• Farawa
  • Na Baya
  • 13 /
  • Na Gaba
  • Karewa
  •  
  • Gurzawa HTML
  • Gurzawa Word
  • Gurzawa PDF
  • Budawa: 17313 / Gurzawa: 5594
Girma Girma Girma
mahdawiyyanci

mahdawiyyanci

Mawallafi:
Hausa

MAKOMAR BINCIKE

[1] Ka koma Ma’ujmu Ahadisil Mahdi j 1 ahadsina biyii (s.a.w).

2 Musnadi Imam ahmad 1: 83 da ibni Abi shaiba 8: 678, Kitabi 40 babi 2 H 190. DaIbni Majah da Na’imu dan Hammad a cikiin littafin Al-fitan daga Ali (a.s) ya ce Manzon Allah (s.a.w) “Mahdi (a.s) daga cikin mu yake Ahlul bait Allah Ta'ala zai tashe shi ya kawo gyara a dare daya” ka koma matain ibni maja 2: 1367 da 3085. Haka ma a cikin hawi lillfatawa,na siyudi, 2: 213, da 210. A cikim sa ma an kawa cewa Ahmad ya fitar daga Abi Shaiba da abu Dauuwa daga Ali (a.s) daga Manzon Allah (s.a.w) ya ce: “ da aba abin da ya rage wa zamani sai rana daya da Allah Ta'ala ya tsawaita wannan zamaninhar sai wani mutum daga mutanen gida na ya zo ya cika ta da adanci kamar yanda ta cika da zalunci”. Kuma ka komazuwa sahihu sunanul mustafa j 2 shafi 207.

Ka kuma wa majma’u Ahadisil mahdi j 1 shafi 137 da abin da ke bayansa, domin ya cirato hadisai masu yawa daga sahihai da masnadai da wannan ma’anar kuma ka koma mausu’ar imam mahdi wanda Mahdawi Fakih Imani ya tsara juzu’i na farko kuma a cikin sa akwai abubuwan da aka cirato na hotuna daga gomomin litattafai malaman sunna da masana hadisinsu kan Mahadi (a.s) da siffofinsa da ma abin da ya rataya da hakan kuma a cikin sa akwai wani shafi mai hoto a cikin leccar Shekh Al-ubbad kan abin da ya zo na daga hadisai da abin da aka gada kan mahdi (aj).

3 Alhawi lillfatawa, Siyudi jalaludddin j 2 sh 214. Kuma abu dauuda ma ya fitar da shi da ibni majah da dabarani da hakim daga ummu Salma, ta ce na ji Manzon Allah (s.a.w) yana cewa : “ Mahdi daga tsatso na yake daga cikin ‘ya’yan Fadima (a.s) , ka duba Sahihu sunananul musdafa na Abi Dawuda j 2 sh 208 da 3087.

4 Hadisin Mahdina daga cikin zuriyar husain kamar yanda yake a masdarori masu zuwa kamar yanda aka cirato daga mu’ujamul Ahadis na wadanda hadisai ne guda arba’in na abi Na’imul Isfahani, kamar yanda ya zo cikin Akadul durri na mukaddami ba shafi’e. Kuma Dabarani ma ya fitar da shi, a cikin ausad, kamar yanda yake cikin manarul munifi na Inbnil Kayyim, da kuma siratul halbiyya j1 sh 193, haka ma a cikin Kaulul mukhtasar na Ibni Hajarul Haisami, ka koma muntakhabul asari na Shekh Ludfullahis Safi na daga abin da ya ciro daga litattafan Shi’a haka ma dalilan raunin ruwayar da ke cewa daga cikin tsatson imam Hasan (a.s) zai fito, littafin Sayyid Amidi: Difa’un anil Kafi” j 1 sh 296.

5 Ka koma ruwayar da ta yi nassi da cewana tara daga cikin ‘ya’yan Husain (a.s) a cikin Yanabi’ul muwadda na Kanduzi, Bahanafe, shafi na 392, da ma cikin Maktalul imam Husaini na Khawarizmi, j 1 shafi 196, da ma cikin fara’idul simdaini na Juwaini Bashafi’e, j 2 shafi 310 – 315. Kuma ka koma Muntakahbul asarna na Allama Shekh Safi, don ya fitar da shi ta hanyoyin bangare biyu.

6 Hadisin “halifofi a baya na guda goma sha biyu ne dukkanin su daga kuraishewa su ke” ko kuma hadisin wannan addinin ba zai taba gushewa ba a tsaye har sai halifofi goma sha biyu sun shugabance shi dukkanin su daga kuraishewa”.

Wannan hadisi ne mutawatiri ingantattau litattafai da musnadodi sun rawaito shi ta hanyoyi mabanabanta, duk da cewa a kwai dan banbanci a matanin sa kadan, na’am sun sassaba a tawilinsa kuma sun kidime , ka koma sahihul buhari j 9: sh 101, kitabul Ahkam - babul istiklaf, sahihu muslim j 6, sh 93 , 97.

7 Ka koma gaibatul kubra,na Sayyid Muhammad Sadr: 272 da abin da ke bayanta.

8 Ka komawa Al-tajul jami’u lil usuli, j 3 sah 40, ya ce shehunnai biyu sun ruwaito shi, da Turmuzi, ka koma Tahkikul hadis wa durukihi wa asanidihi, kitabul imamul Mahdi (a.s) na Ali da muhammad Ali dakhil.

9 Sahihuul Buhari mujalladina 9: sh 101, litafin Ahkam, babin nada halifa, bugun daru ihya’il turasil arabi, beirut.

10 ka koma Tarihin jami’ul usul, j 3 sh 40, ya ce yana mai yin Karin bayani kan hadisin: shehunnai biyu sun ruwaito shi, da Turmuzi, haka ma a cikin hamish, ya ce: abu dauwud ya rawaito shi a cikin littafin Mahdi (a.s), da lafazin: “wannan addinin ba zai gushe ba a tsaye har sai halifofi (imamai) goma sha biyu sun shugabance ku, kuma ka koma sunani Abidauwudj 2 sh 207.

