Kwanakin Mina


Darasi Na Goma Sha Daya: Mas'alolin Da Suka Shafi Mina

Ayyukan Ranar Idi
Bayan mun yi ayyukan ranar idi da suka hada da jifan Akaba, yanka, aski, bayan nan duk wani abu da ya haramta gare mu zai zama ya halatta ke nan, in ban da abubuwan da muka yi nuni da su a baya na amfani da abubuwa masu kamshi, da kuma jima'in miji da mata.
1. Abubuwan da aka haramta na hajji su ne dai abubuwan da aka haramta su a umara, don haka ba zamu tsawaita lokaci wurin maimaita su ba, sai a koma a duba. Mun kawo bayanin cewa wasu suna da kaffara wasu kuwa ba su da kaffara, masu kaffarar ma mun ce idan da gangan ne aka yi kawai suke da kaffara in ban da farauta, ita farauta ko da gafala da rafkanwa ne aka yi farauta to akwai kaffara. Ana iya dubawa a inda muka yi bayanai a kan haka dalla - dalla.
2. Bayan ayyukan ranar Idi guda uku da muka kawo su, sai kuma sauran wajibai da muke da su a Mina shi ne kwana daren sha daya da jifan amudai uku da rana, da kuma kwana daren sha biyu da jifan amudai uku shi ma da rana, wadannan su ne wajibai da suka rage a Mina.
3. Ayyukan wajibi na hajji a ranakun 11, da 12, su ne kwana a Mina.

Kwana
Akwai abubbuwa uku da suka shafi kwana da suka hada da: ma'anar kwana, da zamanin kwana, da wurin kwana
Zamanin Kwana
Kasancewa a Mina da daren sha daya da sha biyu ga watan zulhijja shi ne ake nufi da kwana a Mina, ta yiwu mahajjaci ya yi bacci, ko ya kasance a farke duk dai muhimmi shi ne ya kasance a wurin, sai dai an so ya amfana da kasancewa a wannan wurin da yin ibadoji da ambaton Allah da karanta kur'ani.
4. Lokacin kwana a Mina shi ne rabin dare, ko dai farkon dare zuwa tsakiyarsa, ko kuma daga rabin dare zuwa karshensa dole ne mahajjaci ya kasance a wurin cikin biyun nan, don haka da mahajjaci ya fita zuwa Makka ko wani wuri dole ne ko da ya dawo kafin faduwar rana zuwa rabin dare ya kasance a wurin, in ya so sai bayan rabin dare ya kasance yana da damar zuwa duk inda yake so, ko kuma ya dawo kafin rabin dare sai ya kasance a Mina daga rabin dare zuwa karshensa.
5. Kwanan Mina yana daga ayyukan wajibi na hajji, don haka dole ne ya kasance da niyyar ibada ga Allah kamar sauran ayyukan hajji da umara. Kuma jin cewa zai kasance a wurin don ibada ga Allah wannan ya isar, don haka ba sai ya yi lafazi ba kamar yadda ya gabata a sauran ayyukan da muka yi bayani baya.
6. A Mina babu wani wajibi ne da ya hau kanmu sai kwana a wurin kawai. Sannan kamar yadda muka kawo cewa ba dole ba ne mutum ya kasance a farke, yana iya yin baccinsa, ko zama, ko tafiya, ko hutawa, sai dai an so ya yi ambaton Allah a wannan wurin kamar yadda ya gabata.

