Hakikanin Addu'a

Allama Sheikh Muzaffar Hafiz Muhammad Sa'id
Kur’ani Mai Daraja: "Allah Ya shaida cewa: Lalle ne babu abin bautawa face Shi, kuma Mala'iku da ma'abuta ilmi sun shaida, Yana tsaye da adalci, babu abin bautawa face Shi, Mabuwayi, Mai Hikima". (Surar Aali Imrana, 3: 18) .

Addu'a Gun Ahlul Bait A wannan rubutu mai tarin albarka zamu so kawo muku wani abu wanda yake da amfani matuka game da addu'a kamar yadda ya zo daga littafin nan na mai girma malam muzaffar, hakika addu'a wani munajati ne da Allah (S.W.T) wanda babu wata ganawa da kebewa ta sirri da ta kai ta kima, sannan kuma muna ganin yadda ya zo a littafin kur'ani mai girma da sunnar ma'aiki (S.A.W) da kuma tafarkin nan na halifofinsa ahlul bait (A.S) game da karfafawa matuka game da yin addu'a.
Ahlul Baiti (AS) sun sani tuntuni cewa hukumarsu ba za ta taba dawowa garesu a rayuwarsu ba, kuma su da shi'arsu zasu ci gaba da zama a karkashin shugabannin da ba su ba, wadanda suke ganin wajabcin kawar da su da dukkan wata hanyar takurawa da tsanantawa.
Don haka a bisa dabi'a suka riki "Takiyya" addini kuma dabi'a garesu, su da mabiyansu, matukar zata kare masu jininsu kuma ba zata munana wa wasu ko addini ba, saboda su iya wanzuwa a cikin wannan rutsitsi mai ruruwar fitina mai ingizawa ga kiyayya da Ahlul Baiti (AS).
Don haka ya zama tilas suka koma ga koya wa mabiyansu hukunce-hukuncen Shari'ar musulunci, da kuma fuskantar da su fuskantarwa ta Addini ta gari, da kuma sanya su kan hanya ta tafarkin zamantakewa da jama'a mai amfani, domin su zama misalai na musulmi na gari masu adalci.
Wannan bangaren muna son mu yi nuni da wasu tarbiyyantarwarsu ga shi'arsu da tarbiyyar da zata kai su ga shiga cikin al'amuran zamantakewar al'umma mai amfani, suke kuma kusantar da su zuwa ga Allah madaukaki, suke kuma tsarkake zukatansu daga daudar zunubai da laifuffuka, kuma suke mayar da su adalai masu gaskiya. A nan muna kawo bayanai ne game da addu'a a matsayinta na abu na tarbiyya mai amfani tsakanins shi'an Ahlul Bait (A.S) da ubangijinsu madaukaki.

Game Da Addu'a Annbin Allah (S.A.W) Ya ce: "Addu'a makamin Mumini ce, kuma jigon Addini ce, kuma hasken sammai da kasa ce". Shi ya sa ta zama daga siffofin shi'a da suka kebantu da su, hakika sun wallafa abin da ya kai gomomi na manya da kananan littattafai game da falalarta da ladubbanta, da kuma addu'o'in da aka rawaito daga Ahlul baiti (A.S). Kuma an rabuta abin da manzo da Ahlul Baiti (A.S) suke gurin cim masa na kwadaitarwa a kan yin addu'a a cikin wadannan littattafai. Har ma ya zo daga garesu cewa: "Addu'a ita ce mafifciyar ibada". Da kuma cewa: "Mafi soyuwar aiki a bayan kasa a gun Allah madaukaki ita ce addu'a". Kuma ya zo cewa: "Addu'a tana mayar da kaddara da bala'i". Da kuma cewa: "Addu'a waraka ce daga dukkan cuta".
Kuma ya zo game da Amirul Muminin Ali Dan Abi Dalib (AS) cewa, ya kasance mutum ne ma'abocin addu'a, hakan nan ya kamata shugaban masu Tauhidi kuma shugaban mabiya Ubangiji ya kasance. Kuma addu'o'insa sun zo kamar yadda hudubobinsa suke a matsayin alama daga almomin balagar magana da fasaharta kamar addu'ar Kumail Bn Ziyad wacce ta kunshi ilimin sanin Ubangiji da fuskantarwar Addini, da kuma abin da ya dace ya zamanto madaukakin tafarki ga musulmi na gari.
