuma abin rabawa zuwa gareka a wannan duniya da alheirnsa da sharrinsa, kuma kai abin tambaya ne kan abin da ka koya masa na kyakkyawan ladabi da shiryarwa ga ubangijinsa mai girma da buwaya, da kuma taimaka masa kan biyayyarsa, sai ka yi aiki cikin umarninsa da aikin wanda ya san za a saka masa da kyautata masa, wanda kuma za a yi wa azaba kan musguna masa".

Hakkin Dan'uwa: "Kuma hakkin dan'uwanka shi ne ka sani cewa shi hannunka ne da daukakarka da karfinka, don haka kada ka rike shi makami a kan sabon Allah, ko tanadi don zalunci ga halittar Allah, kuma kada ka gaza taimakonsa a kan makiyinsa, da yi masa nasiha, to idan ya bi Allah, in ba haka ba to Allah ya kasance shi ne mafi girma gareka fiye da shi, kuma babu karfi sai da Allah".

Hakkokin Mutane

Hakkin Mai 'Yantawa: "Amma hakkin mai 'yantaka mai ni'imata maka shi ne ka sani cewa shi ne ya ciyar da dukiyarsa kanka, ya fitar da kai daga kaskanci bauta da dimuwarsa zuwa ga izzar 'yanci da nutsuwarta, sai ya sake ka daga ribacewar mallaka, ya kwance ka daga kaidin bauta, ya fitar da kai daga gidan sarkar (bauta), ya mallaka maka kanka, ya ba ka damar bautar ubangijinka, kuma ka sani shi ne mafi cancantar mutane da kai a rayuwarka da mutuwarka, kuma taimakonsa wajibi ne a kanka da dukkan abin da yake bukata daga gareka, kuma babu karfi sai da da Allah".

Hakkin 'Yantacce: "Amma hakkin wanda aka 'yanta shi ne ka sani cewa wanda ka yi wa ni'ima, sai ka sani cewa Allah mai girma da daukaka ya sanya 'yancin da ka yi masa wata hanya ce zuwa gareshi, kuma tsari ce gareka daga wuta, kuma ladanka a duniya shi ne gadonsa idan ba shi da wasu dangi magada sakamakon abin da ka ciyar na dukiyarka (a kansa), kuma a lahira kana da aljanna".

Hakkin Mai Yin Alheri: "Amma hakkinwanda ya yi maka alheri shi ne ka gode masa, ka kuma ambace shi da alheri, ka samar masa da maganar (mutane) ta alheri (a kansa), ka tsarkake yi masa addu'a a tsakaninka da Allah, mai girma da buwaya. Idan ka yi haka zaizama ka gode masa a boye da a sarari, sannan idan ka samu dama wata rana kai ma ka rama masa (alherin da ya yi maka).

Hakkin Ladani: "Amma hakkim mai kiran sallah shi ne ka sani cewa shi mai tuna maka ubangijinka mai girma da daukaka ne, kuma mai kiran ka zuwa ga rabautarka, mai taimakonka kan sauke wajibin Allah da yake kanka, sai ka gode masa a kan haka irin godiyar da kake yi wa masu kyautatawa".

Hakkin Limami: "Amma hakkin limaminka a sallarka, shi ne ka sani cewa kai kana dora masa nauyin jakadancin tsakaninka da ubangijinka mai girma da buwaya ne, ya yi magana maimakonka kai ba ka yi magana mai makonsa ba, ya yi maka addu'a kai ba ka yi addu'a gareshi ba, kuma ya isar maka da tsoron tsayuwa gaban Allah mai girma da daukaka. Idan an samu wata tawaya tanakansa ban da kai, idan an samu wata kamala to kai kana tarayya da shi, kuma ba shi da wani fifiko a kanka (cikin alherin da ake samu), sai ya kare maka kanka da kansa, sallarka da sallarsa, to sai ka gode masa a kan hakan".

Hakkin Abokin Zama: "Amma hakkin abokin zamanka sai ka tausasa masa dabi'arka, ka yi masa adalci a yin magana, kada ka tashi daga majalisinka sai da izininsa, amma wanda yake zama gunka shi yana da hakkin ya tashi daga gunka ba tare da izini ba, ka manta da munanansa, ka kiyaye alherinsa, kuma kada ka jiyar da shi komai sai alheri".

