Tattaunawar Addinai

Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Kur’ani Mai Daraja:

"Allah Ya shaida cewa: Lalle ne babu abin bautawa face Shi, kuma Mala'iku da ma'abuta ilmi sun shaida, Yana tsaye da adalci, babu abin bautawa face Shi, Mabuwayi, Mai Hikima". (Surar Aali Imrana, 3: 18) .

Gabatarwar Mawallafi

A wannan littafi mai suna "Tattaunawar Addinai" muna so mu yi nuni da wasu Akidu na wasu Addinai da kuma koyar da hanyar tattaunawa mafi kyau daga koyarwar Malamin Malaman Duniya kuma Mafi Ilimin dukkan bayi da Allah ya halitta, kai shi ne ma aka yi kowa dominsa wato Manzo Muhammad Dan Abdullahi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi da alayensa Wannan Hadisi ruwaya ce daga Sadiku Ahlul Bait (A.S) game da tattaunawar Manzo da Ma'abota wadannan Addinai wanda a cikinsa akwai hanya mai kyau ta tattaunawa da ma'abocin wata Akida da ta saba da ta mai muhawara da shi, wanda a cikinta zamu koyi tattaunawa da musayen ra'ayi ta hanya mafi kyau kamar yadda aka yi umarni a Kur'ani mai girma.
Yana kuma koyar da hanyoyin kafa dalili na kai tsaye, da kuma Wanda ba na kai tsaye ba, da kuma hanyar bayar da jawabi da warwara mai gamsarwa, da kuma hanyar bayar da amsa da kama mutum da abin da ya yarda kuma ya yi imani da shi. A lokaci guda kuma yana iya nuna mana hakikanin manufar wadannan Addinai da yadda ma'abotansu suke fassara Akidojin addinansu. Kuma tana nuna mana yadda aka canja koyarwar Addinan da suka gabata, al'amarin da wannan al'umma ba ta tsira daga irinsa ba ta hanyar riko da Raunanan maganganu ko kuma Tafsirin da ya kafu bisa mahanga ta kuskure da yakan kai ga kurakurai wajan fahimtar Addinin Allah.
Da yake mutane a kowane zamani hali daya ne da su, al'ummar karshe ta Manzon Allah (S.A.W) ita ma ba ta fita daga irin wannan ba, shi ya sa aka samu sabani da ya kai su zuwa ga rarraba da Mazhabobi da Kungiyoyi na Akida daban-daban. Amma wani abin da za a gode wa Allah shi ne; al'ummar nan ta bambanta da sauran al'ummu domin su wadancan al'ummu bayan sun yi nesa da Wasiyyan Annabawan sukan kuma yi rashin sa'ar canza Addinin nasu gaba daya a kuma kautar da Akidunsu daga sahihancinta kamar Yahudawa da Kiristoci da Zartush da Sa'ibawa da sauransu. Amma wannan al'umma Allah ya yi alkawarin kare littafinta, shi ya sa ma duk wanda yake ganin wani yana da Kur'ani daban da wanda yake hannun musulmi to yana ganin Allah Ajizi ne daga alkawarin da ya dauka na kare littafinsa, kuma irin wadannan mutane suna a matsayin wadanda suka kafirce wa Allah ta hanyar kafircewa ayar Kur'ani mai girma.
Wannan littafin wata tattaunawa ce da annabi (S.A.W) ya yi da wasu addinai guda biya kamar yadda zamu gani, mun sani cewa; annabin rahama (S.A.W) shi ne shugaban masu hikimar halittar ubangiji gaba daya, sannan kuma shi ne annabin karshe da Allah madaukaki ya aiko domin shiryar da dan adam.
