Ziyarar Kabari

Ziyarar Kabari0%

Ziyarar Kabari Mawallafi:
: Shekh Hafiz Muhammad Sa'id
: Shekh Hafiz Muhammad Sa'id
Gungu: Raddin Shubuhohi

Ziyarar Kabari

Mawallafi: Ayatul-Lahi Subhani
: Shekh Hafiz Muhammad Sa'id
: Shekh Hafiz Muhammad Sa'id
Gungu:

Budawa: 6994
Gurzawa: 2150

Bayanai:

Bincike Cikin Littafi
  • Farawa
  • Na Baya
  • 30 /
  • Na Gaba
  • Karewa
  •  
  • Gurzawa HTML
  • Gurzawa Word
  • Gurzawa PDF
  • Budawa: 6994 / Gurzawa: 2150
Girma Girma Girma
Ziyarar Kabari

Ziyarar Kabari

Mawallafi:
Hausa

HIKIMAR ZIYARAR KABURBURAN WALIYYAI

Wallafar: AyatulLahi Sheikh Ja’afar Subhani

Fassarar: Yunus Muhammad Sani

Dubawar: Hafiz Muhammad Sa’id

Ziyarar Kaburbura Masu Daraja

Da Sunan Allah Ta'ala Mai Rahama Mai Jin Kai

Tsira da amincin su kara tabbata a bisa Manzon rahama Manzonmu Annabi Muhammad amincin Allah Ta'ala ya kara tabbata a gare shi da iyalensa tsarkaka

Makabarta wani wuri ne babba a cikin birni da kauye Wanda yake kunshe da matattun mutane marasa rai wanda yake dauke da babba da yaro mai iko da talaka daga magabata wadanda suke cikin barci mai zurfi da yake kamar ba za a farka ba.

Ziyartar wannan wuri Wanda yake nuna gajiyawar dan Adam, sannan kuma yake da rawar da yake takawa wajen gusar da duk nuna iko ko kwadayin abin duniya ga mutum. Yayin da mutum mai hankali ya ga wannan wuri mai ban tsoro, zai fahimci rashin tabbatuwar duniya daga kusa, sannan ya fara tunani a kan mafita sakamkon fahimtar manufar halittar duniya da ya yi. Kuma zai sanya ya fita daga cikin magagin dimuwa da son kai, sannan ya fara tunanin neman abin zai taimaka masa wajen rayuwar da ba ta da iyaka. A kan wannan al’amari domin tarbiyyantar da al’umma Manzo (S.A.W) yana cewa: “Ku ziyarci kaburbura domin zasu tuna muku ranar karshe”[1].

Sannan a wani wurin daban yana cewa: “Ku ziyarci makabarta domin kuwa akwai darasi gareku a cikin yin hakan”.[2]

Sannan akwai wasu daga cikin mawakan zamani kamar Marigayi Sayyid Sadik Sarmad yayin ziyarar Kasar Misra da kuma ziyarar Kaburburan fir’aunoni, sai ya yi wata a kan haka wadda take fassara hadisin manzo (S.A.W) game da hakan

Ziyartar Kaburburan Masoya

Mutanen da suka rasa wani masoyinsu sakamakon alaka ta jini da soyayyar da take tsakaninsu ba zasu taba mantawa da shi ba, zaka ga kodayaushe suna yin tarurruka domin tunawa da shi sannan suna yin kokari wajen girmama shi.

Yayin da mutuwa ta kare su daga saduwa ta jiki, sai suka koma bangare guda; wato suna saduwa da shi ta hanyar ruhi, don haka ne zaka ga suna zuwa wurin da aka rufe shi ta hanyar daidaiku da cikin jama’a domin su ziyarce shi sannan suna yin tarurruka domin tunawa da shi din.

Taron mutuwa da ziyartar kaburburan wadanda suka rasu wata al’ada ce wadda ta hade ko’ina a cikin al’ummar duniya, ta haka ne zamu iya cewa wannan al’amari yana da alaka da halittar mutum. Sakamkon soyayyar da take tsakanin mutane da danginsu wadda take janyo su da su zo domin su ziyarce su yayin da suke da rai, wannan shi yake janyo su ziyarci kaburburansu yayin da ba su da rai; musamman kamar yadda yake a musulunci cewa ruhin mutum sabanin jikinsa ba ya lalacewa.

Ba ma haka ba kawai; bayan haka yakan kara samun karfi na musamman a wannan duniyar sannan yana jin dadin kulawar da masoya suke yi masa ta hanyar ziyartarsa da yi masa addu’a kamar karanta masa fatiha da makamantanta, ta yadda suke kara masa nishadi da karfi.

Don haka bai dace ba mu sha kan mutanen a kan gudanar da irin wannan al’ada wadda take wani nau’in halittar mutum ce, Abin da ya kamata shi ne mu nuna musu yadda ya kamata su aiwatar da hakan, ta yadda sakamakon soyayya ga masoyansu ba zai kai su zuwa ga sabon ubangiji ba.

Ziyarar Kaburburan Malamai

Abin muka yi Magana a kan shi a sama ya shafi ziyarar sauran mutane ne da suke da alaka ta jini da take tsakanin mamaci da mai ziyararsa. Ta yadda sakamakon wannan ziyara zai biya bukatun wanda ya ziyarta ta hanyar kulawar da ya yi masa, ta yadda masu ziyara zasu tsaftace kabarinsa har ma su sanya wa kabarin turare da sauransu.

Amma a cikin wadannan masoya akwai wadanda suke malamai ne da wadanda suka kawo gyara a cikin duniya wadanda suke da wani matsayi na musamman wanda ya sha bamban da wadanda suka gabata. Wadannan sun kasance tamkar kamar kyandir ne wanda ya kone kansa domin ya haskaka wa waninsa. Haka su ma suka haskaka wa mabiyansu ta yadda suka yi rayuwa a cikin kunci, amma suka bai wa mabiyansu taskar ilimi madawwamiya, sakamakon haka ne suka cancanci yabo da girmamawa.

Musamman malamai wadanda suka koyar da al’umma littafin Allah da Sunnar manzo (S.A.W) ta yadda suka bai wa al’umma abin da zai kai su zuwa ga cin nasarar rayuwar duniya da lahira kuma madawwamiya. Don haka halartar kabarin irin wadannan malaman yana nufin girmama wadanda suke cikin kabarin ne, Sannan kuma sakamakon abin suka yi na yada ilimi ne ya janyo soyuwar al’umma zuwa gare su ta yadda suka yi hidima da kare wadannan ayyuka na su (Littattafai da makamantansu kamar kaburburansu): Hakika duk al’ummar da suke girmama ilimi da malamai ba zasu taba shiga cikin tarkon kuncin ilimi ba.

Ziyarar Kaburburan Shahidai

Haka nan ziyartar kaburburan Shahidai wadanda suka bayar da jininsu domin kare al’ummarsu da addinin Allah shi ma yana da matsayi na musamman wanda ya fi na sauran mutanen da ba su ba.

