Mukaddimar Hajji


Da Sunnan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
Kuma ka yi yekuwa ga mutane da wajabcin Hajji, sun zo maka suna masu tafiya da k'afafu kuma da a kan kowane mad'amfarin rak'umi suna masu zuwa daga kowane zango mai zurfi .

1. Da shi ne muke neman taimako domin shi ne fiyayyaen mataimaki mai agaji, kuma tsira da amici su tabbata ga shugbanmu kuma annabinmu Baban al'Kasim al'Mustafa Muhammad (s.a.w) da alayensa tsarkaka.
Ubangiji madaukaki yana fada a littafinsa: Kuma Allah yana da hajjin dakin (ka'aba da ya dora) kan mutane, ga wanda ya samu damar ikon tafarki zuwa gareshi, kuma duk wanda ya kafrice to hakika Allah mawadaci ne ga barin talikai.

Gabatarwar Ayyukan Hajji da Kashe-kashensa
Gaisuwa gareku masu sauraro masu shaukin ziyarar dakin Allah mai alfarma, musamman masu niyyar tafiya zuwa kasa mai tsarki don yin aikin hajji a wannan shekarar.
Mu a wannan darasin da sauran darussan da zasu zo nan gaba muna son mu yi bayanin hukunci da ayyukan umara da hajji ne bisa fatawar marja'I mai girma da daraja kuma jagoran juyin musulunci wato Ayatullahi sayyid khamna'I (d.z). muna fatan wannan darasin ya ksance mai amfani matuka gare ku. Kokarinmu shi ne mu ga mun kawo mas'alolin da suke faruwa wadanda mutane suke bukatarsu yau da gobe kuma suke cin karo da su a kowace shekara a ayyukan hajji ko umara ba tare da mun shiga cikin mas'aloli kanana ba wadanda ba kasafari ake cin karo da su ba, wadanda wani lokaci ne kawai suek zuwa, kuma ana iya komawa littafin hajji don sanin su, ko kuma a tambayi malamai a lokacin ayyukan hajji da umara.
2. Da farko dai dole ne mu kawo cewa masu zuwa hajjin dakin Allah suna yin wasu ayyuka da ake kira umara ko hajji. Umra ta kasu gida biyu, hajji kuwa ya kasu gida uku. Akwai Umarar tamattu'I, da umarar ifradi. Hajji kuma akwai hajji tamattu'I, da hajji ifradi, da hajjin kirani. Mutanen da a duk tsawon shekara suna makka ne in banda kwanakin hajji to sai su yi umarar ifardi wacce zamu kawo bayanin hukunce-hukuncenta a karshe. Amma wadanda suke son yin aikin hajji to dole ne su yi daya daga cikin ayyukan hajji kala uku: Hajjin tamattu'I yana tare da umarar tamattu'I ne, kuma wannan ne ya hau kan wadanda suke zuwa daga wajen makka wadanda kuma ba 'yan makka ba ne kuma ba sa rayuwa kusa da makka. Kamar wadanda suek zuwa daga wasu garuruwa kamar pakisntan, iran, da sauran kasashen Turai da Amurka da Afrika da suke zuwa domin yin aikin hajji da umara. Su hajjin tamattu'I da umarar tamattu'I ne suka hau kansu.
3. Hajjin Ifradi da kirani su ne ayyukan da suka hau kan mutanen makka da wadanda suke rayuwa kusa da makka har uzwa kilo mita casa'in daga kowane bangare na garin makka. Saboda haka a wannan darasin zamu yi bayanin hajjin tamattu'I da umarar tamattu'I ne a takaice sannan sai daga karshe sai mu kawo bayain umarar mufrada ; duk da cewa hajjin ifradi da hajjin karani ba su da wani bambanci mai yawa a tsakaninsu da hajjin tamattu'I sai wasu 'yan bambance bambance 'yan kadan, sai dai tun da ba su da bukatuwa gun wadanda suke bin wannan darasin don haka zamu kawar da kai daga bayanin su, sai dai a cikin tsakiyar karatu zamu yi dan nuni da wasu daga ciki a takaice.
4. Wani lokaci Umara da hajji wajib ne, wani lokaci kuwa mustahabbi ne, wani lokaci hajjin wajibi yana kan mai yin hajji ne, wani lokaci kuwa na wakilci ne, wato wani lokacin hajjin nasa ne, wani lokaci kuwa na wani ne yake yi. Wani lokaci hajji ne da yake kan wani mutum saboda ya samu iko wanda yake wajibi ne sau daya a rayuwa. Wanda ya samu ikon yin hajji to ya zama wajibi a kansa, kuma wannan wajabcin yana kansa sau daya ne a rayuwarsa wanda ake kiran sa da hajjin musulunci. Wani lokaci hajji yana zama wajibi a kansa ne saboda wani dalili kamar "nuzuri", da "rantsuwa", sai dai wanda mutane suka fi yi shi ne nau'I na farko wanda yake shi ne yin hajji saboda samun iko. Haka nan hajjin wakilcin wani yana da nasa sharuddan na musamman da zamu kawo su a cikin bayanai masu zuwa in Allah ya so.

Hajjin Musulunci
5. hajjin musulunci yana zama wajibi ne saboda samun iko, kuma sau daya ne yake wajibi a kanmu mutum da dukkan tsawon rayuwarsa, don haka ne ma ake kiran sa da hajjin musulunci tun da shi ne yake daga cikin rukunan asasin addinin musulunci.
A wata ruwaya ya zo daga Imam Muhammad bakin (a.s) cewa: "An gina musulunci a kan abubuwan biyar, a kan salla, da zakka, da azumi, da hajji, da jagoranci". A wannan ruwayar an sanya hajji daya daga cikin asasin addinin musulunci, kuma don haka ne ma kae kiran sa da hajjin musuluinc, hajji ne da yake zama wajibi a kan mutum a asalin shari'a, wato mutumin da yake mai iko kawai ne yake zama wajibi, kuma zamu kawo sharuddan iko a nan gaba.
Sannan wajabin wannan hajji na gaggawa ne, wato da zarar mutum ya samu iko to a farkon damar da ya samu dole ne ya yi aikin hajji, bai halatta ba ya yi jinkiri da sunan cewa yanzu ba zai tafi ba sai matarsa ta samu biyan nata kudin kujera, ko wata mace da ta samu ikon tafiya kamar ta hanyar samun kudin ko na gado ne, to ita ma ba zata ce bari in jira sai mijina ya samu biyan nasa kudin kujera ba sai mu tafi tare.
Idan wata mata zata iya zuwa ita kadai to babu wata matasla, sai ta tafi domin yin aikin hajjinta ba tare da jinkirtawa ba, haka nan bai kamata ba wani ya jira abokansa sai sun biya kudin kujera. Don haka da zarar mutum ya samu damar yin aikin hajji dole ne ya hanzata ya yi aikinsa.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
Thursday, December 15, 2011