Ziyarar Kabari4

Ziyarar Kabari4

WALLAFAR: JA'AFAR SUBHANI

Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani
Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id
Al'ummun da suke raye a kasashen da suka cigaba a duniya zaka ga suna kokarin wajen kare kayan tarihi kuma suna nuna soyayyarsu ga wadannan abubuwa na tarihi. Sannan suna iya kokarinsu da su kare wadannan kayan tarihi don kada su bata ko su lalace. Domin kiyaye wadannan kayan tarihi kuwa wadanda suke nuna cigabn su a tsawon tarihi har ma'aikatu na musamman suka samar da ma'aikata kwararru domin kawai wannan aiki. Sakamakon haka ne ba su ba da wata dama da zata sanya wani guntun abu daga cikin wadannan kayan tarihi da suka hada da wani allo wanda aka yi wani rubutu a kai ko guntun jirgin ruwa da ya bata. Domin sun yi imani da cewa wadannan kayan tarihi suna ba da wata sheda ce ta musamman ta su wadannan al'umma. Mutanen da suka yanke daga al'ummarsu da manyan tarihinsu da suka gabata suna da hukuncin yaro ne wanda ya bata daga hannun iyayensa.
Cigaban musulunci wani cigaba ne wanda yake mai girman gaske wanda a karnoni na tsakiya shi ne kawai cigaban da babu kamarsa. Musulmai sakamakon koyarwar da suka samu daga littafinsu na sama, sun kafa cigaban da ba a taba yinsa ba a tarihi. Wanda ya kai kololuwarsa a cikin karni na hudu, ta yadda gabas da yammacin duniya suka shaida haka, kamar yadda ya gina Tajmahal na kasar Indiya da Kasar (Spain) sauran gine-gine masu ban al'ajabi, wanda ta hanyar kaitsaye ko kuma ba kaitsaye ba. Kamar yadda masana na yamacin duniya suka tabbatar da cewa cigaban yammacin duniya ya samu asali ne ta hanyar Andulus ko kuma ta hanyar yakin da ya auku tsakanin musulmi da kiristocin yammacin duniya.
Cigaban musulunci ya fara ne da aiko manzon Musulunci (s.a.w) ko kuma da wata ma'ana ya fara ne da haihuwar shi manzon, Sannan da taimakon mabiyansa ya cigaba ta kafuwa da yaduwa a sauran sassan duniya. Gine-ginen da suke dangane da Manzo ko kuwa wasu daga cikin sahabbansa suna daga cikin wannan cigaba na musulunci. Sannan kuma wannan ba mallakin wani ba ne ta yadda zai yi abin da ya ga dama da su, wannan na dukkan al'ummar musulmi ne. Saboda haka babu wata hukuma ko wasu mutane da zasu yi abin da suka dama da wannan kayan tarihi da cigaban musulunci ba tare da izinin sauran musulmi ba, ta yadda ta hanyar yaki da bidi'a da tsayar da tauhidi su kawar da wadannan kayan tarihi.
Tarihin musulunci yana gaya mana cewa: An haifi manzon musulunci ne a shekara ta 570 bayan haihuwar Annabi Isa (a.s) Sannan bayan ya kai shekara 40 da haihuwa aka aiko shi a manzanci, bayan aiko shi da manzanci ya yi shekara 13 a garin Makka yana isar da wannan sako. Bayan wannan ne tare da umarnin Ubangiji ya bar inda aka haife shi zuwa garin Madina, Inda a can ne ya yi shekara 10 yana isar da wannan sako na musulunci kuma ya yi fito na fito da mushrikai makiya musulunci, sakamkon bayar da shahidai da ya yi a wannan hanyar ya samu damar daga tutar musulunci a dukkan yankin kasashen Makka da kewayenta (yanki mai girma daga cikin Jaziratul Arab) A shekara ta 11 bayan hijara ne ya koma zuwa ga rahamar Ubangijinsa, sannan bayan wafatinsa sahabbansa suka cigaba da wannan aiki na yada musulunci a sassan duniya daban-daban.
Wannan kuwa ya shafi rayuwar da kokarin Manzo da iyalansa da da mabiyansa ne (kamar yadda muka fadi cewa shi ne tushen wannan cigaba) Saboda haka dole mu yi kokari wajen kare wannan asali.
