• Farawa
  • Na Baya
  • 13 /
  • Na Gaba
  • Karewa
  •  
  • Gurzawa HTML
  • Gurzawa Word
  • Gurzawa PDF
  • Budawa: 2328 / Gurzawa: 395
Girma Girma Girma
mahdawiyyanci

mahdawiyyanci

Mawallafi:
Hausa

Kebance-kebancena uku: fakuwar da ta lazimci rayuwa budaddiya tare da budewar zamani.

Daga cikin abubuwan da ke danfare kuma suka kebanta da lamarin mahdawiyanci a wajen Ahlulbaiti (a.s) shi ne kudurce cewa Imam Mahdi (a.s) ya faku daga idanuwan mutane, kuma zai ci gaba da fakuwa har zuwa lokacin da Allah Ta'ala zai yi masa izini ya bayyana kuma zamu tabbatar da wannan hususiyyar (makebanciyar) a bisa marhaloli biyu:-

Ta daya: Marhalar tabbatar da yiyuwar yin d oguwar rayuwa, har zawa karshen zamani.

Hakika tushen masalar dake shafar fahimtar mahdawiyyanci a wajen Ahlulbaiti (a.s) ta na cikin abin da wannan fahimtar ta lazaimce shi na rayuwa mai tsawo tare da tsawon zamani wacce ke ci gaba da ci gabansa, kuma hakika an magance wannan mushkilar da amasoshi masu yawa da a nan zamu zo da amsoshin sayyida Shahid Sadar, hakika ya rubuta yana cewa:-

“Shin zai yiyu mutum ya rayu karnoni masu yawa kamar yadda yake dandage da wannan jagoran da ake sauraro don ya canja duniya, wanda shekarunsa madaukaka a yanzu sun haura shekara dubu daya da dari biyu da arba’in, wato kusan sun ninka kwanakin rayuwar mutum na al’ada sau 14, Wanda yake shude kowace marhala a bisa dabi’a tun daga yaranta har zuwa tsufa?

Kalmar yiyuwa a na tana da ma’ana dayan uku: yiyuwa a aikace, da yiyuwa a ilimance, da yiyuwa a mandikanace ko a falsafance.

Abin da nake nufi fa yiyuwa a aikace shi ne ya zama abu mai yiyuwa ne ta yadda zai yiyu gare ni ko gare ka ko ga wani mutum ya iya tabbatar da shi a aikace. Ka ga tafiya a kan teku, da yin nutso zuwa cen kasan kogi, da hawa kan wata abubuwa ne da suka wayi gari masu yiyuwa a aikace a yanzu haka. Kuma akwai wadanda suke yin wadannan abubuwan da wan nan yanayi n ko da wancen.

Abin da kuma na ke nufi da yiyuwar sa a ilimance: Shi ne cewa akwa wasu abubuwa da ta yiyu yin su a yanzu ba zai yiyu gare ni ko gare ka, saboda takaituwar kayayyakin da muke rayuwa da su a wannan zamanini, amma ba a samu wani abu na ilimi ba, haka ma kuma ilimi ba ya yin nuni bisa ga mafuskantarsa mai motsawa ta nan gaba cewa akwai wata alama da ke musanta yiyuwar wadannan abubuwan, idan aka sami yanayi da wasu kayayyakin rayuwa na musamman, a ce mutum ya hau kan tauraron zuhra, ba wani abu na ilimi da ya musanta yiyuwarsa, ballantana ma mafsukantar ilimi a yanzu na yin nuni kan yiyuwar hakan, duk da cewa zuwan a yanzu ba abu ne mai yiyuwa a gare ni ko gare ka ba, domin banabancin dake tsakanin zuwa duniyar wata da zuwa duniyar zuhra banbancin taki ne (kawai), ba abin da zai sa a je zuhra ( B enus) face kai wa ga matakin rage wahalar da ta samo asali daga kasancewar ta fi nisa, don haka zuwa duniyar zuhra abu ne mai yiyuwa a ilimance ko da kuwa a yanzu bai yiwu a aikace ba,[63] a kasin haka, dangane da yiwuwar zuwa doron kaskon duniyar rana a cikin sararin samaniya, tabbas ba abu ne mai yuwuwa ba a ilimance, da ma’anar cewa lalle ilimi ba shi da fatan faruwar haka, domin ba a da fatan faruwar haka a ilimance da jarrabance wato a gwajence ( edperiment ) cewa za a iya yin wani sulke da zai iya yin kariya daga konewa da zafin rana, wacce (mafi girma atom ce) wato babbar duniya ce da take ruruwa da mafi girman zafin da zai iya darsuwa a zuciyar Dan’adam.