Ziyartar kaburburan shahidai wadanda suka rasa rayukansu a kan tafarkin ubangiji, bayan tasirin da yake ga ruhin mutum, sannan yana nuna rikon alkawari a kan tafarkin da suka bayar da jininsu a kai. Wato mai ziyara kamar yana cewa ne yana nan kan tafarkinsu sannan zai yi kariya a kan wannan abin mai tsarki da suka bayar da jininsu. Domin mu kara fahimtar abin da kyau bari mu ba da wani misali wanda yake raye a halin yanzu:

Mutumin da ya ziyarci Dakin Allah, kafin ya yi dawafi yakan yi wa Hajrul Aswad sallama kuma ya sanya hannu ya shafe shi da ma’anar cewa yana yin bai’a ne ga Annabi Ibrahim (A.S) gwarzon tauhidi, da nufin cewa tauhidi shi ne abu na gaba a wajensa. Ta yadda zai yi iya kokarinsa wajen yada shi, amma tunda yanzu ba zai iya kai hannunsa ba zuwa ga Annabi Ibrahim ta yadda zai yi masa bai’a wajen daukar alkari domin wannan aiki shi ne sai ya kai hannunsa ga abin da shi Annabi Ibrahim (A.S) ya bari ta yadda zai gabatar da bai’arsa ta hanyar wannan abin da ya bari. Ya zo a cikin hadisi cewa yayin da mutum yake mika hannunsa zuwa ga Hajrul Aswad yana cewa ne: ”Na mika amana da alwakarin da na dauka, sannan na jaddada bai’ata ka sheda a kan hakan”.[3]

Ziyartar shahidan Badar da Uhud da Karbala da sauran masoyan da suka bayar da jininsu a tafarkin Allah yana bayyanar da wannan al’amari. Masu ziyarar wadannan wurare masu tsarki sukan yi wa masu wannan wuri sallama da mika gaisuwa zuwa ga ruhinsu tsarkaka, sannan suna daukar alkawari ne a kan cigaba da hanyarsu.

Da wani kalamin muna iya cewa ziyarar kabarin wani nau’i ne na girmama su. Sakamakon an kashe shahidi a kan wani abu mai tsarki da yake girmamawa, duk wanda ya ziyarci shahidi ya girmama shi, a hakikanin gaskiya ya girmama wannan akidar ne wadda a kanta ne aka kashe shi, sannan yana daukar kansa wanda yake biyayya akan wannan hanya.

Ziyarar Kabarin Manzo (S.A.W)

Ziyarar Kabrin Manzo mai girma (S.A.W) ko kuma wasiyyinsa mai tsarki (A.S) yana da matsayin hukuncin yi musu bai’a ne bayan nuna girmama su a kan abin da suka yi na sadaukar da rayukan su wajen shiryar da al’umma zuwa ga hanyar Allah da yake nunawa. Imami na takwas wato wasiyyin Annabi kuma halifansa da ya yi wasiyya da shi imam Ridha (A.S) a cikin maganganunsa dangane da ziyarar kaburburan ma’asumai (A.S) yana cewa: Kowane Imami yana da alkawari tsakaninsa da mabiyansa ziyarar kabarin Imamai daya daga cikin wannan alkawarin ne”.[4]

A hakikanin gaskiya yayin da mutum yake ziyartar kabarin manzo (S.A.W) ko na Imamai kamar yana yin bai’a da alkawari da su ne cewa ba zai taba bin wata hanya ba a cikin rayuwarsa sai hanyar da suka bari.

Ga abin da mai ziyar kabarin manzo yake cewa: Idan Muhajirun da Ansar wadanda suka halarci yakin Hudaibiyya sun yi maka bai‘a a kan kariya ga addini (Fathi: 18).

Sannan idan matan Makka sun yi maka bai’a a kan gujewa daga yin shirka da sabon Allah (Mumtahna: 12).

Idan har Muminai masu sabo sun samu umarni a kan cewa su zo wajenka domin ka nema musu gafara, ni ma ya manzon Allah ya mai ceton al’umma sakamakon halartata zuwa haraminka da sallama zuwa ga kabarinka ina mai yi maka bai’a a kan cewa zan yi kariya ga addininka sannan in yi nesa daga shirka da sabon Allah, sannan sakamakon haka ina rokonka ka nema mini gafara a wurin Allah.

A nan dole mu fahimci cewa ziyarar kaburburan bayin Allah ya sha bamban da yawon shakatawa domin kuwa yana da manufarsa da ta sha bamban da yawon bude ido. Masu yawon bude ido suna zuwa wuri ne domin su more wa idanunsu, suna neman wurare masu kyau ko na tarihi domin su gane wa idanunsu. Saboda haka gurinsu shi ne: shakatawa da hutawa, duk da cewa idan wannan bai kasance tare da sabon Allah ba, to musulunci ba ya hani da wannan. Amma masu ziyarar kaburburan bayin Allah suna yi ne domin kara samun alaka da masoyinsu da kuma jaddada alkawarinsu da shi, don haka duk wata wahala da zasu hadu da ita wajen isa zuwa gare shi koda kuwa zai kai ga su rika gudu a cikin daji da kafafunsu ne da taka kayoyi suna iya jure wa duk hakan.

Dan yawon bude ido yana neman abin da zai biya bukatunsa na kasantuwarsa mai rai ne shi, amma mai ziyara yana kokarin ya shayar da ruhinsa ta hanyar saduwa da masoyinsa, domin kuwa ba zai iya isa zuwa ga masoyinsa ba, sai ya mika hannunsa zuwa ga kabarinsa wanda yake dauke da kanshi da launinsa.

Tarihi yana nuna cewa: Bayan wafatin manzon Allah (S.A.W) wani bakauye ya shigo garin Madina sai ya zauna a gefen kabarin manzo sai ya karanta wannan aya wadda take cewa: “Da wadanda suka zalunci kansu sun zo a gareka suka nemi gafarar Allah Sannan manzo ya nema musu gafara da sun sami Allah mai karbar tuba mai rahama”.

Sai wannan bakauyen balarabe ya ce: Ya kai manzon Allah gani na zo a wannan wuri domin ka nema mini gafara ina mai neman cetonka zuwa ga Allah”. A lokacin yana cikin kuka sai ya karanta wannan baiti na waka inda yake cewa:

Ya mafificin mutumin da aka bisne jikinsa a wadannan kasashe

Kanshinsa ya bice tudu da kwari na wannan yanki

Ina gabatar da kyautar raina zuwa ga wannan kasa wadda ta boye fiyayyen haliitta[5]

Bayan ya gama wannan baiti na waka sai ya nemi gafara ya tashi ya tafi abinsa.

Wannan balarabe da muka ambata ya fahimci ma’anar ziyarar kabarin manzo daga cikin zuciyarsa tsarkakka, saboda haka ne ya taso ya zo domin ya ziyarci shugaban halitta. Wannan ita ce hikimar ziyartar kaburburan ‘yan’uwa, masoya, malamai, shahidai a tafarkin Allah, da shugabannin addini wanda hankali da shari’a suke tabbatar da ingancinsa.

