Ahlul-bait a Hadisai

AHLUL BAIT A HADISAI
 
Mu'assasar Al-Balagh
Tsarawa: Hafiz Muhammad
 
Kur’ani Mai Daraja:
"Allah Ya shaida cewa: Lalle ne babu abin bautawa face Shi, kuma Mala'iku da ma'abuta ilmi sun shaida, Yana tsaye da adalci, babu abin bautawa face Shi, Mabuwayi, Mai Hikima". (Surar Aali Imrana, 3: 18) .
 
Ahlul-baiti A Cikin Hadisai
1- Hadisus Sakalain (Nauyaya Biyu)
Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa: "Na kusata da a kira ni in kuma amsa, amma ni mai bari muku abubuwa masu nauyi guda biyu ne, su ne kuwa: Littafin Allah Mai girma da Daukaka, da kuma zuriyata. Littafin Allah wata igiya ce da aka sako ta daga sama zuwa kasa, zuriyata kuwa su ne mutanen gidana (Ahlulbaiti). Allah Mai tausasawa Ya ba ni labari cewa su biyun ba za su taba rabuwa ba har abada har sai sun iske ni a bakin tafki. To ku lura da yadda za ku rike su a bayana( )".
Al-Shibrawi al-Shafi'i ya nakalto cikin littafinsa mai suna al-Ithafu bi hubbil Ashraf, cewa: "Muslim da Tirmizi sun kyautata shi (hadisin), haka ma Hakim shi ma ya ruwaito shi, lafazin Muslim kuwa daga Zaid bn Arkam cewa ya yi: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya mike a cikinmu domin ya yi mana huduba sai ya yi godiya ga Allah ya yi yabo gare Shi, sannan ya ce:
"Bayan haka, Ya ku mutane, ni dai mai mutuwa ne, kuma zan amsa kiran manzon Ubangijina. To amma na bar muku wasu nauyayan abubuwa guda biyu tare da ku; na farkonsu Littafin Allah, shiriya da haske na cikinsa, to ku kama Littafin Allah ku yi riko da shi". Sannan sai ya ce: "Da Ahlulbaitina, ina gama ku da Allah dangane da Ahlulbaitina( )".
Al-Shibrawi din kuma ya nakalto cewa: "A wata ruwayar kuma Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa ya yi: "Ni mai bari muku al'amurra guda biyu , ba za ku bata ba idan har kun bi su, su ne kuwa; Littafin Allah da Ahlulbaitina". A wata ruwayar kuma (aka cika da cewa) "ba za su rabu ba har sai sun iske ni a bakin tafki, to ku kula da yadda za ku rike su a bayana( )".
Ya kara da cewa: "Ibn Hajar ya fada cikin Sawa'ikul Muhrika cewa: "Annabi (s.a.w.a) ya ambaci Alkur'ani da zuriyarsa da cewa "Nauyaya Biyu" ne saboda nauyin dukkan wani mutum shi ne abu mafi muhimmanci a gare shi, kuma wadannan guda biyu haka suke. Domin kuwa kowane daga cikinsu taska ce ta ilmummukan addini da sirrorin hankali irin na shari'a, domin haka ne ma aka kwadaitar da koyi da su. Wani kaulin kuma ya ce an ambace su da "Nauyaya Biyu" ne domin wajibcin kiyaye hakkokinsu. Sannan kuma wanda kwadaitarwar ta tabbata a gare su, su ne masana Littafin Allah masu riko da sunnar ManzonSa (s.a.w.a), domin su ne wadanda ba su rabuwa da Littafin har zuwa tabki( )".
Allama Shaikh Muhammad Jawad al-Balagi ya nakalto cikin tafsirinsa Ala'u al-Rahman fi tafsiril Kur'an cewa:
"Haka nan ma kamar hadisin Sakalain wanda yake an tabbatar da ingancinsa kamar yadda 'yan'uwanmu Ahlul Sunna suka ambace shi cikin littattafansu suka kawo ruwayarsa daga sahabbai wadanda suka ji shi daga wajen Manzon Allah (s.a.w.a.):
"Ni mai bari muku Nauyaya guda biyu ko kuma halifofi guda biyu, Littafin Allah da zuriyata, Ahlulbaitina, wadanda idan kun yi riko da su ba za ku bata ba har abada, su ba za su rabu da juna ba har sai sun riske ni a bakin tafki".
(1). Imam Ali bn Abi Talib (a.s) (2). Abdullahi bn Abbas.
