Hakkin Harshe

MARUBUCI: Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
Hakkin Harshe
Imam Zainul-abidin (a.s) yana cewa: "Kuma amma hakkin harshe; shi ne ka kare shi daga mummunar Magana ta alfahasha -da batsa-, da saba masa alheri, da barin maganar da ba ta da wani amfani, da kyautata wa mutane, da kyautata zance game da su, da siffanta shi da ladubba, da sanya masa takunkumi sai inda yake akwai bukata, da amfani ga duniya da addini, da kuma kame shi daga shiga dan zance mai karancin amfani, wanda ba kasafai ake kubuta daga sharrinsa ba, tare da karancin amfaninsa, kuma ya kasance bayan duban hankali da kuma dalili a kansa. Kuma adon mai hankali a cikin hankalinsa ya doru bisa kyakkyawar dabi'arsa ne a cikin harshensa. Sannan babu dubara babu karfi sai da Allah".
Harshe kamar yadda bayani zai zo game da sauran gabobi shi ma kamar ji da gani, da hannu, da ciki, da kafa, da farji ne, yana da hakki a kiyaye shi kamar sauran, bai halatta mu yi sabo da su ba, shari'a ta dora mana neman duniya da lahira da su ne, kuma hanyoyi ne na samu da neman Ilimi da sauran ni'imomin Allah a wannan duniya da kuma makoma. Sai mu yi amfani da gani, da ji, da tafiya, wajan neman Ilimi ko neman halal, mu ki amfani da su wurin haram.
Jiki dukkaninsa yana da wadannan dokokin ne, bai halatta a zalunci wani bagare nasa ba, akwai abin da mutane da yawa sun shafa'a daga gareshi. Lalaci yana daga hanyoyin da mutane suke zaluntar kawukansu, amma da yawan mutane sun gafala da shi. Wani lokaci ana zaluntar kai ne da zaman banza har ma kana iya ganin mutum ya shantake yana ta barci wai hutawa yake yi saboda lalacewa alhali bai yi aikin komai ba. Wani kuwa yana alfahari ne da cewa babansa yana da dukiya mai yawa, sai ya zalunci kansa ba zai je ya nemi abin da zai mutunta kansa ba.
Harshe shi ne mafi hadarin abu da ake iya sabo da shi ko aikata lada cikin sauki, domin amfani da shi yana da sauki, idan neman zunubi ne ya isa ka yi giba ko radar wani sai a samu zunubi mai girma, har ma wasu ruwayoyi suna cewa "Giba -yi da wani- ta fi zina muni" , amma cikin sauki a cikin wurin zama daya mutum yana iya yin giba goma. Don haka ya zama wajibi a kare shi daga maganganu munana kamar karya, da hada husuma, da giba, da annamimanci
Haka nan aikin lada da alheri yake da sauki ga harshe, yin salati daya a wurin zama ya isa ya bude wasu kofofin arziki, kuma fadin magana da zata faranta wa wani rai ya isa ya samar da ladan sadaka, ya zo a ruwayoyi cewa harshe mai dadi da kalma ta alheri sadaka ne . Kalma mai dadi da harshe mai hada sulhu tsakanin mutane shi ne wanda Allah ya ke so, kuma shari'a ta karfafa yin hakan musamman tsakanin ma'aurata da abokan zaman tare a matsayin al'umma.
Wasu mutane sun kware wajen kisan mummuke ga wasu da harsunansu saboda kiyayya imma dai mai dalili ko maras dalili, hakika na dandani dacin yi mana hassada har zuwa wannan lokaci alhalin ba mu dauki kanmu a matsayin wasu fiyayyu ba. Jafa'in wasu mutane a kanmu ya kai ga yi mana kisan mummuke da harshe, sai dai Allah yana nan a wurin hisabi. Yin kisa da harshe ta hanyar bata sunan mutane da lalata kimarsu da mutunci, da rufe ido daga kyawawansu, da yin sharri a kansu, da kuma ba wa wasu yabon aikin da suka yi wani abu ne da muka dadani dacinsa. Sai dai da zarar mun tuna da abin da aka yi wa tsarkakan bayi sai mu ga wannan ba komai ba ne don an yi wa irinmu masu laifi da zunubai wurin Allah (s.w.t).