A nan dole ne mu yi bincike ta mahanga daban-daban a kan ziyarar kabari kamar haka:

1-Ziyarar kabarin muminai a mahangar Kur’ani da Sunna

2-Mata da ziyarar kabari

3-Ziyarar kabarin manzo a mahangar manyan malaman musulunci

4-Ziyarar kabarin manzo a mahangar Kur’ani da Sunna

A nan gaba zamu yi bahasi ne a kan wadannan abubuwa guda hudu da muka ambata a sama:

Ziyarar Kabarin Muminai A Mahangar Kur’ani Da Sunna

Ziyarar kabarin muminai musamman wadanda suke da alaka ta jini da mutum, wani abu ne wanda duk mutanen duniya sun hadu akan yin hakan domin kuwa ya dace da halitta mutum, sannan muna iya fahimtar haka daga wannan aya: “Kada ka sallaci kabarin wanda ya mutu daga cikinsu har abada, Sannan kada ka tsaya a kan kabarinsa domin kuwa lallai sun kafirce wa Allah da manzonsa, Sannan sun mutu alhalin suna fasikai”. [6]

Wannan aya mai girama tana ba wa manzo umarnin abubuwa guda biyu kamar haka:

1-Kada ya yi salla ga wadanda suka mutu daga cikinsu da cewa: Har abada kada ka sallaci daya daga cikinsu idan ya mutu.

2-Kada ya je a kabarinsu, domin yi musu addu’a ko makamancin haka: Kada ka tsaya akan kabarinsa.

Bangare na biyu na wannan aya yana da muhimmanci na musamman a gare mu, wannan kuwa shi ne, shin tsayuwa a kan kabari yana nufin yayin rufewa ne ko kuwa yana da ma’ana fiye da hakan? Amma masu tafsiri suna karfafa ma’ana ta biyu ne, wanda zamu yi bayani dangane da abin da suke cewa kan hakan. Bidhawi yana cewa: Ma’anarsa kada ka tsaya a kan kabarinsu yayin rufewa ko ziyara.[7]

Shi ma Suyudi a cikin tafsirul jalalaini[8] ya tafi a kan wannan ra’ayi, Sannan Arif Bursi a cikin tafsirin Ruhul Bayan[9] da Alusi Bagadadi a cikin ruhul ma’ani[10] ya kawo wannan.

Saboda haka Allah madaukaki yana hani ga manzo a kan ya tsaya a kan kabarin munafukai yayin rufewa ne ko kuwa domin ziyara. Wannan yana nuni ne a kan cewa manzo ya kasance yana halartar kabarin muminai yayin rufewa ko kuwa lokacin ziyara, sannan yana yi musu addu’a. Domin kuwa idan ba haka ba, babu ma’ana a yi masa hani a kan wannan al’amari. Saboda haka idan haka ne ma’anar wannan jumla zata kasance kamar haka: Har abada kada ka tsaya a kan kabarin Munafukai.

Sakamakon haka ne zai zamana munafukai sun rasa wannan falala su kuwa muminai suna rabauta daga wannan falala, domin kuwa manzo yana iya halartar kabarin muminai lokacin rufe su ne ko kuwa lokacin ziyara domin ya yi musu addu’a.

Ziyarar Kabari A Cikin Sunnnar Manzo

Bayan ruwayoyi guda biyu da muka kawo farkon wannan bahasi wadanda suke nuna hikimar ziyara, dole a nan mu kara fadakarwa a kan cewa, manzo da kansa ya kasance yana zuwa makabartar “Bakiyya” domin ziyartar kaburburan musulmi. Sannan tarihi ya tabbatar da hakan kamar haka:

1-Musulim a cikin sahih dinsa yana cewa: An ruwaito daga A’isha cewa duk karshen dare yakan tafi makabarta domin ziyara, duk lokacin da ya shiga wannan wuri yana ce musu: “Amincin Allah ya tabbata gareku ya gidan mutane muminai kun samu abin da ake alkwari da zuwansa a gaba, Kuna rayuwa tsakanin mutuwa da tashin kiyama, mu ma zamu hadu daku, Ya Allah ka gafarta wa wadanda suke a cikin” Bakiyya”.

2-Muslim a cikin Sahih dinsa ya ruwaito daga A’isha tana cewa Manzo ya ce mata: Jibril ya sauka zuwa gareshi ya ce masa Allah yana ba da umarni da cewa ku tafi ziyarar mutanen “Bakiyya” Sannan ku nema musu gafara.

A’isha tana cewa: Sai na tambayi manzo cewa, yaya za yi musu addu’a? Sai manzo ya ce ki ce: “Amincin Allah ya tabbata a gareku yaku mutanen wannan gida daga muminai da musulmai, Allah ya jikan wadanda suka riga mu da wadanda zasu zo bayanmu daga cikinsu, Mu ma insha Allah muna nan zuwa mu hadu da ku”. [11]

3- Muslim yana ruwaitowa daga Buraida cewa: Manzo (S.A.W). ya kasance yana koyar da Sahabbansa cewa yayin ziyara ga abin da zasu ce: “Amincin Allah ya tabbata a gare ku ya ku mutanen wannan gida muminai muna nan zamu hadu da ku, Muna rokon Allah da ya ba mu lafiya tare da ku.[12]

Mata Da Ziyarar Kabari

Mata suna da hukunci guda ne da maza dangane da ziyarar masoyansu da waliyyan Allah, domin kuwa hukuncin maza da mata a cikin musulunci duka abu guda ne, sai kawai wurin da aka bambanta maza da mata a wasu wurare na musamman tare da dalili.

Manzo (S.A.W) Yana kira zuwa ga musulmi da cewa: “Ku ziyarci kaburbura domin suna tuna muku lahira”.

Sanan a wani hadisi daban yana cewa: “Ku ziyarci makabarta domin akwai darasi a cikin yin hakan”.

Gaskiya ne wadannan kira tare da lura da yadda aka amfani lamirin maza kamar ya nuna cewa da maza ake, amma kamar yadda muka tunatar cewa kusan dukkan kira da ake yi a cikin Kur’ani da hadisi kamar ana kira ne zuwa ga maza, saboda haka dukkan ayoyin da aka yi amfani da su wajen umartar mutane a kan yin salla da azumi da wannan sigar ne wato an yi amfani da lamirin maza ne, amma wannan umarni ya kunshi mata kamar yadda ya kunshi maza. Kamar yadda yake cewa: Ku tsayar da salla ku bayar da zakka duk abin da kuka gabatar domin kawunanku na alheri to zaku same shi a wajen Allah”[13].

Wannan umarni bisa lura ga ka’idar larabci kamar yana fuskantar maza ne, amma wannan hukunci ya kunshi duka maza da mata ne.

Saboda haka kiran da a aka yi a cikin dukkan wadannan hadisai guda biyu da cewa "ku ziyarci kaburbura” duk da cewa ya fuskantar maza ne amma sakamakon haka ya hada maza da mata ne.