Kaburburan Shugabannin Addinin Musulunci Suna Nuna Tarihin Musulunci
Dole ne mu kula da cewa duk wani abu da zai faru a wani zamani yana kore duk wani shakku ga wadanda suke rayuwa a wannan zamani. Amma tare da gushewar zamani sakamkon ko-in-kula na mutane zai sanya wannan yakini da tabbas da yake ga mutane ya ragu. Ta yadda a hankali zai zama ana shakku da tararrabi a kan faruwar wannan abin, ta yadda wani lokaci ma zai koma kamar wata tatsuniya. Abubuwan da suka faru ga addinan da suka gabata a lokacin da suka faru babu wani shakku ko tardidi a kan faruwarsu, amma sakamakon rashin kulawa a yau sun zama kamar tatsuniya.
Maimaita wannan mummunan al'amari dangane da musulunci yana da matsala fiye da yadda ya faru a sauran addinan da suka gabata. Domin kuwa addinin musulunci addini ne wanda har zuwa ranar tashin kiyama dukkan mutane dole ne su yi biyya a gare shi, ta yadda zasu sadu da haske ta hanyar hakan. Mutanen da zasu zo nan gaba kuwa zasu iya biyayya ga wannan addini yayin da suka kasance sun samu yakini dangane da hakikaninsa.
Babu shakka daya daga cikin hanyar kiyaye wannan tabbaci na hakikanin addinin musulunci kuwa shi ne kiyaye abubuwan da suka shafi rayuwar Manzo da sauran shugabannin addinan musulunci.
Magabatanmu Allah ya rahamshe su, sun yi hidima mai yawa dangane da al'ummar yanzu, ta yadda suka kiyaye mana abubuwan da suka zo tun farkon zuwan musulunci. Sakamakon haka ne kai tsaye muke kiran sauran al'umma zuwa ga wannan addini wanda yake hakikaninsa bai samu wani canji ba, ta yadda muke cewa: Karni goma sha hudu ne da suka gabata shugaban Bani Hashim ya ta shi da manzanci daga Allah ya kuma kira mutane zuwa ga Tauhidi da kaurace wa bautar gumaka da kafirci, bayan Mu'ujizozin da ya zo da su, sannan ya zo da littafi mai girma wanda ya karya makiyansa da shi, sannan har zuwa yanzu wannan Mu'ujizata har abada tana nan ba tare da wani canji ba.
Wanda kafin ya fara bayyana kiransa ya kasance yana tafiya kogon hira domin yin ibada ga Allah madaukaki. Bayan cika shekara arba'in da rayuwarsa ya fara kiransa, wasu mtane daga cikin mutanen Makka suka yi imani da shi, yayin da wasu mafi yawa suka kaurace masa, har ma suka yi nufin su halaka shi, amma Allah da ikonsa ya boye shi a wani kogo da ake kira (Thaur) wanda yake kudancin garin Makka, ta yadda ya tsira da makiya. Bayan nan kuma ya yi hijira zuwa garin Madina, a wannan gari ne mutane Aus da Khazraj (wadanda ake kira da Ansar) suka amsa kiransa suka taimake shi. Manzo a tsawon zamansa a garin Madina ya gwabza yaki mai tsanani tsakaninsa da mushrikai da Yahudawa, Ta wannan hanyar ne ya gabatar da shahidai da dama a tafarkin Allah ta yadda suka ba da jinansu a yakin Uhud, Khaibar da Hunain. Manzo (s.a.w) ta hanyar aika mabiyansa zuwa sassa daban-daban na wannan nahiya ta kasashen larabawa ya samu damar isar da sakonsa zuwa ko'ina a wannan lokaci. A shekara ta 11 ne bayan hijira ya koma zuwa ga ubangijinsa kuma ya yi umarni da rufe shi a cikin dakinsa, bayan wafatinsa mabiyansa suka cigaba da hanyar da ya bari, ta yadda ba tare da bata lokaci ba, ya yada wannan addini tare da al'adun da Kur'ani ya zo da su a dukkan sassan duniya.