Hakika addu'o'in da suka zo daga Annabi (S.A.W) da Ahlul Baiti (AS) su ne mafificin tsarin rayuwa ga musulmi -idan ya yi tunani a kansu- sukan cusa masa karfin imani, da karfin akida, da ruhin sadaukar da kai a tafarkin gaskiya, da sanin kansa, da dadin ganawa da Allah, da yankewa zuwa gareshi, kuma tana lakkana masa abin da ya wajaba a kan mutum ya san shi a addininsa, da kuma abin da yake kusantar da shi zuwa ga Allah Madaukaki, ya kuma nesata shi daga barna da son zuciya da bidi'a batacciya. A takaice dai wadannan addu'o'in sun kunshi sanin Addini ta fuskar kyawawan dabi'u da tsarkake zukata, ta wata fuskar kuma sun kunshi akidar Musulunci, kai ita ce ma mafi girman madogarar ra'ayoyin falsafa, da binciken ilimi dangane da sanin Ubangiji da kyawawan dabi'u.
Idan da mutane sun iya kuma ba dukkansu ne masu iyawa ba, da sun shiriyu da shiriyar da wadannan addu'o'in suke kushe da ita a cikin abin da ta kunsa madaukaka, da ba zaka samu irin wannan fasadin da kasa take cike da shi ba, kuma da wadannan rayukan da sharri ya yi musu katutu sun yi shawagi a sammai domin jin gaskiya, sai dai yaya dan Adam zai saurari maganar salihai da masu kira zuwa ga gaskiya alhalin fadinsa madaukaki ya nuna hakikaninsu da fadinsa: "Hakika rai mai umarni da mummuna ce". Surar Yusuf: 53. "Kuma mafi yawancin mutane ko da kayi kwadayi ba masu shiryuwa ba ne". Surar Yusuf: 103.
Na'am abin da ya kawo kafuwa da damfaruwar munanan ayyuka ga mutum shi ne, rudin kansa, da jahiltar munanan ayyukansa, da yaudarar kansa cewa shi yana aikata aikinsa, sai ya yi zalunci ya ketare iyaka, ya yi karya, ya yi kage, ya bi sha'awarsa yadda ransa yake so, tare da haka yana yaudarar kansa da cewa shi bai yi komai ba sai abin da ya dace ya aikata, kuma ya runtse dagangan daga munin abin da ya aikata, ya kuma karanta kuskurensa a idanunsa. Wadannan addu'o'in daga hadisai da suke samun karfafa daga tushen wahayi, sun yi kokarin sanya mutum ya koyi zargin kansa da kadaita zuwa ga Allah (S.W.T), domin su cusa masa furuci da kuskurensa da kuma cewa shi mai aikata zunubi ne, wanda ya wajaba a kansa ya yanke zuwa ga ubangijinsa domin neman tuba da gafara. Kamar misalin fadin mai addu'a a cikin Addu'ar Kumail:
"Ya Ubangijina! Ya Majibincina! Ashe zaka gudanar da hukunci a kaina a kan abin da na bi son raina a cikinsa, kuma ban kiyaye kawatarwar abokin gabata ba a cikinsa, don haka ya rude ni da abin da ya so, kuma hukuncinka ya taimake shi a kan haka, har na ketare wasu daga cikin dokokinka saboda abin da ya gudana gare ni na daga hakan, kuma na saba wa wasu daga umarce-umarcen ka".
Babu shakka cewa misalin irin wannan ikrarin a cikin kadaici ya fi sauki ga mutum a kan ikrari a cikin jama'a, duk da kuwa yana daga cikin mafi tsananin wahalar halaye ga mutum koda kuwa tsakaninsa ne da ransa. Idan da wannan hali zai samu ga mutum, da ya samu sha'ani mai girma na kamala wajan rage takamar kansa mai sharri, da tarbiyyantar da ita a kan alheri. Duk wanda yake son tarbiyyar zuciyarsa, to babu makawa ya koyar da ita kadaitaka da `yantaccen tunani domin yi mata hisabi, kuma mafificiyar hanyar wannan kadaitakar ita ce dukufa a kan karanta wadannan addu'o'in da aka samo daga ruwayoyi, wadanda kuma suke ratsa zuciya, kamar karanta addu'ar Abi Hamza Assumali (R.A.)
