• Farawa
  • Na Baya
  • 13 /
  • Na Gaba
  • Karewa
  •  
  • Gurzawa HTML
  • Gurzawa Word
  • Gurzawa PDF
  • Budawa: 2334 / Gurzawa: 395
Girma Girma Girma
mahdawiyyanci

mahdawiyyanci

Mawallafi:
Hausa

Fasali Na Biyu

Kebance-Kebancen Fahimtar MahdawiyyanciA Wajen Ahlulbait (a.s)

Bayan tabbatar da inganci fassarar akida kan fahimtar mahdawiyanci a wajen Ahlulbaiti (a.s) zamu shiga wani sabon fage na bincike kan wannan mafhumin, mu kuma tabbatar da cewa wadannan kebance-kebancen tabbatattu ne sun faru a cikin tarihi, kuma suna da samuwa a shari’a, kuma yarda da su (wandannan kebance-kebancen) ba ya taba akida kuma be saba da abin da ya faru a tarihi ba, wadanda su ne kamar haka:-

Kebance-Kabence Na Farko: Tabbatar Haihuwar Imam Mahdi A Wani Boyayyen Yanayi Na Musamman Da Babu Makawa Sai Ya Faru

Tare da tabbatar mahangar mahdawiyyanci a wajen Ahlulbaiti (a.s), hakika lamarin ya yawi gari a sariri cewa daga cikin mafi bayyanar wannan fahimtar, kasancewar haihuwar Imami na goma sha biyu ta faru tare da asirtawa da boyewa (a boye) don ya sami damar fakuwa bayan hakan, ya buya daga idanuwan mutane zuwa amintaccen wajen da Allah Ta'ala ya zaba masa har zuwa lokacin da zai yi masa izini da bayyana, la’akari da cewa shi ne tauraro na karshe a cikin sararin samaniyar imamanci kuma shi ne imamin da musulmai ba su da wani Imami bayansa, kuma wannan ma’anar na lazimta masa ya yi rayuwa a boye da tsawon kwana da haihuwa a boye, domin kujerar imamanci ta ci gaba da aikinta tsawon zamani ta hanyar wanzar da samuwar Imami daga cikin Imamai goma shi biyu (a.s) ya zama ga shi rayayye kuma a fake.

A wannan lokacin be dace ba wani yace : saboda me haihuwar Imam da kuma samuwar sa bayan wafatin babansa, ba su zama abin da kowa ya gani ya sani ba, ta yadda ya zama lamarin da duk wanda yake so zai iya kai wa zuwa gare shi, don mu iya gasgata hakan ba? Tabbas da zai zama kamar haka da be sami damar fakuwa da boyuwa daga idanun mautane ba, kuma da be zama shi ne Imami na goma sha biyu ba, kuma da adadin Imamai ya fi haka, kuma hakan ya sabawa dalilan da suka zo a hadisai Annabi Muhammadu (s.a.w) a baya, hakika boyayyayiyar haihuwa na daga cikin abin da dabi’a take hukuntawa la’akari da wadannan dalilan (na hadisi).

Wannan kuwana karafa cewa tabbatar da wani abu a fili wanda ya yi kama da lamarin haihuwan Imam Mahdi da samuwarsa da rayuwarsa (a.s) na daga cikin abin da ba zai yu yi a dogara da binciken tarihi a kan sa ba, mutukar mun sani tun farko cewa lamari ne da aka gwama shi da tsanannin asirtawa da boyewa. Ballatana ma lamari ne da ya tabbata ta bangaren akida da tarihi, wanda akida ce za ta taka rawar ta asasi a cikinsa, a daidai lokacin da binciken tarihi zai taka rawa a cikin kammaluwarsa (shi lamarin akidar), domin tun farko muna da yakini akwai wadanda suke yin inkarinta da wandanda suke yin shakku a cikinta, mutukar dai zata kasance asirtaccen lamari wanda ake boyewa, kuma wadanda ke da masaniya a kan sa wasu mutane ne ‘yan kadan, ta yadda ba za a bari wasu su sani ba koda kuwa sun kasance daga cikin na kusa da Imam (a.s), kuma ba mamaki ya zama wasu daga cikin masu ikhlasi daga ‘yan shi’a su ma su yi inkari da kokwanton haihuwarsa mutukar akwai shamaki tsakaninsu da hakinin lamarin da yake a asirce a boye, ta yanda da za a tambaye su kan haihuwar Imam Mahdi (a.s) da samuwarsa da rayuwarsa da sun musanta hakan kuma da sun gaya wa mutane cewa suma ba su gan shi ba, kuma ba su ji labarin haihuwar sa ba ko samuwarsa. Hakika mu, ba muna magana kan lamarin da ke da samuwa da jiki a sarari ta kowane bangare da fuskoki, wanda yake karkashin alkalamin tarihi dari bisa dari ba ne, ballantana mu dogara da shi (tarihi) wajen tabbatar da shi (lamarin haihuwar Imam Mahdi (a.s)) ba, ko kuma mu musa shi a bisa dogaro da maganar maruwaita da malaman tarihi ba, kadai dai muna magana ne kan lamarin da asasinsa lamarin ne na gaibu (wato boyayyen abu na akida) illa iyaka dai ba lamarin gaibu ba ne saki ba kaidi, sai cewa shi wannan lamarin yana da wani hasken da wasu zababbu ne suke kaiwa zuwa gare shi, sun san cewa an haife shi sai su bada sheda a kanta, sun san cewa ya yi gajeriyar fakewa sai su yi sheda a kanta kuma sun san cewa ya yi doguwar fakewa sai su bada sheda a kanta. Don haka ne ma mukace hakika fahimtar Ahlulbaiti (a.s) kan mahadaawiyyanci fahimta ce ta akida.