Wannan shi ne wani yanki na tarihimmu wanda bayan wucewar karni 14 ake Maimaita shi. Saboda haka dole mu yi kokarin wajen kare wannan tarihi na mu da duk abin da ya shafi hakan, ba wai ta hanyar wasu dalilai ba marasa tushe mu ruguza wannan tarihi na mu!.
Kmar yadda ya kasance mu shagala game da kiyaye wadannan kayan tarihi, ta yadda babu bambanci a wurin dangane da samuwarsa da rashinsa duk daya yake, (abin da ma ya fi muni shi ne yadda ake ganin cewa rusa wadannan abubuwa yaki ne da yaduwar shirka) Ta yadda acikin kankanen lokaci an manta da wasu abubuwa na tarihin musulunci, don ha ka bayan wani lokaci zai yiwu a fara shakku dangane da wasu abubuwa na hakikanin wannan kira da Manzo ya zo da shi. Ta yadda kamar su Salman Rushdi mai makon canza addini sai ya yi kokarin inkarin addinin da tarihinsa baki daya.

Daukar Darasi Daga Tarihi
Mutum kodayaushe yana kokari ne ya kalli kowane al'amari ta hanyar idanu ko makamancinsu, domin kuwa ilimin da yake samuwa ta wannan hanya mutum ya fi dogara a kansa. Cikinsa a babban hanyar da ake bi domin tabbatar da wani abu dangane da abin da ya shafi rayuwar zamantakewa, kuma wanda aka fi dogara da shi domin yana ba da sakamakon da ake samun yakini, shi ne tarihi, Kur'ani mai girma ya na ba da tarihin magabata ne domin daukar darasi.
Dangane da shari'un da suka zo daga sama muna iya daukar shari'ar Annabi Isa (a.s) a matsayin misali. A akidar musulmi Annabi Isa matsayin annabin Allah yake, wanda yake mai albishiri ne ga zuwan Manzo Muhammad (s.a.w) sannan ya zo da littafi mai suna "Injil" wanda yake dauke da haske a cikinsa. Amma muna samun tabbas a hakan ne ta hanyar Kur'ani mai girma.
Amma sakamakon matashin da yake yammacin duniya ba shi da imani da Kur'ani ta yadda zai kalli Annabi Isa ta wannan fuskar, a yau dangane da zuwan Annabi Isa da littafinsa yana da shakku a kansu. Domin kuwa ba shi da wata alama ta wannan kira a hannunsa ta yadda zata taimaka masa ya samu yakini a kan hakan. Domin kuwa Masih ba shi da kabari ko mahaifiyarsa da sahabbansa da zasu tabbatar da zuwansa. Sannan littafinsa an hakaito shi ta hanyoyi daban-daban ta yadda zai yi wahala mutum ya gane gaskiyar al'amarin.
A takaice babu wani abu wanda zai tabbatar wa matshin yammacin duniya gaskiyar zuwan Annabi Isa da littafinsa. Saboda haka sabanin magabatansa yana shakku a kan hakikanin wannan al'amari.
Saboda haka mu musulmi dole mu dauki darasi daga wannan abin da yake faruwa daga kiristanci, ta yadda zamu kiyaye duk wani abu wanda yake ya zo daga Manzo kuma yana matsayin sheda ne ga da'awar da shi Manzo ya zo da ita, (duk yadda ya kasance abu dan karami ne) ta yadda zamu kare duk wani abu wanda zai sanya wadanda zasu zo bayammu su yi shakku a kan gaskiyar addinin musulunci, kamar yadda matashin yammacin duniya yake shakkun gaskiyar Annabi Isa da Injila.
Muna iya amfana daga ayoyin Kur'ani da suke nuni da cewa: Al'ummun da suka gabata sun kasance suna kiyaye duk wani abin da manzonsu ya zo da shi, ta yadda suke tafiya da shi yayin wani kwami mai zafi da yake a gabansu. ta yadda ta hanyar neman albarkaci da wannan abin daga annabawansu don neman samu cin nasara daga mushrikai abokan gabarsu.
A matsayin misali Bani Isra'il sun kasance suna tsaron wani akwati wanda duk abin da musa da iyalansa suka bari yana cikinsa, sannan suna neman tabarruki daga gare shi kuma yayin karo da makiya suna daukar shi domin neman cin nasara.