"Ya Ubangiji ka rufe ni da suturcewarka, ka yafe mini zargina da girman fuskarka". Yi tunani a kan wannan kalma "Ka rufe ni", a cikinta akwai abin da yake tayar wa zuciya kwadayin suturce abin da ta tattara a kai na mummunan aiki, domin mutum ya fadaka a kan wannan al'amari, ta yanda kuma zai san haka idan ya karanta wannan fakara bayan waccan:
"Idan da yau wani baicin kai ya san da zunubina to da ban aikata ba, kuma da na tsoraci gaggauta ukuba da na nisanci zunubin". Wannan irin furuci daga cikin zuciya, da kuma fadaka zuwa ga kwadayin suturce abin da yake da shi na daga munana, yana tayar da kwadayin neman gafara da yafewa daga Allah (S.W.T) don gudun kada ya tozarta shi a gurin mutane, idan da Ubangiji ya so ya yi masa ukuba a nan duniya ko kuma a lahira a kan ayyukansa, sai mutum ya dandani dadin addu'ar sirri, da zance da Allah a asirce, ya yanke ya koma ga Allah, ya yi godiya gare shi da ya yi masa afuwa alhalin yana da kudura amma bai fallasa shi ba yayin da yake cewa:
"Godiya ta tabbata gareka a kan hakurinka bayan saninka, da yafewarka bayan kudurarka". Sannan kuma addu'ar ta sake nuna wa rai tafarkin neman uzuri daga abin da ta yi sakaci dangane da shi saboda wannan afuwa da hakuri daga gare shi (S.W.T), domin kada alakar da take tsakanin bawa da Ubangijinsa ta yanke, kuma domin koya wa bawa cewa sabonsa ba wai don kafirce wa Allah ba ne ko kuma wulakanta umarninsa, yayin da yake cewa:
"Kuma hakurinka gare ni yana dauka ta yana ja na zuwa ga saba maka, kuma suturcewarka na kira na zuwa ga karancin jin kunya, kuma sanina game da yalwar rahamarka da girman afuwarka yana gaggautar da ni zuwa ga kifuwa a kan abubuwan da ka haramta". Wannan shi ne tsarin salon addu'ar a ganawa ta asirce ta tsarkake zukata, da saba wa son ransu, da yin da'a, da barin aikata sabo, da wannan littafi ba zai wadatar ba ya kawo irin wadannan misalai fiye da haka alhalin ga su da yawan gaske.
Salon tattaunawa da Ubangiji domin neman afuwa da gafara yana kayatar da ni, kamar yadda ya zo a Addu'ar Kumail Bn Ziyad: "Kuma kaicona! Ya shugabana majibincina! Ashe ka sallada wuta a kan fuskokin da suka kifu ga girmanka suna masu sujada, da kuma a kan harsunan da suka yi furuci da gasgatawa, kuma suna yabo da godiyarka, da kuma a kan zukata da suke neman ilimi game da kai har suka zamanto masu tsoro, da kuma gabobi da suka yi kokari zuwa guraren ibadarka suna masu biyayya, suka kuma yi ishara ga afuwarka suna masu mika wuya? Ba haka zato yake game da kai ba, ba kuma mune muka fi sanin falalarka ba."
Ka maimaita karanta wannan fakara sannan ka yi tunani game da taushin wannan irin kafa hujjar da kololuwar fasaharsa, da azancin bayaninsa, a lokaci guda yana mai sanya wa zuciya furuci da takaitawarta ga ibada, kuma tana cusa mata rashin debe tsammani daga rahamar Allah da baiwarsa, sannan kuma tana yi wa zuciya magana da zance na tausasawa ta wani bangare a boye, domin ya cusa mata sanin manyan wajibanta, domin tana kaddara cewa ita dama ta riga ta ba da wadannan wajibai baki daya, sannan kuma tana koya wa mutum cewa da wadannan ayyukan ne yake cancantar falalar Allah da gafararsa, wannan kuwa wani abu ne da kan zaburar da mutum ya koma ga zuciyarsa don ya aikata abin da ya wajaba a kansa idan har bai aikata shi ba.
