Hakkokin Allah

Sakon Hakkoki: Imam Ali Sajjad (a.s) Tarjama da Sharhi: Hafiz Muhammad Sa'id
Hakkokin Allah (s.w.t) Imam Zainul-abidin (a.s) yana cewa: "Amma hakkin Allah mafi girma, shi ne ka bauta masa, ba ka yi tarayya da shi da wani abu, idan ka yi haka da ihlasi, to Allah ya daukar maka alkawari a kansa cewa zai isar maka lamarin duniya da lahira, kuma ya kiyaye maka abin da kake so daga cikinsu".
Imam Sajjad (a.s) ya nuna mana mafi girman hakkin Allah (s.w.t) da cewa shi ne a bauta masa da ikhlasi, wannan kuwa yana nuni ga haramcin yin shirka da wani tare da shi a cikin ibada. Idan mun duba a nan zamu ga kalmar hakki tana nufin wani abu da yake mallakin wani ko wasu. Da kalmar Allah da take nufin sunan mahaliccin bayi. Da kuma bauta da take nufin rusuna wa wani da imani da cewa shi ne ubangiji wanda yake sama da komai.
Kadaita Allah (s.w.t) wani abu ne wanda yake hakki ne nasa , kuma ma'anar kadaita shi tana nufin kore imani da duk wani abu wanda zai kasance tsaransa a kowane abu, kamar a zatinsa da siffarsa, ko a aikinsa da ibadarsa. Sannan yana da hakkin yi masa ibada shi kadai, wannan ibadar ta hada da bin umarninsa, da nisantar haninsa, da Salla, da Zakka , da Azumi, da hajji, da son abin da yake so, da kin abin da yake ki, da tsayawa kan iyakarsa.
Amma ba zai yiwu a bauta wa wanda ake jahilta ba, don haka ne ya kasance wani nauyi na wajibi a kan kowane mai hankali ya san shi. Sai dai saninsa yana da hanyoyinsa da shari'a ta karfafa wacce take ita ce hanyar dogaro da hankali wurin tunani domin sanin mahalicci madaukaki.
Don haka ne ma ba a yarda da bin hanyar ji kawai, ba tare da sanya hankali ba a mahallin imani da Allah, da sanin zatinsa, da siffofinsa. Bai halatta ba a dogara da gado ko fatawa a kan imani da samuwar Allah ko kadaita shi , wajibi ne a akida a yi imani da hakan a zuciya tare da gasgatawa da hakan bisa dalili na hankali, wannan kuwa ba ya dogara bisa fatawar malami.
Da wani malami zai ce da kai: Ka yi sallar Jumma'a da Azahar tare wajibi ne, wato Juma'a ba ta isarwa sai ka hada da Azahar, wannan Malami kuma da shi kake koyi, a nan sai ka yi biyayya gareshi domin fatawa ta hukuncin shari'a furu'a ce da take kama da aikin likita ne a Asibiti da kake koma wa wanda ya fi kwarewa domin magani ko tiyata.
Amma a Akida da wani malami zai ce: Ya gano Allah biyu ne, ko ya gano shi ya halicce halittu, ko ya halatta bauta wa wani gunki!, a nan sai a sanya hankali da Allah ya hore mana cewa ba yadda za a yi karfi biyu su hadu a matsayin ubangiji domin wannan yana nufin rushewa da wargajewa, da rasa halitta baki daya, ko kuturin ita ce ya zama ubangijin da za a bautawa. Domin samuwar karfi maras iyaka guda biyu yana nufin sun samu iyaka ke nan, wato duk inda dayan ya tuke, to a nan ne dayar zai fara, wannan kuwa yana nuna rashin kamalarsu, don haka ke nan a cikinsu babu wanda yake shi ne Ubangiji, don haka sai mu nemi ubangijinmu.
Rashin sanin Allah ya sanya jahiltarsa, jahiltarsa kuwa ta sanya jahiltar kawuka, sai ta sanya rashin sanin kawuka , rashin sanin kawuka kuwa ya kai ga rashin girmama juna. Wannan ne ya sanya marasa sanin Allah ba zaka samu wani daga cikinsu yana girmama ra'ayin dan'uwansa ba har a siyasar duniya, wannan lamarin ya haifar da gaba mai tsananin gaske a yankunanmu. Kuma ya tumbatsa har cikin lamurran addini, sai ga shi an dauki lamarin addini cikin jahilci ana jifan juna da kafirci, ana kafirta juna alhalin babu wani dalili na shari'a da zai hana ma'abota mazhabobi kasancewa tare, da fahimtar juna.
