Nada Jagora

Allah Ke Kafa Jagora

Wai shin Allah ne yake sanya jagora ko kuwa ya bar wannan lamari ne mai muhimmancin gaske a hannun mutane? Idan haka ne waye ya zabi imam mahadi (a.s) a matsayin jagoran duniya a karshen zamani?

Jagora shi ne mai maye gurbin Annabi a zartar da umarnin Allah kuma Allah ne yake zabensa a mahangar Shi'a, kuma yana sanar da shi bayan Manzonsa. Don haka babu wani mutum ko wata jama'a da take da hannun wajan nada shi. Wajabcin zabin Imami daga Allah yana da dalilai masu yawa da suka hada da;

A: Ubangiji shi ne mai hukumci a kan komai ba tare da wani kaidi ba, kuma dole ne kowane abin halitta ya yi biyayya gareshi. A fili yake wannan hukunci da jagoranci Ubangiji yana bayar da shi ga wanda ya so wanda ya dace ne, saboda haka kamar yadda Allah ne yake zabar Annabi haka nan shi ne yake zabar jagora.
B: Kamar yadda muka yi bayanin cewa dole ne Imami ya zama ma'asumi kuma mai ilimi, a fili yake cewa samun mai wannan siffofi mafi daukaka da saninsa, ba ya yiwuwa sai ta hanyar Allah masanin komai, kamar yadda Allah yake fada ga Ibrahim (a.s): "Ni mai sanya ka shugaba ga mutane ne" .

Daga karshe yana da kyau mu kawo wani bangare na maganar Imam Ridha (a.s) game da Imami da siffofinsa:
Masu sabani game da al'amarin halifanci da suke rayawa cewa jagoranci al'amari ne na zabe bisa jahilci… shin mutane sun san matsayin shugabanci a tsakanin al'umma ne don ya zama ya dace a sanya hakkin zaben a hannunsu. Matsayin jagoranci yana da daraja, sha'aninsa yana da girma, matsayinsa madaukaki ne, wurinsa mafifici ne, zurfinsa ya fi karfin abin da mutane suke sawwalawa na cewar suna iya gano shi da hankulansu, ko kuma su san shi da ra'ayoyinsu…
jagoranci matasyi ne mai girma na Ubangiji bayan matsayin annabta da khulla wanda yake shi ne matsayi mai daraja na uku a samansu, wanda a mataki na sama na uku ne aka ba wa Ibrahim (a.s) shi, halifancin Allah na Manzon Allah ne kuma matsayi ne na Ali (a.s) kuma gadon Hasan da Husaini. Da gaskiya ne cewa halifanci jagoranci ne na addini kuma shi ne tsarin musulmi kuma gyaran Duniya da kuma izzar muminai… shi ne kamalar salla, da azumi da hajji da jihadi kuma ana kare iyakoki saboda Imami ne.
Jagora yana halatta halal din Allah ne, kuma yana haramta haram din Allah ne, kuma yana bibiyar dokokin Allah, kuma yana kare addinin Allah ne da hikima da wa'azi mai kyau, da dalili, yana mai kira zuwa ga tafarkin Allah. Jagora yana bullowa ne kamar rana, wanda haskensa yake mamaye Duniya, kuma shi yana sasanni ne da hannaye da gannai ba sa iya kaiwa zuwa gareshi. Imami wata ne mai haskakawa kuma fitila mai haske, haske mai walkiya, kuma tauraro mai shiryarwa a duhu mai tsanani a hanyoyi da watannni da duwatsu da kuma tekuna, kuma mai tseratarwa daga dukkan fitinu da jahilci…
Shi ne mai debe kewa, kuma uba mai tausayi, kuma dan'uwa na jiki, kuma uwa mai kyawawan dabi'u mai kyautatawa ga danta karami, kuma madogara ta bayi a yayin manyan musibu.
Imami shi ne wanda yake tsarkakke daga sabo da aibobi. Shi yana da ilimi kebantacce kuma masani mai hakuri… Imami shi kadai yake ba shi da misali, ba mai iya zuwa kusa da matsayinsa, babu wani masani da zai koma masa, kuma ba mai iya maye gurbinsa, haka nan ba shi misali, kuma ba a samun tamkarsa. Waye zai iya gano shi, sam! ba ya yiwuwa?! ya yi kadan! ya yi kadan! A nan ne hankula suka dakushe, tunanunnuka suka bace suka dimauce, a nan ne masu gani maras haske, da babba, da karami, da masu hikima masu dimuwa… da kuma masana magana, suka gajiya kuma suka kasa bayanin daya daga siffofin Imami ko fifikonsa, a nan ne suka yi furuci da gajiyawarsu da kasawarsu!!…

Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center for Islamic Propagation