Karanta wani salon addu'ar da a ke neman uzuri a cikin ta da cewa: "Ya shugabana majibincina! Ka sani ina iya hakuri a kan azabarka amma ta yaya zan yi hakuri a kan rabuwa da kai! Kuma ko da na iya hakuri a kan zafin wutarka amma yaya zan yi hakuri a kan rashin dubi zuwa ga girmanka!".
Wannan wani irin cusa wa zuciya jin dadin samun kusanci da Allah (S.W.T) ne, da duba zuwa ga karamcinsa da kudurarsa, don soyayya da bege gare shi, da kuma nuna cewa wannan irin jin dadin ya kamata ne ya kai ga darajar da tasirin barinsa a wajan rai ya fi zafin wuta azaba. Idan muka kaddara cewa mutum na iya jure zafin wuta, to da ba zai iya hakuri a kan waccan rabuwar ba, kamar kuma yadda daga wannan bangaren addu'ar za a fahinci cewa wannan soyayyar da jin dadin na kusanci da abin kauna abin bauta shi ne mafificin mai ceto ga mai zunubi a gurin Allah, yadda zai yafe, kuma ya yi masa rangwame. Mamakin taushin wannan salo na kaskantar da kai ga Mai girma, Mai hakuri, Mai karbar tuba, Mai gafarta zunubai, ba zai buya ba.
Babu Iaifi mu rufe wannan bayani da kawo takaitacciyar addu'a da ta kunshi kyawawan dabi'u, da kuma abin da ya kamata kowace gaba ta mutum ko kowane mutum ya siffantu da su na daga siffofi kyawawa ababan yabo:
"Ya Allah ka arzuta mu da muwafakar da'a, da nesantar sabo, da gaskiyar niyya, da sanin abubuwa masu alfarma, kuma ka girmama mu da Shiriya da tsayuwa daidai, da daidaita harsunanmu, da daidaito, da hikima, ka cika zukatanmu da ilimi da sani, ka tsarkake cikkunanmu daga haram da shubuha, ka kame hannayenmu daga zalunci da sata, ka runtsar da idanuwanmu daga fajirci da ha'inci, ka toshe kunnuwanmu daga jin maganar banza da giba, kuma ka yi falala ga malamanmu da zuhudu da nasiha, ga masu neman ilimi kuma da kokari da shauki, ga masu sauraro kuma da biyayya da wa'aztuwa, ga marasa lafiyar musulmi kuma da waraka da hutawa, ga matattunsu kuma da rangwame da rahama, ga tsofaffinmu kuma da nutsuwa da kwanciyar hankali, ga matasanmu kuma da komowa da yawan tuba, ga matanmu kuma da jin kunya da kamewa, ga mawadatanmu kuma da kaskan da kai da yalwatawa, ga matalauta kuma da hakuri da wadatar zuci, ga mayaka kuma da cin nasara da galaba, ga ribatattun yaki kuma da kubuta da hutawa, ga shugabanni kuma da adalci da tausayawa, ga al'umma kuma da yin daidai da kyawun hali. Ka sanya albarka ga mahajjata da masu ziyara da guzuri da ciyarwa, kuma ka hukunta abin da ka wajabta musu na daga hajji da umra don falalarka da rahamarka, Ya mafi rahamar masu rahama".
Kuma ni ina mai wasiyya ga 'yan'uwana masu karatu da cewa, kada damar karanta wannan addu'a ta kubuce musu, tare da sharadin yin tunani a kan ma'anoninta da abubuwan da take nufi, tare da halarto da zuciya da fuskantowa zuwa ga Allah da tsoro da kaskan da kai, da kuma karanta ta tamkar yana magana da kansa ne, tare kuma da bin ladubban da aka ambata daga Ahlul Baiti (A.S), Domin karanta ta ba tare da fuskantar da zuciya ba to maganar baka ce kawai, kuma ba ta kara wa mutum sani, ba ta sama masa kusanci, kuma ba ta yaye masa bakin ciki, kuma ba a amsa masa addu'a da haka. "Hakika Allah mai girma da buwaya ba ya karbar addu'a daga zuciya rafkananniya, don haka idan ka yi addu'a ka fuskanto da zuciyarka, sannan ka ji cewa lalle za a amsa" .