11 Masdariko adrishin da ya gabata.

12 Masdariko adrishin da ya gabata.

13 Musnadi imam Ahmad dan Hambali, 6: 99, da 20359.

14 Almustadrak alal sahihaini j 3 sh 618.

15 Nuni zuwa ga fadinsa madaukakin sarki, {Ba ya yin furuci bisa son rai face sai idan wahayi a ka yi masa}” suratul najami, aya ta 3-4.

16 Bayanin wannan hadisin ya gabata.

17 Bahasin Shahid Sadir (r.a) kan Mahdi (a.j) shafi na 105- 107 wanda Dakta Abduljaaabba Shararata ya bibiya.

18 Ya zame wa Malamai laruru ta yanda suka yi ta yi wa wannan hadisin tawili bayana sun hadu kan ingancinsa, kuma abin da suka ambata na cewa su wane su ake nufi da wannan hadisin abu ne da ba zai taba karbuwa ba, kai wasu tawile-tawilan ma kwata-kwata ba zasu taba karbuwa ba kamar cewa Yazidu dan Mu’awiya yana cikinsu wanda kowa ya san shi da bayyana fasikancinsa, wanda malamai suka yi masa hukuncin wanda ya fita daga Musulunci, da kafirci ko kuma wanda ya ke kamanceceniya da wandanda suka fita ko suka kafirce.

19 SahihuMuslim j 6 sh 306, babain shugabanci, babin mutane su bi shugabancin Kuraishawa.

20 Ka koma Sahihul Bukhari j 4 sh 174, litattafin hukunce-hukunce babin nada khalifa; Musnadi Ahmad j 6 sh 94, hadisai masu numbar, 325, 20366, 20367, 20443, 20503, 20534, sunanu abi Dauwuda,j4 sh 3279- 3280, Mu’ujamul Kabir, Aldabarani, 2:238/1996. Sunanu Turmuzi, j 4 sh 501; Mustadrakul Hakim, j 3 sh 618; Hilyatul Auliya’i, na Abu Na’imi, j 4 sha 333; Fatahul bari, j 13 sh 211; SahihuMuslim mai sarhin Nawawi, j 12 sh 201; Albidaya wal nihaya na Ibni Kasir, j 1 sh 153, Tafsiri Ibni Kasir j 2 sh 24; a Tafsiri aya ta 12 daga surar Ma’idah. Kitabul suluk fi duwalul mulukna Makrizi, j 1 sh 13 - 15 daga kaso na farko, sharhin hafiz, ibni kayyim aljauzi, ala sunani abi dauda, j 11 sh 363, sharhin hadisi na 3259, Sharhil Akidal Dahawi, j 2 sh 736. Alhawi lillfatawi,Siyudi j 2 sh 85. Aunil ma’abudi sharhi sunani abi dauwuud, alazaim abadi, j 11 sh 362, shahin hadisina 4259. Mishkatul masabihi na na tabrizi, 3, shafi 327, j 3 sh 327 , 5983, silsilatul sahiha, albani, hadisi mai number, hadisi mai numba 376m kanzul ummal, 12, 32, 33848, da j12, sha 33/ 33858, da j 12 shafi 34/33861.

Kamar yanda su ma malaman hadisin shi’a suka fitar da wannan hadisin wanda daga cikin su akwai saduk a cikin kamalud dini j 1 shafi na 272, da khisal j 2 shafi 469 da 475, kuma hakika ya bibiyi hanyoyin hadisin da maruwaitansa a cikin Ihkakul hakki j 13 shafi na 1 - 50.

21 Tafsirul Kur’ani Karim, inbi kasir j 2 shafina 24- a cikin Tafsirin aya ta 12 daga cikin suratul ma’aida.

22 Sharhin akidar dahawi, alkadhil damashki, j2 sh 736.

23 Aunul Ma’abudi fi Shahi sunnanani abi Dawuda j 11 sh 246, Sharhin hadisi na 427, littafin Mahdi (a.s)bugun Darul kutubul ilmiyya.

24 Aunul Ma’abudi fi shahi Sunnanani Abi Dawuda j 11 sh 245.

25 Aunul Ma’abudi fi shahi Sunnanani Abi Dawuda j 11 sh 244.

26 Assuluk li Ma’arifatu Duwalul muluk, j 1 sh 13 - 15, kasona farko.

27 Alhawi lil fatawa j 2 shafina 85.

28 Kanzul ummal j 12 sh 34, hadisina 33861 ibni Najjar ne ya fitar da shi daga Anas.

29 Kanzul ummal j 12 shafina 32, hadisi na 33848.

30 Ka koma Gadinrna allama amini j 1 shafi 26-27, hakika ya ambaci wannan yana mai fitar da shi daga litattafan Ahlussuna.

31 Fara’idul Simdaini, j 2 shafina 313 hadisina 564.

32 Algadir wal- muaridhun, Alsayyid Ja'afar Murtadha Amuli: 70 - 72.

33 Yanabiyun Mawadda j 3 shafina 104, babi na 77.

34 Usulul kafi j 1 shafina 328, littafin hujjoji babin yin ishara da yin nassi zuwa sahibul dari.

35 Usulul kafi j a shafina 330, littafi hujja babain ambaton wadanda suka gan shi (a.s).

36 Kamalud dini j 2 sha 424 babina 42.

37 Man huwal Mahadi (a.s), (wanene Mahdi (a.s)) na Abu dalibTajlil Altabrizi : 460 – 506.

38 Kamaludddini j 2 sha 442, babina 43, an kabo daga gare shi a cikin Biharul anwar 52, 3. Babina 26.

39 Al’irshadna Shekh mufid j 2 shafi na 336.

40 Difaf’un an Kulaini j 1 shafina 567 - 568 na Hasan Hashim Smir Al-amidi.

41 Almahdil Muntazar fi Nahjulbalaga : Shekh Mahadi Fakih Imani : sh 16 – 30.

42 Imami na goma sha biyu, SayyidMuhammad Said Almusawai : 27- 70. Kuma hakika wanda ya yi tahkikkin littafin ya riskar da mazaje talatin daga Ahlussunna kan littfin kamar yadda a yazo a cikin Hamishin masdar 72 - 89, Almahdil Mau’udul Muntazar inda ahlussanna wal imamamiyya, na Shekh Najamul dinil Askari j 1 sh 220 – 226.

