Hajji da Mahajjata

Hajji a Mahangar Addini
"…Kuma Allah yana da hakkin yin hajjin daki a kan mutane ga wanda ya samu ikon tafarki zuwa gare shi…" .
Imam Zainul-abidin (a.s) yana cewa: "Kuma hakkin Hajji shi ne ka san cewa shi zuwa ne ga ubangijinka, gudu ne daga zunubanka, kuma da shi ne za a karbi tubanka, da sauke nauyin wajibi da Allah ya wajabta maka shi a kanka".
Wannan makala tana bayani kan wasu abubuwa da suke ci wa alhazawan kasashenmu tuwo a kwarya, sai dai ba komai ake nufi da ita ba sai neman gyara cikin wannan al'ummar tamu, da fatan zata kasance mai amfanarwa. Allah ya sa mu cikin masu dacewa da biyayyar addininsa sau da kafa.

Mahajjatan Kasarmu
Duk wani musulmi yana son zuwa Hajji saboda girman ladan da yake tattare da shi, sai dai wani abu da ya kamata mu sani shi ne zuwa Hajji ba ya zama wajibi sai ga wanda yake da halin hakan. Don haka Allah (s.w.t) bai yarda wani ya kallafa wa kansa ba alhalin ba shi da halin zuwa. Kuma Hajji da Umara suna zama wajibi ne kawai sau daya a rayuwa, don haka duk wanda ya je sau daya, to ya sauke nauyin wajabcin da yake kansa.
Hajji ba gasa ba ce, ba alfahari ba ne, shi ibada ce daga cikin ibadoji masu girma a musulunci, don haka ba wuri ne na shakatawa ba. Don haka halayyar da wasu suke nunawa ta yin Umara kowace shekara don kawai ta zama mahadar hira bai dace ba, da wannan umarar ko hajjin mahadar shakatawa da hirar duniya gwara ba wa talakawan makota, ko makusanta mara hali wannan dukiyar shi ya fiye masa lada.
Da zai yi amfani da ita don gyara titin layinsu, ko biyan kudin makarantar wasu yaran da iyayensu ba su da hali, ko taimaka wa marasa hali da talakawa don dinkin tufafin da zasu sanya, ko taimakon buga wani littafi da zai taimaka wa al'umma sanin yakamata, ko taimaka wa marasa lafiya, duk irin wannan ya fiye masa lada wurin Allah madaukaki.
Sai ka ga mai kudi ga yana zuwa irin wannan umarar duk shekara alhali ga makotansa cikin yunwa ko takalmi ba sa iya saya musu! Ga dan'uwansa ma ba shi da abincin da zai ci a wuni, amma ya tafi Umara ko kwanon hatsi ba ya iya ba shi ba, tare da kuwa ya san halin da yake ciki!. Ga makarantu ba ya iya taimakawa wurin gina su.
Sai dai ba muna cewa kada ya tafi Umara ba, amma da zai hakura da wasu shekaru ta yadda duk shekara biyu ya je, amma shekarar da bai je ba sai ya ware dukiyar don wani alheri da ita, da ya fiye masa lada wurin Allah. Domin ba mumini ba ne wanda yake koshe makocinsa yana cikin yunwa! Ke nan ibadarsa tana da matsala matukar wannan imanin bai tabbata ba!.
Haka nan da zai raya ilimi ta hanyar buga wani littafin da zai shiga hannun al'umma don sanin abin da ya kamata na rayuwarsu ko ibadarsu, ko ya biya kudin makarantar wasu yara ko samari don su zama masu ilimi a cikin al'umma daidai yake da raya su, wanda kuwa ya raya mutum daya kamar ya raya duk al'umma ne.
Maniyyancin Nijeriya yana fara ganin tasku tun daga kasarsa, ba na tsammanin akwai kasar da maniyyaci yake ganin tasku irin Nijeriya, abin da yake sananne a kasashe duk wani mahajjaci ya san ranar da zai tashi, da ranar da zai dawo, da masaukinsa, cikin kima da daraja da mutuntawa. Amma maniyyacin Nijeriya kullum sai an yi maganar an samu matsala, kuma idan za a yi shekara 1000 wannan matsalar zata yi ta maimaituwa wannan kuwa yana nuna karancin hankali da tunani ma'aikatan wannan hukumar.
Rashin tsari da son duniya, da cin hanci da rashawa, da karancin tsoron Allah da suka yi kamari cikin wannan al'umma ya sanya wasu ma suna iya rasa tafiya saboda an maye gurbinsu da wasu. Sannan ga jinkirin daukar maniyyata ta yadda zaka samu wasu suna kwana a sansanin alhazai da filin jirgi suna jiran tsammanin isowar jirgin da zai kwashe su zuwa kasar Saudiyya!. Hada da karancin kula da lafiyar wurin da abin da maniyyata zasu ci a kwanakin da zasu yi suna jira, da rashin sanin takamaimai halin da suke ciki! Da sauran abubuwa da suke nuna mu'amala da mutum irin ta dabba! da rashin sanin kimar dan Adam!. Wani lokaci ma kakan samu maniyyaci ya taso daga wata jahar mai nisa don zuwa Hajji amma sai Hukumar alhazai ta yi watsi da su suna kwana a fili!.
