Abubuwan Haram da Kaffarori

Abubuwan Da Aka Haramta Wa Mai Harami


1. Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
Darasi Na Biyar: Binciken Hukunce-Hukunce Da Mas'aloli Da Suka Shafi Abubuwan Da Aka Haramta Wa Mai Harami Da Kuma Kaffarorinsu

Abubuwan Da Aka Haramta Wa Mai Harami
Bahasinmu game da abubuwan haram a ihrami ne, mun ce abubuwan da kaa haramta a ihrami kala uku ne: Na farko, su ne wadanda suka kebanci maza kawai; wato ga maza suke haram ne amma ga mata ba haramun ba ne; na biyu kuwa: su ne wanda suke kebanta da mata wato ga maza ba haram ba ne, na ku kuwa, su ne abubuwan da suak haramta ga maza da mata duka da aka ce wa da su "abubuwan da maza da mata suka yi tarayya a ciki"; ko da yake abubuwan da aka haramta din suan da wani kashe-kashen daban da ake kasa su a kai kamar haka; abuubwan da aka haramta wadansa suke da kaffara, da abbuwan da aka haramta wadanba ba su da kaffar wadanda daga farko mun dan yi nuni da su. Kuma akwai wani kashin ma da ake yi kamar haka ; abubuwan da suke kafin yin ihrami ma da ma haram ne yin su, sai dai bayan yin ihrami haramcinsu yana karuwa, da abubuwan da su ba haramu ba ne kafin yin ihrami, sai dai suna zama haram ne a yayin yin ihrami.
2. Mu a bayanan da suak gabata mun yi bayanin abubuwan da suka kebanci haramci ga maza da kuam abubuwan da suka suka kebanci mata, kuma mun fadi hukunce-hukunce da mas'alolin hakan, a nan kuma zamu kawo abyanin wasu daga abubuwan da aka yi tarayya da suak harama ga maza da mata ne, wadanda yawanci a kan samu cin karo da su, kuma zai iya yiwuwa su faru, ga wasu daga hukunce-hukunce da zamu yi muku bayanin su a nan.

Amfani Da Abu Mai Kanshi
Daya daga cikin abubuwan da aka haramta da ta yiwu su faru ga mai ihrami, daga ciki akwai shakar wani abu mai kanshi ko wane iri ne, kamr turare ko wani abu, hatta da cin abinci mai kanshi, ko sansana ciyayi da fulawowi masu kanshi, wanan duk hara ne a lokacin ihrami.
3. Ko dai mutum ya sanya turare ko ya sanya a tufarinsa, ko kuma ya sanay tufafin da yake da kanshi duk bai halatta ba. Don haka idan tufafin ihrami ya kasance yana da kanshi kafin a sanya shi, ko kuma wasu 'yan kwanaki kafin a sanay shi, to sai ya sanya shi a cikin rana, domin wannan kanshin ya fita, ta yadda zai kasance a lokacin sanya shi a ihrami ya zama ga shi da kanshi, don haka duk wnai amfani da wani nau'in turare yayin yin ihrami to haram ne, ko da kuwa an sanya wannan turaren kafin yin ihramii ne to a nan ma bai halatta ba.
Haka nan bai halatta a yi amfani da abinci mai kanshi ba kamar wanda yake da za'afaran, musamman ya kamata masu dafa abinci su kula da wannan, don haka lokacin dafa abinci kada su dafa abini da za'afaran kuma su ba wa mahajjata. Idan da wani yana son ya yi abincinsa da kansa, ko kuma ya samu bacewa sauran abokan tafiyarsa, kuma aka ba shi abincin da yake da za'afaran a wani wrui, to ba zai iya amfani da shi lokacin ihrami ba. Gaba daya dai mu samni cewa duk wani abu mai kanshi bai halatta ba haram ne bisa ihtiyad a lokain ihram, sai dai babu komai a ci kayan marmari da 'ya'yan itace amsu kanshi kamar tuffa. Bisa ihtiyadi bai halatta ba ga mai ihiram ya sansana su, sai dai cin su ya halattta gare shi.
4. Daga karshe awaki wata mas'alar kuam ita ce: idan mutum ya wuce wani wuri da yake da wari da doyi, an ce bai halatta ba bisa shari'a mutum ya irke hancinsa, amma idan ya yi tafiya da sauri ya wuce wurin babu wata matsala don ya yi sauri, sai dai rike hanci don kada ya ji wari haram ne.

