Matsayin Ahlul-baiti-1

Matsayi Da Mukamin Ahlulbait (A.S)
 
Mu'assasar Al-Balagh
 
Kur'ani Mai Daraja:
"Allah Ya shaida cewa: Lalle ne babu abin bautawa face Shi, kuma Mala'iku da ma'abuta ilmi sun shaida, Yana tsaye da adalci, babu abin bautawa face Shi, Mabuwayi, Mai Hikima". (Surar Aali Imrana, 3: 18) .
 
Matsayi Da Mukamin Ahlulbait (A.S)
Manzon Allah (S.A.W) ya ce:
"Ni mai bari muku nauyaya biyu ne tare da ku, littafin Allah da dangina, mutanen idana (ahlulbaiti) wadanda in kun yi riko da su ba za ku taba bata ba a bayana har ibada, kuma lalle ne su biyun ba za su rabu da juna ba har su riske ni a bakin tafki".
Ahlulbaiti (a.s) makaranta ce mai haske kuma taurari ne a sararin samaniyar addinin Musulunci madaukaki. Su ne ja-goranci cikakke mai koyi da Manzon Allah (S.A.W), sun sha daga ilminsa a gidansa suka tashi, sannan suka rayu bisa tafarkinsa. Suna masu kira zuwa ga Littafin Allah da kuma riko da sunnar AnnabinSa (S.A.W). Suna nuna misalai madaukaka ta hanyar halayensu, suna kira zuwa ga gaskiya, ba sa karkace mata ko da kamar dan yatsa. Kamar yadda hadisin Manzon tsira ya bayyana mana su (Ahlulbaiti) tagwaye ne na Alkur'ani mai girma, ba sa rabuwa domin su ne hakikanin tamka na Alkur'ani da duk abin da yake tattare da shi na ilminsa da tarbiyyarsa. Domin haka Alkur'ani ya ambace su a sarari:
) إنَّما يُريدُ الله لِيُذْهِبَ عنْكُمُ الرِّجْسَ أهْلَ البَيْتِ ويُطهِّرَكُمْ تَطْهيراً).
"....Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen Babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa" (Surar Ahzab, 33:33)
Domin yawan ayoyin da suka sauka game da Ahlulbaiti (a.s) da kuma hadisai bayyanannu wadanda aka yi furuci da su, lallai Ahlulbaiti (a.s) sun zama abin kauna a zukatan musulmi na kasashe da zamunna daban-daban, suna kwarara zuwa gare su domin su sha daga tabkin ilminsu kuma su nemi karuwa daga hasken masaniyyarsu.
Duk wanda ya kyautata karatun tarihin Ahlulbaiti (a.s) da aikin da suka yi na ilmi, zai san rawar da suka taka, wacce ita ce ta kan gaba, zai kuma san aiki mai girma da suka yi. Lallai sun yi matukar dagewa wajen kiyaye tsarkakar shari'a da kuma tsare asalin akidar Musulunci har ma suka sadaukar da kansu da yin jihadi domin tabbatar da ka'idojin nan madaukaka a aikace da ja-gorancin al'umma bisa shiriyar wadannan ka'idojin. A kullum tarihin Ahlulbaiti (a.s) madaukaka yana bayyana a matsayin rayayyiyar baiwa wadda take da tasiri ga tunanin al'umma da kiyayewarta, tana wadatar da rayuwarta tana kuma daukaka wayewarta. Babu shakka, Ahlulbaiti (a.s) su ne kudubin al'umma, su ne rumfa matattara mai hada kan al'umma don gyara.
A cikin wannan matakaicin littafin, mun yi kokarin bayyana sashin abubuwan da rayuwar Ahlulbaiti (a.s) ya kunsa da kuma abin da ya ta'allaka da martabarsu da rawar da suka taka a tarihi. Game da gabatar da wannan littafin, muna kwadaitar da 'yan'uwa musulmi da su samu fa'idantuwa da shiryarwa ta Ahlulbaiti (a.s) da aiki da ita da komawa wajen wannan ja-gaban da kuma koyi da shi da tsayawa sahu guda don fuskantar 'yan rahoton nan masu kokarin raba kan musulmi da wargaza hadin kansu, a dai-dai lokacin da al'ummarmu ta Musulunci take shiga gumurzu mai tsanani tsakaninta da 'yan mulkin mallaka da 'yan gurguzu da yahudawan sahayoniyya, wannan gumurzun kuwa sakamako ne na tabbatar da sakon Musulunci da kuma (kokarin) rayuwa karkashin inuwar adalcin Ubangiji.
Muna kuma kira ga al'ummar musulmi da su fuskantar da dukkan karfinsu wajen kira zuwa ga Musulunci da kare tsarkakan abubuwansa da tauye damar wadanda suka saba shuka sabani da watsa gubar banga-ranci tsakanin al'ummar musulmi.
Ya ku al'ummar Annabi Muhammadu mai girma! Ya masoya Ahlulbaiti! Ya zama wajibi a gare ku da ku hada kai da kuma karfinku waje guda, domin kuwa wannan al'umma, al'umma ce guda, kuma daukakarku da kara-marku ba sa tabbata sai da riko da sakon Musulunci da kuma aiki da Littafin Allah da Sunnar AnnabinSa (S.A.W).
"Kuma ka ce: ku yi aiki, sa'an nan Allah Zai ga aikinku da ManzonSa da kuma muminai". (Surar Tauba, 9:105)

