Zabar Mace

Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
Zab'ar Mace Ko Namijin Aure Ina godiya ga Allah da ya ba ni damar rubuta wannnan littafi mai suna "Zab'ar Mace Ko Namijin Aure" wanda yake nuni da wane namiji ko wace mace ce za a zab'a don zama tare. Mun rubuta wannan littafi ne daidai yadda zai dace da al'adun mutanenmu da kuma bayaninsa bisa ra'ayoyi mabanbanta, wannan ya taso ne musamman bayan mun ga ya dace mu rubuta wani abu wanda zai zama mai amfani ga al'ummarmu.
Littafin ya k'unshi tak'aitaccen bayani ne game da yadda ya kamata gida ya kasance, da siffofin ma'aurata, da kuma yadda ya kamata su kalli rayuwa, da abin da ya shafi kula da hak'k'in juna kamar yadda musulunci ya gindaya ba tare da k'etare iyaka ba.
Muna fatan littafin ya zama mai amfani ga d'an Adam a yanayin zamantakewar gida, ta yadda zai zama sanadi na gina al'umma saliha da cigaban duniyar musulmi baki d'aya.
Ina rok'on Allah ya bayar da ladan rubuta wannan littafi ga malamaina da dukkan wanda ya sanar da ni wani abu da amfaninsa ya shafi duniya da lahira.

A musulunci an yi umarni ne da a yi aure ba domin biyan buk'ata ta duniya ko ta sha'awa ba kawai, akwai buk'ata ta gina al'umma saliha da zata ci gaba da d'aukar nauyin isar da sak'on Allah a duk fad'in Duniya, wanda wannan yana buk'atar taimakekeniya tsakanin ma'aurata, sa'annan akwai samun nutsuwa ta ruhi da d'an Adam yana buk'atarsa wanda an sanya shi ne ya zamanto ta hanyar zamantakewa tsakanin miji da mata.
Misali mace koda ta yi ilimi kuma ta samu komai na wannan duniya, da dukkan ni'ima, haka nan ma namiji, idan ba su da mai d'ebe musu kewa ta fuskacin zaman auratayya to akwai wani gib'i babba da ba su cike shi ba, wanda ba ya samuwa sai ta hanyar auratayya, wacce kur'ani mai girma ya yi nuni da ita , kamar yadda a zamantakewar tare tsakanin ma'aurata idan aka mayar da k'auna da so suka koma k'iyayya da gaba, abin yakan fi zama ba tare da mai d'ebe kewa ba muni. Kamar yadda haka nan ana son yin aure da wuri ga wanda ya balaga matuk'ar ya samu yalwa, domin a cikin rashin yin hakan akwai fitina a bayan k'asa da fasadi mai girma kamar yadda ya zo daga Ahlul Baiti (a.s) . Mu sani akwai kamalar da ba ta yiwuwa a san ta ko a kai zuwa gareta sai ta hanyar aure, kuma ba ta samuwa ta hanyar zaman banza da fasik'anci. Irin wad'annan abubuwan sun had'a da: sanin ma'anar ciyarwa, yafewa, soyayya, hak'uri, juriya, d'aukar nauyin mutane, reno, tarbiyyar 'ya'ya, fahimtar k'imar iyaye, tunanin gida da sauransu.
Ayatul-Lahi makarim shirazi yana cewa: saudayawa daga cikin abubuwa kamar ma'anar soyayya, da k'auna, da yafewa, da kyauta, da baiwa da tausayi, da fansar rai, ma'anarsu ba ta ganuwa da fahimtuwa sai da aure, wanda zaman banza ba tare da aure ba da matar haram ko zaman gwauranci da rashin aure ba za a iya fahimtar hak'ik'aninsu ba, kuma riskarsu tana yiwuwa ta hanyar zamantakewar aure ne kawai .