Masu Uzurin Kwana
7. Sai dai akwai mutanen da suna iya barin kwana a Mina; wadannan kuwa su ne wadanda zasu iya zuwa Makka su kwana suna ibada suna masu shagaltuwa da ita tun farkon dare har karshensa, kuma babu wani abu da zasu yi sai ibada kawai. Kamar suna iya zuwa su yi dawafin hajji ma da sallar dawafi da sa'ayi da makamantansu kamar karanta Kur'ani da sallar rauwa, da sallar mustahabbi, da addu'o'i, da sauran ayyukan da suke na wajibi ko mustahabbai, suna iya kasancewa a masallaci mai alfarma, ko a gidajensu, ko hotel, da sauran su, muhimmi shi ne ya kasance a gari Makka, kuma da wani bangare na lokacinsa ya kasance a hanya tsakanin Mina da Makka ne to wannan bai yi ba, dole ne ya kasance ya isa Makka tun farkon dare har karshensa.
8. Don haka abin da zai iya zama makwafin kwana kawai shi ne shagaltuwa da ibada, ta yiwu wani lokaci bacci ya rinjaye shi, to sai ya daure ka da ya sake ya tafi cikin bacci, amma da yana cikin karatun Kur'ani sai bacci ya rinjaye shi amma sai ya farka da sauri duk ba komai, muhimmi dai shi ne ka da ya yi bacci bisa zabinsa haka kawai. Sai dai yana iya zuwa domin jadda alwala a tsakiyar ibada wannan ba komai a ciki.
9. Sai kuma marasa lafiya da ba zasu iya zuwa Mina ba, ko suna kan gadon asibiti, su ma ba sai sun kwana a Mina ba.
Sai dai tambaya ita ce: shin zasu iya sanya wani ya wakilce su ya kwana kamar rabin dare maimakon su, rabi kuma ya yi nasa ko kuma wani mutum daban? Amsa a nan shi ne hakan ba zai yiwu ba. Domin kwana a Mina, da tsayuwa a Mash'ar, da tsayuwar Arfa, wadannan abubuwa guda uku ba a iya wakilta wani a kan yin su, don haka mahajjaci ba zai iya wakilta wani ya yi masa su ba. Don haka idan maras lafiya yana kan gadon asibiti ne, ko mai jinyar maras lafiya ko da kuwa shi ba mai rashin lafiya ba ne, ko maras lafiyar da ba shi da wani mai kula da shi ko da ba a asibiti yake ba, ko mai duba marasa lafiya ne da shi ma mahajjaci ne, duk irin wadannan mutane idan sun bar kwana a Mina ba su da wata matsala.
10. Haka nan wanda yake da kaya masu yawa ko na guzuri ko wata dukiya mai yawa da yake jin tsoron idan ya tafi Mina za a iya sace ta, kuma ba zai iya daukar kayan tare da shi ba zuwa Mina don ya kiyaye ta, ba kuma zai iya ba wa wani ajiya ba, to wannan ma zai iya barin kwanan Mina, duk da ba safai ake samun wannan irin yanayin ba.

Jifan Shedan (Bangwaye)
11. Kwana daren sha daya da daren sha biyu duka wajibi ne a Mina kamar yadda ya gabata, haka ma ranar sha daya da ranar sha biyu dole ne a yi jifan amudai guda uku (wato bangwaye guda uku a yau) a jere da za a fara da jamrar farko, sai ta tsakiya, sannan sai a jefi jamrar Akaba, kowanne da duwatsu guda bakwai.
12. Lokacin Jifan dukkan jamrori (bangwaye) guda uku ranar sha daya da sha biyu daidai yake da lokacin da aka fada na ranar idi da ake jifan Akaba kawai ita kadai, wato daga bullowar rana zuwa faduwarta ne.
Sai dai mu lura cewa ranar sha biyu bayan azahara akwai cinkoso mai yawan gaske saboda kowane mahajjaci yana son ya kammala ya wuce, kuma wasu mazhabobin na musulmi suna ganin jifa a ranar sha biyu bayan azahar ne, don haka wanda yake son ya kauce wa wannan cunkoson sai ya gaggauta da sassafe ya je ya yi jifa da zarar rana ta bullo.
13. Sharuddan duwatsun jifa su ne wadanda muka yi bayani game da jifan Akaba ranar idi, a ranar sha daya tun da su ukun duka za a jefa kowanne sau bakwai, don haka muna jefa duwatsu ishirin da daya ke nan a ranar sha daya haka ma ranar sha biyu kowanne sau bakwai. Idan mahajjaci ya jefa tsakuwa bakwai a lokaci daya a tare to ana lissafa shi a matsayin jifan tsakuwa daya ne, don haka dole ne a jefa su daya bayan daya.
Sannan mun yi nuni da cewa idan mai jifa ya samu shakkun cewa ya kai bakwai ko bai kai bakwai ba, to sai ya kara jifan ta yadda zai samu yakini cewa ya kai duwatsu guda bakwai.
Bayan mun yi kwanan daren sha daya, mun yi jifan amudai (bangwaye) guda uku a ranar sha daya kowanne da duwatsu bakwai, kuma mun yi kwanan daren sha biyu, mun yi jifan amudai guda uku a ranar sha biyu kowanne da duwatsu bakwai, bayan azahar ranar sha biyu sai mu bar Mina mu koma Makka don yin sauran ayyukan da suka rage mana.