Don haka dan Nijeriya yana ganin mugun kaskanci da wulakanci tun daga kasarsa kafin ya isa Saudiyya, don haka ne ma ita hukumar Saudiyya take ganin sa kamar wani dabba ko da kuwa shugaba ne a Nijeriya. Domin wanda ya ki mutunta al'ummarsa to kansa ya wulakanta, kuma babu yadda wata al'umma zata ga mutuncinsa!. Mafi muni shi ne girman kan tsiya da yake kan masu alhakin ayyukan Nijeriya ta yadda duk wani laifi da suka yi ba zasu zo su kaskan da kansu gaban mutane su ba su hakuri ba, sai dai ka samu wani uzuri maras amfani, kuma idan wani ya ce bai yarda ba, yanzu ka ga an nuna masa laifn Allah ne! wai haka Allah ya kaddara! Sai ya koma shi ne mai laifi saboda yana neman hakkinsa!. Wani lokaci kuma idan suka san sun yi mugun laifi ga maniyyata, to ba zaka sake ganin wani a cikinsu ba!.
Sai al'ummarmu ta rika rayuwa da jagoranci da ya yi kama da na mahaukatan dabbobin jeji da ba sa iya daukar darasin kurakuran baya, ta yadda duk shekara sai a samu wasu matsaloli suna ta maimaituwa!. Wani lokacin rashin imanin ya kai ga masu kula da hukumar alhazai sai su yi gaba su bar maniyyata barkatai a filin Allah babu tunaninsu, babu jin cewa su tsaya su saukin nauyin wadannan bayin Allah, babu tausayi ko kwarzane!. Sannan bai san yadda zai ga ofishin wanda ake cewa Amirul Hajji ba, balle ya kai kara. Kuma da zai sani shi kansa ba zai doshi wurin don kai kara ba, domin babu wani Amirul Hajji da yake da lokacin maniyyaci, sai dai ya yi Allah ya isa!. Ko kuma a sanya wani mai katon nadi wai shi ne Amirul Hajji, sai ya kasance ba ya iya shiga cikin jama'a balle ma ya san me suke ciki!.
Wani lokaci kuwa wasu jahohin suna fama da masu dakile aikin hajjin ne saboda kawai bambancin addini da kabilanci! Sai ya zama ana rayuwar yaudarar da aka kira ta kasa daya, ko jaha daya, al'umma daya, alhalin idan da wani bangare zasu kashe wani bangare to ba ma ladabtarwa ba, hatta da wanda zai ba su rashin gaskiya tun daga sama har kasa sai ka rasa! Wannan yana faruwa musamman a yankin Jos da ake hawa kan musulmi da kisa na ban mamaki ana gani amma sai ka ga bakin mugun mai mulki maras imani kan al'ummarsa ya kasa fitowa ko da ya soki abin da ake yi wa musulmi! Yana ma iya ba su rashin gaskiya kai tsaye duniya tana ji, su kuma ba su da wani mai magana da yawunsu!.
Ta yiwu wani ya ga cewa ana samun kurakurai ne saboda wani lokaci ana canja ma'aikatan hukumar alhazai duk shekara ko wasu shekaru? Sai in ce masa: Wannan yana nuna cewa babu masu hankali a kasar ke nan, domin ya kamata komai ya zama a rubuce ne a takarda ta yadda idan wani ya zo aikin a yau, zai iya daukar fayalolin baya ya ga matsalar da aka samu duk shekaru da suka gabata baya.
Ta yiwu wani ya yi maganar cewa wani lokacin jirage suna kwashe masu tsada kafin masu arha? Wannan ma sai mu ce: Ana iya yarjejeniya da kamfani ta yadda komai arha idan ya saba wannan yarjejeniya ya ki zuwa to zai fuskanci tarar da zai yi nadamar sabawa, kuma ba zai sake sha'awar yin wulakanci ba!.
Sannan ba don mummunan rashin tsari da cin amana ya yi yawa ba, da maniyyaci yana iya bayar da kudinsa kafin shekarar Hajji ko shekaru masu yawa a baya, ta yadda kafin lokacin Hajji da shekara an san wadanda zasu je!.
Yi wa maniyyata samina kan ayyukan Hajji ta wasu 'yan kwanaki a yankunansu ko a wata cibiya ta musamman kafin zuwa Hajji wani lamari muhimmi a yayin da suka shirya wa zuwa Hajji. Sau da yawa muka ga mutane suna bilinbituwar ba su san me zasu yi ba saboda ba su da wani bayani kan abin da ya hau kansu.
Muna hada hukumar alhazi da gwamnatoci da Allah kada su bari wani ya ketara zuwa aikin Hajji sai sun yi masa bayani mai wayarwa kan hadafi da ayyukan Hajji kafin ya wuce kasa mai tsarki domin aikin Hajji. Da yawa na ga wanda ya yi safa da marwa sau 14 maimakon 7, domin ya dauka zuwa da dawowa ne daya. Na ga wasu Fulani da suka ki yin dawafi wai yana da wahala za a kashe su ko a matse su. Don haka yana da kyau duk mutane kamar arba'in zuwa dari ya kasance akwai mutum daya masani, wayayye, mai tausayi, mai juriya da hakuri, mai iya mu'amala da mutane wanda zai gan su a matsayin 'yan'uwansa, wanda zai rika yi musu bayanin al'amuransu kullum, ya rika koma masu kullum domin amsa tambayoyinsu da binciken abubuwan da suke damun su.
