• Farawa
  • Na Baya
  • 13 /
  • Na Gaba
  • Karewa
  •  
  • Gurzawa HTML
  • Gurzawa Word
  • Gurzawa PDF
  • Budawa: 17332 / Gurzawa: 5596
Girma Girma Girma
mahdawiyyanci

mahdawiyyanci

Mawallafi:
Hausa

Fasalina uku:

Kimar Akida Ga Sanin MahdiA Makarantar Alulbait (a.s)

Akidoji duk daya ne shin sun kasance na kasa ne wadanda dan’adam ya fare su, ko na sama wadanda faruwarsu ke komawa ga Allah Madaukaki, ba makawa suna da alaka da dalili na mutuntaka, idan sun kasance na kasa to suna faruwa ne daga yanayin dan’adam kuma an fassarasu ne da tsinkayensa da kwadayinsa zuwa ga saduwa da mafificiyar rayuwa, in ko sun kasance na sama to suna samar da jin kan Allah (SWT) ga mutum da sonsa gare shi da kwadayinsa bisa sadar da shi zuwa ga farfajiyar arziki, kuma wannan na daga cikin abin da mumini ke yinsa take a cikin asalin akidar Musulunci, duk daya ne wanann manufar ta bayyana ga mutum a warware ne ko kuma warwarata ta wanzu a dunkule a boye a cikin gaibu. (a gare shi).

Shi mutum wani lokacin yana mu’amala tare da akidoji ne a hankalce ta fuskancin dalilai da hujjoji, wani lokacin kuma (yana mu’amala da akida) da jiki ta fuskancin manufofi da amfanunnukan da yake samu daga wadannan akidojin a rayuwarsa ta yau da gobe. Kuma duk yadda wadannan akidojin suka kasance bayyanannu masu karfafa ta fuskancin dalilai da hjujjoji, to murdiyar da ke cikinsu da boyuwarsu ta fuskancin mutumtaka na sa ta zama lamarin da ake kokwanto a kansa, ko dai - a takaice - su zamo marasa muhimmanci wadanda ba su da tasiri a zuci.

Sannan ita akidar Musulunci a matsayin ta na akidar sama ba zai yiwu gare mu mu bayyana manufofinta ga mutum a warware ba, domin warwararren bayani zai kai mu zuwa komawa ga bangare jikin dan’adam wannan kuma ya saba da lamarin da yake shi ne ginshiki kuma tushe na asali a akida wanda yake wakiltar bangaren hankali a sarari, (wato bangare hankali shi ne asasi a cikin akida) da dogaro ta bangaren ruhi a mutuntakar mutum, don haka a dabi’ance za mu isu da wannan akida da bayanin mataki mafi kusa a takaice ga bukatun mutum.

Misalin fadin Allah (Ba mu aiko ka ba face jin kai ga talikai). [110]

Sai dai ita a wannan lokacin tana kwadaitar da mutum mumini da fuskantar da shi zuwa ga hankaltuwa da tuntuntuni wanda ke bada sakamako zuwa yin amfani da hikimomi wadanda ake kyautata tsammanin cin musu d a bukatun dan’adam na fili wadanda ake zato a mabanbantar fuskoki na akida da na shari’a daga Musulunci.

Hakika mun karanci mas’alar Mahdi (a.s) ta fuskancin dalili da hujja, (a.s) kuma ya bayyana cewar fahimtar makarantar Ahlulbait game da mas’alar Mahdi (a.s), in ka kwatanta ta zuwa fahimtar makarantar mazhabobi hudu ta fuskancin dalili da hujja, za ka ga makarantar Ahlulbaiti (a.s) sun fahimci wannan mas’alas a aikace a cikin mafi kammala sura da cika.

Kuma cikarta ta fuskancin akida da dalili yana hukunta kuma yana kai mu zuwa ga kuduri da cikarta a cikin abin da ya gabace shi na hidimtawa da tamakawa ga dan’adam, sannan mararrabar da ke kai da yawan mutane su rika yin kokwanto suna motsa shubuhohi dangane da fahimtar Mahdi (a.s) a wajen Ahlulbait (a.s), suna nuna cewa wadannan mutanen ba sa yin duba ta fuskacin fagen kafa dalili da hujja, gwargwadon yadda suke yin duba ta fuskancin mutuntaka wanda hakan kan sa su yin tambayoyi:

