Mahadi A Kur'ani Da Ruwayoyi

Mahadi A Kur'ani Da Ruwayoyi

Shin an samu bayanai game da imam mahadi (a.s) a cikin Littafin Kur'ani mai girma da sunnar Manzon Allah (s.a.w) da Ahlul Baiti (a.s)?

Littafin Kur'ani mai girma shi ne mashayar ilmomin sanin Allah, kuma tushen hikimomi da sanin da dan Adam yake bukata, littafi ne wanda yake kunshe da labarin da ya gabata da kuma nan gaba, kuma bai bar wata hakika ba sai da ya yi bayaninta. A fili yake cewa da yawa daga ilimin sanin Allah yana boye a ciki zurfin ma'anonin Kur'ani mai girma, kuma ba mai iya gano irin wannan sirri sai Manzo (s.a.w) da Ahlul Baiti (a.s). Bayyanar mai kawo sauyi na karshen Duniya yana daga cikin irin wannan sirri, wannan al'amari ne da ayoyi da dama a cikin Kur'ani suka yi nuni zuwa gareshi, kuma an ruwaito ruwayoyi masu yawa game da tafsirin irin wadannan ayoyin da zamu yi nuni da wasu a nan;
A Surar Anbiya; 105 ya zo kamar haka: "Lallai mun rubuta a cikin Zabura bayan (wucewar) zikr (Attaura) cewa; Hakika wannan duniyar bayina na gari su ne zasu gaje ta". A nan Imam Mahadi (a.s) ya fassara wannan bayi da cewa abin nufi a nan; shi ne Imam Mahadi (a.s) da mataimakansa .
Haka nan a Surur Kasas; aya 5, yana cewa: "Kuma muna son mu yi baiwa ga wadannan da aka raunatar a bayan kasa, kuma mu sanya su shugabanni kuma mu sanya su masu gajewa". A nan Imam Ali (a.s) ya fassara wadanda aka raunatar a bayan kasa da cewa su ne Ahlul Baiti (a.s) kuma masu gajewa shi ne Imam Mahadi (a.s) .
A Surar Hudu (a.s) aya ta 86 ya zo cewa: Ragowar (na) Allah shi ne ya fi gareku idan kun kasance muminai. A tafsirin wannan aya Imam Muhammad Bakir (a.s) ya yi nuni da cewa; idan Imam Mahadi (a.s) ya bayyana zai jingina da jikin ka'aba, kuma farkon maganar da zai yi ita ce wannan aya, sannan sai ya ce: "Ni ne ragowar na Allah a bayan kasa, kuma halifansa, hujjansa a kanku". Daga nan ne duk wanda yake son ya yi masa sallama sai ya ce: Aminci ya tabbata gareka ya ragowar (na Allah) a bayan kasa .
A cikin surar Hadid aya 17 yana cewa: "Ku sani cewa Allah yana raya kasa bayan mutuwarta …". Imam Ja'afar Sadik (a.s) yana cewa: Abin da ake nufi shi ne; Allah yana raya kasa ta hanyar adalcin Imam Mahadi (a.s) bayan an kashe ta …" .

An samu ruwayoyi masu yawa da suka zo game da Imam Mahadi (a.s) da suke bayani game da marhaloli daban-daban na rayuwarsa, kamar haihuwa da lokacin yarinta da buya babba da karami da alamomin bayyanarsa da lokacin bayyanarsa da hukumarsa. Kamar yadda wasu ruwayoyi suka zo suna masu nuni da falalar masu sauraron zuwansa da kuma siffofin lokacin bayyanarsa, wadannan ruwayoyi kamar yadda suka zo a littattafan Shi'a haka nan suka zo a littattafan Sunna. Kuma wani abin kayatarwa shi ne; kowanne daga ma'asumai (a.s) ya yi bayani game da zuwansa a ruwayoyi masu yawa da suke, ba mu samu wasu ruwayoyi kan wani al'amari masu tarin yawa irin ruwayoyin da suka zo game da Imam Mahadi (a.s) ba, da kuma bayani game da tashinsa mai girma domin kafa hukumar adalci.
Manzon rahama (s.a.w) yana cewa: Farin ciki ya tabbata ga wanda ya ga Mahadi (a.s), farin ciki ya tabbata ga wanda ya so shi, farin ciki ya tabbata ga wanda ya yi imani da jagorancinsa (a.s).
Imam Ali (a.s) yana cewa: Ku kasance masu sauraron bayyanar farin cikin alayen Muhammad (s.a.w), kada ku yanke kauna daga rahamar Allah, ku sani mafi soyuwar ayyuka wajan Allah shi ne sauraron farin cikin bayyanar Imam Mahadi.
A ciki Allon Fadimatuz Zahara (a.s) ya zo cewa: "… sai saboda rahamar Allah (s.w.t) a kan talikai salsalar wasiyyai ta cika da samuwar dan Imam Hasan Askari (a.s), wanda yake da kamalar Musa (a.s) da kyawun Isa (a.s) kuma da hakurin Ayyub (a.s) …". Kamar yadda ruwayoyi masu yawa suka zo daga sauran imamai goma tun daga Imam Hasan Mujtaba (a.s) zuwa Imam Hasan Askari (a.s) , suna masu bayani kan maudu'ai masu yawa game da Imam Mahadi (a.s), wanda yake son dubawa sai ya koma zuwa ga littattafan da muka yi nuni da su a kasa.

Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center for Islamic Propagation