Abin da na ke nufi da yiyuwar sa a mandikance ko a falsafance shi ne hankali ba shi da wani abu da yake riska na dokoki a da cen - ma’ana dokanin da suka gabaci gwaji- da suke tabbatar da kore wani abu ko yin hukunci da rashin yiwuwarsa.

Ka ga samuwar lemon zaki guda uku da ake so a raba su biyu kuma ba tare da an yanka wani daga cikinsu gunduwa biyu ba, ba abu ne da zai yuwa a mandikance ba, domin hankali yana riska kafin ya gwada yin kowane abu cewa lalle uku adadi ne daiwa - (wato Odd) (kishiyar biwa wato Eben ) - ba biwa ba ne, ba zai yiyu a iya raba shi biyu ba, domin raba shi biyu (daidai ba tare da yankawa ba) yana nufin cewa shi biwa ne sai ya zama daiwa kuma biwa a lokaci guda, kuma wannan tufka da warwara ce, ita kuma tukafa da warwara ba zata taba yuwuwa ba a hankalce (mandikance) sai dai shigar mutum cikin wuta ba tare da ya kone ba da hawa kaskon rana ko zuwa duniyarta ba tare da rana ta kona mutum da zafinta ba ba abu ne korarre ba a mahangar mandiki, domin ba cin karo a tsakani, a cikin kaddara cewa zafi baya yin naso daga jiki mai zafi zuwa wanda be kai shi zafi ba, kadai dai ya sabawa gwajejeniyar da ta tabbatar da cewo jiki mafi zafi yana yin naso zuwa jikin da be kai shi zafi ba, har sai sun daidaita zafinsu ya zama daya.

Ta haka ne zamu san cewa yiwuwa ta mandiki (hankali) ta fi fadi fiye da yiwuwar ilimi, ita kuma wannan (ta ilimi) ta fi fadi fiye da ta aiki.

Kuma babu shakka cewa tsahon rayuwar Imam mutum zuwa dubban shekaru abu ne mai yiyuwa a mandikance (hankalce) domin wannan ba korarren abu ba ne ta fuskacin mahangar hankali zalla ba, kuma a cikin kaddara wani abu makamancin haka babu wani cin karo, domin rayuwa kamar tadda aka fahimce ta, lalle ba ta lazimtar mutuwar gaggawa, (wato ba ta kunshe da mutuwar gaggawa) kuma ba wata tattannawa da ja-in-ja kan haka.

Kamar yadda ba kokwanto kuma ba ja kan cewa wannan doguwar rayuwar ba aba ce da ba zata yuwu a aikace ba kamar yadda ya yiyu a yi nutso can cikin kuryar kogi da hawa kaskon wata, wannan kuwa saboda ilimi yana da kayayyakinsa da abubuwan aikin da ake bukata a yanzu a kintse, haka ma kuma kasantuwar Dan’adam ya kai ci gaban da ya ba shi damar ya iya yin gwajin a kan jikin mutum a wannan zamanin, hakan ba zai sa ya iya tsawaita rayuwar mutum zuwa daruruwan shekaru ba, don haka ne ma zamu ga mutanen da suka fi kowa kwadayin rayuwa da kuma iko kan sarrafa tanade-tanade da damar da suke da ita ta ilimi ba ta sa su samu tsawon rayuwa sai gwargwadon da ka saba.