Wane amfani ake samu ta hanyar yin kuduri da fahimtar Mahdin da ya siffantu da ma’anonin fakuwa ba irin fakuwar da aka saba ba, ga shekaru masu yawa, ga imamanci sabo? A lokacin da ba sa saduwa da gamsasshen jawabi, sai bangaren mutuntakar wannan fahimtar ya wanzu yana kewaye da shakka da rudewa, wanda jahilci zai rika tura su zuwa gare su, kuma gazawae masu wannan fahimtar ga barin iya suranta lamarin kamar yadda yake na sa masu ita su rika tuhumar cewa an wuce iyaka kuma karya ake, sai su musanya ta da wata fahimtar wacce ta sha bamban da wannan mahangar, wacce wofinta daga wadannan shubuhohin da tambayoyin, wanda ba ya bukatar kawo wani boyayyen lamari mai girman gaske, ba tare da sun gane cewa wannan aikin nasu da suka yi - na cire abin da ba su sani ba daga fahimtar mahdawiyyanci - ya sa sun ciratu daga kamala zuwa tawaya, kuma hakika wannan bujeriwar ta su daga wannan bangaren na mahangar fakuwa kawai bujerew ga wani ginshiki mai girma ga mafahimtar Mahdi (a.s) a Musulunci ne, balle ma lalle hakan ya saba da mahangar hankali wanda shi ne yake yin hukunci a babin akida da kudiri kan mika wuya ga dalili da hujja duk inda suka fuskanta, ba a canja su a juya su ta fuskancin son rai da soye-soyen zuciya da bukatar dan’adam ba.

Da ace za su yi tunani, kan mahanga da fahimtar Ahlulbait (a.s) kan Mahdawyyanci (a.s), da sun samu fahimta mafi cika a kan haka fiye da fahimtar makarantar khalifofi ta bangaren mutuntaka, hakika Sayyid Shahid Muhammad Bakid Sadar ya yi bayanin wannan nahiyar bayani mai kaye a inda ya rubuta yana cewa: [111]

“Za mu dauki tambaya ta biyu, yana cewa: Don me duk wannan kwadayin na musamman daga Allah Madaukaki a kan wannan dan’adam din, ya zamana an kautar da dokoki ne dabi’a ta hanyar tsawaita rayuwarsa? Kuma don me ba za a bar jagorancin ranar alkawarin ga wani mutum a nan gaba ba da zamani yake jiransa, sai abubuwan mamakin ranar alkawari su nuna a hannunsa sai ya fito a lokacin ya aiwata r da aikinsa wanda ake jira sa ya gabata r

Da wata kalmar za mu iya cewa: Mecece fa’idar wannan doguwar fakuwa kuma meye manufarta?

Da yawan mutane suna yin wannan tambayar alhali ba sa bukatar sauraren boyayyiyar amsa, (amsa ta ta gaibu) to mu mun yi imani da cewar Imamai sha biyu gunge ne guda na musamman [112] ba zai yiwu a mayarwa ko wane daya daga cikinsu ba, sai dai wadannan masu tambayar suna neman bayanai masu yawa ga wannan matakin ta hanya hakikoki bayyanannu ga wannan aiki na kawo babban canji, da abubuwan da ake bukata da za su s aa fahimci ma’anar wannan rana ta alkawari.

A kan wannan tushen ne muka yanke duba na wani dan lokaci a kan kebance-kebancen da muka yi imani da cewa sun cika a cikin halayya da dabi’un wadannan shugabanni ma’asumai, [113] sai kuma mu jeho tambaya mai zuwa:

Mu dangane da aikin canji mai faruwa game da ranar alkawari, gwargwadon yadda aka fahimce shi bisa ga sunnar rayuwa da gogayyar ta, shin zai yiwu mu kalli wannan doguwar rayuwar ga jagoran da aka ajiye mata a matsayin wani dalili daga dalilan cin nasararta, kuma wannan zai sa shi ya gubatar da wannan aikin ya kuma jagorance shi da daraja mafi girma?

Zamu amsa muku da cewa e, haka ne, wannan kuma saboda wasu dalilai da dama daga ciki akwai wannan maganar mai zuwa cewa: hakika yinkurin kawo babba gyara yana bukata yanayi na ruhi makadaici ga jagoran da zai ja ragamar yin sa, ya zama yana cike da (hamasa ko) himma da kulawa da daukaka da kuma ganin rashin girman babban aikin da ya sa a gaba wanda aka shirya shi da ya aiwatar da shi da kuma canja tsarin rayuwa a zamanance zuwa wata sabuwar wayewa.

