Infidar Zuwa Naba

Hafiz Muhammad Sa'id   hfazah@yahoo.com

 

SURAR INFID'AR ZUWA NABA'I



سورة الإنفطار

Surar Tsagewa

Tana karantar da gaskiyar Tashin Kiyama, kuma ayyukan mutum na duniya ana tsare da su domin hisabi da sakamako.


بِِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin K'ai

إِذَا السَّمَاءُ انفَطَرَتْ

1. Idan sama ta tsage.

وَإِذَا الْكَوَاكِبُ انتَثَرَتْ

2. Kuma idan taurari suka watse.

وَإِذَا الْبِحَارُ فُجِّرَتْ

3. Kuma idan tekuna aka facce su.

وَإِذَا الْقُبُورُ بُعْثِرَتْ

4. Kuma idan kaburbura aka tone su.

عَلِمَتْ نَفْسٌ مَّا قَدَّمَتْ وَأَخَّرَتْ

5. Rai ya san abin da ya gabatar, da abin da ya jinkirtar.

يَا أَيُّهَا الْإِنسَانُ مَا غَرَّكَ بِرَبِّكَ الْكَرِيمِ

6. Ya kai mutum! Me ya ruءe ka game da Ubangijinka, Mai karimci.

الَّذِي خَلَقَكَ فَسَوَّاكَ فَعَدَلَكَ

7. Wanda Ya halitta ka sa'an nan ya daidaita ka, Ya kuma tsakaita ka.

فِي أَيِّ صُورَةٍ مَّا شَاءَ رَكَّبَكَ

8. Ya gina ka a kan kowace irin sura Ya so.

كَلَّا بَلْ تُكَذِّبُونَ بِالدِّينِ

9. A'aha, ba haka ba, kuna k'aryatawa game da sakamako!ٍ

وَإِنَّ عَلَيْكُمْ لَحَافِظِينَ

10. Lalle ne akwai matsara a kanku.

كِرَامًا كَاتِبِينَ

11. Masu daraja, marubuta.

يَعْلَمُونَ مَا تَفْعَلُونَ

12. Suna sanin abin da kuke aikatawa.

إِنَّ الْأَبْرَارَ لَفِي نَعِيمٍ

13. Lalle ne, masu d'a'a ga Allah suna cikin ni'ima.

وَإِنَّ الْفُجَّارَ لَفِي جَحِيمٍ

14. Kuma lalle ne, fajirai, suna cikin Jahim.

يَصْلَوْنَهَا يَوْمَ الدِّينِ

15. Za su shige ta a ranar sakamako.

وَمَا هُمْ عَنْهَا بِغَائِبِينَ

16. Ba za su faku daga gare ta ba.

وَمَا أَدْرَاكَ مَا يَوْمُ الدِّينِ

17. Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa ranar sakamako?

ثُمَّ مَا أَدْرَاكَ مَا يَوْمُ الدِّينِ

18. Sa'an nan, me ya sanar da kai abin da ake ce wa ranar sakamako?

يَوْمَ لَا تَمْلِكُ نَفْسٌ لِّنَفْسٍ شَيْئًا وَالْأَمْرُ يَوْمَئِذٍ لِلَّهِ

19. Rana ce da wani rai ba ya iya mallakar komai domin wani rai, al'amari a ranar nan ga Allah yake.



سورة التكوير

Surar Kisfewa

Tana karantar da Tashin kiyama gaskiya ne, kuma Kur'ani gaskiya ne, daga Allah yake, babu ragi babu kari, ya taho ta hannun aminci daga Allah zuwa ga Annabi.

بِِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin K'ai

إِذَا الشَّمْسُ كُوِّرَتْ

1. Idan aka kisfe rana.

وَإِذَا النُّجُومُ انكَدَرَتْ

2. Kuma idan taurari suka gurb'ace.

وَإِذَا الْجِبَالُ سُيِّرَتْ

3. Kuma idan duwatsu aka tafiyar da su.

وَإِذَا الْعِشَارُ عُطِّلَتْ

4. Kuma idan rak'uma masu cikkuna aka sake su wawai.

وَإِذَا الْوُحُوشُ حُشِرَتْ

5. Kuma idan dabbobin daji aka tattara su.

وَإِذَا الْبِحَارُ سُجِّرَتْ

6. Kuma idan tekuna aka mayar da su wuta.

وَإِذَا النُّفُوسُ زُوِّجَتْ

7. Kuma idan rayuka aka aurar da su (ga matattu).

وَإِذَا الْمَوْؤُودَةُ سُئِلَتْ

8. Kuma idan wadda aka turbud'e ta da rai aka tambaye ta.

بِأَيِّ ذَنبٍ قُتِلَتْ

9. Saboda wane laifi ne aka kashe ta?

وَإِذَا الصُّحُفُ نُشِرَتْ

10. Kuma idan takardun ayyuka aka watsa su.

وَإِذَا السَّمَاءُ كُشِطَتْ

11. Kuma idan sama aka fed'e ta.

وَإِذَا الْجَحِيمُ سُعِّرَتْ

12. Kuma idan Jahim aka hura ta.

وَإِذَا الْجَنَّةُ أُزْلِفَتْ

13. Kuma idan Aljanna aka kusantar da ita.

عَلِمَتْ نَفْسٌ مَّا أَحْضَرَتْ

14. Rai ya san abin da ya halartar.

فَلَا أُقْسِمُ بِالْخُنَّسِ

15. To, ba sai Na yi rantsuwa da taurari matafa ba.

الْجَوَارِ الْكُنَّسِ

16. Masu gudu suna b'uya.

وَاللَّيْلِ إِذَا عَسْعَسَ

17. Da dare idan ya bayar da baya.

وَالصُّبْحِ إِذَا تَنَفَّسَ

18. Da safiya idan ta yi lumfashi.

إِنَّهُ لَقَوْلُ رَسُولٍ كَرِيمٍ

19. Lalle ne shi (Kur'ani), maganar wani manzo ne mai girma.

ذِي قُوَّةٍ عِندَ ذِي الْعَرْشِ مَكِينٍ

20. Mai k'arfi, mai daraja a wurin Mai Al'arshi.

مُطَاعٍ ثَمَّ أَمِينٍ

21. Wanda ake yi wa d'a'a ne, amintacce a can.

وَمَا صَاحِبُكُم بِمَجْنُونٍ

22. Kuma abokinku ba mahaukaci ba ne.

وَلَقَدْ رَآهُ بِالْأُفُقِ الْمُبِينِ

23. Kuma lalle ne, ya gan shi a cikin sararin sama mabayyani.

وَمَا هُوَ عَلَى الْغَيْبِ بِضَنِينٍ

24. Kuma shi, ga gaibi ba mai rowa ba ne.

وَمَا هُوَ بِقَوْلِ شَيْطَانٍ رَجِيمٍ

25. Kuma shi ba maganar shed'ni abin la'ana, ba ce.

فَأَيْنَ تَذْهَبُونَ

26. Shin, to ina za ku tafi?

إِنْ هُوَ إِلَّا ذِكْرٌ لِّلْعَالَمِينَ

27. Lalle ne shi ba komai ba ne sai ambato ga talikai.

لِمَن شَاءَ مِنكُمْ أَن يَسْتَقِيمَ

28. Ga wanda ya so daga cikinku, ya shiryu.

وَمَا تَشَاؤُونَ إِلَّا أَن يَشَاء اللَّهُ رَبُّ الْعَالَمِينَ

29. Kuma ba zaku so ba sai idan Allah Ubangijin talikai ya yarda.



سورة عبس

Surar Had'a Fuska

Tana karantar da rashin bambanci tsakanin musulmi, rik'on addini da gaskiya shi ne d'aukaka, An ce wannan sura ta sauka ne lokaci da Abdullahi bn Maktum ya zo wajen Usman sai ya d'aure fuskarsa saboda yana makaho kuma mabuk'aci



بِِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin kai.
عَبَسَ وَتَوَلَّى

1. Ya had'a fuska kuma ya juya baya.

أَن جَاءَهُ الْأَعْمَى

2. Saboda makaho ya zo masa.

وَمَا يُدْرِيكَ لَعَلَّهُ يَزَّكَّى

3. To, me ya sanar da kai cewa watak'ila shi ne zai tsarkaka.

أَوْ يَذَّكَّرُ فَتَنفَعَهُ الذِّكْرَى

4. Ko ya tuna, sai tunawar ta amfane shi?

أَمَّا مَنِ اسْتَغْنَى

5. Amma wanda ya wadatu da dukiya.

فَأَنتَ لَهُ تَصَدَّى

6. Sa'an nan kai kuma ka bijira zuwa gare shi!

وَمَا عَلَيْكَ أَلَّا يَزَّكَّى

7. To, me zai cuce ka idan bai tsarkaka ba?

وَأَمَّا مَن جَاءَكَ يَسْعَى

8. Kuma, amma wanda ya zomaka yana gaugawa.

وَهُوَ يَخْشَى

9. Alhali shi yana jin tsoron Allah.

فَأَنتَ عَنْهُ تَلَهَّى

10. Kai kuma ka shagala ga barinsa!

كَلَّا إِنَّهَا تَذْكِرَةٌ

11. A'aha! Lalle ne, wannan tunatarwa ce.

فَمَن شَاء ذَكَرَهُ

12. Saboda wanda ya so ya tuna Shi.

فِي صُحُفٍ مُّكَرَّمَةٍ

13. A cikin littattafai ababan girmamawa.

مَّرْفُوعَةٍ مُّطَهَّرَةٍ

14. Ababan d'aukakawa, ababan tsarkakewa.

بِأَيْدِي سَفَرَةٍ

15. A hannayen mala'iku marubuta.

كِرَامٍ بَرَرَةٍ

16. Masu daraja, masu d'a'a ga Allah.

قُتِلَ الْإِنسَانُ مَا أَكْفَرَهُ

17. An la'ani mutum (kafiri), mamakin yawan kafircinsa!

مِنْ أَيِّ شَيْءٍ خَلَقَهُ

18. Daga wane abu, (Allah) Ya halitta shi?

مِن نُّطْفَةٍ خَلَقَهُ فَقَدَّرَهُ

19. Daga d'igon maniyyi, Ya halitta shi sa'an nan Ya k'addara shi.

ثُمَّ السَّبِيلَ يَسَّرَهُ

20. Sa'an nan Ya saukake masa hanyarsa.

ثُمَّ أَمَاتَهُ فَأَقْبَرَهُ

21. Sa'an nan, Ya matar da shi sai Ya sanya shi a cikin kabari.

ثُمَّ إِذَا شَاءَ أَنشَرَهُ

22. Sa'an nan, idan Ya so lalle ne zai tayar da shi.

كَلَّا لَمَّا يَقْضِ مَا أَمَرَهُ

23. Hak'ik'a bai wada aikata abin da (Allah) Ya umurce shi ba.

فَلْيَنظُرِ الْإِنسَانُ إِلَى طَعَامِهِ

24. To, mutum ya duba zuwa ga abincinsa.

أَنَّا صَبَبْنَا الْمَاءَ صَبًّا

25. Lalle ne Mu, Mun zubo ruwa, zubowa.

ثُمَّ شَقَقْنَا الْأَرْضَ شَقًّا

26. Sa'an nan, Muka tsattsage kasa tsattsagewa.

فَأَنبَتْنَا فِيهَا حَبًّا

27. Sa'an nan, Muka tsirar da k'waya ,a cikinta.

وَعِنَبًا وَقَضْبًا

28. Da inabi da ciyawa.

وَزَيْتُونًا وَنَخْلًا

29. Da zaituni da itacen dabino.

وَحَدَائِقَ غُلْبًا

30. Da lambuna, masu yawan itace.

وَفَاكِهَةً وَأَبًّا

31. Da 'ya'yan itacen marmari, da makiyaya ta dabbobi.