Amma yiwuwa ta ilimi, a yau a ilimance ba a samu wani da ya kafa dalili ya kuma fayyace kore yiwuwar hakan ta bangaren nazari ba[64] Kuma wannan binceke ne wanda a hakika yana da alaka da yadda aka fassara yadda hakikar sakar manyanta da tsufa suke a wajen Dan’adam, shin wannan lamarin yana yin bayanin wata doka ta dabi’a da ta tilasta sakar jikin Dan’adam da jijiyoyinsa - bayan sun kai mutuka wajen nuna (manyantaka) - su rika bushewa a hankali a hankali har su wayi gari suna da karancin ikon yin aiki wajen ci gaba da aiki har zuwa lokacin da zasu dena aiki baki daya, ko da kuwa mun raba ta daga tasirin ko wani irin abu da ko wane irin dalili daga wajen jiki? Ko kuma wannan bushewar da cin karon da ke cikin tanadin sakar jiki da jijiyoyinsa wajen yin ayyuka a cikin sa, yana kasancewa ne sakamakon tashi-fadi da abubuwan da ke wajen jiki na daka kwayoyin cutuka ko guba da suke shiga cikin jiki ta hanyar abin da mutum yake ci na daga abinci mai maiko ko wani abu daban?.

Wannan tambaya ce da ilimi ke yi wa kansa a yau, kuma ya tsaya kai da fata wajen bada amsa kuma bai gushe ba sai da ya bada sama amsa da daya a bisa asasin matakin ilimi.

Idan kuma muka dauki bangaren mahangar ilimin da ta fassara manyanta da raunin tsufa ta siffanta shi da cewa hakan na faruwa a sakamakon tashi fadi da gogayyar da jiki yake yi tare da wasu ayyanannun abubuwan da ke waje, a nazarce ke nan wannan yana nufin cewa idan muka raba sakar jikin mutum, wacce ita ke samar da jikin mutum daga ainihin wadannan abubuwan da suke da tasiri (wajen sa mutum ya tsufa) to lalle rayuwar mutum zata yi tsaho ta wuce matakin tsufa daga baya sai ta yi galaba a kansa daga karshe.

Idan kuma muka yi riko da daya mahangar da ta karkata kan cewa tsufa doka ce ta dabi’a ga tsarin kwayoyin da garkuwar jiki shi a kan kansa, da ma’anar cewa hakika shi jiki a cikin hanjinsa yana dauke da kwayar da zata kawo karshensa ba makawa, bisa shudewa daga marhalar girma da tsufa tare da tukewa zuwa ga mutuwa.

Nake cewa: idan muka yi duba zuwa wannan mahangar wannan ba ya nufin rashin yiyuwar kaddara kowane irin sauyi a wannan doka ta dabi’a, balle ma a bisa tsammanin samuwar ta - doka ce mai chanja wa; domin a cikin rayuwarmu ta yau da kullum muna samu, kuma saboda malamai a dakin gwaje-gwajensu na ilimi suna ganin cewa hakika tsufa a matsayinsa na tsarin jikin Dan’adam ba shi da lokaci ta yiyu ya zo wa mutum da wuri, kuma ta yiyu ya yi jinkirin zuwa ya ki kuma bayana sai bayan tsahon wai lokaci, har yakan zama cewa mutum ya yi shekaru masu yawa amma yana da danyantakar gabban jiki, kuma alamun manyantaka ba su bayyana a jikinsa ba, kamar yadda likitoci suka bayyana haka[65] Ballantana ma hakika malamai, a aikace sun iya yin amfani da yanayin yadda wannan dokar da dabi’ar da muke magana kanta take canajawa, sai suka tsawaita rayuwar wasu daga cikin dabbobi sau daruruwan ninki idan ka kwatanta da rayuwar ta ta asali; kuma sun yi wannan ne ta hanyar halittar yanayoyi da abubuwan da suka temaka wajen jinkirta mothin dokokin tsufa.

Da wannan ya tabbata a ilimance cewa lalle jinkirta ko tsawaita wannan dokar ta hanyar samar da yanayi da sababai na musamman lamari ne mai yiyuwa, kuma idan har ilimi bai iya jinkirta wannan ga wasu daga cikin halittu ba kamar mutum, to wannan be kasance ba face sai don bambanci daraja ko mataki da ke tsakanin wahalar gudanar da wannan lamarin kan Dan’adam, da kuma wahalar yin hakan danagane da sauaran halittu. Kuma wannan na nufi cewa lalle ilimi ta nahiyar nazari da mahanga bisa gwargwadon abin da mafuskantarsa (hasashensa) mai motsi (ta nan gaba) take bayyanawa, kwata - kwata a wajensa ba abin da ke nuna rashin yiwuwar tsawaita rayuwar Dan’adam, daidai ne mun fassara tsufa da ma’anar tashi-fadi ga cakudedeniyar da ke yin tasisi a cikin jiki daga waje ko kuma yana kasancewa ne sakamokon doka ta dabi’a da ke damfare da kwayoyi rayuwar ko halittar jiki wacce take shimfida wa jiki hanya zuwa mutuwa da karewa.