Gwargwadon yadda zuciyar mai kawo canji take ciki da ganin raunin wannan wayewar da yake yaka da kuma jin cewa a sarari ita ba komai ba ce face dan dugo a kan dogon layin zanen ci gaban dan’adam, zai wayi gari mafi jin karfin gwaiwa ta bangaren ruhinsa [114] kan fuskantar wannan wayewar ko hukumar da kuma dakewa kyam a gabanta da ci gaba da kokarin tunbuke ta.

Abu ne a sarari kan cewa lalle gwargwado da ake bukata na jin nauyi na musamman ga wannan aikin, lalle ne ya zama ya dace da girman shi kansa kawo cnaji da ma kuma abin da ake so a ga karshensa na wayewa da samuwa, kuma dun likacin da fito-na-fito don kawar da wani abu ya zama mafi girma kuma ya zama na wayewa ce mafi kafuwa da ta kai kololowa a mbanbantan matakan rayuwa, to hakika aikin na bukatar zage dantse mafi girma fiye da yadda ake jin nauyin aikin.

A yayain da sakon ranar da aka yi alkawari ta zama ta kawo canji a dukkanin duniyar da ta cika da zalunci da danniya ce, to a dabi’ance dole ne wannan sakon ya nemo mafi girman mutum wanda ke da cikakken sani da jin cewa aikin da ke gabansa ya fi girman wannan duniyar baki dayanta, sabanin mutumin da a waccen duniyar aka haife shi ba wadanda suka rayu a cikin inuwar wancan ci gaban da ake nufin canja shi da wani sabon ci gaban adalci da gaskiya, domin wanda ya rayu a inuwar cigaba mai bunkasa, da duniya ta cika da darajarta da tunaninta, to jin kwarjini - zamaninsa - zai rayu a zuciyarsa, domin shi an haife shi a lokacin da wannan wayewar yake cin gashinta, kuma ya taso tun yana dan karami a lokacin da hukumar take kan ganiyarta, ya bude idandunansa a cikinta be san wani abu ba sai fuskokin ta mabanbanta.

Sabanin wancan, a ce ga wani mutum, wanda shi mutum ne da ya ke cikin tarihi tsundum ya rayu a duniya tun kafin duniya ta shedi wannan ci gaban na haske, kuma ya ga babban ci gaba yana jagorantar duniya daya bayan daya, sannan suka raunana kuma suka rushe, [115] ya ga wannan da idanunsa ba karantawa ya yi a littattafan tarihi ba.

Sannan ya ga ci gaban da yake da iko gare shi da ya kasance aji na karshe daga kissar mutum kafin ranar alkawari, ya ga babbar bishiya tun tana matsayin karamin iri da ba shi da alamar bayyana.

Sannan ya ganta ta dauki matsayi a cikin mutane tana yin yado tana neman dama don ta girma ta bayyana.

Sannan ya rayu da ita wato ya yi zamani daya da ita a lokacin da ta fara habbaka tana bunkasa wani lokacin tawaya ta same ta wani lokacin kuma ci gaba da dacewa su abotakance ta.

Sannan ya same ta tana bunkasa tana mamaya a hankali a bisa yanayin duniya baki daya, to ta wannan fuskar dan’adam din da ya rayu a dukkan wadannan matakan da kaifin hankali da fadaka cikakku yana duba zuwa ga wannan tazgaron - wanda yake so ya yi fada da shi - daga wancan dogon tarihi mai tsayi wanda ya rayu shi da jikinsa ba ta cukkunan litattafan tarihi kawai ba, yana duba zuwa gare shi ba da ‘yar karamar sura ba, ba kuma kamar yadda (John Jack Roso) [116] yake duba zuwa mulkin mallaka a Faransa ba, hakika labari ya zo daga gare shi cewa; ya kasance yana jin tsoro da zarar ya suranta kasantuwar Faransa ba tare da samuwar Sarki ba, tare da kasantuwarsa daga manyan masu tunani da hikima kuma yana daga cikin msu yin kira ta fuskancin ci gaban siyasa mai ci a wannan lokacin, domin shi wannan (Rosen) ya rayu ne a inuwar mulkin mallaka, ya sheki iskar ta tsahon rayuwarsa, amma ka ga Mutumin da ya shiga cikin tarihi to yana da kwarjinin tarihi, da karfin tarihi da kyakkyawan sani kan cewa abin da ke kewawye da shi na daga kasantuwa da ci gaba wani abu ne da aka haife shi a wani yini daga kwanakin Tarihi, wasu dalilai suka faru gare shi sai aka samar da shi kuma wasu dalilan za su faru sai ya gushe, kuma ba abin da zai wanzu daga gare shi dindindin kai ka ce a jiya ko a shekaran jiya wani abu be faru ba, kuma lallai kwanakin da tarihi ke bawa samuwar wayewa da ci gaba, duk yadda suka yi tsayi ba wasu abubuwa ba ne face ‘yan kwanaki gajeru a cikin doguwar rayuwar Tarihi.