Bayan wannan hadisi kuma a kawai wasu ruwayoyi da suke nuni da halascin ziyarar kabari ga mace, saboda haka a nan zamu ambaci wadannann hadisai kamar haka:

1-Muslim yana ruwatowa a cikin sahih dinsa daga manzo cewa: Jibril ya sauko zuwa gare ni ya ce da ni: Ubangijinka yana ba da umarni da a ziyarci kaburburan mutanen “Bakiyya” Sannan ka nema musu gafara a wajen Allah”.

Sai manzo ya tashi daga bisa shimfidarsa ya tafi Bakiyya domin ziyara, sai A’isha ta bi manzo (S.A.W) daga baya, sai ta fahimci umarnin da Allah ya aiko wa manzo.

A lokacin sai ta tambayi manzo cewa: to yaya zan ziyarci mutanen baki? Sai manzo ya ce: “Ki ce amincin Allah ya tabbata ga nutanen wannan gida daga musulmai da muminai, Allah ya gafarta wa wadanda suka riga mu da wadanda zasu zo bayammu. [14] Wurin da ake kafa dalili a nan shi ne wajen koyar da A’isha yadda ake ziyara, saboda haka idan ya zamana bai halitta ba mace ta ziyarci makabarta, a nan babu ma’ana manzo ya koyar da matarsa.

Sannan bugu da kari A’isha ta kasance tana gaya wa sauran mata dangane da abin da ya auku, saboda haka da wannan zamu iya gane cewa ya hada kowa da kowa cewa ziyarar baki daya ta halatta ga mace da namiji. Domin kuwa matar manzo da sauran mata duk daya suke a wajen hukuncin Allah!

2-Fadima (A.S) ‘yar manzo (S.A.W), kuma daya daga cikin mutanen mayafi (wadanda aka saukar da aya ta 33 suratul ahzab a kansu) Bayan wafatin manzo ta kasance tana ziyartar kabarin amminta wato shahidin Uhud inda take yin salla raka’a biyu sannan ta yi kuka a kabarinsa.

Hakim Nishaburi bayan ya ruwaito wannan ruwaya yana cewa: wadanda suka ruwaito wannan ruwaya dukkansu amintattu ne kuma adalai, ta wannan fuskar ba su da bambanci da maruwaitan Bukahri da Muslim [15].

3-Tirmizi ya ruwaito daga Abdullahi Bn Abi Malika yana cewa: Lokacin da Abdurrahman bn Abibakar ya rasu a wani wuri da ake kira da (Hubsha) Sai aka dauki jana’izarsa zuwa Makka aka rufe shi a can. Bayan wani lokaci sai A'isha wadda take ‘yar uwa ce a gare shi ta zo Makka domin ziyarar kabarin Abdurrahaman dan’uwanta, Sannan ta yi wasu wakoki guda biyu wadanda suke nuna tsananin damuwarta a kan rashinsa.[16]

4-Bukhari yana rubuta cewa: Wata rana Mnazo ya ga wata mata gefen wani kabari tana kuka, sai ya ce mata “Ki mallaki kanki sannan ki yi hakuri a kan rasa wani naki da kika yi”.[17]

Amma bukhari bai ruwaito cigaban wannan hadisi ba, amma Abu Da’ud a cikin sunan dinsa ya cigaba da wannan hadisi ga abin yake kawowa: Wannan mata ba ta gane manzo ba, sai ta kalubalanci manzo ta ce: Me ya dame ka dangane da abin da musibar da ta same ni? A wannan lokaci sai wata mata da take gefenta ta ce mata kin gane kuwa wannan kowane ne?, Manzon Allah ne (S.A.W).

A wannan lokaci wannan matar domin ta gyara abin da ta yi wa manzo sai ta tafi gidan manzo ta ce masa: Ya manzon Allah ka yi hakuri ban gane kai ne ba. Sa manzo ya amsa mata da cewa: Hakuri a cikin musibar da ta samu mutum shi ne abin da ya dace.[18]

Idan da ziyartar kabarin ‘yan uwa ya kasan ce wani aiki ne da ya haramta, maimakon manzo ya yi umarni da yin hakuri, zai ce da ita ne: Ke wannan aiki naki ya haramata a fili. Amma sai ya umurce ta da yin hakuri a kan abin da ya same ta ba wai ta nisanci kabarin ba.

Amsar wasu tambayoyi guda biyu

Wasu sun haramta ziyarar mata zuwa kaburbura, suna kafa hujjarsu ne kuwa da wadannan hadisai guda biyu kamar haka:

1-“Allah ya la’anci mata masu ziyarar kabari”.

Amsa:

Wannan Hadisi ya rasa sharuddan da ya kamata ya kasance yana da su kafin a iya kafa hujja da shi. Domin bisa ga dogara da dalilai da aka ambata a baya dole ne mu dauka wannan hadisi an shafe shi, Sannan cikin sa’a wasu daga cikin malaman hadisi na Sunna sun dauki wannan hadisi matsayin shafaffe. Tirmiz maruwaicin wannan hadisi yana cewa: Wannan hadisi an shafe shi domin yana nuna lokacin kafin halasta ziyartar kabari ne, amma lokacin da manzo ya halasta ziyarar kaburbura wannan hukunci ya hade mace da namiji babu bambanci.

Kurdabi yana cewa: Wannan hadisi yana Magana ne a kan matan da suke bada dukkan lokacinsu a makabarta ne, ta yadda sakamakon haka ba su bayar da hakkokin mazansu da ya hau kansu. Kuma sheda a kan haka shi ne manzo ya yi amfani da kalmar “Zuwwar” wadda take da ma’anar kambamawa, wato wadanda suke yi yawaita ziyara.

2-Ibn maja yana ruwaito daga Ali bn Abi Dalib cewa: Manzo (S.A.W). Ya fito sai ya ga wasu mata a zaune, sai ya tambaue su me ya sa suke zaune? sai suka ce: Muna jiran jana’iza ne.

Sai ya ce zaku yi wa jana’izar wanka ne?

Suka ce: A’a.

Sai ya ce: zaku dauki gawar ne?

Suka ce: A’a.

Ya ce: zaku saka gawar kabari ne?

Suka ce: A’a.

Sai manzo ya ce: ku koma gida kuma su masu sabo ne ba masu neman lada ba.

Amsa:

Wannan hadisi ta fuskar ma’ana da isnadi ba a bin dogaro ba ne da za a iya kafa hujja da shi, saboda sanadin wannan hadisi (maruwaita hadisin) akwai Dinar bn Amru ya shiga a cikinsu, ta fuskar masu ilimin ruwaya suna cewa ba a san shi ba, kuma mutum ne mai karya mai sabo kuma wanda ake bari. Shin ana iya dogara wajen kafa hujja da irin wannan hadisi wanda maruwaicinsa yake da wadannan siffofi na rauni?

Mu dauka ma dangane wannan hadisi yana da inganci, sam ba shi da alaka da ziyarar kabari, domin kuwa Allah wadai din da manzo ya yi ya shafi matan da suka fito domin kallon janaza, ba tare da wani aiki da zasu yi ba wajen kai jana’zar, saboda haka wannan bai shafi batun ziyarar kaburbura ba.

