Fa'idar Boyuwa

Fa'idar Boyuwa

Fai'dojin Boyuwar Shugba
Yanzu daruruwan shekaru ke nan dan Adam ya rasa alherin bayyanar Imam Mahadi (a.s) kuma al'ummar musulmi ta ci gaba da asarar rashin amfanuwa daga jagoran da Allah ya ayyana wa Duniya wanda yake ma'asumi. Kuma hikimar rayuwarsa da boyuwarsa ta buya ga mutane, don haka nisantarsa daga Duniya ta zama abin tambaya cewa wane amfani yake da shi ga mutanen Duniya. Shin a nan kusa ba za a samu bayyanarsa ba domin a kawar da wannan wahala ta shi'arsa da ta kasance sakamakon boyuwarsa?. Wannan tambaya da makamantanta duk suna tasowa ne sakamakon rashin sanin Imami ma'asumi da matsayinsa wanda yake hujjar Allah a Duniya. Hakika matsayin Imami a duniyar samammu yaya zai kasance, shin almomin samuwarsa sun takaita da bayyanarsa ko kuma shi domin jagorancin mutane ne kawai yake, shin samuwarsa tana da albarka da tasiri ga dukkan samammu ne ko kuwa?

Ginshikin Samuwa
A mahangar Shi'a da kuma koyarwar addini Imami shi ne wasida domin samun falalar Allah ga dukkan halittu, kuma shi ne wanda yake ginshiki na tsarin samuwar kuma madogara, idan babu shi to dukkan Duniya da 'yan Adam da aljanu da mala'iku da dabbobi da sandararru ba zasu rage ba.
An tambayi Imam Ja'afar Sadik (a.s) cewa, shin Duniya zata kasance ba tare da Imami ba? Sai ya ce: idan Duniya ta kasance babu Imami to kowane mai samuwa a doronta zai kawu.
Kuma shi ne a matsayin tsani kuma wasila ta isar da sakon Allah da shiryar da mutane zuwa ga kamalar dan Adam kuma dukkan wata falala da albarka ta Ubangiji ta hanyarsa ne take isa zuwa ga kowa. Wannan kuwa wani abu ne bayyananne domin Allah ya sanya annabawansa hanyar shiryay ga mutane da kuma masu mayewa bayansa, Kuma mun samu daga maganganun ma'asumai cewa samuwar imamai a fadin Duniya yana kasancewa ne domin isar da ni'imar Allah da falalarsa zuwa ga dukkan manya da kananan halittunsa, wato dukkan abin da yake isa zuwa ga halittu na falalar Allah (s.w.t) suna samunsa ne ta hannun imamai (a.s). Don haka samuwarsu ta hanyar imamai ne, haka ma ni'imar Allah garesu a tsawon rayuwarsu ta hannunsu ne.
Game da sanin Imami (a.s) ya zo a cikin ziyarar jami'a babba cewa: Da ku ne Allah ya bude da ku ne kuma zai cika, da ku ne yake saukar da ruwa da kuma yake rike da sama don kada ta fado kan ma'abotanta. Don haka albarka da ni'imar samuwar Imami ba sai yana bayyane ba, samuwarsa tana da albarkarta koda kuwa yana boye ne, kuma shi ne ruwan rayuwar halittu gaba daya, kuma Allah ne ya so hakan ta kasance da ikonsa da nufinsa, ya sanya mafifitan halittunsa su kasance tsaka-tsaki wajen kwararar ni'imarsa ga sauran bayinsa, kuma a wannan fage babu bambanci tsakanin bayyanarsa da boyuwarsa. Don haka dukkan halittu ba su da wani matsala da zasu samu domin boyuwarsa. Wani abin kayatarwa shi ne an tambayi Imam Mahadi (a.s) game da boyuwarsa da kuma amfana daga gareta sai ya ce: Amma yadda za a amfana daga gareni a boyuwata kamar yadda rana take amfanar mutane ne koda kuwa ta shamakance da gajemare.
A wasu ruwayoyin kuma an kamanta samuwar Imam Mahadi (a.s) da rana da take buya a bayan gajimare kuma an kamanta boyuwarsa da kisfewarta, a nan akwai muhimman bayanai masu yawa wadanda zamu yi nuni da wasu a nan.
Rana a tsarin taurari da duniyoyi ita ce a tsakiya, kuma dukkansu suna kewaya ta, haka ma samuwar Imami (a.s) kamar cibiyar duniyoyi ce da sauran duniyoyi da taurari suke kewayarta. "Da wanzuwarsa ne Duniya ta wanzu kuma da albarkarsa ne aka arzuta halittu, da samuwarsa ne kasa da sama suka tabbata suka tsaya.
Rana ba ta barin haskakawa a kowane lokaci, kuma kowa yana da rana daidai alakarsa da ita, kuma yana amfana daga haskenta, haka nan samuwar waliyyi shuganba wannan zamani yake samar da dukkan ni'ima ta Duniya da ta lahira, wacce take daga Ubangijin halitta gaba daya, amma kuma kowa yana samu ne daidai gwargwadon kamalarsa yake amfana daga shi.
Idan rana ba ta kasance a bayan gajimare ba, to tsananin sanyi da duhu za su kawu, haka nan ne ma Duniya idan ba ta da Imami (a.s) a cikinta, to bala'i da wahalhalu da musibu marasa dadi zasu sanya ci gaban rayuwa ya kasance wani abu ne da ba zai yiwu ba.
A cikin wasikar Imam (a.s) zuwa ga sheikh Mufid (K.S) yana cewa: Mu ba masu barin kiyaye wa gareku ba ne, kuma ba masu mantawa da ambatonku ba ne, ba domin haka ba da bala'o'i sun sauka a kanku, kuma da makiya suna kawar da ku daga doron kasa.
Don haka ranar samuwar Imami (a.s) tana haskaka wannan Duniya, kuma tana kwararo falalar Allah (s.w.t) ga dukkan samammu, kuma a cikin al'ummu musamman musulmi al'ummarsa shi'arsa suka yi imani da shi to sun fi kowa amfana daga albarkarsa kuma zamu kawo wasu misalai game da hakan.

Karfafa Buri
Buri jarin tafiyar da rayuwa ne, mu burinmu shi ne jarinmu na rayuwa da nishadinmu mai ci gaba ba yankewa, kuma shi ne yake sanya mu motsawa da aiwatarwa. Samuwar Imami a Duniya yana sanya mana burin samun nan gaba mai haske, kuma yana sanya shauki. Shi'a a tsawon tarihinsu sama da shekaru dubu daya da dari hudu, sun fuskanci bala'o'i daban daban, amma burin samun cewa akwai nan gaba mai haske ga muminai ya hana su samun rauni da gajiyawa da tsayawa kyam da kokari da rashin mika wuya. Addini imani ne kuma samun nan gaba ba tatsuniya b ace, nan gaba mai zuwa wacce take mai kusanci da take kusa, domin shugaban wannan zamani mai zuwa a raye yake, kuma a kowane sakand zai iya bayyana, don haka a kodayaushe da ni da kai dole mu kasance a shirye.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center for Islamic Propagation