Shin ka karanta Surar Kahfi?

Kuma shin ka ranta game da wadannan samarin da suka yi imani da Ubangijinsu ya kara musu shirya [117] ? Suka fuskanci wani mugun gwamna me bautar gunki, mara tausayi, baya kaikawo cikin tsige dukkan wani tsiro daga ire-iren nau’o’in tsiron bishiyar tauhidi, ko kadan baya daga kafa idan mutum ya bar shirka, wannan ya sa rayuwa ta yi musu kunci, kuma debe tsammani ya kutsa cikin kofofin zukatansu, har ya toshe tagogin fata da buri a gaban idanuwansu, sannan suka fake a kogo suna neman warwarar matsalarsu daga Allah bayan da suka gaza samarwa kansu warwara da mafita, kuma lamarin ya yi musu nauyi a zuciya a ce barna ita ce ke yin mulki, tana zalunci, kuma ga shi ta fi karfin gaskiya, sannan duk wani sauti da ya yinkuro yana kishiyantarta ba ta barin sa har sai ta ga bayansa.

Shin ka san abin da Allah Madaukaki ya yi da su?

Hakika y a sa su bacci na shekara dari uku da tara [118] a wannan kogon, sannan ya tashe su daga baccinsu ya dawo da su fagen dagar rayuwa, bayan tuni wancan tsarin da suke jin tsoro wanda ya rinjaye su da karfinsa da zaluncinsa ya riga ya fadi, ya wayi gari a cikin kundin Tarihi ba ya iya tsoratar da kowa baya iya motsa abin da ke ajiye, duk wannan don wadannan samarin su ga mutuwar wannan bataccen mutumin wanda fadin ikonsa da karfinsa da kuma zartarwarsa ta girmama gare su, kuma su ga karshen lamarinsa da idanuwansu kuma suga yadda bata ya kwashi kaskanci a lokacin da suke raye.

Idan har wannan ganayya mabayyaniya ya tabbata ga ashabul kahfi a sarari, tare da dukkanin abin da take dauke da shi na girma da buyawa masu matukar kima ta hanyar wannan tilon abin da ya faru, wanda ya tsawaita rayuwarsu har shekara dari uku, hakika wannan shi ne ainihin abin da zai faru da jagora sha sauraro Imam Mahdi (a.s) ta hanyar rayuwarsa mai tsawo, da zata ba shi damar ya ga gagarau alhali a lokacin yana dan’karami kuma ya shedi bishiya kangaran alhali a lokacin tana kwarar iri wadda ake shukawa, sannan kuma ya ga zamanoni tun suna lokacin asubarsu ta fari[119] (tun farkon faruwar su), kara kan haka cewa, lalle ilimin gwajin wanda ya yi wa tafiyar wannan wayewa rakiya, kuma ya rako ci gabanta na nan gaba, ya kuma fuskance ta kai tsaye domin motsota da ci gabantar da ita, lalle yana da tasiri babba wajen kintsa tunani da zurfafa kwarewa a jagoranci domin yinkuri a ranar da aka yi alkawari, domin - wadannan gogayyar zasu sa wanda aka tanada ya samu kansa a gaban gogayyar mutane da dama da dukkanin abin da ke cikinta na bangaren rauni da karfi, da ma nau’o’in kuskure da daidai, kuma zata sa wannan mutumin ya sami iko mafi girma wajen kimanta zahirin marayar dan’adam ya kuma dorata kan wayewa cikakkiya bisa sababinta, da ma dukkanin abin da ya cakuda da ita na Tarihi.