A nan dole mu yi tunatarwa a kan wani al’amari shi ne, addinin musulunci addini ne wanda ya dace da halitta mutum, kuma mai sauki, manzo yana cewa: “Akidun musulunci akidu ne tabbatattu duk wanda zai shiga cikinsu ya shiga tare da dalilai na hankali”.

Mu dauka cewa mahaifiyar mumini sai ta rasa danta aka kuma rufe shi a karkashin kasa, sai ta damu a kan hakan, abin da kawai zata iya yi a nan shi ne ta ziyarci kabarinsa. A nan idan aka hana ta yin wannan aiki wanda ya dace da hankali kuma dukkan mutanen duniya sun tafi a kan hakan, wannan zai haifar da muguwar damuwa ga zuciyar uwa. Shin musulunci zai yi hani da irin wannan aiki sannan kuma ya zama addini mai sauki?

Kai asali ma ziyarar kaburbura wani darasi ne kuma mai sanya mutum ya rika tunawa da lahira wanda kuma ya kunshi karanta wa wadanda aka ziyarta fatiha. Ta yaya za a hana mata dangane da samun wannan falala?

Da wani kalamin kasantuwar hikimar ziyarar kaburbura tana kunshe da daukar darasi da tunawa da lahira, ta yaya za a kebance maza kawai ban da mata a ciki?

Kasantuwar ziyarar kaburbura ya nisanta da duk wani sabo, idan muka dauka haka kuma sai aka hana mata a wancan lokaci, to kila sakamakon cewa ba su kiyaye sharuddan da suka kamata ne.

Ziyarar Kabarin Manzo Mai Girma A Mahangar Malaman Hadisi Da Fikihu

Tare da bibiyar maganganun manyan malaman hadisi da malaman fikihu, zamu ga yadda kodayauhse malaman musulunci suke karfafawa a kan kasantuwar ziyarar kabarin manzo a matsayin mustahbbi mai karfi, Sannan suna kiran mutane zuwa ga ziyarar kabarin manzo mai tsarki.

Takiyyuddin Subki Shafi’i (ya rasu shekara ta 756) Wanda yake daya daga cikin manyan malaman karni na takwas. Yayin da yake kalu balantar akidun Ibn Taimiyya wanda yake inkarin ziyarar kabarin manzo (S.A.W), ya rubuta littafi mai suna (shifa’us sikam fi ziyarati khairil anam) a cikin wannan littafi ya yi kokari ya tattaro ra’ayoyin malaman Ahlus Sunna tun daga karni na hudu har ya zuwa lokacinsa a kan wannan al’amari, a cikin wannan littafi nasa ya yi kokarin tabbatar da nuna cewa ziyarar kabarin manzo yana daga cikin abubuwan da aka sallama a cikin fikihu a kan cewa mustahabbi ne. Manyan malaman hadisi da fikhu sun ruwaito hadisai daban-daban a kan kasantuwar ziyar manzo a matsayin mustahabbi, sannan suka ba da fatawa a kan hakan.[19]

Allama Amini wanda yake bincike na wannan zamani kuma mai tsanantawa wajen bincikensa (1320-1390), a cikin babban littafin nan nasa “Algadir” Ya yi kokari wajen cike abin da ya ragu a kan wannan batu na ziyar kabarin manzo, inda ya yi kokari ya zo da ra'ayoyin malamai arbai’n wadanda suka hada da malaman hadisi da na fikhu har ya zuwa malaman zamaninsa. [20]

Wannan marubuci shi ma ya yi kokari ya samo wasu daga fatwoyin da ba su zo ba a cikin wadancan littattafan guda biyu da muka ambata. Ta yadda ya kawo su a cikin wani karamin littafi da ya rubuta a cikin harshen larabci. Kai har da babban mai fatawar Kasar Sa’udiyya wato sheikh Abdul Aziz bn Baz ya ba da fatwa a kan mustahabancin ziyarar kabarin manzo mai girma.[21]

Kawo dukkan maganganun malamai a kan wannan batu ba zai yiwu ba wannan wuri, saboda haka kawai zamu wadatu da kawo wasu daga ciki ne kawai kamar haka:

1-Abu Abdullaji Jujani Shafi’i (ya rasu a shekara ta 403) Bayan ya yi maganganu a kan girmama manzo sai yake cewa: A matsayin tuanatarwa a yau ziyarar manzo shi ne ziyarar kabarinsa mai albarka.[22]

2-Abu Hasan mawardi (ya rasu a shekara ta 450) Yana rubuta cewa: Jaogoran matafiya zuwa aikin hajji bayan an gama aikin hajji sai ya jagoranci twagarsa zuwa madina domin mahajjata su hada ziyara guda biyu, wato ziyarar dakin ka’aba da ziyarar kabarin manzo. Ta haka ne zasu kiyaye martabar manzo suka kuma bayar da hakkinsa na biyayya gare shi. Ziyarar kabarin manzo ba ya daga cikin farillan ayyukan hajji, amma yana daga cikin mustahabban aikin hajji.[23]

3-Gazali ya yi bayani mai fadi dangane da ziyar manzo (S.A.W), Sannan ya yi bayani a kan ladubban ziyarar manzo Yana cewa: Manzo yace: ziyarata yayin da ba ni da rai duk daya ne da ziyarata a lokacin da nake raye. Sannan duk wanda yake da karfin jiki da dukiya amma bai ziyarce ni ba to ya yi mani tozarci.

Gazali yana karawa da cewa: Duk wanda ya yi nufin ziyarar manzo to ya aika masa da gaisuwa a bisa hanya, sannan a lokacin da idonsa ya hangi itatuwa da bangayen madina sai ya ce: Ya Allah wannan shi ne haramin Manzonka ka sanya shi kariya a gareni daga wuta, Sannan ya zama aminci a gare ni daga azabar wuta da munin hisabi.

Sannan Gazali ya yi tunatarwa dangane da ladubban ziyarar Manzo yana rubuta cewa: Wanda ya ziyarci manzo sai wuce a “Bakiyya” don ya ziyarci kabarin Imam Hasan bn Ali (A.S) Sannan ya yi salla a masallacin Fadima (A.S).[24]

4-Alkali Iyadh maliki (ya rasu a shekara ta 544) yana rubuta cewa: Ziyartar manzo wata Sunna ce wadda kowa ya aminta da ita. Sannan ya ruwaito wasu hadisai dangane da ziyarar kabarin Manzo sannan yana karawa da cewa: Maziyarcin kabarin manzo, to ya kamata ya nemi tabaraki da wurin ibadar manzo (Raudha) Minbarinsa, wurin da yake tsayawa, da shika-shikan da manzo yake jingina a wurinsu da kuma wurin da jibra’il yake saukar wa manzo da wahayi. [25]

5-Ibn Hajjaj Muhammad bn Abdali Kirawani Maliki (ya rasu a shekara ta 738) bayan ya yi magana dangane da ziyarar manzanni da ladubbanta da yadda ake yin kamun kafa (tawassuli) da su da neman biyan bukata daga garesu, sai ya tunatar dangane da ziyarar kamar haka:

“Abin da muka fada dangane da wadansu, a kan abin da ya shafi ziyarar shugaban wadanda suka gabata da wadanda zasu zo kuwa da yadda ake yi masa salla dole ne mu fadi abin da ya wuce hakan. Abin da ya dace shi ne mutum tare da kaskantar da kai ya halarci haramin manzo domin kuwa shi mai ceto wanda ba a mayar da cetonsa. Duk wanda ya tunkare shi ba zai koma ba yana mai yanke kauna ba. Sannan duk wanda ya zo haraminsa yana neman taimakonsa da biyan bukatarsa ba zai rasa abin da yake nema ba”.

