SURATUN NAZI'ATI

 
بِِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ
 
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin Kai
 
وَالنَّازِعَاتِ غَرْقًا
1. Ina rantsuwa da mala'iku masu fisgar rayuka da karfi.
 
وَالنَّاشِطَاتِ نَشْطًا 
2. Da masu daukar rayuka da sauki a cikin nishadi.
 
وَالسَّابِحَاتِ سَبْحاً 
3. Da masu sauka daga sama da umurnin Allah kamar suna iyo.
 
فَالسَّابِقَاتِ سَبْقًا 
4. Sa'an nan, su zama masu gaugawa (da umurnin Allah) kamar suna tsere.
 
فَالْمُدَبِّرَاتِ أَمْرًا 
5. Sa,an nan, su kasance masu shirya gudanar da umurni.
 
يَوْمَ تَرْجُفُ الرَّاجِفَةُ 
6. Ranar da mai girgiza abubuwa (busar farko) za ta kada.
 
تَتْبَعُهَا الرَّادِفَةُ 
7. Mai biyar ta (busa ta biyu) na biye.
 
قُلُوبٌ يَوْمَئِذٍ وَاجِفَةٌ 
8. Wasu zukata, a ranar nan, masu jin tsoro ne.
 
أَبْصَارُهَا خَاشِعَةٌ 
9. Alhali idanunsu na kaskantattu.
 
يَقُولُونَ أَئِنَّا لَمَرْدُودُونَ فِي الْحَافِرَةِ 
10. Suna cewa; Ashe lalle za a iya mayar da mu a kan sawunmu?
 
أَئِذَا كُنَّا عِظَامًا نَّخِرَةً 
11. Ashe, idan muka zama kasusuwa rududdugaggu?
 
قَالُوا تِلْكَ إِذًا كَرَّةٌ خَاسِرَةٌ 
12. Suka ce; Waccan kam komawa ce, tababbiya!
 
فَإِنَّمَا هِيَ زَجْرَةٌ وَاحِدَةٌ 
13. To, ita kam, tsawa guda kawai ce.
 
فَإِذَا هُم بِالسَّاهِرَةِ 
14. Sai kawai ga su a bayan kasa.
 
هَلْ أتَاكَ حَدِيثُ مُوسَى 
15. Shin, labarin Musa ya zo maka?
 
إِذْ نَادَاهُ رَبُّهُ بِالْوَادِ الْمُقَدَّسِ طُوًى 
16. A lokacin da Ubangijinsa Ya kiraye shi, a cikin kwari mai tsarki, wato Duwa?
 
اذْهَبْ إِلَى فِرْعَوْنَ إِنَّهُ طَغَى 
17. Ka tafi zuwa ga Fir'auna, lalle ne shi ya ketare haddi.
 
فَقُلْ هَل لَّكَ إِلَى أَن تَزَكَّى 
18. Sai ka ce masa, Ko za ka so ka tsarkaka.
 
وَأَهْدِيَكَ إِلَى رَبِّكَ فَتَخْشَى 
19. Kuma in shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka domin ka ji tsoronSa?
 
فَأَرَاهُ الْآيَةَ الْكُبْرَى 
20. Sai ya nuna masa ayar nan mafi girma.
 
فَكَذَّبَ وَعَصَى 
21. Sai ya karyata, kuma ya saba.
 
ثُمَّ أَدْبَرَ يَسْعَى 
22. Sa'an nan ya juya baya, yana tafiya da sauri.
 
فَحَشَرَ فَنَادَى 
23. Sai ya yi gayya, sa'an nan ya yi kira.
 
فَقَالَ أَنَا رَبُّكُمُ الْأَعْلَى 
24. Sai ya ce; Ni ne Ubangijinku mafi daukaka.
 
فَأَخَذَهُ اللَّهُ نَكَالَ الْآخِرَةِ وَالْأُولَى 
 
25. Saboda haka Allah Ya kama shi, domin azabar maganar karshe da ta farko.
 
إِنَّ فِي ذَلِكَ لَعِبْرَةً لِّمَن يَخْشَى 
26. Lalle ne, a cikin wannan hakika akwai abin kula ga wanda yake tsoron Allah.
 
أَأَنتُمْ أَشَدُّ خَلْقًا أَمِ السَّمَاءَ بَنَاهَا 
27. Shin, ku ne mafi wuyar halitta ko sama? Allah Ya gina ta.
 
رَفَعَ سَمْكَهَا فَسَوَّاهَا 
28. Ya daukaka rufinta, sa'an nan Ya daidaita ta.
 
وَأَغْطَشَ لَيْلَهَا وَأَخْرَجَ ضُحَاهَا 
29. Kuma Ya duhuntar da darenta, kuma Ya fitar da hantsinta.
 
وَالْأَرْضَ بَعْدَ ذَلِكَ دَحَاهَا 
30. Kuma, kasa a bayan haka Ya mulmula ta.
 
أَخْرَجَ مِنْهَا مَاءَهَا وَمَرْعَاهَا 
31. Ya fitar da ruwanta daga gare ta da makiyayarta.
 
وَالْجِبَالَ أَرْسَاهَا 
32. Da duwatsu, Ya kafe su.
 
مَتَاعًا لَّكُمْ وَلِأَنْعَامِكُمْ 
33. Domin jiyarwar dadi a gare ku, kuma ga dabbobinku.
 
فَإِذَا جَاءَتِ الطَّامَّةُ الْكُبْرَى 
34. To, idan uwar masifu mafi girma, ta zo.
 
يَوْمَ يَتَذَكَّرُ الْإِنسَانُ مَا سَعَى 
35. Ranar da mutum zai yi tunanin abin da ya aikata.
 
وَبُرِّزَتِ الْجَحِيمُ لِمَن يَرَى 
36. Kuma, a bayyana Jahim ga mai gani.
 
فَأَمَّا مَن طَغَى 
37. To, amma wanda ya yi girman kai.
 
وَآثَرَ الْحَيَاةَ الدُّنْيَا 
38. Kuma, ya zabi rayuwar duniya.
 
فَإِنَّ الْجَحِيمَ هِيَ الْمَأْوَى 
39. To, hakika Jahim ita ce makoma.
 
وَأَمَّا مَنْ خَافَ مَقَامَ رَبِّهِ وَنَهَى النَّفْسَ عَنِ الْهَوَى 
40. Kuma, amma wanda ya ji tsoron tsayi a gaban Ubangijinsa, kuma ya kange kansa daga son rai.
 
فَإِنَّ الْجَنَّةَ هِيَ الْمَأْوَى 
41. To, lalle ne Aljanna ita ce makoma.
 
يَسْأَلُونَكَ عَنِ السَّاعَةِ أَيَّانَ مُرْسَاهَا 
42. Suna tambayar ka game da alkiyama, wai yaushe ne matabbatarta?
 
فِيمَ أَنتَ مِن ذِكْرَاهَا 
43. Me ya hada ka da ambatonta?
 
إِلَى رَبِّكَ مُنتَهَاهَا 
44. Zuwa ga Ubangijinka karshen al'amarinta yake.
 
إِنَّمَا أَنتَ مُنذِرُ مَن يَخْشَاهَا 
45. Kai mai gargadi kawai ne ga mai tsoronta.
 
كَأَنَّهُمْ يَوْمَ يَرَوْنَهَا لَمْ يَلْبَثُوا إِلَّا عَشِيَّةً أَوْ ضُحَاهَا 
46. Kamar su a ranar da za su gan ta, ba su zauna ba face a lokacin marece ko hantsinta.