Ahlulbaiti (A.S) suna ne mai haskakawa, kuma daukaka ce madawwamiya, sannan suna ne da yake abin kauna ne ga duk rai mai kaunar Manzon Allah (S.A.W) kuma ya yi imani da shi, kuma yake rayuwa bisa shiriyarsa (S.A.W). Hakika musulmi sun san wannan madaukakin suna cikin tarihi da kuma cikin martabar nan da take rataye da Alkur'ani mai girma, tun lokacin da Alkur'anin ya yi furuci da wannan sunan mai albarka, kuma ya sanyawa wannan tauraruwan (Ahlulbaiti) lakabin da babu irinsa a duniyar dan Adam:
( إنَّما يُريدُ الله لِيُذْهِبَ عنْكُمُ الرِّجْسَ أهْلَ البَيْتِ ويُطهِّرَكُمْ تَطْهيراً ).
"....Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa" (Surar Ahzab, 33:33) Da saukar wannan aya mai albarka wani tafarki ya ayyana a matsayin wani abin dogaro da mafuskanta a rayuwar Musulunci. Alkur'ani ya juya fuskoki zuwa ga wannan tafarki tare da tabbatar da dukkan haske a bisa wannan a kan gaba wajen ja-goranci. Har ila yau ya bayyana rawar da Ahlulbaiti (a.s) za su taka a rayuwar al'ummar musulmi, ya kuma kebance su da nufin tsarkakewa, abin karfafawa daga Gwani, Masani.
Lalle wannan aukuwa mai girma tana da wata kebantacciyar ma'ana a rayuwar al'umma da gina tarihinta da wayewarta. Wannan ma'ana kuwa dukkan masu bincike da tahkikin Musulunci da kuma fagen rayuwar siyasar wannan al'umma sun san da ita.
Hakika wadannan ayoyin sun ayyana wata cibiyar harkar tarihi bayan Manzon Allah (S.A.W), harkar da ta dace da al'ada da tsarin hujjar da Musulunci ke dogara da shi. Wannan ya biyo bayan baiwar da Allah Ya yi wa tatattun nan masu albarka (Ahlulbaiti), baiwa ta tsarka-kewa daga zunubai da sabo da kuma laifi. Hakika Alkur'ani mai girma ya tabbatar musu da mafificiyar darajar falala da kuma mafi girman martabobin cancanta, da'a da shugabanci a rayuwa ta Musulunci wacce falsafarta a rayuwa ita ce: "Lalle mafificinku daraja a wurin Allah shi ne wanda yake mafificinku a takawa". (Surar Hujurat, 349:13
Babu shakka duk wanda ya bibiyi Alkur'ani mai girma da sunnar Annabi (S.A.W)
tsarkakkiya zai samu cewa mutanen gidan Annabi mai daraja (S.A.W) suna da matsayi kebantacce da muhalli mabayyani. Za a ga cewa shugabannin wannan al'umma da malamanta da masu fassara da masu ruwaya da ma'abuta tarihi da malaman fikihu da masu yawan ibada duk suna ba da labarin wannan matsayi na Ahlulbaiti (a.s) ta dukkan fuskoki da hanyoyi. Lallai littattafan hadisi, tarihi, tafsiri da na adabi da wake da darajoji wadanda musulmi daga mazhabobi da hanyoyin ilmi daban-daban suka wallafa, sun bayyana kebantaccen matsayin da muhalli muhimmi na Ahlulbaiti (a.s). Wadannan littattafai suna magana a kan daukakar wannan itaciya
mai albarka. Ana auna imanin mumini ne da kaunar Annabi (S.A.W) da Ahlubaitinsa da rige-rigen sanar da al'umma darajojin Alayen Manzo masu daraja da nutsar da kaunarsu cikin rayuka, da bayyana gajin hakuri da jin ciwon halayyar wadanda suka yi gaba da mutanen gidan Annabi mai daraja, kuma suka cutar da su da ababen kunya da kuma bala'u.