Sannan ya cigaba da cewa: Malamammu (Allah ya gafarta musu) Suna cewa abin ya dace shi ne: wanda ya ziyarci manzo ya rika jin cewa kamar manzo yana raye ne ya ziyarce shi. ”[26]

6-Ibn Hajar Haisami Makki Shafi’i (ya rasu shekara ta 973) Ya kasance ya yi riko da dalilin da dukkan malamai suka hadu a kansu wajen kafa hujja a kan kasantuwar mustahabbancin ziyarar manzo. Sannan yana karawa da cewa: Sabawar wani malami guda a kan wandannan dalilai kamar Ibn Taimiyya ba ya cutar da wadannan dalilai da a ka hadu a kan ingancinsu. Domin kuwa malamai da yawa sun bibiyi maganganunsa kuma suna tabbatar da rashin ingancinsu.

Daya daga cikinsu kuwa shi ne Izz bn Jama’a, kamar yadda Ibn Hajar yake cewa: “Ibn Taimiyya mutum ne wanda Allah ya batar da shi, Sannan ya sanya masa tufafin kaskanci”. Sannan Sheikh Takiyyuddin Subki wanda dangane da matsayinsa na ilimi kowa ya aminta da shi, littafi na musamman ya rubuta don kalubalantar fatawoyin Ibn Taimiyya.[27]

7-Muhammad bn Abdul wahab yana cewa: Mustahabbi ne ziyayar manzo amma wajibi ne mutum ya yi tafiya zuwa wajen domin ziyara da yin salla a wajen.[28]

8-Abdurrahman Jaziri marubucin littafin nan (Alfikhu Ala Mazahibil Arba’a) Inda ya kawo fatawoyin dukkan malaman mazahaba guda hudu na Sunna, yana cewa: Ziyarar kabarin manzo yana daya daga cikin manyan mustahabbai, sannan hadisai sun zo a kan hakan, sannan ya cigaba da kawo hadisai guda shida da suka yi bayani a kan ziyarar manzo da ladubbanta. [29]

Sakamakon cewa duk shugabannin fikihu guda hudu ba su yi wani karin bayani ba a kan abin da aka ambata a sama ba, yana nuna cewa duk malaman wannan zamani suma sun tafi a kan hakan.

9-Shekh Abdul Aziz bn Baz yana cewa: Duk wanda ya ziyarci manzo mustahabbi ne ya yi salla raka’a biyu a (raudhar Manzo) Sanna ya yi wa manzo sallama, Sannan mustahabbi ne ya je “Bakiyya” domin ya yi sallama ga shahidan da a ka rufe a wajen.[30]

A nan zamu takaita da wannan abin da muka kawo dangane da wannan al’amari mai son karin bayani dangane da haka, sai ya koma zuwa ga “Risalar da muka rubuta a kan haka a cikin harshen larabci. [31]

Ziyarar Kabarin Manzo A Mahangar Kur’ani Da Sunna

A: A Mahangar Kur’ani Maigirma

Kur’ani mai girma yana bai wa al'ummar musulmi umarni da su je wajen manzo su nemi gafararsa sannan su nemi manzo (S.A.W) don ya nema musu gafarar Allah madaukaki: "Duk lokacin da suka zalunci kawunansu (suka yi zunubi) idan suka zo wajen manzo suka nemi gafara kuma Manzon ya nema musu gafara wajen Allah, lallai Allah mai rahama ne kuma mai karbar tuba. "[32]

A wani wurin ciki Kur’ani Allah madaukaki yana zargin munafukai da cewa duk lokacin da aka neme su da su je wajen ma'aiki don ya nema musu gafara sai su ki: "Idan aka ce musu ko zo manzo ya nema muku gafara, sai su juya fusakunsu (don nuna rashin amincewa) zaka ga suna kin maganarka suna masu nuna girman kai. "[33]

Shehin malamin nan kuma Ahlussunna, Takiyyuddin Subki, Ya yi imani da cewa: Msuslmi a wannan lokacin ma tare da amfani da wannan aya suna iya zuwa wajen manzo su nemi gafararsa kuma Allah ya gafarta musu. Ya kara da cewa duk da yake wannan aya ta shafi lokacin da manzo yake a raye ne, amma neman gafara ta hanyarsa bai kebanta da lokacin da yake a raye ba. Saboda wannan wani matsayi ne wanda aka bai wa manzo (S.A.W) don haka sakamakon rabuwarsa da duniya wannan matsayi ba zai kau ba.

Mai yiwuwa a ce: Wannan abin da ya zo a cikin wannan aya da muka ambata a sama, ya kunshi nuna matsayi da daukaka ta manzo ne kawai, amma aiwatar da wannan ya kebanci lokacin rayuwarsa ne kawai, amma ba lokacin da baya duniya ba, ta yadda alakarmu da shi ta yanke.

Amma wannan magana sam ba abin karba ba ce, domin kuwa dalilan da zamu ambata a nan gaba suna bayyana cewa rasuwar manzo sam ba ta da wani tasiri a kan wannan al'amari, don haka mutuwa da rayuwarsa babu wani bambanci duk daya ne:

1-Mutuwa ba tana nuna karshen dan Adam ba ne, mutuwa wata sabuwar kofa ce don shiga wata sabuwar rayuwa kuma duniyar da duk abin da yake a ckinta ya fi abin da yake a duniyar da ta gabata ga rayuwar dan Adam, saboda haka mutum rayayye ne a waccan duniya yana gani kuma yana ji. Musamman shahidai wadanda bayan sun dandana shahada zasu cigaba da karbar ci da sha daga Allah madaukaki, kuma suna cikin jin dadi na musamman ta hanyar ruhinsu. Saboda haka zamu yi bayani a kan wannan a nan gaba a cikin bahasin rayuwar barzahu.[34]

2-Ya zo da yawa a cikin ruwaya cewa: Salatin da musulmi suke yi wa manzo akwai mala'iku na musamman masu isar da wannan salati zuwa ga manzo (S.A.W) don haka duk inda mutum yake idan ya yi wa manzo salati zai isa zuwa ga manzon. Kamar yadda yake cewa: "Ku yi mani salati, salatin yana isa zuwa gare ni daga duk inda kuke".[35]

3-Musulmi a wajen tahiyar salla an umurce su da su yi wa manzo sallama, sannan su yi masa gaisuwa, "Assalamu alaika ayyuhan nabiyu warahamatullahi wa barakatuhu" Wannan gaisuwa ba wai kawai an umurci musulmi ba ne da su yi ta zuwa ga manzo amma shi ba ya jin abin da suke yi, Manzo yana raye kuma yana sauraren mu lokacin da muke yi masa salati.