Sannan wannan aikin na kawo canji wanda aka tanadi jagora don ya tsaya da shi ya tsaya ne kan asasin sako ayyananne wanda shi ne sakon musulunci, kuma abu ne na dabi’a cewa tsayuwa da wannan aikin a irin wannan yanayi zai zama yana bukaci jagora na daban, wanda ya rayu a kusa da masdarin musulunci na farko, wanda an riga an gina mutumtakarsa wato (shakhsiyyarsa) cikakkiyar ginawa, da yanayi na daban wanda ya nisanta daga tasirin wayewar zamanin da aka hukuntawa kawo karshensa wanda shi ne zamanin da aka yi alakawarin idan Imam (a.s) ya zo zai yake shi. (Ma’ana be tasirantu da wayewar zamanin da aka umarce shi ya yake ba).

Sabanin wancenenka, mutumin da aka haifa kuma ya tashi a zanin goyon wannan zamanin kuma ya zama a nan tunaninsa da shu’irinsa suka bude, hakika wannan bisa mafi rinjaye ba zai iya kubuta daga kura-kuran wannan zamanin da ma abin da zamanin yake damfare da shi ba, ko da kuwa ya jagorancin motsin kawo canja yana mai kisiyantarsa.

Domin a tabbatar da rashin tasirantuwar jagoran da aka tanada da wayewar da aka dora masa aikin canja ta, ya zama ba makawa ga mutumtakarsa ta zama an gina ta cikakken gini a lokacin wayewar zamanin da ya gabata wacce ta fi kusa da ginuwa kan gamammiyar kauna, ta bangare tushe kuma ta zama ta fi kusa da wayewar da aka umarci wanda aka yi alkawari zuwansa ya canja ta”[120]

Sannan mai girman daraja ya kara jefo wata tambaya wacce ke da alaka da bangaren mutumtaka daga akidar mahdawiyyanci, saboda me wannan jagora na duniya be taba bayyana ba tsawon wannan lokacin? Kuma idan har ya kintsa kansa don yin aikin jama’a, me ya hana shi ya bayyana a fagen fama a tsawon lokacin da ya yi karamar fakewa ko kuma a karshe-karshenta a maimaikon ya mayar da ita babbar fakuwa, a lokacin da yanayin da sharuddan zamantakewa suka fi sauki, kuma a lokacin alakarsa da mutane ta hanyar gungun mutane a gajeriyar fakuwarsa zata ba shi dama ya tsara mabiyansa ya fara aikinsa farawa mai karfi, kuma hukumar lokacinsa ba ta kasance tana da karfin da ya kai girman karfin ikon da mutumtaka ta kai zuwa gare shi bayan wancen lokacin ta hanyar ci gaban ilimi da na masana’anta ba?[121]

Amsa: hakika dukkanin wani aikin kawo canji cikin al’umma lamarin sa na damfare da wasu sharudda da wasu yanayoyi na waje da ba zai iya yiyuwa canjin ya kai ga hadafinsa ko ya sami mazauni ba sai in har wadannan shardan da yanayoyin sun cika.

Kuma wannan aiki na kawo canji wanda sama zata tsarge shi a bayan kasa ya fifitu da cewa ba ya da wata alaka da yanayin[122] lokacin kawo canjin, domin ayyukan da kokarin kawa canji ya doru a kansu ta bangare sa na isar da sako, domin sakon da kawo canji da aka daro masa sako ne na ubangij, kuma sama ce ta samar da shi, ba yanayin da ake ciki ne ya samar da shi ba, amma ta banagren zartarwa sakon ya dogara da yanayin da ake ciki kuma nasararsa da lokacin zartar da shi ya dogara bisa gwamata da lokacin wannan yanayin. Saboda haka ne ma, sama ta saurari wucewar karni biyar na jiahiliyya har lokacin da ta saukar da sakonta na karshe a hannun Annabi Muhammadu (s.a.w) domin alakar da ke tsakanin yanayin don zartar da abin da ya kamata a jinkirta shi duk da tsananin bukatuwar duniya zuwa gare ta tun lokaci da dama da ya shude kafin wannan lokacin.

Kuma yanayi na da tasiri ta bangaren zarta da aikin kawo gyara, daga ciki akwai abin da yake shimfida gamemmen yanayin da ya dace domin samun canjin da ake buri, daga ciki kuma akwai abin da yake fayyace abubuwan da wannan motsi ke bukata ta hanayar bin lamarin loko loko.