A wannan tattaunawa muna iya ganin yadda manzon rahama ya yi amfani da hankali a matsayin asasin tattaunawa domin tabbatar da gaskiyar samuwa ko kuma kore karyar da aka jingina wa samuwar ubangiji.
Duk sadda aka samu jingina wa samuwar ubangiji madaukaki wani abu da bai cancance shi ba, ko kuma aka kore masa wani abu da ya cancance shi a siffofinsa na zatinsa ne ko kuma na aikinsa, ko kuma na abin da ya labarta wadanda hankali a kowane yare yana da irin wadannan kalmoki na aro da kinaya da sauransu, to a nan sai a samu kaucewa gabarin gaskiya, sai a samu abin da ya kai ga kafirce wa Allah ko kuma shirka da shi, wannan kuwa wani abu ne da Allah ya tabbatar da ba zai yafe shi ba.
Ginin addini sahihi shi ne zai iya bayar da tsari sahihi wanda ya bubbugo daga mashaya ta gari, mai iya isar da dan adam kamalar da Allah ya tsaga masa ya ba shi, kuma muna iya gani a wannan tattaunawar manzon rahama da ma'abota addinai a fili. A al'amarin akida tunda ya kafu kan hankali ne wanda Allah madaukaki ya yi umarni da binsa da bincike cikinsa domin kai wa ga sa'adar duniya da lahira wani abu ne wanda yake nuna mana a fili cewa; duk wanda aka kayar, hujjarsa ta kasance mai rauni to dole ne ya sallama wa daya bangaren. Domin yana kama da gida ne da ya rushe, babu wani abu da ya rage wa mai zama cikinsa sai ya sake wuri. To tunda akwai gini mai karfi da rushewar ta kasance sakamakon haduwa da shi ne; wannan yana nuna mana a fili kenan cewa babu abin da ya rage wa mai irin waccan rusasshiyar akidar sai ya koma zuwa ga wannan gini mai kyawun gaske kuma mai karfi. Wannan kuwa shi ne abin da ya faru ga wadannan al'ummu ma'abota addinai a cikin tattaunawarsu da manzon rahama, amma fa muna iya ganin yadda suka samu dacewa da komawa wannan gini mai karfi mai kayatarwa na musulunci da yake cike da sakon Allah madaukaki da ya aiko da shi ta hannun manzonsa mai tsira da aminci bayan sun kawar da son ransu gefe guda, suka mika wuya ga al'amarin ubangijinsu madaukaki.
Wannan bayanin wata ruwaya ce da annabi mai daraja ya tattauna da ma'abota addinai kuma zamu kawo maka ita kamar yadda aka karbo ta daga jikan annabi (S.A.W) wanda yake da shigen irin wadannan daruruwa da dubunnai munazarori da tattaunawa wato; imam sadik (A.S), daga littafin ihtijaj na dabrasi :
Da yake kare littafin ya zo daidai da Ranar Shahadar Waliyyul Auliya Amirul Muminin Ali Dan Abi Dalib (A.S) wato ranan Lailatul Kadari ta biyu Lahadi 21 Ramadan 1424 H.K. Da ya zo daidai da 16 Nuwamba 2003 M. daidai da 25 Aban 1382 H.Sh. Saboda haka ne muke neman Allah madaukaki da ya bayar da ladan rubutun ga Amirul muminin (A.S) kuma ya yafe mana kurakuran ciki da tuntuben alkalami, ya sanya shi mai amfani ga al'umma kuma dalili na bincike da kara kaimi wajan neman sani.