Da ma’anar cewa inkarin masu musantawa a cikin lamari irin na samuwar Imam Mahdi, tarihi ba zai taba zama dalilin da za a iya kore samuwar sa da shi ba, tun dama tun a farko mun bayyana cewa lamarinsa asirtaccen boyayyen lamari ne. Kuma ta bangaren binciken tarihi ya zama dole mu tabbatar da samuwar wanda ya gan shi ta hanyar isuwa da labarin wanda ya ce ya gan shi ya sami tsinkayi a kansa kuma ya ji labarin samuwarsa kuma ya yi yakini da hakan, ba tare da waiwayawa ga zuwa inkarin masu inkari ba wadanda suke daukar zahiri a matsayin ma’aunin tantance asirtaccen boyayyen lamari.

Anan zamu yi bincike guda biyu: Bahasi na farko kan dalilai da shedun da ke tabbatar da haihuwar Imam (a.s) da kuma ci gaban samuwasa, a bincike na biyu kuma zamu tattauna dalilan masu inkarin samuwarsa (a.s).

Shedu Na Tarihi Da Ke Nuni Kan Samuwar Imam Mahdi (a.s)

Wannan wani bangare ne mai fadin gaskewanda maganganu masu yawa, na adadi mai yawa na masana tarihi suka zo a kansa, kuma zamu kasa su zuwa wasu adadi kamar haka:-

Shedar Imam Hasan Askari (a.s)kan haihuwar dansa Imam Mahdi (a.s).

A cikin hadisai masu yawa da managartan malaman hadisai da masu ruwayana Mazhabar Shi’a suka rawaito, wanda daga cikin su akwai:-

Hadisin da aka rawaito daga Muhammad dan Yahaya, daga Ahmad dan Ishak daga baban Hisham, Baja’fare, yace “na ce da baban Abdullahi kwarjinika na hana ni in yi maka tambaya, shin ka yi mini izini? Sai yace yi tanbayarka. Saina ce: sai na ce ya shugabana shin kana da da? Sai yace e”.[34]

A cikin wannan hadisin akwai isuwa kan sanadinsa da manuniyarsa, ga ma litattafan mazaje (rijal) na bada sheda kan girman matsayin Muhammad dan Yahya dan Ja'afar Addar mutumin Kum, wanda kabarin sa be gushe ba sananne shahararre kuma Ahmad dan Ishak dan Abdullahi dan Sa’ad dan Akhwas Ba’ash’are dan abu Ali bakumme, ya bada sheda kan girman katsayinsa a wajen Imam Hasan Askari, (a.s).hakama Dawud dan Kasim dan Ishak dan Abdullahi dan Ja'afar dan Abidalib baban Hashin Baja’afare shi ma ya bada sheda kan grman matsayinsa.....sannan ka duba karancin wasidodin da ke cikin isnadin wannan hadisin wanda irinsa ana kiran sa da makusancin isnadi (mai isnadi makusanci) wanda ake ganin hakan na daga cikin abin da ke kara wa hadisin karfi.

Shedar Unguwar-zoma

wacce ita ‘yar’uwar Imami ce kuma goggo Imami, kuma diyar imami, Ba’alawiyya tsarkakakka Hakima ‘yar Muhammad Jawad kuma ‘yar ‘uwar Imam Hadi kuma goggon Imam Askari, a yayin da ta bayyana cewa ta halarci haihuwar Imamul hujja (a.s) a daren haihuwar sa,[35] kuma ita ce ta jibinci al’amarin - (ta kula da ita, wato ta yi wa mahaifiyar Imam Mahdi (a.s) unguwar zonci) - Narjis mahaifiyar Imamul Hujja (a.s) da izinin mahaifinsa Imam Hasan Askari (a.s).[36]

Gomomin shedu ta hanyar ruwaya daga Imam (a.s)

Tabbas akwai jerin sunaye masu yawa na wadanda suka ga Imam Mahdi (a.s) kuma suka sami saduwa da shi kuma suka bada sheda kan cewa sun gan shi da idanunsu, wanda litattafan tarihi suka rubuta hakan, kuma wasu daga cikin marubuta suka tattarasu, a cikin litattafai na musannan misalin littafin: (tabsiratul wali fi man ra’al Ka’imul Mahdi) (a.s) na Sayyid Hashim Baharani, a cikin litattafin ya ambaci mutum (79) wadanda suka yi sheda kan cewa sun ga Imam (a.s) a lokacin yaraontarsa ko lokacin gaibar sa (fakewarsa) karama, kuma ya ambaci sunayen litattafan da ya dogara da su a kan haka. Kuma Shekh Abudalib Tajlil Al-tabrizi ya lissafo mutum (304) daga cikin wadanda suka ga Imam (a.s) kuma suka ba da shedakan haka.[37] shi kuma Shekh Saduk wanda ya rasu a shekara ta (381bh) shi ma ya lissafo mutun (64) da suka tabbatar masu sun ga imam (a.s) ya ce wandannan mutanen sun bada sheda kan cewa sun ga Imam (a.s) kuma da yawa daga cikinsu ma sun kasance daga cikin wakilansa,[38] wadanda ke zaune a garuruwa mabanbanta.

Daga cikin wakilansa akwai: daga Azarbijan: Akwai Kasim. Daga Ahwaz: kuma akwai Muhammad dan Ibrahim dan Mihziyar daga Bagdad: Akwai Hajiz Bilali.Da Usman dan Sa’idul Amri, da Muhammad dan Usman, dan Sa’idul Amri da Ada’u. Daga kufa kuma akwai Al’asumi, daga Kum akwai Ahmad dan Ishak. Daga Nishabur akwaiMuhammad dan Shazana, daga Hamadan akwai Basami da Muhammad dan Abi Abdullahil Kufi Al-asadi, da Muhammad dan Salihu.