Kallon Cikin Madubi
5. Daya daga cikin ayyukan da suak haram ga mai ihrami wadanda zasu iya yiwuwa su wakana gare shi shi ne kallon madubu, ko dayake ba kawai kallon madubuin ne haram ba, sai dai idan ya kalal don ado da yin gayra shi ne haram; idan mutum yana osn ya gyara ksansa, ko ya gayara gashin sa, ko ya gani idan akwai wani abu da ya hau kan fuskarsa, ko ya dan gyara jikinsa, wannan duka shi ne nau'in kallon da kaka haramta wa mai ihrami ya yi wa madubi; amma idan babu wannan nufin, misali mai tukin mota yayin da yake tukin motada yake son ya kalli madubi don ya ga hanya wannan ba shi da wata matsala. Haka nan idan yana da wani nufin da ban wanda bai shafin gyara jiki ba, ko kuma idonsa ya fada kan madubi, duk babu wata matsala ga hakan.
Amma wata mas'alar ita ce; shin kallon abubuwa masu haske kamar tasa ko kallon ruwa da yake iya ganin kasa a ciki su ma suan da hukuncin haram irin na madubi? Haka ne, su ma idan mutum ya kale su da nufin yin ado da gyara jikinsa, shi ma suan da hukuncin kallon madubi ne, amma idan babu wannan nufin ko kuma ganin sa ya fada kan ruwa ne, ko ya ga wasu hotuna, ko kuma ya kalla, amma ba yana son ya gayra kansa ba ne, to babu wata matsala.
Wani lokaci kuma muna shiga wani daki mai madubi, kuma ya zama dole ga mai ihrami ya kula cewa zai iya shiga daki mai madubi tun da a lokaicn yana da harami misali, kamar lift da ake shiga a gini don hawa sama, da yawanci ana yi musu madubi, ko kuma ban daki, ko wani dakin taro, ko dakin hotel, yaya ke nan game da kallon madubi? Amma idan yana da nufin kallon to akwai matsala, don haka shin idan akwai madubi a daki shin wajibi ne ya rufe shi ko kuwa? Ba wajibi ba ne, sai dai ya fi kyau ya rufe shi, tun da zai iya yiwuwa ya kalle shi.
Sai dai idan wannan madubin bai kalle shi da nufin ado ba, to babu matsala, duk da cewa ta yiwu a wasu kwanakin da masu harami suke yin ayyukan ibadarsu, masu yi musu hidima ta yiwu su sanya wani tufafi don rufe wannan madubin, to idan su ba su yi ba, to shi mai harami yana da kyau ya yi hakan, don kada kallonsa ya afda kan maduban.
6. Shin a kwanakin yin harami mutum zai iya sanya tubarau? Babu wata matsala ga sanya tubarau tun da ba madubi ba ne kuma ba shi da hukuncin madubi, don haka za a iya sanya kamarar yin hoto, da daukar film, ko kuma a dauki hotonsa, wannan duk babu wata matsala. Yanzu shin kuna gani zai iya yiwawa a dauki hoto, ko kuma a kalli kamara, ko kuma wani ya dauki hoto yayin da ake yin ihrami da ayyukan umara ko hajji, ko kuma mu daukai wani hoto, duk babu wata matsala a nan. Wannan ba shi da hukuncin madubi, kuam babu wata matsala ga wannan yayin haram da umara ko hajji.
7. Kallon madubi ba shi da kaffara sai dai duk wanda ya kalli madubi to bisa ihtiyadi sai ya ce "Labbaik", kuma wannan idan ya kasance bisa gagnganci ne. kuma mun riga mun fada cewa duk wani abu na haram da mai haram ya yi da gaban, to haram ne kuma yana da zunubi, wani lokaci akwai kaffara, wani lokaci kuma babu kaffara idan ba da gangan ba ne, misali bai kula ba, kuma ya kalli mafubi, haka ma har ya gyara gashin kansa, haka nan sai kawai ya lura cewa yana kallon madubi, wannan bai yi laifi ba, kuma babu kaffara, duk da cewa kallon sa ga madubi ba shi da wata kaffara, sai dai ihtiyadi ne cewa idan ya kalli madubi to bayan nan sai ya ce "Labbaik".