مَّتَاعًا لَّكُمْ وَلِأَنْعَامِكُمْ

32. Domin jin dad'i a gareku, ku da dabbobinku.

فَإِذَا جَاءَتِ الصَّاخَّةُ

33. To, idan mai tsawa (busa ta biyu) ta zo.

يَوْمَ يَفِرُّ الْمَرْءُ مِنْ أَخِيهِ

34. Ranar da mutum yake gudu daga dan'uwansa.

وَأُمِّهِ وَأَبِيهِ

35. Da uwarsa da ubansa.

وَصَاحِبَتِهِ وَبَنِيهِ

36. Da matarsa da d'iyansa.

لِكُلِّ امْرِئٍ مِّنْهُمْ يَوْمَئِذٍ شَأْنٌ يُغْنِيهِ

37. Ga kowane mutum daga cikinsu, a ranar nan akwai wani sha'ani da ya ishe shi.

وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ مُّسْفِرَةٌ

38. Wasu fuskoki, a ranar nan, masu haske ne.

ضَاحِكَةٌ مُّسْتَبْشِرَةٌ

39. Masu dariya ne, masu bushara.

وَوُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ عَلَيْهَا غَبَرَةٌ

40. Wasu fuskoki, a ranar nan, akwai k'ura a kansu.

تَرْهَقُهَا قَتَرَةٌ

41. Bak'i zai rufe su.

أُوْلَئِكَ هُمُ الْكَفَرَةُ الْفَجَرَةُ

42. Wad'annan su ne kafirai fajirai.



سورة النازعات

Surar Masu Fizga

بِِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin K'ai

وَالنَّازِعَاتِ غَرْقًا

1. Ina rantsuwa da mala'iku masu fisgar rayuka da k'arfi.

وَالنَّاشِطَاتِ نَشْطًا

2. Da masu d'aukar rayuka da sauk'i a cikin nishad'i.

وَالسَّابِحَاتِ سَبْحاً

3. Da masu sauka daga sama da umurnin Allah kamar suna iyo.

فَالسَّابِقَاتِ سَبْقًا

4. Sa'an nan, su zama masu gaugawa (da umurnin Allah) kamar suna tsere.

فَالْمُدَبِّرَاتِ أَمْرًا

5. Sa,an nan, su kasance masu shirya gudanar da umurni.

يَوْمَ تَرْجُفُ الرَّاجِفَةُ

6. Ranar da mai girgiza abubuwa (busar farko) za ta kad'a.

تَتْبَعُهَا الرَّادِفَةُ

7. Mai biyar ta (busa ta biyu) na biye.

قُلُوبٌ يَوْمَئِذٍ وَاجِفَةٌ

8. Wasu zukata, a ranar nan, masu jin tsoro ne.

أَبْصَارُهَا خَاشِعَةٌ

9. Alhali idanunsu na k'ask'antattu.

يَقُولُونَ أَئِنَّا لَمَرْدُودُونَ فِي الْحَافِرَةِ

10. Suna cewa; Ashe lalle za a iya mayar da mu a kan sawunmu?

أَئِذَا كُنَّا عِظَامًا نَّخِرَةً

11. Ashe, idan muka zama k'asusuwa rududdugaggu?

قَالُوا تِلْكَ إِذًا كَرَّةٌ خَاسِرَةٌ

12. Suka ce; Waccan kam komawa ce, tab'ab'b'iya!

فَإِنَّمَا هِيَ زَجْرَةٌ وَاحِدَةٌ

13. To, ita kam, tsawa guda kawai ce.

فَإِذَا هُم بِالسَّاهِرَةِ

14. Sai kawai ga su a bayan k'asa.

هَلْ أتَاكَ حَدِيثُ مُوسَى

15. Shin, labarin Musa ya zo maka?

إِذْ نَادَاهُ رَبُّهُ بِالْوَادِ الْمُقَدَّسِ طُوًى