Masu ilimi sun kawo wasu abubuwa kamar haka da sukan kawo jinkirin aure:
1- Tsawon muddar lokacin karatu: ta yadda saurayi ko budurwa kafin ya kai ga kammala jami'a ya kai shekara talatin zuwa talatin da biyar a mafi yawan lokuta, saudayawa wannan yakan jefa wasu cikin halin da suka katse karatu idan ba zasu iya had'a biyun ba, don haka yana kan al'umma da gwamnatocinsu su yi tunanin maganin wannan koda ta hanyar tallafi ne a kan 'yan makaranta. Misali a nan a k'asar farisa sukan yi k'ok'arin yi wa dubunnan d'aliban jami'a aure a kyauta kowace shekara da kuma ba su tallafi.
2- Samun damar yin alak'ar haram: Yawaitar gidajen karuwai da wajajen fasik'anci saudayawa yakan sanya wasu samari su ga ya fi musu sauk'i su je su yi mummunar mu'amala ta haram da matan banza na wani d'an lokaci tsawon rayuwar samartakarsu. Wannan ma wani abu ne da musulunci ya sanya mafita gareshi ta hanyoyi da dama kamar haka:
a- Tallafin aure da wuri daga baitul mali ga dukkan wanda ba zai iya aure ba kuma da buk'atar hakan domin ya balaga.
b- Tarbiyyantarwa ta hannun malamai, da kafafen watsa labaru da jaridu da makarantu.
c- Hana gidajen fasadi da kulle duk wani waje da ake ashararanci.
d- Wayar da kan mutane a ilmance domin su san illar wannan mummunan hali da abin da yake jawowa.
e- Idan ma'abota wannan halin ba a shirye suke su yi aure ba koda kuwa suna da yalwa, to musulunci har yanzu ya ba su damar yin auren mutu'a, don haka ne ma idan irin wad'annan wajajen ba zasu kullu ba, sai wad'annan mata masu zaman kansu su tuba daga wannan ayyuka, maimakon su rik'a zina sai su yi auren mutu'a da duk wanda suke so, bayan muddar ta k'are sai su yi idda. Wasu malamai suna ganin gwamnatin musulunci tana iya mayar da gidajen banza su koma gidajen shari'a ta wannan hanya, musamman gudun cewa irin wad'annan mutane idan aka kore su, to zasu koma suna fasik'anci a b'oye, maimakon haka sai su tuba su bi hanyar da shari'a ta gindaya musu.
3- Rashin yalwa da talauci da tsadar aure: yana daga cikin abin da kan kawo jinkirin aure ga samari, don haka bai kamata ba a bi al'ada da k'untatawa da tsanantawa ga kud'in aure da zata kai ga wannan jinkiri har ruhin samari da budurwa su gurb'ata da ciwowwuka, ko miyagun halaye, saudayawa jinkirin yana faruwa sakamakon:
a- Sanya sharud'd'a masu wahala ga saurayi.
b- Yawan kud'in da zai kashe kan kayan tanadin gida da sauransu.
A game da matsalar farko, al'umma ne ya kamata su sanya hannu wajen warwareta, amma matsala ta biyu al'umma da hukuma su ne zai zama sun sanya hannu wajen maganinta.
4- k'arancin amintuwa da juna tsakanin saurayi da budurwa, musamman akan samu wasu da yawan munana zato ga duk wanda suka had'u da shi, ta yadda yakan yi musu wahala su yarda da shi .
Ta wani b'angaren kuma wani lokaci jinkirin yakan taso ne saboda ruwan ido ko kuma tsanantawa wajen sharud'd'an saurayi ko budurwa da zasu aura wanda wannan ya kan d'aukar musu tsawon lokaci ba su samu mai wannan sharud'd'an ba, ko ma suka samun mai wad'annan sharud'd'an. Mu sani binciken halin wanda za a aura saurayi ne ko budurwa yana da kyau, amma kada ya kai ga matsananci da zai fita daga al'adarsa.
Warware wannan matsalar yana hannun samari da 'yan mata ne.