Addu'o'in Sahifatus Sajjadiyya Bayan aukuwar al'amarin karbala mai ban takaici, da kuma kame ragamar shugabancin al'ummar musulmi da Banu Umayya suka yi, kuma suka dulmuya a cikin danniya, suka yi dumu-dumu da jinin mutane, sannan suka yi watsi da koyarwar Addini, sai Imam Zainul Abidin kuma Sayyiddus Sajidin ya zauna a gidansa yana bakin ciki da jin takaici, yana gida babu wani mai kusantarsa, kuma ba zai iya yada wa mutane abin da ya wajaba a kansu ko ya kamata su sani ba.
Sai ya tilastu a kan ya dauki salon addu'a wanda muka ambata na cewa, yana daga cikin hanyoyin tsarkake zukata a matsayin hanyar yada koyarwar Kur'ani da ladubban musulunci, da kuma sanar da tafarkin Ahlul Baiti (AS), kuma hanyar cusa wa mutane ruhin addini da zuhudu, da abin da ya wajaba na daga gyaran zukata da kuma kyawawan dabi'u.
Wannan hanya ce da ya fare ta a fakaice don koyar da mutane ba tare da ya jawo hankalin azzaluman Shugabanni da suke matsa masa ba, kuma ba zasu iya kafa masa wata hujja ba, don haka ne ya yawaita yin wadannan addu'o'i masu zurfi, kuma an tattara wadansunsu a littafin Sahifatus Sajjadiyya da ake yi wa lakabi da Zaburar Zuriyar Muhammad (S.A.W). Salonta da manufofinta sun zo da siga da salon Larabci mafi daukaka, kuma mafi daukakar addini, da mafi ingancin asiran tauhidi da annabci, kuma mafi ingancin hanyar koyar da kyawawan dabi'u ababan yabo, da kuma ladubban musulunci. Kuma ta kunshi maudu'ai daban-daban ne na tarbiyya ta Addini da ta shafi koyarwar Addini, da kyawawan dabi'u, ta hanyar addu'a, ko kuma addu'a ce amma da salon koyar da Addini da kuma kyawawan dabi'u. Ita ce salon bayanin Larabci mafifici, kuma mafi daukakar mashayar manufar sanin Ubangiji da kyawawan dabi'u bayan Kur'ani da Littafin Nahjul Balagha.
Daga cikinsu akwai wanda yake sanar da kai yadda zaka daukaka Allah kuma ka tsarkake shi, da yabonsa da gode masa da komawa zuwa gareshi. Daga ciki akwai wacce take sanar da kai yadda zaka yi zance da Allah, da kebewa da shi da sirrinka, da yankewa zuwa gareshi, daga cikinta akwai wadanda ke shimfida maka ma'anar Salati ga Annabi (S.A.W) da manzannin Allah da zababbunsa daga cikin halittunsa, da yadda ake yin sa, daga cikinsu akwai wadanda zasu fahimtar da kai abin da ya dace ka bi iyayenka da shi, da kuma abin da zai yi maka sharhin hakkokin Uba a kan dansa, da na da a kan mahaifinsa, ko kuma hakkokin makwabta, ko na dangi, ko hakkokin musulmi baki daya, ko hakkokin matalauta a kan mawadata da kuma akasin haka. Daga cikin addu'o'in akwai wadanda zai fadakar da kai kan abin da ya wajaba na basussukan mutane a kanka, da kuma abin da ya kamata ka sani na al'amuran tattalin arziki da dukiya, a abin da ya kamata ka yi mu'amala da shi ga abokanka da sauran mutane baki daya, da wadanda kake neman yin mu'mala da su a maslaharka, da kuma abin da zai hada maka dukkan kyawawan dabi'u, kuma ya zama maka tafarki cikakke na ilimin kyawawan dabi'u.