Kuma daga wannan zamu raiarayo cewa hakika tsawon rayuwa gun Dan’adam da wanzuwarsa karnoni masu yawa abu ne mai yiwuwa a hankalce kuma mai yiwuwa ne a ilimance, sai dai har yanzu be gushe ba (yana cikin abin da) be yiwuwu a ilimance ba, sai dai hasashen ilimi na tunkarar hanyar tabbatar wannan abu mai yiwuwa a kan doguwar hanya ta tabbatawa a aikace.

Bisa wannan hasken (da bayanin da ya gabata), zamu dauki rayuwar Imam Mahdi (a.s) da abin da ke kewaye da ita na daga tambayoyi da neman karin bayani, sannan kuma mu yi hasashe kan cewa:

Bayan tabbatar yuwuwar yin rayuwa mai tsawo a hankalce da ilimance kuma ya tabbata cewa ilimi na tunkarar hanyarsa ta chanja wannan yiyuwar ta mahanga zuwa yiyuwa ta aiwatarwa (a aikace) a hankali a hankali ba wata ma’ana ta yin mamaki da zasu yi saura in banda (yin mamaki kan cewa) Imam Mahdi (a.s) ya rigayi shi kansa ilimin. (wato tun kafin ilimi ya ma fara tunanin yiyuwar haka balle ya kai ga gano shi a nazari har zuwa zartar da shi a aikace ta hanyar gwada shi a kan wasu dabbobi, tuni hakan ya wakana a cikin rayuwar Imam Mahdi (a.s) a aikace), sai ya zama abin da ke yiyuwa a nazarce ya zamo mai yiyuwa a aikace a cikin shi kansa Imam Mahdi (a.s) tun kafin ilimi a cikin ci gabansa ya kai matsayin iya yin wannan canjin a aikace, ya zama kamar wanda ya rigayi ilimi wajen gano maganin meningitis ( cutar da ke kama fata wacce ta ke kaiwa cutar ta kai ga kwakwalwa a sakamakon birus ko kumburi ) ko maganin ciwon daji.

To idan kuma mas’alar ta kasance ita ce cewa ta yaya aka yi musulunci - wanda ya tsara rayuwar wannan shugaba da ake sauraro (a.s) - ya zama ya rigayi motsin ilimi a fagen chajawa?

Amsaita ce: Ba a nan ne kadai musulunci ya rigayi motsin ilimi ba.

Ashe shari’ara musulunci a dunkule ba ta rigayi motsin ilimi da ci gaban dabi’ana tunanin Dan’adam da karnoni masu yawa ba?[66]

Ashe ba ta yi kira da muryar aza harsashin dabbakawar da Dan’adam be kai ga cin musu a motsinsana ci gaba, sai bayan daruruwan shekaru ba?

Ashe ba ta zo da shar’o’in da suke cike da hakimar da Dan’adam be iya riskar surrikanta kume be iya fuskar hikimar da ke cikinsu ba har sai bayan wani dan takina zamani ba? Ashe sakonsama be yaye sirrika samuwar da ba su taba darsuwa a zukatan mutane ba, sannan kuma ilimi ya zo yana tabbadar da su yana karfafafarau ba?

Idan har mun yi imani da dukkanin wadannan to don me zamu rika ganin cewa abu ne mai wuya wanda ya aiko wadannan sakonnin na Manzonci - tsarki ya tabbata a gare shi - a ce ya rigayi imini wajen tsarawa da zartar da shekarun Imam Mahdi (a.s),[67] alhali a ana ban yi magan kan komai ba sai kan lamarin gabata wanda mu kan mu kai tsaye zamu iya riskarsa? Kuma zamu iya karo wasu tabbatattun abubuwa da suka gabata wadanda shi dakansa sakon da ya zo daga sama ne yake ba mu labarinsu. (a nan Karin Magana ce marubucin ya yi, Ma’ana wadanda muke samun labarinsu a cikin sakon day a zo daga sama).