(3). Abu Zar Giffari (4). Jabir al-Ansari.
(5). Abdullahi bn Umar (6). Hudhaifa bn Usaid.
(7). Zaid bn Arkam. (8). Abdurrahman bn Awf.
(9). Dhamratul Aslami. (10). Amir bn Laili.
(11). Abu Ra'fi'. (12). Abu Huraira.
(13). Abdullah bn Handab (14). Zaid bn Thabit.
(15). Ummu Salama. (16). Ummu Hani.
(17). Khazima bn Thabit. (18). Sahl bn Sa'ad.
(19). Adi bn Hatam. (20). Ukba bn Amir.
(21). Abu Ayyub Ansari. (22). Abu Sai'd al-Khudri.
(23). Abu Shuraih Khuza'i. (24). Abu Kadama Ansari.
(25). Abu Laili. (26). Abu Haitham bn Al-Tayhan.

Allama al-Balagi ya ci gaba da cewa: Wadannan su ne muka riga muka ambaci sunayensu bayan Ummu Hani. Kowannensu ya ruwaito shi, shi kadai, kamar wadanda suka gabace shi, sun tsaya a dandalin Kufa tare da mutum bakwai Kuraishawa, suka tabbatar da cewa sun ji wannan hadisi daga Manzon Allah (s.a.w.a.), adadinsu kuwa shi ne talatin da uku.
Kuma abu Nu'aim Al-Isfahani ya ruwaito shi cikin littafin Munkabatu al-Mudahharin da isnadi daga Jabir bn Mad'am da kuma wani isnadin daga Anas bn Malik da Al-Barra'u bn Azib, haka nan Muwaffak bn Ahmad ya ruwaito shi daga Amr bn al-As.
Da wuya a sami wani littafin hadisi babba ko karami ko littafin falaloli da Ahlussunna suka rubuta wanda bai kawo wannan hadisin ba, daga farkon wadanda suka kawo hadisin daga hadda da kuma zukatan mahaddata har zuwa takardun malaman hadisi. Kuma bai gushe ba ana ruwaito shi daga sahabbai guda ko masu yawa. Ta yiwu ma a ruwaito shi daga sama da sahabbai ashirin a littafi guda, ko dai a game kamar yadda ya zo cikin littafin Sawa'ikul Muhrika, ko kuma da isnadi rarrabe kamar yadda ya zo cikin littattafan al-Sakhawi da Suyudi da Samhudi da dai sauransu".
Sannan sai ya ce: "Malaman Imamiyya sun ruwaito shi cikin litattafan-su da isnadinsu masu maimaita juna daga Imam Bakir, Ridha da Kazim da Sadik (a.s.) daga iyayensu (a.s.) daga Manzon Allah (s.a.w.a.) da kuma wadansu isnadan na daban daga Amirul Muminina (a.s) da Umar da Ubayyu da Jabir da Abu Sa'id da Zaid bn Arkam da Zaid bn Thabit da Huzaifa bn Usaid da Abu Huraira da sauransu, dukkanninsu sun ji daga Manzon Allah (s.a.w.a.) ( ).
A cikin Musnad na Ahmad bn Hambal, ya ruwaito ta hanyar Abi Sa'id al-Khudri daga Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa: "Ni na kusanta da a kira ni in amsa, ni kuma mai barin nauyayan abubuwa ne guda biyu tare da ku, Littafin Allah Mai Girma da Daukaka da kuma Ahlulbaitna, shi Littafin Allah igiya ce da aka sako daga sama zuwa kasa. Kuma lalle Mai Tausasawa Masani, Ya ba ni labarin cewa ba za su taba rabuwa da juna ba har sai sun iske ni a bakin tafki, don haka ku kula da yadda za ku rike su a bayana( )".
Haka nan kuma idan muka duba za mu ga kusan dukkan maruwaita sun ruwaito wannan hadisi da ke gwama Ahlulbaiti (a.s) da Littafin Allah Mai Tsarki. Daga wannan ne musulmi za su fahimci cewa Ahlulbaiti (a.s) su ne makoma baicin Littafin Allah kuma su ne aka bar wa amanar Littafin har su isa ga tabki.