Kasantuwar albarkar da muhimmancin wannan akwati ya zamana mala'iku suke daukarsa. Idan har ya kasance kiyaye wasu abubuwa na magabata (kamar wannan akwatin) wani abu ne marar kyau, to me ya sa Kur'ani mai girma yake ambaton wannan al'amari da harshe na yabo, kuma me ya sa mala'iku suke daukarsa, sannan me ya sa bayan dauke wannan akwati daga "Amalika" a cikin wannan aya ya zama wata alama ce da take nuna wanda zai jagoranci wannan runduna ta yaki?!
Yara wadanda ba su balaga ba su ne, suke wasa da kayan da iyayensu suka bar musu, ta yadda cikin sauki suna iya batar da su. Amma magadan da suke da hankali kuma sukan amfani da matsayin wannan abin da iyayensu suka bar musu, suna rike wadan kaya ne iya karfinsu. Al'ummar muslmi ma sakamakon cigaban da suka samu bayan wafatin Manzo (s.a.w) su kiyaye duk wani abu da ya bari, wannan kuwa har da kwarar gashinsa sun kasance sun sanya ta wani wuri na musamman suka ajiye ta.
Matsayin Gidajen Annabawa A Cikin Kur'ani
Gidajen annabawa da manyan bayin Allah suna da wani matsayi na musamman, wannan kuwa a fili yake matsayin da suke da shi bai shafi wani abu na duniya ba ne, domin idan da haka ne, gidajensu ba su da wani bambanci da sauran gidajen mutane domin an gina su ne da yumbu da tubali kamar na kowa, wadannan gidaje suna da wannan matsayi ne sakamakon mutane masu matsayi da suka zauna a cikinsu.
Kur'ani mai girma yana siffanta hasken Ubangiji da fitila mai haske ta yadda yake haske kamar tauraruwa. A ayar da take biye wa wannan aya kuwa ya nuna cewa wurin wannan haske yana gidajen wasu mutane masu girma wadanda suke ambaton Allah a ciki safiya da yamma.
A cikin wannan aya jimalr da take cewa "Ana tasbihinsa safiya da yamma, tana nuna dalilin da ya sa aka daukaka wadannan gidajen wadanda aka ambata a cikin ayar da ta gabata. A ayar da take biye mata kuwa an siffanta masu yin ibada a cikin wadannan gidaje ne, inda yake cewa: "Mutane ne wadanda kasuwanci ba ya shagaltar da su daga ambaton Allah da tsayar da salla, domin suna jin tsoron ranar da zukata da idanu suke jujjuyawa suna tsorata.
Wannan aya tana bayani ne a kan girma da daukakar gidajen da ake zikirin Allah ake kuma tsarkake shi a cikinsu. A nan dole ne mu yi bayani a kan abubuwa guda biyu kamar haka:
1-Me ake nufi da gidaje a cikin wannan aya?
Masu tafsiri sun yi sabani a kan ma'anar wannan ayar ta yadda kowane ya dauki daya daga cikin ma'anonin kasa:
A-Ana nufin gidaje a cikin wannan aya da masallatai guda hudu.
B-Ana nufin dukkan masallata ne a cikin wannan aya.
C-Ana nufin gidajen Manzo ne.
D-Masallatai da gidajen Manzo.
A cikin wadannan ma'anoni da aka ambata a kasa ma'ana ta uku ce kawai zata iya daidai kamar yadda zamu kawo dalilai da suke karfafa hakan.
1-Ta fuskar lugga kalmar Buyut jam'i ne na bait wato gidan kwana. Ibn manzur ya tafi akan cewa bait yana nufin gidan mutum. Ragib kuwa yana cewa: Bait shi ne inda mutum yake fakewa da dare. Amma mawallafin "Almunjid" kuwa cewa ya yi, ma'anar bait tana nufin wurin zama wanda ya hada da hema da gidan da aka gina kasa da tubali.
Saboda haka fassara kalmar bait da masallaci wanda yake wurin ibada na kowa da kowa bai inganta ba, domin kuwa ba wurin da mutum yake fake wa ba ne da daddare. Saboda haka idan ma har ya inganta, amma abin zai zo ga kwakwalwar mutum shi ne gidan kwana, don haka idan har yana nufin masallaci ne ana bukatar abin zai nuna hakan. Ba tare da hakan ba, ba za a karbi wannan ma'ana ba.
