Mutane Shi'awa

Mutane Shi'awa

SHEIKH WA'ILI
Wadannan wasu bayanai ne, na `yan kadan da na so su zama kawai matashiya a kan rigyangyantun Shi'a wajen yin hidima ga tunanin larabawa, da kuma daukaka shi, don haka mai karatu zai iya komawa zuwa masdarori domin ya sami kari a kan wannan.
1- Mawakan Shi'a:
Matsayan mawakan Shi'a wajen kare larabawa da kishin larabci abu da yake shahararre, haka makariyar su ga dukkanin abin da yake da sila da samuwar larabawa da kuma girman su da kuma tsayawa daura da abokan fadan larabawa wannan ma wata doguwar tafiya ce da za a hada ta, a waje guda, kuma da sannu zan nuna maka misalsali: Na daga matsayar su a kan hakan, daga cikin su akwai:
A- Abul Asad Nabata dan Abdullahil Hamani:
Yana cewa: Ya yi shiru daga ayyana mazhabarsa, kowane daga cikin Abil faraj a cikin Agani, da kuma Abbas a cikin Ma'ahidul tansis, da kuma Ibn Kutaiba a cikin Ashshi'iri wash shu'ara, sai dai lalle shi dan Shi'a ne saboda wasu dalilai daga ciki akwai cewa: Na daya alakar sa da Ahlul-baiti a cikin wakarsa, da kuma haihuwar sa a cikin Unguwar hamana, a Kufa wacce take tushen shi'anci, da kuma yanke alakar sa da Abi dulfi jagoran shi'anci, kuma ma ga wakarsa da yake zargin kabilanci a cikin ta, tare da yin zambo ga Ali dan Yahya Almunajjim, kuma da sannu za mu ga tsananin kulawar sa da kalmomin gida:
Su halitta ce ta Allah, kuma tuni na riga na san ku*
*a bangaren hagu, kun kasance kuna sanye da gyauto (zani guntu, gajere)
Wata Sunna ba ta taba shudewa ba, face sai na gan ku*
*Suna tafiya a cikin tufafin hariri, da yanga, kuma a karairaya.
A can kasashen gabas, har yanzu mataikan su ba su gushe ba*
*Suna rabewa a karkashin injin ba da ruwa da kuma bayan rakuma.
Har dai zuwa karshen wakar, (mai bukata sai ya koma ainihin littafin da aka rubuta da larabci don fassara wakar ba zai isar da abin da ke so a fitar a cikin ta ba, na daga na kalmomin larabci na asali na gida).
Fun Karimi a cikin littafinsa Hadharatul Islamiyya ya na cewa: Lalle wannan wakar tana kamanta bangarancin larabci kamantawa ta hakika.
B- Ashsharifur Radhi Muhammad dan Husain:
Ya cika diwaninsa da kokarin daukaka larabawa da kishin larabci, daga cikin wannan akwai fadinsa:
Ka fifita ta saboda abin da take kunshe da shi na gajiyarwa*
*kuma shekaru tamanin zuwa sama da haka su na kai komo a cikin ma'anonin ta.
Kuma lalle mu muna ganin cewa makota na zamantakewa suna da*
*Hakkoki, to ina kuma ga makota na nasaba, (na jini).
Idan har ka lura/kula da haduwar dagantakar mu*
*gaba daya to wannan shi ne addinin larabawa.
Idan rundunar ta gauraya da wata rundauna*
Ko da kuwa tsoho ya daura igiyar hemarsa domin hutawa, (zai fito wajen yaki) .
Kuma yana fadi a cikin Ra'i'atus Saniya:
Lalle babbar bishiyar nan ta nasaba wacce daga ita aka samo*
*Daukaka wadanda su ne rassan kakanni tsarkaka.
Mun daukaka har zuwa adadin da yafi karfin kididdigewa, kuma sai dai wata (kabilar) ba dai mu ba*
*Ta fi karfin dukkanin babbar musiba Idan har wani mai neman musiba ya tunkare ta da ita.
Idan har ka ga mummunan farmaki da girman kai daga gare mu (ga wadanda ba larabawa ba)*
*To ka sani cewa jini da jijiyar kakanni larabawa ne suka hada mu.
Yana daga cikin abin da ya kamata a ambata shi ne cewa diwanin Sharifur Radhiyyi da diwanin dan'uwansa Murtadha, da sauran wallafe-wallafen su ana sanya su daga cikin boyayyun wakokin larabawa masu dadi da sa nishadi, kuma daga cikin saukakansu kuma mai dadi da gardi.