Imam Sadik (A.S) ya ce: "Daga Babana Albakir (A.S) daga Kakana Ali Dan Al-Husain (A.S) daga Babansa Husain Shugaban Shahidai (A.S) daga Babansa Ali Dan Abi Dalib (A.S) cewa, wata rana ma'abota Addinai biyar suka hadu a wajan Manzon Allah (S.A.W); Yahudawa da Kiristoci da Dahariyya da Sanawiyya da Mushrikan larabawa.
Sai Yahudawa suka ce: Ya Muhammad! Mu muna cewa: Uzairu (A.S) dan Allah ne, mun zo mu ga me kake cewa, idan ka bi mu to mun riga ka shiryuwa zuwa ga gaskiya, amma idan ka saba mana zamu yi jayayya da kai. Kiristoci suka ce: Mu muna cewa Isa (A.S) dan Allah ne da ya shiga cikinsa ya hade da shi idan ka bi mu mun riga ka zuwa ga gaskiya amma idan ka saba to ma ja da kai . Dahariyya suka ce: Ya Muhammad! mu muna cewa: Halittu ba su da farko ba su da karshe suna nan har abada, kuma mun zo mu ga me kake cewa, idan ka bi mu mun riga ka fahimtar gaskiya idan kuma ka saba mana to ma ja da kai. Sanawiyya suka ce: Ya Muhammad! mu muna cewa haske da duhu su ne masu juya dukkan al'amura, mun zo mu ga me kake cewa, idan ka bi mu to mun riga ka fahimtar gaskiya amma idan ka saba mana ma ja da kai. Mushrikan larabawa suka ce: Ya Muhammad! Mu muna cewa: Gumaka Ubangizai ne, mun zo mu ga me kake cewa, idan ka bi mu mu mun fika mun riga ka zuwa ga gaskiya da shiriya amma idan ka saba mana to ma ja da kai.
Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Na yi imani da Allah daya ba shi da abokin tarayya, na kuma kafirce wa duk wani abin bauta ba shi ba. Sannan ya ce: Allah (S.W.T) ya aiko ni zuwa ga mutane gaba daya Mai albishir da gargadi ga mutane, sannan zai mayar da kaidin duk mai kaidi kansa.