Sanya Zobe Don Ado
8. Sanya zobe don ado yana daya daga cikin ayyukan da suke haram ne yayin ihrami, kuma ta yiwu ya faru ga mai harama. Kuma ya zama wajibi ne bisa ihtiyadi a nisance hakan, wato bai halatta ba a sanya zobe don ado yayin harami. Amma sanya zobe kamar akik don neman lada da mustahabbanci, ko kuma wani tsohon zobe da ba shi da wani ado da ake gani game da shi, to duk babu wani hani kan hakan. Haka nan zoben da ma can yana da shi kamar wata mata ko wani namiji da da ma can yana da zobe a hannuns, to shi ma ba wajibi ba ne ya cire shi yayin harami ko da kuwa yana da hado, kuma babu hani ga hakan, wato ba dole ne ya cire shi ba.

Sanya Mai A Jiki
9. Sanya mai a jiki yana daga abubuwan da aka haramta su ga mai yin aikin harami, ko da kuwa ba mayuka ne masu kanshi ba kamar mai sanya fata fari, ko masu ado ba, to duk bai halatta ba ko da kuwa babu ado. Ko dai yaya ne dai duk wani mai bai halatta ba a yayin yin harami da umara ko hajji, kuma babu bambanci ko yana da kanshi ko babu kanshi, sai dai idanyana da aanshi to laifi biyu ne ke nan; daya na sanya mai a jiki, dayan kuwa shi ne na amfani da wani abu mai kashi wanda daga farko mun yi magana a kansa. Idan ya kasance yana da kanshi to yana da kaffara ke nan, don haka bisa ihtiyadi sai ya bayar da kaffarar tunkiya/rago ke nan, amma idan mai ne ya sanya a jikinsa wanda ba shi da kanshi to babu wata kaffara a kansa.
10. Tambaya: Idan wani yana da matsalar fata, ko kuma ba zai iay zama kasan rana ba, kuma likita ya gaya masa dole ne ya yi amfani da mai, shin hakan haram ne ko kuwa? Amsa: idan ya zama dole ne babu yadda zai yi sai ay yi amfani da mai babu komai na zunubi a kansa, kuma idan ba shi da kanshi ma babu kuma kaffara a kansa, amma idan yana da kanshi to sai ya bayar da kaffara ko da kuwa ya sanya shi ne sakamakon rashin lafiya da larura, don haka idan haka ne sai ya bayar da kaffrar tunkiya/rago bisa ihtiyadi, da zai ba wa talakawa naman ta.
11. Amfani da mai da sauran mayukan shafawa a lokacin larura kamar wanda yake da matsalar fata da rashin lafiyar fata, ko kuma wanda yake da matsalar yanayi mai zafi da jikinsa yake yin gumi duk haram ne; misali idan zai iya amfani da hoda maimakon mai, sai ya ki shafa mai ya yi amfani da hodar, tun da wani lokaci a kan samu abin da zai maye gurbin wannan man. Amma idan babu wani abu da zai zama a maimakonsa to babu yadda zai yi sai ya yi amfani da shi, kuma bai yi sabo ba.
Sai dai shin akwai kaffara a kansa ko babu?
12. Amsa ita ce babu kaffara kansa, matukar dai wannan man ba shi da kanshi, amma idan yana da kanshi to bisa ihtiyadi wajibi sai ya yi kaffara, wato ya yanka tunkiya/rago.
Tambaya a nan kuam ita ce: Shin cin mai lokacin harami - kamar abin ci mai yawan maiko da kitse- duk haram ne ko kuwa?
13. Cin mai a lokacin harami ba haram ba ne, kuma ba shi da wata matsala.
Amma idan yana da kanshi fa?
Amma idan yana da kanshi kamar yadda muka fada a baya ne cewa; yin amfani da abu mai kanshi ko da kuwa abinci ne, to haram ne. kuma sau da yawa mai ba shi da kanshi shi a kansa, don haka ba his da wata matsala, don haka cin mai ko abinci mai maiko a lokacin harami ba haram ba ne, abin da yake haram shi ne shafa mai a jiki, sai dai inda aka toge.

