• Farawa
  • Na Baya
  • 19 /
  • Na Gaba
  • Karewa
  •  
  • Gurzawa HTML
  • Gurzawa Word
  • Gurzawa PDF
  • Budawa: 1790 / Gurzawa: 732
Girma Girma Girma
Tawassuli

Tawassuli

Mawallafi:
Hausa

KAMUN KAFA(Tawassuli)

Wallafar: Ayatullahi Ja'afar Subhani

Fassarar: Hafiz Muhammad Sa’id

KAMUN KAFA DA ANNABAWA DA WALIYYAN ALLAH

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Imam Mahadi (A.S) yana cewa : “Kuma Kowane mutum daga cikinku ya yi aiki da abin da zai kusanta da shi zuwa ga soyayyarmu, kuma ya nisanci abin da zai kusantar da shi ga kinmu da fushinmu” Biharul Anwar: 53, shafi 126.

Kamun kafa

Tsarin duniya yana bisa ka'idoji da dalili a kan komai, saboda haka duk wani abu wanda zai faru a duniya yakan faruwa tare da dalili wanda ya kebanci shi abin da ya farun, sannan shi ma wannan abin da ya faru zai tasiri ga wani abu na daban, tasirin da wani abu yake sanya a cikin wani daban duk yana faruwa ne da izinin Allah madaukaki. Allah shi ne wanda ya halicci duniya sannan ya sanya alaka tsakanin abubuwan da suke duniya ta yadda wasu sukan yi tasiri a cikin wasu. Babu shakka rana tana bayar da wani sinadari wanda sauran halittu suke amfani da shi don su rayu, haka nan wata yana bayar da haske, sannan wuta tana bayar da zafi. Dukkan wadannan abubuwa suna yin tasiri ga waninsu, sannan akwai alaka ta musamman tsakanin rana da wata da wuta da kuma abin da suke bayarwa. Sannan dukkan wannan tasirin da ake gani babu wanda yake sanya shi sai Allah wanda shi ne ya halicce su, sannan kuma shi ne ya sanya wannan alakar da take akwai abin da yake faruwa tsakanin abubuwa daban-daban, kuma dukkansu suna samuwa daga gare shi maudakaki. Sakamakon haka ne wani lokaci yakan dauke tasirin da abu yake da shi, kamar yadda ya dauke zafin wuta ga annabi Ibrahim (A.S) ya kuma daidaita ta tamkar wani lambu mai sanyi, wannan kuwa duk don ya nuna cewa daga gare shi ne dukkan wannan tasirin na hakika yake da kuma niyyarsa ne.

Daga wannan bayanin muna iya daukar sakamako cewa: duk wani abu wanda yake faruwa a cikin duniya muke ganinta, a lokacin da muke ganin cewa ta samu ne daga wani abu daga cikin abubuwan da suke a cikin duniya, a daida- wannan lokacin kuma suna zuwa ne daga Allah kuma aikinsa ne. Sannan wannan abin bai saba wa hankali ba ta yadda za a ce ba zai yiwuwa ba. Domin kuwa Allah shi ne wanda yake da cikakken iko yake kuma yin wani abu ba tare da taimakon wani ba, amma dukkan wani yayin da zai aikata wani abu sai da taimakon Allah. wato duk abin da suke aikatawa tare da izinin Allah suke aikata shi, don haka muna iya cewa su ne suka aikata kuma muna iya cewa Allah ne domin kuwa a hakikanin gaskiya shi ne ya aikata, domin kuwa da bai bayar da izini ba, ba za ayi hakan ba.

Sannan kowa ya san daya daga cikin matakan tauhidi ko kadaita Allah shi ne kataita Allah a cikin halitta, wato babu wani mai halittawa sai Allah madaukaki, amma duk da haka kadaita Allah a cikin halittawa ba yana nufin kore duk wani tasiri daga wani abu ba, wato ma'anarsa shi ne halitta ba tare da dogara da wani ba, shi kadai ne yake iya yin haka, sannan duk wani tasiri na sauran wasu halittu yana samuwa ne da izinin Allah.

A cikin wasu ayoyin an yi nuni da dukkan wadannan nau'o'i guda biyu na yin tasiri. Misali aiki guda a daidai lokaci guda ana a jingina shi zuwa ga Mutum, sannan kuma ana jingina shi zuwa ga Allah, duk da cewa aiki guda yana gangarowa ne kawai daga abu guda. Amma tunda wadannan masu aikin daya yana karkashin daya ne babu matsala, wato daya shi ne na asali dayan kuwa yana bin na asalin, saboda haka babu abin da zai hana hakan.

Allah yana cewa wa Manzo (S.A.W): "Ba kai ne ka yi jifa ba a lokacin da ka yi jifa". A nan Kur'ani yana jingina aiki guda daya zuwa ga masu aiki guda biyu kamar haka:

1- Lokacin da ka yi jifa.

2- Allah ne ya yi jifar.

Dukkan wannan jinginawa guda ta yi daidai kuma ta dace da wurin, domin kuwa aikin Manzo ya faru ne da taimako da izinin Allah, saboda haka jingina wannan aiki guda daya ga dukkansu ya yi daidai. Sannan kamar aiki guda a jingina shi ga Allah sannan a jingina zuwa ga wani daban ya zo da yawa a cikin Kur'ani. Amma a nan kawai zamu bayar da misali guda biyu kawai:

1-Kur'ani a lokaci guda yana jingina rubuta ayyukan bayi zuwa ga mala'iku, sannan a wani wurin daban yana jingina wannan aiki zuwa ga Allah madaukaki.

2- A wani wuri ana jingina daukar rayukan mutane zuwa ga mala'ikun mutuwa, amma a wani wuri ana jingina wannan aiki zuwa ga Allah. Wadannan ayoyin suna bayyanar da yadda tsarin halitta yake karkashin ka'idar tasiri da mai tasiri, ta yadda abubwan da suke fauwa suke tasiri tsakanin juna. Amma dukkan wannan tsari suna jingina ne zuwa ga Allah madaukaki, sannan a karkashin nufinsa da izininsa suke ci gaba da rayuwarsu. Saboda haka duk wani abu wanda yake yin tasiri a cikin tsarin duniya, yana karkashin rundunar Ubangiji ne sannan kuma aikata abin da Allah ya umurce su ne. Sannan Allah kawai ne ya san yawan wannan runduna ta Allah.