Hakkin Makoci: "Amma hakkin makocinka shi ne ka kiyaye shi idan ba ya nan, ka girmama shi idan yana nan, ka taimaka masa idan ana zaluntarsa, kada ka bibiyi sirrinsa, kuma idan ka san wani mummuna nasa sai ka boye masa shi (kada ka yada shi), idan ka san yana karbar nasiharksa sai ka yi masa ita tsakaninka da shi, kada ka rabu da shi gun tsanani, ka yafe masa kurakuransa, ka yafe masa laifinsa, ka zauna da shi zaman mutunci, kuma babu karfi sai da Allah".

Hakkin Aboki: "Amma hakkin aboki shi ne ka yi abota shi da fifita (shi) da yin adalci, ka girmama shi kamar yadda yake girmama ka, kada ka bar shi ya riga (ka) gaggawa zuwa ga wani alheri, idan kuwa ya riga (ka yin alheri) to sai ka saka masa, ka so shi kamar yadda yake son ka, ka kare shi daga abin da yake nufinsa na wani sabo, ka kasance rahama gareshi kada ka zama azaba a kansa, kuma babu karfi sai da Allah".

Hakkin Abokin Tarayya: "Amma hakkin abokin tarayya (wanda kuka hada hannun cinikayya) shi ne idan ba ya nan sai ka kare shi, idan yana nan sai ka kiyaye shi, kada ka yi wani hukunci sai da nasa hukuncin, kada ka yi aiki da ra'ayinka ba tare da tasa mahangar ba, ka kiyaye masa dukiyarsa, kada ka ha'ince shi cikin abin da yake babba ne ko karami na lamarinsa, ka sani hannun Allah yana tare da hannayen masu tarayyar (hada hannun jari) matukar ba su ha'inci juna ba, kuma babu karfi sai da Allah".

Hakkin Dukiya: "Amma hakkin dukiyarka shi ne kada ka dauke ta sai ta hanyar halal dinta, kada ka ciyar da ita sai ta inda ta dace, kuma kada ka zabi kanka da ita a kan wanda ba ya yabonka, to sai ka yi aiki da ita wurin biyayyar ubangijinka, kuma kada ka yi rowa da ita sai ka koma da hasara da nadama tare da jama'ar (tababbu), kuma babu karfi sai da Allah".

Hakkin Mai bin Bashi: "Amma hakkin mai bin ka bashi da yake neman ka biya, to idan kana da yalwa sai ka ba shi, kuma idan ka kasancemaras yalwa, to sai ka nemi yardar da shi da kyautata magana, ka mayar da shi daga kanka mayarwa mai taushi".

Hakkin Abokin Cudanya: "Amma hakkin Abokin cudanya shi ne kada ka yi masa 'yar rufe, kada ka yi maza zambo, kada ka yi masa yaudara, ka ji tsoron Allah madaukaki da girmama a kan lamarinsa".

Hakkin Mai Kara: "Amma hakkin abokin shari'a wanda ya yi da'awar wani abu a kanka, shi ne idan abin da yake da'awarsa a kanka gaskiya ne to sai ka yarda da shi yana kanka, kada ka zalunce shi, ka biya shi hakkinsa, idan kuwa abin da yake da'awarsa a kanka ya kasance karya ne, to sai ka tausasa masa, kada ka zo da wani abu kan lamarinsa sai tausasawa, kuma kada ka fusata ubangijinka game da lamarinsa, kuma babu karfi sai da Allah.

Hakkin Wanda ake Kara: "Amma hakkin abokin shari'a da ka kai shi kara, (ka sani) idan ka kasance mai gaskiya a kararka to sai ka kyautata maganarsa, kada ka yi musun nasa hakkin, idan kuwa ka kasance mai karya ne a kararka, to sai ka ji tsoron Allah mai girma da daukaka, ka tuba zuwa gareshi, ka janye wannan karar".

Hakkin Maineman Shawara: "Amma hakkin mai neman shawara shi ne; idan ka san yana da wani ra'ayi (mai kyau ne) sai ka yi masa nuni da shi, amma idan ba ka sani ba, to sai ka shiryar da shi zuwa ga wanda ya sani".