Misalin haka: Sama ta bada labarin cewa an yi tafiya da Annabi Muhammadu (s.a.w) da daddare daga masallacin Harami zuwa masallacin Aksa, kuma wannan tafiyar daren[68] idan muka so mu fahimce ta a karkashin gewayen dokokin dabi’a, tabbas bisa hakika yana bada labari ne ta hanyar yin amfani da dokokin na dabi’a, bisa yanayin da ba a bawa ilimi damar ya yi bincike da tahkiki[69] a kanta ba, sai bayan darururwan shekaru, to ainihin wannan kwarewar ta ubangiji da ta bawa Manzon Allah (s.a.w) damar motsawa cikin sauri tun kafin a bawa ilimi wannan damar, ita ce wacce ta bawa na karshen halifofin da a ka yi nassi da su wannan doguwar rayuwa kafin a bawa ilimi damar yin tahkiki a kan hakan.

Na’am, wannan rayuwa mai tsawo da Allah Ta'ala ya bawa mai ceto sha sauraro, da alama abin ban mamaki ne bisa iyakon abin da akasaba a rayuwar mutane, har zuwa yau din nan, haka ma (akwai ban mamaki a cikin) abin da aka cimma zuwa yanzu ta hanaya gogayyar malamai.

Saidai , ashe a ce wannan rawar ta musamman da aka tanade ta saboda shi waccce ita ake so wannan mai ceton ya taka, shin ita ma (wannan rawar ta kasance ne) bisa iyakoki da dokokin da mutane suka saba da su a rayuwarsu take, (kuma ta yi kama) da irin abubuwan da suka faru da su a tsawon tarihi?

Ashe ba a jingina masa aikin kawo canji a duniya ba da sakegina ta bisa ci gaba bisa asasin gaskiya da adalci ba?

To don me zamu yi mamaki idan share hanyar zuwan wannan lokacin taka wannan babbar rawa ya siffatu da wasu abubuwana ban mamaki wadanda suka sabawa abin da aka saba kamar tsawon rayuwa mai ceto, sha sauraro? Hakika bakuntar (wato ban mamakin) wadannan lamurran da fitar su daga zagayen abin da aka saba duk yanda ya kai, ba yadda za a yi su wuce bakuntar (ban mamakin) wannan rawar mai girma wacce ya wajaba ga wanda aka yi alkawwarin zuwansa ya taka!. Idan mun kasance mun yarda da yiyuwar wannan rawar tilo, wato wannan aikin da babu irinsa[70] a tsawon tarihi, tare da cewa babu wata rawa irin ta a tarihi dan’adam, to don me ya sa ba zamu yarda da yiyuwar wannan rayuuwa mai tsawo ba wacce ba mu sami wata rayuwa mai tsawo makamancinta a irin yadda muka saba rayuwa ba? Kuma ban sani ba shin wannan ya kafu ne bisa sudufa (katsaham) ta yanda zai zama an sami wasu mutane guda biyu wadanda su su kadai ne zasu zazzage barnan da ke cikin tsarin rayuwar dan’adam su sake gina ta daga farko, sai ya zama ko wanne daga cikinsu ya rayu rayuwa mai tsawon da ta wuce tsawon kwanakin rayuwarmu irin wacce muka saba ninkin ba ninki?

Na farkon su: ya taka tasa rawar a farkon zamani da danadam ya rayu, wanda shi ne Annabni Nuhu (a.s), wanda kur’ani ya bada labarin sa,[71] cewa ya zauna cikin mutanen sa shekara gudu ba hamsin, kuma aka ba shi ikon sake gina wata sabuwar duniya daga farko.

Na biyunsu kuma: da sannu zai yina sa aikin nan gaba kuma shi ne Mahdi (a.s) wanda zuwa yanzu ya zauna cikin mutanensa sama da shekara dubu kuma idan ranar da aka yi masa alkawar ta cika da sannau za a ba shi dama da ya kuma yi wa duniya sabon gini fil.

