Hadafin Halittar Mu

HADAFIN HALITTARMU DA SANIN IMAMIN ZAMANINMU.

Bismillahirrahmanirrahim.

Abu na  1:

Allah ta'ala yana fadi a cikin Alkur'ani mai girma

 وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالْإِنْسَ إِلَّا لِيَعْبُدُونِ  [سوره الذاريات : 56]

Cewa ban halicci mutum da aljan ba sai dan su bautamin.

Wannan yake nuna mana cewa hadafi na halittan ba yi da Allah ta'ala ya yi shi ne domin su san shi kuma su bautamasa, kuma su zamto cikin hanyar bauta masa, amma wannan bayana nufin cewa Allah ta'ala nada buka tuwa zuwa ga bautarmu ba ne, a'a da dukkanin mutane zasu zama kafirai su ki bautar Allah ta'ala to babu abin da zasu kare shi da shi.

Da dukkanin mutane zasu zama kamar fir'auna ko kuma dukkanin mutane su zama kamar Imama Ali (A.S) to ba zasu kari Allah da komaiba, bautar Allah domin anfanuwar kan mune da kuma samun kamala a karan kanmu, saboda haka Allah ya haliccemu kuma ya sanya mu a hanyar bautarsa domin mukai ga wannan kamalan da ba'a iya samunta sai ta hanyar bautar.

Abu na 2:

Idan muka kalli abin da ke kaikawo a wannan duniyar zamuga wasu daga cikin mutane a wannan duniyar bautar gumaka suke yi, wasu daga cikinsu bautar dabbobi sukeyi, idan mukalli afrikanmu akwai addinai masu tarin yawan gaske, a bangaren Amerika suma idan muka waiwaya zamuga suma haka akwai masu bautar gumaka kai harda masu bautar ma son zukatansu ta yanda babu abin da suke aikatawa sai abin da zukatansu suka umarcesu koda ko ya sabama 'yan adamtaka koda ko bai yi kama da aiki na hankali ba, kai idan muka yi duba zuwa ga kusan rabin mutanen duniya da dama ba bautar Allah suke yi ba.

Acikin kusan biliyon 7 na mutanen duniya kusan rabinsu bautar wanin Allah sukeyi, kodai basu yarda da Allah ba wato suna karyata samuwan Allah din ko kuma suna bautar gumaka.

To wannan yake nuna cewa su ba bautar Allah suke yi ba , kaga ya nuna cewa su ba su san ma wancan hadafin halitta din da Allah yayi halintar domin saba, to idan muka koma ga kusan rabin mutanen duniyar ma da suka rage kusan rabinsu kiristocine  wanda suma idan muka kalli kiristocin bautar Annabi Isah suke yi wasu da yawa daga cikin su, wasu har sujada sukeyi ga Annabi Isah (A.S) suna ganinsa a matsayin zati na Allah, wadannan kaga suma basu fahimci hadafin Allah ta'ala ba na yin halitta.

Idan muka juyo kan musulmi ma sai muga a yaya suke wani irin hali suke ciki, zamuga da yawansu ba su fahimci abin da alkur'ani yake kokarin doramu a kai ba, saboda haka idan muka yi duba na gaba daya ga dukkanin al'umma sai muga kadanne daga cikinta suka fuskanci hadafin yin halittan dan adam

Abu na: 3: Mafitar al'umma.

Mafitar Al'umma idan muka duba shine komawa ga koyarwa na addinin manzon tsira da kuma wasiccin daya yi ga wannan al'ummar, yazo acikin hadisai masu yawan gaske wanda sunkai haddin tawatur daga dukkanin mazahabobi na musulunci cewa manzon Allah yana cewa a cikin wasiccinsa ga wannan Al'ummar cewa :

Nabar muku nauyayan abubuwa guda biyu wanda idan kukayi rko dasu a bayana bazaku taba bata ba har abada, sune Littafin Allah da iyalan gidana.