Yahudawa

Sannan ya ce da Yahudawa: Shin kun taru ne nan domin in karbi maganarku babu wata hujja sai suka ce: A'a,. Ya ce: Me ya kai ku ga cewa Uzairu (A.S) dan Allah ne? Sai suka ce: Domin ya raya wa Bani Isra'ila Attaura kuma ba wanda Allah zai yi masa haka sai dansa. Sai Manzon Allah ya ce: Domin me Uzairu (A.S) zai zama dan Allah ga Musa (A.S) alhalin shi ne ya zo wa Bani Isra'ila da Attaura kuma aka ga mu'ujizozi daga gare shi kamar yadda kuka sani. Idan kuwa Uzairu (A.S) zai zama dan Allah saboda karamar raya Attaura, me ya sa kuka kira shi dan Allah ba Musa ba? Sai suka ce: Saboda ya raya wa Bani Isra'ila Attaura bayan ta bace, kuma ba yadda zai ba wani damar haka sai wanda yake dansa. Sai Manzo (S.A.W) ya ce: Ya ya Uzairu (A.S) ya zama dan Allah ba Musa (A.S) ba wanda shi ne ya zo da Attaura din aka ga mu'ujizozi a hannunsa kamar yadda kuka sani? Idan kuwa Uzairu (A.S) zai samu wannan matsayi saboda ya raya Attaura to Musa (A.S) shi ne ya fi cancanta da ya zama dan ba shi ba, domin shi ne ya zo da Attaurar tun farko.
Idan kuma shi Uzairu (A.S) ya cancanci girmama wa a matsayin da saboda ya raya Attaura to Musa ya cancanci matsayin da ya fi na da, domin ku idan kuna nufi da da ma'anar da kuke gani a Duniya na 'ya'ya da iyaye suke haifarsu ta hanyar takinsu (kwanciya) daga iyaye maza ga su matan to kun kafircewa Allah kun kwatanta shi da bayinsa kuma kun wajabta masa abin da yake da siffa na fararru, saboda haka ya wajaba ke nan ya zama Fararre abin halitta a wajanku ya zama yana da mahalicci da ya fare shi.
Sai suka ce: Ba haka muke nufi ba, hakika wannan kafirci ne kamar yadda ka fada sai dai mu muna nufin girmamawa kamar yadda wasu malamai sukan kira wanda suke son girmamawa da wani matsayi da "Ya dana!" ko kuma ya ce: "Wannan dana ne" ba domin ya haife shi ba, domin saudayawa yakan gaya wa wanda ba su da wata nasaba da shi hakan. Haka nan yayin da Allah ya yi wa Uzairu (A.S) wannan ni'ima sai muka fahimci cewa bai yi masa haka ba sai don ya rike shi dansa ta hanyar girmamawa ba domin ya haife shi ba. Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Wannan shi ne abin da nake gaya muku cewa, idan da wannan Uzairu (A.S) ya zama dansa to wannan matsayi ya fi cancanta ga Musa (A.S) kuma Allah zai kunyata duk mai karya da furucinsa da kansa kuma aniyarsa zata dawo kansa. Ku sani cewa abin da kuka kafa dalili da shi zai lizimta muku fiye da abin da ya wuce haka, domin ku (a misali) kuna cewa: Wani mai girma daga cikinku yakan gaya wa waninsa da ba su da nasaba: "Ya dana!" ba don ya haife shi ba, sai don girmamawa, kuma zaku iya samun wannan mai girma din yana gaya wa wani cewa: "Dan'uwana ne" ya kira wani kuma da "Wannan shehina ne" ko "Babana ne" ko "Shugabana ne" ko "Ya shugabana!" ta hanyar girmamawa, wato duk sa'adda aka samu wanda ya fi girma to sai ya dada masa kalma ta girmamawa fiye da dayan, idan kuwa haka ne a bisa abin da kuke cewa ya halatta Musa (A.S) ya zama Dan'uwan Allah ko Shehinsa ko Babansa ko Shugabansa, domin ya fi Uzairu (A.S) daraja, kamar yadda idan wani ya fi da daraja sai a ba shi girmamawa fiye da shi, sai ya ce masa: "Ya Shugabana! Ko Ya Shehina! Da Ya Ammina! Da Ya Shugabana! ta hanyar girmamawa domin karin girma, shin ya halatta a ganinku Musa (A.S) ya zama Dan'uwan Allah ko Shehinsa ko Amminsa ko Shugabansa ta hanyar girmamawa domin girmansa ya fi na Uzairu (A.S) kamar yadda ake dada girma ga wanda ya fi da a fadarku a ce da shi: "Ya Shugabana! Ya Shehina! Ya Ammina! Ya Sarkina".
Imam Sadik (A.S) Ya ce: Sai mutanen suka dimauce suka ce "Ya Muhammad! Ka saurara mana mu yi tunani tukuna game da abin da ka ce. Sai Manzo (S.A.W) ya ce: Ku yi duba da zukata masu kudurce yin adalci, Allah ya shiryar da ku.