Tare da la'akari da wannan bayani, wanda yake matsayin nuni daga wahayi, (cewa babu mai halitta da gaskiya sai Allah) sakamakon binciken dan Adam na ilimi (ta yadda suka tabbatar da yadda tasirin da yake akwai tsakanin halittu a cikin duniya) ba ya nuni da sabani a kan abin da muka ambata kokadan. Wadanda suke ganin wahayi ya saba wa ilimi ko kuma addini ya sabawa ilimi, ba su yi kyakkyawar fassara ba ne a kan hakan. Ko kuma sun yi wa ilimin zamani mummunar fahimta. Da wata ma'anar kuwa, duk wadannan abubuwa guda biyu na kasa sun dace kuma sun yi daidai su ne kamar haka:

1-Imani da kadaita Allah a cikin halittawa cewa babu wani wanda yake yin wani abu ba tare da dogara da wani ba sai Allah.

2-Tasirin wasu abubuwan a cikin wasu ayyuka dukkansu suna faruwa ne da izinin Allah da nufinsa. Idan muka ga wadannan asali guda biyu wani lokaci suna karo da juna, wannan ya samu asali ne ta yadda wasu suke fassara kadaita Allah a cikin halitta da wata ma'ana wacce ba ta inganta ba. Ta yadda suke daukar babu wani mai yin wani abu sai Allah kawai, wato duk wani mai yin wani abu, ba shi yake yin abin ba, kawai Allah ne yake yin komai, dan Adam ba shi da hannu wajen yin ayyukansa (nazarin Asha'ira). Ko kuma kamar yadda wasu suke ganin bayan wadannan abubuwan da muke gani a cikin duniya suna da tasiri ga wasu abubuwa, babu wani da sunan Allah wanda yake da tasiri a cikin duniya, wato duk abin da mutum ya yi daga gareshi ne babu hannun Allah a cikin. (Nazarin wadanda ba su yarda da wani abu ba a bayan wannan duniyar da muke gani).

Saboda haka dukkan wannan fahimta guda biyu kuskure ce kuma ba ta inganta ba, wanda dukkan biyun yana nuni ne ga takaitawa da kuma wuce wuri. Rashin ingancin fahimta ta biyu kuwa ya faru ne sakamakon yadda suke ganin duniya kawai ta takaita ne ga wannan duniya da muke gani kuma muke iya jinta, wato ba su yi imani da duniyar gaibu ba, wanda ba ya bukatar wani Karin bayani. Domin kuwa a nan muna magana ne da wadanda suka yi imani da Allah kuma suna ganin rashin ingancin akidar daukar wannan duniyar ita ce kawai kuma babu wani abu a bayanta. Amma rashin ingancin fahimta ta farko kuwa yana komawa ne ga wasu daga cikin malaman akida wadanda suka tafi a kan wannan fahimta, alhali kuwa Allah madaukaki a fili yana nuna yadda halittu suke da tasiri a cikin rayuwa, wajen faruwar wasu abubuwa. Sannan kuma kowa zai iya shaida hakan domin kuwa wani abu ne wanda muke gani da idanummu.

Saboda haka ta yaya zamu ki yarda da tasirin da halittu suke da shi a cikin rayuwa, shi kuwa wahayi yana bayyana gaskiyar wannan al'amari. A matsayin misali yana bayyanar da ruwa a matsayin wanda yake da tasiri wajen rayuwar tsirrai, kamar yadda yake cewa: "Shi ne wanda ya sanya muku kasa a shimfide, sannan ya gina muku sama, Kuma yana saukar da ruwa daga sama, sannan yana fitar da 'ya'yan itatuwa daga ruwa wadanda arziki ne a gare ku. "

Saboda haka nufin Allah ya yi rigaye a kan cewa duk da cewa dole ne mutum ya yi imani da cewa komai yana zuwa ne daga Allah, amma duk da haka mutum dole ne ya tanaji wasu abubuwa wadanda zasu kai shi zuwa ga cimma abin da yake nema.

Wannan asali da ka'ida kuwa, tana gudana har da abubuwan da suka shafi shiryarwa da makamantansu, sakamakon haka ne Allah madaukai ya bai wa mutum wata halitta a cikin zatinsa wacce zata taimaka masa wajen yin imani da Allah, haka hankali, annabawa da malamai da masana da makamantan wannan, Allah madaukaki ya sanya su a matsayin wadanda zasu yi mana jagora domin mu samu shiriyar Ubangiji. Kamar yadda ya kasance a wasu wurare a cikin Kur'ani mai girma Allah yana bayyana cewa shiriya wani abu ne daga gare shi, kamar inda yake cewa: "Yana batar da wanda ya so yana kuma shiryar da wanda ya so" .

Sannan wani wurin yana cewa: "Lallai kana shiryarwa zuwa ga hanya madaidaiciya".

Sannan babu karo da juna don an jingina shiryarwa zuwa ga dukkansu su biyun, wato asalin shiryarwa yana ga Allah, sannan Manzo wanda yake kamar sila ne na aiwatar da wannan aiki, babu laifi a jingina wannan aiki zuwa gare shi.

Takaitaccen tunanin wasu wadanda suke aibata kasantuwar tasirin wasu halittu ya samu asali ne sakamakon rashin fahimta mai kyau a kan koyarwar Kur'ani mai girma kamar yadda suke ganinsa ya saba da azirtawar Ubangiji da kuma tawakkali da shi, don haka ne ba su iya fassara koyarwar Kur'ani ba da kyau kamar yadda ya kamata.

Kasantuwar tasirin wasu daga cikin abubuwan halitta, sama ba ya karo da tawakkalli ko kadaita Allah a cikin tafiyar da al'amura, haka nan a cikin kadaita Allah a cikin ayyukansa. Domin kuwa a wajen mutum mai tauhidi wanda kuma yake da ilimi, dukkan wasu abubuwan da suke tasiri a cikin rayuwa suna yin wannan tasiri ne a karkashin inuwar Ubangiji da izininsa. Sannan yana ganin duk wani tasiri da yake a cikin duniya yana bayyana nufin Ubangiji wanda ba shi da iyaka wajen aikinsa kuma wanda ya halicci duniya baki daya.

Sannan dangane da bukatun ruhi da na zahiri a wajen hakan, babu wani bambanci. Sakamakon haka ne Allah yake umurtar masu imani da su tashi domin su yi kamun kafa a wajensa inda yake cewa: "Yaku wadanda kuka yi imani, ku ji tsoron Allah, sannan ko nemi tsani zuwa gare shi, Kuma ku yi jihadi a tafarkin Allah ko kun rabauta".

A nan dole mu yi bincike a kan ma'anar wannan tsani da aka ambata a aya ta sama me ake nufi da shi?

Marubuta kamusun lugga sun bayani a kan yadda ake amfani da lafazin wasila cikin harshen larabci kamar haka:

1-Makami da matsayi: a wani hadisi Manzo (S.A.W) yana cewa: "Ku nema mini matsayi a wajen Allah"

2- Kusanci zuwa wajen Allah.