43 Difa’un anil Kafi j I sha 568.

44 Wannan daidai yake da a samo kwanon da ake auna tattasai da tumaturi da shi, a ce za a auna nuno, tare da cewa, kwanon awon nasu su zai iya zama yana da huda, alhali na nuno dole ya zama mai tsafta ta musamman, kuma mara huda dss, sabanin na tattasai da tumaturi.

45 Ka duba Usulul Kafi j 1 Sahfina 321 littafin hujja babin haihuwar Abu Muhammad Hasan dan Ali (a.s).Kamaluddin j 1 sh 40 Mukaddimar Mawallafi. Al’irshad j 2 sh 321 A’alamul wara bi A’alamulhuda na Fadhlu dan Hasan Altabari, shafi 357.Haka ma ka duba kamalul dini j 2 sh 475 babin 43 wandanda suka ga ka’im Mahdi (a.s).

46 Surar Maryam aya ta 12.

47 Al-sawa’ikul Muhrika Shafina 256 Darul Kutubul Ilmiyya.

48 Alfusulul Muhimma li ibni Sabbag Al - Maliki, sh 253, da Irshadna Shehul Mufid j 2 sh 274 da abin da ke bayansa.

49 Al - tattimma fi tawarikhul a’imma, na Sayyid Tajuddin Al’amuli daga manyan malaman karni na sha daya na hijiara, Nashri Mu’assat albi’isa Kum, ka koma sawa’ikul muhrika na ibni hajar 321 - 313 dominn ya ambaci wani bangare daga tarihin Imam da karamominsa.

50 Al-irshadna shehul Mufid j 2 sh 281, da abin da ya zo bayansa.Sawa’ikul Muhrika sh 312-313. Hakika ya kawo kissar da ta kasance tsakanin Imam Jawad (a.s) da yahaya dan aksam a lokacin ma’amun, da kuma yadda Imam (a.s) ya tabbatar da fifikonsa a sani da kwarewarsa wajenkure shi Alhali yana da ‘yan wadannan shekarun?

51 Alfusulum mihimma fi ma’arifatul A’imma na Ibni Sabbag Bamalike shafi na 253, da Irshad na ShehulMufid j2 sh 274 da abin da ya biyo bayansa.

52 Ka koma Al-majalisul Sanyya na Sayyid Amin Al-amuli, 2 j sh 468. Kuma wannan lamari ne shahararre da hassawa da ammawa (kebantattun mutane da ma game dari) suka cirato shi, ka koma Sihahul Akhbari,na muhamad dan Sirajud dini sh 44 ya cirato daga Imam Sadik wal mazahibul arba’a na Asad Haidar j 1 sh 55. Kuma Ibni Hajar ya fadi a cikin Sawa’ikul muhrika sh 305, “Ja'afar dan Muhammad hakika mutane sun cirato ilimi daga gare shi wanda mahaya suka yi tafiye-tafiye da shi kuma majiyarsa ta shahara cikin dukkanin garuruwa kuma manya shuwagabanni (malamai) sun rawaito daga gare shi kamar yahaya dan dan sa’idu da ibnu juraiji da maliku da Sufyanu guda biyu da Abi-Hanifa da Shu’uba da Ayyuba Al-sajastani.......”.

53 Kasancewar imami shi ne mafi ilimin mutanen zamaninsa lamarin da dukkanin mabiya imamai suka sallama a kansa, ka koma babul hadi ashara na Allama Hilli: 44 wannan ke nan kuma kuma haqiqa an jarraba su a kan haka bas au daya ba ba sai biyu ba amincin Allah ya qara tabbata a gare su, kuma sun ci wannan jarrabawoyin, ka koma sawa’iqul muhriqa, na ibni hajar shafi na 312, haqiqa Yahya dan Aksam ya nakalto wannan lamarin kan Imam Jawad dalla-dalla.

54 Hakika yin imani da Imamai ya kallafawa mabiyansu musibu masu yawa wannan abu ne da ya tabbata a tarihi kuma ba wata hanya da za a iya musa hakan, kuma wannan ya halarci lamari, shi ke bawawanda ba ya nan labari, duba makatilul dalibiyyin na abil farajil Isfahani.

55 Ka koma tarihin Imamai (a.s) da yadda suka fuskanci matsi da kora da kurkuku da kisa a wani lokaci.

Alfusulul muhimmana Ibni Sabbaga Bamalike.

Makatilul dalibiyyinna Ibni Faraj Al-isfahani.

Al’isrshadna Shehul mufid.

56 Yana yin nuni kan Imam Mahdi (a.s), wanda kafin sa kuma akwai Imam Jawad (a.s).

57 Kan cewa yazama wajibi ya zama mafifificin mutane kuma mafi iliminsu kamar yadda akidar imamiyya isna ashariyya take, ka koma littafin: Hakkin yakin fi ma’arifatul Usuludiini na sayyid Abdullahi Shubbar wanda ya rasu a shekara ta (1242 BH) j 1 sh 141, maksadi na uku.