Dangane da juyin juya halin da Linin ya jagoranta a kasar rasha - bisa misali - har ya kai ga nasara, motshin na sa ya kasance yana damfare da sababi na daga tsayuwar motsin kawo canji na farko a duniya da raunanar sarautar kaisaranci (tsarin masarauta), wannan na daga cikin abin da zai temaka wajen kawo cnaji na juyin juya hali, kuma matsin ya kasance yana danfare da wani sababai na biyu na gefe iyakantancce, na daga kasancewar Linin cikin koshin lafiya a cikin tafiyar sa da ya yi da ya samu ya kutsa cikin kasar Rasha ya jagoranci jujin juya hali, domin da wani abu ya faru da shi da zai hana shi shiga rasha da akwai yiyuwar jiyun ya rasa karfinsa saboda wannan abin sai ya zama ya kasa bayyana a sarira cikin sauri.

Kuma hakika haka sunnar Allah Ta'ala ta gudana wancce ba ta canjawa a wajen motsin kawo canjin da yake daga ubangiji, wanda yake iyakantacce ta bangaren zartarwa daidai da yanayin da ake ciki wanda hakan ke samar da gammamen yanayin da ya dace domin tabbatar da wannan aikin, wannan ne ma ya sa musulunci be zo ba sai bayan wani lokaci na rashin manzanni da tazara mai daci da ta dore tsawon karnoni.

Duk da ikon da Allah Ta'ala yake da shi kan karanta wahalhalu wajen isar da sakon ubangijintaka, da iya halittar yanayin da ya dace bisa mu’ujiza, sai dai be so ya yi amfani da wannan yanayin ba, domin ita jarrabawa da da musiba da wahalar da mutum ke sha kan hanyarsu ne mutum yake samun kamala, ta wannan nahiyar hakan ya hukunta motsin kawo canjin ubungiji shi ma ya zama bisa dabi’a, kuma wannan ba zai hana Allah Ta'ala ya sa hannu - a wani lokaci ba - kan abin da ya shafi fayyace wasu lamura da yanayi bai zama ya dace da su ba, kadai dai wani lokaci a kan bukaci, yin motsi daidai da yanayin da ya dace ne, daga nan ne ake samun temako da mika hannun ubangiji a boye wanda Allah Ta'ala yake yi wa waliyyansa a lokacin da suke cikin kunci sai ya kare manzanci da shi, sai ga wutar Namarudu ta wayi gari mai sanyi da aminci ga Annabi Ibrahim (a.s)[123] sai ga hannun mugun bayahuden da ya daga takobinsa a kan Annabi Muhammadu (s.a.w) ya shanye ya rasa ikon da yake da shi na motsa shi,[124] sai ga iska mai karfi ta daddage hemomin kafirai da msuhrikan da suka kewaye madina a ranar handak tana jefa tsoru cikin zukatansu, [125] sai dai gaba dayan wannan be wace fayyacewa da bada gudun mawa a lokacin da ake bukata ba bayan yanayin ya kasance ya dace da ayi kokarin kawo canji a dunkule da zai iya zama bisa yanayi na yau-da-gobe, daidai da yanayin da ake ciki.

Bisa wannan haskakawar zamu karanta matsayar Imam Mahdi (a.s), don mu ga cewa lalle motsin yin jujin juya hali da aka zabe shi don ya gabatar ta bangaren zartarwa -kamr dai ko wane motsi ne na kawo canji - yana da alaka ta bangaren zartarwa da yanayin da ake ciki wanda zai temaka wajen lamarin ya yi daidadi da aikin, daga nan ne ya zama a dabi’ance ya zama ya tsaya a kan haka.

Sanannen abu ne cewa Imam Mahdi (a.s) be riga ya kintsa kansa kan wani iyakantaccen lamarin na jama’a na musamman ba ko kuma wani aikin kawo sauyi a wani yanki ko wancen ba, domin sakon da aka tanade shi don ya isar ta bangaren ubangiji madaukaki sarki shi ne ya canja duniya canjawa na baki daya, kuma ya fitar da dan’adama daga dukkanin dan’adam daga duhun zalunci zuwa hasken adalci, [126] kuma wannan babbana aikin na kawo canji wajen gudanar sa shi be isar ace kawai akwai sako tare da jagora na gari ba, in ba haka ba da tuni sharadan yin hakan sun cika tun a zamanin annabta kanta (zamanin da Annabi Muhammadu (s.a.w) yake raye), lalle kadai lamarin na bukatar yanayin da duniya ta dace da hakan, da gamammen yanayin da zai temaka. Ta bangaren mutumtaka ana ganin yadda mutumin wayewa yake jin cewa narkewa dalili ne na asasi wajen halittar wannan yanayin da zai sa a karbi wannan sabon sakon na adalci, kuma wannan jin narkewar yana samuwa ne kuma yana kafuwa a jikin mutum ta hanyar gogayyar zamani kala-kala, wacce mutumin wayewa ya fito daga cikinta yana mai nauyaya da tufafin da aka gina yana mai riskar bukatarsa zuwa temako yana mai waiwayar fidirarsa zuwa gaibu ko zuwa abin da be sani ba.