3- Samar da abubuwan da zasu kusantar da mutum ta yadda zai samu kusanci zuwa ga Allah.

Tabbas ma'ana ta farko ba ita ake nufi ba a nan, domin kuwa matsayin da Manzo yake da shi a wajen Allah babu wanda yake da shi, kuma babu wanda zai samu kamarsa. Saboda haka dole ne mu fassara wannan aya da daya daga cikin ma'anoni biyu na karshe, kuma ga dukkan alamu wannan aya tana daukar ma'ana ta uku ne, domin kuwa abin da yake tabbatar da hakan bayan an yi umarni da neman tsani, yana yin umarni da jihadi wanda yana sanya kusanci zuwa ga Allah. Sannan wannan ya zo a cikin hadubar Imam Ali (A.S) wanda ya dauki ma'anar tsani da cewa shi ne riko da abin da zai kusantar da mutum zuwa ga Ubangiji, inda yake cewa: Mafificin abin da masu neman kusanci zuwa ga Allah zasu nemi kusanci zuwa gare shi, shi ne yin imani da shi, da manzonsa da yin jihadi a tafarkin Allah, sannan da tsayar da salla domin kuwa hanya ce kuma shari'a ce, sannan fitar da zakka.

A cikin wannan huduba ta Imam yana kawo wajibai na shari'a wanda yake nuna cewa su ne suke kusantar da mutum zuwa ga Allah. Ayar da aka ambata a sama, tare da hukuncin hankali tana yi mana nuni ne tana cewa: Dan Adam, wajen samun daukaka ta ruhi kamar kusanci zuwa ga Allah, kamar yadda ya kasance yana neman abin da zai biya bukatunsa na duniya, suma haka dole ne ya nemi abin da zai kusantar da shi zuwa ga wadannan abubuwan da yake bukata na ruhi, sannan ba tare da wannan ba mutum ba zai iya cimma abin da yake bukata ba.

Abin da yake akwai a nan shi ne abubuwan da suke kusantar da mutum zuwa ga Allah dole shari'a ce zata bayyana su. Domin kuwa hankalin dan Adam ba zai iya gano wadannan abubuwan ba, ta yadda zai gano abubuwan da zasu kusantar da shi zuwa ga Allah da abubuwan da zasu kai shi zuwa ga gafara da makamantansu, sannan bai kamata ba a nan wani ya yi tunanin cewa da wannan ayar ne kawai za a iya kafa hujja a kan ingancin kamun kafa da annabawa da waliyyai. Wannan aya kamar wata ka'ida ce ta baki daya wacce kuma hankali yake hukunci a kan ingancinta, amma dangane da abubuwan da zasu kusantar da mutum ko su sanya ya samu gafara ko ya samu biyan bukatunsa na ruhi, hankali ba zai iya gane wannan ba, saboda haka dole ne Allah ko manzonsa da ma'asumai (A.S) su bayyanar da hakan. Kamar yadda imam a huduba ta sama yake bayyanar da cewa imani da Allah da manzonsa da jihadi a tafarkin Allah, da tsayar da salla da bayar da zakka suna daga cikin muhimman abubuwan da suke kusantar da mutum zuwa ga Allah.

Yanzu kuma lokaci ya yi inda zamu bayyanar da kashe-kashen neman tsani ko kamun kafa da wata ma'anar, sannan mu yi bayanin hukuncin kowane ta yadda ya dace da Kur'ani da Sunna ko kuma sabanin hakan.

Kamun kafa yana da kashe-kashe kamar yadda zamu ambata a kasa kamar haka:

1-Kamun kafa Da Sunaye Da Siffofin Allah

Daya daga cikin rabe-raben kamun kafa ko neman tsani zuwa ga Allah shi ne neman kusanci zuwa ga Allah ta hanyar kiran sunaye da siffofinsa. Wannan nau'i kuwa na kamun kafa ko tawassuli ya zo da yawa a cikin ruwayoyin Ahlul baiti (A.S), amma a nan kawai zamu wadatu da hadisai guda biyu da suke nuni a kan haka:

Tirmizi a cikin Sunan dinsa ya ruwaito daga Buraida shi kuma daga Manzo (S.A.W) cewa yaji wani mutum yana cewa: Ya Allah ina rokon da kasantuwar na sheda cewa babu abin bauta da gaskiya sai kai, sannan kai kadai ne kuma mai biyan bukata, sannan ba a haife ka ba kuma ba ka haifa ba, sannan babu wani wanda ya yi daidai da kai.

Sai Manzo ya ce masa lallai ka roki Allah da babban suna wanda idan aka kira sa da shi zai amsa, idan kuwa aka roke shi da shi zai bai wa mutum abin da ya nema.

2-Ya zo a cikin wata addu'a Imam Bakir da Imam Sadik (A.S) suna cewa: "Ya Allah ina rokon ka da babban sunanka wanda ya fi kowane girma, mafigirma da daukaka wanda idan aka roke ka da shi domin kofofin da suke a kulle a sama ana so su bude zasu bude, sannan idan aka kira ka da shi domin fadada kofofin da suke kasa zasu fadada, kuma idan aka roke ka da shi domin samun sauki, za a samu saukin. "

2-Kamun kafa Da Kur'ani

Daya daga cikin hanyoyin da ake kamun kafa da su domin neman kusanci ga Ubangiji shi ne mutum ya karanta Kur'ani, ta wannan hanyar sai Allah ya biya masa bukatarsa. A hakikanin gaskiya wannan nau'in kamun kafa, kamun kafa ne da ayyukan Ubangiji, domin kuwa Kur'ani maganar Allah ce wacce ta sauka a kan zuciyar Manzo (S.A.W)

Ahmad Bn Hambal ya ruwaito daga Imran Bn Husaini yana cewa: Na ji daga manzon Allah (S.A.W) yana cewa: "Ku karanta Kur'ani ku roki Allah da shi, kafin wasu gungun mutane su zo wadanda zasu roki mutane da shi.