Amma wadanda suka gan shi daga cikin wadanda ba wakilai ba ne, daga cikin su akwai mutanen Isfahan: akwai Ibin- Basha Shazale daga Ahwaz: akwai Husaini daga Bagdad akwai: Ahmad dan Hasan da Ishak Marubuci daga Banu Naubakht, da Abu Abdulllahil Khubairi, da Abu Abdullahi dan Farakh, da Abu Abdullahil kindi, da Abu Kasim bin Abi khulaisi, da Abu Kasim dan Dubaisu, da Masrurur Al-dabbakh, bawan abin Hasan (a.s), da Nabili, da Harunal Fazari. Daga Dainawar kuma akwai, Ahmad dan Abinl Hasan dan Haruna, da Ammainsa Hasan dan Haruna, daMuhammad dan Muhammad Al-kulaini. Daga Kazwain kuma akwai Ali dan Ahmad da Muradas, daga Kum kuma akwai Hasan dan Nadhir da Husain dan Yakub da Ali dan Muhammad dan Ishak dan Muhammad dan Ishak, daMuhammad dan Muhammad daga Misra kuma akwai abu raja. Daga Nasibaini kuma akwai abuMuhammad bin Wajna’u Annasibi.Daga Hamadana kuma akwai Ja'afar dan Hamdan da Muhammad dan Kishmurdu, da Muhammad dan Haruna. Daga Yeman kuma akwai Ibnil A’ajami, da Ja’afari da Hasan dan Fadhl dan Yazidu, da Abul Fadhl dan Yazid, da babansa Al-fadhlu bin Yazid da Shamshadi, kamar yanda ya ambaci wadanda suka gan shi daga mutanen Shahrruz da Saimara da Faris da Kabis da Marwa.

Shin hankali zai karbi cewa wadannan mutanen bakidayan su, su hadu a kan su yi karya?Alhali kuma daga cikin su akwai managarta, amintattau wadanda litattafan mazaje sun bayyana nagartarsu.

Matakin da masarautar Abbasiyya ta daukakan lamarin

Hakika masarautar abbasiya bayan da Imam Hasan Al-askari ya yi wafati ta fuskanci iyalan sa da ma’amalar da ke nuna cewa suna jin tsoron wani yaro da aka haifa wanda ke da hadari wanda ya buya daga idanunta, sai ta fara bincike ta ko wace hanya da dukkan karfin ta na iko a yayin da (Sarki) Mu’tamada ba’abbase wanda ya rasu a shekara ta (270H) ya bawa yan sandansa umarnin su bincike gidan Imamaul Askari (a.s) bincike na bin kwakkwafi, kuma ya sa a binciko dansa Mahdi (a.s) kuma ya sa aka tsare kuyangun Abu Muhammad (a.s) kuma aka kama ‘ya’yansa mata tare da temakon Ja'afar makaryaci kuma a sakamakon haka wakilan Abi Muhammad (a.s) sun kwashi mummunar jarrabawa na daga kamu da daurewa da tsoratarwa da kaskantarwa da walakantarwa da kaskanci.[39]

Dukkaninn wannan alhali Imam Mahadi (a.s) yana dan shekara biyar daga rayuwarsa, shi kuma sarki shekarun ba su sha masa kai ba, bayan ya riga ya san cewa wannan yaron shi ne imamin da zai ruguza mulkin dagutu saboda abin da ya yadu na daga hadisi, cewa imami na goma sha biyu daga Ahlulbaiti (a.s) shi ne wanda zai cika dunya da adalci kamar yanda ta cika da zalunci da danniya, sai matsayin sa kan Mahdi (a.s) ya kasance kamar matsayin fir’auna a wajen musa (a.s) wanda mahaifiyar sa ta wurgar da shi - saboda jin tsoron - cikin korama yana dan jariri.

Mu’utamadul Abbasi ba shi kadai ne wanda ya san da wannan tabbataccen lamarin ba, hakika sarakunan da suka gabace shi kamar Mu’utaz da Muhtadi ma sun san haka, don haka ne ma Imam Hasan Askari ya kasanace yana son kar labarin haihuwarsa ya yadu, in ba tsakanin zababbun mutane daga ‘Yan Shi’arsa da bayinsa ba.

Hakika motsin da masarauta ta yi a sarari ya nuna cewa ita da sauran mutane sun yi Idrakin cewa hadisin Jabiru dan Samarata ba zai dabbaku (aywatu) a kansu ba haka ma wadanda suka gabace su daga banu umayya, wadanda wannan hadisin zai hau kansu su kadai su ne ‘yan gidan Annabta, masaukar wahayi da abin saukarwa (a.s).

In ba haka ba to wane hadari ne ke zekewa mulkin su ta hanyar dan karaminyaron da shekarun sa ba su wuce biyar ba, kuma ba su yarda cewa shi ne Imam Mahdi (a.s) wanda hadisai mutawatirai suka yi magana a kansa ba?! Wani marubuci yana cewa da da gaske ba a haife shi ba to meye ma’anar tsare bayi mata da kulle su da tura unguwar zomomi don su tabbatar da wacece ke da ciki a cikinsu, da kuma bibiyar su tsawon lokacin da hankali ba zai karba ba, don daya daga cikinsu ta wanzu karkashin kulawa tsawon shekara biyu! Dukkanin wannan tare da fafakar sahabban Imam Hasan Askari (a.s) da munana musu tare da yada ‘yan leken asiri don su bi diddigin labarin Mahadi (a.s) da binceke gidansa lokaci bayan lokaci?.

Kuma me ya yasa masarauta taki gamsuwa da abin da Ja'afar ya yi da’awa na cewa dan’uwansa ya rasu be bar magaji ba.

Ashe ba za ta iya ba shi hakkinsana gado ba, tun da kamai ya zo karshe, ba tare da wanann sakaran daukar matakin ba, wanda ke yin nuni kan firgicin ta da tsoronta daga dan Hasan Allah Ta'ala ya gaggauta bayyanarsa?!

Na’am zaa iya cewa za a iya cewa kwadayin masarauta kan taga ta bawa ko wane ma’abocin hakki hakkinsa ne ya sa ta damu da yin bincike kan samuwar da don kar Ja'afar ya cinye gadon shi kadai bisa shedar da shi da kansa ya bayar!