C- Abul Dabibu Almutanabbi, Ahmad dan Husain:
Mutanabbi larabci ne a jini da tunani ne mai tafiya da kafarsa kuma ya a tsawon rayuwar say a rayu yana mai neman tabbatar da samuwar larabci, a bisa mabambantan ayyuka kum yana danganta mutukar kowace falala da cewa nan ce mafara daukakar larabawa, ya yawaita abin da yake da shi na yabo a cikin wakokin sa na daukaka larabawa da larabci da alfahari da ji da daukaka da wannan jinin da wannan tushen, ya na cewa a cikin yabon Saifud daula:
Larabawa sun daukaka ginshiki da kai kama sun zamar da*
*Kololowar mazaunar masu mulki wajen hasa wuta (murhu).
Nasabar su ta alfahari tana komawa zuwa gare ka*
*Asalin nasabobin su zuwa Adnan yake.
Kuma yana cewa:
Takubban mutanen Hindu na tsarata alhali masu kaifi ne*
*Ina ga idan ta kasance 'yar Banizariya ce kuma balaraba.
Kuma zamu ga yana tsinkayarwa a kan jagorancin larabawa da kuma hukumar larabawa don haka babu alheri ga mutanen da bare daga cikin su wanda ba dan kabilar su ba yake mulkar su:
Kadai mutane da sarakuna ne, kuma sam sam*
*larabawa ba zasu taba rabauta a ce sarakunan su ajamawa ne ba.
Ba su da adabi kuma ba su da dangantaka*
*Kuma ba su da alkawari ko yarjejeniya.
Duk wata kasa da al'ummu suka salladu a kan ta*
*Bawa zai rika jagorantar ta kai ka ce su dabbobi ne.
Alharisul Hamdani Abu Faras:
Daga cikin harasan da suke larabawa masu fasaha kuma wanda ya yi fice a cikin yabon su akwai, kuma ya ji ciwon abin da ya auka wa mimbarin su, a yayin da wasu suka yi rabebeniyar wannan mimbarin ko ikon, na su: Yana fadi a cikin kasidar sa shafiyya:
Ka isar da wannan sakon ga bani Abbas*
*Suna da'awar mulkin (al'umma) alhali ajamawa sun mallake su.
Ina wani abin alfahari da ya wayi gari a kan mimbaran ku*
*Alhali wanin ku ne ya ke ba da umarni, a cikin su har da (mata) (ta yiwu matar sarki ce) akwai mai yanke hukunci.
Wannan ba komai ba ne face sai `yan misalsali daga matsayar mawakan Shi'a a kan dangane da larabawa da kuma kishin larabci, kuma mai karatu zai iya komawa litattafan mawakan Shi'a na zamuna mabambanta don ya ga gejin kishin larabcin su.
D- Masu riko da kabilanci wadanda suka yi fice, ba `yan Shi'a ba ne:
Daga cikin wadanda suka yi fice aka san su da kabilanci a fagage daban-daban na tunani da zamantakewa ba Shi'a ba ne, kuma da sannu zan ambata maka wata jimla `yar guntuwa, daga tarihin su wanda ke bubbugar da abin da ake nema:
A- Mu'ammar dan Musanna Abu Ubaida:
Yana daga cikin mawallafa kuma daga cikin wadanda aka sani da bangaranci kuma yana daga cikin mawali din bani Taim a Basra kuma asalin sa Bayahude ne kakan sa ya musulunta a hannun `ya`yan Abubakar kuma shi ne wanda ya jaddada littafin masalibu; Arab kuma ya yi kari a kan sa, ya kasance bahawariji yana da ra'ayin Ibadhiyya.
B- Haisam dan Udayyi dan Zaid:
Babarsa ta kasance baiwa ce babansa kuma balarabe ne, ya kasance daga cikin wadanda suka fi yin fice a kabilanci, a akidarsa ma ya kasance bahawarije kuma ya bayyana hakan a cikin dukkanin littafin da ya rubuta, daga ciki akwai littafin masalibus sagira.
C- Ala'ush Sha'abi:
Shi ne Ala'u dan Hasan alwarrak ya kasance daga cikin mafi yin fice a wajen kabilanci, Alusi ya kasasnce yana cewa zindiki ne mai bautar gumaka ya rubuta littafi ga Dahiru dan Husain da wannan a litafin ya fara ne da abubuwan kunya da aibobin kabilun kuraishawa sannan bani Hashim sannan sauran larabawa.