 
2- Hadisus Safina (Hadisin Jirgin Ruwa):
Yayin da Hadisus Sakalain yake gwama Ahlulbaiti (a.s) da Alkur'ani waje guda domin nauyin da aka dora musu na bayyana Alkur'anin da kwaranye boyayyun abubuwansa da asirorinsa da abubuwan da ke kewaye da shi, to wannan hadisi na Safina kuwa yana bayyana wa al'umma ne cewa su Ahlulbaiti (a.s) su ne jirgin tsira, kuma hanyar kubutar wannan al'umma bayan Manzon Allah (s.a.w.a.). Domin haka, lallai rashin riskan wannan jirgin da rashin hawansa, zai ja wadanda suka ki shiga jirgin zuwa ga nutsewa da halaka. Domin kin binsu, kin bin ja-gora zuwa gabar shiriya da tsira ne.
Al-Shibrawi al-Shafi'i ya nakalto daga Rafi Maulan Abu Zarri, ya ce:
"(Wata rana) Abu Zar (r.a.) ya hau dokin kofar Ka'aba, ya kama marikin kofar ya dogara da shi, sai ya ce: "Ya ku mutane, wanda ya sanni to ya sanni, wanda kuma bai sanni ba, to ni ne Abu Zar, na ji Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:
"Ahlulbaitina tamkar jirgin Nuhu suke, wanda ya hau shi ya tsira wanda kuwa ya ki hawa ya fada wuta".
Na kuma ji Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa: "Ku sanya Alayena (a gareku) matsayin da kai yake da shi a jiki, kuma matsayin idanu ga kai. Domin shi jiki baya shiryuwa sai da kai, shi kuma kai ba ya shiryuwa sai da idanu( )".
Abu Nu'aim( ) ya ruwaito ta hanyar Sa'id bn Jubair daga Ibn Abbas, ya ce: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Misalin Ahlulbaitina a cikinku, tamkar jirgin (Annabi) Nuhu ne, wanda ya hau shi ya tsira, wanda kuwa ya ki hawa ya nutse (ya halaka) ( )".
An ruwaito ta hanyar Anas bn Malik, cewa, ya ce Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Abin sani kawai shi ne cewa, misalin Ahlulbaitina a cikinku, kamar jirgin Nuhu ne, wanda ya hau shi ya tsira, wanda kuwa ya ki hawansa ya halaka( )".
Suyudi ma ya ruwaito wannan hadisin cikin littafinsa Durrul Mansur karkashin tafsirin fadin Allah Madauka-kin Sarki cewa:
(وإذ قُلنَا آدخُلوا هَذِه القَرْيةَ فَكُلُوا مِنْهَا حَيْثُ شِئْتُمْ رَغَداً وادْخُلُوا البابَ سُجَّداً وقُولوُا حِطَّة نَغْفِر لكُمْ خَطاياكُمْ)
"Kuma lokacin da Muka ce: "Ku shiga wannan alkarya, sa'an nan ku ci daga gare ta, inda kuka so, bisa wadata, kuma ku shiga kofa kuna masu tawali'u, kuma ku ce: "Kayar da zunubai" Mu gafarta muku laifukanku".
Inda ya ce: "Ibn Abi Shaiba ya fitar da hadisi daga Aliyu bn Abi Talib (a.s.) ya ce:
"Abin sani dai, misalinmu (Ahlulbaiti) cikin wannan al'umma kamar misalin jirgin Nuhu ne, kuma kamar Kofar Yafuwa (Hidda) ce( )".
Al-Muttaki ya ruwaito shi cikin littafin Kanzul Ummal (juzu'i na 6 shafi na 216) cewa, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Misalin Ahlulbaitina a cikinku, tamkar jirgin Nuhu ne, wanda ya hau shi ya tsira, wanda kuwa ya ki hawansa ya halaka, kuma tamkar kofar Hidda ne ta Bani Isra'ila". Sannan ya ce Dabarani ma ya ruwaito wannan hadisi daga Abu Zarri( ).

 
3- Hadisin Aminta Daga Sassabawa:
A cikin wannan hadisin, Manzon Allah (s.a.w.a.) yana bayyana rawar da Ahlulbaiti (a.s) ke takawa a fagen akida da siyasa. Domin mafi hadarin abin da yake samun al'umma shi ne rarraba da sabawa cikin ra'ayi da akida da kuma fuskantarwa ta siyasa. Don haka ne ya sa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance yana tsoratar da al'ummarsa wannan fitinar, ya kasance yana tsare-tsare saboda hadin kanta da riko da juna ta bangaren tunani da siyasa. Kana kuma yake fuskantar da al'ummar tasa zuwa ga lizimta da riko da Ahlulbaitinsa da komawa gare su. A saboda hakan ne kuma, ya siffanta su da cewa su masu lizimtar Alkur'ani da kiransa ne, kuma ba za su rabu da juna ba har ranar tashin kiyama. Ya kuma siffanta su da cewa su jirgin tsira ne, kuma kofar yafuwar zunubbai. To a nan kuma yana siffanta su ne da cewa su ne mattara, kuma su ne madogara mai hada kan wannan al'umma ta musulmi ne, da kuma cewa riko da su da rayuwa bisa tafarkinsu lamuni ne daga rarraba da sabawa.