Daga cikinsu akwai wadanda zasu koya maka yadda zaka yi hakuri a kan munanan abubuwan da suke faruwa, da kuma yadda zaka yi yayin da kake rashin lafiya, da kuma yayin da kake lafiya lau. Daga cikinsu akwai wadanda suke yi maka sharhin ayyukan wajibi da suka hau kan sojojin musulunci da wajiban mutane dangane da su, da dai sauran wadannan da kyawawan dabi'u abin yabo suke farlanta su, duk ta hanyar addu'a. Abubuwan da suke kunshe cikin addu'ar imam su ne:

Na farko: Sanin Allah da girman kudurarsa, da bayanin kadaita Shi, da tsarkake shi da mafi zurfin kalmomi na ilimi, wannan kuwa yana maimaituwa ne a kowace addu'a da salo daban-daban, kamar yayin da kake karantawa a addu'a ta farko: "Godiya ta tabbata ga Allah na farko wanda babu wani na farko da ya kasance kafin shi, na karshen da babu wani na karshe da zai kasance bayansa, wanda idanuwan masu gani suka gaza ganin sa, wahamce-wahamcen masu siffantawa suka gajiya wajen siffanta Shi, Ya fari halittu da kudurarsa a farkon farawa, ya kuma kago su kamar yadda ya so kagowa.". Karanta ma'anar na farko da na karshe da kyau da kuma tsarkake Allah (S.W.T) daga kasancewar wani gani ko wahami ya kewaye shi, da kuma tunani kan zurfin ma'anar halittawa da samarwa.
Sannan ka karanta wani salon wajen bayyana kudurar Allah da tadabburi a cikin addu'a ta 6: "Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya halitta dare da rana da karfinsa, ya rarrabe tsakaninsu da kudurarsa, ya sanya wa kowanne daga cikinsu iyaka ayyananniya, yana shigar da kowane daya daga cikinsu a cikin dan'uwansa, da kaddarawarsa ga bayi a cikin abin da yake ciyar da su, kuma yake sanya su su girma. Sai ya halitta musu dare domin su huta daga wahalar kaiwa da komowa da dawainiya, kuma ya sanya shi sutura domin su lulluba da hutunsa, sai ya zama wartsakewa da karfi garesu domin su sami jin dadi da sha'awa da shi. Har zuwa karshen abubuwan da ya ambata na fa'idar halittar rana da dare, da kuma abin da ya kamata mutum ya yi godiyarsa na daga wadannan ni'imomi.
A wani salon kuma na bayanin dukkan al'amura a hannun Allah (S.W.T) suke zaka karanta a addu'a ta 7 cewa: "Ya wanda da Shi ne ake warware kulle-kulle! Ya wanda da shi ne kaifin tsanani yake dakushewa! Ya wanda daga gareShi ake neman mafita zuwa yalwar sauki! mawuyatan al'amura na rusunawa ga kudurarka! sabubba suna tasiri ne da ludufinka, kuma kaddarawarka ta gudana ne a bisa ikonka, abubuwa suna zartuwa da nufinka ne, suna masu umartuwa da nufinka ba tare da fadarka ba, kuma masu tsawatuwa ne da nufinka ba tare da haninka ba.

Na Biyu: Bayani game da falalar Ubangiji ga bawansa, da kuma gazawar bawa wajen bayar da hakkin Ubangiji komai abin da ya yi na da'a da ibada kuwa, da kuma yankewa domin komawa zuwa ga Ubangiji kamar yadda kake karantawa a addu'a ta 37: "Ya Allah hakika babu wani da zai kai ga matukar godiya gare ka sai wata Kyautatawarka ta same shi wacce zata sake lizimta masa wata godiyar, kuma ba ya kaiwa ga matukar da'arka koda kuwa ya dage sai ya gaza yin yadda ka cancanta ga falalarka, Mafificin mai godiya gareka a bayinka ya gaza a kan godiyarka, kuma mafi bautarsu mai takaitawa ne ga bautarKa".
Saboda girman ni'imomin Allah (S.W.T) kan bawansa da ba su da iyaka bawan ya yi kadan ya ba da hakkinsa komai kokarin da ya yi, yaya kenan idan kuma ya sabe shi yana mai tsaurin kai, yayin nan kuma ba zai taba iya kankare sabo koda guda daya ba, kuma wannan shi ne abin da fakara mai zuwa ta addu'a ta 16 take nunawa: "Ya Ubangijina idan da zan yi kuka har fatar idona ta fadi, kuma na yi kururuwa har muryata ta dushe, kuma na tsaya gare ka har kafafuwana su tsattsage, kuma in yi ruku'u gareka har bayana ya sance, kuma na yi maka sujada har kwayoyin idanuna su faffado, kuma turbayar kasa ta cinye duk tsawon rayuwata, kuma na sha ruwan toka har zuwa karshen rayuwata, sannan na yi ta ambaton ka duk tsawon wannan lokacin har sai harshena ya gaza, sannan kuma na zama ban taba daga ganina na dubi sama ba don jin kunyar ka, duk wannan ba zai wajabta shafe mini mummunan aiki daya daga munanan ayyukana ba".