Idan muka lura da kyau a cikin wannan hadisi yana nuna mana wani abu, wannan kuwa shi ne, kamun kafa da duk wanda yake da girma da matsayi a wajen Allah wani abu ne wanda ya halatta, saboda mustahabbi ne a daren lailatul kadari mutum ya buda Kur'ani ya karanta ya roki Allah da shi tare da wannan addu'a kamar haka: "Ya Allah ina rokonka da wannan Kur'ani da abin da ka saukar a cikinsa, a cikinsa akwai babban sunanka da sunayenka kyawawa…

3-Kamun kafa Da Kyawawan Ayyuka

Kamar yadda muka ambata a farkon wannan Bahasi cewa idab mutum yana so ya cimma wani abu na rayuwar duniya ta hanyar hankalinsa ne zai gano ta wace hanya ce ya kamata ya bi domin ya cimma wannan abin da yake nema. Wato mutum ya san abin da ya dace ya aikata domin ya biya bukatunsa na rayuwa, misali kamar idan mutum yana jin yunwa ko kishirwa ya san cewa abinci ko ruwa zai sha don ya yi maganin wannan kishirwa da yunwar. Amma dangane da abin da ya shafi ruhi ko lahira, ba zai yiwu ba mutum ya iya gano hanyar da zai bi don ya cimma abin da yake so ya cimmawa, saboda haka a nan yana da bukatuwa zuwa Allah ko wakilinsa wanda zai gwada masa hanyar da ya kamata ya bi, sannan ba tare da jagorancinsa ba babu yadda zai yi ya isa zuwa ga hadafinsa, domin kuwa bin wata hanya wacce ba shari'a ba ce ta bayyana hakan zai zama bidi'a a cikin addini. Saboda haka musulmi dole ne a nan dangane da abin da ya shafi addini ya yi riko da abin da yazo a cikin Kur'ani da Sunna.

Kamun kafa da kyawawa kyawawa wanda shi ne nau'i na uku a cikin wannan Bahasi, a cikin Kur'ani an yi nuni da shi duk da cewa ba a bayyane ba ne kamar yadda ya zo a bayyana ne a cikin hadisai, bayaninsa kuwa atakaice shi ne, idan mutum ya aikata wani aiki domin Allah, yayin da mutum ya shiga wata matsala, yana iya ambatar wannan aikin da ya yi mai kyau domin Allah madaukaki ya yaye masa matsalar da ya shiga. Kai duk lokacin da mutum ya aikata wani aiki mai kyau yana iya rokon Allah da ya biya masa bukata da wannan aiki da ya aikata. Ga wasu abubuwa da suka zo a tarihi wadanda suke ba da sheda a kan hakan.

1-Annabi Ibrahim yayin da yake gina dakin ka'aba, ya roki Allah da ya sanya shi da dansa Isma'il su kasance masu biyayya ga Allah. Ga abin da Kur'ani yake cewa a kan haka: "A lokacin da Ibarahim shi da Isma'il suke daga ginin Ka'aba, sai suka ce ya Allah ka karba mana kai ne mai ji masani. Ya Allah ka sanya mu masu mika wuya gare ka, sannan daga zuriyar mu ka sanya su masu mika wuya a gareka, ya Allah ka koyar da mu ayyukan hajji, ka kuma karbi tubarmu, lallai kaine mai karbar tuba mai jin kai. " Mun ga yadda annabi Ibarahim da dansa Isma'il suka yi kyakkyawan aiki na ginin dakin ka'aba, a wannan lokaci sai suka roki Allah wasu abubuwa kamar haka:

A-Karbar wannan aiki daga dukkan su biyun.

B-Allah ya sanya su masu biyayya a gare shi.

C-Koyar da su aikin hajji.

D-Karbar tubarsu da sanya su a cikin rahama.

2-A cikin wata ayar ga abin da ya zo: "Muminai wadanda suke cewa: Ya Allah lallai mun yi imani ka yi mana gafara a kan zunubbammu, sannan ka tseratar da mu daga azabar wuta".

A cikin wannan aya sun roki Allah da cewa ya gafarta musu zunubbansu sakamakon ayyukan kyawawa inda suke cewa "lallai mun yi imani da kai".

Kamar yadda muka yi bayani a baya, ayoyin Kur'ani sun yi nuni da halascin kamun kafa da ayyuka na gari duk da cewa ba a bayyane ba ne. Amma a cikin ruwayoyi an yi bayanin hakan a fili. Sannan masu ruwaito hadisi daga bangarori guda biyu, sun ruwaito cewa wasu muminai guda uku sun kasance a cikin daji, sai ruwan sama ya taso, sai suka shiga cikin wani kogo domin su buya. Amma cikin rashin sa'a sakamakon wannan ruwa da iska sai wani bangaren dutse ya gangaro daga sama ya rufe kofar wannan kogo, a wannan lokaci sai daya daga cikinsu ya ce: Fadin gaskiya ce kawai abin da zai fitar da mu daga cikin wannan dutse, don haka ku zo duk wanda ya yi wani kyakkyawan aiki ya fada, sai mu roki Allah sakamakon albarkacin wannan aiki ya tseratar da mu. Dukkansu ukun suka fadi wani aiki wanda suka yi saboda Allah, kamun kafar da suka yi da wadannan ayyuka na su, cikin ikon Allah sai wannan dutse ya bude suka fita daga wannan hali da suka shiga.

Malamin Hadisi Baraki (ya rasu shekra ta 274) bayan ya ambaci wannan labari sai ya ce: Daya daga cikinsu cewa ya yi, ya kasance na baiwa wata mace kudi domin mu aikata wani aiki wanda bai dace ba, sannan kuma ita ma ta shirya a kan hakan, amma sai na tuna cewa akwai azabar lahira ga masu yin hakan, sai na kaurace wa wannan aiki, a wannan lokaci sai kofar ta dan bude kadan.

Sai daya kuma daga cikinsu shi ma ya ce:

Na ksance na tara wasu mutane domin su yi mini aikin kwadago, sannan zan ba kowane daya daga cikinsu rabin darhami matsayin ladar aikinsu. Bayan sun gama wannan aiki sai wani daga cikinsu ya nemi in ba shi darhami guda, wato a matsayin shi ya yi aikin mutum biyu ne, amma sai ban amince da abin da ya fada ba, sai bai amshi komai ba ya fita, (sai na kasance na yi amfani da kudin na wadanda suke a hannuna) na yi noma sannan kuma na samu amfani mai yawa. lokacin da ya ji wannan labari sai ya zo a wajena, sai ba shi darhami dubu goma, ya Allah na yi wannan aiki ne domin neman yardarka. a wannan lokaci sai kofar kogo ta dan kara budewa.

Sai na ukkunsu ya ce: Wata rana na kawo wa babana da mamana kwanon madara sai na tarar da su duk suna barci. Sai na yi tunani a cikin raina cewa idan na ajiye musu wannan madara a kasa na tafi gida mai yiwuwa kafin su tashi kuda ko sauro ya fada musu a cikin wannan madara, sannan kuma ba ni so in tayar da su daga barci. saboda haka sai na yi tsaye da wannan madara har suka ta shi daga barci sannan suka sha wannan madara. A wannan lokaci sai kofar kogo ta bude dukkanta suka fita daga wannan hali da suka shiga.