58 Yana nufin gabatar da Imami yaro don a jarrabashi a gaban mutane don a bayyana hakikanin lamari.

59 Hakika ma’mun ya aikata hakan kuma gaskiya ta bayyana musamman ga malamai kuma sun san gejin ilimin da Imam Jwada (a.s) yake da shina fikihu da kalam. Ka koma Sawa’ikul muhrika na ibni hajar al’askalani. Shafi na 312.

60 Suran Maryam (a.s). aya ta 12.

61 Hakika hassawan Shi’a sun ga Imam Mahdi (a.s) kuma sun sami ittisali da shi kuma sun karba daga gare shi kamar yadda ya faru ta hanyar wakilai hudu, ka koma Tabsirar waliyyi fi man ra’al ka’imi Al- Mahdi (a.s), na Baharani , da Irshad, na Shehul Mifid, Shafi na 345. Kuma ka koma zuwa bayani gamsasshe a cikin Difa’u anil Kafi, na Sayyid Samir Sl-amidi j 1 sh 535 da abin da ke bayanta.

62 Bah usun haular Mahdi (a.s)na Sayyid Shahid Sadar (r.a) 93-99 Tahkikin Dakta Abduljabbar Shararah.

63 Magana kan lokacinsa a lissafe yake a ilimance, yana cewa hakika abu ne mai yiwuwa a ilimance sai dai be tabbata ba a aikace bisa hakika da yawa daga cikin nasarar da aka cimma a duniyar sararin samaniya da saukake abin hawa a sararin samaniya zuwa sauran taurari da sauran duniyoyi da makamancin su sun wayi gari tabbataccen abu a karshen karni na ishirin.

64 Na’am ba wani dalili na ilimi kwara daya da ya kore wannan mahangar, balle ma lallae malamai likitanci sun shagaltu a yanzu haka da kokarin gaske wajen ganin sun tsawaita rayuwar Dan’adam, kuma lalle akwai gomomin gwaje-gwaje da ka yi a wannan fagen, kuma wannan ma kadai ya isa a matsayin dalili mai karfi kan yiyuwa a nazarce ko a ilmance.

65 Likitocin da karatun likitanci sun tabbatar da wannan maganar kuma suna da sheda da waya a wannan fagen kuma ta yiyu wannan ne ya sa suka yi ta kokari da gabatar da gwaje-gwaje don tsawaita rayuwar mutane a bisa dabi’a kuma kamar dai yadda aka saba mahallin gwaji na farko su ne dabbobi don hakan ya sa lamarin ya zama da sauki kuma kar a sami wani abun gudu da zai hana a gudanar da wannan gwajin a kan Dan’adam.

66 Wadannan tambayoyin da Shahid Sadar yake kawowa hadafinsu shi ne kafa muhummiyar hakika, wacce ita ce cewa Manzon Allah (s.a.w) a lokacin da ya yi bushara da zuwan Imam Mahdi (a.s) , wanda yake ba yanayi ne na al’ada a rayuwar mutane ba, a dunkule hakan na bada labari kan tabbatar da wani abu da ya gabaci abin da zai iya yiyuwa ta hanyar ilimi, bayan karfafa yiyuwar hakan a ilimance, ma’ana wanzuwar mutum wani lokaci mafi tsaho sosai fiye da yadda aka saba, hakika misalin wadannan rigayar wajen fadakarwa kan tabbatattun abubuwa a wannan duniyar tuni kur’ani da hadisi madankaki sun rubuta hakan a wajaje masu yawa a cikin mas’aloli na dabi’a da halittu da rayuwa. Ka koma kur’ani da ilimi hadisi na Dukta Abdulrazak Naufal.

67 Yana yin nuni zuwa cewa wannan mana daga cikin gajiyarwa, kuma wannan baiwa ce ta musamman daga Allah Ta'ala kuma wannan lamari ne da musulmi ba zai iya musanta shi ba, bayan litattafan sama sun bada labarin ire-irensa. Musamman ma alkur’ani mai girma kamar abin da ya zo kan sha’ani shekarun Annabi Nuhu (a.s), haka ma abin da kur’ani ya bada alabari da shi na daga sauran gaibobi, bisa cewa da yawa daga ahlussunna da ma daga cikin mabiya sufaye da Ahlin irfani sun yi imani da faruwar karamomi, da abin da ya yi kama da mu’jiza ga waliyyai da salihai da makusanta a halarar Allah Ta'ala. Ka koma At-tasawwwufu wal karamat na ShekhMuhammad Jawad Mugniyya.Kuma ka koma Tajul Jami’u lil Usuli, j 5 sh 228. Kitabul zuhudu wal raka’iki.

68 Nuni ne zuwa wannan aya maialbarka : { Tsarki ya tabbata ga wanda ya yi tafiyar dare da bawansa daga masallaci mai alfarma zuwa masallaci mai nisa......} surar isra’i aya ta 1.

69 Wannan Nuni ne zuwa samar da ababan hawa na sararin samaniya, da hawa kan iska da yin tafiya mai yawa daga kasashenmu, da yanke hanya a cikin ‘yan awanni ko ‘yan kwanaki, kuma wadannan abubbuwan sun wayi gari hakika a rayuwarmu a wannan zamanin a karshen karni na ishirin.

70 Yana yin nuni kan abin da ka tanadawa Imam Mahdi (a.s) ma’abocin zamani na daga mihimmiyar rawar da zai taka wajen kawo sauyi bisa matakin samuwar dan adam, baki dayanta kamar yadda hadisi ingantacce yake yin nuni, -> ingantacce: “zai cika duniya da adalci da raba daidai kamar yadda ta cika da zalunci da danniya” wannan rawar da wannan aikin dukkanin malaman musulmai su yi ijma’i a kanta, sun yi sabani ne kan wasu abubuwa na gefe. Daganan ne zai zama tambayoyin da Shahid Sadar (a.s), ya jefo zasu zama sana da dalili na hankali mai karfi.