Wasu daga Matsalolin da saurayi ko budurwa kan iya fuskanta kafin aure ko bayan aure: Wani lokaci saurayi da budurwa sukan fuskanci matsala ne kamar haka:
1- Burin da kowane b'angare da iyayen saurayi da budurwa, ko su kansu saurayi da budurwa suke ci game da saurayi ko budurwa. Kamar kayan d'aki da yake tunanin a kawo ta da shi da sauransu, ko kuma shi kayana da take tunanin ya kai gidansu.
2- Nau'in sadakin da ake ayyanawa, ko kuma in ce kayan mun gani muna so da lefe a al'adunmu da ake sanyawa a kan saurayi, da idan suna da yawa yakan sanya jinkirin aurensa.
3- Kud'ad'en kashewa domin bikin aure;
4- Tsanantawa wajen binciken laifuffukan juna;
5- Binciken matsayin dangin juna ta fuskacin wani muk'ami ko dukiya;
6- Makahon so da zai rufe idanuwan juna da zai sanya kowanne ya kasa ganin laifin d'ayan domin a lokacin suna k'ishirwar juna, amma da zaran sun kawar da wannan k'ishirwar sha'awar sai a gane laifin juna: Da man burinsa shi ne ya san ta a matsayin 'ya mace, shi kenan sai ya yi wurgi da ita.
7- zargin juna da sukan yi ko son gaskiya ne ko na k'arya tsakanin duka b'angarorin biyu na saurayi da budurwa, ta yadda d'ayansu yakan ji tsoron ko son gaskiya ko na k'arya d'ayan yake yi masa, ta yadda a nan gaba d'ayan su zai yi watse ya yi wurgi da abokin zamansa .

Saudayawa mukan ga samari da 'yan mata da yawa sun samu lalacewa sakamakon rashin yin aure da wuri, domin mutum idan ya balaga yakan zama kamar d'anyar itaciya ce da idan ba a shayar da ita ba sai ta bushe. Wannan al'amari na halitta saudayawa ya sanya wasu suka kasa kuma suka gajiya gaban sha'awarsu suka sallama mata, al'amarin da yakan janyo fasadi mai girma a cikin al'umma. Daga cikin irin wannan fasadi zamu yi k'ok'arin kawo misali da d'aya ne daga ciki da ake cewa da shi istimna'i: Istimna'i wata mummunar d'abi'a ce da takan samu samari ko 'yan mata masu tashen balaga da sukan yi amfani da jikinsu ko hannunsu ko kayansu ko wani abu domin fitar da maniyyi daga garesu.
Babbar musifar da istimna'i yake jawowa ta had'a da:
1- Rauni da rashin k'arfin jiki;
2- Raunin k'wak'walwa da kasa rik'e karatu ko kad'an;
3- Rasa gani da makancewa daga k'arshe;
4- Karkarwar jiki;
5- Rashin nutsuwa;
6- Yawan tunani;
7- Son warewa waje d'aya, shi kad'ai;

