Bayanin Humusi

MARUBUCI: Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
HUMUSI DA ZAKKA Humusi a shari'ance shi ne karbar daya bisa biyar din abin da musulmi yake samu wanda ya yi saura daga bukatunsa na rana, ko sati, ko wata, ko shekara. Da yawa malamai sun yi magana kan shar'anta shi, da iyakokinsa, da kuma dalilan da suka sanya imamai suka muhimmantar da shi da tsanantawa kan wanda ya ki fitar da shi.
Mutum yana iya fitar da humusin dukiyarsa a kowace rana ko sati, ko wata, ko shekara, ta yadda da zai ci ribar dala 100 a rana, sai ya ga ran nan ba shi da wata bukata, to yana iya fitar da dala 20 humusi daga wannan ribar ta wannan ranar.
Ko kuma ya ga cewa bayan ya biya bukatunsa na ran nan akwai sauran dala 50 ta ribar da ya samu a wannan ranar, ko kuma kyautar da ya samu da sauransu, to yana iya fitar da humusin wannan ragowar da ke hannunsa idan ya so wato dala 10 ke nan. Haka nan zamu kwatanta a kowane janibi, kamar a ribar da aka samu ta kasuwanci ko wani ladan aiki da kwangila, ko wata haka daga ma'adinai, ko kuma taska da ya samu.
Mafi yawan mutane suna fitarwa a shekara musamman masu kasuwanci domin ya fiye musu dadin lissafi, don haka ne ma a littattafan fikihu yawanci akan yi maganar shekara ba don tana ka'ida ba, sai don yawancin mutane suna amfani da shekara ne. Don haka wanda shi yana fitarwa a sati, ko wata, ko kullum ne, da wannan ne zai yi lissafi. Sayyid Adil Alawi daga malamanmu yakan ce yana fitar da humusi kullum ne na abin da ya rage daga abin da ya samu ya ragu bayan bukatunsa. Humusi yana wajaba a cikin abubuwa shida:
1- Ribar kasuwanci
2- Ma'adanai
3- Taska
4- Dukiyar da ta cakuda da haram
5- Abin da ake tsamowa a kasan ruwa ta hanyar nutso
6- Ganimar yaki
Idan mutum ya ci riba a cikin kasuwanci ko sana'a ko sauran nau'o'in kasuwanci, kai har ma cikin kudin jingar da ya yi don rama sallar mamaci ko azuminsa, kuma bayan ya biya bukatunsa wani abu ya hau kai da ya dadu a kan bukatunsa na shekara tare da na iyalinsa, to ya wajaba ya fitar da humusinsa ya sarrafa su a inda zamu yi bayani nan gaba in Allah ya so.
Idan da akwai wani mutum da zai zai dauke masa nauyinsa ko da kuwa kyauta ne, ta yadda dukkan abin da ya samu yana ajiyewa ne, to wajibi ne ya fitar da humusin dukkan ribar da ya samu.
Wajibi ne ga attajiri, da dan kasuwa, da mai sana'a, da ma'aikata, da sauransu, su ba da humusin abin da ya dadu a kan bukatunsu na shekara, yayin da shekarar da suka fara kasuwanci ta kewayo.
Ya halatta a ba da humusin ribar da aka samu da zarar an same ta, kuma ya halatta a jinkirta har zuwa karshen shekara.
Dukkan abin da mutum ya kashe na ribar kasuwanci a tsakiyar shekara, na daga abinci da tufafi da kayayyakin gida da sayen gida da aurar da 'ya'yansa maza da mata, da makamancin wannan, idan har bai dadu a kan abin da ya dace da matsayinsa ba, kuma bai yi barna ba, to za a kirga shi a cikin bukatunsa na shekara, haka nan ma bai wajaba ya fitar da humusin abin da ya kashe bisa bakance, da kaffara, da kyauta ba.
Idan abin da ya saya don ya ajiye don bukatun shekara na daga alkama da sha'ir da shinkafa da sauransu ya ragu a karshen shekara, to ya wajaba ya ba da humusinsa.
Ya halatta ga mutum ya ba da humusin komai daga ainihinsa ne, ko kuma ya bayar da kimarsa. Kamar idan yana sayar da motoci, to yana iya bayar da mota a matsayin humusi idan dai ita ce kimar daya cikin biyar na abin da ya rage bayan bukatunsa, ko kuma ya bayar da kimarta.
Humusi ya wajaba a cikin abin da ake fitarwa na daga ma'adinai kamar fetur, da zinare, da azurfa, da tagulla, da uraniyom, da sauransu, idan ya kai nisabi. Nisabin ma'adinai kuwa shi ne awo 15 na zinare wanda aka sani.
Idan ya kai haka sai a fitar da 1/5 na abin da rage bayan an fitar da kudin da aka kashe wurin fitar da shi da suka hada gyara shi, da tace shi, da kudin ma'aikata, daga cikin kudin sayar da shi. To bayan an cire duk abin da aka kashe masa hatta da kudin ma'aikatan hakowa an fitar da shi, abin da ya rage ko miliyan nawa ne zai fitar da 1/5 daga ciki a matsayin humusi.
Idan dukiyar halal ta hadu da ta haram ta yadda ba za a iya tantance ta ba kamar idan ba a san mai dukiyar haram din ba kuma ba a san gwargwadonta ba, to ya wajaba a ba da humusin dukkan dukiyar.
Idan dukiyar halal ta hadu da ta haram, kuma aka san mikdarin dukiyar haram din sai dai ba a san mai ita ba, to ya wajaba a yi sadaka da gwargwadonta a maimakon mai ita, amma mafi kyau a hada da neman izinin shugaba na shari'a, idan kuma halal ta hadu da haram kuma ba a san gwargwadon haram din ba, sai dai an san mai dukiyar, to ya wajaba a yi yarjejeniya tare da mai ita.
Idan kafirin amana ya sai fili a wajen musulmi, ya wajaba ya ba da humusin filin, haka nan idan ya sayar da kasar da ya saya daga wajen musulmi zuwa wani wusulmin daban, to humusinta bai saraya ba, lalle ya wajaba ga mai sayen ya ba da humusinta.
Ana kasa humusi zuwa kaso biyu: Rabinsa kason sharifai ne kuma ya wajaba a ba da shi ga bahashime talaka ko maraya ko mabukaci a cikin tafiya daga cikinsu. Daya kason kuwa na Imam ne kuma ya wajaba a mika shi zuwa mujtahidin da ya cika sharadai a lokacin boyuwar Imam (a.s) ko kuma a sarrafa shi a inda mujtahidin ya yi izini, ko mika ta ga wakilinsa da ya ayyana don karba.
Duk abin da aka ambata na kaso biyu na humusi hukuncinsa shi ne a mika shi ga mujtahidin ko wakilinsa, humusin na imami (a.s) ne ko na sharifai. Sai dai idan mujtahidin ko wakilinsa ya bayar da izinin raba shi ga mai fitarwa, ko kuma izinin yin wani aiki na musamman da shi.