Kenan sai ka ce: baya daga cikin abin da ya shifi masarautar da mulki ke hannunta a wannan lokacin ta yi ta bibiyar wannan lamarin da irin wannan yanayin da ke sa a yi shakku, balle ma abin da ya kamata halifan Abbasawa ya yi shi ne ya jingina da‘awar da Ja'afar makaryaci yake yi zuwa daya daga cikin alkalai, musammamn ma da yake lamarin na daga cikin lamarin gado wanda ko da yaushe irin hakan na faruwa sau da yawa, a wannan lokacin zai zama cewa alkali na da ikon ya kafa comitin bincike, a misali sai ya kira gwaggon Imam Hasan Askari (a.s) da mahaifiyarsa, da kuyangun Imam Hasan Askari daga banu Hashim, sannan ya saurarai maganganunusu, ya dawwana shedarsu sannan komai ya zo karshe. Amma fitar wannan lamarin daga hannun alkali tare da cewa abin da ya shafi shi ne, kari a kan matakin da azzalumar hukuma ta dauka kamar yadda bayaninsa ya gabata, dukkanin wannan na tabbatar da cewa hukuma na da tabbaci kan cewa mahadin da aka yi alkawari shi ne zurin sarka na karshe daga cikin zuriya tsarkakakka wanda ba zai taba yiyuwa sarkar ta tsinke daga kan Imami na goma sha daya Imam Askari (a.s) ba, musamman ma da yake hadisai masu yawa sun zo ta bangaren kowa inda Manzon Allah (s.a.w) yake cewa: “lalle su biyun nan: ma’ana kur’ani da Ahlulbaiti (a.s) - ba za su taba rabuwa ba har sai sun iske shi a tafki”. Kuma ma’anar rashin haihuwar Imam Mahdi (a.s) ko kuma rashin wanzuwarsa a raye ita ce karewar Ahlulbaiti (a.s), kuma ba wanda ke fadin wannan daga cikin wadnda ake kira da (shuwagabannin muminai) daga Abbasawa, domin hakan karyatawa ne ga mafi girman Annanbawa, Manzonmu Muhammad (s.a.w), kai kwata-katwa ba daya daga cikin musulmai da yake fadin haka in ba wanda ya dauki karyata wannan al’amarin ba a bakin komai ba, ko wanda ya yaudari kansa a wajen yin ta’awilin hadisin nauyaya biyu ba ya karkatar da manuniyarsa zuwa ga abin tafarki mabayyani be tabbatar da shi ba.[40]

Tabbatar da haihuwar Imam Mahdi (a.s) daga bakunan malaman Ahlussuna

Sayyid Samir Umaidi yace a cikin wannan kan wannan lamarin:

Malaman fakihai da masana hadisi da mafassara kur’ani malaman tarihi da masu tahkiki da malaman adabi, da marubuta daga cikin Ahlussunna sun tabbatar da haihuwar Imam Mahdi (a.s) tabbatarwa mabayyaniya sama da sau dari, kuma sama da rabinsu sun bayyana cewa Imam Muhammad dan Hasan Al-Mahdi (aj) shi ne shi ne limamain da aka yi alkawarin zai bayyana a kardshen zamani.

Kuma hakikana jeranta wadannan maganganun bisa shekarun rasuwar ma’abotan su, sai na samu cewa lokacin rayuwarsu ya hade da juna, ta yadda yin zamani daya da wanda aka gabace shi da kuma wanda ya gabata ba zai zama abu mai wahala ba. Wanna kuma tun daga zamanin gajeriyar fakuwa har zuwa wannan lokacin namu, kuma da sannu zamu ambaci maganganun da suka zo hannuna daga wasunsu daga masdarorinsu yayin da muka zo magana kanasu, tare da isuwa da ambaton sunayen wasu daga cikinsu, ba tare da fadin sunansu ba, saboda lissafosu a cikin wannan fasalin ya ci tura, ta yadda maganganunsu sun kai kimanin zantuka ishirin da tara, a cikin daya daga cikinsu (wadannan litattafan) a littafin Ilzamil Nasib ya zo cewa akwai kimanin sama da littafi dari (da aka yi magana a cikinsu kan hakan),[41] ya kake gani da za a ce mu jero dukkanin maganganunsu, baki dayansu? Bisa cewa abin da zamu ambata a cikin matani yake, ba tare da mun yi nuni zuwa masdarinsa ba a hamishi (ruburn kasan takarda) ba, wannan dalili ne kan cewa mun cirato shi daga cikin litattafan shi’a imamaiyya wadanda sun rigaya a wannan fagen tare da kiyayewa wajen dauwana lambar littafi da lamba shafi da waje da kuma shekarar bugawa, ta yiyu ya zama daga cikin mafi yalwatawa a cikin wannan babin littafin “Al-Mahdil Muntazar Fi Nahjul Balaga”. Na shekh Mahdi Fakih Imani, a inda ya ambaci mutum dari da biyu daga mazajen ahlussunna wadanda suka tabbatar da hakan,[42] yana mai isuwa da ambaton sunayensu da masdarorinsu tare da juzu’in da shafukansu ba tare da bijiro da maganganunsu ba, ta yiyu ya bukaci bayyana wassidar sa zuwa gare su cikin mutukar kiyayewa, kuma hakika kimanin sunaye talatin ne suka tsere masa, kuma shi ne babbar madogarar mu, kuma ba mu iya riskar wani abu ba, domin abin da ya tsere masa wani na ya rigaye ni zuwa gare shi, har sai da rawar da na taka a cikn wannan dalilin ta zama ita ce hadawa da jarantawa a tsawon karnoni kawai.[43]

Sannan ya ambaci sunayen marubuta (128), daga cikin marubutan Ahlussunna da suka ambaci imama Mahdi (a.s) a matsayin imamina goma sha biyu da ga imaman Ahlulbaiti (a.s).

Daga cikinsa akwai wanda ya yi zamani da lokacin da aka haife shi da kuma gajeriyar fakewa kuma shedar wadannan malamai abar la’akari ce a tarihi kamar yanda aka sani, daga cikinsu akwai

Abubakar Ruyani, Muhammad dan Haruna (wanda ya rasu a shekara ta 307 a cikin littafinsa (musnad).

