Ajali da Wa'adi

Hafiz Muhammad Sa’id hfazah@yahoo.com
Ajali Ko Cikar Wa'adi Sau da yawa akan yi magana kan ajali a matsayin wani abu da Allah ya sanya shi a matsayin hanyar katse rayuwar mutum ta wannan duniyar da ciratarsa zuwa lahira ko kuma duniyar barzahu.
Idan muka duba ajaloli zamu ga sun bambanta ta yadda wasu gajeru ne wasu kuma masu tsayi, sannan kuma wasu ana jinkirta su wasu kuma ana gabatar da su, ta yadda mutum zai iya mutuwa da wuri ko kuma ya mutu ba da wuri ba, da ma'anar cewa yana iya mutuwa ajalinsa na asali bai yi ba, kuma yana iya ketare ajalili masu yawa da ya kamata ya mutu amma sai ya wuce bai mutu ba. Amma ajalin asali dukkan maganganu sun zo a kan cewa ba a iya ketare shi don haka idan ya zo ko babu wani dalili na zahiri to dole ne a wuce.
Sannan tafiya zuwa barzahu ta hanyar ajali ne kawai wanda yake wata haihuwa ce da takan kai mutum wani gida da ya saba wa wannan gida na duniya a dukkan dokokinta da yanayinta, musamman da yake gidan barzahu ya kasu gida biyu ne kawai, koda yake yana iya kai wa gida uku idan mun kira kabarin masu sabo daga musulmi wadanda ba muminai ba a matsayin wani gidan daban. Idan ina son in yi bayani sosai, duniya gida daya ne wanda ba shi da bambanci tsakanin mutane musulminsu da wadanda ba musulmi ba, kuma wannan a fili yake cewa; babu wani bambanci tsakanin wadannan halittun guda biyu, don haka ne ma Allah madaukaki ya sanya ta a bisa asasin riko da sabubba ta yadda duk wanda ya rike sababi to zai samu wannan duniya.
Muna iya ganin ci gaban zamani da ake ganin yana hannun yammacin duniya a yau, wanda a da yana hannun kasashen musulmi ne, hasali ma su kasashen musulmi su suka fara kawo shi suka dankara shi a kan yammacin duniya, amma yau sai ga shi ta juye. Don haka muna iya ganin lokacin da musulmi ya yi riko da sababi a wannan duniya sai ya mallake ta amma lokacin da yammancin duniya ya rike sababi sai ya mallake ta a hannunsa; sai suka zama madogara a karfin soja da tsaro da ilimin fasaha da kere-kere, da siyasa da tafiyarwa, sai suka zama su ne masu hukunci da kotunan duniya da bankuna da dukkan manyan cibiyoyin tattalin arziki. Don haka babu ruwan Allah a matsayin shi na mai arzutawa, yana kwararo arzikinsa ne inda sabubban hakan suka kammala amma wannan fa ba yana nufin ba shi da hannun gaibi na taimako ta wani janibin ba, sai dai lallai muna bukatar riko da sabubba, don haka ne duniya ta kasance gida daya tilo.
Amma a duniyar barzahu gidaje biyu ne kacal, wato "Barhut" da "Wadis salam" sai ya kasance ma'aunin hakan shi ne wanda ya kyautata ayyuka da suka dogara da imani sahihi, don haka ne duk wanda ya yi aiki da Allah ya karba idan ya mutu yana "Wadis salam" ne, wadannan su ne muminai da suka yi aiki bisa jagorancin da Allah ya sanya da shugabanci sahihi da ya yi umarni, kuma su ne wadanda ya shardanta karbar ayyukansu, sai ya kasance da imani ne ake karbar ayyuka, amma da musulunci ne ake auratayya da raba gado da cin yanka da kare jini da dukiya da mutunci, kuma dukkan wanda ya yi musulunci to yana da wannan falala, amma kuma idan bai yi imani ba zai rasa gidan "Wadis salam", wannan wuri a Iraki yake kamar yadda ya zo a wasu ruwayoyi.
Amma wanda bai yi imani ba koda kuwa ya yi musulunci ya yi aiki karkashin wannan musuluncin amma ya yi gaba da waliyyan Allah to da shi da wanda bai yi musulunci ba zasu tsinci kansu a "Barhut" wanda wuri ne da yake a Yaman da Allah ya halicce shi a gabashin duniya da yake da wata rijiya da ake kiranta da "Barhut" kamar yadda ya zo a wasu ruwayoyi. Wannan yana nuan cewa; Barzahu duniya ce mai gidaje biyu kuma ana nufin duk wanda yake "Barhut" zai azabtu, amma kuma wanda yake ya yi musulunci daidai gwargwadon yadda Allah ya yi umarni kamar yadda sako ya zo masa ba kamar yadda Allah ya aiko da sakon ba to Allah ba zai kai shi "Barhut" ba kuma zai huda kabarinsa yana samun sanyin da yake a aljannar da ya halitta a yammacin duniya da ake kiranta "Wadis Salam" da asasinta yake a Iraki, don haka irin wadannan mutane zasu ji dadi a wannan rami na kabari da suke ciki koda kuwa ba a kai su "Wadis salam" ba.