Kiristoci

Sa'annan sai ya fuskanci Kiristoci ya ce da su: Ku kuna cewa Dadadde Madaukaki (S.W.T) ya hade da Masihi Dansa (A.S). Me kuka nufi da wannan magana?. Shin kuna nufin Dadadde ya zama Fararre saboda wannan Fararren da ya hade da shi wanda shi ne Isa (A.S) ko kuna nufin Fararren da yake shi ne Isa (A.S) ya koma Maras farko kamar samuwar Dadadde wanda yake shi ne Allah?. Ko kuma ma'anar ya hade da shi ya shiga jikinsa a wajanku yana nufin ya kebance shi da karama da girmamawa ne wacce bai girmama waninsa da irinta ba?. Idan kuka ce: Dadadde ya koma Fararre to kun rushe, domin Dadadde bai yiwuwa ya juya ya koma Fararre. Idan kuma kuna nufin Fararre ya koma Dadadde to kun yi warwarar magana domin mustahili ne Fararre ya koma Dadadde. Idan kuma kuna nufin ya hade da shi domin ya kebance shi ya zabe shi a kan sauran bayi to kun yi furuci da cewa Isa (A.S) Fararre ne da ma'anar ya hade shi saboda haka, domin idan Isa (A.S) ya kasance Fararre Allah (S.W.T) ya kasance ya hade da shi da ma'anar ya sanya shi Mafificin halitta a wajansa to Isa (A.S) ya zama daya daga cikin fararru da wannan ma'ana, wannan kuwa sabanin abin da ku kuke bayyanawa ne.
Sai Kiristocin suka ce: Ya Muhammad! Yayin da Allah ya bayyanar da abubuwan mamaki a hannun Isa (A.S) to ya rike shi da ne ta hanyar girmamawa. Sai Manzo (S.A.W) ya ce: Ai kun ji abin da na gaya wa Yahudawa a irin wannan ma'ana da kuka ambata, sannan ya maimaita abin da ya fada wa Yahudawa dalla -dalla, sai suka yi shiru banda mutum daya a cikinsu da ya ce da shi: Ya Muhammad! Shin ba kuna cewa Ibrahim (A.S) Khalilul-Lahi ba? Sai Manzo (S.A.W) ya ce: Mu Muna cewa hakan. Sai ya ce: Idan kuna cewa haka domin me zaku hana mu fadar waccan maganar? Sai Manzo (S.A.W) ya ce: Maganganun ba su yi kama da juna ba, domin ma'anar Khalilul-Lahi an ciro shi daga Khulla wato Bukata da Talauci domin shi ya kasance Mabukaci zuwa ga Ubangijinsa ne, Mai yankewa zuwa gare shi, Mai kamewa ga barin waninsa, wannan a lokacin da aka jefa shi wuta da manjanik (majaujawa) ne sai Allah ya aika Jibra'il (A.S) da ka je ka riski bawana, sai ya zo ya riske shi a cikin iska, Ya ce da shi: Ka umarce ni da duk abin da kake so hakika Allah ya aiko ni da in taimake ka, Sai Ibrahim (A.S) ya ce da shi: "Hasbiyal-Lahu Wa ni'imal Wakil", Ni ba na tambayar wani wata bukata sai Shi, ba na bukata sai gare Shi". Saboda haka sai ya kira shi da Khalilinsa wato Mabukaci Mai yankewa daga komai sai zuwa gare shi, idan ya zama ma'anar Khulla wato ya tsaya a kan wasu sirri da babu wanda ya same su, ma'anar Khulla zata zama masani da sirrinsa, a nan babu wani kamanta shi da halittarsa.
Shin ba kwa gani ne cewa idan bai yanke zuwa gare shi ba bai zama Khalilinsa ba haka ma idan bai san sirrinsa ba bai zama Khalilinsa ba? Amma wanda mutum ya haifa ko da kuwa ya wulakanta shi ya nesantar da shi daga gare shi ba ya fita daga kasancewa dansa ne, domin ma'anar haihuwa ta tsayu da wannan. Sa'anan idan ya wajaba domin ya ce da Ibrahim (A.S) Khalili ku kiyasta ku ce da Isa (A.S) dansa ya wajaba kenan ku ce da Musa (A.S) dansa domin mu'ujizar da take tare da shi ba ta gaza ta Isa (A.S) ba. Sai ku ce Musa (A.S) shi ma dansa ne, kuma ya halatta inda haka ne ku ce da shi: Shaihin Allah ko Shugabansa ko Amminsa ko Amirinsa kamar yadda na riga na gaya wa Yahudawa hakan.
Sai wadansunsu suka ce: Ai a cikin Littafi saukakke hakika Isa (A.S) ya ce: "Ni zan tafi zuwa ga Babana kuma Babanku". Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Idan kun kasance kuna amfani da Littafin ne, to a cikinsa an ce: "Ni mai tafiya ne zuwa ga Babana kuma Babanku", Idan haka ne ku ce da wadanda Isa (A.S) ya yi magana da su gaba daya 'Ya'yan Allah ne kamar yadda Isa (A.S) yake dansa ta fuskar da Isa (A.S) yake dansa.
Sa'annan abin da yake cikin wannan littafin yana karyata abin da kuke rayawa cewa Isa (A.S) ya zama dansa ta fuskacin kebanta, domin kuna cewa shi dansa ne ta fuskacin kebantarsa da ya yi da abin da bai kebanci wani da shi ba, sannan kun sani cewa abin da ya kebanci Isa (A.S) da shi bai kebanci wadannan mutane da Isa (A.S) ya ce da su "Ni mai tafiya ne zuwa ga Babana kuma Babanku" da shi ba, sai wannan ya nuna cewa bai kebanta da Isa (A.S) ba domin ya tabbata a wajanku cewa Isa (A.S) ya gayawa wanda bai da wannan matsayi irin nasa, sai kuka hakaito maganar Isa (A.S) kuka yi tawilinsa ba bisa ma'anarsa ba, domin shi da ya ce: "Ni mai tafiya ne zuwa ga Babana kuma Babanku" abin da yake nufi ba shi ne abin da kuka tafi a kai ba. Me ya sanar da ku ko yana nufin ni mai tafiya ne zuwa ga Babana Adam (A.S) ko zuwa ga Nuhu (A.S) kuma Allah zai daukaka ni zuwa gare su ya hada ni tare da su, tare da Adam Babana kuma Babanku, kai ba abin da yake nufi sai wannan. Imam Sadik (A.S) ya ce: Sai Kiristoci suka yi shiru suka ce: Ba mu taba ganin mai wuyar kayarwa mai hujjoji masu karfi irinka ba, zamu tafi mu duba al'amuranmu.