D- Abdullahi dan Maslamata dan Kutaiba:
Ya kasance daga cikin imaman Ahlus-sunna kuma daga cikin fitattun su ya kasance daga cikin masu kabilanci kamar yadda ibini Abdi rabbihi ba'andaluse ya bayyana a cikin akadul farid sai Dakta Muhammad Nabih Hijab ya yi kokarin tsarkake shi daga sha'abiyyanci, domin -kamar yadda yake cewa- ya zo cewa an tsunto yabon larabawa daga gare shi, a yayin da an sami sama sa nassi daga ibinil Mukaffa wanda yake yabon larabawa a cikin su, tare da haka Dr. Muhammad Nabih idan ya shude ta kan nassin Ibinil Mukaffa wanda ya yabi larabawa a cikin sa sai ya ce: Lalle ya yi wannan ne don ya boye kan sa, dalilin da ya sa Muhammad Nabih ya tsaya a wannan matsayar shi ne; Abdullah dan Muslim yana daga cikin Ahlus-sunna ne, a yayin da Ibinil Mukaffa ba dan Shi'a ba ne, domin kawai ya na da karkata zuwa Alawiyyawa, Muhammad Nabih yake cewa, idan har a ka san sababi to mamaki ya kare.
E- Abdullah dan Mukaffa':
Masu bincike sun sa shi daga cikin masu kabilanci, amma Ustaz Muhammad Kard Ali a cikin littafinsa Amra'ul bayan ya tsaya kai da fata wajen kare shi, ya dauke shi a matsayin wanda ya musulunta kuma ya kyautata musuluncinsa, a yayin da wasu jama'u daga masana tarhih magabata kamar su Abil Faraj Al-isfahani da mas'udi da Jahshiyari duk sun tafi a kan cewa shi zindiki ne, amma Dr. Muhammad Nabih Hijab yan ganin cewa shi bamajuse ne a addini kuma mai bautar gumaka a akida, kuma lalle bai bar ibadun majusanci ba, amma tare da ra'ayoyin magabata a kan sa da kuma ra'ayin shi kansa Muhammad Nabihi, duk da haka amma yake cewa ba'alawiyyar siyasa gare shi, yana mai jingina zuwa wani ra'ayi na Hana Fakhuri da ya gani cikin littafinsa Tarihul Adab, amma ban san a ina alawiyyancin na sa ya ke tare da dukkan abin da a ka fadi a kan sa ba?.
F- Sahalu dan Harun dan Rahbunil Farisi:
Ya kasance daga cikin kirar barmakawa, kuma shugaban Darul hikima na Mamun, sama da mutum daya sun bayyana rayuwar sa, daga cikin su akwai Yakutul Hamawi a cikin Mu'ujamun nudaba'u da kuma Ibini Nadim a cikin fihras, da Farid Wajdi a cikin Da'iratul Ma'arif da makamancin sa, kuma a kan wadannan ne Muhammad dan Nabih ya dogara a wajen tarjamar sa kuma bai zo da nassi a kan cewa daya daga cikin wadannan sun kawo tarihin sa, a kan cewa shi Shi'a ne ba, amma suk da haka Nabih Hijab yake cewa ya kasance Ba'alawiyye ne a mazhaba mai karkata zuwa Mu'utazilanci kamar dai wasun sa daga shi'ar Irak na zamanin sa, kuma ya kasance mai dabi'ar farisawa, a yayin da Muhammad Kard Ali a cikin littafinsa Umara'ul Bayan ya tafi a kan kare shi da kuma kubutar da shi daga kabilanci.
G- Basar dan Burdi:
Ya kasance zindiki, yana kafirta mutane baki dayan su tare da cewa akwai hashimawa a cikin su kuma yana kafirta al'umma dukkanin ta saboda ta karkace daga tafarki madaidaici a mahangar sa, sai aka ce da shi Ali dan Abi Dalib fa sai ya buga misali da wannan baitin:
Ba babar amru ce tafi sharri fiye da guda ukun ba*
*Fiye da sahibin kan nan wanda ba ka sa shi a cikin sahabban mu.
