Imam Mahadi A Wata Mahanga

Wasu Ra'ayoyin

Imam Mahadi A Wata Mahanga

Jagoran Shi'a na karshe kuma halifan Manzon Allah (s.a.w) na goma sha biyu, ya zo Duniya ne a ranar juma'a a watan sha'aban shekarar hijira kamariyya 255, wato miladiyya 868 a garin Samra'u (ko samarra) daya daga garuruwan Iraki. Babansa shi ne imamin Shi'a na goma sha daya Imam Hasan Askari (a.s) kuma babarsa ita ce: "Narjis" wacce a wata ruwaya ya zo cewa tana daga zuriyar Yasha'u ne dan shugaban Rum, kuma babarsa daga zuriyar Sham'un take wasiyyin Annabi Isa (a.s). A wata ruwaya ya zo cewa: Narjis ta tafi yaki ne da shiryarwa da kuma umarnin Imam Hasan Askari (a.s) sannan kuma a yaki ta fada cikin ribatattun yakin musulmi, sannan sai Imam Hasan da kansa ya aika wani domin ya je ya sayo masa ita ya kuma kawo masa ita garin Samra'u . Amma abin da yafi muhimmanci shi ne Narjis ta kasance a karkashin kulawar Hakima 'yar'uwar Imam Hadi (a.s) kuma ta samu ilimi da tarbiyya a hannunta kuma ta samu girmamawar Hakima sosai. Narjis ta samu yabo daga zantuttukan Manzo (s.a.w) da Imam Ali (a.s) da Imam Ja'afar Sadik (a.s) kuma sun yaba ta sosai, sun kuma ambace da mafificiyar baiwa. Kuma akwai wasu sunaye da suka zo game da sunan mahaifiyar Imam Mahadi (a.s) kamar; Susan, Raihana, Malika, Saikal.
Suna Da Alkunya Da Lakabi
Sunan Imam Mahadi da alkunyarsa kamar suna da alkunyar Annabi (s.a.w) ne, a wasu ruwayoyi kuwa an hana ambaton sunansa har sai ya bayyana. Lakabin da ya shahara su ne Mahadi, ka'im, bakiyyatul-Lahi, muntazar, hujjat, khalaf salih, mansur, sahibul amr, sahibuz zaman, waliyyul asr wanda mafi shahararsu shi ne Mahadi. Kowanne daga wadannan lakabobi yana bayar da wani sako game da wannan Imami mai girma ne.
An ce ana ce masa Mahadi ne saboda shi ne zai shiryar da mutane zuwa ga gaskiya, kuma ana ce masa ka'im domin shi ne zai tashi da yaki, kuma ana cewa da shi muntazar domin ana sauraron zuwansa, kuma ana ce masa bakiyyatul-Lahi domn shi ne ya rage daga cikin hujjojin Allah a bayan kasa. Kuma hujja yana da ma'anar mai sheda ga bayi, kuma khalafussalih da ma'anar cewa shi ne halifan waliyyan Allah da suka gabata, kuma ana ce masa mansur domin Allah zai taimake shi, kuma sahibul amr domin shi ne wanda zai samar da hukuma mai tsayar da umarnin Allah da adalcin Allah, kuma shi ne sahibuzzaman da kuma waliyyul asr da ma'anar wanda yake shi ne mai hukunci da umarni shi kadai a wannan zamani.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center for Islamic Propagation