Cire Gashin Jiki
14. Cire gashin jki yana daga daya daga ayyukan harami da suka haramta ga maza da mata duka, kamar cire gashi, da tsige shi, da jansa, da sanya reza ko aska; kadan ne aka fitar ko da yawa, daga jikinmu ne ko daga jikn wani ne, don haka bisa ihtiyadi sai mu yi hankali kada mu fitar da gashi daga jikinkmu, ko kuam daga jikin wani.
Idan da wani ya sanya hannu a kansa ya sosa sai ya yi tsammanin gashi ya fita ba tare da ya kula ba, ba dole ba ne ya duba ya gani shin gashi ya fita ko kuwa! Ko kuma lokacin yin alwala ko wanka, misali mahajjata ko masu umara sai su yi alwalarsu ko wankansu kamar yadda suak saba, kuma da wani gashi zai fita suan yin wanka ko alwala to da babu komai. Amma wanda ya fitar da gashi ko ya tsige shi ko kamar don ado ya cire gashin da ya karu a wani wuri, to duk wannan haram ne, kuma ya wajaba ya nisanci yin hakan.

Sanya Kwalli
15. Sanya kwalli yana daga cikin ayyukan da suak haramta bisa ihtiyadi ga maza da mata yayin harami. Haka nan sanay shi a gefen idanuwa shi ma haram ne, babu bambanci kuma tsakanin bakar kala da sauran kaloli.
16. Ko da yake sau da yawa a lokacin harami ba ya faruwa wani ya sanya kwalli ko ya yi ado, sai dai wani abu ne mai yiwuwa ya faru.

Yanke Akaifa
Yanke akaifa yaan daga cikin abubuwan da suke haram yayin harami, akaifar ahnnu ce ko ta kafa, kuma da ko mene ne aka yanke ta, kamar almakashi, ko abin yanke akaifa, da sauran duk wani abu, kai ko ma tsige shi ne aka yi. Wasu mutane suan da dabi'a mummuna ta yanke farcensu da hakora, wannan duka haram ne a yayin yin ihrami da harami. Haka nan cire farcen wani mutum shi ma haram ne, don haka don haka mai harammi ba zai iya yanke wa wasu akaifarsu ba.
17. Tambayar da takan zo game da yanke sumar kai ita ce: shin wanda yake mai harama zai iya aske gashin wani ko kuwa? Kamar yadda muka ce ba zai iya yanke sumar kan wani ba, aski ne ko rage suma duka biyu bai halatta gare shi ba. Don haka cire gashi daga jikin wani gare shi bai halatta ba, kuma ba zai iya yin sa ba, kuma wannan mutumin ko mai harama ne ko maras harama da umara ko aikin hajji duk bai halatta ba; misali wanda yake da harami kuma yana son ya gyara gashin wasu to ba zai yiwu ba. Ko da yake yanke akifarmu haram ne, amma cire akaifar wani ba haram ba ne; duk da cewa ba kasafai haka yake faruwa ba sai dai a yanke sumar kai. Don haka idan mun cire akifar wani ba haram muka yi ba, haka nan idan ya zama tilas muka cire akaifarmu da take damun mu, to idan muna son mu cire ta babu wani abu ko da lokacin harami ne, haka nan ma maras lafiya da aka ce ya cire akifarsa, shi ma ya hau kansa ya cire ta, kuma idan ya cire babu komai.