Rashin sanin Allah ya sanya ana iya yi wa mutane fashin tunani wanda ya fi fashin kaya da rayuka muni da hadari, har al'umma ta koma jayayya kan abin da bai kamata ya kai ga sabani ba. An jefa rikici cikin al'ummu game da lamurran siyasar duniya da rikin kungiyanci da jam'iyyanci, saboda jahiltar kawuka.
Har ma cikin Addini kamar sabani a rikicin 'yan kabalu da 'yan sadalu, da rikicin shin Annabi ya san gaibi ko bai sani ba? Sau da yawa da zaka tambayi masu rikicin mene ne ma'anar gaibi da ka samu maganganu masu karo da juna, amma ana iya kashe juna a kan irin wadannan. Nisantar tunani ingantacce mai kyau ya kai ga yin fada a kan Bushanci da Sadamanci, har da kashe juna a lokacin Yakin Gabas Ta Tsakiya Na Biyu. Haka nan a wannan lokaci wasu makiya wannan al'ummar suke tayar da rikice-rikicen da aka dade ana hura masa wuta domin tarwatsa wannan al'ummar kamar rikicin Shi'a da Sunna.
Bambancin fahimta ba matasla ba ne matukar Allah daya, manzo daya, Littafi daya, kasancewar wannan mabiyin Ahlul-baiti (a.s) ne, wancan kuma mabiyin hanafiyya ne, ko shafi'iyya, ko malikiyya, ko kuma wancan Sufi ne ko Arifi, bai kamata ya cutar ko ya jawo rigima da fitina ba. Ba ma tsakanin musulmi ba, har ma tsakaninsu da wasunsu bai kamata ba a samu sabani da rigima!.
Ilimi shi ne kamalar hankali, ita kuwa kamalar hankali tana cikin sanin Allah ne, kuma Allah yana saka wa mutane da ladan aiki gwargwadon saninsu da shi ne. Idan mun duba zamu ga misalin Annabi Nuhu (a.s) duk da ya dade yana shan wahala, an ce tun yana shekara arba'in yake kira ga Allah (s.w.t) kuma ya rayu kusan shekara 2500 amma bai kai darajar Annabi Muhammad ba, domin ya fi shi sanin Allah (s.w.t), shi kuwa Allah yana sakawa gwargwadon saninsa ne ga masu aiki na gari a cikin bayinsa. Da wannan ne zamu ga cewa bauta ke nan tana bukatar sani kafin ta kasance karbabbiya cikakkiya, a kan haka ne zamu ga misali a wannan kissa mai kayatarwa.
Wata rana wani Mala'ika ya yi mamakin karancin ladan wani mutum mai yawan bauta ga Allah, sai yake cewa da Ubangiji: Ya Ubangiji yaya wannan bawa yana bauta mai yawa amma ladansa kadan ne? Sai Allah ya ce da shi: Ina sakawa gwargawdon sanina ne amma tafi wajansa ka gani, sai Mala'ika ya tafi wajansa, da safiya ta yi suna maganar ciyawa da take fitowa lokacin damuna ta mutu lokacin rani sai mai bauta ya ce da Mala'ika: Ai da Ubangijinka yana da jaki da ciyawan nan ba ta lalace a banza ba, da yana da jaki da mun kiwata shi. Haka nan Mala'ika ya ga karancin hankalin wanann bawan shi ya jawo masa karancin lada: don haka ne wanda ya fi sanin Allah ibadarsa daya ta fi ta jahili sau saba'in.
Ga kissar kamar yadda take a ruwaya: Wata rana wani Mala'ika yana yawo sai ya wuce wani tsibiri da wani mai bauta yake rayuwa a ciki sai ya tambayi Allah ya nuna masa ladan wannan mai bauta, sai Allah ya nuna masa, sai Mala'ika ya karanta ladansa, sai Allah ya ce da shi: Ka zama tare da shi, sai Mala'ika ya zo masa a surar mutum, sai ya tambayi Mala'ika: Wane ne kai? Sai Mala'ika ya ce: Ni wani mai bautar Allah ne na ji labarinka ne da ibadarka sai na zo don in kasance tare da kai, sai ya zauna da mai bauta wuni daya, da safiya sai Mala'ika ya ce: Wannan wuri yana da shuke-shuke bai dace da komai ba sai ibada. Sai mai bauta ya ce: Ai wurin yana da aibi. Mala'ika ya ce: Mene ne aibin? Sai ya ce: Ubangijinmu ba shi da dabbobi, da Ubangijinmu yana da jaki da mun kiwata shi a nan, ga ciyawa nan tana lalacewa a banza. Sai Mala'ika ya ce: Shin Ubangijinka ba shi da jaki ne? Sai ya ce: Ai da yana da jaki da wannan ciyawa ba ta lalace ba! Sai Allah ya yi wa Mala'ika wahayi da cewa ni ina saka masa daidai gwargwadon hankalinsa ne .