71 A cikin aya mai albarka ta {sai ya zauna a cikinsu shekara dubu ba hamsin}, surara Ankabutu: 14.

72 Ya fuskantar da wannan tambayar zuwa musulman da suka yi imani da kur’ani da hadisin Annabi (s.a.w) madaukaki, hakika malaman Ahlussuna sun rawaito cewa Annabi Nuhu ya rayu sama da haka, ka koma Tahzibul asma’a wallugat na Nawawi j 1 sh 176, kuma be inganta ba wani ya yi ishkali da cewa wance kur’ani ne ya bada labarinsa saboda haka nassin an yanke da tabbatarsa, kuma ya ta’allaka da Annabi mursali Nuhu (a.s) ne kawai, amma a nan ba mu da wani nassi yankakke.

Amsa: hakika aiki dai iri daya ne, shi ne kawo canji da kawar da zalunci da barna, kuma kamar yadda aka dorawa Annabi wannan aiki hakika a nan ma an dorwa wanda Allah Ta'ala ya zaba kamar yadda harshen ruwaya yake, Manzon Allah (s.a.w) ya ce: “Da ace ba abin da ya yi saura daga tashin duniya sai sai rana daya kawai da Allah Ta'ala ya tsawaita wannan ranar har sai an tashi wani mutum daga ‘yangidana sai ya cika da adalci kamar yadda ta cika da zalunci da danniya.....” Al-tajul jami’u lil’usul.

Amma ta bangaren kasancewarsa nassin ne tabbatacce hakika hadisan da suak zo kan Mahdi (a.s) sun kai haddin tawatiri wanda yake lazimta yankewa, babau banbanci tsakanin matsayoyin biyun, ka koma Tajul jami’u lil’usuli, j 5 sh 341 da 360, hakika an rawaito tawaturnancin wannan hadisin daga shaukani, kuma muhakkikai daga malaman bangarori biyu sun tafi kan cewa, wanda ya kafirce wa Mahdi (a.s) ya karfirce wa Manzo (s.a.w), wannan be kasance ba sai bisa la’akari da cewa lamarin ya tabbata a tawaturance, kuma yana daga cikin larurar addini kuma wanda ya musa haka ya kafirta a ijma’ance, kuma ka koma Al-isha’atu li Ashradul Sa’ati, na burzanji, a cikin bincikensa kan Mahdi (a.s) kuma mun nakaltu hikayar tawaturanci a gabatarwa ma.

73 Ai lamarin ya zama daga mu’ujiza kuma wannan ne abi da kur’ani ya fada, kuma ya zo a cikin Sunna mai tsarki, kuma ita mu’ujiza hakika ita ce wacce take hade da da’awar Annabta, da kuma da’awar wakilcinsu daga halarar ubanjiji, kuma ba wani musulmi da ya isa ya yi inkarin haka ko ya yi kokwanto a cikinsa, balle ma wanda ba musulmi ba ma ya yi tarayya da musulmai a yin imani da mu’ujizoji.

74 Surar Anbiya’u (Annabawa ) aya ta 69.

75 Yana yin nuni zuwa fadinsa madaukakin sarki: {sai muka yiwa Musa wahayi ka bugi kogi da sandarka sai ya tsage sai kowane banbare ya zama kamar babban dutse}. Surar Shu’ara’u aya ta 63.

76 Yanayin nuni zuwa dafinsa madaukakin sarki: {ba su kashe shi ba kuma ba su tsire shi ba, saidai an kamanta musu shi ne.....}. surar Nisa’i aya ta 157.

77 Ka koma Sirar Ibni Hisham j 2 sh 483, hakika ya nakalto wannan hadisar kuma abu ce da aka hadu a kanta.

78 Ta yiyu a ce: hakika doka a matsayin ta na doka babu makawa ta yi hukunci kan duk abin da ta hau kansa, kuma ba za a sauwara rashin yin aikinta ko karya ta ba, kuma lalle wasu masana sun lura cewa wata dokar ce take sabbaba a karya dokar dabi’a, kamar yadda lamarin yake dangane da dokar fusga (irin ta mayen karfe) (kamar yadda mayen karfe ke fusgar sauran karafa), wacce take lazimta fusgar abububwa zuwa mazauni tare da haka ruwa yana ta shi sama sakamakon zukarsa da tsrrai suke yi daga saiwa zuwa gaggar jiki zuwa cen saman bishiya ta hanyar tsiron kananan ganyayyaki, wannan kuma yana tabbata ne ta hanyar wata doka ta (kebance-kebancen kananan ganyayyaki). Ka koma al-kur’ani muhawalatan li fahmin asri). Dakta Msutafa Mahmud.

79 Hakika Shahid Sadar ya shimfida magana a wannan mas’alar a cikin littafinsa Falsafatuna, ka komamasa : shafi na 295 da 299.

80 Ka komaFalsafatuna : shafi na 282 da abin ya zo a bayansa.

81 Ka koma Basdi wa Sharhin nazariyya, a cikin “Usasul mandikiyya lil istikra’i”, a yayin da Shahid (r.a) ya isa ga gano mihimmin lamari mai tsananin mihimmanci mai tasiri kan nazarin masaniya a fadade.

82 Bahasi ne da aka yi amfana da shi daga littafin bahasikan imam Mahdi (a.s) na Sayyid Shahid sadar (r.a) shafi na 65-80, tahkikikn Dakta Abduljabbar Shararata.