Fitar Da Jini Daga Jiki
18. Fitar da jini daga jiki yana daga cikin abubuwan da suka haramta ga mai harami, don haka sai a kiyaye cewa kada a ji wa jiki ciwo kada jini ya fita daga jiki, kuma wannan yana daga haram bisa ihtiyadi wajibi. Amma sosa jiki idan dai jini bai fito ba, to babu komai, haka ma lokacin day zama dole ne mutun ya fitar da jini kamar idan ya yi rashin lafiya, kuma asibiti likita ya dauki jininsa shi ma babu komai a kansa musamman idan dan binciken lafiyarsa ne.
19. To wata tambayar ita ce; yaya cire hakori yayin harami? Amsa: idan dai jini zai zubo to haram ne, amma idan jini ba zai zubo ba, to babu komai a kan hakan, kuma a fatawar sayyid fitar da hakori da jan hakori duk ba sa cikin haram, misali idan hakori ya rube kuma fita da shi yaan da sauki kuma jiniu ba zai zubo ba idan an fitar da shi to duk wannan ba ya cikin ayyukan haram ga mai harami. Amma idan jan hakori da fitar da shi zai kasance sababin fitar jini, to wannan yana daga cikin haram.
Sai dai zai iya yiwuwa a ce ai hakorin da ba ya zafi ba a cire shi, don haka hakorin da yake yin zafi ne kawai ake cirewa wanda ya zama dole ne a cire shi. A nan sai mu ce idan ya kasacne haokori yana zafi kuma ya kasance ya zama dole a cire shi don magani to babu komai a cire shi ko da kuwa jini zai fito, babu komai, kuma ba a lissafa shi cikin abubuwan da aka haramta.

Fasikanci da Jidali
20. Fasikanci yaan daga cikin abubuwan da ba ka safai ake samun su a lokacin harami ba in Allah ya so; shi yana nufin idan wani ya yi karya a lokacin yaan harami, ko ya yi zagi ya yi batanci ga wani, ko ya yi alfahari da cika baki, wadannan duk wasu abubuwan da aka haramta ne ga mai harami. Ta yiwu wasu su ce wannan ai kafin yin harami ma haram ne yin su. Haka ne, sai dai a lokacin yin harami laifinsu da zunubinsu yana karuwa sosai ne.
Jidali yana daga cikin abubuwan da ba ma fatan su faru tare da ku a lokacin harami, idan mutum ya yi shi kamar ya yi rantsuwa da Allah, kamar wallahi kaza, wallahi ba haka ba ne, da suaran su, to idan ya yi rantsuwa da Allah haram ne, amma idan dai bai yi rantsuwa da sunan da ya kunshi kalmar Allah ba shi ma dai bisa ihtiyadai haram ne.
Amma idan ya yi rantsuwa da wasu abubuwa masu tsarki kamar kur'ani da sunan ma'asumai da sauran su wannan bai dace ba, sai dai ba haram ba ne yayin harami.

Cire da Yanke Shukar Harami
21. Cire da yanke shukar harami shi ma haram ne, don haka a garin makka akwai iyakokin da ake kiran su iyakacin haram ne wanda akan samu zanen su, kuma suan da hukunci na musamman. Wannan yankin shuke-shukensa da dabbobinsa duk suna da wani hurumi na musamman da aminci, don haka bai halatta wani ya yi farautar su ba, ko kuma ya cutar da su.
Wadannan iyakokin sun hada da Tan'im, Hudaibiyya, Ji'irranata, da Wadi Arana.
Shukokin da suka girma da kansu da ciyayin da suka fito da kansu su ne cire su da yanke su yake haram, amma shukar da mutum ya shuka da ciyayin da ya dasa kamar kayan kore wadannan duk babu haramci mutum ya yanke ko ya cire kayansa.
Don haka abubuwan da aka toge daga wannnan hukunci sun hada da shukar 'ya'yan itaciya da ake ci, dabino da aka shuka da kayan korra da aka dada ko shuka, duk babu komai. Amma shuka da ciyawar da ita da kanta ne ta fito ta tsiru, to cire ta ko yanke ta bai halatta ba. Hatta da kayoyi da sauran busassun shukoki da suka fito a duwatsu cire su bai halatta ba, su ma suna daga cikin abubuwan da aka haramta cire su a harami.
22. Yana da kyau mu san cewa wannan haramcin na cire ko tsige ko yanke shuka da ciyawar harami bai kebanci lokacin ihrami ba, don haka duk wanda yake mai harami ko ba mai harami ba, bai halatta ya cire ciyawa ko shukar haram ba.
Saboda haka wannan haramcin ya shafi duk wanda yake harami ne, kuma duk wanda ya tsinci kansa a harami ko bai harama da umara ko hajji ba ne, to bai halatta ya cire shuka ko ciyawar da ta fito da kanta a harami ba.

