Umarar Mufrada

Umarar Mufrada


Darasi Na Sha Uku: Mas'aloli Da Tarurrukan Da Suka Shafi Umara Mufrada

Kashe-kashen Umara da Hajji
A darussan da suka gabata mun kawo ayyukan Umarar Tamattu'i da Hajji Tamattu'i a takaice, kuma muna cewa a takaice ne saboda ayyukan hajji suna da yawan gaske matuka. Sai dai mun kawo mafi muhimmancinsu ne wadanda sau da yawa a kan samu kai cikinsu, sai muka bar fadadawa ga mai son haka ya duba littattafai da aka rubuta kan hajji da umara.
1. Da farkon darasin mun yi bayani da cewa umara kala biyu ce: Umarar Tamattu'i, da kuma umarar Mufrada. Amma hajji mun ce kala uku ne: Hajji Tamattu'i, da hajjin ifradi, da hajjin karani. Mun kawar da kai daga bayanin hajjin ifradi da na kirani saboda bai shafi wadanda suke wajen Makka ba, su sun shafi wadanda suke mazauna Makka ne, duk da cewa a yanayin yadda ake yin ayyukan su ba su da wani bambanci. Ko da yake suna da wasu 'yan mas'aloli da suka bambanta su.
Shi Hajji Tamattu'i yana tare da umararsa ne kamar yadda muka kawo a darussan farko, haka ma Umarar Tamattu'i tana tare da Hajji Tamattu'i ne kamar yadda muka kawo. Amam Umara Mufrada ita kadai ce ake yin ta.
2. Haka nan umarara tamattu'i da Hajji Tamattu'i dole ne su kasance a watannin hajji, mutum ba zai iya yin su a wasu watannin na tsawon shekara ba, amma umarar Mufrada ko da yaushe a tsawon shekara mutane suna zuwa don yin ta, yanzu kuma muna son mu kawo wasu daga hukunce - hukunceta a nan.
3. Mutanen da suke son yin Umarar Tamattu'i da Hajji Tamattu'i su ma suna iya yin umarar Mufrada, don haka ne mu a karshen wadanann darussan muke son kawo wasu bayanai game da umarar Mufrada.

Ayyukan Umara Mufrada
4. Umarar Mufrada tana da ayyuka bakwai ne da zamu jero su a yanzu kamar haka: yin harami, dawafi, sallar dawafi, sa'ayi tsakanin Safa da Marwa, yin aske ko rage suma, dawafin mata, sallar dawafin mata. Wadannan su ne ayyukan Umara Mufrada, wadanda suke zuwa Hajji Tamattu'i suna iya yin ta bayan sun gama ayyukan su na umara da Hajji Tamattu'i ko kafin hakan idan zasu iya suna da dama, haka nan masu zuwa yin umara tsawon shekara su ma aikin da zasu yi ke nan game da umara.