To don me ya sa zamu yarda da labarin annabi Nuhu wanda ya kusa shekara dubu a kalla, amma ba za mu yarda da na Imam Mahdi (a.s) ba?[72]

Kuma zuwa yanzu mun rigaya mun san cewa: lalle rayuwa mai tsaho mai yiwuwa ce a ilimance, sai dai idan muka kaddara cewa ba abu ne mai miyuwa ba, kuma dokar tsufa da girma ba zai taba yiyuwa ga dan’adam din yau, kuma ba zai yiwu ma ga ci gaban da yake samu ya yi galaba kan dokar tsufa ba, haka ma canjawar yanayinsa da sharuddansa, to me hakan yake nufi? Wannan na nufin cewa tsawon kwanakin mutum kamar - Nuhu ko Mahdi (a.s) - har karnoni masu yawa, ya kasance rayuwa ce wacce take bisa sabanin dokokin dabi’ar da ilimi ya tabbatar da ita, ta hanyar gwaji, da karantar abubuwa a zamanance, da wannan zai zama cewa wannan mu’ujizar ta bata dokar dabi’a a wani yanayi ayyananne, don kare rayuwar mutum, wanda aka dorawa kare sakon sama kuma wannan mu’ujizar ba tilo ba ce a ire-irenta, ko kuma ba abin mamaki ba ne a wajen akidar musulmin da wance ta samo asali daga kur’ani da sunna,[73] dokar tsufa da manyantaka ba ta fi karfin dokar nason da zafi yake dauka daga wani jiki zuwa wani jikin da be kai shi zafi har su daidaita a - zafi - ba, sai ga shi Allah Ta'ala ya tashi dokar daga aiki don ya kare rayuwar Annabi Ibrahim (a.s) a yayayin da ya zama kadai hanyar da ta rage wajen kare rayuwar Annabi Ibrahim (a.s) ita ce ta hanyar bata wannan dokar, don haka sai aka ce da wuta a yayin da aka wurga shi a ciki, {sai muka ce ya ke wuta ki kasaance sanyi da aminci ga Annabi Ibrahim (a.s)}[74] sai ya fita daga cikinta kamar yadda ya shiga da koshin lafiya ba wata ba abin da ya same shi, kari a kan cewa akwai da yawa daga cikin dokokin dabi’a da aka bata aikinsu don kare rayuwar wasu mutane daga Annabawa da Hujjujin Allah Ta'ala a bayan kasa, an tsaga tafki ga Annabi musa (a.s),[75] kuma an kamantawa rumawa cewa Annabi isa (a.s)[76] suka kama alhali ba shi suka kama ba, kuma Annabi Muhammadu (s.a.w), ya fita daga gidansa alhali yana kewaye da dakarun kuraishawa wadanda suka shafe awannai suna dakonsa don su kai masa farmaki, sai Allah Ta'ala ya suturta shi daga idanuwansu a lokacin da yake tafiya tsakatsakinsu[77] dukkanin wadannan yanayoyin misali ne na dokokin dabi’ar da aka karya domiin kare rayuwar mutum, hikimar Allah Ta'ala ta zartar da a kare ruyuwarsa, kenan me zai hana dokar tsufa ita ma ta kasance daga cikin wadannan dokokin.

Kuma ta yiyu mu iya fita daga wannan da gamammiyar fahimta, shi ne cewa duk lokacin da kiyaye rayuwar hujjar Allah Ta'ala a bayan kasa ta dogara kan karya dokar dabi’a kuma ci gaban rayuwarsa ya zama larura domin zartar da abin da aka sa shi, sai ikon Ubangiji ya yi aikinsa wajen karya dokar dabi’a domin ya sami damar isar da abin da aka dora masa, haka ma akasin haka, idan bawan Allah Ta'ala ya gama aikin da ya hau kansa, wanda Ubangiji ya dora masa, tabbas da sannu zai gamu da ajalinsa ya rasu ko ya yi shahada, daidai da yadda dokoki dabi’a suke.

Kumaa al’adance dangane da wannan fahimtar da ta game zamu iya fuskanta tambaya mai zuwa: ta yaya za a iya karya dokar dabi’a?[78] kuma ta yaya za iya raba alakar larura wacce dabi’a ta tsayu a akai? Shin wannan ba kishiyantar ilimi ba newanda ya gano Wannan dokar ta dabi’a kuma ya iyakance wadannan alakokin na ba makawa bisa asasin gwaji da bin diddigi?