Al-Dabarani ya kawo hadisi daga Ibn Abbas (r.a.) cew, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Taurari aminci ne ga mazauna kasa daga nutsewa (halaka), Ahlulbaitina kuwa aminci ne ga mazauna kasa daga sassabawa (rarrabuwa)( )".
Muhibbuddin Dabari ya ruwaito daga Aliyu (a.s.) yana cewa: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Taurari aminci ne ga mazowa sama, idan taurari suka tafi, mazowa sama sai su tafi, Ahlulbaitina kuwa aminci ne ga mazowa kasa, idan Ahlulbaitina sun tafi, mazowa kasa sai su tafi".
Sai al-Dabarani ya ce: "Ahmad bn Hambal ya ruwaito wannan hadisi cikin al-Manakib( ).

 
4- Hadisul Kisa'i (Hadisin Mayafi):
Hadisin Mayafi shi ne hadisin da ya zo daga Manzon Allah (s.a.w.a.) dangane da Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (a.s.) yayin da Ayar Tsarkakewa ta sauka. Mun riga da dai mun gabatar da wannan hadisi kuma mun yi magana a kan shi tare da kawo ra'ayuyyukan wasu malaman tafsiri, da kuma ruwayoyin da suka yi batun wadannan wadanda aka tsarkake a cikin babin "Ahlulbaiti (a.s) Cikin Alkur'ani". To amma a nan za mu kawo wasu ruwayoyi ne daban domin karfafa wannan fikirar da kuma kafa wannan manufar da Manzon Allah (s.a.w.a.) yake da ita wajen yin hakan (wato lullube su da mayafinsa da kuma yi musu addu'a).
Hanyoyin da wannan hadisi ya zo suna da yawan gaske cikin littattafan hadisi da ruwaya da tafsiri, to amma za mu ambaci wasu daga cikinsu ne kawai: "Dangane da abin da aka ruwaito daga Ummu Salama, matar Annabi (s.a.w.a), Imam Ahmad ya ruwaito shi cikin Musnad dinsa har ya zuwa ga Ummu Salama, inda ta ce: "Wata rana Manzon Allah (s.a.w.a.) yana dakina, sai wani hadimi ya zo ya ce: 'Aliyu da Fadima na nan bakin kofa', sai ta ce: sai Annabi (s.a.w.a) ya ce da ni: "Ki tashi ki kauce wa Ahlulbaitina". "Sai na tashi na kauce gefe guda. Sai Aliyu da Fadima da Hasan da Husaini suka shigo. A yayin nan Hasan da Husaini suna yara kanana, sai Annabi (s.a.w.a) ya dauke su ya dora su a kan cinyarsa, ya sumbace su, ya rungume Aliyu da hannunsa, Fadima kuma da dayan, sannan ya lullube su da wani bakin mayafi, ya ce: "Ya Allah! Zuwa gare Ka ba zuwa wuta ba, ni da Ahlulbaitina". Sai Ummu Salama ta ce: 'Da ni ya Manzon Allah', sai ya ce: "Na'am da ke( )".
Al-Wahidi ya ruwaito cikin littafinsa Asbabun Nuzul marfu'i ta hanyar Ummu Salama (r.a.) ta ce: (Wata rana Annabi (s.a.w.a) ya kasance a dakinta sai Fadima (a.s.) ta zo da tukunya da wani abinci na alkama a ciki, sai ta shiga da shi. Sai yace da ita: "Ki kira mini mijinki da 'ya'yanki biyu". Sai Ali da Hasan da Husaini suka zo, suka shiga suka zauna suna cin abincin, Annabi (s.a.w.a) kuma yana zaune a kan wani benci, a kan wani mayafi wanda aka saka a Khaibara. Sai Ummu Salama ta ce: Ni kuma ina cikin dakin, kusa da su, sai Annabi (s.a.w.a) ya kama mayafin ya lullube su da shi, sannan ya ce: "Ya Allah! Mutanen gidana, kebantattuna (kenan), to Ka tafiyar da kazanta daga gare su Ka tsarkake su, tsarkakewa".