Ahmad dan Ibrahim dan Ali al-kindi, daga cikin daliban ibni jariri al-dabariwanda ya rasu a shekara ta (320BH).

Muhammad dan Ahmad dan Abis-Salji, Abubakar Albagdadi (wanda ya rasu a shekara ta 322) a cikin (Mawalidil A’imma) an buga shi tare da littafin (al- fusul Ashara fil gaiba) na shehul mufidi, tare da littafin (Nawadirul Rawandi) bugun Najaf Madaukakiya shekara ta (1370BH), daga cikin wadanda suke kusa da shi a zamani daga cikin masana akwai: Khawarizmi (wanda ya rasu shekara ta 387) a cikin (Mafatihul Ulum 32, 33) bugun London 1895M).

‘Yar Matsaya Tare Da Masu Musantawa

Ya bayyana a sarari daga abin da ya gabata cewa mas’alar mahdawiyyanci ma’ala ce ta akida tun kafin ta kasance mas’ala ta tarihi kuma dalilin da ke tabbatar da ita dalili ne na Akida kafin ya kasance dalili na tarihi, kuma ya bayyana a sarari cewa akwai tarin dalilan da suke tabbatar da ita kuma ya bayyana cewa tabbas boyayyen lamari na gaibu kamar irin na Imam Mahdi (a.s) a al’adance ya gaji fuskantar masu musanta shi, domin abin da ke boyuwa daga idanuwan mutane na da manufa daga manufofi, wanda abin da ake nufi da hakan kar wani daga cikin mutane ya gan shi ta yanda idan an tambayi mutane a kan sa zasu ce: ba mu ganshi ba, ko da kuwa suna daga cikin mafi kusancin mutane zuwa gare shi, kuma mun fadi cewa musantawar irin wadannan mutanen ga abin da yake boyayye ba zai zama ingantaccen dalili kan rashin samuwar abin ba, wannan ce mararraba ta asasi wacce masu musanta haihuwa da samuwar Imam Mahadi (a.s) suka fada ciki, domin su sun tafi suna ta binciken iran wannan nau’in madogarar a cikin tarihi, a yayain da suka kasa samun wani abu daga irinta (madogarar) sai suka dauke shi a matsayin dalili kan rashin haihuwa da samuwar Imam Mahdi (a.s), tamkar dai sabanin Shi’a kan lokacin da aka haifi Imam Mahdi (a.s) da sunansa da shaidar Ja'afar makaryaci baffan Imam Mahdi (a.s) ta cewa dan’uwansa ya rasu be bar magaji ba.

Kuma asasin tattaunawar mu tare da wadannan shi ne cewa hakika tafarkin nan na tarihi za a iya yin hukunci da shi kan mas’alolin da ake iya riska (da hawas guda biyar) wadanda tun daga farkon su har karshe sun faru ne a idon muruwaita da marubuta tarihi misalin waki’ar siffin da waki’ar karbala.....da sauransa, kuma ba daidai ba ne a hukunta mas’alolin gaibu na akida da wannan ma’aunin (na ruwayar tarihi) kan asalin samuwarsu ba,[44] kuma wannan lamarin na da hasken da ake iya riska a wajen zababbabun mutane ta yadda, da za a tambayi mutane game gari kan wannan lamarin da sun musanta shi. To ta yaya kuma zamu dauki musanatawar game gari daga mutane a matsayin dalilikan rashin samuwar wani lamarin da masu shi tun tuni suka yi imani da cewa ba abu ne da za a iya gani ba, in ba ga daidaikun zababbaun mutane ba?

Hakika abin da ya kamata ga wanda yake so ya yi jayyaya kan mas’alar Imam Mahdi (a.s) ya fara ne tun daga tushen mas’alar ta akida ba ya dauke ta daga wani yankin ta da ya danganci tarihi ba, domin lamari ne da ya zama, da gangan ake so ya zama boyayye a asirce daga idanuwan mutane mafiya kusanci, ta yadda da ba za a rasa samun sabani a kan wasu bangarorin lamarin ba, na daga irin sabani da aka samu kan lokacin haihuwar Imam da sabani kan sunan mahiafiyarsa, kuma sheda irin shedar Ja’afar makaryaci ba zata cutar ba, domin a dabi’anci amsar da za a bayar a irin wannan yanayin ita ce: hakika sabanin kan shekarar haihuwa da sunan mahaifiya, wannan abu ne na dabi’a a sarari sakamomakon dagewar Imam Hasan Al-askari kan boye yadda lamarin yake dalla-dalla cikakkiyar buyewa daga idanun mafiya kusanci makusanta, Don toshe kafar isar labarin zuwa mahukunta Abbasawa, kamar yadda shedar da Ja'afar makaryaci ya bayar kan cewa dan’uwansa ya rasu be bar baya ba (wato be bar da ko ‘ya ba), ta faru ne sakamakun haka, ta yadda Imam Hasan Al’askari ya so ya boye haihuwar dan’sa ga dan’uwansa, sai Al’amarin ya zama a wajensa kai ka ce Imam ba shi da magaji a baynasa kuma wannan matakin da Imam ya dauka a kan dan’uwansa ya yi daidai da hankali ko da kuwa dan’uwan na sa be zama makaryaci da aka yi masa sheda da fasikanci ba, ta yaya kuwa!, ballantana ma an shedi Ja'afar makaryaci da yin haka.[45]

Kebance-kebancenna biyu Imamamanci a kananan shekaru

Daga cikin abin da ke damfare da imamancin Imam Mahdi (a.s) a wajen Ahlulbaiti (a.s) kudurcewar su da imamanci Imam mahda (a.s) tun yana da karancin shekaru (yana yaro), kuma wadannan kebance-kebance wani lokaci mun kalle su da mahangar musulunci da nufin kafa hujja da ije abin da zai yuyi a ije shi na daga ishkali a addinance, wani lokaci kuma mukan kalla su da mahamgar hakika da bayanin cewa lalle wannan imamancin imamanci ne na gaskiya da ya tattaro dukkanin abubuwan da suka tabbatar masa da nagarta gamsashshiya kuma ba imamanci ba ne na rayawa ko na jeka-na-yi-ka ba.