Na uku: Sanar da lada da azaba, da aljanna da wuta, da kuma cewa ladan Ubangiji dukkaninsa kyauta ne kawai, kuma bawa yana cancantar azaba ne da mafi karancin sabo da ya yi, kuma Ubangiji yana da hujja a kansa game da haka.
Haka nan dukkan addu'o'in Sahifatus Sajjaddiya sun kawo maganar irin wannan azaba mai tasiri, domin tsoratarwa da sanya tsoro a zuciya, da sanya mata sa tsammani da ladan Ubangiji, dukkan wannan shaida ce a kan haka ta salo daban- daban da yake sa wa zuciya tsoro kan sabo. Kamar abin da zaka karanta a addu'a ta 46:- "Hujjarka tabbatacciya, Shugabancinka tsayayye ne ba ya gushewa, don haka tsananin azaba madawwamiya ta tabbata ga wanda ya nisance ka, tabewar tozartuwa ta tabbata ga wanda ya karkace daga gareka, tsiyacewa ta tabbata ga wanda ya rudu ya bar ka, jujjuyawarsa a azabarka ta yawaita, kaikawonsa a cikin ukubarka ya tsawaita, bukatarsa ga burinsa na samun sauki ya nisanta, saukin samun mafitarsa abin yanke kauna ne, adalci ne daga hukuncinka ba ka zalunci a cikinsa, kuma yin daidai a hukuncinka ba ya kaucewa, hakika ka bayyanar da hujjoji kuma ka jarraba uzurori".
Kuma kamar yadda kake karanta addu'a ta 31: "Ya Allah! ka ji kan kadaitakata ta gabanka, da kidimewar zuciyata daga tsoronka, da firgicewar gabobina don haibarka, kuma ya Ubangijina! zunubina ya sanya ni a matsayin kaskanci a farfajiyarka, idan na yi shiru babu wani da zai yi magana madadina, idan kuma na nemi a cece ni to ni ban cancanci ceto ba.".
Kamar kuma karantawarka a addu'a ta 39: "Domin kai idan har ka saka mini da gaskiya to zaka halakar da ni, idan kuma ba ka lullube ni da rahamarka ba to zaka halakar da ni, kuma ina rokon ka ka dauke daga zunubina wanda daukar nauyinsa ya gajiyar da ni, ka yi tsira ga Muhammad da Zuriyarsa, kuma ka ba wa raina kanta saboda zaluncinta".

Na Hudu: Jan mai addu'a zuwa ga dauke sawunsa daga aikata munanan ayyuka, da siffantuwa da munanan siffofi domin wanke ruhinsa da tsarikake zuciyarsa, kamar yadda kake karantawa a addu'a ta 20: "Ya Allah ka cika mini niyyata da ludufinka, kuma ka inganta mini yakinina da abin da yake gare ka, ka gyara min abin da ya baci daga gare ni da kudurarka, Ya Allah! Ka yi tsira ga Muhammad da Zuriyar Muhammad ka jiyar da ni dadi daga shiriya ingantacciya da ba zan taba neman musanya daga gareta ba, da kuma hanya ta gaskiya wacce ba zan taba karkacewa daga kanta ba, da kuma niyyar shiriya da ba zan taba kokwanto a cikinta ba.
Ya Allah kada ka bar wani hali da yake aibi ne da ake aibata ni da shi sai ka gyara shi, ko kuma wani laifi da za a zarge ni da shi sai ka kyautata shi, ko kuma wani halin karimci da yake tauyayye gare ni har sai ka cika Shi".