A bisa dabi'ar dan Adam da ya gada daga nau'in halittarsa, kuma ta samu karfafuwa a tafarkin annabawa (a.s) ilimi shi ne yake bayar da kima da daukaka, kuma saba wa dabi'ar haka tana nufin rushewar dan Adam. Wannan al'amari na saba wa dabi'ar dan Adam shi ne ya sanya rushewar tsarin gurguzu, shi tsari ne da ya shahara da yakar dabi'ar dan Adam musamman a abin da ya shafi mallaka.
A tunanin Gurguzu aiki shi ne yake bayar da kima ko mallaka, saboda haka a misali mai kaya idan ya kai zinarensa wajan makeri don ya yi masa dan kunne da shi, idan ya kera ba zai ba shi dankunne ba sai ya ba shi kudin zinarinsa, domin aikin kira da ya yi shi ne yake bayar da kima da mallaka, wannan kuwa al'amari ne da ya saba wa dabi'ar dan Adam, a sakamakon haka ne ba su je ko'ina ba suka rushe.
Yanzu ta kai ga cewa hatta Akidun da suka dasa na rashin samuwar mahallicci sun rushe, har a ranar 1 ga Disamba 2002 Gidan Rediyo/Telebijin na IRNA ya shelanta cewa: A yanzu kashi sittin cikin dari na mutanen Rasha sun yarda akwai Allah, al'amarin da su Lenin suke ganin haka a matsayin rashin hankali ne sakamakon maye na banju da Duniyar dan Adam ta sha ta fada cikin dimuwa.
Kwatanta aikin Lebura da Purincipal, haka nan kwatanta aikin Manajan banki da na Masinja, da na Saje da Janar, me ya sa albashin aikin na sama na rana daya ya fi albashin aikin dayan da tazara mai yawa, wannan ba domin komai ba ne sai bambancin sani da tunani da na sama yake amfani da shi fiye da na kasa.
Sanin Allah madaukaki ya dogara da samar da yanyi mai inganci da zai bayar da damar hakan ta yadda masu koyarwa da ilmantarwa zasu kasance annabawa ko wasiyyansu, sai dai ba a bari annabawa (a.s) sun kafa Daular Allah ba, hatta lokacin Manzo (s.a.w) ya sha matsala da munafukai, amma duk da haka annabawa (a.s) sun kafa ci gaban da ba kamarsa a Duniya.
A dukkan hukumomin musulmi hatta da wadanda suke aiwatar da shari'ar musulunci a hukumance har yanzu babu wanda ya kai kashi hamsin cikin dari sakamakon yanayi. Ya zo a ruwayoyi cewa; Imam Mahadi (a.s) ne kawai zai samu ikon kafa hukumar Allah mai aiki da cikakkiyar shari'a , shi kuwa zai samu wannan ne saboda Allah zai ba shi damar hukunci da hakikanin yadda abu yake ne ba da zahiri kawai ba .
Imam Ja'afar Sadik (a.s) yana cewa: Idan imam Mahadi (a.s) ya shugabanci mutane zai yi hukunci tsakanin mutane da hukuncin Dawud (a.s), ba ya bukatar sheda ko rantsuwa, a kowane hukunci Allah yana yi masa ilhamar hakikanin abin da ya wakana, kuma da dogaro da wannan ilimin nasa ne zai yi hukunci .
Sai ga wasu wadanda suke kiran kansu musulmi ba sa son a san Allah, suna kokarin hana sanin Allah ta kowane hali, da kokarin toshe duk wani kokarin fahimtar addininsa da hakkokinsa a kanmu. Sai ga Addini ana wasa da shi kowa ya fiye bangaranci da mazhabanci sai ga rarraba, sai ga jifan juna da kafirci.
Da mutane sun san Allah hakikanin sani kuma suka bi umarninsa, da sun ci arzikinsa mai yalwa, da duniya ta yalwata gunsu. Rashin saninsa ya sabbaba rashin sanin yadda za a bauta masa da gode masa, domin su malam tsutsa sun shiga cikin goro sun hana shi sakat, wannan ya sanya aka kasa aiwatar da abin da Allah ya zo da shi ta hannun Annabawansa. Don haka ne ya bar wasiyyan Annabi su ci gaba da shiryar da mutane bayansa (a.s), amma duka an kashe su ne daya bayan daya .