83 Yanabi’ul muwadda j 3 shafina 297 babi na saba’in da takwas.

84 Yanabi’ul muwadda j 3 shafi na 297 babi na saba’in da takwas.

85 Yanabi’ul muwadda j 3 shafina 310 babi na tamanin.

86 Yanabi’ul muwadda j 3 shafina 386 babi na casa’in da hudu.

87 Yanabi’ul muwadda j 3 shafina 397.

88 Shubuhohi da raddodi, Halka ta hudu shafina 32.

89 Waye Mahadi (a.s) shafina 460.

90 Al-Mahdi (a.s) sadaruddin Sadar.

91 Cutar (Al-tausa) kurji ne mai ruwa.

92 Yanabi’ul Muwadda j 3 shafina 315- 317.

93 Is’aful ragibina shafina 157.

94 Is’aful ragibina shafina 227.

95 Yanabi’ul muwaddah j 3 shafina 304 babi na saba’in da tara.

96 Yanabi’ul muwaddah j 3 shafina 340 babi na tamanin da hudu.

97 Yanabi’ul muwaddah j 3 shafi na352 babi na tamanin da bakwai.

98 Al - Mahdi (a.s) shafi na 146- 148.

99 Ka koma llittafin gaibatul kubura, na SayyidMuhammad Sadar hakika ya yalwata a cikin bahasinsa,

100 Yana yin nuni zuwa gaibatul kubura.

101 Ka koma tabsiratul waliyyi fi man ra’al ka’imi na sayyid hashim bahrani, dafa’un anil kafi Alsayyid na samir Al-amidi j 1 shafi na 568 da abin da ke bayansa.

Tarihin wafatin safir (wakilin Imam Mahdi (a.s)na farko kusan a shekara ta 280h na biyu kuma a 305h na uku kuma a 326 shi kuma na hudu a shekara ta 328.

102 Ka koma tarihin rayuwar wadannan bayin Allah Ta'ala guda hudu a cikin littafin gaibatul sugura naMuhammad Sadar fasali na uku shafi na 395 da bayansa, bugun darul ta’aruf beruit 1980.

103 Kuma wannan tabbatar da samuwar wasikunsa ne wadanda su ne rubutattaun amsoshin da na baki da aka cirato daga Imam Mahdi (a.s), ka koma litattafin Ihtijaj na Dabrasi j 2 shafi na 523 da abin da ke bayansa.

104 Daga cikin abin da ya tabbata a tsakatsakin malaman adabin larabci da masu nakadin adabin na da, da na yanzu cewa salo shi ne mutum kuma wannan mahangar haka ta ke, daga nan ne muka ga kuma muka ji cewa da yawa daga malaman adabi da makaratar adabi suna banbanta da zarar an karanta nassinsu na wake ne ko na zube, sai kaga an ce wannan ta wane ko na wane ne, hakan be kasance ba face sai don kasancewar salo ko kace uslubi shi ne mutum kuma ko wane marubuci yana da tandu da tambura na musamman a cikin rubutunsa da za a iya tantance shi daga waninsa, wannan kenan ballantana kuma tantance rubutunsa madaukaki daga waninsa na daga rubuce-rubuce.

105 Yana yin nuni zuwa wakilannan hudu da aka ambata,

106 Wannan shi ake kira da (makomar addini) kuma a nan zamu lura da siffofin da Imam yake ganin sun zama dole mar’ja’i ya siffanta da su.

107 Hakika hanyar da Imam Mahdi (a.s) yake ganawa da cibiyoyinsa na ‘yan’shi’a ta hanyar matemakansa wakilansa ko ta wasu hanyiyin na daban, abu ne tabbatacce a tarihi wanda ke da samuwa ta yadda ba hanyar da za a iya musanta shi kamar yadda lamarin yake dangane da wakilci, ballantana kuma akwai wasu dalilai na daban masu yawa da suka jingina da labaran wadanda gasgata su ya wajaba, sannan hakika manufar hadisan nan masu yawa da suka zo, kamar hadisin da yake cewa “Duk wanda ya mutu be san imamamin zamaninsa ba hakika ya yi mutuwar jahiliyya” da makamancin haka. Hakika dukkanin wadannan baki dayansu, - wanda yake lamari ne da mafi yawan bangarorin musulmai suka tafi a kansa- yanke yana rusa dukkanin wani abu da masu kawo shakku suke tayarwa kan samuwar Imam da ci gaban rayuwarsa mai almarka madaukakiya , ka koma alkaibatul sugura na Sayyid Muhammad Sadar, shafi na 566.

108 Bayani mai tsarki ya zo daga jagora mai tsayuwa Mahdi (a.s)kan rashin yiyuwar ganinsa a sarari (wato bisa yanayin na bayyana ta yadda kowa zai gan shi ya ce ga shi nan), kuma wannan mahallin ittifakin dukkanin malaman imamiyya ne. Ka koma inda ka tattauna wannan matsalar a gaiba babba, na Sayyid Muhamma Sadar shafi na 639.Da abn da ke bayanta.

109 Bahsun haular Imam Mahdi (a.s) shafina 108- 111, wanda Dakta Abduljabbar Sharara ya yi wa tahkika da ta’aliki.

110 Surar Nabiya, aya ta: 107.

111 Bahsun haular Imam Mahdi (a.s) shafi na 83- 89 , wanda Dakta Abduljabbar Sharara ya yi wa tahkika da ta’aliki.

112 Yana yin nuni zuwa ga Akidar imamiyya masu bin Imamai sha biyu wanda suka dogara da dalilai na hanakali da wadanda aka cirato musammam ma Hadisin nauyaya biyu wanda ya zo mutawatiri: “ni mai bar muku nauyaya biyu ne a baya na ba za ku taba bata ba matukar kun yi riko da su littafin Allah Ta'ala da turaka ta Ahlin gida na”. Ka kuma ka duba SahihuMuslim j 4 shafi na 1873, kuma ka duba Sawa’ikul muhrika na Ibni Hajar Askalani: 89 ya ce: sannan ka sani cewa wannan hadisi na yin riko yana da hanyoyi masu yawa, kuma ya zo daga sahabi ishirin da wani abu.