Wannan kissa kuwa masu hadisi daga bangare guda biyu Sunna da Shi'a sun kawo ta duk da cewa akwai sabani a wasu abubuwa.

4-Kamun kafa Da Adu'ar Manzo (S.A.W)

Manzo (S.A.W) mutum ne wanda yake ya fi kowa girma da daukaka a cikin dukkan halittar da Allah ya yi, Ayoyin Kur'ani sun yi nuni da haka a wurare da dama, saboda haka ba zai yiwu ba mu kawo dukkansu a wannan wuri.

Dangane da darajar Manzo ya wadatar da mu a kan cewa yana matsayin mai kare al'umma daga azabar Allah, Allah yana bayyanarwa a cikin Kur'ani cewa, matukar Manzo yana a cikin al'umma to Allah ba zai kama wannan al'ummar ba da azaba ba, kamar yadda yake cewa: Allah bai kasance zai azabtar da su ba matukar kanacikinsu, sannan Allah ba zai azabtar da sub a matukar suna neman gafara".

Sannan ya wadatar da mu a kan girman Manzo inda Allah madaukaki ya sanya sunan Manzo a gefen sunansa, sannan ya sanya biyayya ga Manzo tare da biyayya ga Allah, a kan haka Allah yana cewe: "Duk wanda ya bi Allah ya bi Manzo, lallai ya samu babban rabo".

Wadannan ayoyi da masu kama da su suna bayyanar da dajara da karama ta Manzo (S.A.W) matsayi da darajar da babu wani a cikin halitta wanda yake da shi, sakamakon wannan matsayin da daukaka da Manzo yake da shi a wajen Allah duk abin da yaroka za a biya masa bukatarsa. Don haka ne aka bai wa masu laifuka da zunubbai umurnin cewa, su nemi Manzo daya nema musu gafara a wajen Allah, inda Allah madaukaki yake cewa: "Da wadanda suka zalunci kawunansu zasu zo maka suna masu neman gafara a wajen Allah, kuma Manzo ya nema musu gafara, da sun samu Allah yana mai gafara kuma mai karbar tuba".

Sannan zamu iya fahimta daga wasu ayoyi cewa, sakamakon matsayi da daukaka manzanni sun kasance ana iya kamun kafa da su a wajen Allah kamar yadda zamu gani dangane da 'ya'yan annabi Yakub (A.S) lokacin da kuskuransu ya bayyana a fili, sai suka cewa mahaifinsu: "Ya babanmu ka nema mana gafara lallai mun kasance masu kuskure. Sai ya ce musu zan nema muku gafara a wajen ubangijina, kuma lallai shi mai gafara ne mai rahama".

Dangane da halascin wannan nau'i na kamun kafa babu wani shakku a cikinsa, domin kuwa babu sabani a kan haka. Abin da yake da muhimmanci a nan shi ne, sanin dalilin da ya sa nya ake karbar addu'ar annabawa.

Babu shakka tushen abin da ya sanya ake karbar addu'ar annabi ya samo asali ne daga tsarkin ruhinsa, sannan da kusancinsa ga Allah madaukaki. Don haka sakamakon wannan girma da daukaka ne na ruhi ya sanya Allah yake karbar addu'arsu.

Babu shakka addu'ar da ta taso daga ruhi mai tsarki wanda yake cike da soyayyar Ubangiji, ba tare da wani bata lokaci ba zata samu karbuwa a wajen Allah madaukaki.

Idan har akwai wata magana a kan halascin wannan kamun kafa kuwa, zai kasance ne dangane da kamun kafa da annabawa yayin da suka rasu wato lokacin da ba su raye a duniya. Tare da kula da abin da muka fada a wajen ziyarar kabari, mun yi bayani kan cewa babu wani bambanci tsakanin lokacin da annabawa suke a raye da lokacin da ba su raye a duniya, domin kuwa Manzo a cikin wadannan hali guda biyu yana iya nema wa mutum gafara a wajen Allah. Zamu yi cikakken bayani a kan wannan a cikin nau'in kamun kafa na shida insha Allah.

5-Kamun kafa Da Addu'ar Dan'uwa Mumini

Kur'ani yana bayyanar da cewa mala'iku suna yi wa masu imani addu'a, kamar haka:

"Wadanda suke daukar al'arshi da na gefensa, suna tasbihi da godiyar ubangijinsu, kuma suna masu imani da shi, sannan suna neman gafara ga wadanda suka yi imani" .

Wannan ba yana nuna cewa ba mala'iku ne kawai suke yi wa masu imani addu'a. Domin kuwa Kur'ani a fifli yana bayar da labarin yadda muminai suke wa junansu addu'ga abin da Kur'ani yake cewa: "Wadanda suka zo a bayansu, suna cewa, ya ubangijinmu! Ka yi mana gafara da 'yan'uwammu wadanda suka riga mu da imani, ya Allah kada ka sanya jin zafin a cikin zukatanmu dangane da wadanda suka yi imani, ya Allah kai ne mai rangwame mai rahama".

A cikin ayoyin da muka ambata a sama zamu iya fahimtar cewa, addu'ar mala'iku masu daukar al'arshi da kuma addu'ar muminai a kan 'yan'uwansu ta cancanci karbuwa. Saboda haka wannan aya tana nuna mana cewa mutum yana iya neman addu'a daga mala'ku da kuma sauran 'yan'uwansa masu imani.

Dangane da karbar adduar mumini kuwa, ya wadatar da mu inda Manzo (S.A.W) yake neman muminai su yi masa addu'a, inda yake cewa: Ku nema mini tsani a wajen Allah domin kuwa matsayi ne a cikin aljanna, babu kuwa wanda zai samu wannan matsayin sai wasu da suka cancanta daga cikin bayinsa, ina fata in zama nine, don haka duk wanda ya nemi kamun kafa da ni, cetona ya halasta gare shi". Kasantuwar wannan kamun kafar ya karbu a wajen dukkan musulmi ba tare da wani sabani ba, muna iya wadatuwa da wannan.

6-Kamun kafa Da Addu'ar Manzo Bayan Rasuwarsa

Bahsin da ya gabata ya tabbatar mana yadda kofofin rahama suka kasance a bude ga masu laifuka, ta yadda zasu iya kamun kafa da Manzo kamar yadda aya take nuni da hakan (da wadanda suka zalunci kawunansu sun…) wato suka nemi Manzo da ya neman musu gafara a wajen Allah. Sakamakon haka ne Kur'ani yake zargin munafukai domin kasantuwarsu sun rasa wannan falalar mai dimbin yawa. Ga abin da yake cewa: "Duk lokacin da aka ce musu, ku tafi zuwa Manzo domin ya nema muku gafara sai su kawar da kansu".