Zakka Zakka: Tana daga cikin wajibai na tattalin arziki da aka ambata a cikin Kur'ani bayan salla, kuma an san ta a matsayin alama ta imani, kuma sababi na rabauta.
Zakka ta wajaba a cikin wadannan abubu-wan:
(Alkama, Sha'ir, Dabino, Zabib, Zinare, Azurfa, Rakumi, Saniya, da Awaki/Tumaki, daidai da sharudda na musamman da ma'auni ayyananne da za a ambace su daga baya. Kuma wajibi ne ga mutane su bayar da zakka da nufin nema yardar Allah (s.w.t).
Zakka tana wajaba a cikin kayan abinci masu daraja guda hudu wadanda aka ambata, idan har suka kai nisabi. Nisabi shi ne: kilogram 850, kuma ana kiransa nisabi idan kuma ya yi kasa da haka to babu zakka a cikinsa.
Ya wajaba a ba da zakkar zinare da azurfa wadanda aka kera a kowace shekara har sai ya yi kasa da gejin nisabi, wanda shi ne: awo 15 na zinariya da kuma awo 105 na azurfa.

Zakkar Dabbabobi: Rakumi Rakumi yana da nisabi goma sha biyu:
1-Rakuma biyar, zakkarsu, akuya daya ce.
2-Rakuma goma, zakkarsu awakai guda biyu.
3-Rakuma goma sha biyar, zakkarsu awakai uku.
4-Rakuma ishirin, zakkarsu awakai hudu.
5-Rakuma ishirin da biyar, zakkarsu awakai biyar.
6-Rakuma ishirin da shida, zakkarsu "Bintu mahadh" guda daya ta rakumi: ita ce wacce ta shiga shekara ta biyu. 7-Rakuma talatin da shida, zakkarsu "Bintu labun" ita ce wacce ta shiga shekara ta uku.
8-Rakuma arba'in da shida, zakkarsu "Hikka", ita ce wacce ta shiga shekara ta hudu.
9-Rakuma sittin da daya, zakkarsu "Jaza'a" ita ce wacce ta shiga shekara ta biyar.
10-Rakuma saba'in da shida, zakkarsu "Bintu labun" guda biyu.
11-Rakuma casa'in da daya, zakkarsu "Hikka" guda biyu. 12-Rakuma dari da ishirin da daya, ko sama da haka, sai ya fitar da "Bintu labun" a cikin dukkan arba'in.

Zakkar Shanu Zakkar saniya talatin 30 akuya daya ce wacce ta shiga shekara ta biyu. Shanu arba'in 40 kuwa, akuya daya ce wacce ta shiga shekara ta uku, shanu 60 zakkarsu akuya biyu ce "Labun" wadanda suka shiga shekara ta biyu. Idan kuwa suka haura haka, sai a fitar da akuya daya wacce ta shiga shekara ta biyu ga dukkan talatin.