Kuma ya yi wa Ibrahim dan Abdullah dan Hasan yabo mai yawa, yayin da ya yi fito na fito da Mansur, a cikin wasu baitotci da yake cewa a cikin su:
Ina cewa da mai yawan murmushi; buwaya ta tabbata a gare shi*
*Ya wayi dagi hutacce mai shaukin karamci.
Daga cikin Fadimawan da suke yin kira zuwa shiriya*
*A bayyane wa ke iya shiryar da kai kamar dan Fatima.
Fitila ce ga idanun mai neman shiriya a wani lokaci kuma*
*ya kan zama duhu ga makiyi mai takurawa.
Sai Nabih dan Hijab ya kafa hujja da wannan baitin da cewa shi Shi'a ne tare da cewa ya yabi abbasawa da baitoci mafiya yawa, da kuma baitocin da suka fi wadannan zafi, kamar haka:
Kun yi mana adalci sai suka aibata hukuncinku saboda hassada*
*Allah ya kare ku daga ketar mai hassada.
Ba don halifa ba, da ba mu sami sabani da shi ba*
*hakika taki-taki, mun fuskanci juna a fagen fama
Kuma ya yabi wasun su, kuma wannan bayyananne ne a cikin diwanin sa kuma ba a jingina shi da wadanda ya yaba ba sai don ya yabi Ibrahim dan Abdullah sai ya zama Shi'a, kuma manufar hakan shi ne: Ya kasance dan Shi'a ne kuma a lokaci guda mai kabilance ne, kaga ke nan daga baya sai a sami kafar jingina kabilanci da shi'anci, saurari abin da Muhammad Nabih Hijab yake cewa: Yana cewa a karshen tarjamar sa: Wannan shi ne Bashshar zindiki fitacce daga cikin addini mai waken shagali, mara kunya, mai bin akidar Zaradashtiyya, mai bin mazhabar Shi'a, bashu'ubiyye mai bangaranci.
Wannan karfin hankalin mai ban mamaki na Nabih Hijab wanda yake kai bara da farmaki da shi, ya tunatar dani wata hikaya makamanciyar ta, zan fada maka ita yanzu, Abdulhayyi Alkattani ne ya ruwaito ta a cikn lattafin sa: Attarabibul shubiya al'idariyya. Ya ce:
Ya kasance a wajen `ya`yan Tamimul dari akwai littafin Annabi (s.a.w) a cikin guntuwar fata, "Da sunan Allah mai rahama mai jin kai: Wannan ne abin da Muhammad Manzon Allah ya bawa Tamimud dari, ya yanka masa alkaryar jabaran da kuma baitu-uyun na garin khalil, sai wannan ya wanzu a hannun sa kuma mutane suna ganin takardar ta sa, har lokacin da Ifrinjawa (Faransawa) suka yi galaba a kan Kudus da khalil shekara ta 492 bh. Ya ce: Sashin masu mulki sun nufaci alayen Tamim a lokacin da na kasance a Sham- hadisin na Abubakar Alkali ne- kuma suka nufaci kwace ta daga gare su, sai alkali Hamid Alharawi ya zo, ya kasance bahanife ne a zahiri, bamu'utazile a badini, malhidi dan Shi'a, sai `ya`yan Tamim suka kafa hujja akan littafin sai alkalin ya ce wannan littafin ba abin dogara ba ne har dai zuwa karshin kissar. A she baka ga yadda furicin masu tunzurawa yake yin daidai da na juna ba a kowane zamani: Alkali ne daga cikin hanifawa yake so ya kare hanifawa, sai wani lokaci ya mayar da shi bamu'utazile, a lokaci guda bahanife, mulhidi, dan Shi'a, haka dai ainihin furucin Nabih Hijab. Lalle irin wadannan maganganun ya kamata mu wurgar da su cikin kwandon shara domin mu hutar da na bayan mu daga wadannan mushen.
H- Yazid dan Dhbbata Maula Sakif:
Ya kasance tare da ummayyawa kuma ana jifan sa da manuwiyyanci da kuma shu'ubiyyanci, kuma ya kasance masuyin Walid dan Yazid, sannan sama da marubuci daya ne suka sa shi a cikin `yan kabilanci.
I- Hammad dan Sabur:
Ibini Mubarak wanda aka fi sani da Hammad Arrawiya asalin sa badailame ne babakeren haihuwa, yana daga cikin manya-manyan masu kabilanci.