Koyarwa da wayarwa ga alhazawan Nigeria amana ce da take wuyan gwamntoci da hukumarsu, kuma wannan amana ce da zata ci duk wanda aka dora wa ita amma ya yi sakaci da ita, sannan mu sani akwai hisabi kan dukkan wanda ya fada cikin wannan barna da sabon. Sannan su kuma al'umma yana da kyau su san cewa suna da hakkin kan hukumarsu da duk wanda aka sanya shi a matsayin mai kula da hakkinsu sannan ya ci amanarsu, don haka suna da hakkin neman sa da hakkokinsu idan bai kiyaye ba koda kuwa ta hanyar kotu ce.
Sannan yana da kyau mu san cewa aikin Hajji da zamu tafi yana da hakki mai girma a kanmu, wasu sun dauka kamar neman sunan alhaji ne, ko kuma yawon shakatawa, ko kuma kawai neman addu'ar bude ce alhalin lamarin ya wuce haka:
Imam Zainul-abidin (a.s) yana cewa: "Kuma hakkin Hajji shi ne ka san cewa shi zuwa ne ga ubangijinka, gudu ne daga zunubanka, kuma da shi ne za a karbi tubanka, da sauke nauyin wajibi da Allah ya wajabta maka shi a kanka".
Don haka aikin Hajji wuri ne na sabunta rayuwa kamar sabuwar haihuwar mutum, ta yadda zai gama Hajji ya dawo tamkar wanda bai taba yin zunubi ba, don haka wuri ne na ganawa da ubangiji da neman kusanci da shi, da neman shafe duk zunubai. Sai dai kash! Tsananin nisanta da ubangiji ya sanya wasu zuwa Hajji don karuwanci da neman mata, wasu kuma don su yi sata da yaudara, da sauran miyagun halaye munana!.
Aikin Hajji ibada ce mai sirri matuka, kuma ya hada dukkan wani abu da ya shafi ibadar Allah madaukaki kamar salla, ambaton Allah madaukaki, da 'yan'uwantaka tsakanin musulmi, da sadaukar da kai, da sadaukar da dukiya, da taimakon bayin Allah, kuma taro ne da yake nuna wa musulmi makomarsu ta shekara, da tattauna matsalolin da suke fama da su domin magance su.
Hajji wuri ne da yake nuna mana kaskan da kai, da jefar da duk wata mummunar dabi'a, da jefar da bambancin kabilanci, da wurgi da kimar duniya ta sarauta sai ga Allah kawai, da kawar da dukkan sabo. Wuri ne da ake nuna godiya ga Allah da ya hada mu kan addinin annabi Ibrahim (a.s) wanda ya kauce wa dukkan addinan bata sai dai na gaskiya.
Imam Zainul-abidin (a.s) yana cewa: Haka nan kaskantar da kai ya fiye maka daga kai, domin dora wa kai nauyi da wahalar da kai suna cikin halin masu tsaurin kai, amma kaskan da kai da rusanawa babu dora wa kai nauyi da wahalar da kai a cikinsu domin su ne asalin halitta, su ne suke tare da halitta. Sai ya yi nuni da cewa taurin rawanin tsiya ne, daga wa mutane kai shi ne ainihin wahalar da kai da fita daga halayyar 'yan'adamtaka.
Hajji wuri ne da ake kauce wa sha'awar duniya da nutsewa cikin kogin ganawa da Allah madakaki, da ninkayo cikin tekun ambaton Allah domin nemo lu'ulu'un zaman samuwar duniya don keta haske zuwa ga rayuwar daukaka mai dawwama. Don haka ne mai yin Hajji yake kasancewa kamar mutumin da yake rayuwa tsakanin duniya da lahira, yana samun kansa tsakanin zahiri da badinin samuwarsa, ba shi da komai sai kyallaye biyu kawai masu kama da likkafani!.
Sai aka haramta masa wasu abubuwan da ba don Hajji ba, su halal ne gareshi, kuma domin kawai ya dulmuya cikin kogin jin dadin ganawa da Allah sai aka haramta masa auren mace ko kusantar mace mafi dadin abin rayuwar duniya, aka hana shi turare da dukkan kayan adon duniya na more rayuwa masu sanya shi annashuwa, kuma aka hana shi cutar da komai na halittun allah balle kuma ya kashe su, aka hana shi kawar da gashin kansa da jikinsa da sauran dokoki da iyakoki masu kangewa.
Hajji taro ne wanda yake tuna mana sadaukarwar Isma'il da Hajar a wannan sahara a kusan shekaru dubu hudu da suka wuce, sai mutum ya tuna sadaukarwar da suka yi. Sannan kuma ya sadaukar da kansa ga Allah kamar yadda Isma'il (a.s) ya mika wuyansa ga Allah domin a yi layya da shi, ya sadaukar da kansa da juriya kamar yadda Hajar ta jure wa kishirwa a wannan duwatsu masu zafi tsakanin safa da marwa domin neman yardar Allah madaukaki.
Hajji aiki ne da yake muhimmantar da shagaltuwar mutum da kansa da Ubangijinsa ta yadda ba ya ganin komai sai Allah mahaliccinsa tamkar ranar tashin kiyama! Don haka ne Hajji ya zama aiki ne mai nuna cewa duk da kuwa akwai mata da maza a cakude, amma babu wani wanda yake kula da cewa yana kusa da dayan ne! Namiji ba ya kula da na kusa da shi cewa mace ce, kamar yadda ita ma ba ta kula da na kusa da ita cewa namiji ne!.