Dahriyya

Sa'annan sai ya fuskanci 'yan Dahriyya ya ce da su: Me ya sa kuke cewa abubuwa ba su da farko ba su da karshe?. Kuma ba su gushe ba kuma ba sa gushewa?. Sai suka ce: Domin mu ba ma hukunci sai da abin da muka gani, kuma ba mu samu farko ga abubuwa ba sai muka yi hukunci da cewa ba su gushe ba tun farko samammu ne, ba mu gan su suna karewa ba sai muka yi musu hukunci da cewa su madawwama ne. Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Shin kun same ta Maras farko ko kun same ta Mai wanzuwa har abada ba za ta gushe ba?. Idan kuka ce: Kun same ta hakan, to kun tabbatar wa kawukanku cewa ba ku gushe ba a kamanninku da hankulanku ba ku da farko kamar yadda ba zaku gushe ba a halinku kamar yadda kuke, kuma idan kuka ce haka, to kun yi musun hakikanin zahiri kuma masana wadanda suke ganinku zasu karyata ku.
Sai suka ce: A'a, mu ba mu ga farko gare ta ba kuma ba mu ga karshe gareta ba. Sai Manzo (S.A.W) ya ce: Saboda me kuke hukunci da rashin farkonta da rashin karshenta har abada ga ku ba ku ga farkonta ba, kuma karewarta shi ya fi cancanta ya wakana fiye daga bayanin da irinku yake yi game da ita, sai a yi mata hukunci da faruwa da karewa da yankewa domin ba ku ga dadewa ko wanzuwa gareta ba har abada.
Ba kuna ganin dare da rana ba?. Suka ce: Na'am. Sai ya ce: Shin kuna ganinsu ba su gushe ba kuma ba zasu gushe ba? Suka ce: Na'am. Sai ya ce: Shin yanzu ya halatta ku yi hukunci da haduwar dare da rana waje daya? Suka ce: A'a, Sai Manzo (S.A.W) ya ce: Ashe kenan kowannensu rabe yake da dayan sai daya ya riga daya ya zama duk inda daya ya yanke dayan yana gudana bayansa. Suka ce: Haka yake. Sai ya ce: Kun yi hukunci a nan da faruwar abin da ya gabata na daga dare da rana alhalin kuma ba ku gan su ba, saboda haka kada ku musa wa Allah ikonsa.
Sa'annan sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Shin kuna cewa duk abin da ya gabata na daga dare da rana yana da karshe ko ba shi da karshe? Idan kun ce: Yana da karshe, to kun sami karshen da ba shi da farkonsa, idan kuma kuka ce: Yana da karshe to an sami lokacin da babu wani abu da ya kasance daga cikinsu. Sai suka ce: Na'am.
Sai ya ce da su: Shin kun ce Duniya Dadaddiya ce ba Fararriya ba kuna sane da ma'anar da kuke nufi da furucin da kuka yi da kuma abin da kuke musawa? Suka ce: E. Sai Manzo (S.A.W) ya ce: Wannan halittu da kuke gani sashensu suna bukatuwa zuwa ga sashe, domin kowanne ya dogara ne ga samuwa da daya sashen nasa kamar yadda zaku ga gini sashe yana bukatar sashe, in ba haka ba, da bai yi karfi ba bai hadu ba haka ma sauran abubuwan da muke gani.
Ya ce da su kuma: Idan wannan bangaren da sashensa yake bukatar sashe domin ya yi karfi ya cika shi ma Dadadde ne to ku bani labari da ya kasance Fararre da yaya ya kamata ya kasance? kuma yaya siffarsa ya kamata ta kasance?.
Imam Sadik ya ce: Sai suka dimauce suka san cewa ba yadda za a yi a samu Fararre da sifa da suke siffanta shi da ita sai sun same ta ga wannan abin da suka raya cewa Kadimi (Dadadde) ne. Saboda haka sai suka tage suka ce: Zamu duba al'amarinmu tukuna.


Sanawiyya

Sa'annan sai Manzo (S.A.W) ya fuskanci Sanawiyya da suka ce: Haske da Duhu su ne masu tafiyar da al'amuran rayuwar halittu, ya ce: Menene ya kai ku ga fadin haka? Sai suka ce: Saboda mun samu Duniya kala biyu akwai Sharri da Alheri, kuma muka sami Alheri yana kishiyantar Sharri, saboda haka sai muka yi musun ya zama mai aikata wadannan abubuwa ya zama daya da yake aikata abu sannan ya zo da kishiyarsa, don haka dole ne ya zama kowanne yana da mai aikata shi, shin ba ka ganin cewa mustahili ne kankara ta kona ruwa kamar yadda ba yadda zai yiwu wuta ta sanyaya ruwa? Don haka ne muka tabbatar da cewa akwai Dadaddu biyu Masu kagowa ga Duhu da Haske.
Sai Manzo (S.A.W) ya ce: Shin ba kwa ganin Baki da Fari da Ja da Yalo da Kore da Bulu, kowanne yana kishiyantar juna, domin mustahili ne guda biyu daga cikinsu su hadu waje daya kamar yadda zafi da sanyi kishiyoyi biyu ne da mustahili ne su hadu waje daya? Suka ce: Na'am. Ya ce: Don me ba ku tabbatar da Kadimai da adadin launinsu ba, ku sanya wa kowanne daga cikin kishiyoyin nan Kadimi mai yin sa da ya zama ba mai yin dayan ba?. Sai suka yi shiru. Sannan ya ce: Yaya a ka yi Haske da Duhu su ka cakuda, alhalin wannan sha'aninsa shi ne ya yi sama wancan kuma ya yi kasa!? Shin kuna ganin da wani mutum ya yi Gabas yana mai tafiya wani kuma ya yi Yamma yana mai tafiya a ganinku zai yiwu su hadu? Suka ce: A'a,. Sai ya ce: Ashe kenan dole ne kada su Hasken da Duhun su hadu, domin kowanne ya fuskanci fuskar da dayan bai fuskanta ba! Yaya aka yi kuka samu faruwar haduwar wannan Duniya daga abubuwan da suke bai yiwuwa su hadu? Hakika su dai ababan juyawa ne ababan halitta. Sai suka ce: Zamu duba al'amarinmu.