J- Isma'il dan Yassar:
Ya kasance mai tsananin son alayen Zubair, sannan sai ya karkata ga zuwa `ya`yan Marwan, sai wasun su suka yi masa alkawari saboda su yi amfani da wannan damar, ya kasance ana sa shi daga cikin wadanda suka yi fice a fagen sha'abiyyanci, kuma mafi tsananin su bangaranci a kan larabawa.
K- Ishak dan Hassanul Harimi:
Ba a zo da wani nassi da ya nuna daga kowace mazhaba yake ba ko makamancin haka. Ya kasance daga cikin manya `yan bangaranci, sai dai Khadibul Bagdadi yana fadi game da shi ya kasance yana kadaita Allah kuma yana bin addini, a wajen sa shi musulmi ne ke nan.
L- Ibrahim dan Hanshazl Mutawakkili:
Ya kasance daga cikin `yan zaman dandin Mutawakkil halifan Abbsawa, (mai raya Sunna) ya kasance yana zaman da shi a wajen shan giya har sai da aka jingina shi zuwa gare shi, kuma ba su fadi wata akida ta musamman da yake da ita ba, sai dai karkatar sa ga Mutawakkil ta yiwu ya zama alama ta hadauwa a kan ra'ayi, kuma ya kasance daga cikin shu'ubiyyawa.
M- Alhasan dan Hani Abu Nuwas:
Bawan (maulan) Jarrah dan Hasan ne wasun su suna ganin sa a matsayin mara kunya ne kawai, wasu kuma suna ganin sa zindiki wasu kuma sun dauke shi a matsayin bamanuwe, kuma sun jefe shi da kabilanci, Nabih Hijab ya bayyana shi a matsayin kafiri mulhidi mara addini.

N- Ibnur Rumi Ali dan Abbas dan Juraih:
Nabih Hijab yana fadi a kan sa: Ba bu daya daga cikin marubuta Adab da malaman tarihin sa da ya yi nuni a kan cewa ya kasance mai bangaranci ga mutanen sa, sai dai wakokinsa ba sa wofinta daga wannan dabi'ar, koda kuwa sun bayyana ne a cikin `yan baitoci `yan kadan, daga cikin wadannan baitocin akwai fadinsa:
Kuma mu ne `ya`yan Unan mutane ne mu masu hankali*
*Da karamci da goge (garaya) kuma tsatson ajamawa.
Daga ciki akwai fadinsa:
Idan har zan hakaito (zan bada labari) to Rumawa su ne ahlina*
*kuma ni ahlin (ma'abocin) yin magana da larabci ne.
Amma baitin da ya sa Nabih Hijab ya tabbatar da cewa Ibnul Rumi yana da bangaranci shi ne baiti mai zuwa:
Iyaye na sune Ruma Taufil da taufalasu*
*Kuma Rubi da Shabsu ba su haife ni ba.
Tare da cewa Ibnul Rumi ba yana nufin Rubi gaba daya ba, sai dai yana nufin shabsu wanda sunan babansa Rubi wanda ya tabbata cewa daya ne daga cikin wadanda suka kashe Imam Husain (a.s), Inbul Rumi ya kasance yana so ya ce, tare da cewa ni dan Taufil ne sai dai ni masoyi ne ga Alayen Muhammad, kuma tare da cewa Shabsu da Rubi daga cikin larabawa su ke kuma daga cikin wadanda sakon Annabi ya daukaka su, amma kuma su makiyan `ya`yan gidan sa ne, a takaice shi Ibnul Rumi dan Shi'a ne shahararre, wannan ne sirrin da ya sa Nabih Hijab ya dauke shi a matsayin mai bangaranci, in ba haka ba ai ka ji shaidar Nabih Hijab a kansa da cewa, ba daya daga cikin masana tarihi da littafin Adab da yi shaida a kan bangarancin sa ga mutanen sa.