Mumini ba ya kisan mumini da harshensa, ba ya cin mutuncinsa, ba ya tona sirrinsa, mumini yana kare sirrin mumini ne a duk inda yake, yana kuma yaba masa, yana kuma toshe munanansa, yana yi masa nasiha a boye ne. Ruwaya ta zo cewa: "Mumini madubin mumini ne" , idan kuwa ya kasance ke nan bai zama madubin muminai ba, to lallai ba mumini ba ne.
Kisan da ake iya yi wa mutuncin mutum da harshe ya fi muni fiye da kisan da ake iya yi masa da wuka ko harsashi, da yawa wasu mutane suka cutar da wasunsu saboda hassada, ko keta da mugunta, ko don suna da sabanin akida ko na siyasa. Shia'anci yana daga cikin mazhabin da tun lokacin Manzon Allah da alayensa Ahlul-baiti (a.s) ake yi masa kisan mummuke da harsuna, wannan kuwa ya kai ga salwanta rayuka da dukiyoyi da Allah ne kawai zai yi hisabi a kai.
Cikin sauki harshe yana iya shafe ladan mace na biyayyar miji, ko ya tarwatsa aure zaka samu irin wannan a al'adu yayin da wasu lokutan wasu mata sukan gaya wa mazajensu "Me ka taba yi mini" wato duk alherinsa maimakon godiya sai su kushe shi da butulci. Ko kuma wasu matan idan suna magana da mazajensu kamar suna magana da wani azzalumi babu wata kalma ko magana mai dadi. Kamar yadda akan samu shigen irin wannan rashin kimantawa da girmama mata daga wasu mazaje, sai su yi zagi, su tsine, su ci mutuncin matansu, wadannan nau'o'in mata da maza dukkaninsu sun jahilci rayuwa da manufa da hadafin yin aurensu ne.
Harshe yana da hadarin da zai iya tarwatsa gari daya ko kasa guda, jita-jita daya takan iya fin bom din kare dangi da makamin Nukiliya hadari, sau da yawa masu kin kasashen musulmi da masu ganin hada husuma tsakanin musulmi da 'yan'uwansu na zaman kasa daya sukan yi amfani da harshe da yada jita-jita don ganin sun kawo husuma da yaki. Kuma sau da yawa irin wannan ya faru a kasashenmu da biranenmu ya jawo kashe dubunnan mutane! mu sani babu wani abu da ya fi harshe santsi da hadari don haka sai a kiyaye shi.
Hadarin harshe ya sanya shi ya kasance iyaka ce tsakanin kafirci da imani, da yin isgili da addini, ko wani abu mai tsarki na addini kamar annabi, ko littafin Allah, ko kiyayya da wasiyyan annabawa waliyyan bayin Allah, ko wani abu na tilas na larurar addini kawai, ya isa ya jefa mutum cikin kafirci ya tunkuda shi wuta. Haka nan da yin kalma daya ta imani ba tare da ayyukan alheri ba, kamar dai wanda ya musulunta a lokacin annabi (s.a.w) kuma ga shi bai taba salla ko wani aiki ba na ibada, sai kuma ya yi shahada nan take, amma wannan sai ya wajabta masa aljanna har abada.
Sai dai duk da haka Allah yana karba ne idan ya kasance daga masu takawa , domin Fir'auna ya yi kalmar shahada yayin da ya ga halaka sai ya yi kalmar shahada amma Allah bai karba ba, domin ya yi ta ne domin ya kubuta daga halaka ba don imani da takawa ba. Amma wanda ya yi ta da takawa da imani ya fadi kalma mai sauki a kan harshe, mai nauyi a awon lada to hakika shi zai rabauta har abada.
Idan mun duba wannan magana mai tsarki da daraja ta Imam Zainul-abidin (a.s), zamu ga yana cewa: "Kuma amma hakkin harshe; shi ne ka kare shi daga mummunar magana, da saba masa alheri", da mutane sun yi amfani da wannan wasiyya da an samu karancin bakin ciki a duniya, da cututtukan rai da yake da mun mutane da aka fi sani da yawan fushi ya yi karanci, sai dai dan Adam bai shirya wa kiyaye hakan ba saboda jahilcinsa da son ransa. Babban abin da ake nema daga kowane mutum a nan shi ne ya kiyaye kuma ya saba wa harshensa da fadin alheri, don haka ne duk maganar da zai yi to dole ya fara tattauna ta tukun sannan sai ya furta, idan ba haka ba kuskurensa da nadamarsa zasu yawaita.