Mas'alolin Ayyukan Umara Mufrada
5. A nan yanzu zamu yi wasu bayanai ne game da umarar Mufrada kamar haka: na farko mu sani cewa Umara Mufrada ba wajibi ba ce mustahabbi ce ita kadai, don haka idan mutum ya je Hajji Tamattu'i bayan ya gama Umarar Tamattu'i da Hajji Tamattu'i ya kammala baki daya, to yana da zabi ya yi Umara Mufrada idan ya so don wajibi ba ce a kansa.
Hatta wanda ba shi da damar zuwa hajji wajibi amma yana da kudin da zai iya yin umarar mafrada shi ma ba wajibi ba ne ya yi umarar mufarada sai dai mustahabbi ne. Don haka Umara Mufrada baki daya ta kowane hali mustahabbi ce ba wajibi ba ce.
Sai dai akwai wasu wurare da Umara Mufrada take zama wajibi kan mutum kamar haka:
Na farko: Wanda ya yi hajjin ifradi to shi wannan bayan ya kammala hajji dole ne ya yi umara mufrda.
Na biyu: Wanda Hajji Tamattu'insa ya koma hajjin ifradi to shi ma wajibi ne bayan ya kammala hajjinsa ya yi Umara Mufrada.
Na uku: wanda ya yi hajjin kirani shi ma wajibi ne ya yi Umara Mufrada bayan ya kammala hajjin nasa.
Wannan kuwa tun da ya shafi wasu mutanen ne daidaiku don haka ba mu tsawaita magana a kai ba, don haka Umara Mufrada ita a kanta ba wajiba ba ce.
6. Idan mutum ya tafi hajji kafin ya tafi Makka don yin Umarar Tamattu'i, sai ya ga yana damar yin Umara Mufrada sannan ya zo Madina ya yi harami ya tafi Makka don yin ayyukan Hajji Tamattu'i, to wannan yana iya yin umara mufrda wacce take mustahabbi ce. Haka nan wanda ya kammala Hajji Tamattu'i shi ma yana iya yin Umara Mufrada mustahabbi ce duka babu bambanci.
7. Wanda yake son yin tafiya zuwa Madina ko fita daga Makka kafin yin aikin Umarar Tamattu'i da Hajji Tamattu'i, to wannan mutumin dole ne ya yi Umara Mufrada, wadanda daga karshe idan suna son su dawo Makka ba zasu iya yin Umarar Tamattu'i ba, a misali saboda suna zirga - zirgar sha'anin mahajjata, wadanda suke kaikawo zuwa jidda da sauran su, to irin wadannan mutanen da ba yadda zasu yi, to sai su yi Umara Mufrada su fita daga Makka zuwa ayyukansu, daga baya kuma idan sun dawo Makka don yin Hajji Tamattu'i sai su yi Umarar Tamattu'i a wannan lokacin kafin fara ayyukan hajjinsu.
8. Haka nan wanda ya yi aikin Hajji Tamattu'i ya kammala yana son ya yi Umara Mufrada shi ma babu wata matsala amma da sharadi daya, wato ya kasance watan hijira kamariyya ya canja, misali da ya yi Umara Mufrada a watan zulka'ada to zai iya yin wata uamara mafrdar a watan zulhijja bayan ya kammala aikin hajji. Haka nan da ya yi Umara Mufrada a watan rajab, to zai iya yin wata a watan sha'aban, muhimmi shi ne bayan Umara Mufrada to sai wani watan ne za a sake yin wata, sai dai ko da yake zai iya yin wata da nufin neman ladan Umara Mufrada kawai, amma ba da nufin yin umarar mustahabbi ba. Amma dawafin mustahabbi wanda ba tare da yin umara yake ba, to shi yin sa ko da yaushe mustahabbi ne.
9. Kamar yadda muka ce Umara Mufrada mustahabbi ce, kuma idan aka yi ta, kuma ana son yi wata to mustahabbacin yin ta biyun yana kasancewa bayan wata da yin ta farko ne. Don haka mutum zai iya yin Umara Mufrada da yawa amma da sharadin wata wata tsakaninsu, idan ba haka ba, to sai dai ya yi ta da nufin neman samun ladan umarar Mufrada ba da nufin mustahabbanci ba.
Sannan wata mas'ala muhimmiya ita ce: Idan mutum ya yi Umara Mufrada yana cikin garin Makka bai fita ya wuce wurin da yake mikati ba, kuma ya yi Umara Mufrada a watan da ya wuce, yanzu ma yana son yin wata, to wannan mutumin zai iya yin harama daga Makka babu wata matsala. Amma da a ce misali ya yi wata Umara Mufrada a watan rajab, sai kuma ya tafi Madina, kuma yanzu yana son yin wata umarar Mufrada a watan sha'aban don haka yana son ya tafi Makka, to wannan mutumin tun da ya fita daga Makka bayan umarar da ya yi a rajab har ya wuce mikati, don haka idan zai dawo watan sha'aban don yi wata umarar dole ne ya yi haraminsa daga mikati, sannan ya kama hanyar Makka don yin umarar watan sha'aban din.
Sai dai maganarmu a nan ta asali kan wanda ya yi Umara Mufrada ne da yake cikin garin Makka bai fita ba, kuma yana son ya sake yin wata alhalin wata bai wuce da yin waccan ba, to idan yana son ya yi wata, sai ya yi ta da nufin neman ladan umara ba da nufin mustahabbi ba.
10. Sai dai idan umarar ta biyu ba ta mai yin umara ba ce, wato yana son ya yi wa wani ne, ko wani ya wakilta shi ya yi masa ita, to a nan babu wata matsala don ya yi wata umarar mustahabbi ba tare da wani sabon wata ya kama ba.

