Haramar Hajjin Tamattu'i


Darasi Na Tara: Bayanin Hukunce-hukunce da Mas'alolin da Suka Shafi Haramar Hajjin Tamattu'i

Mas'alolin Haramar yin Hajjin Tamattu'i
Bayan mun kammala umara, mun saurari zuwa ranakun Hajji Tamattu'i a Makka, mun gama wadannan kwanakin sai mu yi haramar kuma yin Hajji Tamattu'i.
1. Kamar yadda muka fara yin ayyukan Umarar Tamattu'i da yin harami, haka nan muke fara ayyukan hajji da yin harami.
Akwai mas'aloli uku game da hakan game da yin haramin Hajji Tamattu'i kamar haka: na farko zamanin yin harami, na biyu wurin yin harami, na uku yadda ake yin haramin.

Lokacin Yin Harama
2. Duk sa'adda mutum ya kammala ayyukan umara yana da damar ya yi haramin yin aikin Hajji Tamattu'i inda na ya so, sai da an fi so ya yi shi ranar takwas ga wata zulhijja da aka fi sani da ranar "Tarwiyya", ranar tara ga wata ana kiran ta ranar "Arfa", rana goma kuma ana kiranta ranar "Idi".
3. Bayan mun yi harami a Makka sai mu kama hanya don zuwa Arfa da za a yi ayyukan ta gobe ranar tara ga wata. Ayyukan da zamu yi bayan yin harami sun hada da: Zama da kasance a ranar tara a filin Arfa, sannan kuma sai Tsayuwar Mash'arul Haram a daren ranar idi, sai kuma da safe ranar Idi mu je Mina mu yi jifa, mu yi yanka, mu yi aski ko rage suma. Bayan mun gama wadannan ayyukan ne sai mu zauna a Mina don ayyukan daren sha daya ga wata, da ayyukan sha biyu ga wata wanda shi ne kwana a Mina wanda yake daga cikin ayyukan hajji, sai kuma jifan shedan a ranar sha daya da ranar sha biyu. Bayan an yi sallar azahar a ranar sha biyu sai mu kama hanya zuwa Makka don mu yi sauran ayyukan da suka rage na ayyukan hajji da suka hada da: dawafin hajji (dawafin Ifadha), sai sallar dawafin hajji, sai sa'ayi tsakanin Safa da Marwa, sai kuma dawafin mata, sai sallar dawafin mata.
4. Idan mutum ya samu damar yin wadannan ayyukan na Makka ranakun Mina zai iya dawowa Makka ranar Idi bayan jifa sai ya yi wadannan ayyukan, ko kuma ya dawo ranar sha daya ko ranar sha biyu ya yi su. Idan bai samu damar yin hakan ba, sai ya bari sai ya dawo daga Mina zuwa Makka baki daya sai ya yi su. Don haka sai mu fara ayyukan hajji da yin talbiyya.
5. Labbaikal lahumma labbaik, labbaika la sharika laka labbaik, innal hamda wan ni'imata laka wal mulk, la sharika laka labbaik.
6. Wannan shi ne lokacin yin harami, sai dai mutum yana da ikon yin haraminsa ranar biyar, ko shida, ko bakwai, kuma ya yi, sai dai zai zama cikin harami ta yadda duk abin da ya haramta ga mai aikin hajji ya haramta kansa, haka nan yana iya yin haraminsa ranar Arfa da safe idan ya san zai iya isa zuwa Arfa kafin azahar.