16. A lokacin da Ubangijinsa Ya kiraye shi, a cikin kwari mai tsarki, wato D'uwa?

اذْهَبْ إِلَى فِرْعَوْنَ إِنَّهُ طَغَى

17. Ka tafi zuwa ga Fir'auna, lalle ne shi ya k'etare haddi.

فَقُلْ هَل لَّكَ إِلَى أَن تَزَكَّى

18. Sai ka ce masa, Ko za ka so ka tsarkaka.

وَأَهْدِيَكَ إِلَى رَبِّكَ فَتَخْشَى

19. Kuma in shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka domin ka ji tsoronSa?

فَأَرَاهُ الْآيَةَ الْكُبْرَى

20. Sai ya nuna masa ayar nan mafi girma.

فَكَذَّبَ وَعَصَى

21. Sai ya k'aryata, kuma ya sab'a.

ثُمَّ أَدْبَرَ يَسْعَى

22. Sa'an nan ya juya baya, yana tafiya da sauri.

فَحَشَرَ فَنَادَى

23. Sai ya yi gayya, sa'an nan ya yi kira.

فَقَالَ أَنَا رَبُّكُمُ الْأَعْلَى

24. Sai ya ce; Ni ne Ubangijinku mafi d'aukaka.

فَأَخَذَهُ اللَّهُ نَكَالَ الْآخِرَةِ وَالْأُولَى

25. Saboda haka Allah Ya kama shi, domin azabar maganar k'arshe da ta farko.

إِنَّ فِي ذَلِكَ لَعِبْرَةً لِّمَن يَخْشَى

26. Lalle ne, a cikin wannan hak'ik'a akwai abin kula ga wanda yake tsoron Allah.

أَأَنتُمْ أَشَدُّ خَلْقًا أَمِ السَّمَاءَ بَنَاهَا

27. Shin, ku ne mafi wuyar halitta ko sama? Allah Ya gina ta.

رَفَعَ سَمْكَهَا فَسَوَّاهَا

28. Ya d'aukaka rufinta, sa'an nan Ya daidaita ta.

وَأَغْطَشَ لَيْلَهَا وَأَخْرَجَ ضُحَاهَا

29. Kuma Ya duhuntar da darenta, kuma Ya fitar da hantsinta.

وَالْأَرْضَ بَعْدَ ذَلِكَ دَحَاهَا

30. Kuma, k'asa a bayan haka Ya mulmula ta.

أَخْرَجَ مِنْهَا مَاءَهَا وَمَرْعَاهَا

31. Ya fitar da ruwanta daga gare ta da makiyayarta.

وَالْجِبَالَ أَرْسَاهَا

32. Da duwatsu, Ya kafe su.

مَتَاعًا لَّكُمْ وَلِأَنْعَامِكُمْ

33. Domin jiyarwar dad'i a gare ku, kuma ga dabbobinku.

فَإِذَا جَاءَتِ الطَّامَّةُ الْكُبْرَى

34. To, idan uwar masifu mafi girma, ta zo.

يَوْمَ يَتَذَكَّرُ الْإِنسَانُ مَا سَعَى

35. Ranar da mutum zai yi tunanin abin da ya aikata.

وَبُرِّزَتِ الْجَحِيمُ لِمَن يَرَى

36. Kuma, a bayyana Jahim ga mai gani.

فَأَمَّا مَن طَغَى

37. To, amma wanda ya yi girman kai.

وَآثَرَ الْحَيَاةَ الدُّنْيَا

38. Kuma, ya zab'i rayuwar duniya.

فَإِنَّ الْجَحِيمَ هِيَ الْمَأْوَى

39. To, hak'ik'a Jahim ita ce makoma.

وَأَمَّا مَنْ خَافَ مَقَامَ رَبِّهِ وَنَهَى النَّفْسَ عَنِ الْهَوَى

40. Kuma, amma wanda ya ji tsoron tsayi a gaban Ubangijinsa, kuma ya kange kansa daga son rai.