Wata mas'ala game da Umara Mufrada
11. A lura cewa da Umara Mufrada da Umarar Tamattu'i duka biyu dole ne mutum ya yi ayyukansu a daidai, don haka ne idan mutum ya yi ayyukansu bisa kuskure, ko ayyukansa suka kasance sun samu tawaya kamar ya manta bai yi dawafin mata da sallarsa ba, to ya zama dole ne ya zauna cikin kayan haraminsa. Don haka sai ya samu malami don ya warware masa yadda zai yi don yin wata umarar.

Jerin ayyukan Umara Mufrada
12. A yanzu zamu yi bayanin jerin ayyukan umara mufrda kamar haka: Yin harami daga wurin da yake wajen harami da zamu yi bayaninsa; dawafin umara a ka'aba; sallar dawafin umara a bayan makamu Ibrahim; sa'ayi tsakanin Safa da Marwa; rage suma ko aski; dawafin mata; sallar dawafin mata a bayan makamu Ibrahim. Wadanann su ne jerin ayyukan Umara Mufrada.

Wasu mas'aloli
13. Umarar Mufrada da Umarar Tamattu'i ba su da wani bambanci ta fasukacin abubuwan da suke haramtawa, da wajibai, da mustahabbai. Sai dai wasu 'yan bambance - bambance ta fuskancin wajibai kawai, amma ta fuskacin sharuda duk babu wani bambanci sai a niyya kawai, domin a umarar Mufrada da niyyar yin ta, a Umarar Tamattu'i ita ma da niyyar yin ta. Sai dai ta fuskacin wuri suna da wani bambanci, don haka zamu yi bayani game da wannan.
14. Kamar yadda muka ce ne cewa ta fuskacin wuri suna da wani bambanci, domin ana yin harama da Umarar Tamattu'i daga daya daga cikin mikatoti biyar da muka yi bayani ne wato Masallacin Shajara, Juhufa, Wadil Akik ko Zatu Irkin, Karnul Manazil, da kuma Yalamlam. Wadannan su ne wuraren da idan mutum ya fito zuwa Makka ta daya daga cikinsu to zai yi harami a nan. Haka nan wanda yake Makka sai ya fita zuwa wadannan mikatotin don ya yi harami ya yi niyya da talbiyya sannan sai ya dawo Makka domin aikinsa na Umarar Tamattu'i.
Amma a Umara Mufrada duk wanda yake zuwa daga wajen Makka ko daga wane wuri ne na duniya yana iya yin haraminsa a mikatin da ya wuce ta wurinsa, ko kuma ya yi harami a wurin da yake daurantar mikati. Idan kuwa yana Makka ne to sai ya fita karshen haramin Makka ya je wajensa da muka yi bayani a can baya kamar Tan'im, Hudaibiyya, Ji'irana, Wadi Arana, sai ya yi haraminsa daga nan ya yi harama da aikin Umara Mufrada ya yi niyya da talbiyya, sannan sai ya kamo hanya zuwa masallacin ka'aba don yin ayyukansa na umarar Mufrada.
Da yawan mahajjata sukan tafi Tan'im, yanzu garin Makka har ya wuce Tan'im, sai dai ita Tan'im din tana wajen harami ne, don haka sai a yi harami daga nan, akwai wani masallaci da suka gina a Tan'im, to mutum yana iya yi a masallacin ko wajen masallacin duka daya ne, domin muhimmi shi ne ya kasance wajen harami kawai.