Sai ta ce: Sai na shigar da kaina, na ce: "Ni ma ina tare da ku, Ya Manzon Allah". Sai ya ce: "Ke kina tare da alheri, ke kina tare da alheri". Sai Allah Mai girma da Daukaka Ya saukar da ayar: (إنَّما يُريدُ الله لِيُذْهِبَ عنْكُمُ الرِّجْسَ أهْلَ البَيْتِ ويُطهِّرَكُمْ تَطْهيراً )
"...Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa( )". (Surar Ahzabi, 33:33)

 
5- Hadisin Soyayya:
Mun riga da mun yi magana kan Hadisin Soyayya wajen tafsirin Ayar Soyayya, kuma mun ambaci wasu masu ruwaya da suka ruwaito shi da kuma daga wajen wadanda suka ruwaito shi. A nan za mu sake ambaton hadisin ta hanyoyin daban ne, kuma zai kasance mai amfani mu ambaci sashin abin da ya taho daga Annabi (s.a.w.a) a kan son Ahlulbaiti (a.s) da kaunarsu a wasu ruwayoyin na daban.
(Imam Ahmad da Dabarani duk sun ruwaito daga Ibn Abbas (r.a.) ya ce: "Yayin da Ayar Soyayya, wato "Ka ce: "Bana tambayarku wani lada a kansa face dai soyayya ga makusanta", ta sauka, sai mutane suka ce: Ya Manzon Allah, su wane ne makusanta wadanda soyay-yarsu ta wajaba a kanmu?, sai yace:
"Aliyu da Fadima da 'ya'yansu guda biyu".
Al-Bazzaz da Dabarani sun ruwaito cewa Hasan dan Aliyu (a.s.) yayi huduba wata rana yana cewa: "Wanda ya sanni to ya sanni, wanda kuwa bai sanni ba, to ni ne Hasan dan Muhammadu (s.a.w.a). Ni ne dan Mai albishir, ni ne dan Mai gargadi, ni ne dan mutanen gida wadanda Allah Ya farlanta son su a kan kowane musulmi, Ya kuma saukar a kansu (da ayar), "Ka ce: Ba ni tambayar ku wani lada a kansa face dai soyayya ga makusanta. Kuma wanda ya aikata wani abu mai kyau,
Za mu kara masa kyau a cikinsa". To aikata kyawawan shi ne soyayyarmu, Ahlulbaiti( )".
Al-Saddi ya ruwaito daga Abi Malik daga ibn Abbas (r.a.) dangane da fadin Allah Madaukaki cewa: "...wanda ya aikata wani abu mai kyau, Za mu kara masa kyau a cikinsa".
Al-Saddi ya ruwaito daga Abi Malik daga ibn Abbas (r.a.) dangane da fadin Allah Madaukaki cewa: "...wanda ya aikata wani abu mai kyau, Za mu kara masa kyau a cikinsa".
Inda ya ce: "Soyayyar ta Alayen Muhammadu (s.a.w.a) ce( )".
Hadisan da suka zo game da so da kaunar Ahlulbaiti (a.s) da kuma yin musu da'a da lizimtarsu, ba za su kirgu ba cikin wannan dan karamin littafi, sai dai mun zabi sashi ne daga cikinsu kawai, don kuwa kowanne daya daga cikinsu (Ahlulbaiti) (a.s.) rana ce mai haske a cikin littattafan hadisi da ruwayoyi.
To amma domin a kara arzurta mai karatu da kara karfafa abin da zai kara masa sanin Ahlulbaiti (a.s) da kuma karfafa dangantaka da su, da mai da shi mai ta'allaka da su, mai rayuwa bisa tafarkinsu, don ya samu nasarar samun cetonsu, bari mu sake ambaton wasu daga cikin hadisan da suka zo game da su: (Dabarani ya fitar da hadisi cikin littafin al-Awsad daga ibn Hajar (r.a.) cewa; "Karshen abin da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya furta shi ne: "Ku wakilce ni cikin Ahlulbaitina( )").
(Dabarani ya fitar da hadisi cikin littafin Al-Awsad daga Jabir bn Abdullah (r.a.) ya ce: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi mana huduba, na ji yana cewa: "Ya ku mutane! (Duk) wanda ya fusata mu, mu Ahlulbaiti, Allah Zai tashe shi ranar kiyama yana bayahude( )".