To sai mukoma akaran kanmu mukalla cewa shin wannan wasiccin da Manzo yayi mana munyi riko da ita?

Shin yanzu rayuwar mu hukuncin Allah ke tafiyar da ita ko kuwa son zukatanmu?

Shin munyi riko da iyalan manzon Allah din ko kuwa bamuyi ba?

To wadannan tambayoyine daya kamata muba kanmu amsoshinsu, domin mafitarmu da tsiranmu na cikin wadannan amsoshin na cewa munyi riko da Alkur'ani kuma shike tafiyar da rayuwarmu, kuma munyi riko da Ahlul baitin manzon tsira domin sukaimu ga tsira.

Manzon Allah na cewa: Misalin iyalan gidana a cikinku kamar misalin jirgin Annabi Nuhu ne, duk wanda ya hauta ya tsira , duk kuma wanda bai hauba ya halaka.

4- Abu na hudu shine ina so inyi nuni da ishara zuwa ga mahimmancin sanin Shugaba na wannan lokacin namu damuke ciki.

Wanda yazo a cikin hadisai Manzon Allah yana cewa:

 Duk wanda ya mutu baisan limamin zamaninsa ba to yayi mutuwa irin mutuwar Jahiliyya.

To tambaya anan wane ne lmamin zamanin namu?

Kuma wane hakki yake dashi akanmu?

To amsa a nan shi ne limamin zamanin mu shi ne Imam Mahdi (A.S) kuma shi ne dan Imama Hasan Al'askari wanda aka haifeshi tun a cikin shekara da dari biyu da hamsin da biyar bayan hijira kuma yana cikin gaiba(wato bama iya ganinsa) wanda shine Allah ta'ala yayi alkawarin cewa zai cika wannan duniyar da gaskiya da adalci kamar yanda taka cika da danniya da zalunci.

Wanda shine kuma Allah ta'ala ya wajabtamana da'a gare shi , wanda babu wani da zai iya kaiwa ga allah ta'ala sai ta hanyarsu هم باب الله الذي منه يأتى wato sune kofofi na Allah wanda ta hanyarau ake iya kaiwa ga Allah.

Kuma shi Imam Mahdi yana raye a tare damu sai dai bamu iya saninsa a cikinmu kamar yanda yazo cewa يرونه ولا يعرفونه ma'ana muna iya ganin sa amma bamusan shine ban.

Kuma muna amfanuwa dashi duk da kuwa bama iya ganeshi domin yazo cikin kalaman A'immatu Ahlul baiti cewa wannan duniyar bazata taba kasan cewa babu Hujjar Allah abayan kasaba muna ganinsa a cikinmu kamar yanda sauran A'imma suka rayu da al'umma ko kuwa suna cikin gaiba kamar Imaminmu Imam Mahdi (A.S).

Maganar dangane da Imamu Mahdi(A.S) to magana ce mai fadin gaske, domin shi al'amarinsa abune dake cewa dukkanin  littafan al'ummar musulmi sunyi ittifakin cewa lallai ne a karshen zamani za'a sami wani bawan Allah daga cikin zurriyar Manzon Allah  (S.A.W) wanda ta hannunsane zai zamto ansamu wannan duniyar ta cika da gaskiya kamar yanda ta ka cika da zalunci da danniya.

Saboda haka yana da kyau mukomo cikin hayyacinmu domin sanin Limamin zamaninmu gudaun kada mu yi mutuwar da ba mu da shugaba a ranar tashin alkiyama.

Muna kara taya Al'ummar musulmin duniya baki daya murna na zagayowar wannan rana ta haihuwar Imaminmu Imamin wannan zamani wato Imami na sha biyu daga cikin Imaman tsira wato Imam Mahdi (A.S) Allah ta'ala ka gaggaura bayyanarsa kuma kasanyamu daga cikinabiyansa na gari kasanyamu kuma cikin wanda zasu yi shahada a cikin rindinar sa tare da shi.