Idan mutum ya juya ya kalli Saudiyya, daya daga cikin abin da yake cikin tunanin al'ummarmu sun dauka kamar yadda wurin yake da tsarki haka ma zasu samu mutanen wurin! Sai dai wuri ba ya iya tsarkake mutum, abin da kawai zai iya tsarkake mutum shi ne aikinsa, kuma shi ne alamar tsarkinsa!.
Wuraren da ake ajiye alhazawan Nigeria wurare ne masu tsananin kazanta, ko da yake wasu suna ganin bai takaita da 'yan Nigeria ba, domin ya shafi duk wata al'umma da kazanta ta kasance al'adarta. Al'umma ce da ta saba da zuba shara ko'ina don haka ba ta tanadar wurin zuba ta, da sayar da abinci a bakin hanyoyi ta yadda duk wani wuri da zaka ga ana sayar da wani abin da za a ci, to ka tabbata wuri ne da yake hanyar wucewa har ma kura tana tashi. Kuma ta saba da kama ruwa ko yin bayan gida a duk inda za a iya tsuguno ko da kuwa wurin zaman mutane ne!.
Don haka ne sai al'ummarmu ta fi saukin kamuwa da cututtuka, ta fi karancin lafiya, ta fi fama da ciwuka! Hada da karancin masu kula da lafiyarsu a himominsu da masaukansu. Wannan lamarin duk sai ya mayar da al'ummarmu ci baya a kowane fage, jahilci da karancin tunani ya mamaye ta, sai aka bar ta da hira a bakin titina, da zauruka!.
Kamar yadda a gida Nigeria babu wata gwamnati mai tsawatawa kan hakan, haka nan a kasa mai tsarki babu wasu masu kula da wannan tsaftar yadda ya dace!.
Amma wasu suna ganin ai alhakin gwamnatin Saudiyya ce don haka ita za a zarga! Sai dai wannan ba dalili ba ne, domin idan ka je sauran kasashe babu wannan kazantar kuma ba yawa al'ummarmu ta fi su ba! Leka masaukan Indunisiyawa da Iraniyawa ka gane wa idanuwanka, zaka ga bambanci tsakaninsu da al'ummarmu duk da kuwa sun fi mu yawa!.
Mu dai al'ummarmu ta fi kowacce dakon rashin sanin hukuncin Allah na rashin kimanta kanta da wulakanta kanta ta hanyar rashin jin cewa akwai wani mutuncinta da ya kamata ta kare wa kanta, don haka ne babu wani mai jin cewa idan ya kazanta wurin zamansa to mutuncinsa da na al'ummarsa ne yake zubewa! Don haka sai al'ummarmu ta kasance kaskantacciya a mahangar sauran al'ummu, sai masu zuwa Hajji suka rasa wani abin kirki na wannan al'ummar da zasu nuna wa duniya sai kazanta! Don haka sai al'ummarmu ta rasa wani kyakkyawan wakilci daga sauran masu wakiltarta a duniya!.
Rashin tsarin ya kai ga a cikin kewayen da na yi masaukan alhazai a "Mina" 1431, wani lokaci na ga maza suna shiga bandakin da aka tanadar wa mata a masaukin alhazan sakkwato! Babu ruwan mutumin kasarmu, bai damu ba ko da an rubuta wannan ban dakin na mata ne, shi dai kawai yayin da ya ji wata bukatarsa ta taso, to sai ya samu wuri ko da kuwa bai dace da shi ba!.
Ko da yake ba mamaki al'ummarmu ta koma hakan, domin duk wanda yake ganin kansa a wulakance to babu wani fatan alheri daga gareshi. Imam Aliyyu dan Abu Dalib (a.s) yana cewa: "Duk wanda ransa ta wulakanta gunsa, to kada ka yi tsammanin alherinsa" . Don haka ne sakamakon al'ummar ba ta dauki kanta mai hakki da tunani ba, sai tsammanin samun wannan alheri da kyakkyawan misali ya yi wahala gun ta.
A wata ruwayar Imam Aliyyu alHadi, dan Muhamamd alJawad (a.s) yana cewa: "Duk wanda ransa ta wulakanta gunsa, to kada ka aminta daga sharrinsa" . Wannan ma yana nuna cewa idan mutum yana ganin kasan a wulakance to babu mamaki don kada abubuwan sharri, da rashin alheri daga gare shi.
Akwai wani abu da ya yi muni matuka wanda a shekarar 1426 da abin da ya yi baya ya munana matuka, sai dai a yanzu ya samu sauki sosai sakamakon hadin gwiwar gwamnatin Nijeriya da ta Saudiyya, wannan lamarin kuwa shi ne mummunar al'adar nan ta yin bara da ta addabi al'ummarmu. Wani yana ba ni labari cewa hatta da nakasassun yara da kake gani a nan Saudiyya wasunsu mutanen da suke kawo su daga gida Nijeriya da karfin tsiya suke nakasa su don kawai a yi bara da su!