فَإِنَّ الْجَنَّةَ هِيَ الْمَأْوَى

41. To, lalle ne Aljanna ita ce makoma.

يَسْأَلُونَكَ عَنِ السَّاعَةِ أَيَّانَ مُرْسَاهَا

42. Suna tambayar ka game da alk'iyama, wai yaushe ne matabbatarta?

فِيمَ أَنتَ مِن ذِكْرَاهَا

43. Me ya had'a ka da ambatonta?

إِلَى رَبِّكَ مُنتَهَاهَا

44. Zuwa ga Ubangijinka k'arshen al'amarinta yake.

إِنَّمَا أَنتَ مُنذِرُ مَن يَخْشَاهَا

45. Kai mai gargad'i kawai ne ga mai tsoronta.

كَأَنَّهُمْ يَوْمَ يَرَوْنَهَا لَمْ يَلْبَثُوا إِلَّا عَشِيَّةً أَوْ ضُحَاهَا

46. Kamar su a ranar da za su gan ta, ba su zauna ba face a lokacin marece ko hantsinta.



سورة النبإ
Surar Labari

بِِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin K'ai

عَمَّ يَتَسَاءَلُونَ

1. A kan me suke tambayar juna?

عَنِ النَّبَإِ الْعَظِيمِ

2. A kan muhimmin labari mai girma?

الَّذِي هُمْ فِيهِ مُخْتَلِفُونَ

3. Wanda suke sab'a wa juna a cikinsa?

كَلَّا سَيَعْلَمُونَ

4. A'aha! Za su sani.

ثُمَّ كَلَّا سَيَعْلَمُونَ

5. Kuma, a'aha! Za su sani.

أَلَمْ نَجْعَلِ الْأَرْضَ مِهَادًا

6. Ashe, ba Mu sanya k'asa shimfida ba?

وَالْجِبَالَ أَوْتَادًا

7. Da duwatsu turaku (ga rik'e k'asa)?

وَخَلَقْنَاكُمْ أَزْوَاجًا

8. Kuma, Mun halitta ku maza da mata?

وَجَعَلْنَا نَوْمَكُمْ سُبَاتًا

9. Kuma, Muka sanya barcinku hutawa?

وَجَعَلْنَا اللَّيْلَ لِبَاسًا

10. Kuma, Muka sanya dare (ya zama) sutura?

وَجَعَلْنَا النَّهَارَ مَعَاشًا

11. Kuma, Muka sanya lokacin rana na neman abin rayuwa?

وَبَنَيْنَا فَوْقَكُمْ سَبْعًا شِدَادًا

12. Kuma, Muka gina sammai bakwai masu k'arfi, , a samanku?

وَجَعَلْنَا سِرَاجًا وَهَّاجًا

13. Kuma, Muka sanya fitila mai tsanin haske (rana(.

وَأَنزَلْنَا مِنَ الْمُعْصِرَاتِ مَاءً ثَجَّاجًا

14. Kuma, Muka saukar ruwa mai yawan zuba daga cikakkun giragizai?

لِنُخْرِجَ بِهِ حَبًّا وَنَبَاتًا

15. Domin, Mu fitar da k'waya da tsiri da shi?

وَجَنَّاتٍ أَلْفَافًا

16. Da itacen lambuna masu lillibniya?

إِنَّ يَوْمَ الْفَصْلِ كَانَ مِيقَاتًا

17. Lalle ne, ranar rarrabewa ta kasance abin k'ayyade wa lokaci.

يَوْمَ يُنفَخُ فِي الصُّورِ فَتَأْتُونَ أَفْوَاجًا

18. Ranar da za a yi busa a cikin k'aho, sai ku zo, jama'a-jama'a.

وَفُتِحَتِ السَّمَاءُ فَكَانَتْ أَبْوَابًا

19. Kuma, aka bud'e sama, sai ta kasance k'ofofi.

وَسُيِّرَتِ الْجِبَالُ فَكَانَتْ سَرَابًا

20. Kuma, aka tafiyar da duwatsu, sai suka kasance k'ura.