Amsa: Tabbas shi kansa ilimi ya bada amasar wannan tambayar ta hanyar sassautowa da yin kasa-kasa da ya yi daga mahangar tilasaci a dokar dabi’a, bayanin haka:- hakika ilimi ne ya ke gano dokokin dabi’a bisa asasin gwaji da bin diddigi, a yayin da ya kore faruwar wani abu na dabi’a a daidai faruwar wani abu to wannan abin da ya faru yana yin nuni kan doka ta dani’a, wacce ita ce duk lokacin da abu kaza na farko ya faru to abu kaza na biyu ma zai faru bayansa, duk da cewa shi ilimi a irin wannan doka ta dabi’a ba ya kaddara samuwar alaka ta dabi’a tsakanin abubuwan guda biyu irin alakar da ta samo asali daga ainihin abu na farko da ainihin na biyun, domin ba makawar da ke tsakaninsu ko a ce domin (larurur da ke tsakaninsu) yanayi ne na gaibu wanda ba za a iya gano ta ta hanyar gwaji da bin diddigin ilimi ba, don haka ma hakika yaren ilimin zamani, yana karfafa cewa hakika dokar dabi’a - kamar yanda ilimi ya bayyana ta - ba ta magana kan doka ta larura (ta ba makawa), balle ma yana magana ne kan kaddarawa mai ci gaba, tsakanin abubuwa biyu,[79] dan haka idan mu’ujiza ta zo ta shiga tsakanin wadannan abubuwan guda biyu ta raba su da juna hakan ba raba alaka ta ba kamawa tsakanin abubuwa biyu ba ne.

Hakika, Tabbasita mu’ujiza bisa yadda aka fahimce ta a addinance ta wayi gari a cikin hasken harshen ilimin zamani ana fahimtar ta da daraja (a mataki) mafi girma fiye da yadda take a karkashin inuwar mahangar ta ta musamman irin ta mutanen da zuwa ga alaka ta sababi.

Hakika tsohuwar fuskar mahanga na ganin (na kaddara) cewa ko wanne daga abubuwan nan guda biyu samuwar dayan su na tabbatar da samuwar na biyun don haka alakar dake tsakaninsu alaka ce ta larura (ba makawa), larura kuma tana nufin ba zai taba yiyuwa dayansu ya rabu da dayan ba, sai dai wannan alakar ta juye ta canja zani a mahangar ilimin yanzu ta zamo dokar gwamuwa ko bibiya na ko da yaushe[80] tsakanin abubun biyu, ba tare da kaddara wannan larurar ta gaibu ba.

Da wannan ne mu’ujiza ta wayi gari ana kallonta a matsayin yanayina togaciya ga wannan salon na haduwa ko bibiya ba tare da ta ci karo da wata larura ko ta kai mu ga abin da ba zai yiyu ba.

Amma bisa mahangar (usasul mandikiyya lil istikra’i) tushen hankalin bibiya,[81] mu mun yi ittafiki da sabuwar mahangar ilimi cewa shi bin diddgi, ba ya kafa hujja kan alakar larura tsakanin bayyanannun abubuwa guda biyu, sai dai muna ganin hakan na yin nuni kan samuwar wata fassara mai tarayyaya ba da ma’anar ci gaban maimatuwar gwamayya ko bibiya tsakanin abubun biyu ba, kuma wannan fassarar ta gamayya kamar yadda tushen ta ke yin nuni kan yiyuwar tsayuwar ta kan asasin larura (ba makawa), haka ma zai iya dankar ma’anar tsayuwarsa bisa asasin kaddara wata hikima da ta sa wanda ya tsara Duniya ya alakanta zahirin abubuwa kaza da na wadancen abubuwan kaza tare da ci gaban (maimatuwar hakan). Kumaita kanta wannan hikimar a wani lokaci ana kiranta da togaciya, sai mu’ujiza[82] ta afku.

Da wannan ya bayyana a mahangar ilimin mandikyana mai kafa hujja cewa rayuwa mai tsawo abu ne mai yiyuwa, kuma ba wani dalili na ilimi da yake kore yiyuwarsa haka ma ba wata hujja ta falsafa da take kore shi. Kuma da wannan ne marhalar bincike ta farkokan abin da ya shafi gaibu ta zo karshe.