Hakkin Maibayar da Shawara: "Amma hakkin mai ba ka shawara shi ne kada ka tuhume shi idan ra'ayinsa cikin abin da bai yi muwafaka da kai ba na ra'ayinsa, idan kuwa ya yi muwafaka da kai to sai ka gode wa Allah mai girma da daukaka".

Hakkin Maineman Nasiha: "Amma hakkim mai neman nasiha shi ne ka ba shi nasihar, kuma ya kasance kai abin da kake nufi shi ne tausayi gareshi da tausasa masa".

Hakkin Mai yin Nasiha: "Amma hakkin mai yin nasiha shi ne ka tausasa masa dabi'arka, ka saurara zuwa gareshi da jinka, to idan ya zo maka da dacewa sai ka gode wa Allah mai girma da daukaka, amma idan bai dace ba, sai ka mantar kada kuma ka tuhume shi, ka sani shi ya yi kuskure ne kawai kuma kada ka rike shi da wannan sai dai idan ya cancanci tuhumar ne, kowane hali dai to kada ka damu da lamarinsa, kuma babu karfi sai da Allah".

Hakkin Babba: "Amma hakkin babba shi ne ka girmama shi saboda shekarunsa, da daukaka shi saboda rigon da ya yi maka a musulunci kafin ka zo duniya, da barin jayayya da shi yayin husuma, kuma kada ka riga shi kan hanya, kada ka shiga gabansa, kada ka nuna jahilcinsa, idan kuwa ya yi maka wauta to sai ka jure ka daure, ka girmama shi saboda hakkin musulunci da alfarmarsa".

Hakkin Karami: "Amma hakkin karami shi ne ka tausaya masa cikin koyar da shi, da yin rangwame gareshi, da suturta masa, da tausasa masa, da taimaka masa".

Hakkin Mai Roko: "Amma hakkin mai roko shi ne ka ba shi daidai gwargwadon bukatarsa".

Hakkin Wanda ake Roka: "Amma hakkinwanda ake roka shi ne idan ya bayar to sai ka karba daga gareshi da godiya da sanin kyautatawa, amma idan ya hana sai ka karbi uzurinsa".

Hakkin Mai Farantawa: "Amma hakkinwanda ya faranta maka rai shi ne ka godewa Allah madaukaki sannan sai ka gode masa".

Hakkin Mai Batawa: "Amma hakkin mai munana maka shi ne ka yi masa afuwa, amma idan ka san yin afuwa zai cutar to sai ka nemi taimako (kansa). Allah madaukakiyana cewa: "Kuma duk wanda ya nemi taimako bayan zaluntarsa, to wadannan babu wani laifi a kansau". (Shura: 40)".

Hakkin Al'umma: "Amma hakkin al'ummarka shi ne ka sanya aminci garesu, da tausaya musu, da tausasawa ga mai sabawarsu, da sabo da su, daneman gyaransu, da godiya ga mai kyautatawarsu, da kame cutar da su, da so musu abin da kake so wa kansa, da ki musu abin da kake ki wa kanka.Tsofaffinsu su kasance tamkar baba ne gareka, samarinsu su kasance kamar 'yan'uwa ne gareka, gyatumominsu su kasance kamar uwa ce gareka, kanana su kasance tamkar 'ya'ya".

Hakkin 'Yan Amana: "Amma hakkin 'yan amana (wadanda ba musulmi ba da suke rayuwa tare da musulmi bisa yarjejeniyar rayuwa tare), shi ne ka karba daga garesu abin da Allah ya karba daga garesu (na su yi nasu addinin da rayuwarsu), kada ka zalunce su matukar sun cika wa Allah alkawarinsa (ba su zalunce ka ba suna masu karya yarjejeniya".

Hafiz Muhammad Sa'id

hfazah@yahoo.com

www.hikima.org

Saturday, June 04, 2011

Abin Da Littafi Ya Kunsa

Gabatarwar Mafassari 3

Imam Aliyyu Zainul-abidin (a.s) 6

Sanadin Ruwaya 8

Matanin Bayanin Hakkoki Hakkokin Allah da Sassan Jiki Hakkin Allah 10

Hakkokin Ibadoji 11

Hakkokin Al'umma Hakkin Jama'a: 12

Hakkokin Makusanta 13

Hakkokin Mutane 15