Haka nan duk wanda yake a "Wadis salam" zai ji dadi, domin wuri ne da ake kai wadanda suka yi imani suka yi aiki na gari, wannan yana nuna mana a fili cewa duk wanda yake a Barhut to yana shan wuya, kuma duk wanda yake a Wadis salam yana jin dadi ne. Wannan dai lamari ne da yake da wahalar yin hukunci, kuma akwai tambayoyi da ake ta jefawa kan wannan mas'alar cewa; shin zai yiwu a yi aiki mai kyau ba imani kuma ya samu karbuwa har mai shi ya samu jin dadi a kabarinsa sakamakon yana da uzurin rashi samun sako daidai ko rashinsa gaba daya kamar irin su Hatimud Da'i? ko kuwa zai yiwu a yi aiki maras kyau alhalin akwai imani sai ya kasance shi kuma tun daga kabarinsa yana samun shi ma ni'imar wannan aiki da ya yi sakamakon yana da uzurin rashin samun sako kamar sauran muminai masu zunubi? Ko kuwa zai yiwu a raba aiki mai kyau da imani ta yadda zai kasance yana aiki na gari amma ba mumini ba ne? Sannan kuma shin akwai alaka mai karfi ta lizimtar imani da sanin Allah ko kuwa? Wadannan tambayoyi ne mabambanta da malamai da yawa suka yi sabani kan wasunsu.
Amma idan muka dogara da abin da muka ambata a baya muna iya cewa; Kenan ayyukan mutane su ne ma'aunin jin dadi a Barzahu, sai dai su kasance karkashin imani sahihi ko kuma uzurin rashin samun sako na gari. Kuma idan akwai wanda ya yi imani amma ba shi da aiki na gari to zai sha wahala ke nan sai dai idan ya samu ceton waliyyai daga alayen manzon Allah (s.a.w) kuma wasiyyansa (a.s) kamar yadda wasu hadisai suka yi nuni. Don haka asasin sakamako ya kasance aiki ne mai lasisi daga Allah, don haka wanda bai yi samu sako ba ko bai zo masa daidai ba, amma ya tsayar da adalci tsakanin mutane, ya yi kyauta bai yi keta da hassada ba, bai cuci kowa ba, bai hada sharri ba, ya kiyaye hakkokin mutane to zai samu jin dadi, amma wanda bai yi ayyuka na gari ba koda kuwa ya yi imani to zai samu fuskantar matsaloli. Sai dai kamar yadda muka kawo akwai maganganu masu yawa kan mas'alolin "Barzahu" da ba mu da isasshen lokacin tattauna su a wannan makala gajeriya.
Amma lahira sai ta kasance ita ce haihuwa ta uku ta mutum kuma fadinta ya fi na barzahu kamar yadda fadin ciki yake ne da bambancinsa da wannan duniya haka ma fadin duniya yake tsakaninsa da na barzahu, sannan kuma tsakanin fadin barzahu da lahira da za a koma gaba daya kamar nisan da yake tsakanin fadin duniya da barzahu ne, don haka ita wuri ne da ba shi da iyaka.
Lahira tana da gidaje uku ne da suka hada da; gidan wuta, da na aljanna, da wata duniyar daban a gidan wuta amma ita tana da ni'ima ne, sai dai ni'imarta ba ta kai ta aljanna ba, domin ita aljanna ba ta da iyaka kuma sakamakon imani ce, don haka lahira sai ta kasance duniyoyi uku ne, sai dai maganganu suna kaikawo kan cewa irin wadannan mutane za a aika musu da dan sako ko tun a Barzahu ko kuma a wannan duniya domin a jarraba su sai a kai wadanda suka yi ban gaskiya aljanna wadanda kuwa suka karyata a kai su wuta.
Sannan kuma an sanya imani a matsayin sakamakon sa'ada da rabauta da jin dadi a wannan gida na lahira, sai ya kasance ayyuka ba sa tasiri a wannan rana sai wanda ya yi imani na gari sahihi shi ne zai samu rabauta maras iyaka kuma ya shiga aljanna, amma wanda bai samu sako ba yana da uzuri saboda sako bai je masa ba sai a kai shi waccan duniyar mai makotaka da jahannama domin ya ji dadinsa a can, amma wanda bai yi imani ba kuma ba shi da uzurin da za a karba na hana shi yin imani to sai ya tafi gidan azaba.