Kuma Idan muka kalle shi da mahanga ta musulunci zamu ga yazama larura mu tantance mas’alar imamanci tun a farko da cewa shin ita mas’ala ce ta akida?ko kuma mas’alar shari’a ce? Idan ta kasance mas’alar akida kamar yadda Shi’a suka kudurce zamu ga kur’anina bayyana tabbatuwar Annabtar karamin yaro a sari -wacce ita mas’ala ce ta akida- Allah madaukakin sarki ya ce: {ya Yahaya ka riki littafi da karfi kuma mun ba shi hukunci yana dan yaro}[46]

Idan kuma mas’alar ta kasnce ta shar’a to lalleyana daga cikin fayyatattun lamuran musulunci cewa an kange yaro, kuma duk wanda aka kange shi to ya rasa walicci a kan kansa, kenan ta yaya zai iya zama waliyyin waninsa don haka waliccin yaro ba zai tabbata ba kenan.

Hakika musulmai sun yi sabani a cikin wannan mas’alar, ita makarantar mazhabobi hudu ta sanya halifanci da imamanci da shugabanci daga cikin sha’anin shari’a da ayyukan mukallafai, a yayin da makarantar Ahlulbaiti (a.s) ta yi imani da cewa wannan mas’ala ce ta akida kuma tana daga cikin tushen addinin da take daga cikin sha’anin ubangijin talikai, kuma ba ta daga cikin abin da ya kebanci mukallafai kuma ba ta gada cikin abin da ya kebanci ayyukan bayi, don haka makarantar Ahlulbaiti (a.s) ta yi imanin da imamancin yaro na wasu adadi daga Imamai, wanda daga cikinsu akwai Imam Mahdi (a.s), saboda haka akidar ta dace da abin da makarantar Ahlulbaiti (a.s) ta yi imani da shi a wannan mahallin ba wani ishkali da zai zo mata ta bangaren akida mutukar karara kur’ani ya tabbatar da Annabci Annabi Yahaya (a.s) yana yaro, haka ma basu ishkali ta bangaren shari’a mutukar dai a mahangar Ahlulbaiti (a.s) wannan mas’alar ta fita daga iyakar shari’a ta fada shingen akida, kuma hukuncin shari’a na babin kange yaro tana danbbakuwa sannan tana gudana ne kan mukallafai, kuma ba ta dabbakuwa kan Allah Ta'ala, domin ita shari’a dakon Allah Ta'ala ce da ya dora wa mukallafai.

Da haka ne zai bayyana a sarari cewa, da muka kafa hujja da Annabcin Annabi Yahaya (a.s) abin da muke nufi shi ne, mu yi bayanin cewa, Imamanci kamar Annabta yake shi ma mas’ala ce ta Akida kuma lalle ita mas’alar akida ba ta doruwa kan kiyasin (wato ma’aunin) mutane, ballantana ma ba ta doruwa hatta a kan kiyasin shari’ar da ta zo don ta tsara rayuwar mukallafai, don haka be inganta a dabbaka ta a kan ubangijin talikai ba, domin Annabtar Annabi Yahaya (a.s) tana fa’dantar da mu cewa lalle mas’alar Akida ta tsayu ne kan dalili da hujja, idan hujja ta akida ta tsayu kan imamancin yaro karami, babu makawa sai mun yi imani da ita kamar yanda muka yi imani da annabcin yaro karami a yayin da dalili na akida ya tsayu a kanta, a wannan lokaci ba shi da ma’ana a ce kafa hujja da annabcin Annabi Yahaya (a.s) ba shi da mahalli, domin an anbace shi a sarari a cikin kur’ani sabanin mas’alar Imam Mahdi (a.s).

Daganan ne ibni Hajar Askalani Al-haisami shi da makamancisa suka kalubalanci imamancin Imam Mahdi (a.s) da cewa ba ta da asasi kwata-kwata. A yayin da ya rubuta hakan da salon be dace ba,yana mai cewa: “sannan abin da ya tabbata a shari’a mai tsarki lalle waliccin yaro baya inganta, ta yaya ya yiyu ga wadannan wawayen su yi da’awar imamancin dan shekara biyar ......”[47]

Hakika ya bayyana cewa wannan ba ya daga cikin abin da shari’a ta tabbatar kadaidai yana daga cikin abin da fikihun su ya tabbatar wanda be inganta su lazimta mana shi ba.(Wato su hukunta mu da shi ba).

Kuma idan muka kalli lamarin ta bangaren Tarihiza mu samu cewa lalle Mahdi (a.s) ya gaji babansa a shugabancin musulmai yana dan shekara biyar, kuma wannan yana nufin lalle ya kasance Imami da dukkanin abin da imamanci ya tattaro na tunani da ruhi tun da wurwuri a cikin rayuwarsa madaukakiya.

Sayyid shahid Assadr yana fadi a kan wannan lamarin imamanci a kananan shekaru kanana a sarari lamarin da da dama daga cikin mahaifan Imaman Ahlulbaiti (a.s) suka rigaye shi a kai, ka ga Imam Muhammad dan Ali Al-jawad, ya hau imamanci yana dan shekara takwas a rayuwarsa[48] , kuma Imam Ali dan Muhammad Al-hadi (a.s) ya karbi imamanci yana dan shekara tara[49] a rayuwarsa, kuma Imam abu Muhammad Hasan Al-askari (a.s)[50] mahaifinimam Mahdi (a.s), ya karbi jagoranci yan adan shekara ashirin da biyu, idan an lura za a ga cewa rike mukamin imamanci da karancin shekaru ya kai kokoluwarsa da matuka a cikin Imam Mahdi (a.s) da Imam Jawad (a.s), kuma mun ambace ta da mabayyanin abu wato abu na sarari wanda da aka saba gani saboda idan aka danganta ta da wani adadi na mahaifan Imam Mahdi (a.s) tana tabbatar mana da wani abu na sarari na ilimi da musulmai suka rayu da shi, kuma suka kiyaye shi a cikin gogayyar rayuwa tare da Imami da wannan yanayin ko wancen. Kuma ba zai yiyu a nemi mu tabbatar da wani abuna sarari ba wanda yake mafi bayyana kuma mafi karfi fiye da gogayyar al’umma ba,[51] kuma da sannu zamu bayyana haka bisa jeri mai zuwa.