إِنَّ جَهَنَّمَ كَانَتْ مِرْصَادًا

21. Lalle ne, Jahannama ta kasance madakata.

لِلْطَّاغِينَ مَآبًا

22. Makoma ce ga masu k'etare iyakoki.

لَابِثِينَ فِيهَا أَحْقَابًا

23. Suna, masu zama a cikinta, zamunna.

لَّا يَذُوقُونَ فِيهَا بَرْدًا وَلَا شَرَابًا

24. Ba su d'and'anar wani sanyi a cikinta, kuma ba su d'and'anar wani abin sha.

إِلَّا حَمِيمًا وَغَسَّاقًا

25. Sai dai tafasasshen ruwa da rub'ab'b'en jini.

جَزَاءً وِفَاقًا

26. Sakamako mai dacewa.

إِنَّهُمْ كَانُوا لَا يَرْجُونَ حِسَابًا

27. Lalle ne, su, sun kasance ba su fatar wani sauk'in hisabi.

وَكَذَّبُوا بِآيَاتِنَا كِذَّابًا

28. Kuma, suka k'aryata da ayoyinMu, k'aryatawa!

وَكُلَّ شَيْءٍ أَحْصَيْنَاهُ كِتَابًا

29. Kuma kowane abu Mun k'ididdige shi, a rubuce.

فَذُوقُوا فَلَن نَّزِيدَكُمْ إِلَّا عَذَابًا

30. Saboda haka ku d'and'ana, domin haka ba za Mu k'ara muku komai ba sai azaba.

إِنَّ لِلْمُتَّقِينَ مَفَازًا

31. Lalle ne, masu tak'awa na da wani wurin samun babban rabo.

حَدَائِقَ وَأَعْنَابًا

32. Lambuna da inabobi.

وَكَوَاعِبَ أَتْرَابًا

33. Da cikakkun 'yan mata, tsaran juna.

وَكَأْسًا دِهَاقًا

34. Da hinjalan giya cikakku.

لَّا يَسْمَعُونَ فِيهَا لَغْوًا وَلَا كِذَّابًا

35. Ba sa jin yasassar magana a cikinta, kuma ba sa jin k'aryatawa.

جَزَاءً مِّن رَّبِّكَ عَطَاءً حِسَابًا

36. Sakamako daga Ubangijinka, kyauta mai yawa.

رَبِّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا الرحْمَنِ لَا يَمْلِكُونَ مِنْهُ خِطَابًا

37. Ubangijin sammai da k'asa da abin da yake a tsakaninsu, Mai rahama, ba su da ikon yin wata magana daga gare Shi.

يَوْمَ يَقُومُ الرُّوحُ وَالْمَلَائِكَةُ صَفًّا لَّا يَتَكَلَّمُونَ إِلَّا مَنْ أَذِنَ لَهُ الرحْمَنُ وَقَالَ صَوَابًا

38. Ranar da Ruhi da mala'iku zasu tsaya a cikin sahu, ba sa magana, sai wanda Allah Ya yi masa izini, kuma ya fad'i abin da yake daidai.

ذَلِكَ الْيَوْمُ الْحَقُّ فَمَن شَاءَ اتَّخَذَ إِلَى رَبِّهِ مَآبًا

39. Wancan shi ne yini na gaskiya, to wanda ya so, ya rik'i makoma zuwa ga Ubangijinsa.

إِنَّا أَنذَرْنَاكُمْ عَذَابًا قَرِيبًا يَوْمَ يَنظُرُ الْمَرْءُ مَا قَدَّمَتْ يَدَاهُ وَيَقُولُ الْكَافِرُ يَا لَيْتَنِي كُنتُ تُرَابًا

40. Lalle ne, Mu, Mun yi muku gargad'in azaba makusanciya, ranar da mutum ke dubi zuwa ga abin da hannayensa suka aikata, kuma kafiri ya ce; Kaicona, da dai na zama turb'aya!