A nan akwai abin tambaya: shin sakamakon tafiyar Manzo zuwa ga rahamar Ubangiji wannan kofar gafarar da jin kai shi kenan ta kulle, ta yadda babu wani musulmi da zai je wajen Manzo ya roke shi da ya nema masa gafara a wajen Allah, ko kuwa wannan kofar albarka tananan bude kamar lokacin da yana raye? Wato musulmi har yanzu idan suka je haraminsa suna iya neman addu'arsa, ta yadda wannan ayar da muka ambata; "Da wadanda suka zalunci kansu sun zo wajenka suka neme ka da nema musu gafarar..". tana amfani a dukkan lokuta guda biyu, wato zamanin raywarsa da kuma bayan wafatinsa?

A wajen bayar da wannan masa dole ne a ce: Musulmi daga sahabbai da tabi'ai har zuwa yanzu sun kasance a aikace suna daukar wannan kofa a bude take, sannan musulmai a lokacin da suka ziyarci raudhar Manzo bayan yi wa manzon tsira sallama sukan karanta wannan ayar da muka ambata, tare da neman gafara daga Allah kuma suna rokon Manzo da ya nema musu gafara a wajen Allah madaukaki, saboda haka duk lokacin da mutum ya je ziyarar Manzo zai ga wannan al'amari daga al'ummar musulmi.

Bayan abin da tarihi yake nunawa ta hanyar ayyukan al'ummar musulmi danagane da neman addu'ar Manzo, addu'ar ziyarar Manzo ma wacce sunna da Shi'a suka ruwaito wannan addu'a tana tabbatar da wannan magana ta neman addu'ar Manzo. Domin jan hankalin masu karatu kuma suka kara natsuwa da abin da muke magana a kai, zamu kawo wassu daga cikin maganganunsu, ta yadda zai bayyanar mana yadda manyan malamai tun tsawon zamani suke neman kamun kafa da Manzo wajen yi musu addu'a:

1-Zakariya Muhyiddin Nawawi (631-676) Yana rubuta cewa: Mai ziyara yakan fuskanci Manzo ya yi kamun kafa da Manzo a kan abin da yake bukata kuma ta hanyarsa ya nemi ceto daga Allah, yana daga abu mafi kyau kasantuwar Mawardi, Alkali Abu Tayyib da wasu daga cikin manyan malamai suka ruwaito daga Utba tare da yabo suna cewa:

Utba yana cewa: Na kasance a wajen Manzo (S.A.W) wani mutum daga daji ya zo wajen Manzo ya ce "Assalamu alaika ya rasulullah, na ji Allah yana cewa: "Da wadanda suka zalunci kansu sun zo wajenka suka nemi gafara, kuma Manzo ya nema musu gafara, da sun samu Allah yana mai karbar tuba kuma mai jin kai"Lallai na zo wajenka ina mai neman gafara daga zunubaina sannan mai neman ceto a wajen Allah tare da kamun kafa da kai".

Kada mu yi tunanin cewa Nawawi ne kawai da malamansa suka tafi a kan ingancin kamun kafa da neman ceto daga Manzo. Malaman fikhu da na hadisi da dama sun kawo wannan a cikin littafansu na ziyara.

2-Kuddama Hambali (ya rasu shekara ta 620) a cikin ladubban ziyarar kabarin Manzo inda yake kawo maganar cewa"Mustahabbi ne ziyarar Manzo" Yaruwaito daga Abu Huraira yana cewa Manzo (S.A.W) ya ce: Duk wanda ya yi mini sallama, zan amsa masa sallamarsa. Sannan sai ya ruwaito daga Utba abin da muka ambata a baya kadan cikin hadisin Nawawi. Ya ce manufarsa wajen kawo wannan hadisi shi ne, don ya nuna cewa ana gabatar da ziyarar Manzo kamar haka:

3-Samhudi a cikin littafin "Mustau'ab" wanda Muhammad Bn Abdullah Samiri Hambali ya rubuta, yana ruwaito yadda ake ziyarar Manzo kamar haka:

Assalamu Alaika ya Rasulallah, assalamu alaika ya Nabiyyallah! Ya Allah kai ne ka fada a cikin littafinka ga annabinka cewa: "Da wadanda suka zalunci kawunansu…Ya Allah ga ni na zo wajen manzonka (S.A.W) ina mai neman gafara, ya Allah ina rokonka a kan ka wajabta mini rahamarka, kamar yadda ka wajabta ga wanda ya zo wajensa yayin da yake a raye, ya Allah ina ina kamun kafa da annabinka zuwa gare ka".

4- Gazali (ya rasu 505) Dangane da falalar ziyarar Madina da yadda ake ziyarar Manzo ya ruwaito a bayyane yana cewa: Bayan mutum ya gama sallama ga Manzo, sai ya dubi kabarin Manzo yana tsaye, sannan ya yi godiya ga Allah da yabonsa, sai ya aika gaisuwa mai yawa zuwa ga Manzo, sannan ya karanta wannna ayar da take cewa: Da wadanda suka zalunci kawunansu sun zo, sannan ya ce ya Allah mun ji kiran ka kuma mun amsa umurninka, sannan mun yi kamun kafa da manzonka muna neman cetonka daga zunubbammu, lallai zunubbai masu nauyi sun yi mana yawa…"

5- Sheikh Hasan Bn Ammar sharanbalani a cikin littafinsa "Murakil falah" yana ruwaito ziyarar Manzo kamar haka:

"Amincin Allah ya tabbata gareka ya kai shugabana ya manzon Allah, Amincin Allah ya tabbata a gareka ya annabin Allah! Lallai kurakurai sun karya mana kashin baya, sannan nauyin zunubban ya yi mana yawa a kan kafadummu. Kai ne mai ceto kuma wanda ake karbar cetonsa. Allah madaukaki ya yi maka alkawarin ceto da matsayi mai girma kuma abin yabo a wurinsa, sannan yana cewa: "Duk lokacin da suka zalunci kawunansu sannan suka zo wajenka suna masu neman gafarar Allah sannan Manzo ya nema musu gafara a wajen Allah, zamu samu Allah mai karbar tuba kuma mai jin kai.

Mun kasance mun zalunci kawunammu ga mu mun zo wajenka sannan muna neman gafara dangane da zunubbammu, ka nema mana gafara a wajen Allah".

6- Sayyid Ibn Dawus (ya rasu 664) ya ruwaito yadda ake ziyarar Manzo daga Imam Sadik (A.S) ga abin da yake cewa: Ya Ubangiji kai ne ka ce wa manzonka duk lokacin da suka zalunci kawunansu kuma suka zo wajenka suna neman gafarar Allah, sannan Manzo yanema musu gafara, zasu samu Allah yana mai karbar tuba kuma mai jin kai"

Ya Ubangiji ban kasance ina rayuwa a zamanin Manzo ba, amma yanzu na zo ziyararsa, kuma ina mai tuba daga munanan ayyukana, kuma ina neman gafara daga zunubbaina kuma ina mai ikrari a kan aikata su".