Wani wulakanta kai mai cin rai da na gani a 1426 shi ne yawan masu bara, dukkaninsu ko kusan kashe 95 % daga Nigeria suke. Sai dai na ji dadi matuka da na shafa ban ga yawancinsu ba a 1429, sai wani yake ba mu labarin cewa gwamnatin Nigeria da ta Saudiyya ce suka yi hadin gwiwa domin kwashe su gaba daya. Amma a shekarar 1426 mun sha kunya wurin abokanmu na sauran kasashe da muka je yin aikin Hajji tare da su. Sai dai ba kawai a Saudiyya ba, kamar yadda gwamnatin Nigeria ta yi wannan kokarin a Saudiyya, muna fatan nan da 'yan shekaru wannan mummunar dabi'ar ta bara mu ga ta kau daga arewacin Nigeria.
Bara wata mummunar al'ada ce da ta faru sakamakon rashin gata da al'ummar ta ki yi wa kanta na fuskantar neman ilimin addini cikin gata, iyayen da suke da abincin shekara a aje, maimakon su kawo dansu da guzuri da kudin da zai ishe shi duk shekara, sai su turo shi birni domin ta ciyar da shi da sunan ya samo ilimi! Ko da yake akwai masu yin hakan da kyakkyawan nufi, sai dai waye zai wayar da kan al'umma ta sanya 'ya'yanta cikin mutunci ba wulakanta kai!
Bara ba addini ne ba ne kaskanci ne, wannan al'adar ta sanya da yawa daga mutanen kudancin Nijeriya sun dauka addinin arewa ne, har ma ana iya yi wa dan arewa isgili da shi, kuma mafi muni sai aka samu wasu jahilai masu kiran kansu malamai suka ba shi halacci, sai wannan mummunan kaskanci ya ki kawuwa.
Don haka ne ya kamata al'ummar nan ta farka ta gane kimarta, ta fita daga abin da yake nuna wulakantuwa, ta tashi ta yi wa kanata gyara, su kama hannun juna, idan kuwa ba haka ba, babu wani canji da za a iya samu daga gare ta. Kuma batun yin addu'a babu wani aikin ganin samun wannan canjin ba inda zai kaita sai kara nisa daga cimma hadafi! Kamar mai nesa da rijiyar da zai samu ruwa ne, amma yana addu'a Allah ya kawo shi kusa da ita!.
Masu ganin cewa alhazan Nigeria suna daga cikin wadanda babu wanda ya kai su rashin tsari sakamakon babu wata makoma ta gari da zasu koma mata domin sanin abin da ya dace su yi, a cikin abin da na gani a shekarun baya akwai abin takaici idan aka kwatanta da wasu kasashe tun daga nau'in wurin zama da gidajen da muke rayuwa a matsayin alhazan Nigeria, har zuwa kayan rayuwa da jin dadi da ake tanadar mana, da kuma motocin da zasu taimaka mana zirga-zirga, da ma adreshin wurin da ake ajiye alhazan Nigeria.
Magana kan wannan lamari tana bukatar littattafai masu yawa, domin idan ana son fayyace abubuwan da suke faruwa to zai bukaci littattafai masu yawa. Ina tuna wahalhalu kawai da muka sha domin kai mutanen da suka bata wurinsu saboda Allah ba don aikin an dora mana shi ba, to wannan kawai ya ishe mu yin littafi. Sai ka ga alhaji ko hajiya sun bata amma abin takaicin shi ne a jikin hannunsu abin da aka sanya musu na adreshin ba adreshin wurin zaman su ba ne, adreshin wurin masu kula da alhazawan ne, sai kuma ka kai su can sai a yi maka wani irin kwatancen wurinsu mai nisa daga nan ofishin!. Wahala dai tana nan kan alhajin Nigeria!.
Alhajin Nigeria bai samu girmamawa daga masu kula da shi ba, balle mu yi tunanin ma'aikatan Hajji na Saudiyya su kula da shi yadda ya dace. Da yana da kima gun kasarsa, to da a kan wulakanta alhaji daya kawai ya kamata a gyara wa kasar Saudiyya zamanta! Hajjin ma ana iya yanke zuwa har sai sun yarda da mutanta al'ummarmu!. Amma sai rashin kimanta alhaji ya fara daga gida, don haka yaya kake tsammanin na waje ya girmama shi!?.
Dan Nigeria yana ganin motar Nigeria komai wahalar da ya sha ba zata dauke shi ba sai idan dan mai matsayi da mukami ne! Dan Nigeria ba zai ga wani abin more rayuwa daga gwamnatinsa ba kamar yadda yake ga sauran kasashe.
Mafi muhimmanci shi ne kare mutuncinsa da kimarsa, wani abin mamaki hatta da kotun Saudiyya idan ta kama kowane dan kasa da laifi tana jiran sai dole kasarsa ta daukar masa lauya ta tabbatar da ya yi laifi sannan a iya hukunta shi, amma ban da maras gata da kima wanda hukumarsa ba ta san mutuncinsa ba kamar dan Nigeria .