Farautar Dabbobin Sahara
Farauntar dabbobin shahara yana daga cikin abubuwan da suka haramta. Dabbobin harami suan da kima da daraja. Ta yiwu wani yana da harami amma ba harami yake ba, yana wajen haram ne, to shi ma bai halatta ya yi farauta ba. Haka nan wanda yake ba mai harami ba amma yana cikin yankin harami, shi ma dai bai halatta ya farauci dabbobi ba, wani lokaci kuma dabbobi ne kamar kwari sukan zo kamar fari, to nan ma sai a yi hankali kada a kama su, kada a farauce su, kada a karya su, kuma wasu dabbobin kamar kudan zuma da sauran kwarin da ba sa cutar da mutum, ba sa cutarwa, su ma ba a kashe su. Sai dai idan suak cutar kamar kudan zuma yana son ya yi cizo, to kashe su ba shi da wata matsala.

Haramcin Mata da Maza ga Junansu
23. Haramcin maza da mata ga junansu yana daga ckin abubuwan da suka haramta ga mai harami. A dunkule muna iya cewa jin dadi saboda kulla aure da yake halal kafin sanya harami, to bayan harami haram ne yin sa. Sai dai ba ana nufin cewa mace da miji sun zama ajnabi ga junansu ba, sai dai sun haramta ga juna ne ta fuskancin jiyar da junansu dadi, don haka suna iya ganin jikin juna, ko mace ta zama ba ta da lullubi ga mijinta a daki da suke tare. Kuma za ma su iya rike hannun juna a hanya idan suna tafiya idan ba da niyyar jin dadi ba ne. Don haka neman jin dadi shi ne haram wanda kafin sanya harami halal ne da yake zama haram yayin sanya harami. Wannan su ne bayanai a takaice da suak shafi abubuwan da suka haramta ga mai harami da sau da yawa suna iya faruwa.

Kaffarar Aikata Abubuwa Haram
24. Amma kaffarar abubuwan da aka haramta kamar yadda aka sani da can mun ce wasu abubuwan da aka harmta suna da kaffara da muka ce a wani kashin ana kasa su gida biyu ne: wato abubuwan da aka haramta masu kaffara da marasa kaffara. Mun bayar da alkawari cewa zamu yi bayani game da kaffarori.
Bayani a nan shi ne ba fatan muke wani ya yi abin da zai kawo masa yin kaffara ba, amma idan wani ya yi kamar ya kalli madubi bisa rafkanwa, ko ya shaki kanshi, ko ya yi tafiya karkashin inuwa, idan duk bisa rafkanwa ne to babu kaffara. Da fatan da gangan ma ba zaku yi wadannan ayyukan ba, ta yadda zasu sanya muku daukar lokacin ku domin yin kaffara.
Ko da yake mun yi nuni da wasu kaffarorin amma idan wani ya yi wani abu da zai kawo masa yin kaffara to sai ya koma wa littafin fikihu domin ya ga me malamai suka kawo game da amsar kaffararsa sai ya yi aiki da wannan.
25. Sai dai kaffarar wajibi idan ta kasance yanka dabba ne kamar rago/tunkiya to dole ne ya yanka a nan Mina, sai dai idan bai samu abin yanka ba, ko kuma ba zai iya yankawa ba, misali bai samu talakawa da zai iya raba musu naman ba a nan Mina, to sai ya yanka a kasarsa, ya ba wa talakawa dukkan naman da masu neman bukatu.
Sai dai ba dole ba ne ita wannan abin yankan ta kasance tana da sharudan abin yanakn layya, wato kamar bkada ya zama ramamme, ko maras lafiya. Don haka ko da kuwa ramamme ne, ko karami babu matsala, amma idan ya zama mai kiba to ya fi.
Kuma lallai ne a kula cewa dole ne a yanka da niyyar yin kaffara, kuma dukkan naman ne za a rabar hatta da kafa da kai da kayan ciki kamar hanta dole ne a bayar da su ga talakawa da masu neman taimako.
Wassalamu alaikum wa rahmatul-Lah!
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
Sunday, January 15, 2012