Wuri da Yadda Ake Yin Harama
7. Makka ita ce wurin yin haramin Hajji Tamattu'i: duk inda mutum yake a Makka kamar gidansa ko hotel zai iya yin haraminsa, ko da yake an so idan zai iya zuwa sai ya fara daga masallacin ka'aba mai alfarma sai ya yi harama daga can ya yi talbiyya. Sai dai zuwa masallacin ka'aba ranar takwas yana da wahala matuka da cunkoso, sai mu yi haramin daga hotel ko gidanmu sai mu kama hanyar Afrfa. Kuma babu bambanci tsakanin tsohuwar Makka da sababbin unguwannin Makka a yau.
8. Amma yadda ake yin haramin hajjin ba shi da wani bambanci da yadda ake yin haramin umara. Kuma wajiban harami su uku ne:
1- Sanya tufafin harami
2- Niyya
3- Talbiyya
Bambancin umara da hajji a gun yin harami a nan a cikin niyya ne kawai, a can mun yi niyyar umara, amma yanzu zamu yi niyyar yin hajji ne, wannan shi ne kawai bambancin. Domin duk abin da yake wajibi a can a nan ma wajibi ne, kuma duk abin da yake mustahabbi ne a can, to a nan ma mustahabbi ne. Kamar mustahabbancin yin wanka, da kasancewar ihrami bayan sallar wajibi ko bayan wata sallar mustahbbi, ko mafi karanci bayan raka'a biyu na mustahabbi.
9. Tufafin yin harami kamar yadda aka yi bayani ne cewa maza ba sa sanya wani abu dinkakke.
Mata suna yin harami da tufafinsu da suka saba ne na gida, ba muhimmi shi ne tufafinsu ya zama fari ba, duk da wasu matan suna sanyawa sai dai muhimmi shi ne tufafinsu ya zama mai tsarki kuma na halal kamar dai sharuddan tufafin salla, sai kuma karin sharadin cewa ka da ya kasance zallan alhariri ne.
10. Mahajjata suna sanya tufafi da niyyar yin harami sai su yi harama da fadain labbaika su shirya wa yin ayyukansu na hajji.
11. Labbaikal lahumma labbaik, labbaika la sharika laka labbaik.
12. Maimaita fadin labbai shi ma mustahabbi ne kamar na Umarar Tamattu'i, idan mutum bai iya ta baki daya ba, sai ya yi ta maimaita wannan fakarar da muka kawo a sama, idan ita ma ba zai iya ta ba, sai ya yi ta maimaita fadin "Labbaik" kawai. Fadin labbaik mustahabbi ne a yi ta maimaita shi har azahar din ranar Arfa. Idan azahar ta yi shi ke nan sai a dakatar da fadin labbaik. Idan an lura a umara mun ce da an hango gidajen garin Makka ne za a dakatar da fadin labbaik, to a hajji kuwa da azahar din ranar Arfa ta yi ne za a dakatar da fadin labbaik.

Tsayawa a Arfa
13. Bayan yin harami sai zuwa Arfa don yin ayyukan Hajji Tamattu'i.
14. Mahajjata suna Tsayuwa a Arfa wanda shi ne abu na biyu na aikin Hajji Tamattu'i. zamu yi magana kan mas'aloli uku ne game da tsayuwa a Arfa da suka hada da: ma'anar tsayuwa, wurin tsayuwa, zamanin tsayuwa.
15. Tsayuwar Arfa yana nufin halarta gun Arfa a wani wuri a wannan wuri da ake kira Arfa, kuma babu wani aiki da yake wajibi sai halartar wannnan wurin kawai. Sai dai akwai abubuwa masu yawa da suke mustahabbi ne yin su da ya hada da zikirori da addu'o'I da suka zo a littattafai, wadanda suna da lada mai yawan gaske, da gina ran mutum da gyara badininsa.
16. Tsayuwa a nan yana nufin wurin tsayuwa ke nan, wato wannan saharar ta Arfa wacce tana da iyaka da aka sanya mata yalon allon sanarwa da yake nuna iyakarta da farkon Arfa, da kuma karshen Arfa. Kuma mu sani babu damar fita daga wannan iyakar ta Arfa kafin faduwar rana, don haka ko da mutane sun fara tafiya don su fita, amma ka da su sake su fita daga wannan filin na Arfa kafin faduwar rana.
17. Mutanen da suke da larura kamar rashin lafiya su ma dole ne su halarci wannan wurin na Arfa ko da wasu 'yan mintina ne sannan su mayar da su gari, domin halartar Arfa yana daga rukunai wajibai na aikin hajji, kuma ba a iya wakiltar mutum a kansa.
18. Lokacin tsayuwar Arfa daga azahar ne zuwa faduwar ranar tara ga watan zulhijja a matsayin daya daga ayyukan hajji.
19. Kuma tun da wannan aikin ibada ne, dole ne ya kasance da niyyar ibada, kuma jin cewa mahajjaci ya zo ne wurin ya tasya daga azahar zuwa magariba don biyayya ga umarnin Allah ya isa matsayin niyya ba sai ya fada da baki ba.
20. Kasancewa a wurin shi ne muhimmi, don haka tsayuwa ko zama ko tafiya ba shi ne muhimmi ba, ko da ma mun yi bacci wani dan lokaci duk ba shi da matsala, sai dai akwai mustahabbai masu yawa da aka so yi a wurin.