Babu wani abin da ya ba ni mamaki sai abin da na gani a 1429 na labarin yadda rayuwar dan Nigeria take ta wulakanta kai da rashin hadin kai a mash'ar; mun fita da wasu abokai don mu ga yanayin al'ummarmu da gudummuwar da zamu iya ba wa al'ummarmu, sai muka zo wani wurin masu sayar da abinci irin dahuwar gida, akwa wata budurwa 'yar Kano mazauniyar Saudiyya mai suna Hawwa da wani mutum dan kasar Niger da yake son ta ya wuce sai ta harare shi domin ba ta son sa, sai kawarta ta ce da ita: Ki yi hattara kin san dan kasar Niger ne! Sai ya yi miki wulakanci ya yi miki duka a banza!. Da na ga alamar tsoron hakan tare da ita sai na ce: Me ye na jin tsoro haka? Sai ta ce: Malam kai ba Saudiyya kake ba? Sai na ce: Na zo aikin Hajji ne. Sai ta ce: Lallai ai mu muna jin tsoron dan kasar Niger, saboda sai su taru su yi maka duka ko kai ke da gaskiya idan ka yi fada da dayansu, kuma 'yan Nigeria suna kallo sai dai a kashe ka!.
Kamar yadda mutum yake wulakantuwa idan ya kaskantar da kansa, haka nan sauran al'ummu zasu wulakanta shi. Ko da yake mutanen wasu kasashen suna wulakanta dan Afrika da Ba'indiye ne saboda suna ganin su kazamai, domin mutane ne idan ka je yankunansu sai ka daure saboda rashin tsafta. Ina tuna wani dattijo dan Afrika da ya durkusa yana fitsari da kashi a bakin hanyar komawa cikin garin Makka daga Mina, ga al'aurarsa duk masu wucewa suna gani babu kunya! Sai na ga wani Baturke da ya hango shi yana nuna wa 'yan'uwansa suna cewa: Kalli 'yan Afrika marasa hankali! Kalli wulakantacciyar dabba!. (Hajji 1431)
Idan muka juya game da kimar alhazawan Nigeria a Saudiyya zamu iya cewa ne sai bango ya tsage kadangare ke shiga, domin matukar wata al'umma ba ta girmama kanta ba, to babu wani mutum ko wata al'umma da zata girmama ta. Don haka wani nauyi ne da ya rataya kan gwamnati ta tabbatar da hakkin alhazawanta. Muna iya ganin cewa duk shekara alhazawanmu suna zaman kwanakin Mina a cikin karsen Muzdalifa ne ta yadda wasu sukan fada muzdalifa, wannan kuwa yana tasiri kan aikin hajjinsu, domin duk wanda bai yi kwanakinsa a Mina ba, to dole ya yi yankan Fidiya, sai dai waye zai lurasshe da alhazawanmu kan hakan, gwamnati ba ta yi! malamai ba su yi ba!
Don haka hakki ne da ya rataya kan malamai su wayar da kan alhazawanmu, ita kuwa gwamnati ta nemi hakkinsu, ta tabbatar da duk wani abu da ake yi wa alhazawan sauran kasashe na hakkinsu an ba su shi.
Nauyi ne da ya rataya kan hukuma idan idan wani maniyyaci ya fada wani hali, ko kuma aka kama shi a matsayin mai laifi a Saudiyya to dole ne ta karbar masa 'yancinsa, idan ya kama ya zama dole ta daukar masa Lauyansa domin kare 'yancinsa har sai ta bayyana cewa ya yi laifin. Idan kuwa aka sake a zartar masa da hukunci ba tare da sanin ta ba, to a kan mutum daya yana da kyau ta nuna fushinta ko da kuwa ta hanyar yanke alaka ne da huldar jakadanci!.
A wuraren ibadar alhazawa a kwanakin Hajji akwai rashin tsarin da yake addabar alhazawa, misali idan wani zai bace, ko ya yi kwatancen inda yake, yana yin wahala matuka saboda babu wasu alamomi muhimmai a wuraren da zasu sanya alhaji ya gane inda yake.
Da misali za a yi wa kowace dirkar lantarki wato falwayar wutar bakin hanyoyi ko hemar alhazawa lambobi a jere masu bin juna, ta yadda duk inda mutum yake zai iya kwatance da wannan lambar, kuma zai iya bin lambar a jere har inda aka kwatanta masa, da an samu saukin kai masu bacewa wurin da suke, da kuma yin kwatance bai yi wahala ba sosai.
Batun alaka tsakanin al'ummar musulmi wani lamari ne mai matukar muhimmaci a aikin Hajji, domin Hajji wata mahada ce domin tattaunawa da ganawa tsakanin al'ummar musulmi. Haduwar al'ummar musulmi domin yawaita ambaton Allah da sanin halin da juna suke ciki, da agaza wa juna, da tausaya wa juna, da sanayyar juna domin hada zumunci tsakanin al'ummar musulmi kamar yadda Adam (a.s) da Hawwa suka hadu a dutsen Arfa.
A wannan dutsen na Arfa akwai addu'a ta musamman da aka fi sani da addu'ar Arfa da imam Husain (a.s) ya yi a wannan dutse kafin ya fita daga Makka saboda tsoron sharrin azzaluman 'yan barandan Yazid.
Sai dai tuni aka yi wurgi da tausaya wa juna aka watsa shi a kwandon sharar tarihin musulunci, hakika na yi kuka a wurin jifan shedan da wurin dawafi yayin da na ga al'ummar musulmi kowa yana ta kansa, babu mai tausaya wa waninsa, babu rahama a tsakaninsu! Da abin ya tsaya a haka da ya yi kyau, sai dai ya wuce haka ya kai ga yin fada da zage-zage har lokacin dawafi a gefen Ka'aba!.