Mun kawo wasu daga cikin misalai dangane da yadda ake ziyarar Manzo, sannan mun ga yadda suka hadu a kan karanta wannan aya ga mai ziyara. A hakikanin gaskiya wannan aya wani nauyi ne aka aza wa mai ziyara aka kuma aza wa Manzo:

Amma nauyin da aka aza wa mai ziyara shi ne, mutum ya je wajen Manzo ya nemi gafarar zubbansa, sannan nauyin da ya hau kan Manzo shi ne ya neman wa mai ziyara gafara a wajen Allah.

Dukkan wadannan ladubban ziyara suna nuna mana yadda mai ziyara yake neman ceto daga Manzo a yayin da ba shi duniya, babu bambanci da lokacin da yake raye ta yadda mutum zai yi kamun kafa da shi.

Ibn Taimiyya Da Mabiyansa

Ibn Taimiyya da mabiyansa suna cewa: Neman addu'a daga Manzo ya kebanta ne da zamanin rayuwarsa ne a duniya kawai, don haka wannan ba ya halatta bayan wafatin Manzo! Haka ne zai yiwu mutum ya ziyarci Manzo, sannan ya yi addu'a a gefen kabarinsa sannan ya nemi abin da yake so a wajen Allah.

Dangane da amsar wannan magana kuwa zamu yi fadakarwa a kan cewa, dole ne a fahimci matsayi da darajar Manzo a wajen Allah, wato matsayin da zai sanya al'ummar musulmi masu zunubi su zo wajensa domin ya nema musu gafarar Ubangiji ta yadda addu'arsa karbabba ce.

Shin wannan matsayi da daraja ta Manzo ya samu asali ne daga jikinsa ko kuwa wani abu wanda ya shafi rayuwar duniya, ta yadda sakamakon wafatinsa zai kawo karshe, ko kuwa wannan matsayin sakamakon tsarki da daukakar ruhinsa ne?

Ra'ayi na farko kuwa ya saba wa hankali da shari'a, domin kuwa kamar yadda muka yi bayani a cikin bahsin rayuwar barzahu mun ga yadda ya kasance cewa; hakikanin mutum ruhinsa ne ba jikinsa ba. Sannan mun ga cewa ruhin mutum bayan rasuwarsa zai ci gaba da rayuwa a rayuwar barzahu, wato mutuwa ba yana nufin karshen rayuwa ba ne, ci gaba ne da rayuwa a wata duniyar ta daban. Don haka matsayi da daukakar Manzo ta samo asali ne daga girma da daukaka na ruhinsa, don haka bayan wafatinsa wannan matsayi yananan kamar yadda yake lokacin da yake a raye.

Sannan a bahsimmu da ya gabata mun tabbatar da kasantuwar alakarmu da wadanda suka riga mu gidan gaskiya, ta yadda suna jin duk abin da muke fada.

Tare da kula da abin da muka ambata, ayar da muka ambata a baya ba ta kebanta da lokacin rayuwar Manzo ba, kuma riko da hakan wani abu ne marar dalili. Sannan zamu tambayi wadanda suke inkarin kamun kafa da Manzo da cewa: me ya sanya bai halatta a yi kamun kafa da Manzo bayan wafatinsa ba? Shin don ya kasance ne duk wani girma da daukaka da kusanci ya samu ne a gare shi sakamakon yanayin jikinsa ne, ta yadda sakamakon rasuwarsa wannan matsayin da kusancinsa a wurin Allah zai kawo karshe?! Shin mutuwa shi ne karshen rayuwar mutum ta yadda Manzo bayan wafatinsa ba shi da sauran rayuwa?!

Shin sakamakon wafatin Manzo shi kenan ba mu da sauran wata alaka da shi?!

Amsar dukkan wannan tambayoyi kuwa ita ce; a 'a, don haka dole ne mu amince da cewa kamun kafa da Manzo a dukkan lokuta guda biyu (rayuwa da rasuwarsa) babu bambanci.

Daga karshe zamu yi tunatarwa da cewa, Sheikh Khalil Ahmad saharnafuri ya tattara fatawowin malaman AhlusSunna 75 dangane da halascin kamun kafa da Manzo.

A cikin wannan littafi da muka ambata a sama, an yi Karin bayani da cewa: A nazarimmu da manyan malamammu shi ne, ziyarar kabarin Manzo yana daya daga cikin manyan hanyoyi wajen neman kusanci zuwa ga Allah madaukaki, sannan yana daya daga cikin muhimman ayyuka masu lada kuma wata hanya ce domin samun matsayi da daraja madaukakiya. Wannan kuwa wani umarni ne wanda yake kusa na wajibi da farillai na shari'a, madamar isa zuwa ga hakan ba zai janyo tsanani ko asarar rayuwarka ba. Kamun kafa kuwa da annabawa da waliyyai da manyan bayin Allah, shahidai da siddikai, a cikin addu'a a lokacin rayuwarsu ne ko kuwa bayan rayuwarsu ya halatta.

Tambayoyi Da Amsoshi

Dalilai a kan halascin kamun kafa da Manzo bayan wafatinsa wani abu ne wanda ya bayyanar mana. Amma dangane da hakan akwai wasu tambayoyi wadanda dole ne mu bayar da amsarsu.

Tambaya ta farko: Shin neman addu'a daga mamaci shirka ne?

Wasu suna tunanin cewa neman addu'a daga wanda yake raye, wato yana iya yin addu'ar wani abu ne wanda ya halasta, amma yin haka ga mamaci shirka ne. Amma shin wannan tunani daidai ne?

Abin da ake nufi da shirka kuwa a cikin wannan tambaya da tagabata shi ne shirka a cikin ibada, (hadallah da wani a cikin bauta) wato neman addu'a daga mamaci yana nufin yi masa bauta kenan.

Wannan tunani na sama sam ba ya inganta, saboda:

Na farko: Idan neman addu'a ga mamaci yana nufin yi masa bauta, to wannan ya nuna cewa neman addua'a daga mutumin da yake a raye shi ma yi masa bauta ne domin kuwa babu bambanci, domin kuwa neman addu'a ne tare da kaskantar da kai, don haka wadanda suke ganin neman addu'a daga wanda yake raye ba ya nufin bauta masa ba ne, don haka dole ne su amince da cewa yin hakan bayan rasuwa ma ba yana nufin bauta ba ne, ballantana ya zama shirka ko sabanin tauhidi.