Imamanci Imami daga Ahlulbaiti (a.s) be zamo wani bangare daga bangarorin hukuma ba, kuma be zama irin iko ko mulkin da ke ciratuwa daga mahaifi zuwa da ba, irin wanda tsarin mulki ke ba shi kariya, kamar imamancin halifofin fadimawa da halifancin abbasawa ba, kadai (irin wannan ikon) ya kasance yana tabbata ta hanyar samun biyayya daga mutane ta hanyar wakilansa da mutane masu yawa ke bi tahanyar yin tasiri a zukatan mutane da da gamsar da tunaninsu a kan wannan tsarin da nuna sun cancanci shugabancin musulunci da jagorancin sa ta bangaren ruhi da tunani.

Hakika wannan tsarin wakilcin da mutane ke bi tun a farkon musulunici aka gina shi, sannan ya girmama ya yadu a lokacin Imam Bakir da Sadik (a.s), kuma makarantar da wadannan Imamai biyu suka kafa ta wayi gari a cikin wannan tsarin a tana dauke da wani tunanu faffada wanda ya yadu a cikin a duniyar musulmai, kuma wannan tsari ya tattaro darurawan fakihai da malaman Kalam da na tafsiri da ma malamai a cikin fagagen lilmi Musulnci da na Dan’adam din da aka sani a waccen zamanin, har sai da Hasan dan Aliyyul Washa ya ce: hakika na shiga masallacin kufa sai na ga shehunnai[52] dari tara dukkaninsu suna cewa Ja'afar dan Muhammad (a.s) ya zantar da mu.

Hakika sharadan da wannan makarantar ta doru a kan su ita da abin da yake kamantata na daga wakilcin mutane a cikin marayar al’ummar musulmi, sun yi imani da su kuma suna kayyadantuwa da abin da suka kunsa wajen ayyana Imamai da sanin cancantarsa a matsayin Imami, an gindaya sharadai masu tsanani, domin sun yi imani da cewa Imami ba zai taba zama Imami ba sai ya zama ya fi kowa ilimi a zamaninsa.[53]

Hakika wannan makarantar ita da jagorancinta na jama’a ta kasance tana gabatar da babbar fansar da kai (mabiyanta sun sadaukar da kansu sun bada jini da tsoka) a hanyar ta ta ganin ta tabbata kan akidarta ta imamanci; saboda ta kasance babar barazana a mahangar hukumar da take ci, ko da kuwa ta bangaren tunani ne kawai, al’amarin da ya sa hukumar wancen lokacin ta ci gaba da kai musu hari na kar a bar iri, sai aka kashe wanda aka kashe aka daure wanda aka daure kuma daruruwa suka mutu a cikin duhun kurkuku, kuma wannan na nufin imaninsu da imamancin Ahlulbaiti (a.s) yana jawo musu musiba,[54] kuma ba shi da wani abu da yake da shi wanda ake samun karawa ( ta wani abin duniya ) da shi face abin da mai akidantuwa da shi yake ji ko yake tsammani na kusanci da Allah Ta'ala da kuma samun matsayi a wajensa.

Hakika Imamin da wannan (tsarin na wakilcin) gugun al’umma ya tabbatar da imamancinsu, ba su kasance sun kebance kansu daga jama’ar ba, kuma ba su kai kansu can tsororruwar matsayi a cikin manyan gidaje kamar dai yadda sarakuna suke yi wa jama’arsu ba, kuma (imamai) ba su taba yarda an sa shamaki tsakanin su da jama’a (mabiyansu) ba, sai dai in hukumar da ke mulki ce ta shiga tsakanin su (da mabiya) ta hanyar jefa su (imaman) kurkuku ko nisantasu, kuma wannan abu ne da muka sani ta hanya adadi masu yawa na marawaita da masana hadisi game da ko wane daya daga cikin Imamai goma sha daya, da ma ta hanyar abin da aka cirato na daga wasikun da suka kasance tsakanin Imam da wadanda suka yi zamani da shi, da kuma tafiye-tafiyen da Imam yake yi ta wani bangaren, da kuma abin da ya kasance yana yadawa ta hanyar wakilansa a mabanbanta sasannin Duniyar musulunci da wani bangaren daban, da ma kuma abin da Shi’a suka yi sabo da shi a kansa na bibiyar yanayin da imamansu suke ciki da kai musu ziyara a madina mai haske yayin da suke dafifi zuwa gidaje masu tsarki don gudanar da faralin hajji.[55] Dukkanin wadannan a sarari sosai suna tabbatar da kaikawo mai cigaba tsakanin Imam (s.a) da wakilansa da suka yadu cikin fadin sassan duniyar musulunci bisa mabanbantan matsayinsu na daga malamai da wasunsu.

Hakika masarautar da ke ci wacce ta yi zamani da Imamai ta kasance ta na kallon su kuma tana kallon wannan shuganacin na su na ruhi a matsayin babban hadari kan samuwarsu da ikonsu, bisa wannan ne suka zage dantsensu wajen ganin sun yi kaca-kaca da wannan shugabancin kuma suka yi ta aikata munanna abubuwa saboda haka wani lokaci ma sukan nuna kekashewar zuciya da dagawa idan haka ya zame musu larura wajen kare kujerarsu ta mulki, kuma dauri da kora sun kasance abubuwan yau da gobe da su kansu Imamai[56] suka yi ta fama da su, duk da abin da hakan ke sabbabawa na jin damuwa da kyamar da masulmai da mutanen mabiya - Ahlulbaiti (a.s) - ke bayyanawa a bisa mabanbantan matsayinsu.