Ba kawai sanin Allah (s.w.t) mahalicci ba har ma furu'a kamar siyasa, da hukunce-hukunce, da zamantakewar dan Adam, da dokoki, da tsarin musulunci, duk an jahilci da yawansu a kasashen musulmi. Amma matsalar yammacin Duniya ta bambanta da ta sauran kasashen musulmi ta wani banbare, domin su wannan hasken da yake hannunmu da ba a aiki da shi su ba su da shi.
Kamar yadda Turai suka yi mummunar fahimta da jahiltar musulunci, haka su kansu musulmi suka yi masa mummunar fahimta suka jahilce shi. Da zaka ambaci kalmar shari'a a cikin musulmi sai mutane su yi tunanin fille kai, da jefewa, da gutsure hannaye da kafafu. Da zaka tambayi wanda ba musulmi ba a sabanin da makiyan kasarmu na ciki ko na waje suka haifar kan batun shari'a a Arewa me yake nufi da ba shari'a? Zai ce: Ba gutsure hannu, ba fille kai. Haka nan amsar da musulmi zai iya ba ka ke nan idan yana maganar shari'a.
Wannan yana nuna wajabcin tashi don kawar da jahilci da miyagun hannayensa masu guba da suke tafiyar da tunanin mutane game da musulunci har aka kai ga fadawa cikin irin wannan dimuwa. Musulunci yana da fadi ba babi daya ba ne, ya kamata a nemi saninsa daga masanansa na ainihi.
Babbar matsala a cikin al'ummarmu ita ce kauracewa Ilimin sanin Allah da shagaltuwa da furu'a kawai, wannan kuwa ya tauye tunanin mutane game da saninsa (s.w.t). Ash'arawa sukan takaita a kan Littafin Kawa'idi ne da mafi yawan mutane ba sa ma fahimtarsa, wanda ya yi zurfi shi ne wanda ya kai ga Sharhi Ummul Barahin, da kyar zaka sami wanda ya wuce hakan sai daidaiku. Ba a ma san Al'makalat da Al'ibana na Al'ash'ari shi kansa mai mazhabar Ash'ariyya ba, yawanci ba a san wanda ake bi a mazhaba ko Akida ba.
Haka sanin Allah ya yi nesa da mutane suka yi nisa da shi, haka ma al'amarin tarihin musulunci da ba a karanta shi wai akwai rigima a ciki da ba a so a sani, wai idan aka yi fada da uwa da uba shin ka so ka sani? Sai dai wannan tunanin kuskure ne babba, domin rikicin iyaye bai shafi makomar Lahira ba, kuma a ciki babu batun sanin waye Manzo (s.a.w) ya bari tsakaninsu wanda bin sa ya zama hujja a kanka. Amma na tarihin musulunci ya shafe ka, domin zai gaya maka makomarka ne, da abin da Manzo (s.a.w) ya bar maka a matsayin tsiranka a duniya da lahira. Kuma ana bukatar ma'aunin waye maganarsa ta fi zama hujja don ka yi aiki da ita, wannan duk ya shafi makomarka ne.
Haka aka haramta wa al'ummarmu sanin Akidu da ilimomi har ka san mene ne gasakiya ka bi, mene ne ba daidai ba ka bari, sai aka dogara da koyi a cikin jiga-jigan addini. Koda yake wasu malamai sun tafi a kan cewa wanda ya fadaka, ya yarda har a zuciyarsa, ya yi imani da samuwar Allah da kadaita shi a bisa sahihiyar Akidar musulunci, duk da tun yana yaro ya yi koyi da malamai ne ko iyaye, to irin wannan imanin yana isarwa gare shi.
Sannan sanin tsarin Allah wani abu ne da ya hau kan dukkan musulmi, tsarin musulunci ya doru kan sanin Allah mai tsari da mulki mai sanya dokoki da ba wa kowane mutum hakkinsa da ya hada mace, namiji, mai kudi, talaka, mai mulki, da wanda ake mulka, da yaro, da babba. Ba zalunci, ba zalunta, ba take hakkin juna, babu yakar dabi'ar halittar dan Adam, ba bambanci ko fifiko sai da takawa. Musulunci tsari ne cikakke bai zo da tsari irin na demokradiyya ba, ya zo ne da AsalatusShura. Wato yin shawara tsakanin musulmi kan wani al'amari, a sani yin shawara a nan da sharadin bai fita daga asasin dokokin Musulunci ba.
Cibiyar Al'adun Musulunci
www.hikima.org
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Tuesday, May 18, 2010