Sannan da yake cewa: "da barin maganar da ba ta da wani amfani, da kyautata wa mutane, da kyautata zance game da su, da siffanta shi da ladubba, da sanya masa takunkumi sai inda yake akwai bukata, da amfani ga duniya da addini, da kuma kame shi daga shiga dan zance mai karancin amfani, wanda ba kasafai ake kubuta daga sharrinsa ba, tare da karancin amfaninsa, kuma ya kasance bayan duban hankali da kuma dalili a kansa. Kuma adon mai hankali a cikin hankalinsa ya doru bisa kyakkyawar dabi'arsa ne a cikin harshensa", yana nuni ga cewa kamalar harshe da karanta magana ne, karancin magana yana nuna hankalin mutum ne, don haka ne ya zo a cikin hikima daga abin da Imam Ali (a.s) ya nakalto daga ma'aikin Allah (s.a.w) cewa: "Idan hankali ya cika sai magana ta yi karanci". Mizanul hikima: Muhammad RaiShahari; j 3, s 2052.
Wannan magana mai daraja tana da karfafuwa da hadisai masu kima daga annabin Allah (s.a.w) da kuma ruwayoyin da Ahlul-baiti suka karbo daga gareshi. Imam Ali (a.s) yana cewa: "Harshen mumini yana bayan zuciyarsa, amma zuciyar munafuki tana bayan harshensa". Nahajul-balag: Huduba, j 2, s 93. Wannan kuwa domin mumini idan ya so yin magana sai ya lura da shi, idan alheri ne sai ya fada, idan kuwa sharri ne sai ya fasa. Amma munafuki yana magana da dukkan abin da ya zo wa harshensa ne, ba ruwansa da abin da yake nasa da wanda yake kansa.
Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: "Imanin mutum ba ya daidaituwa har sai ya daidaita zuciyarsa, kuma zuciyarta ba ta daidaituwa har sai ya daidaita harshensa, duk wanda ya zai iya daga cikinku ya hadu da Allah yana mai kubutaccen hannu daga jinin musulmi da dukiyoyinsu, mai kubutaccen harshe to ya yi hakan". A'alamuddin fi sifatil Muminin: Addailami; s 106.
Imam Ali (a.s) yana cewa: "Wanda ya san cewa maganarsa daga iliminsa ne to zai karanta maganarsa sai dai cikin abin da yake akwai ruwansa". Nahajul-balag: Hikima 349.
Mazon Allah (s.a.w) yana cewa: "Wanda ya karanta maganarsa zunubansa zasu yi karanci". Uyunul Hikam wal Mawa'iz: Ali bn Muhammad allaisi, alwasidi, s 448.
Mazon Allah (s.a.w) yana cewa: "Wanda ya karanta maganarsa aibinsa zai boyu". Uyunul Hikam wal Mawa'iz: Ali bn Muhammad allaisi, alwasidi, s 455.
Dogaro da wadannan koyarwa mai kima da daraja zamu ga munin hirar mutane a bakin titi, akwai mutane masu yawa a kasashenmu da suke da dakalin hira na musamman, wannan hirar da ta kasance ta karuwa ko don sadar da zumunci, ko tattauna matsaya ta ilimi, ko wata matsalar al'umma da za a warware da ta yi kyau. Amma sai ta kasance sabanin haka ne in ban da 'yan kadan daga ciki, da yawa irin wadannan wuraren suka kasance wuraren hada husuma, da yi da mutane, da gulma, da annamimanci, da karairayi.
Daya daga cikin masu hikima yana cewa: "A kwai fa'ida dubu bakwai a cikin yin shiru, kuma sun hadu cikin kalmomi bakwai, da kowace kalma akwai dubu a cikinta. Yin shiru ibada ce ba tare da wahala ba, kuma ado ne ba tare da kwalliya ba, kwarjini ne ba tare da mulki ba, katanga ce ba tare da wani garu ba, wadatuwa ne daga kawo uzuri gun mutane, hutun mala'iku masu rubutu ne, sutura ne ga aibobi".
Cibiyar Al'adun Musulunci
www.hikima.org
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Saturday, June 19, 2010