Hanyoyin Tafsiri

Hafiz Muhammad Sa'id Kur'ani Mai Daraja: "Allah Ya shaida cewa: Lalle ne babu abin bautawa face Shi, kuma Mala'iku da ma'abuta ilmi sun shaida, Yana tsaye da adalci, babu abin bautawa face Shi, Mabuwayi, Mai Hikima". (Surar Aali Imrana, 3: 18) .

Hanyoyin Tafsirii Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
Hakika Mu ne muka saukar da (Littafin) Kur'ani kuma Mu masu kariya ne gareshi. Hijr: 9.
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya saukar da littafi mabayyani domin ya kasance shiriya da haske ga halittun duniya, Kuma tsira da amincin Allah su tabbata ga cikamakin Annabawa da manzanni, wanda aka aiko shi ya zama mai bushara da gargadi ga talikai, shugabanmu kuma Annabinmu Muhammad Al-mustafa da alayensa masu shiryarwa kuma tsarkaka
Bayan haka, hakika bukatuwar fassara kur'ani mai girma ba ta yankewa a kowane zamani, domin kuwa zamani yana sabuntuwa domin kodayaushe yana motsawa ne yana mai tafiya ba tare da tsayawa ba, kuma sababbun maudu'ai suna sake bubbugowa da kunno kai, ga kuma girma da kima da wannan littafin yake da shi, don haka rashin samun tafsiri daga ma'abota ilimi masu fahimtar wannan littafin kamar yadda ya zo daga Allah (S.W.T) da koyarwar Ahlul-baiti (A.S) to yana nufin hana biliyoyin 'yan adam jin wannan haske da ya sauko daga ubangiji madaukaki, da hana su sanin manufar halittarsu da kuma nauyin da Allah (S.W.T) ya dora musu. Da kuma hana su sanin takamaiman hakikanin sakon da yake kunshe cikin wannan littafin kararre daga dukkanin kura-kurai kuma saukakke daga madaukaki mai baiwa, kuma mu'ujiza madawwamiya daga Allah domin kafa hujja kan bayinsa gaba daya, kuma rashin tafsirinsa kangiya ce daga sanin hadafin da yake dauke da shi na shiryarwa da haskakawa.

Tafsirin kur'ani yana iya nuna mana abubuwa kamar haka:
Nuni da fahimtar ayoyin Allah madaukaki: Ubangiji madaukaki yana fada a cikin littafinsa mai girma "Da sannu zamu nuna musu ayoyinmu a sasanni (sammai da kassai) da kuma a kawunansu, har sai ya bayyana gare su cewa shi (Ubangiji) gaskiya ne" Fusilat: 53.
Domin fassara da kur'ani mai girma akwai hanyoyi da malamai suka gabatar wadanda suka hada da:
Ta farko: Tafsirin Kur'ani da Kur'ani, wato fassara Kur'ani ta hanyar amfani da ayoyinsa;
Ta biyu: Yin tafsirin Kur'ani ta hanyar yin amfani da sunnar Annabi (S.A.W) tare da ruwayoyin da aka samo daga Imaman Ahlul-baiti (A.S.) Bisa dogaro da ruwayar nan mutawatira wacce littattafan hadisan dukkan bangarorin musulmi suke cike makil da ita, a inda Ma'aiki (S.A.W) yake cewa: Hakika ni na bar muku nauyaya guda biyu: Littafin Allah da zuriyata 'ya'yan gidana, domin lallai wadannan ababe biyu ba zasu taba rabuwa da juna ba har sai sun iske ni a tafkina (aljanna).
Wannan ruwayar ta zo cikin littafai da dama, ga kadan daga Irinsu:
1- Sahih Muslim babin falalar Ali bin Abi Talib
2- Musnad Ahmad bin Hanbal juzu'i na 4 shaft na 366
3- Sahih Tirmizi juzu'i na 13 shafi na 199 babin manakibu Ahlul-baiti (A.S)
4- Sunanul Baihaki juzu'i na 3 shafi na 148 da kuma juzu'i na 7 shafi na 30
5- Mustadrakus sahihain juzu'i na 3 shafi na 109
6- Usdul Gaba juzu'i na 2 shafi na 12
7- Hilyatul Auliya juzu'i na 1 shafi na 355
8- Tarikhu Bagdad juzu'i na 8 shafi na 442
9- Majma'uz zawa'id juzu'i na 9 shafi na 163
10-Kanzul Ummal juzu'i na 1 shafi na 48
11- (a.s)-sahawi fi mushkilil Asar juzu'i na 4 shafi na 368

Yana da kyau masu tafsirn Kur'ani da tarjama ma'anoninsa su yi amfani da yare mai sauki da zai iya isan da sakon ga dukkan samari da matasa domin ya kasance mai amfani ka kowane musulmi da yake neman sanin Kur'ani mai grima.
Wannan al'amari ya zama dole musamman da yake har yanzu a harshen hausa dukkan tafsirai da tarjamomin da aka yi ba su iya magance dukkan bukatun da al'ummar musulmi ke da su a yau ba, na daga abin da ya shafi ci gaban rayuwar zamani, saboda haka ne ma masu magana da wannan harshe ba su gushe ba suna bukatar sabon tafsiri na Kur'ani wanda zai bijiro da ilimin da zai warware muhimman abubuwan da musulmi suka isa gare shi na ci gaban rayuwa a harkoki daban daban, kamar yanda wannan, matsala ta bukatuwa ga samun sabon tafsiri na Hausa wanda ya dace da zamani ta fi shafan wadanda ba su jin yaren larabci kana ba su sanin tsofaffin kalmomin Hausa wadanda malamai magabata suka yi amfani da su a tafsirin Kur'ani da tarjamarsa .
An fara samun yunkuri da kokari daga al'ummarmu da muke fatan ya dore domin ganin an samu cigaba a tafsirin Kur'ani da tarjamarsa cikin harshe Hausa kamar yadda malamai marubuta littafin nan na "Rabi'ul Mu'uniinina fi tafsiril kitabil Mubin". Wanda suka fassara cikin harshen na Hausa da ma'anar; "Dausayin muminai cikin tafsirin littafi mabayyani". Kuma sun yi bayanin manhajar da suka bi cikin wannan tafsirin kamar haka: "Lallai mun bi hanyar fayyace ababen da suke bukatan bayani tare da bayyana mahangar Mazhabar Ahlul Bait (A.S.) na daga ababen da suka shafi: tarihi da akida, kana da tarbiyya da wanin wadannan, kamar yanda muka yi kokarin bayyana falalar surorin Kur'ani a farkon kowace sura bisa dogaro da hadisan da aka samo daga Annabi (S.A.W) da Ahlul-baiti (A.S.)".
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
May 10, 2010