(Muslim da Tirmizi da Nasa'i duka sun ruwaito daga Zaid bn Arkam cewa, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Ina tunatar da ku Allah game da Ahlulbaitina( )".
Alkhatib ya fitar a cikin littafin Tarihinsa daga Aliyu (r.a.) cewa: Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Cetona ga al'ummata, na ga wanda ya so Ahlulbaitina( )".
 
6- Wasu Ruwayoyi Na Daban
Kamar dai yadda muka bayyana, hadisai da ruwayoyi daga Manzon Allah (s.a.w.a.) game da Ahlulbaitinsa (a.s.) suna da yawan gaske, kuma ba za su kidayu ba a wannan karamin littafin. Malamai da masu hadisi sun kebance musu litattafai, ko kuma fasulla a littattafan hadisai, ko kuma sun ambata a wuraren da suka dace cikin litattafan tafsiri da ruwaya. Ga kadan daga ciki: "Mu Ahlulbaiti ba a gwada mu da kowa( )".
A cikin wannan hadisin Manzon Allah (s.a.w.a.) yana bayyana mukamin Ahlulbaiti (a.s) ne, da kuma matsa-yinsu madayanci, domin ya sanar da al'umma mahal-linsu, ya kuma shiryar da ita zuwa ga riko da su da lizimtar hanyar su a bayansa, domin a auna su da wasu wadanda ba su ba, don a gani.
A cikin wani hadisi na daban kuma, Manzon Allah (s.a.w.a.) yana magana ne kan Ahlulbaitisa (a.s.), inda yake cewa: "Mu Ahlulbaiti, Allah Ya zaba mana lahira bisa ga duniya, kuma lalle Ahlulbaitina za a nuna musu son kai da tsanani da kora cikin garuruwa, har wasu mutane za su zo ta nan - sai ya yi nuni da hannunsa ta gabas - ma'abutan bakar tuta, za su tambayi hakki, ba za a ba su ba, za su yi yaki kuma su yi nasara. Za a ba su abin da suka so kuma ba za su karbe shi ba har su mika ta (tutar) ga wani mutum daga Ahlulbaitina, har sai ya cika duniya da adalci kamar yadda aka cika ta da zalunci. To duk wanda ya riski wannan ya taho musu ko da da jan ciki ne a kan kankara( )".
(Dailami ya kawo hadisi daga Abu Sa'id (r.a.) cewa: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Fushin Allah ya tsananta kan wanda ya cutar da ni dangane da Ahlulbaitina( )".
(Daga Aliyu (r.a.) ya ce: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Ku yi wa 'ya'yanku tarbiyya kan halaye guda uku: son Annabinku da son Ahlulbaitinsa da kuma karatun Alkur'ani, domin mahaddatan Alkur'ani na cikin inuwar Allah a ranar da babu wata inuwa sai inuwarSa, tare da AnnabawanSa da ZababbunSa( )").
(Dabarani ya ruwaito daga Ibn Abbas (r.a.) yana cewa: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Digadigan bawa ba za su gushe ba har sai an tambaye shi abubuwa hudu: Kan rayuwarsa, yadda ya karar da ita; da jikinsa, yadda ya tsufar da shi, da dukiyarsa, yadda ya kashe ta da inda ya same ta da kuma soyayyarmu, Ahlulbaiti( )").
A wata ruwayar kuma, Manzon Allah (s.a.w.a.) yana shiryar da al'ummarsa zuwa ga Ahlulbaitinsa, yana kuma bayyana matsayinsu na ilmi, da kuma fuskantar da al'ummar zuwa gare su yayin da fitinu suka tsananta, ra'ayoyi kuma suka sassaba. Yana gwama su da Littafin Allah, domin su ne malamai masu bayyana abin da Alkur'ani ya kunsa, masana hakikaninsa da abubuwan da ya tattara.
(Dabarani ya fitar da hadisi daga Al-Mudallabi bn Abdullahi bn Handabi daga babansa, ya ce: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi mana huduba a Juhfa, ya ce: "Ashe ban fi ku cancanta ba a kan kanku", sai suka ce: "Haka nan ne Ya Manzon Allah". Sai ya ce: "To ni mai tambayar ku ne kan abubuwa biyu: kan Alkur'ani da Ahlulbaitina( )").