Da wani kalamin ma Bait ya samu asali ne daga baituta wato mutum ya tsaya wani wuri har zuwa safe. Idan har ana mabata gidan mutum da bait saboda mutum yana kwana a cikin wannan gida ne har zuwa safe.
Tare da kula da wannan ma'ana ta kalamar bait, fassara ta da ma'anar masallaci yana bukatar abin da yake nuna hakan, ba tare da wannan ba ba za a karbi wannan fassara ba.
2-Kur'ani duk lokacin da zai yi Magana a kan wurin da al'umma suke bauta yana amfani ne da kalmar "Masjid" ko "Masajid" ne. Sakamakon haka ne wannan kalma an yi amfani da ita sau 28 acikin Kur'ani mai girma. Amma duk lokacin da za a yi Magana a kan wurin da mutane suke kwana a kan yi amfani da kalmar "Maskan, Ma'awa" ne. Sannan an yi amfani da kalmar bait ta fuskar jam'i ko tilo. Saboda haka wannan kalma ta zo sau 66 a cikin Kur'ani da wannan manufa. Sakamakon haka muna iya fahimata cewa a cikin Kur'ani kalmar "Masjid" da "bait" ba suna nufin ma'ana guda ba ne. saboda haka idan aka nemi fassara su da ma'ana guda zai zama da'awa ba tare da dalili ba.
Idan Kur'ani ya kira masallacin Ka'aba da "BaitulLahi" ba don yana wurin bautar Allah ba ne, domin kuwa mun san cewa Ka'aba alkibla ce ta masu bautar Allah ba wurin da ake ibada ba. Saboda haka hada sunan Allah da wannan wurin kawai yana nuna girmamawa ne, kai ka ce wannan gida na Allah ta yadda za a girmama shi girmamawa ta musamman.
3-Akwai muhimmin bambanci tsakanin masallaci da gida. Bait ana nufin bangaye guda hudu da aka yi wa rufi, amma masjid kawai bangaye guda hudu ne, wato rufi ba sharadi ba ne kafin ya zama masallaci. Da yawan akan gina masallatai a wuraren da suke da zafi ba tare da rufi ba, wanda daya daga cikinsu shi ne masallacin ka'aba, alhalin kuwa gidan da mutum yake kwana yana bukatar rufi.
Wannan aya da zata zo a kasa tana bayar da sheda a kan bukatar gida daga rufi:
"Ba don hikimar Allah ta yi rigaye ba akan cewa komai zai kasance bai daya, da mun sanya gidajen wadanda suka kafirce wa Ubangiji mai rahama masu rufi da azurfa da tsanin da suke amfani zuwa sama".
Wannan aya tana bayyana cewa "bait" sabanin "Masjid" yana da rufi, sannan ba don wata maslaha ba da Allah madaukaki ya bambanta gidajen kafirai da na muminai ta yadda zai sanya gidajen Kafirai rufinsu ya zama na azurfa, amma sai ba yi hakan ba.
4-Jalaluddin Suyudi ya ruwaito daga Anas Bn Malik Yana cewa: Yayin wannan aya wadda take cewa "A cikin gidajen da Allah ya yi Umarni da a daukaka…". Sai ya karanta a cikin masallaci, sai wani daga cikin sahabban Manzo ya mike ya tambayi Manzo me ake nufi da wadannan gidaje?
Sai Manzo ya amsa masa da cewa: Ana nufin gidajen Annabawa, a wannan lokaci sai Abubakar ya mike ya ce: Ya nuna gidan Ali da Fadima (a.s) ya ce: Wadannan gidajen suna cikin wadanda Allah ya yi izini da daukaka su? Sai Manzo (s.a.w). Ya amsa masa da cewa: E, suna ma daga cikin mafi daukakarsu.
Imam Bakir (a.s) yana cewa: Abin da ake nufi da gidaje a cikin wannan aya shi ne, gidajen Annabawa da gidan Ali (a.s)
Bisa dogaro da wadannan dalilai muna iya fahimtar cewa abin da ake nufi da gidaje a cikin wannan aya ta cikin Suratun Nurr shi ne gidajen annabawa da waliyyan Allah, sakamakon tasbihi da tsarkake Allah da ake yi a cikinsu yake da wani matsayi na musamman, kuma Allah ya yi izini da yin kokari wajen a daukaka su.