Da wannan bayani muna iya ganin cewa duniyoyin rayuwa da a sakamakon ajaloli ne ake ciratuwa zuwa garesu sun kasu gida uku ne ke nan:
Duniyarmu ta yau wacce take gida daya ce kuma babu bambancin ni'ima da jin dadi da rabauta tsakanin mumini da wanda ba mumini ba, don haka duk wanda ya riki sababi zai same ta, kuma babu bambancin masu ayyuka na alheri da marasa alheri, ko imani sahihi da wanda ba sahihi ba.
Duniyar barzahu wacce take gida biyu ce, "Barhut" da kuma "Wadis salam" kuma wanda yake da aiki na gari to shi ne zai ji dadi kuma ya sami sararawa da rabauta da arzuta koda kuwa yana da karancin aiki matukar imaninsa ya inganta.
Duniyar lahira wacce take da gidaje uku da ya hada da aljanna, da duniyar wuta, da kuma wancan gida mai makotaka da wuta da muka nuna cewa za a aika musu da nasu dan sako, kuma babban asasi na samun rabauta da sa'ada a wannan duniyar tana karkashin yin imani ne.
Sannan akwai wani bahasi da wasu sun so su ba shi muhimmanci wanda yake nuna cewa; shin wadannan gidaje da suka hada da duniya, da barzahu, da lahira a wannan duniyar suke ko kuma a duniyoyi mabanbata? wannan al'amura ne masu bukatar dogon bayani, sai dai an samu sabani game da hakan, domin wasu suna ganin a wannan duniyar komai yake, wato; barzahu kamar yadda take gida biyu daya a Iraki wato Wadis salam, daya kuma a Barhut da yake a Yaman, don haka ma suka tafi a kan cewa; wannan lahirar ma a nan take, ba wani wuri mai nisa ba. Sai ta kasance: "Ranar da za a canja kasa ba kamar wannan kasar ba" da muke a kai, sai a canja mata hukunce-hukunce sabanin na wannan duniya. Akwai ra'ayoyi masu yawa na sakamakon bincike sai dai har yanzu a wasu ra'ayoyi bincike yana ci gaba domin samun hakika, wannan lamari da masana suka samu makalewa a cikinsa.
Idan mun duba maganar Imam Ali (a.s) cewa: "Ya halicci ajaloli sai ya tsawaita su kuma ya gajarta su, ya gabatar kuma ya jinkirtar, ya sanya mutuwa ce sababinsu[1]. Zamu ga tana nuna mana abin da muka kawo a baya na jinkirta ajali ko kuma tsawaita shi.
Zuwan ajali wani abu ne na gaskiya da babu yadda zai saba kuma babu makawa sai ya riski kowane mai rai, wannan doka ce da babu wani wanda ya fita daga cikinta, domin zuwan ajali yana kama da haihuwa ne da babu makawa sai an fita daga cikin uwa sannan za a zo wannan duniya. Don haka ne ma a wasu kalamai na Imam Ali (a.s) yake nuni da cewa; Babu abin da ya fi ajali gaskiya[2]. Kamar yadda ya yi nuni da cewa ajlai magani ne na cututtuka, ita wannan duniya gida ce ta wahalhalu, da cututtuka, da rauni, da rakwarkwashewa, da tankwacewa, da gushewa, don haka sai aka sanya maganin dukkan wannan shi ne ajali, don haka ne wanda ya bar wannan duniya to fa ya bar wadancan nakasoshin har abada[3] kuma ya kama hanyar kamala mai dawwama.
Haka nan ajali wani wuri ne da aka tanada wanda sai an je masa, kuma babu wani abu da zai kai mu zuwa gareshi sai ta hanyar karewar adadin lumfashin da zamu yi a duniya, don haka ne ma a hikimomin Imam Ali (a.s) ya zo cewa; Lumfashin mutum takunsa ne zuwa ga ajalinsa[4].
Haka nan a wasu hikimomi nasa an yi nuni da cewa ajali kariya ce ga dan Adam mai girma, kuma bisa bayanan da muka gabatar muna iya ganin hakan a fili, kuma lallai ajali ya isa mai gadi[5], Kuma shi katanga ce mai kariya[6]. Sannan kuma komai yana da mudda da ajali ayyananne[7] domin Allah madaukaki ya sanya wa komai gwargwado, kuma ya sanya wa kowane gwargwado ajali[8], don haka wannan lamarin ba wani abu ba ne da za a iya guje masa, don haka ne ma a cikin hikima ya zo cewa; duk wanda yake gudun mutuwa to yana gudun kansa ne.