Idan muka kalli wadanna nukududin guda shida da idon basira wadannan suke tabbatatun abubuwa ne na tarihi, da ba shakka a cikinsu zai iya yiyuwa mu fita da sakamako kamar haka: Tabbas samuwar imamanci na wuri lamari ne a fili wanda yake da tabbacin samuwa, kuma be kasance wahami da wahamomi ba, domin imamin da ya bayyana a fage aiki yana karamin yaro ya kuma shelamta kansa a matsayin Imam na ruhi da tunani ga musulmai ba ki daya, kuma dukkanin wadannan tarin jama’ar suka zama suna yi masa biyayya a matsayin Imami, babu makawa sai ya kasance yana da wani matsayi bayyananne abin la’alari kuma ya zama yana da matsayi a ilimi da sani mai fadi sasanni kuma ya zama yana da kwarewa a fikihu da tafsiri da akida domin idan har be zama haka ba, da ba zai yiyu wannnan gungun jama’ar su yarda da imamancinsa ba, tare da cewa Imamai sun kasance a wajen da zai yiyu ga mabiyansu su su yi ma’amala tare da su kuma a yanayoyi mabanbanta zasu iya yin tasiri a rayuwarsu da ma ma’aunin mutuntakarsu. Shin kana ganin zai yiyu wani dan karamin yaro ya yi kira zuwa imamancinsa, kuma ya dora kansa a matsayin alamin musulunci - ta hanyar imamamnci - alhali yana kan ido da majiyar mutanen da suke yi masa biyayya, sai su yi imani da shi sannan su sadaukar da abu mai kima a kansa na daga abincinsu da rayuwarsu ba tare da sun kallafawa kansu gano hakikanin sha’aninsa ba, kuma ba tare yanayin imamancinsa na yarinta ya girgiza su ba, don su sami masaniya kan hakikanin matsayinsa ta hanyar gudanar da gwaji da jarraba wannan yaron Imami ba? Kuma ka kaddara cewa mutane ba su motsa wajen sanin yanayinsa ba, shin zai yiyu matsalar ta shude tsawon kwanaki da watanni ba tare da hakika ta bayyana gare su ba, dun da kai kawo da alaka ta dabi’a mai cigaba tsakanin wannan yaron da sausan mutane? Kuma shin hankali zai karbi cewa ga shi yaro ne a tunaninsa da aikinsa da gaske amma kuma hakan be tabbata akansa ta hanyar doguwar alaka ta yau da gobe ba?

Idan kuma muka kaddara cewa lalle tsayin al’ummakan imamancin Ahlulbaiti (a.s) bai bada dama su gane hakikanni lamari ba to don me ya sa masarauta mai ci ta yi shiru ba ta yi kokarin bayyana hakika ba idan har tana da riba kan hakan? Ya tsananin saukin yin hakan ga masarauta mai ci da ace Imami yaro, yaro ne shi a tunani da wayewa kamar yanda aka san yara, ya isa ya zama mafi cin nasarar hanya idan aka gabatar da wannan yaron ga Shi’arsa da wadanda ma ba Shi’arsa ba kan hakikar yadda yake, kuma ta tabbada da dalili kan rashin cancantar sa ga imamanci da shugabancin mutane a ruhi da tunani, idan har ya zama yana da wahala a kasa tabbatar da rashin cancantar mutumin da yake dan shekara arba’in ko dan shekara hamsin saboda ya kewaye sani da wani babban gwargwado a wayewar zamaninsa kan yanda ake darewa kujerar imamacni, ke nan babu wata wahala wajen tabbatar da rashin cancantar yaro na al’ada duk yanda ya kasance mai kaifin basira da hazaka kan imamanci da ma’anarsa kamar yadda Shi’a imamiyya[57] suka san shi, kuma da hakan ya kasance mafi saukin hanya (wajen kawo karshen Shi’a ) fiye da bin hanya mai murdiya da bin tafarkin yin kof daya da ta’anatin da masarautar wancen lokacin ta zaba kuma ta yi ta bi (don ta kawo karshen shi’anci).

Kadai fassarar da za a bayar kan yin shirun hukumar wancen lokaci ga barin yin wasa da lamarin[58] ita cecewa ta riski cewa imamanci tare da karancin shekaru lamari ne na gaskiya ba abu ne da aka kirkira ba.

Kuma bisa hakika hukuma ta gane haka a aikace bayan da ta yi kokarin yin wasan kura da wannan lamarin na imamanci sai ya zamana ta gaza yin komai a kai, kuma tarihi sheda ne kan wadannan kokarce-kokarcen da kuma gazawarsu[59] a daidai lokacin da ko sau daya ba a taba ba mu labarin girgizar matsayan imamancin yaro ba ko kuma aka ce Imami mai karancin shekaru ya fuskanci wani yanayi na tsanani da ya fi karfinsa ko ya sa amincin mutane da shi ya yi rauni ba.

Wannan muke nufi a lokacin da muke cewa hakika imamancin karamin yaro lamari nena hakika a rayuwar Ahlulbaiti (a.s) ba kawai rayawa ba ne kamar yadda wannan lamarin yana da tushensa da yanayoyinsa masu kamanceceniya a cikin kundin abin da aka saukar da sama wanda ya shude tsahon tarihin manzanci da shugabancin da Allah Ta'ala yake nadawa.

Kuma Yahaya (a.s) ya isa misalikan tabbacin lamarin imamancin yaro daga Ahlulbaiti (a.s) a cikin taskar ubangiji, yayin da Allah Ta'ala yake cewa: {ya Yahaya ka riki littafi da karfi kuma mun ba shi hukunci yana dan karamin yaro}[60]

A lokacin da ya tabbata cewa imamancin wanda ke da karancin shekaru lamari ne na hakika kuma ya tabbata a aikace a cikin rayuwar Ahlulbaiti (a.s) ba wata ja-in-ja da zata yi saura kan lamarin imam mahdi (a.s), da halifancin sa ga babansa a lokacin yana dan yaro[61] [62] .