O- Abdussalam dan Ragbar:
Ya sanya shi daga cikin masu asabiyya (bangaranci), kuma Nabih Hijab yana cewa ba mu sami baitin sa guda daya da yake yin nuni a kan bangarancin sa ba ga mutanen sa, tare da haka Ibnul Khalkhan ya yi nassi a kan bangarancinsa ga mutanen sa, saboda fadinsa: Ba su da -yana nufin larabawa -fifici a kan mu mun musulunta su ma sun musulunta. A daidai lokacin da Nabih Hijab yake fadin abin da kaji a kan sa, amma daga karshe sai ga shi yana cewa: Idan har muka san cewa shi dan Shi'a ne, kuma ya kasance mai waken soyayya, kuma dan ba ruwana (kurarren kabila), wanda ya dukufa a wajen wargi da wasanni, kamar yadda Ibn Khalkan yake cewa, wadannan abubuwan guda biyu suna daga cikin alamomin bangaranci, kuma lalle bayan wannan ya cancanta mu sa shi daga cikin jerin masu kabilanci, kamar yadda Ustazus Suba'i bayumi , ya yi da Huzaimi da kuma Bashshar da makamancin su.
Ina so in tambayi mai karatu cewa: Shi mai karatu ya kuwa lura da wadannan dalilan masu karfi a kan kabilancin da wadannan gagara badau (masana) din su ke yin amfani dasu wajen rarraba wa mutane shaidar bangaranci dama da hagu, da dalilai kamar irin wadannan? ya Allah ka shaida cewa lalle muna jin takaici ga masu zuwa nan gaba wadanda misalin wadannan mutanen suke rena, Jarrabawar Ilimi da adabi da tunani babba ce ga wadannan mutanen, abin da zan gabatar maka a misali na karshe shi yafi zama a sarari fiye da wannan, shi ne tunaninsa da sa hankalinsa a wajen kafa hujja a bisa kabilancin Du'ubal (Di'ibal) dan Ali, Alkhuza'i saurare shi ka ji:-
p- Du'ubal bn Ali Al'khuza'i:
Shi dan kabilar Khuza'a ne kuma ba ya daga cikin mawali kamar yadda wasu suke son kawowa, kuma litattafan ilimin nasabobi sun karfafa hakan. Kuma ya kasance daga shahararrun Shi'a kuma daga malaman adabinsu kuma yana da kasidu masu kayatarwa a game da yabon Ahlul-baiti (a.s) da kuma juyayinsu. Litattafan adabi sun siffanta shi da cewa mutum ne mai kaifin harshe wajen zambo da suka kuma babu wani wanda ya kubuta daga harshensa, kuma Nabih dan Hijab yana cewa yana da kabilanci matuka saboda ya yi wa ma'amun zambo, a kan haka ne Nabih yake cewa: Sukan da ya yi wa ma'amun yana nuna kabilancinsa yayin da ya yi alfahari da mutanensa da kuma tsananinsu a yaki da taimakawarsu wajen daukakar kujerar mulki, saurara ka ji me yake cewa a fadinsa:
A yanzu ma'amun ni yake siffantawa da raunin ragwanta, shin Ma'amun bai ga kan Muhammad ba ne a jiya? Shin bai ga cewa ni ina daga mutanen nan da takubbansu? Suka kashe dan'uwanka suka dora ka wannan matsayin, sun daukaka matsayinka bayan tsawon dakushewarsa, sun tseratar da kai a kwarin gefen duwatsu manisanci.
A karshen bayani game da tarihinsa sai yake cewa shi ne Du'ubal al'khuza'i, wannan kuma shi ne harshensa mai kaifi wanda ya wasa shi kan Larabawa da 'yan kawancensu .
Wannan kuwa shin ne dalilin da ake kawowa a kan bangarancinsa na Shi'anci kuma sai aka kara da abin da muka fada sama na tuhumomi.
Bayan wannan bayani muna iya komawa domin mu tambayi Dakta Ahmad Amin, mene ne dalilin danganta shi da Shi'anci, domin muna ganin yayin da ya yi magana kan abin da muka kawo wannan sai ya yi alkawari cewa zai yi bincike game da bangaranci da kabilanci a gun da zai ambaci bayanai game da mazhabobi idan ya zo kan fasalin magana kan Shi'a.
Daga karshe ina cika wannan fasali da zan sanya shi gabanka da cewa: Shukuri Alusi yana fada a cikin littafinsa na "Bulugul Irab fi Ma'arifati Ahwalil Arab" cewa Abu Ubaida Albakari ya fada a cikin sharhin amalil kali: Littafin bayani game da aibobin Larabawa cewa asalinsa tun daga ziyad dan babansa ne yayin da ya yi da'awar cewa abu sufyan babansa ne, ya san cewa Larabawa ba zasu yarda da hakan ba tare da saninsu ga nasabarsa, sai ya yi littafin nan na "Masalib" ya sanya wa Larabawa duk wani aibi da abin kunya da barna da kage, sannan kuma sai alhaisam dan udayyi shi ma ya yi hakan, sai ya so ya aibata ma'abota daukaka domin ya huce haushinsa kansu, sannan kuma sai abu Ubaida Muhammad dan almusannan ya maimaita hakan ya kuma dada kari a kan hakan, domin shi asalinsa bayahude ne da kakansa ya musulunta a hannun wasu daga alayen Abubakar, sai ya zama daga mawalin taimi, haka nan ne dai Alusi ya kawo a fasalin "Asshu'ubiyya" a littafin da aka ambata.