Zakkar Tumaki da Awaki
Zakkar akuyoyi 40, akuya daya ce. Akuyoyi 121 kuma zakkarsu akuya biyu ce.
Akuyoyi 201, zakkarsu guda uku ce. 301 kuwa, zakkarsu guda hudu ce.
Idan adadinsu ya kai 400 ko sama da haka, to sai zakkar kowace dari daga cikinsu ta zama akuya daya.

Mas'alolin Zakka An shardanta a cikin wajabcin zakkar rakumi da shanu da awaki/tumaki, su kasance masu yin kiwo "Ba wadanda ake ciyarwa ba" a tsawon shekara, kuma ba wadanda ake amfani da su ba a wajen aiki.
Zakka ba ta wajaba a kan abin da ke tsakanin nisabi biyu.
Ana sarrafa dukiyar zakka a wurare 8:-
1. Talaka: Shi ne wanda ba shi da abincin da zai ciyar da kansa da iyalansa tsawon shekara.
2. Miskini: Shi ne wanda ya fi kasancewa cikin mummunan yanayi fiye da talaka.
3. Masu yin aiki a kan lamarin zakka; Ma'ana wadanda Imami (a.s) ko mataimakinsa na musamman ya ayyana don su tara zakka da kiyaye ta.
4. Wadanda ake lallashin zukatansu: su ne kafiran da idan aka ba su wani abu daga zakka zai sanya su yi kwadayin musulunci ko kuma su tausasa zukatansu ga musulmi, saboda haka, sai su iya taimakarsu a wajen yakar sauran kafirai.
5. Sayen bayi da 'yanta su.
6. Ma'abota bashi: wadanda ake bi bashi, shi ne wanda ya kasa biyan bashinsa.
7. Tafarkin Allah: Wannan yana nufin dukkanin maslahohi masu amfani na addini ne, ko na tarayyar musulmi, kamar gina masallaci, ko makaranta, ko koyar da ilimin addini.
8. Dan tafarki shi ne matafiyin da ya wayi gari, a lokacin tafiyarsa; misali, idan abin hawansa ya kasa tafiya ko abincinsa ya kare to yana iya karbar zakka da sharadin kada tafiyarsa ta kasance ta sabo, kuma ba zai yiwu ya isa inda za shi ba ta hanyar rance ko sayar da wani abu ba.
Fakirin da ba shi da abincinsa na shekara tare da iyalansa, idan ya mallaki mahallin zama ko wata dabba kuma ya kasance yana bukatuwa zuwa garesu gwargwadon yanayinsa da sha'aninsa, to ya hallatta, gareshi ya karbi zakka, haka nan lamarin yake a kan abin da ya shafi kayayyakinsa na gida, kamar yadda idan talaka bai da sashin wadannan abubuwan kuma yana bukatuwa zuwa garesu, to ya halatta ya saye su daga kudin zakka.
Abin da ake ba wa talaka da sunan zakka bai zama wajibi a sanar da shi ba cewa zakka ce, gami da haka, idan talaka ya zama daga cikin wadanda suke girmama kansu saboda kunya, an so a ba shi ita da sunan kyauta, amma a zuci da nufin zakka.
Bai halatta ba a sarrafa zakka a cikin ciyarwar wanda ya wajaba a ciyar da shi, kamar 'ya'ya. Sai dai in babu wata dukiya da zai ciyar da su da ita in ba ta zakkar ba. Haka kuma idan ba ya ciyar da su, to ya halatta ga waninsa ya b a su zakka.
An so a ba da zakkar dabbobin ni'ima guda uku ga ma'abota mutunci daga talakawa, kuma ana gabatar da makusanta da ma'abota ilimi, da kamala, a bisa wasunsu, a gabatar da wadanda ba sa bara a kan masu yin bara, haka nan idan wani talaka yana da wani hali mai kyau da za a gabatar da shi a kan waninsa, to an so ba shi zakkar.

Zakkar Fiddakai Zakkar Fiddakai tana wajaba yayin faduwar ranar daren idin karamar salla, a kan wanda yake baligi, mai hankali (kuma hankalinsa bai gushe ba ta hanyar suma ko waninsa), mawadaci, kuma da.
Wajbi ne ya fitar wa kansa da wanda yake daukar nauyinsa. Ta yadda zai ba da kwanon alkama ko sha`ir ko dabino, ko zabibi, ko shinkafa ko makamancinsu. Kwano; kilo uku ne, kuma idan aka bayar da kimar kudin abin fitarwa ya isar.
Bakon da ya sauka da izinin mai gida, kafin faduwar ranar daren idin, idan ya kasance daga cikin wadanda zai ciyar to wajibi ne ya fitar masa da zakkar.
Ana sarrafa zakkar fiddakai a cikin dayan guraren nan guda takwas da suka gabata, a cikin zakkar dukiya.
Bai halatta a bayar da ita ga wanda zai sarafa ta a cikin haram ba.
Wajibi ne ga wanda zai yi sallar idi ya ba da fiddakai kafin sallar, kuma ya halatta ga wanda ba zai sallace ta ba ya jinkirta bayar da fiddakai zuwa karkatar rana.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
Monday, Nobember 30, 2009