Haka ma fadin sa Manzo (saw) mai tsira da amincin Allah Ta'ala “ba za su taba rabuwa ba sai sun iske ni a tabki, har inda Manzon Allah (s.a.w) yake cewa: “halifofi a baya na guda goma sha biyu ne dukkanin su daga kuraishu su ka fito”. Kuma dukkanin wadannan suna yin nunikan tabbatar da wannan ma’anar.

113 Manzon Allah (s.a.w) mafi girma Annabawa ya yi magana a waje da yawa kan abin da ya kebance su da rawar da suka taka, da ayyukansu da nauyyaye nauyayeynsu ya kuma ce su ne masu kula da shari’a kuma su ne jirgin tsira, kuma su ne amincin mutane kuma masu kare su daga bata kamar yadda nuni ya tabbata kan hakan a cikin hadisin sakalaini da hadisin ba zasu taba rabuwa ba kuma dukkanin su suna tabbatar da ismar su (Ahlulbaiti (a.s)), don ba yadda hankali zai karbi cewa su zama sune masu kare daga bata kuma ba zasu taba rabuwa da kur’ani da yake ma’asumi ba, alhali su ba ma’asumai ba ne!! Ka koma Usulul amma lillfikihul mukaran,na Allama Muhammand Taki Hakim, bahasin hujjancin sunna shafi na 169 da bayansa.

114 Wannnan jagora na tsawon Tarihi ya zama wanda aka kintsa shi a ruhi kuma an tanade shi dukkanin tanadi, wanda ya dace da ayyukan da zai gabatar, lamari ne da aka gama bincike a kan sa. Da zamu koma zuwa kur’an mai girma da zamu same shi yana magana kan wannan mas’alar a cikin tarihin annabawa a sarari musamman ma kan abin da ya shafi Annabi Nuhu (a.s), kuma lalle wannan lamarin ne da ke jan hakali, wata kila saboda kamancecceniya da tarayyar da ke tsakanin su kan rawa da ayyukan da aka dora musu kamar yadda shahid sadar ya fadakar zuwa ga hakan.

Ka duda Ma’al Anbiya’ina Afif Abdulfattah Dabara.

115 Kuma zan iya yiwuwa mu kusanto da wannan ma’anar da abin da muka rayu da shi kuma muka gan shi na faffadar gamammiyar tarayyar rashawa da daukakarta har sai da ta zama ita ce babbar daula ta biyu a duniya da suka yi rabebeniyar iko da tasirin karfin ci gaba da mamaya a siyasa su da America kuma tare su ka hau sararin samaniya, sannan sai muka ga rushewar gamayyar kasar rasha, ta yi kaca-kaca ta daidaice cikin gaggawa a irin wannan dan lokaci,dan kankani, hakika wane irin tasiri ne mai girma wannan lamarin ke da shi?Ya tsananin yadda wannan lamari ke cike da darasin? Ya tsananani yadda manuniya mai zurfi ke cike da wannan hadisa?

116 Ganjack roso (1712-1778) marubutu na malamain falsafa na faransa wasu daga cikin masu warwara suna ganin shi ne ya fi kowa tasiri a adabin faransa na wannnan zamanin da falsafar zamani kuma hakika rubuce rubucensa sun share hanya kan juyin juya halin faransa kuma mafi shaharan litattafansa suna magana kan tsarin zamantakewa. Ka koma littafin mausu’atul maurid,na Munir al-ba’alabaki, j 8 shafi na 169.

117 Yana yin nunikan wannan ayar ta kau’ani mai girma {Hakika su wani gungu ne daga samari da suka yi imani da ubangijin su sai muka kare su da shiriya} Surar Kahfi aya ta 13 kuma ka duba tafsirin ta a cikin Kashshaf na Zamakhshari j 2 shafi na 706.Bugun darul kitabul Arabi- bairut.

118 Yana nuni zuwa ayar: {sun zauna a cikin koginsu shekara dari uku kuma sukakara tara a kai} surar Kahfi aya ta 25.

119 Dukkanin wannanyana da alaka da tarbiyantar da shi da kintsa shi kintsawa ta musamman, da ma abin da yake cikin haka na mallakarsa ga mahanga gamammiya mai zurfi, ballantana kuma ka duba irin yadda da kansa ya ga raunin wadannan masu kambama kansu wadanda suka cika duniya da kurauruwa da iface- iface, suna bautar da mutane. Wannan abin da ya gani zai dada ba shi cancantar sosai da sosai, ya iya yin aikinsa da aka halicce shi don shi, ma’anana cika duniya da adalci kamar yadda ta cika da zalunci da danniya, wannan idan aka runtse ido daga cancantar sa ta zati da kulawar ubangiji ta musamman.

120 Kuma be kamata wani ya kawo ishkali da cewa Annabi Muhammadu (s.a.w) tare da cewa sakonsa zuwa ga duniya ne kuma aikinsa na kawo canji babban aiki ne sai dai shi ga shi ya rayu a cikin zagayen wayewar jahiliyya kuma be tasirantu da ita ba, haka ma annabawa magabata ta wace fuska za a kalli wannan lamarin?

Amsa: hakika Annabi Muhammadu (s.a.w) a aikace ya kasance cikin yanayi na kadaici kaco-kaf daga wayewar jahiliyya, kuma lalle kamar yadda a ya zo a tarihinsa an soyar da shi kebewa da kadaita, kuma ya kasance yana tafiya kogon hira yana yin bauta a cikinsa haka ma annabawa sun kasance suna nisantar abin da al’ummar su suke kai kuma sun kacance suna nisantarsu kuma zuwa ga haka ne wannan ayar ta yi nuni, {kuma yayin da ya nisance su, su tare da abin da suke bautawa ba Allah ba sai muka ba shi ishak}.Maryam aya ta 49.