Ziyad yana daga mutanen da masu tarihin Sunna da marubutansu suke ganinsa misali ne shi a daular Larabawa, kuma matsayinsa game da Larabawa kamar dai yadda ka ji ne matsayi ne mai munanawa ga tarihinsu mai suka ga nasabarsu mai binciken aibobinsu. Bayan haka bari in kawo maka matakin dan Shi'a duk da ya kasance daga asalin da ba na Larabawa ba ne domin ka yi hukunci da kanka a kan wadannan al'amura biyu ka ga abin da yake nuni zuwa ga ra'ayin kowanne daga cikinsu domin ka ga ina ne ake da bangaranci da kabilanci tsakanin wadannan biyun.
Badi'uzzaman alhamdani yana cewa: Na kasance gun Assahib Isma'il dan Ubbada wata rana sai wani mawaki ya shigo masa daga mawakan ajamawa, sai ya yi masa wata waka da yake fifita al'ummarsa a cikinta a kan Larabawa kuma yana sukan Larabawa yana yi musu waka har ya zo wani wuri kamar haka:
Da dai a ce Farisawa ba su da komai sai
Najarus sahib gwarzo mai hazaka
Da sun samu fiyayyen alfahari da wannan
Kuma zuriyarsu ta kasance mafificiyar zuriya
Yayin da ya zo wannan wurin sai sahib ya ce masa ya yi haka, sannan sai ya rika mike wuyansa yana dubawa, ni kuma na makale a cikin wani loko, sai ya ce: Ina Abul fadal. Sai na mike na sumbanci kasa, sannan sai na ce; amsawarka, sai ya ce: Amsa mana. Sai na ce: Me ke nan. Sai ya ce: Adabinka da nasabarka da mazhabarka. Sai na ce: Babu wata damar magana babu wani hutu sai dai kawai jerin magana ne kamar dai yadda ka ji. Sannan sai na yi wakata: (wata waka ce da take kushe abin da mawakin baya ya kawo).
Yayin da na gama wakata sai sahib ya juya ya kalle shi ya ce: Yaya ka ga wannan wakar. Sai ya ce: Da na ji ta da ban gaskata ba. Sai ya ce: Kyautar da zan yi maka shi ne in kyale ka, idan na sake ganin ka daga yanzu to sai na sare wuyanka. Sannan sai ya ce: Ban ga wani yana fifita ajamawa ba kan Larabawa sai wanda yake da jinin majusanci .
Ina ganin kai ma ka ga abin da yake a nan na mahangar Shi'anci ta yabo da take ga Larabawa a matsayin wani daukaka da girmama saboda rikonsu ga sakon musulunci, wanda yake sako madawwami. Bai kamata ba in tsawaita, don haka sai in bar ka domin ka samu jin dadin bayanin wannan matsayin, kuma ka yawata da kwakwalwarka cikinsa. Kuma bayan haka ina fatan na sanya wani bayani mai nuni ga hakikanin Shi'anci a gaban ka mai karatu, kuma Allah ya sani ba ina son in dauki fansa ba ne ko suka, shin musulmi ya dauki fansa kan musulmi? Wannan kuwa dai raha ce.
Kuma dai manufata dai kwadaituwa ne na yaye duhun da ya shamakance ido gabarin ganin Shi'a mabiya Ahlul-baiti (a.s) a zamani mai tsawo, al'amarin da ya sabbaba rudu mai yawa. Allah ne muke neman ya hada kan musulmi ya dinke barakarsu, kuma godiya ta tabbata ga Allah tun daga farko har zuwa karshe. Karshen addu'armu dai ita ce godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai.
Hafiz Muhammad Sa'id / hfazah@yahoo.com / www.hikima.org / www.haidarcip.org / Facebook: Haidar Center
Haidar Center for Islamic Propagation
Monday, December 10, 2012