Wadannan abubuwan da muka fada a sama suna nuna cewa Manzo yana raye a rayuwar barzahu, sannan yana da alaka da mu kuma yana jin abin da muke yi. Sannan yana jin rokonmu kuma yana biya mana bukatunmu a lokacin da ya dace. Saboda haka a nan ya kamata mu ce wadannan ayoyi da muka yi bayani a sama, Suna da ma'ana mai fadi, saboda haka yanzu ma suna kiranmu da ziyarar manzo a kabarinsa kuma mu nemi gafara kuma ya nema mana gafara ga Allah, sannan mu nemi bukatunmu daga gareshi. Saboda haka ya zo a cikin ziyarar manzo da ake karantawa a haraminsa cewa mai ziyara ya nemi gafarar Allah ta hanyar manzon tare da kula da ma'anar ayar da muka yi bayani a sama. Saboda haka ziyarar manzo ba wani abu ba ne sai kawai yin salati ga manzo da kuma neman bukatu da gafarar Allah ta hanyar mazon. Saboda haka wadannan ayoyi na sama suna iya zama sheda a kan inganci da mustahabbancin ziyarar manzo (S.A.W).

Wata sheda kuma a kan wannan batu shi ne, bayan rasuwar Manzo wani balarabe ya shigo Madina yana karanta wannan aya da muka ambata, sai ya ce: "Na zo wajenka ina mai neman gafara daga zunubaina kuma ina mai neman ceto gareka zuwa ga Ubangijina".[36]

Sannan muhimmin abu kamar yadda Subki yake cewa: Kiran al'ummar musulmi da su ziyarci manzo kuma su nemi gafara da bukatunsu daga gareshi wata alama ce ta karrama manzo da girmama shi. Kuma tabbas wannan girmamawa ba ta kebanci lokacin rayuwarsa ba, saboda girma da mukamin ruhinsa a wajen Allah wani abu ne wanda ba mai shakku a kansa kuma madawwami ne, saboda haka bai kebanta da wani zamani ba sabanin waninsa.

Saboda haka ne malaman Tafisri suka tafi a kan cewa, girmama manzo bai kebanci lokacin rayuwarsa ba, saboda haka dole ne a kiyaye shi har bayan rasuwarsa. Har ma ayar da ke umurta musulmi da su rika magana a hanakali a gaban manzo, tana nan a matsayinta, inda Allah yake cewa: "Ya ku wadanda kuka yi Imani kada ku daga muryarku saman muryar Annabi[37]".

Saboda haka bai kamata mutum ya rika magana da karfi a cikin haramin mazon mai tsaira ba. Sannan wannan aya an rubuta ta a kan kabarin manzo, wanda duk ya je wannan wuri ya gane wa idonsa hakan.

B: A Mahangar Sunna

Mun ga hukunci da matsayin Kur’ani a kan wannan al'amri, yanzu abin da ya rage shi ne ku ga kuma me Sunnar manzo ke cewa a kan hakan..

Ruwayoyi da dama sun zo akan wannan batu na ziyarar kabarin manzo, kuma malamai sun yi kokarin tattara su da kuma tabbatar da danganensu. Saboda haka a nan a matsayin misali zamu kawo wasu daga cikinsu kamar haka:

1-Takiyyuddin subki (ya yi wafati a shekara ta756h) a cikin littafinsa "Shifa'us sikam" ya ruwaito hadisi tare da sanadi ingantacce. [38]

2-Nuruddin Ali bn sahmudi (ya yi wafati 911H) ya ruwaito ruwaya 17 akan wannan batu, a cikin littafinsa na tarihin Madina sannan kuma ya inganta sanadinsa.[39]

3-Muhammad fukki daya daga cikin Malam Azahar tare da shafe sanadi ya ruwaito matanin ruwayoyi 22 a kan ziyarar manzo.[40]

4-Allama Amini tare da tare da bin diddigi wanda ya ci a yaba masa, ya tattara ruwayoyi da dama a kan ziyarar manzo (S.A.W) saboda haka a nan kawai zamu yi nuni da daya daga cikin ruwayoyi da ya samo daga littafi 41 da a ka ruwaito a kan hakan. Al-Gadir

Saboda haka kawo dukkan ruwayoyin da danganensu ba zai yiwu ba a nan, saboda haka kawai a nan zamu takaita ne da kawo wasu kawai daga cikinsu. Wadanda suke son karin bayani sai su koma zuwa littafin da aka ambata a sama.

Hadisi na farko: "Wanda duk ya ziyarci kabarina aljanna ta wajaba a gareshi"[41]. wannan hadisi Allama Amini ya ruwaito shi tare da sanadi daga littafi 41.

Hadisi na biyu: Dabarani a cikin mu'ujamul Kabir, Gazali a cikin ihya'u ulum daga Abdullahi bn umar, Manzo yana cewa: "Duk wanda yazo ziyara kuma saboda kawai ziyarata ya zo, to ya wajaba in cece shi a ranar kiyama. "

Hadisi na uku: Darul Kutni ya ruwaito daga Abdullahi bn umar cewa manzo (S.A.W) ya ce: Duk wanda ya ziyarce ni bayan wafatina a lokacin aikn hajji, to kamar ya ziyarce ni a lokacin da nake a raye. "

Hadisi na hudu: Darul kutni ya ruwaito daga bn Umar cewa manzo (S.A.W) ya ce: "Duk wanda ya ziyarci kabarina kamar ya ziyarce ni a lokacin da nake a raye. " A nan ya kamata mu yi nazarin matsayin ziyara a wajen Imaman Ahlul-bait (A.S)

Ziyar Manzo A Ruwayar Ahlul-Bait (A.S)

1-Imam Bakir (A.S) yana cewa Manzo (S.A.W) yana cewa: "Duk wanda ya ziyarce ni ina raye ko bayan na yi wafati zan kasance mai cetonsa a ranar kiyama"[42]

2-Imam Ali (A.S) yana cewa: "Ku cika hajjinku da manzon Allah a lokacin da kuka fito daga dakin Allah, domin kin ziyartarsa rashin girmamawa ne gare shi, an umurce ku da yin hakan, tare da ziyarar kaburburan da aka umurce ku zaku karashe hajjinku."

3-Imam Sadik (A.S) daga manzon tsira (S.A.W) yana cewa: "Duk wanda ya zo Makka don aikin hajji amma bai ziyarce ni ba, zan banzatar da shi a ranar tashin kiyama, wanda kuwa ya ziyarce ni cetona ya wajaba a garesa, duk wanda cetona ya wajaba a garesa, aljanna ta wajaba a garesa. Saduk: Ilalish shara'i'i

4-Imam Sadik (A.S) yana cewa Manzo. (S.A.W) yana cewa: "Duk wanda ya ziyarce ni zan zama mai cetonsa a ranar tashin kiyama". [43]

Ruwayoyin da dukkan bagarori guda biyu suka ruwaito ta fuskar ma'ana ba su da bambanci, saboda haka suna karfafa abubuwa guda biyu kamar haka:

A-Duk wanda ya je Makka bai ziyarci Manzo ba, to ya yi wa manzon jafa'i.