5-Sannan dalili wanda yake a fili a kan cewa abin da ake nufi da gidaje a cikin wannan aya su ne, ayoyi guda biyu da suka zo kamar haka:
Allah madaukaki yana yi wa Annnabi Ibrahim da matarsa magana kamar haka:
A-"Rahmar Allah da albarkarsa ta tabbata a gare ku ya ku ma'abota gida .
B-Allah Kawai ya yi nufi ya tafiyar muku da kazanta yaku Ahlul baiti, ya kuma tsarkake ku tsarkakewa.
Kai ka ce wadannan gidaje su ne cibiyar hasken Ubangiji.
Tare da kula da wadannan dalilai guda biyar da muka kawo muna iya cewa: Masati da daukakar wadannan gidaje sakamakon wadanda suke zaune a cikinsu ne, suna tasbihin Ubangiji suna tsarkake shi. A hakikanin gaskiya wannan aya tana magana ne dangane da gidaje irin gidajen Annabi Ibrahim da Manzo (s.a.w), a nan kuwa sakamakon tasbihi da tsarkake Ubangiji da ake yi a cikinsu, shi ne ya sanya Allah madaukaki ya daga martaba da darajarsu.
Mai yiwuwa a ce: Karkashin wannan aya ana cewa: "Yana tasbihinsa a cikinsu safiya da yamma". Wato abin da ake nufi da "Buyut" Masallatai. Domin kuwa muslmin farkon zuwan musulunci sun kasance suna halarta sallar jam'i baki dayansu. Saboda haka tasbihi da tsarkake Ubangiji ana yin sa ne a cikin masallaci.
Amma wannan fahimta ba dai-dai ba ce, domin kuwa ana aiwatar da sallar wajibi ne kawai a cikin masallatai, sannan mustahabbi ne a gabatar da sauran sallolin mustahabbi a cikin gidaje. Sannan ya kamata ma mutum ya kasa ibadarsa zuwa gida biyu, wato wani bangare na farilla ya aiwatar da su a cikin masallaci, sannan bangaren nafiloli ya gabatar da su a cikin gida.
Mai yiwuwa wasu suga wannan bai inganta ba, amma hakikanin al'amarin haka yake domin kuwa ruwayoyi da dama sun karfafa hakan. Muslim acikin sahih dinsa, ya kawo babi mai zaman kansa wanda yake nuna mustahabbancin sallar nafila a cikin gida. A kan haka ya ruwaito ruwayoyi da dama, amma a nan kawai zamu kawo wasu a matsayin misali:
Manzo mai tsira da aminci yana cewa: "Fiyayyar sallar mutum a cikin gidansa, sai dai sallolin wajibi" .
Wannan ruwaya tana nuna mana cewa Manzo (s.a.w) da sauran sahabbansa suna yin sallolinsu na nafila a cikin gidajensu, sakamakon haka ne gidajen annabawa da na salihan bayi suka zama wurin zikirin Allah da tsarkake shi. Sannan kuma dalilin wannan ne Allah ya ba da izini a kan daukaka su. A yanzu dole ne mu ga me ake nufi daga matsayin wadannan gidaje?
Me ake nufi da daukaka wadannan gidaje?
A baya mun yi bayanin cewa, kafa hujja da wannan aya yana bayyanar da abubuwa guda biyu ne. Abu na farko kuwa shi ne, bayyanar da ma'anar "buyut" wanda muka yi cikakken bayaninsa a baya, yanzu lokaci ya yi da zamu yi bayani a kan abu na biyu wanda shi ne daukaka wadannan gidaje da Allah yake horo da shi.
Hakika kalmar "Rafa'a" cikin Kur'ani tana zuwa ne da ma'anar daga gini kamar yadda ta zo a cikin wannan ayar: "Shin halittar su ita ce tafi wahala ko kuwa sama wadda ya gina ta? Sannan ya daga rufinta ya kuma daidaita ta?