Babu abin da ya sanya ni yin kuka a wurin jifan shedan sai irin wulakanta juna da nake ganin yana faruwa daga musulmi, sai duniyar musulmi suna wulakanta juna, kowa yana dauka da zafi kamar ya zo fada ne ba aikin ibada da nuna tausayi da kauna ga juna ba, ta yadda a jikin ka'aba sai a yi fada da zage-zage tsakanin wani musulmi da wani, idan ba ka sanya hakurinka ya wuce 100 % ba, to lallai kana iya bugawa da wani musamman idan kana jin yarurruka daban-daban, sai ka ga babu rahama tsakanin juna, babu tausayin juna.
Idan kana son magana kan yankin gabas ta tsakiya musamman da ya hada Indiyawa, da Pakistanawa, da Iraniyawa, da Turkawa fadi abin da ka ga dama, magana a nan ne take tsawaita. Sai dai kowane mutane suna da ta su matsalolin, mutanen Afrika suna da nasu matsaloli, wadancan yankuna suna da nasu.
Aikin Hajji a wannan zamani yana daga cikin abubuwan da suke da matukar muhimmanci a zaman tare na al'umma da tattalin arziki, da alakar siyasa tsakanin al'ummu da kasashe, wuri ne mai muhimmnci domin haduwar al'ummar musulmi da tattauna matsalolin rayuwa da suke addabar su. Sai dai kash! abin takaici al'amarin ba haka yake ba, domin duniyar musulmi bayan ta bar wasiyyar annabi (s.a.w) na su yi riko da littafin Allah da alayensa kamar yadda ya zo a ruwaya mutawatira, sai suka kasa maye wannan da wani abu makamancinsa domin babu shi.
Don haka sai kaskanci ya mamaye su, marasa kishinsu suka kame jagoranci, wadanda suke sama babu tausayin al'ummar a zukatansu, kuma suka riki jahilai a matsayin malamai kamar yadda wasu ruwayoyi suka yi nuni da karshen zamani da abin da zai faru. Sai teburin tattaunawa tsakanin musulmi domin warware matsalolin duniyarsu da lahirarsu, da taimakon junansu, ya zama wata kofa da su musulmi suka toshe ta!.
Don haka sai dimuwa da rikirkicewa suka mamaye su, tsoro ya lullube su, rashin hadin kai da rashin tausaya wa juna ya shige su, sai suka fada cikin faganniya da ba wanda ya san karshenta sai Allah madaukaki. Alamomi suna nuna fushin Allah da wannan al'umma sakamakon kaskancin da ya fada mata, wannan kaskancin kuwa ya zo ne domin ta bar wasiyyarsa, kuma ba shirye take ta koma kan abin da ya zaba mata ba! Sai abin da Allah ya zaba wa al'umma ya kasance abin da al'umma take ki, abin da ya ki mata kuwa ya zama shi ne abin da ta zaba! Allah kuwa ba ya canja wa mutane abu sai sun canja wa kansu!.
Sai dai duk da abin da muka gabatar na sakaci da takaitawar al'ummarmu, wannan ba yana nufin mu yanke kaunar samun gyara ba domin babu wata hanya da Allah ya toshe mana domin samun sauki da shiriya, sai dai su mutane ne suka toshe ta da kansu, kuma Allah ya yi mana ludufin cewa idan muna son koma wa wannan hanya tasa kofarsa a bude take, wannan shi ne babban buri da falala da ni'imar da Allah ya yi mana a rayuwarmu.
Jahilcin da aka jefa al'umma game da addininsu ya sanya miliyoyinsu ba su san hikimar Hajji ba, sai masu jagorantar su zuwa Hajji suka kasance tamkar makafi ne da suke jan makafi. Wannan lamarin na fahimce shi ne sosai sakamakon wata lacca da na yi game da hikimar yin Hajji a 1426 kusa da kamp din alhajan Kano da Zamfara a kwanakin Mina da ke kusa da garin Makka mai girma.
Na yi bayani game da hadafin sanya Hajji ga mutane kamar yadda sayyida zahara (a.s) ta kawo a hudubarta, da kuma hikimar yin safa da marwa, da yin layya, da zuwanmu mina, da jifan shedan, da sanya tufafi irin wadannan, da yadda wurin yake kama da lahira. A nan ne wani alhaji ya yi godiya, ya ce mana ya yi Hajji sau da yawa a rayuwarsa, amma bai taba fahimtar hikimar yin Hajji ba sai a yau.
Mutum zai tausaya wa al'ummar musulmi domin da yawa sun je Hajji amma sai suka yi hajijiya ba su san me ye sirrin da yake cikinsa ba, sai suka dauka sun je kallon Makka ne da Ka'aba da duwatsun da suke wuraren. Sau da yawa na ga mutane suna yawo a titinan Makka amma idan na tambaye su kan hadafin yin Hajji ba su sani ba. Ba su san sirrin rayuwarsu ta dan wannan lokacin ba, ba su san hukuncinsa ba, sannan masu kula da sha'aninsu ko dai ba su sani ba, ko kuwa ba su damu da su ba.