Abubuwan Haramtawa Lokacin yin Harami
15. Duk abubuwan da suka haramta ga wanda ya yi haramin Umarar Tamattu'i suna haramta ga wanda ya yi haramin Umara Mufrada kamar yadda muka kawo su duka a bahasin Umarar Tamattu'i ba tare da wani bambanci ba tsakaninsu. Haka nan ma kamar yadda muka ce wanda ya yi harami da Umarar Tamattu'i ya shigo garin Makka da rana, kuma yana son daga hotel ko gida din da ya sauka ya tafi masallaci mai alfarma na ka'aba da rana, to bisa ihtiyadi wajibi babu dama ya hau mota ko wani abu mai rufi yayin tafiya zuwa masallacin. To haka ma a Umara Mufrada wanda ya je karshen harami ya fita daga cikinsa kamar a Tan'im, sannan sai ya yi harami da Umara Mufrada, matukar shi ma da rana ne, to shi ma bisa ihtiyadi wajibi ba zai iya shiga wata mota ko wani abu mai rufi ba don zuwa masallacin harami na ka'aba don yin ayyukansa.
16. Haka nan game da ayyukan Umarar Tamattu'i da na Umara Mufrada ba su da wani bambanci, tun daga tsarki, dawafi gewayen ka'aba sau bakwai da fara shi daga hajarul aswad, da karewa da shi, da sanya Hijru Isma'il cikin dawafi. Da sauran sharuda da wajibai da suke ga Umarar Tamattu'i su ma akwai su a Umara Mufrada duka.
Haka ma tsarki da alwala yayin sallar dawafi da rashin yin kiran salla ko ikama ga sallar dawafi, da bayanin yanayin karatun maza da mata, da surorin da zasu karanta da rashin karanta sura mai sujada da muka yi bayani duk iri daya ne.
17. Haka nan mustahabbancin karanta surar ikhlas bayan fatiha a raka'a ta farko, da karanta surar kafirun bayan fatiha a raka'a ta farko, da sauran mustahabbai, da salla bayan makamu Ibrahim, da rashin wajabcin fadin niyya da harshe da cewa nufi ya wadatar, duk babu bambanci tsakanin Umara Mufrada da Umarar Tamattu'i, sai a koma wa bayanan da muka gabatar game da Umarar Tamattu'i bayanin yana daidai da shi.
18. Haka ma game da sa'ayi tsakanin Safa da Marwa duk wani abu da muka fada na yadda ake yin sa guda bakwai farawa daga Safa da Karewa da marwa, da rashin tafiya da gefe gefe ko da baya baya, da sassarfa ga maza a wani yanki nasa da aka yi wa alama da koriyar fitila, duk komai iri daya ne.

Aski ko Rage Suma
Akwai bambanci mai yawa a batun aski da rage suma tsakanin Umarar Tamattu'i da Umara Mufrada, domin a Umarar Tamattu'i da maza da mata duka ba su da hakkin yin aski, dole ne kowa ya rage sumarsa kawai, ba man bayan Umarar Tamattu'i ba, idan za a iya tunawa mun kawo cewa hatta bayan Umarar Tamattu'i matukar goma ga watan zulhijja ba ta zo ba, bayan jifan Akaba da yanka bai halatta mahajjaci ya yi aski ba.
19. Amma a Umara Mufrada; ya zama dole kan mata su dan yanke wani abu daga gashinsu, amma maza suna da zabi ne ko su yi aski ko kuma su rage sumarsu, sai dai aski ya fi.

Dawafin Mata da Sallarsa
20. Akwai bambanci na asasi game da dawafin mata da sallarsa tsakanin Umarar Tamattu'i da Umara Mufrada, domin babu wajabcin shi a Umarar Tamattu'i, sai dai idan wani yana so ya yi to babu komai. Amma a umarar Mufrada wajibi ne yin dawafin mata da sallarsa, ba shi da wani bambanci da sauran dawafin sai a niyya, kuma fadin niyya da harshe ba dole ba ne.

Ayyukan Umara Mufrada
A takaice
Karshen aikin Umara Mufrada shi ne dawafin mata da sallar dawafin mata.
21. Wannan shi ne hukunce - hukuncen ayyukan Umara Mufrada a takaice, kuma su ne a takaice kamar yadda suka gabata: yin harami, dawafi, sallar dawafi, sa'ayi tsakanin Safa da Marwa, aski ko rage suma, dawafin mata, sallar dawafin mata.
22. Da godiyar Allah da neman dacewarsa a cikin wadannan darussa ne muka kawo wasu daga hukunce - hukuncen umara da hajji daidai gwargwadon bukata da ake cin karo da su, bisa fatawar Marja'i mai daraja jagoran juyin musulunci Ayatul-Lahi Sayyid Khamna'i (d.z).
Muna fatan wadannan bayanai su kasance masu amfani gare ku, muna rokon Allah ya ba mu kyakkyawan karshe, kuma muna yi wa kowa fatan samun dacewa da zuwa ziyarar Madina mai haske da aikin hajji a Makka mai daraja, da yin ayyukan umara da hajji. Kuma muna rokon Allah ya sanya dacewa cikin ayyukan duk wadanda suka samu zuwa aikin umara da hajji a wannan wurare masu daraja, ta yadda zasu samu karbuwa wurin Allah madaukaki. Muna kuma neman addu'a daga kowa.
Wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
Thursday, April 12, 2012