B-Duk wanda ya ziyarci Manzo, Manzo zai cece shi a ranar kiyama. Saboda haka don mu takaita wadannan ruwayoyi guda takwas daga Shi’a da Sunna sun wadatar wanda yake son karin bayani sai ya koma zuwa ga littfan da muka ambata.

Tattaunawar Imam Malik Tare Da Mansur Dawaniki

Kadhi Iyadh ya nakalto tattaunawar Imam Malik tare da Mansur Dawaniki kamar haka:

Mansur Dawaniki wanda yake khalifa ne mashahuri na Abbasiyya, wata rana ya shiga haramin Manzo yana magana da karfi. Malik a lokacin shi ne Fakih a Madina sai ya juya zuwa ga Mansur ya ce: Ya kai shugaban Muminai, kada ka daga muryarka a cikin wannan masallaci, Allah madaukaki ya koya wa wasu mutane ladabi inda yake cewa: "Kada ku daga muryarku saman muryar Annabi"[44] Sannan ya ya bi wasu gungu daga cikin mutane ya ce: Lallai wadanda suke kasa da muryarsu a gaban manzon Allah, su ne wadanda Allah ya jarabba zukatansu da takawa"[45] Sannan Allah yana cewa Wasu gungun mutane wadanda suke hayaniya a bayan gidan Manzo suna cewa: Ya Muhammad ka yi sauri ka fito daga cikin gida, Allah yana kaico da halinsu, yan cewa: "Lallai wadanda suke kiranka daga bayan gida mafi yawansu ba su da hankali".[46] Sannan ya cigaba da cewa girmama Manzo a lokacin da ba shi da rai kamar lokacin da yake da rai ne babu bambanci.

Lokacin da Mansur ya ji wannan magana sai ya zo da kansa wajen Malik ya ce: A lokacin da nake addu'a zan kalli kibla ne ko kuwa kabarin Manzo?

Sai Malik ya ba shi amsa da cewa: Me ya sa zaka juya wa Manzo baya alhali kuwa shi ne tsaninka kuma tsani ga babanka Adam har zuwa ranar tashin kiyama, don haka ka kalli kabarin Manzo ka nemi ceto daga gare shi Allah ya amshi cetonka. Allah yana cewa: A lokacin da suka zalunci kawunansu suka zo gare ka suna neman gafarar Allah manzon zai nema musu gafara..."[47]

Ziyarar Kabari Da Kiyaye Asali

A cikin wannan bahasi namu mai tsawo kawai mun yi amfani ne da ruwayoyin da suke nuni a kan wannan al'amari daga ruwayoyin Ahlus Sunna. Amma muna da ruwayoyi da dama daga maruwaitanmu na Shi’a da suka ruwaito daga Imaman Ahlul Bait (A.S). Wadanda ba mu yi nazari a kansu ba. Sdaboda haka idan aka duba littattafan hadisai na Shi’a za a tabbatar da wannan al'amari cewa, ziyarar Manzo da Ahlul Bait (A.S) yana daga cikin abin da yake karbabbe ga kowa a cikin wannan mazahaba ta Ahlul Bait (A.S) sakamakon haka ne aka rubuta littattafai? da dama a kan hakan wadanda a ka fi sani da suna "almazar" wato wurin ziyara, daga cikin wadannan littattafai? kuwa wanda duk ya fi shahara shi ne, "Alkamil Ziyarat" wanda shehin malamin nan mai suna Ja'afar bn muhammad bn kulawaihi ya rubuta. (ya yi wafati 367H).

A nan zamu kara da cewa, kiyaye abubuwan da suke na asali yana daya daga cikin ayyukan addinin musulunci. Abin da muke nufi da asali kuwa shi ne abin da yake bayyanar da gaskiyar musulunci da cigabansa har ya isa zuwa ga dukkan zamuna.

Addinin musulunci addini ne da yake na duniya baki daya, don haka har zuwa tashin kiyama zai kasance matsayin addini cikakke har karshen duniya. Saboda haka dole ne mu yi iya kokarinmu mu ga cewa mun kiyaye asalin wannan addini don ya isa kamar yadda ya zo zuwa ga wadanda zasu zo a nan gaba.

Saboda haka ziyarar kabarin Manzo da Ahlul Bait (A.S) yana daya daga cikin kiyaye asalin addini, don haka barin hakan bayan wani tsawon zamani sai ya zamana an manta da wannan babban aiki mai albarka. Saboda haka dangane da wadanda zasu zo nan gaba sai ya zamana wadannan wurare na musamman na manyan bayin Allah ya koma kamar wani abin tatsuniya.

Kasancewar zuwan Isa (A.S) a yau wani abu ne wanda ba abin shakka ba ga al'ummar musulmi, amma a yammacin duniya musamman ga matasa al'amarin Annabi Isa ya zama kamar wani abin tatsuniya, wannan kuwa ya faru ne sakamakon rashin wani abu wanda yake nuna gaskiyar samuwar shi Annabi Isa (A.S) a hannayen mutane. Wannan kuwa ya faru ne sakamakaon canza littafinsa da a ka yi, don haka dangane da shi kansa Masih da mahaifiyarsa da sauran manyan sahabbansa babu wani abu na hakika wanda yake tabbas daga garesu yake. Don haka sakamakon tsawon zamani a yau al'marin masihiyya ya zamana kimarsa ta rage kuma ya shiga cikin wani halin kokwanto da rashin tabbas. Kamar yadda a yau ziyarar Manzo wadda take daya daga cikin abu na asali a cikin addinin musulunci kuma mai nuna hakikanin matsayi da samuwar Manzo tana neman ta zama wani abu marar muhimmanci a cikin al'ummar musulmi, kuma ya zamana an ajiye ta a gefe guda. Don haka sakamakon tsawon zamani akwai yiwuwar abubuwan asali na addinin musulunci da waliyyan Allah, su shiga cikin wannan hadari mai girma.

Saboda haka al'ummar musulmi dole ne su tashi tsaye domin kare wannan hadari da ya fuskanto su, wannan kuwa yana samuwa ne ta hanyar kiyaye duk wani abu da ya shafi sakon manzanci da Imamanci, ta yadda za a rika tuna shi a kowane zamani. Saboda haka ziyarar wadannan manyan bayin Allah tana daya daga cikin hanyoyin kiyaye su daga bacewa da kuma yin tunani a kansu a kowane lokaci. Saboda haka sakamakon yin hakan ba za a taba watsi da matsayin wannan muhimmin al'amari ba, ta yadda za iya kulle kofar ganawa ta hanyar ruhi da wadannan manyan bayin Allah ga al'ummar musulmi. Saboda haka da ikon Allah a nan gaba zamu yi magana a kan kiyaye wadannan wurare masu tsarki.