shahadar Imam Musa AlKazim

shahadar Imam Musa Kazeem[AS]
 
Shi dai Imam Musa Ibn Ja'afar Al-Kazeem[AS] yayi shahada ne a rana irin ta 25 ga watan Rajab shekara ta 183 bayan hijirar Manzon Allah[SAWA].

Yayi shahada ne bayan shayar da shi guba da aka yi tare da umurnin sarkin Abbasiyawa Haruna wanda ya shahara da Haruna Rasheed, haramin sa na nan a Kazimiyyah a kasar Iraki inda ake ziyarar sa.

An haife shi ne a ranar 7 ga watan Safar shekara ta 128 a Abwa, wani gari kusa da birnin Madina.

Mahaifin sa shine limami na shida cikin jerin limaman shiriya na gidan Manzon Allah[SAWA] watau Imam Ja'afar Ibn Muhammad Assadiq[AS], mahaifiyar sa kuwa wata baiwar Allah ce da ake kira Hameedah[RA], yar Saeed Al-Barbariyyah.

Ya rayu a duniya tsawon shekaru 55 amma shekarun limancin sa sune shekaru 35.

 

wanda ya cirato ya shigar Dan'uwa Sa'idu Funtua