Wasu Mas'aloli Da Mustahabban Tsayuwa A Arafa
Ranar Arfa tana da falala mai yawan gaske, da addu'o'I da zikirori, daga ciki akwai yin azumi, sai dai idan mutum ya san idan ya yi azumi zai samu rauni wurin yin addu'a da zikirorinsa to sai ya fasa azumin ya shagaltu da ibadojinsa. Kuma ruwaya ta zo cewa wanda ba a yafe masa ranar lailatul kadri ba, to ranar Arfa zai iya samu idan ya dace, idan kuwa bai samu ranar Arfa ba, to babu wani fatan samu sai kuma wata lailatul kadri din ko wata Arfa.
21. Akwai addu'o'I masu yawa da suka zo a wannan ranar kamar addu'ar Imam Husain (Tsira da amincin Allah su tabbata gare shi, da zuriyarsa da kakanninsa masu daraja) da addu'ar Imam Aliyyu Zainul-abidin (Tsira da amincin Allah su tabbata gare shi, da zuriyarsa da kakanninsa masu daraja), sai kuma neman gafara da tuba daga zunubai da sauran su, farin ciki ya tabbata ga wanda aka yafe masa a wannan ranar.
22. Daga nan Arfa kuma sai a kama hanya lokacin faduwar rana zuwa Mash'arul Haram wato Muzdalifa domin yin wani aikin na wajibin Hajji Tamattu'i wato tsayuwa a Muzdalifa.

Tsayuwa a Mash'arul Haram
Bayan mun yi sallar magari da issah sai kuma mu kama hanyar zuwa Mash'arul Haram wato Muzdalifa, zamu ga allon sanarwa a wurin an sanya Farkon Muzdalifa, karshenta kuwa an rubuta Karshen Muzdalifa. Sai ma kwana a wurin, kuma daga kiran sallar asuba zuwa bullowar rana ne zamu niyyar ibada ga Allah, bayan mun yi sallar asuba mun dakata a wurin har sai rana ta fito sannan ne zamu iya barin wurin don mu kama hanya zuwa Mina, fadin niyya da harshe ba dole ba ne, shi wannan nufin ya wadatar, kuma za mu iya barin wurin ne bayan ranar goma ga wata ta bullo sai mu kama hanya zuwa Mina.
Ladubba Da Mustahabban Tsayuwa A Mash'arul Haram
23. A nan ma akwai mustahabbai masu yawa da za a yi a wannan filin kamar yawaita ambaton Allah da fadin "Allahu Akbar! La'ilaha illallah! Subhanan Lah!". Sannan cintar duwatsun da za a yi jifar shedan a ranar goma da sha daya da sha biyu yana daga mustahabban wannan wurin. Haka nan wanda bai cinta daga nan ba, har sai da je Mina tukun ko Makka sannan ya tara duwatsun jifar shedan shi ma babu wata matsala.

Lokacin Tsayuwa a Mash'arul Haram Da Mas'alolin Da Suka Shafi Hakan
24. Mun riga mun ce lokacin tsayuwar Muzdalifa daga bullowar alfijir ne, wato kiran asuba zuwa bullowar rana, kuma babu halin barin wurin don tafiya Mina matukar rana ba ta bullo ba. Sai dai wasu mutane suna iya barin wurin kafin wannan lokaci cikin dare akamakon su mata ne ko kuma suna da uzuri. Mata su suna iya tafiya ko 'yan mata ne, ko tsofaffi, suna jin tsoron kada a bar su a baya ne ko ba su da wannan tsoron duk suna iya tafiya matukar mata ne. Sai kuma tsofaffi masu raunin jiki da rashin kwarin jiki, da kuma marasa lafiya. Su duka wadannan da dare da sun shigo Mash'arul Haram suka dan tsaya da niyyar tsayuwa a Muzdalifa to wannan ya wadatar musu, suna iya sucewa zuwa Mina. Da duka wadannan sun shigo kafin rabin dare, kuma suka dan tsaya da niyyar tsayuwa a Muzdalifa to ya yi hakan, suna iya tafiya zuwa Mina.

Ayyukan Mina a Ranar Idi
25. Bayan rana ta bullo ranar Idi sai mu tafi Mina mu yi ayyukan wannan ranar da suka hada da: Jifan bangon Akaba kawai, yanka layya, aski ko saisaye, kamar yadda muka fada a baya.
Wadannan bayanai zamu kawo muku su game da ayyukan Mina in Allah ya so.
Wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh.

Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
Thursday, April 12, 2012