Mushrikai

Sa'annan sai Manzo (S.A.W) ya fuskanci Mushrikan larabawa ya ce: Ku me ya sa kuke bautawa gumaka sabanin Allah (S.W.T)? Sai suka ce: Muna neman kusanci da Allah da wannan ne. Sai ya ce da su: Shin ita (gumakan) tana mai ji mai biyayya ga Ubangijinta ne kuma mai bauta gareshi shi ya sa kuke neman kusancin Allah da bauta mata da girmama ta? Sai suka ce: A'a. Ya ce: Ku ne kuka saka ta da hannunku? Suka ce: Na'am. Ya ce: To ai da ya halatta bauta ga wanin Allah, da ita tafi cancanta da ta bauta muku da fiye da ku ku bauta mata! Ashe kenan wanda ya umarce ku da bauta mata bai san maslaharku ba da sakamakon al'amarinku! Kuma ba shi da hikima cikin abin da ya kallafa muku.
Yayin da Manzo ya fadi wannan Magana sai suka yi sabani, wadansunsu suka ce da wasunsu: Allah ya shiga cikin wasu mutane ne da suke da wannan kamanni saboda haka ne muka suranta surarsu muna girmamata saboda mu girmama Ubangijinmu ta hanyar wannan sura da Ubangijinmu ya shige ta ya surantu da ita.
Wasunsu suka ce: Wannan surar ta wasu mutane ce da suka gabata suna masu bauta ga Allah kafinmu sai muka suranta surarsu muka bauta mata domin girmama Allah. Wasu kuma suka ce: Yayin Allah da ya halicci Annabi Adam (A.S) ya umarci Mala'iku da su yi masa sujada domin neman kusanci ga Allah, ashe kenan mu muka fi cancanta da yin sujada a kan Mala'iku, amma tun da wannan ya kubuce mana shi ya sa muka suranta su muna yi musu sujada domin neman kusanci zuwa ga Allah kamar yadda Mala'iku suka nemi kusanci da Allah ta hanyar yin sujada ga Adam (A.S).

Amsawa Ga Ra'ayin Farko

Sai Manzo (S.A.W) ya ce: Kun kuskure hanya kun bace. Amma ku (yana Magana da masu ra'ayin farko) da kuka ce: Allah ya shiga jikkunan wasu mutane ne nagari da kuka suranta surarsu kuna girmamata don girmama wannan surar da ya shiga ciki, da haka kun siffanta Ubangijinku da siffofin ababan halitta, shin zai yiwu Ubangijinku ya shiga cikin wani abu har ya zama wannan abin ya kewaye da shi?. To menene bambancinsa da sauran abin da ya ke abubuwa na shiga cikinsa na daga launi da dandano da kanshi da taushi da kaushi da nauyi da sako-sako? Don me abin da ake shiga cikinsa ya zama Fararre kuma Kadimi ba tare da an samu warewar wannan Kadimi kuma wancan Fararre ba daban-daban? Yaya wanda bai gushe samamme ba kafin waje zai bukaci waje? alhalin shi Mabuwayi Madaukaki ya kasance kuma bai gushe ba yana nan yadda yake.
Idan kuwa kuka siffanta shi da siffar ababan halitta to ya lizimta muku ku siffanta shi da siffar gushewa, idan kuwa kuka siffanta shi da gushewa da faruwa to dole ku siffanta shi da karewa, domin wannan su ne suka hada siffofin masu shiga da wadanda ake shiga cikinsu, kuma dukkan wadannan siffofin masu jirkita ne, idan kuwa zatin Ubangiji Madaukaki bai jirkita ba sakamakon shigarsa cikin wani abu to ashe kenan haka yana yiwuwa!?
Yana yiwuwa kada ya canja ya zama yana motsi yana zama baki, yana fari, yana ja, yana yalo, kuma siffofin ababan halitta suna faruwa a kan mai siffantuwa da su, har ya zama yana da siffar fararru gaba daya, ya zama Fararre, (Allah kuwa ya daukaka daga haka daukaka mai girma). Sa'annan (S.A.W) ya ce: Idan abin da kuke tsammani na Allah yana shiga cikin wani abu to abin da kuka yi gini a kai yana rusa maganarku ne. Sai mutanen suka yi shiru suka ce: Zamu duba al'amarinmu.