Malamai sun kawo wasu abubuwa da suke maganin wannan mummunan ciwo mai haifar da miyagun halaye da munanan d'abi'u kamar haka:
1- Nisantar duk wani abu mai kawo sha'awa, kamar kallon fila-falai da mata suke rawa ko suke sanya kayan da bai dace ba, da duk abin da ya san yana sanya shi jin sha'awa.
2- Shagaltar da kansa da wasu abubuwan, kamar tsara lokutansa, na karatu da na zuwa filin wasa, ya kuma rik'a yin wasan motsa jiki, da karanta littattafai kamar na ilimi ko jaridu, da zuwa wajan hutawa da shak'atawa domin ya samu sauk'in k'uncin ransa, da ware lokacin da zai rik'a yin yawace-yawace a lokacin da ba shi da komai, da yawan karanta kur'ani koda fatiha ce a kan hanyarsa, da zuwan wajen tarurrukan wa'azi da shirya irinsu, da yawaitar zuwa masallaci a lokacin kowace salla.
3- Sanya wa kansa ayyukan da zasu cike lokacin hutawarsa.
3- Kula da wasannin motsa jiki kamar gudu a filin wasa, da d'aga abubuwa masu nauyi da sauransu;
4- Idan akwai lokutan da ya saba aikata wannan mummunan hali a cikinsu sai ya k'irk'iro wa kansa wani abu daban da zai shagaltar da shi a irin wad'annan lokutan: kamar zuwa hawan sukuwar doki da sauransu.
5- Ya nisanci zama shi kad'ai har abada koda bacci zai yi to ya kasance cikin mutane, wato ta yadda idan ba wani abu na lalura ba kamar kama ruwa da bahaya to ba yadda za a yi ya kasance shi kad'ai.
6- Da zarar ya samu yalwa da dama to ya yi maza ya yi aure kada ya jinkirta ko kad'an.
7- Raya k'arfin ruhinsa ta hanyar jin cewa zai iya maganin wannan halin da taimakon Allah.
8- Nisantar masu irin wannan hali nasa.
9- Cin abinci mai kyau da tsara lokutan cinsa, ta yadda ba kodayaushe ne zai ci wani abu ba, da kuma wanka da ruwan sanyi a wasu lokuta, da nisantar sanya tufafi masu matse masa jiki.
10- Addu'a da neman taimakon Allah, da jin cewa Allah yana ganin sa duk inda yake koda ya shiga d'aki ya rufe ne shi kad'ai, ya ji cewa kuma Allah zai yafe masa abin da ya yi, kuma ya d'aukar wa Allah alk'awarin ba zai sake ba .
Wasu malamai sun kawo shi kamar haka:
1- Ya san cewa istimna'i yana daga zunubai da aka yi alk'awari azaba ga mai yinsa .
2- Ya san cewa mutane zasu k'yamace shi idan suka san yana yinsa .
3- Ya taimakawa kansa da yin azumi domin dawo da k'arfin iradarsa.
4- Ya shagaltu da mud'ali'ar littattafai, da nau'o'in irin wasanni kamar wasan gudu da tseran doki da sauransu.
5- Iyaye su kula da tarbiyyar 'ya'yansu tun farkon rayuwarsa, ta yanda zasu kula da dukkan halayensa domin gyara da ba shi tarbiyya ta gari.
6- Dole ne al'umma da hukuma su bayar da muhimmanci na musamman kan sha'anin aure.
7- Mai wannan halin ya duba irin bala'in da yake fad'a masa na cututtukan ruhi da na jiki, kamar cututtukan fata, rashin jin cikakken dad'in kusantar mace, rashin matsayi a al'umma saboda matsalar jijiyoyi da gajiyawar jiki, da sauransu .
Mu sani yawan duba littattafan hikima da na ilimi , da yawan tafiye-tafiye , da wasannin motsa jiki , da koyon harbe-harbe, da koyon sukuwar doki, da iyo a ruwa, suna daga cikin abubuwan da suke k'arfafa ruhin mutum , kuma suna kawo lafiyar jiki da ta ruhi da nishad'i ga rayuwar mutum, kamar yadda suna kawo farin ciki da annashuwa.

Daga cikin shawarwari da aka bayar ga mai yawan sha'awar da ta fita daga al'ada, musamman wad'anda sha'awarsu ta kai su ga lalacewa da babu wani haramun da ba zasu iya bari ba ta hanyar biyan buk'atarsu ta haram, sun had'a da:
1- Tunawa da munin wannan hali, da abin da yake haifarwa na cututtukan ruhi da jiki, da jawo wa mai wannan hali saurin tsufa da mutuwa a rayuwarsa ta duniya.
2- Karya k'arfin sha'awarsa da yawaita yin azumi, da zama da yunwa, da k'aranta cin abinci .
3- k'ok'arin ganin ya yi maganin duk wata hanya da takan iya kai shi ga jin sha'awa, kamar; tunanin abubuwan da sukan jawo masa sha'awa, da magana da mata, da kallon mata, da keb'ewa da mace, da kallon fila-filan banza da dukkan wani abu da zai iya sanya shi jin sha'awa.
4- Yin amfani da hanyoyin da zasu hana shi aikta haram da sha'awarsa kamar gaggauta yin aure da zaran ya samu dama; auren na da'imi ne ko kuma na mutu'a.
5- Tuna ni'imar da Allah yake bayar wa ga wanda ya bar sha'awarsa ya k'i aikata haramun da ita, saboda Allah.
6- Sanin cewa wannan siffa ce ta dabbobi, shi kuwa mutum ne bai kamata ba ya zama kamar dabba domin shi an halicce shi ne domin kamala.
7- Ya yi duba da tunani da lura zuwa ga ayoyin kur'ani da ruwayoyi da suka kwad'aitar da tuba, suka kuma zargi mai wannan hali .
8- Ya yawaita karatun kur'ani da karanta littattafai na ilimi na hikima, da yawaita addu'a, da jin cewa shi zai iya barin wannan hali, had'a da matakan da muka ambata a sama.

Rabi'ul Awwl 1424