Na biyar: Sanya wa mai karanta addu'ar dauke sawunsa daga mutane, da rashin kaskantar da kansa gunsu, kuma kada ya kai kukan bukatarsa gun wani ba Allah ba, domin kwadayin abin da yake hannun mutune yana daga cikin mafi munin abin da mutum zai siffantu da shi kamar yadda zaka karanta a addu'a ta 20: "Kuma kada ka fitine ni da neman taimakon waninka idan na matsu, da kuma kaskan da kai don tambayar wani ba kai ba idan na bukatu, da kuma mika wuya gaba ga wanda ba kai ba idan na tsorata, saboda haka sai in cancanci tabarwarka da haninka da kawar da kanka".
Da kuma misalin addu'a ta 28: "Ya Allah ni na tsarkake niyyata da yankewa zuwa gareka, kuma na juyo zuwa gareka baki daya, kuma na kawar da fuskata daga dukkan wanda bai wadata da falalarka ba, na ga cewa bukatar mabukaci zuwa ga wani mabukacin wauta ce, kuma bacewar hankalinsa ne."
Da kuma misalin abin da kake karantawa a addu'a ta 13: "Duk wanda ya yi kokarin magance rashinsa ta gurinka, kuma ya yi kokarin kawar da talauci da taimakonka, hakika ya nemi bukatarsa a gurin da ake tsammani, kuma ya zo wa bukatarsa ta gurin da ake zaton samu, kuma ya zo wa bukatarsa ta fuskarta da ta dace. Wanda kuma ya juya da bukatarsa kuwa ga daya daga cikin halittunka, ko kuma ya sanya shi sababin samunta ba kai ba, to hakika ya jawo wa kansa hani, kuma ya cancanci kubucewar kyautatawa daga gare ka".

Na Shida: Koya wa mutane wajabcin kiyaye hakkokin wasu, da taimaka wa sashensu ga sashe, da fifita juna a tsakaninsu domin tabbatar da ma'anar yan'uwantakar Musulunci, kamar yadda kake karantawa a addu'a ta 38: "Ya Allah! ni ina mai neman uzuri daga gareka a kan dukkan wani da aka zalunta a gabana amma ban taimake shi ba, da wani kyakkyawan abu da aka kwararo mini shi amma ban yi godiyarsa ba, da duk wani mummunan aiki da aka nemi uzurina ban bayar da uzuri ba, da duk wani mabukaci da ya roke ni ban ba shi ba, da hakkin mai hakki da ya hau kaina daga muminai amma ban cika masa ba, da kuma daga dukkan wani aibi na mumini da ya bayyana gare ni amma ban suturce shi ba".
Hakika irin wannan neman uzuri yana daga cikin mafi bayyanar abin da zai fadakar da zuciya zuwa ga abin da aikata shi ya kamata na wadannan kyawawan dabi'u madaukaka.
A addu'a ta 39 akwai karin haske a kan hakan, sai ya sanar da kai yadda zaka yafe wa wanda ya munana maka, kuma yana gargadin ka game da yin ramuwar gayya, yana kuma daukaka zuciyarka zuwa matsayin tsarkakku: "Ya Allah duk wani bawa da ya yi mini abin da na hana shi a kansa, ya kuma keta mini abin da na kange shi gareshi, da nauyin zaluntata, ko zuciyata ta tuna shi yana rayayye, to ka gafarta masa abin da ya yi mini, ka yafe masa abin da ya riga ya gabatar gareni, kada ka tsayar da shi don tambaya a kan abin da ya aikata a kaina, kuma kada ka tona asirinsa a kan abin da ya aikata a kaina, kuma ka sanya rangwamen da na yi masa na afuwa gare su, da kuma kyautar da na yi musu na daga sadaka garesu, ya zama mafi tsarkin sadakar masu sadaka, kuma mafi daukakar addu'ar ma'abota kusanci gare ka. Kuma ka musanya mini afuwata gare su da afuwarka, da addu'ata garesu da rahamarka, har kowanne daga cikinmu ya rabauta da falalarka".
Mamaki ya girmama ga wannan fakarar ta karshe! da kuma yawan girman tasirinta a cikin zukatan masu alheri! Domin fadakar da su a kan kyakkyawan nufi ga dukkan mutane, da nema wa kowa sa'ada hatta ga wanda ya zalunce su. Irin wannan yana da yawa a cikin addu'o'in Sahifatus sajjadiyya, a cikinta akwai da yawa daga irin wadannan koyarwa ta ubangiji don tsarkake rayukan 'yan Adam wacce da sun yi riko da ita da sun kasance masu shiryuwa.