AHLULBAITI (A.S) A KUR'ANI DA HADISI 2

CIGABA DAGA MAKALA TA FARKO:-

 

A MAHANGAR SUNNAR
MA’AIKI

Akwai hadisai masu yawan gaske da aka ruwaito daga Manzon Allah (s.a.w) da suke magana kan falalar Zuriyarsa da wajibcin kaunarsu, da kuma cewa su ne jiragen ruwan tsira. Ga wasu daga cikinsu:

  1. An ruwaito halifa Abubakar yana cewa: “Na ga Manzon Allah (s.a.w) ya kafa wata haima ya jingina da ita a cikin haimar akwai Ali da Fatima da Hasan da Husain sai ya ce: Ya ku jama’ar musulmi ina zaman lafiya da wanda ya zauna lafiya da wadanda suke cikin wannan haimar, kuma mai yaki da wanda ya yake su, mai kaunar wanda ya mika musu wuya (wanda ya so su), babu mai sonsu sai mai halaltattun iyaye, sannan ba mai kinsu sai haramtattun iyaye, wanda ba dan halal ba[1]”.
  2. Zaid bn Arkam ya ruwaito cewa Manzon Allah (s.a.w) ya ce wa Ali da Fatima da Hasan da Husain (a.s) cewa: Ina fada da wanda ya yi fada da ku kuma ina zaman lafiya da wanda ya zauna lafiya da ku[2].
  3. Ahmad bn Hambal ya ruwaito cewa Manzon Allah (s.a.w) ya rike hannayen Hasan da Husain ya ce: Duk wanda ya so ni ya kuma so wadannan biyu da babansu da mahaifiyarsu lalle zai kasance tare da ni a inda nake a ranar Kiyama[3].
  4. Jabir yana cewa: “Wata rana Manzon Allah (s.a.w) a Arafa alhali Ali yana kusa da shi ya ce: Matso kusa da ni Ya Ali an halicce ni da kai daga wata bishiya wacce ni ne tushenta kai kuma kai ne reshenta Hasan da Husain kuma su ne gabbanta, duk wanda ya rike rassanta Allah Zai shigar da shi Aljanna[4].
  5. Ibn Abbas ya ruwaito cewa Manzon Allah (s.a.w) ya ce: Taurari kariya ce ga mutanen kasa daga nutsewa (halaka), Ahlubaitina kariya ce ga al’ummata daga sabani, idan wata kabila daga larabawa ta saba musu, za su rarraba su zamanto kungiyar Ibilis[5].
  6. Zaid bn Arkam ya ruwaito cewa Manzon Allah (s.a.w) ya ce: Lalle ni na bar muku wasu nauyayan abubuwa guda biyu da idan kuka yi riko da su ba za ku taba bata ba, dayansu yafi dayan, Littafin Allah mikakkiyar igiya daga sama zuwa kasa da kuma Zuriyata Ahlubaitina, lalle ba za su taba rabuwa da juna ba har sai sun hadu da ni a bakin tafki. Ku kula da yadda za ku wakilce ni dangane da su[6].

Hadisin nauyaya biyu (al-Thakalain) na daga cikin sanannun hadisan Ma’aiki (s.a.w) tsakanin musulmi, a lokuta da dama Manzon Allah (s.a.w) ya sha nanata wannan hadisi. Daga cikin hakan har da abin da Zaid bn Arkam ya ruwaito yana cewa: ‘wata rana Manzon Allah (s.a.w) ya sauka a Juhfa ya fuskanci jama’a bayan ya mika godiya ga Allah da tsarkake Shi sai ya ce: Hakika ban ga wani Annabi da ya wuce rabin shekarun wanda ya gabace shi ba, lalle an kusan kirana kuma in amsa, me za ku ce?

Sai suka ce: Lalle ka yi mana nasiha.

Sai ya ce: Ashe ba ku shaida babu wani Ubangiji sai Allah ba, kuma Muhammad bawanSa ne kuma manzonSa, kuma Aljanna gaskiya ce wuta ma gaskiya ce ba?

Suka ce: Mun shaida.

Sai Annabi (s.a.w) ya daga hannunsa ya sanya shi a kan kirjinsa ya ce: Ni ma na shaida tare da ku. Sai ya kalle su ya ce:

  • “Ba ku ji ba?...”.
  • “Na’am…”.

Sai ya ce: Lalle ne zan gabato tafki, ku ma za ku same ni a bakin tafkin wanda fadinsa ya kai abin da ke tsakanin San’a da Basra, akwai kofunan azurfa adadin taurari a cikinsa, don haka ku kula da yadda za ku halifce ni cikin nauyaya biyu?...”.

Sai wani daga cikinsu ya ce masa: Ya Rasulallah! Mene ne wadannan nauyaya biyu”.