Amsawa Ga Ra'ayi Na Biyu

Sannan Manzo (S.A.W) ya fuskanci jama'a ta biyu ya ce: Ku ba ni labari idan kuka bauta wa surar wanda yake bauta wa Allah kuka yi mata sujuda, kuma kuka yi mata salla kuka dora fuskokinku masu daraja a kan kasa domin sujada a gareta me kuka rage wa Ubangijin Talikai?, amma kun sani cewa yana daga hakkin wanda ya lizimci a girmama shi da ibada kada a daidaita shi da bawansa.
Shin ba ku sani ba ne cewa da wani sarki ko wani mai girma zaku daidaita shi da bawansa a girmamawa da kaskantar da kai da tsoronsa, shin wannan ba kaskantarwa ba ne ga babba kamar yadda yake girmamawa ga karami ba? Suka ce: Na'am. Sai ya ce: Shin ba ku san cewa idan kuna bautawa Allah ta fuskacin bauta wa surar bayinsa masu bauta a gareshi kuna kaskantar da Ubangijin talikai ba ne? Ya ce: Sai mutanen suka yi shuru kadan suka ce: Zamu duba al'amarinmu.

Amsawa Ga Ra'ayi Na Uku

Sannan Manzo (S.A.W) ya ce da jama'a ta uku: Kun buga misali da mu da ku kuka kamanta mu da juna, alhali da mu da ku ba daya ba ne, saboda mu Bayin Allah ne ababan halitta da muke biyayya ga abin da aka umarce mu da shi, muke hanuwa da abin da aka hana mu ga barinsa, muke kuma bauta masa kamar yadda ya so, idan ya umarce mu ta wata fuska daga fuskoki sai mu bi shi, kuma ba zamu ketare wannan iyakar ba zuwa ga abin da bai umarce mu ba, domin ba mu sani ba ta yiwu da ya nufe mu da na farko ba ya son mu yi na biyun, kuma ga shi ya hana mu shiga gaba gareshi, yayin da ya umarce mu da mu fuskanci Ka'aba sai muka bi shi, sannan ya umarce mu da bauta a gareshi ta hanyar fuskantarta duk inda muke a sauran garuruwa wanda a cikinta ne muke yi masa biyayya, da wannan ba mu fita daga wani abu na daga biyayya a gareshi ba.
Yayin da Ubangiji (S.W.T) ya yi umarni da sujada ga Adam (A.S) bai yi umarni da yi masa sujada ba saboda surarsa da take ba ita ce shi (Adam) din ba, saboda haka ba ku da ikon kiyasta wancan a kan haka, domin ku ba ku sani ba tayiwu yana kin abin da kuke yi, domin bai umarce ku da shi ba.
Sannan Manzo (S.A.W) ya ce: Shin kuna ganin da wani mutum ya umarce ku da ku shiga gidansa wata rana da kansa shin zaku iya shiga bayan nan ba da umarninsa ba, ko kuma ku shiga wani gidan nasa daban ba wanda ya yi muku umarni da ku shiga ba? Ko kuma kuna ganin da wani mutum ya ba ku tufafi daga tufafinsa ko bawa daga bayinsa ko dabba daga dabbobinsa shin kuna iya karbar wannan?. Suka ce: Na'am. Sai ya ce: To zai yiwu ku dauki wani daban ba wanda ya ba ku ba? Suka ce: A'a, domin bai yi mana izini kan na biyun ba kamar yadda ya yi izini a na farko. Sai Manzo (S.A.W) ya ce: To ku gaya mini shin Allah (S.W.T) shi ne ya fi cancanta kada a shiga gaba gareshi ba tare da umarninsa ba ko kuma sashen ababan mallaka na daga bayi?. Suka ce: Allah ne ya fi cancanta kada a shiga gabansa a mulkinsa ba tare da izininsa ba. Sai ya ce: To me ya sa kuka yi haka? Yaushe ya umarce ku da ku yi sujada ga wadannan surorin? Imam Sadik (A.S) ya ce: Sai suka ce: "Zamu duba al'amarinmu".
Imam Sadik (a.s) Ya ce: "Na rantse da wanda ya aiko shi (S.A.W) da gaskiya kwana uku bai yi musu ba sai da suka zo wajan Manzon Allah (S.A.W) suka musulunta, sun kasance mutane ishirin da biyar ne; Biyar daga kowace kungiya. Suka ce: Ya Muhammad! Ba mu ga Mai dalili kamar naka ba, mun shaida kai Manzon Allah ne!" .