Na biyu: A cikin fasali na hudu na wannan littafi mun bayani a kan ma'anar ibada bisa dalilai na hankali, ta yadda muka nuna cewa ba duk neman wani abu ko addu'a ko makamancinsa ba ne ibada. Abin da ake nufi da ibada shi ne wani nau'i ne na girmamata musamman wacce take tare da wata akida ta musamman, wato mutum ya dauki wanda yake kaskantar da kansa a gare shi a matsayin Allah, wa'iyazu billah, ko kuma mutum ya dauka cewa wani abin halitta ne yake tafiyar da wasu daga cikin ayyukan Allah kamar yadda masu bautar gumaka suke dauka.

Amma girmamawa da kaskantar da kai wanda ya koru daga wannan akida marar tushe, ta yadda mutum yana ganin wanda yake girmamawa a matsayin wani bawan Allah ne, kuma wanda yake da kusanci zuwa ga Allah, sakamakon haka ne yake kamun kafa da shi yana neman addu'arsa, sam ba a kiran wannan bauta, ballantana ya zama shirka da Allah.

Tambaya ta biyu: Shin neman addu'a daga mamaci ba shi da wani amfani?

Daya daga cikin abin da masu inkarin wannan al'amari suke kawowa shi ne, mutumin da ya mutu sam ba shi da ikon da zai iya biya wa mutum bukatarsa. Saboda haka neman wani abu daga wanda ya mutu sam wani abu ne marar amfani.

Amsa: Tushen wannan tamabaya yana komawa ga yadda mutum yake ganin duniya, wato kamar cewa wannan duniyar da muke gani ita kawai ce duniya bayan wannan babu wani abu, wdan da suke kuma ganin cewa mutum da zarar ya mutu shi kenan babu sauran wata rayuwa, don haka wadanda suka gabata sama ba su da wata rayuwa, don haka neman wani abu daga gare su wani abu ne marar amfani.

Amma tare da kula da ka'idojin da muka ambata a sama, amsar wannan tambaya a fili yake, haka ne mutum da ya mutu ba shi da rayuwa irinta duniya, amma yana da wata rayuwar ta lahira, sannan tare da izinin Ubangiji yana iya amsa na bukatocinmu.

Tambaya ta uku: Shin tsakanimmu da wadanda suka rasu akwai wani shamaki wanda zai hana su jin maganarmu?

Wadanda suke da wannan tunani suna ganin tsakaninmu da wadanda suka rasu akwai wani abu wanda ya kare tsakanimmu, wanda Kur'ani yake ambata da barzahu. "A bayansu a kwai barzahu, har zuwa ranar tashin kiyama". Don haka kirammu ba zai isa zuwa gare su ba.

Amsa: Barzakh a harshen larabci ba tana nufin shamaki ko hijabi ba, wato ana nufin shamaki wanda yake hana su dawowa zuwa rayuwar wannan duniya, ba wai abin da zai hana su alaka da wadanda suke a raye ba. tare da kula da ayar da take da alaka da barzahu muna iya fahimtar wannan al'amari kamar yadda Kur'ani yake cewa:

"Zuwa lokacin da mutuwa zata zo wa daya daga cikinsu, zai ce: Ubangiji ka mai da ni zuwa duniya, domin kuwa zanyi aiki mai kyau a cikin abin ya ragu gare ni, sam ba haka ba ne kawai magana ce wacce mai yin ta yake fada".

Tare da kula da abin da mamaci yake fada shi ne Kur'ani yake ba shi amsa da cewa: "A bayansu akwai abin da ya kare su ta yadda ba zasu koma ba har zuwa ranar kiyama". Saboda haka wannan shamaki na hana dawowa a duniya ne, ba wanda zai hana wadanda suka rasu ba su yi alaka da wadanda suke a raye.

Tambaya ta hudu: Shin Manzo yana jin maganarmu?

Kur'ani yana kamanta yadda mushirikai suke da matattu, manufarsa kuwa da wannan shi ne, kamar yadda matacce ba ya jin magana, masu shirka suma haka suke, a kan haka ne yake cewa: "Lallai kai ba ka iya jiyar da matattu" "sannan ba ka iya jiyar da wadanda suke cikin kabari" Dangane da kamanta mushirikai da matattu dangane da rashin jin magana, muna iya cewa wani abu ne wanda babu shakku a cikinsa cewa an kamanta mushirikai da matattu.

Amsa: Babu shakka a cikin kowace kamantawa ko misaltawa a kwai wata fuska da abu guda biyu a kan kamanta su, misali lokacin da za a ce Ali kamar zaki yake, tabbas a nan an dauki fuskar jarunta ne aka siffanta Ali da zaki domin kuwa duka guda biyun suna da wannan siffa. Saboda haka a nan zamu ga menene fuskar da ta sanya a kamanta matacce da mushiriki?

Tabbas babu yadda za a ce ta fuskar cewa sam ba su ji ko kadan, domin kuwa idan muka dauki hakan cewa mamaci ba ya ji, to shi ma mushiriki zai rasa wannan halitta ta ji ke nan, ga shi kuwa mushiriki yana jin maganar Manzo da ma ta sauran al'umma.

Saboda haka wannan kama da ta sanya aka kamanta su da wani abu daban, wannan kuwa shi ne rashin sauraren magana mai amfani. Wato kamar yada kiran wanda ya mutu zuwa ga aiki mai kyau ba shi da amfani, domin kuwa lokacin aikin ya riga ya gabata, haka nan kiran mushrikai zuwa ga aiki mai kyau ba shi da wani amfani, domin kuwa sam ba su da niyyar amsa wannan kira, tare da lura da ayoyin da suke magana a kan rayuwar barzahu zamu iya fahimtar wannan hakika.

Saboda haka magana guda a nan ita ce, kiran mushrikai zuwa ga imani kamar kiran wadanda suka mutu ne zuwa ga aiki mai kyau. Don haka kiran wadannan gungu guda biyu (Mushrikai da matattu) sam ba zai samu wata riba ba. Mushiriki yana ji amma ba shi niyyar karbar gaskiya, mamaci shi ma yana ji amma lokacin aiki ya riga ya wuce yanzu lokacin sakayya ne ga abin da mutum ya aikata ne.

Abin burgewa a nan shi ne almajirin Ibn Taimiyya wato Ibn Jauziyya, shi ma a cikin littafinsa (Arruh) ya fassara wannan aya da ake tambaya a kanta kamar yadda muka fassara. Yarda da wannan tafsiri da Ibn jauziyya ya yi, yana nuna kaucewa daga ra'ayin malaminsa Ibn Taimiyya a kan wannan magana.