Sai Manzon Allah (s.a.w) ya ce: Littafin Allah, wani sashi yana hannun Allah Madaukakin Sarki daya sashin kuma yana hannunku, ku yi riko da shi, dayan kuma Zuriyata. Hakika Allah Madaukakin Sarki Ya bani labarin cewa ba za su taba rabuwa da juna ba har sai sun hadu da ni a bakin tafki, na roki hakan gare su daga wajen Ubangijina, kada ku gabace su sai ku halaka, kada ku nuna gazawa daga gare su, kada ku ce za ku sanar da su saboda sun fi ku ilimi. Sai ya kama hannun Ali (a.s) ya ce: Duk wanda na zamanto mafi soyuwa a gare shi sama da kansa, to Aliyu shugabansa ne. Ya Allah ka so wanda ya so shi, ka ki wanda ya ki shi”[7].

Har ila yau Manzon Allah (s.a.w) ya ambaci wannan hadisi na nauyaya biyu a lokacin rashin lafiyarsa na karshe, yana gaya wa sahabbansa cewa:

“Ya ku mutane! An kusan daukana cikin gaggawa, lalle na bar muku wata magana da za ta fisshe ku. Na bar muku Littafin Ubangijina Madaukakin Sarki da Zuriyata Ahlubaitina. Sai ya kama hannun Ali (a.s) ya daga shi sama ya ce: Ga Aliyu nan yana tare da Alkur’ani kuma Alkur’ani na tare da Aliyu, ba za su taba rabuwa ba har sai sun hadu da ni a bakin tafki”[8].

Hadisin Thakalain yana daga cikin mafiya ingancin hadisan Ma’aiki (s.a.w). Al-Manawi ya ruwaito daga al-Samhudi yana cewa: Akwai sama da sahabbai ashirin da suka ruwaito wannan hadisi[9]. Ibn Hajr yana cewa: Wannan hadisi yana da hanyoyi da yawa daga wajen sama da sahabbai ashirin[10].

Hadisin Thakalain ya kebance Ahlulbaiti (a.s) ga lamarin shugabanci (imamanci), kuma yana nuni da ismarsu wato tsarkakansu daga dukkan dauda da zunubi. Ya kwatanta su da Littafin Allah mai girma wanda bata ba ta zuwa masa daga gabansa da kuma bayansa. A fili yake cewa kaurace musu rabuwa ne da Littafin Allah sannan ismarsu a cikin wannan hadisi a fili yake.

7- Abu Sa’id al-Khudri ya ce: “Na ji Manzon Allah (s.a.w) ya ce: Hakika misalin Ahlubaitina a cikinku kamar jigin Annabi Nuhu ne wanda ya hau shi ya tsira wanda kuwa ya saba masa ya halaka. Hakika matsayin Ahlubaitina a cikinku matsayin kofar tsira ne ga Bani Isra’ila wanda ya shige ta an gafarta masa”[11].

Imam Sharafuddeen ya yi karin bayani kan wannan hadisi da cewa: Ka riga da kasan cewa abin nufi da kwatanta su da yayi da jirgin (Annabi) Nuhu shi ne cewa duk wanda ya koma gare su cikin lamurran addininsa yayi riko da rassa da tushensa daga Imamansu ya tsira daga azabar wuta, wanda kuwa ya saba musu tamkar mutumin da ya koma ga dutse ne don ya tseratar da shi daga ruwan dufana amma ya nutse cikin ruwan, babu shakka yana cikin ruwan Jahannama – Allah Ya tsare mu -. Sannan bangaren kwatanci da kofar tsira (ta Bani Isra’ila) shi ne cewa Allah Madaukakin Sarki ya sanya wannan kofa ta zamanto alamar tawali’u ga girmanSa Madaukakin Sarki da mika kai ga ikonsa, hakan shi ne dalilin gafarar. Wannan shi ne bangaren kwatanci. Ibn Hajr ya kawo wannan hadisi da waninsa da suke kama da shi:

“Fuskar kwatantasu da jirgin (Annabi Nuhu) shi ne wanda ya so su ya kuma girmama su don nuna godiya ga ni’imar samuwarsu da riko da shiriyar malamansu ya tsira daga duhun rarrabuwa. Wanda ya saba wa hakan ya nitse cikin kogin kafircewa ni’ima da kuma halaka cikin ramin dagawa” har zuwa inda yake cewa: “Dangane da babin tuba kuwa – wato fuskar kwatanci da kofar tuba – shi ne cewa Allah Ta’ala ya sanya shiga wannan kofar wanda ita ce kofar Baitul Mukaddis cikin tawali’u da neman gafara sababi ne na gafara. Don haka aka sanya wa wannan al’umma kaunar Ahlulbaiti dalilin gafara”[12]. Manzon Allah (s.a.w) ya sanya Ahlubaitinsa tamkar jirgin Nuhu, komawa gare su da kaunarsu hanya ce ta tsira, sannan gaba da su kuwa hanyar bata da halaka.