Amma kalmar "rafa'a" a cikin wannan aya ba yana nufi yin gini ba, domin kuwa an dauka cewa akwai gida ne, Kur'ani yana magana a kan siffofin wannan gida ne. Saboda haka abin da ake nufi da wannan kalma a cikin wannan aya shi ne daga matsayinsu da girmama su, mafi yawan masu tafisiri sun dauki wannan ma'ana duk da cewa wasu daga ciki sun tafi a kan ma'anar da muka ambata a baya.
A bayyane zamu iya cewa: Wuraren da Allah yake ambatar "Buyut" yana nufin gidajen da bayin Allah suke kwana suna yin tasbihin Ubangiji kuma suna tsarkake shi. Saboda haka daukaka wadannan gidaje ba ya nufin daga gininsu ko rufinsu ba ne, abin da ake nufi shi ne daga matsayi da martabarsu. Daya daga cikin wannan girmamawa da daga matsayinsu kuwa shi ne ya zamana an tsarkake su daga dukkan wata kazamta, sannan duk inda suka dan lalace a gyara su. Dukkan wannan aiki za a yi shi ne saboda girmama wadanda suka kasance a cikin wadannan gidaje suna tasbihin Ubangiji suna salloli kuma ba su kin fitar da zakka. Domin girmama wadannan mutane ne Allah ya yi horo da a girmama wadannan gidaje, sannan a kare su daga rushewa.
Kowa ya san cewa an rufe Manzo (s.a.w), a cikin gidansa, wato a wurin da ya kasance yana ambaton Allah da yabonsa. Saboda haka tare da bin hukuncin wannan aya gidan Manzo ya cancanci girmamawa da daukaka matsayinsa, sannan a kiyaye shi daga kowane irin rushewa da lalacewa. Sannan kuma a kaurace wa sanya masa duk wani nau'i na kazanta, kai da yawa daga bangarorin Madina kaburburan manyan bayin Allah ne. Kamar yadda ya zo a cikin ingantattun ruwayoyi sayyida Fadima (a.s) ita an rufe ta ne a cikin gidanta
Haka nan Imam Hadi da Imam Askari (a.s) an rufe su a gidajensu wadanda suka kasance suna ibada da zikirin Ubangiji a cikinsu. Saboda haka wadan gidaje bisa la'akari da wannan aya sun cancanci a daukaka su, sannan dole ne a kauce wa rusa su domin ya saba wa wannan aya.
A unguwar Bani Hashim a garin Madina shekaru kadan da suka gabata gidan Imam Hasan da Husain (a.s) da makaranta Imam Sadik (a.s) sun kasance a wadannan wurare, Marubucin wannan littafi shi kansa ya ziyarci wadannan wurare, amma abin bakin ciki tare da fakewa da fadada masallacin Manzo duk an rusa wadannan wurare masu dinbin tarihi da albarka. Duk da cewa ana iya yin wannan aiki na fadada masallacin Manzo (s.a.w) ba tare da rusa wadan wurare ba.

Soyayyar Manzo (s.a.w) Da Iyalansa
Ayoyin da hadisai da dama sun zo domin bayani a kan soyayya ga Manzo da 'yan gidansa (a.s).
Kur'ani ya nuna mana cewa imanin mai ceto shi ne yana tare da wanda yake son Manzo da jihadi a tafarkin Allah fiye da komai a cikin zuciyarsa: "Ka ce idan iyayenku da 'ya'yanku da matanku da 'yan'uwanku da dukiyoyinku wadda kuka tara, da kasuwanci da kuke tsoran ku fadi a cikinsa, da gidajenku da kuke kaunarsu, idan sun kasance sun fi soyuwa a gareku daga Allah da manzonsa da jihadi a tafarkin Allah sai ku saurara har al'amarin Allah ya zo, Allah ba ya shiryar da mutane fasikai".
Ayar sama tana Magana ne a kan abubuwa guda uku wadanda mafi yawa soyayyar mutum takan ta'allaka da su, wato Iyalai da dukiya da gidaje da saye da sayarwa. Amma mumini na hakika shi ne wanda Allah da mazonsa da jihadi a tafarkin Allah ya fi soyuwa a gare shi fiye da wadancan abubuwa da aka ambata.
Amma a wata aya ana bayani ne a kan soyayyar iyalan gidan Manzo ga abin da take cewa: "Ka ce ban nemi wani abu a kan sakon manzancin da na zo da shi ba a matsayin lada sai soyayya ga iyalan gidana".
