Haihuwar imam Ali

Haihuwar imam Ali

AMIRUL MIMINA IMAM ALI (A.S.) Lakabinsa: Amirul munin, Sayyidul muslimin, Imamul muttakin, Ka’idul gurril muhajjalin, sayyidul ausiya, sayyidul arab, Almurtada, Ya’asubuddini, Haidar, Al-anza’al badin, Asadul-Lah. Alkunyarsa: Abul Hasan, Abul Hasanain, Abul Sibtain, Abu Raihanatain, Abu Turab. Mahaifinsa: Abu Talib (Baffan Annabi) Imran ko kuma Abdu manaf dan Abdul Mutallib. Mahaifiyarsa: Fatima Bintu Asad. Ranar Haihuwarsa: Ranar Juma' a 13 ga Rajab. Gurin Haihuwarsa: Cikin Ka'aba Dakin Allah mai alfarma. Shekarar Haihuwarsa: Shekara talatin bayan Shekarar Giwaye. Adadin ‘ya’yansa: masu tarihi sun yi sabani kan yawan ‘ya’yansa amma suna tsakanin 25 ne zuwa 33 a ruwayoyin daban daban. Wasu na cewa, `ya'yansa: 36, 18 da cikinsu maza ne 18 kuma mata, Mazan su ne: 1) Al- Hasan Mujtaba 2) Husain 3) Muhammad Bin Hanafiyya 4) Abbas Akbar wanda ake yi wa alkunya da Abul Fadli 5) Abdullahil Akbar 6) Ja'afarul Akbar 7) Usmanul Akbar 8) Muhammad Asgar 9)Abdullahil Asgar 10)Abdullah wanda ake yi wa Alkunya da Abu Ali. 11) Aun 12) Yahya 13) Muhammadul Awsat 14) Usmanul Asgar 15) Abbasul Asgar 16) Ja'afarul Asgar 17) Umarul Akbar 18) Umarul Asgar Mata kuwa su ne: 1 ) Zainabul Kubra, 2) Zainabul Sugra wadda ake kira Ummu Kulsum, 3) Ramlatal Kubra 4) Ummul Hasan 5) Nafisatu 6)Rukayyatus Sugra 7) Ramlatul Kubra 8) Rukayyatul Kubra 9) Maimunatu 10) Zainabus Sugra 11 ) Ummu Hani 12) Fatimatus Sugra 13) Imamatu 14) Khadijatus Sugra 15) Ummu Kulsum 16) Ummu Salama 17) Hamamata 18) Ummu Kiram Matansa: 1-Fadimatuz-Zahra’yar manzon Allah (A.S) 2- Amama ‘yar Abil Asi 3-Ummul banin Alkilabiyya 4-Laila ‘yar Mas’ud 5-Asma’u ‘yar Amis 6-Assahba’u ‘yar Rabi’a (ummu Habib) 7-Khaula ‘yar Ja’afar 8-Ummu Sa’ad ‘yar Urwa 9-Makhba’a ‘yar Imru’ul kais. Hatiminsa: Almulku Lillahi Wahidul Kahhar (Mulki na Allah ne Shi kadai mai cikakken rinjaye). Haihuwar Imam Ali (A.S): Imam Ali (A.S) shi ne na farko cikin jerin imaman gidan Annabta kuma shi ne wasiyyin manzon Allah (S.A.W). An haife shi ne a cikin dakin Allah mai alfarma watau ka'abah a daidai ranar 13 ga watan Rajab shekara ta 23 kafin hijira. Yanzu haka dai kabarinsa yana Najaf dake kasar Iraki. Yakokinsa: ya yi musharaka a yakokin manzo (S.A.W) gaba daya banda yakin Tabuka da manzo ya umarce shi da ya zauna a Madina domin tafiyar da al’amuranta amma yakokin da ya jagoranta da kansa a lokacin halifancinsa su ne: Aljamal da Siffaini da Annahrawan. Dalilin Rasuwarsa: Ibn Muljam ne ya kashe shi sakamakon harin ba zata da ya kai masa yana salla a cikin masallacin Kufa. Tsawon rayuwarsa: shekar 63. Tsayin imamancinsa: shekara 30. Tarihin shahadarsa: Daren jumma’a 21 ga watan azumi 40H. Wurin da ya yi shahada: Masallacin Kufa. Dalilin shahadarsa: Saran takobin nan na la’ananne Abdurrahman dan maljam yana mai sujada a mihrabin masallacin kufa. Inda aka binne shi: Yankin nan na gariyyi a garin Najaf madaukaki.

wanda ya cirato ya shigar Dan'uwa Sa'idu Funtua