Wasu Mas'alolin Mina da Jifa
14. Idan mutum ya ki barin Mina a ranar sha biyu har rana ta fadi, to ya zama wajibi ya sake kwana a Mina, kuma idan ya kwana dare na sha uku, ya zama wajibi a ranar sha uku kafin ya bar Mina ya je ya yi jifan wadannan amudai guda uku.
15. Akwai wasu bayanai masu muhimmanci da suka rage da ya kamata mu kawo muku bayaninsu a nan kamar haka; Na farko: Game da jifa da dare mun ce a daren goma ga wata wato daren ranar idi mata dukkansu da mai uzuri da maras uzuri zasu iya jifan Akaba (kawai saboda ranar jifan ta ne), sai kuma masu uzuri da ba zasu iya yi da rana ba.
Amma game da jifan ranar sha daya da sha biyu da dare sai mai uzuri kawai ne zai iya jifa a daren sha daya da daren sha biyu maimakon ranakunsu. Mace ma a jifan 11, da 12 ba ta da bambanci da namiji, don haka ba zata iya jifa da dare ba, sai dai idan tana cikin masu uzurin da ba sa iya jifa da rana saboda dalilan da muka kawo kamar tsufa ko rashin lafiya da sauran su.
16. Na biyu: Idan mutum baki daya ya zama ba ya iya yin jifa da rana, haka ma ba ya iyawa da dare, to a wannan halin ne kawai zai iya wakilta wani ya yi masa jifan, kuma dole ne wanda ya wakilta ya kasance zai yi masa jifan da rana ne ba dare ba, domin wanda aka wakilta don jifa ba zai yiwu ya yi da dare ba sai dai da rana. Haka nan yake babu bambanci a ranar sha daya ne ko ranar sha biyu ne.
17. Na uku: Game da mustahabbancin jifa; a sani cewa ana iya yin jifa ta kowane bangare ne na wadannan bangwayen (amudai), ko da yake bangon ta bangarore biyu wato ta bangaren da muke zuwa daga Mina, da ta bangaren alkibla siriri ne, don haka jifa ta wadannan bangarorin yana da wahala, don haka muna iya jifa ne ta bangarensa guda biyu masu fadi, don haka yayin jifa don a ba wa alkibla ko an sanya ta gefe babu wata matsala ga hakan. Sannan kuma ana son yin kabbara duk sa'adda aka jefa dutse. Wannan lamarin yana hada wilaya (jibinta lamari ga Allah) ta hanyar fadin "Allahu Akbar" da kuma barranta (nisanta daga shedan) ta hanyar yin jifa.
18. Bayanin karshe game da jifa shi ne: idan wani mahajjaci a ranar sha daya ga wata ya tuna cewa ya jefa duwatsu shida ne, to dole ne ya rama wannan jifan na bakwai a ranar sha biyu yayin da ya je jifan ranar sha biyu. Haka nan da ya manta bai jifa ba gaba daya a ranar sha daya, ko kuma bai san ma da akwai jifa ba a ranar sha daya, sai ya sani a ranar sha biyu ga wata, to dole ne ya rama wannan jifan a ranar sha biyu ga wata.
19. Wannan shi ne bayanin kwana Mina da jifa a dunkule.

Ayyukan Hajji a Takaice
Bayan mun shirya mun yi harami a Makka sai mu kama hanyar Arfa, a ranar tara ga wata dole ne mu kasance a Arfa daga azahar zuwa faduwar rana, bayan nan sai mu tafi Muzdalifa wato Mash'arul Haram da nufin tsayuwa a can, sai mu zauna a can da daren ranar idi, bayan safiya ta yi sai mu kama hanya zuwa Mina, a ranar idi zamu jefi Akaba, mu yi yanka, mu yi aski ko rage suma kamar yadda aka yi bayani. Sai dai mai hajjin farko dole ne ya yi aski.
20. A daren sha daya da daren sha biyu zamu kwana da nufin kwanan Mina, sannan da rana a ranakun sha daya da sha biyu zamu jefi bangwaye uku, a ranar sha biyu ba zamu fita ba kafin azahar, don haka sai mu bari sai bayan azahar sai mu bar Mina mu koma Makka domin sauran ayyukan hajji da suka hada da: 1.Dawafin hajji, 2.Sallar dawafin hajji, 3.Sa'ayi tsakanin Safa da Marwa, 4.Dawafin mata, 5.Sallar dawafin mata. Wadanda zamu yi bayani game da su a nan gaba.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
Thursday, April 12, 2012