Wakilcin Hajji


Wakilci a Hajji
1. Da can mun ce wani lokacin wani nau'in aikin hajji kamar hajjin musulunci yana hawa kanmu, amma wani lokaci muna wakiltar wasu ne don yin aikin hajji, wannan shi ma yana da nasa hukucnin, saboda a wadanan shekarun wasu sukan je hajji don su wakilci wasu; misali uba ya sayi kujera sai ya kasa zuwa saboda ya samu raunin jiki da rashin karfi, ko kuma ya rasu ya taafi zuwa ga rahamr Allah, yanzu kuma dansa ko 'yarsa ko wani mutum yana son ya je maimamonsa ya yi msa ahhau, ko ya yi wasiyya ga wani mutum ya yi masa hajji a dukiyarsa, to a yanzu idan wani yana son ya je ya yi masa aikin hajji.
Magana a nan ita ce; da farko waye ya zama wajibi ya daukar masa wakili? Waye kuma ya zama wajibi mu daukar masa wakili? Mutumin da ya zama mai iko, kuma da yana iya zuwa makka amma bai tafi ba, kuma yanzu yana da niyyar tafiya sai dai ba shi da ikon jiki na karfin jiki, kuma ba shi da tsammanin cewa matsalarsa zata kawu nan gaba ta yadda zai iya zuwa ya yi aikin hajji, to irin wannan mutumin ya zama wajibi a kansa ya dauki wakili da zai yi masa aikin hajji!.
2. Na biyu: Wanda hajji ya zama wajibi a kansa ya tabbata kuma zai iya zuwa hajji, sai dai bai je ba har ya mutu, to ya zama wajibi kan magadansa su fitar masa da dukiya daga abin da ya bari domin a yi masa hajji. Ko da yake idan aka samu wai wanda zai yi masa a kyauta babu wata matsala a kan haka.
Na uku: Wanda ya yi wasiyya a yi masa hajji sai a fitar daga sulusin dukiyarsa don a yi masa hajji, wannan ma dole ne magada su yi aiki da shi, ko kuma idan yana da wasiyyi da ya yi masa wasiyya, to sai ya yi aiki da abin da ya gaya masa, sai a fitar da kudi daga sulusin dukiyarsa don a yi masa hajji, wannan ma zai zama hajjin wakilci.

Sharuddan Wakilci a Hajji
3. Amma wanda yake son ya wakilci wani ya yi masa hajji, wato ya kasance wakilin wani, wane sharuda ne yake da su? Kuma waye zai iya zama wakili? To sharudan asali na asasi su ne:
Na daya: Ya kasance yana da masaniya da aikin hajji ta yadda zai iya yin sa daidai bisa inganci. Ta yiwu ya zama yanzu bai san aikin hajji ba, amma yana tare da malami ko wani mutum wanda ya san masl'alar aikin hajji da zasu tafi tare kuma ya yi aikin daidai, wato ya koya a wurinsa ya aikata, to wannan ba shi da matsala.
Na biyu: Ya kasance hajji bai zama wajibi a kansa ba. Wannan abu ne muhimmi matuka, mutanen da suek son su wakilci wasu a aikin ahjji, su sani cewa dole ne su kansu su kasance ba masu iko ba ne. Don haka idan wani mutum ya kasance mai iko, kuma hajji ya zama wajibi a kansa, ba zai iya yin wani hajji da wakilci ga wani ba, idan ma ya je ya aiwatar da shi, to wannan hajjin na wakilci bai yi ba.
4. Na uku: Kada ya kasance yana da uzurin yin ayyukan hajji na bisa zabi, wato ya kasance zai iya yin ayyukan hajji bisa daidai shi da kansa, sai aiki daya ne kawai da zai iya bayar da wakilci shi ma wanda ba dole ba ne ya yi da kansa wanda zai iya ba wa wani ya yi masa shi wato shi ne yanka layyarsa ranar idi, ko da kuwa shi ma ya iya, zai iya ba wa wani ya yi masa shi. Hatta wanda shi ma bai iya yankan ba tun farko, ya zama ba zai iya yanka ba, shi ma zai iya wakilta wani ya yanka masa kuma babu komai.
Amma a sauran mas'aloli idan wani ya kasance ba zai iya jifa ba, ko kuwa wanda sallarsa ba daidai ba ce, to wannan mas'ala tana da muhimmanci matuka, don haka wannan mutumin ba zai iya zama wakili ba. Don haka mutanen da suke tafiya don wakiltar wasu ya zama dole su samu wani malami su yi salla wurinsa don ya gani, idan sallarsu tana da matsala sai su gyara domin su iya wakilcin yin ayyukan hajji.
5. Na daya: Akwai mas'aloli uku da suka ragi a batun waiklic da zamu akwo muku su: daya shi ne mutuminda yake zama mai wakilci ba dole ba ne ya kasance shi ma ya taba yin hajji, duk da cewa da ya taba yin hajji da ya yi kyau, amma idan ma tafiyarsa ce ta farko, kuma yana da sharuda, to zai iya zma wakili babu komai.
Na biyu: Mai wakilcin yin hajji ba dole ba ne ya kasance namiji, idan ma mace tana da sharuda kuma zata iya yin hajji daidai, to zata iya zama wakiliyar wani ko da kuwa wanda ake wakilta namiji ko mace, haka nan ma akasin haka, duk babu komai. Misali idan wata mata ta mutum kuma danta namiji ne yana son ya yi mata aikin hajji bisa wakilci to babu komai.
Na uku: Mai wakilci a aikin hajji zai yi aikin ne bisa aikin hajji a mahangarsa ba bisa mahangar wanda yake wakilta ba. Wato idan wani zai wakilci wani mamaci kan ya yi masa aikin hajji, to zai yi aikin ne bisa fatawar marja'insa ba bisa fatawar marja'in mamaci ba.
Wani misali a nan shi ne; Idan marja'in wanda ake yi wa aikin hajji yana da fatawar cewa a dawafi dole ne ya kasance tsakanin makami Ibrahim da Ka'aba, amma marja'in mai wakilci yana ganin cewa ya isa a yi dawafi ko da fasila tsakanin mai hajji da Ka'aba ta fi haka nisa, to shi mai wakilcin yana iya yin aikin hajjin bisa wannan fasilar mai fadi. Sabada me? Domin dole ne ya yi aikin bisa fatawar marja'insa.
6. Wannan shi ne takaitaccen bayani game da mas'alar da ta shafi wasu mas'aloli kafin tafiya aikin hajji, mu zamu yi nuni da wasu nasihohin gareku, muna fatan zaku bayar da hankulanku.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
Saturday, December 24, 2011