Sa'annan a bisa wanna doka ta ajali wacce ta mamaye komai kuma babu wani abu da ya isa ya fita daga wannan doka ta Allah mai gama-gari, kamar yadda daidaikun mutane suke da ajali haka nan ma al'umma take da ajali, muna iya ganin fadin madaukaki a kan wanna lamari: “Kuma kowace al’umma tana da ajali, idan ajalinsu ya zo ba sa jinkirin awa daya, kuma ba sa gabata. gaggauta musu”[9]. Da fadinsa mai girma; “Ba ma halakar da alkarya sai tana da lokaci kayyadajje. Babu wata al’umma da take rigon ajalinta kuma ba ta jinkiri[10].
Amma kamar yadda ya gabata dukkan al'umma da kuma daidaikun mutane suna da ajali iri biyu ne, akwai ratayayyen ajali wanda yana nufin koda yaushe mutuwa da ajali suna iya riskar halittu, amma wadannan ajaloli ne da ana iya ketare su a wuce su da kiyayewa da sadaka da sadar da zumunci da ayyukan alheri, da sadaka[11], wadannan abubuwa ne da suke fadada nisan ajaloli. A irin wannan lamarin ne Imam Sadik (a.s) yake cewa: Mutane suna rayuwa da kyawawan ayyukansu fiye da yadda suke rayuwa da shekarunsu, kuma suna mutuwa da zunubansu fiye da yadda suke mutuwa da ajalolinsu[12].
Kuma a nan muna iya ganin yadda kur'ani mai daraja ya yi nuni da wannan a fadin madaukaki (s.w.t) “Shi ne wanda ya halicce ku da tabo sannan sai ya kaddara muku ajali kuma da akwai wani ajalin ambatacce gunsa…[13]. Don haka ne a game da tafsirin wannan ayar sai muka ga abin da gidan annabta daya daga alayen Annabi Muhammad (s.a.w) ya karfafa a kan haka yana mai cewa: Ajalin nan da ba ambatacce ba dakatacce ne, yana gabatar da wanda ya so daga gareshi kuma ya jirkinta wanda ya so daga gareshi, amma ajali ambatacce shi ne wannan da yake saukar da abin da yake so ya kasance daga dare mai daraja (Lailatul kadr) zuwa irin wannan dare shekara mai zuwa, kuma wannan shi ne fadin Allah madaukaki: “… Idan ajalinsu ya zo ba sa jinkirin awa daya, kuma ba sa gabata[14].
Sannan akwai tambayoyi masu yawa da amsa su zai iya sanya wannan bahasin ya yi tsayi; kamar shin gidan lahira zai koma gida daya ne daga karshe saboda a samu cikakkiyar amsar cewa komai zai kai zuwa ga kamalarsa da ta dace kamar yadda wasu ma'abota irfani suke gani ko kuwa gidajen nan musamman biyu daga ciki wato gidan wuta da na aljanna zasu dawwama ne har abada.
Da kuma tambayar bambancin siffofi da halaye da yanayin rayuwar duniya da ta barzahu da ta lahira, da matsayin jiki da ruhi a wadannan duniyoyi, da kuma bahasin nan na yadda mutum yakan iya cancanjawa yadda ya so a lahira, amma a barzahu yana zama da surar aikinsa ne, a duniya kuwa ba shi da zabi wajen gina kamanninsa domin Allah ne ya halitta masa shi yadda ya so.
Sannan akwai bahasin nau'in abubuwan rayuwa a wadannan duniya da suka hada da tufafi, da abinci, da gidaje, da yadda ake mallakarsu da kuma yanayinsu da kamanninsu da juna. Da kuma bahasin alakar bayi da Allah (s.w.t), da kuma matsayin alakar maza da mata a wadannan duniyoyi, wadanan dukkansu bahasosi ne masu tarin yawa da zasu daukar mana lokaci, sai dai abin da muka kawo ya wadatar zuwa wani lokaci in Allah ya so.

Hafiz Muhammad Sa'id Kano
Cibiyar Al'adun Musulunci Kano Nigeria
hfazah@yahoo.com
2/13/2009
----------------------------------------

[1] Sharhin nahajul balaga, ibn abil hadid: 7/21.

[2] Gurarul hikam: 10648.

[3] Gurarul hikam: 9905.

[4] Sharhin nahajul balaga, ibn abil hadidi: 7/21.

[5] Alibhar: 5/142/14.

[6] Gurarul hikam: 494.

[7] Nahajul balaga: huduba: 190.

[8] Gurarul hikam: 4778.

[9] A’araf: 24.

[10] Alhijr: 4,5.

[11] Gurarul hikam: 4239.

[12] Albihar: 5/140/7.

[13] Al’an’am: 2.

[14] Albihar: 5/139/3.