B- hakika Annabin da aka aiko wahayi ake yi masa, kuma kai tsaye ana karfafashi daga sama kuma ana isar masa da ayyukan da matakan da zai dauka daya bayan daya, amma imamami (a.s) ba a yi masa wahayi kamar yadda akidar imamaiyya take, kuma ba a isar masa da umarni daga sama, na’am ana daidaita masa tafiyarsu da kiyayewar ubangiji, don haka yana da bukatar kulawa ta musamman. A lokaci guda kuma a daidai lokacin da ya kasance ya kusanci kuma ya sadu da wayewar musulunci, zai zama ana karfafafrsa daga iyayensa ta hanyar tushe da masaniya da ilimi, zai zama yana da tsinkaye kan gogayya dan’adam da wayewarsa a wajen ci gabanta da abubuwan da suka samar da ita da karfinta, haka ma tuntubenta da dalilan rauninta da rushewarta sai ya sami kwarewa da iko da kewayewa ga al’amura ba ki daya, wannan tare da kudurcewa da karfin ikon Imam na ilimin zati wanda Allah Ta'ala ya ba shi da kuma kasancewar sa wanda ake nusarwa daga sama.

121 Bahasikan Imam Mahdi (a.s) na Shahid Bakir Muhammad Sadr (r.a) shafi 89, a hamishi, tahkiki da ta’alifin, Dakta Abduljabbar Sharara, bugun markazin Gadir liddirasatul Islamiyya.

122 Duk da Mihmmancin da Shahid Sadr ya bawa wannan lamarin a nan, da kuma fagen nunar ta ko kuma nunar da ita a wajen cin nasarar juyin juya hali- wannan fahimta ce mai zurfin gaske, a cikin tasirin kan tsarin zamantakewa da na kashin kai sai dai shahid ya bujuro da sabuwar mahanga a cikin fahimtar nazariyyar motsin kawo canjin da sama ta yi magana a kansa, ta hanyar manzancin sama, shi wannan lamarin ta bangaren manzanci yana danfare da doka ta musammman amma ta bangaren zartarwa yana ta dogare da yanayin da duniya take ciki kuma tana da alaka da wannan yanayin a matakin lokaci da nasara, kuma abin da nake nufi da yanayin da ake ciki shi ne: yanayi na siyasa da yanayin zamantakewa da rayuwar al’umma da yanayin daulolin zamanin da kuma iyakacin ikon mutane a abin da suke da nagarta a kai da tanadinsu na ruhi.

123 Yana mai yin nunikan fadinsa madaukakin sarki: {sai suka ce ku kona shi ku kubutar da allolinku in har ku masu yin haka ne* sai muka ce ya ke wuta ki zama sanyi da da aminci ga ibrahim * kuma sun yi nifin yi masa kaidi sai muka mayar da su su ne hasararru}.

124 Ka komawa ruwayar a cikin tafsirin Ibni Kasir 2: 33 kuma ka koma Biharul Anwar na Majlisi, 18, da 47 da 52 da 60, da 75, babin mu’ujizojin Annabi Muhammadu (s.a.w)

125 Tarihul Dabari 2: 244 abubuwan da suka faru a shekara ta biyar bayan hijira.

126 Kamar yadda nassin hadisin Annabi Muhammadu (s.a.w) yake “da ace ba abin da ya rage wa duniya sai rana daya tal, sai Allah Ta'ala ya tsawaita wannan ranar har wani mutum ya zo daga yan’gida na ya cikita da adalci da daidato kamar yadda ta ciki da zalunci da danniya” ka koma Al-tajul jami’u lilusul j 5: 343 ya ce abu Dauda da Trimuzi sun rawaito shi.

127 Hakika mun ga a farkon shekaru na 90 abin da ya gaskata wannan mahangar da Shahid ya fitar da ita dogara da kwarewarsa mai zurfi da sanin mazaunar dan’adam hakika tarayyan kasashen guruguzu sun rushe rushewa mai sauri sosai da yanayin da ya bawa kowa mamaki, alhali kuma daya ce daga cikin manya-manyan zakaru biyu da suke da tasiri a cikin fadin duniya.

Abin Da Littafin Ya Kunsa

Mahdawiyyanci1

Mawallafi: Shekh Abdulkarim Al-Bahbahani1

Fassarar: Munir Mhumamad Sa’id 1

Da Suanna Allah Mai Raham Amai Jin Kai2

Mahdiyanci a wajen Ahlulbaiti2

Imamai goma sha hudu su ne sirrin fahimtar mahdawiyya2

Fasali na daya7

Tabbatar Mahangar Mahdawiyyanci A Akidance A Wajen Ahlulbaiti (a.s)7

Rudewar Makarantar Halifofi Kan Fassasrar Wannan Hadisin 13

Fasali Na Biyu 25

Kebance-Kebancen Fahimtar Mahdawiyyanci A Wajen Ahlulbait (a.s)25

Kebance-Kabence Na Farko: Tabbatar Haihuwar Imam Mahdi A Wani Boyayyen Yanayi Na Musamman Da Babu Makawa Sai Ya Faru 25

Shedu Na Tarihi Da Ke Nuni Kan Samuwar Imam Mahdi (a.s)28

‘Yar Matsaya Tare Da Masu Musantawa39

Kebance-kebancen na biyu Imamamanci a kananan shekaru 43

Kebance-kebance na uku: fakuwar da ta lazimci rayuwa budaddiya tare da budewar zamani 56

Ta biyu:- marahalar tabbatar da tabbatuwar hakan a aikace dangane da Imam Mahdi (a.s)76

Ta biyu: HANYA TA TARIHI: 82

KISSA TA BIYU: 88

Fasali na uku: 97

Kimar Akida Ga Sanin Mahdi A Makarantar Alulbait (a.s) 97

Sakamakon Bincike119