Ta bangaren bukatun jiki kuma ta yiyu sharadin sabuwar rayuwar bukatun jiki su zama sun fi iko fiya da sharadin rayuwa a da, a lokaci irin lokacin fakuwa, wajen isar da sakon a matakin duniya baki dayanta, wannan kuwa saboda abin da zamanin ya tabbatar da shi na kusanto da nesa da iko mai mai kirman gaske kan kai-kawo tsakanin al’ummun duniya, da yalwatar hanyoyi da kayan aikin da hedkwata ke da bukatuwa zuwa gare su don gudanar da ayyukan wayar da kan mutanen duniya, da cigabantar da su kan asasin sabon manzanci (sako).

Amma abin da aka yi nuni kan sa a cikin tambaya na karuwar karfin soji da makaminsu wanda jagora zai fuskanta a ranar da aka yi alkawari, duk lokacin da aka kara jinkirta bayyanarsa, wannan abu ne ingantacce, sai dai da me kara ci gaban karfin soji zai amfanar tare da faduwar ruhi da zukata warwas daga cikin jiki. Tare da zubewar ginin ruhin dan’adam din da ya mallaki wadannan makaman kasa-kasa makami ba shi da wani tasiri? Sau nawa ya faru a tarihi, sai kaga ginin ci gaba mai girma a zube sakamakon dan karamin kai hari na farko, saboda dama a zube yake kafin nan, kuma ya riga ya rasa kwarin guiwa kan samuwarsa da gamsuwa kan kasancewarsa, da samun nutsuwa kan hakikaninsa [127] Anan ne abin da - Sayyid Shahid Sadar - ya fa’idantar ya kare, Allah Ta'ala ya tsarkake ruhinsa.

Kuma zamu iya yin bayanin abin da mutumtaka zata samu daga mahdawiyyanci a mahangar Ahlulbaiti (a.s) ta wani bangaren.

Sai muce :

Hakika kudurcewa da mahdawiyyanci (Imam Mahdi (a.s), wanda ya faku daga idanuwa duk da yana raye kuma yana yin tasiri wajen gudanar lamura, hakika al’ummar muminai tana cin ribar hakan, kuma Imam na dauke da dukkanin khususiyyar Imamanci na daga Isma da nassin Annabci da kamala ta ilimi da aiki, kuma yana daga cikin sha’aninsa yada wannan jawwin (wato yanayin da lamarin) na imamanci da Kanshinta na ma’anawiyya (na ma’ana wato mai tasiri a boye) da na ruhi madaukai, kuma mutum yana jin ya koshi da kyakkyawan shu’uri mai dadi saboda samuwar dorewar alaka tsakanin sama da kasa da ci gaban samun kulawar sama ga doron kasa, da canja haka zuwa ma’ana da ake dosana sosai da tafi tasiri a zuciya, bayan hakan ya kasance abu karbabbe a tushenta na akida, kuma za a tafiyar da hukumar tauhidi a fagen rayuwar zamantakewar mutane da siyasa, kuma zai sanya ta ta zama tana da tasirin da yake kusa da riskar dan’adam, la’akari da cewa lalle mahdin nan (a.s) da ya faku ba mutum ne game gari ba, lalle shi ne Imami na goma sha biyu wanda aka ayyana daga sama wanda ya hau kujerar imamanci har zuwa karshin tarihi, da gaske ne cewa mutane ba su saduwa da shi a sarari, sai dai akidantuwa da kasancewar sa hakika wacce ake riska, wacce riskar mu ta tawaya daga ganota, hakan na sa ruhi ya zama cikin yanayin jin alaka ta ruhi mai kyau da tafarkin imamamanci ma’asumi na ubangiji a matsayinsa na cewa shi cigaban hukumar tauhidi ne a doron kasa.