Sannan Manzo yana bayyana wasu abubuwa guda uku wadanda suke nuna dandana zakin imanin mutum, daya daga cikinsu shi ne soyayya ga Allah da shi manzon: Abubuwa guda uku ne duk wanda yake da su to ya dandana zakin imani, daya daga cikinsu kuwa shi ne ya kasance a wajan mutum son Allah da manzonsa ya fi komai a wajensa…
Ruwayoyi da suka zo dangane da son Manzo da iyalansa sun wuce gaban mu kawo su a cikin wannan littafi, saboda haka a nan zamu taikata da wasu ruwayoyi a matsayin misali dangane da wannan al'amari, muhimmin abu a nan shi ne mu san ta yaya wannan soyayya zata tabbata, domin mutum ya isa zuwa ga wannan hadafi akwai hanyoyi guda biyu:
1-Mutum ta hanyar magana da ayyukansa ya yi koyi da koyarwar Allah da manzonsa, ta yadda zai kasance a rayuwa ya yi kokari ya ga bai kauce wa koyarwarsu ba, domin kuwa idan mutum ya zamana yana tsananin soyayya ga wani ba zai taba saba masa ba. Saboda haka ne ake cewa "soyayya ita ce biyayya". wato sonka da abu yana lizimta maka da yi masa biyayya.
Sannan Imam Sadik (a.s) a wasu baituka yana bayyana bambanci tsakanin soyayya ta gaskiya da nuna soyayya da ba ta hakika ba, Inda yake bayani akan cewa:
kana sabon Allah alhali kana nuna soyayya gare shi,
wannan ba zai taba yiwuwa ba.
Domin da sonka ya kasance a gaskinya ne to da ka yi biyayya a gare shi,
domin kuwa masoyi yana bin abin da yake so.
2-Bayyana soyayya ta hanyoyi daban-daban kamar haka:
A- Nuna farin cikin yayin da masoyi yake cikin farin ciki. Da nuna bakin ciki yayin da masoyi yake cikin bakin ciki.
B-Gabatar da buki na farin cikin a lokacin haiwuwar Manzo ko lokacin tayar da shi a matsayin ma'aiki.
C-Yada maganganunsa da abin da ya rubuta.
D-kiyaye kayan tarihin da suka shafe shi.
D-Girmama Kabarinsa da yin gini domin kiyaye shi daga lalacewa.
Aikata wadannan abubuwa da makamantansu wadanda suke sun halasta a musulunci, yin su ga Manzo da iyalan gidansa ya nuna kauna ne a gare su.
Tirmizi yana ruwaitowa a cikin sunan dinsa: "Manzo (s.a.w) ya kama hannun Hasan da Husain sai ya ce: Duk wanda yake so na ya kuma so wadannan yara guda biyu da babansu da mamansu, to zai kasance a matsayina a ranar kiyama.
Kowannenmu ya san da cewa babban jikan Manzo yana rufe ne a "Bakiyya", sannan mai biye masa yana rufe a Karbala, Sannan wadannan wurare kodayaushe suna ganin al'ummar musulmi masu ziyara, saboda haka duk wani gini kowane abu wanda za a yi domin kiyaye wadannan wurare, nau'i ne na nuna soyayya ga wadannan jikoki na Manzo kuma bin umurnin Manzo ne a kan soyayya gare su, kamar yadda muka yi bayani a ruwayar da ta gabata.
A yau al'ummu da dama suna kokari wajen tunawa da manyan tarihinsu (kamar sojoji da 'yan siyasa da wadanda suka yi wasu ayyuka na gyara) ta hanyoyi daban-daban, sakamakon haka ne suke halarta jana'izarsu yadda ya kamata. Sannan su rufe a wani wuri na musamman a karkashin gini mai kawatarwa, ta yadda wadanda zasu zo a nan gaba kamar yadda na yanzu suke kulawa ta musamman a kan su, suma su yi kulawa da girmamamawa ta musamman a kan wadannan manyan mutane. Don haka mu ma musulmi dole mu yi kokari don yin gine-gine da zasu kare kabuburan manyan mutanenmu.
Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com - www.hikima.org - www.haidarcip.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center - December, 2012