Sirrorin da suke cikin dawafi, da safa da marwa, da yanka layya, da taron al'umma, da ambaton Allah, da sanayya tsakanin juna, da taron mutane masu launuka iri-iri, dukkan wannan yana nuna mana hikimar Allah a wannan taro. Taro ne wanda ya yi kama da na lahira a wani lokaci, daya daga cikin abin da nake tunawa shi ne yayin da na ga malamina da kaya ya yin barin masha'ar sai na so in karba, amma sai na kasa karba domin idan na karba sai dai in jefar da nawa ne, sai wannan ya tuna mini lahira da cewa kowa zai shagaltu da abin da ya dame shi ne.
Dawafi yana daga cikin mafi muhimmancin rukunai a aikin Hajji, a kowane kewayen Ka'aba ana son mu shagaltu da addu'o'i, kuma kowane gewaye a gefen Ka'aba guda bakwai yana daukaka mu ne zuwa ga Allah, kamar dai matattakalai ne na hawa sammai har guda bakwai, sannan sai a nufi makamu Ibrahim (a.s) domin yin salla, da godiya, da addu'a, da nema, da ganawa da Ubangijin duka.
Babban hadafin Hajji shi ne bayan al'umma ta gama dukkan abin da take yi na aikin Hajji sai ta koma wurin imaminta jagoranta wanda Allah ya sanya mata domin sanin mene ne aikin da zasu yi a wannan shekarar. Sai dai al'ummar nan ta yi watsi da wadannan jagorori har ta sanya boyuwar na karshensu saboda tsoron kisa daga su kansu musulmin, Imam Mahadi (a.s) jagoran al'ummar karshe ya boyu kuma ba zai bayyana ba har sai ranar da umarnin Allah ya zo na hikimarsa, sai ya bayyanar da shi domin cika wannan duniya da adalci bayan an cika ta da zalunci.
Aikin Hajji wuri ne da jagoran al'ummar musulmi a duniya zai ba su umarni da matakai da zasu dauka a duk fadin duniya, wadannan matakan suna iya yiwuwa na alaka da wasu kasashe ne, ko kuma na kasuwanci, ko na tsaro, ko na ilmantarwa, ko na sha'anin makomarsu ta lahira, da sauran matakai da zasu dauka. Sai dai kauce wa wannan hanya ta wasiyyar annabi da makomar da al'umma zata koma ya sanya su zama kara zube babu wani wanda zasu koma zuwa gareshi a bayan Hajji domin sanin wannan.
Da al'umma ta yi riko da wasiyyar annabi (s.a.w) ta karbi makomar da ya sanya mata, da ta zama ita ce mai daukak a duk fadin duniya, da dukkan duniya ta rusuna mata, da ludufin Allah (s.w.t) ya mamaye ta!. Sai dai kash! abin takaici al'amarin ba haka yake ba, domin bayan duniyar musulmi ta bar wasiyyar annabi (s.a.w) ta yin riko da littafin Allah da alayensa wasiyyansa kamar yadda ya zo a ruwaya mutawatira, sai suka kasa maye wannan da wani abu makwafinsa domin babu shi, don haka sai kaskanci ya mamaye su, marasa kishinsu suka maye gurbin jagoranci wadanda babu tausayin al'ummar a zukatansu, kuma suka riki jahilai a matsayin malamai kamar yadda wasu ruwayoyi suka yi nuni da karshen zamani da abin da zai faru.
Manzon rahama (s.a.w) ya isar da sakon Allah madukaki, ya yanke uzuri kan duk wani mutum mai neman shiriya da gaskiya, an saukar masa da ayar cikar addini, da umarnin isarwa, don haka sai ya kafa Ali dan Abu Dalib (a.s) a matsayin shugaba kuma makomar al'umma halifansa bayansa. Wannan lamarin kuwa ya faru a ranar Gadir ne goma sha takwas ga zulhajji a shekarar hajjin bankwana wanda bisa hakika sunansa "Hajjin isar da sako" sai Allah ya saukar da ayar: "A yau ne na kammala muku addininku, na cika ni'imata gareku kuma na yardar muku da musulunci shi ne addini" . Sai Annabi ya yi rashin lafiya mai sauki na 'yan kwanaki sakamon guba da ya sha!, sai dai cutar ta yi tsanani har sai da ya hadu da Ubangijinsa a 18 ga watan safar na 11H!. Sai wasiyyinsa bisa umarnin Allah kuma halifansa bayansa Imam Ali (a.s) ya yi masa wanka da salla da binne shi a dakinsa a Madina inda kabarinsa yake yanzu.
Don haka mafi girman lamari shi ne mu fahimci cewa Hajji mahada ce domin ganawar musulmi da jagoransu mai shiryar da su, kuma wannan shi ne babban kololuwar ma'anar Hajji da dalilin da ya sanya wajbta shi a kan mutane gaba daya, musulminsu da kafiransu. Ruwayoyi masu yawa sun zo suna masu tunatar da al'ummar musulmi cewa daga cikin cikar hajjinsu shi ne su ziyarci imaminsu su gana da shi, a lokacin manzon Allah (s.a.w) shi ne wannan imamin nasu wanda yake shi annabi ne, a lokacin wasiyyansa tun daga imam Ali (a.s) har zuwa imam mahadi (a.s) kowanne a zamaninsa shi ne makomar al'umma bayan Hajji domin su san umarni da sakon shekara daga gareshi!.
Inna Lil-Lahi wa inna ilaihi raji'un!!!
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
December, 2010