Kuma wannan alakana bayyana sosai a lokacin fakakkiyar mahdawiyya ma’asuma wacce zata yi bayanin kanta bayani na siyasa a sarari, ta hanyar farkon fara gamemmen wakilci na musamman na (na wakilia hudu) a lokacin gajeriyar fakuwa. Da kuma fara gamemmen wakilci na musamman na fakihai a lokacin doguwar fakuwa a matsayuns u na jagorori na siyasa ta shari’a da al’uammar musulmai, ta yadda matsayin nan mai girma na imamanci zai wanzu, tamkar mai sa ido yana bibiyar gogayyar siyasa da ta zamantakewa yana temaka musu, kuma tamkar wata mashaya da t ake temaka m usu a shari’anc e idan ya ga ta dace da musulunci.

Daga cikin tarin wadannan bayanan ma’anar kamala a cikin abin da Imam Mahdi (a.s) zai gabatar za ta bayyana a sarari, na daga abin da mutumtaka zata bayar, kuma abu ne da ya dace dari bisa dari da tsaftatacciyar mahangar mahdawiyyanci, domin hakika mahdawiyyanacin da yake ma’asumi wanda da ya faku mahdawiyyanci ne mai motsi mai tasiri mai amfani ga dan’adam, kuma ba ta wuce bada labarin abin da zai zo nan gaba ba. Kai ka ce mahdin Ahlulbaiti (a.s) ya dauki nauyin abin da aka dora masa ta hanyar motsa ainihin yadda dan’adam yake da kuma yin alaka mai kyau da shi.

Kuma wannan a kan kansa shi ne mafi kyau abin da za a iya bayyana ma’anar sauraro da shi domin sauraron yayewa ba shi ne yin shiru da nuna gazawa ba, kadai da shi ruhi ne mai amfani mai motsi zuwa tafarkin kawo canjin da ake bukata a mahdawiyyance.

Sakamakon Bincike

A karshen wannan zagayen, zamu iya rairayo abin da sakamakon wannan bahasin ke dauke da shi, da wadannan ‘yan kalmomi kamar haka:

Hakika addini shi ne mafi kamalar bayani kan hakikar dan’adam kuma musulunci ne bayani mafi cika kan hakikanin addini, kuma shi’anci shi ne bayani mafi kamala kan hakikanin musulunci, baya ga haka mahdawiyyancin Ahlulbaiti (a.s), shi ne mafi kamalar bayani kan asalin mahdawiyyanci, wanda dukkanin musulmai suka hadu kan akidantuwa da shi.

Hakika zinaren banbancin da ke tsakanin mahdawiyya a wajen Ahlulbaiti (a.s), da mahdawiyyancin mafi yawan malaman musulmai, yana komawa ne, zuwa mas’alar imamamnci, hakika dai shi Mahdi (a.s) a mahangar makarantar Ahlulbaiti (a.s) shi ne Imami na goma sha biyu, a yayin da a wajen makarantar sahabai mas’ala ce ta abin da zai faru nan gaba kawai.

A yayin da mas’alar Imam Mahdi (a.s) a wajen Ahlulbaiti (a.s) ta zama mas’alace ta Imami na goma shi biyu wanda al’umma ba su da wani Imam a bayansa, daga nan ne ya zama fahimtar mahdawiyya a wajensu ta siffatu da kebance-kebance guda uku, wadanda su ne haihuwar Imam Mahdi (a.s) a asirce a boye, kuma ya zama imami yana karami, da kuma fakuwarsa da ta lazimta masa rayuwa mai tsawon zamani kuma wadannan kebance-kebance guda uku sun tabbata ta hanyar tabbatar asalin imamanci Imamai sha biyu ma’asumai (a.s), wanda daga nan ne ya samo asali, ballantana ma mun riga mun jero muku dalilansa dalla-dalla, daya bayan daya tun a baya.

Hakika wadannan kebance-kebancen guda uku ba a tabbatar da su ta hanyar dalilai na akida da hankali da na gamsuwa ba, kuma sam ba wani ishakali da yake lazimtarsu, na hankali ne ko na addini, ma’ana; (ba kawai sun kubuta daga ishkalin hankali ko na addini kawai ba ne), bisa hakika su ne ma ke fitar da ma’ana ta kamala wajen fahimtar mahdawiyyanci kuma su mayar da shi ya zama faminta mai kima ta akida mai kima ta mutuntaka madaukakiya wacce ke tattare da kyawawan halaye a matakin al’umma, wacce ta zama ta sami kamala kuma ta dace da abin da tushen addini ya doru a kai a cikin rayuwar dan’Adam.

Tsira da aminci su kara tabbata a bisa Manzon AllahMuhammad ( s.a.w) tare da alayensa tsarkaka (a.s).