8- Manzon Allah (s.a.w) ya ce: “Sanin Zuriyar Muhammad barranta ne daga wuta, kaunar Zuriyar Muhammad nasarar ketare siradi ne, mika wilaya ga Zuriyar Muhammad kariya ce daga azaba”[13].

9- Manzon Allah (s.a.w) ya ce: “Ku sanya matsayin Ahlubaitina a wajenku tamkar matsayin kai ga jiki, da kuma matsayin idanuwa ga kai, kai ba zai shiriya ba tare da idanuwa ba”[14].

10- Manzon Allah (s.a.w) ya ce: “Kafar bawa ba ta motsawa ranar tashin kiyama har sai an tambaye shi kan abubuwa hudu: kan rayuwarsa yadda ya tafiyar da ita, kan jikinsa yadda ya sarrafa shi, kan dukiyarsa yadda ya ciyar da ita da kuma yadda ya samo ta da kuma soyayyarmu Ahlulbaiti”[15].

11- Manzon Allah (s.a.w) ya ce: “Duk wanda yake son ya yi rayuwa irin tawa kuma ya mutu irin mutuwa ta, ya shiga Aljannar da Ubangijina ya tsara ta, to ya riki Ali a matsayin shugabansa a bayana, kuma ya riki waliyinsa, ya yi koyi da Ahlubaitina a bayana don su ne zuriyata, an halicce su daga kasar da aka halicce ni, aka arzurta su da fahimtata da ilimina. Bone ya tabbata ga masu karyata falalarsu daga cikin al’ummata, masu yanke zumuncina a cikinsu, ba za su taba samun cetona ba”[16].

Akwai hadisai masu yawan gaske makamantan wannan hadisi da suka zo daga wajen Manzon Allah (s.a.w) kan falalar Zuriyarsa da nuni da irin matsayin da suke da shi mai girma a wajen Allah Madaukakin Sarki. Dubi cikin wadannan hadisai da ayoyin da suka gabata za a iya fahimtar abin da Allah Ta’ala da ManzonSa (s.a.w) suke nufi shi ne ayyana Ahlulbaiti (a.s) a matsayin shugabanci da jagorancin al’umma cikin lamurran duniya da lahira, saboda su ne suka fi cancanta da matsayin Annabi (s.a.w) sama da wasunsu. Sun tashi ne cikin shiriyarsa sannan kuma suka sha daga kogin hikima da dabi’unsa.

Hakika Allah Madaukakin Sarki Ya zabe su a matsayin jagorori, masu shiryar da bayinSa kuma aminai wajen isar da sakonSa. Babu shakka da a ce al’umma sun rike su bayan wafatin Ma’aiki (s.a.w) da ba su fuskanci matsaloli da bala’oin da suka fuskanta ba. Hakika daga wajen Allah muke kuma wajenSa za mu koma.

ZAMU CI GABA AFITOWA MAI ZUWA:-

 

[1]- Al-Riyadh al-Nadhra, 25/252.

[2]- Sahih Tirmidhi, 2/319, Ibn Majah ya ruwaito cikin Sunan nasa 1/52 cewa Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: “Ina zaman lafiya da wanda kuka zauna lafiya da shi sannan ina fada da wanda kuka yi fada da shi” haka nan Al-Hakim ya ruwaito makamancin hakan cikin Al-Mustadrak nasa 3/149 da Ibn Athir cikin Asad al-Gahbah, 5/523 da Ahmad cikin Musnad dinsa 25/242.

[3]- Musnad Ahmad, 1/77 da Sahih Tirmidhi, 2/301.

[4]- Musnad Ahmad, 1/77.

[5]- Mustadrak al-Hakim 3/149 a cikin Kanzul Ummal 6/116 da Sawa’ik al-Muhrika shafi na 111 Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: “Taurari kariya ce ga mutanen kasa Ahlubaitina kuma kariya ce ga al’umma ta”, Al-Manawi ma ya ruwaito shi cikin Faidhul Ghadir, 6/297 da Al-Haithami cikin Majma’ansa 9/174.

[6]- Sahih Tirmidhi 2/308 da Asadul Ghabah, 2/12.

[7]- Majma’a al-Haithami, 9/163.

[8]- Al-Sawa’ik al-Muhrika, shafi na 75.

[9]- Faidhul Ghadir 3/14.

[10]- Sawa’ik al-Muhrika, shafi na 136.

[11]- Majma’ al-Zawa’id 9/168, Mustadrak al-Hakim 2/43 da Tarikh Bagdad 2/19.

[12]- Al-Muraja’at, shafi na 54.

[13]- Al-Muraja’at shafi na 58 ya nakalto shi daga littafin al-Shifa’, shafi na 40.

[14]- Al-Muraja’at shafi na 58 ya nakalto shi daga Al-Sharaf al-Mu’abbad, shafi na 58.

[15]- Al-Muraja’at ya nakalto shi daga al-Suyiti cikin Ihya al-Mayyit da al-Nabahani cikin Arba’in dinsa.

[16]- Kanzul Ummal, 6/217.