Lallai mutanen wannan gida tamkar tauraruwa ce wacce babu kamarta, domin ilmin da suke dauke da shi da kuma takawa da halayen kwarai da darajoji madau-kaka da kare Musulunci da ilminsu da kuma daukar takobi da yaki da zalunci da keta haddi. Domin haka ne musulmi suka dace a kan cewa babu wani daga cikin wannan al'ummar da ya mallaki mukami da daukaka da daraja irin wanda Allah Ya kebance Ahlulbaiti da su…su kadai Allah Ya kebance da tsarkakewa daga dauda da zunubi: "...Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa" Kuma su kadai ne Allah Ya kebance da wajabta kaunarsu a kan wannan al'ummar Ya kuma sanya kaunar ta su wani hakki na Annabi (S.A.W) a kan al'umma: Ka ce: "Ban tambayar ku wata lada a kansa, face dai soyayya ga makusanta....". (Surar Shura, 42:23)
Kuma su kadai ne Allah Madaukakin Sarki Ya wajabta yi musu salati a cikin salloli biyar, Yana gwama ambatonsu da ambaton ManzonSa (S.A.W): "Lalle Allah da Mala'ikunSa suna yin salati wa Annabi, Ya ku wadanda suka yi imani! Ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama domin amintarwa a gare shi". (Surar Ahzab, 33:56) Manzon Allah (S.A.W) ya riga ya koyawa al'um-marsa yadda za ta yi salati a gare shi da alayensa yayin da suka tambaye shi: Ya ya za mu yi salati a gare ka Ya Rasulallah? Sai ya ce da su: "Ku ce: Ya Allah! Ka yi salati ga Muhammadu da Alayen Muhammadu kamar yadda Ka yi salati ga Ibrahim da Alayen Ibrahim, lallai Kai ne Abin godiya, Mai girma" To babu wanda yake da wadannan darajoji da siffofi cikin wanna al'umma face su.
Wannan shi ya sanar da mu daukakar Ahlulbaiti (a.s) da matsayinsu, da wajibcin kaunarsu da koyi da su da kuma tafiya bisa turbarsu. Ba don kome ne Alkur'ani ya jaddada a kan mutanen wannan gida, ya kuma bayyana matsayi da mukaminsu ba, sai domin a yi koyi da su bayan Manzon Allah (S.A.W) da kuma riko da sonsu da karbar (dukkan ilmi da shiriya) daga gare su.
Babu abin da yasa Alkur'ani ya sanar mana da Ahlulbaiti (a.s) ta hanyar da ya nuna mana su face domin wasu dalilai na akida da abin da ya danganci sakon Musulunci kaco-kam, dalilan da suke sa dukkan wani musulmi ya dora tunani mai zurfi da lura da kuma kokarin riskar da kwakwalwarsa hakikanin wannan jama'a (Ahlulbaiti) da take a kan gaba wajen karbar sako. Wannan jama'a kuwa ita ce Allah Ya yi wa baiwar matsayi na shugabanci a cikin al'umma, bayan Alkur'ani da Manzo (S.A.W) sun yi masu wannan gabatarwa. A nan gaba za mu bijiro da gabatarwar da Alkur'ani mai girma da Sunna mai tsarki da shuwagabannin musulmi da malamansu da masu adabi suka yi wa wannan itaciya mai albarka, zuriyar mai tsarki, wacce ita ce madugun al'umma.
Ahlulbait (a.s) Cikin Alkur'ani Mai Girma Alkur'ani mai girma shi ne tushen dukkan tunani, shi ne mabubbugar shari'a da ka'idoji. Duk abin da Alkur'-ani ya zo da shi wahayi ne abin saukarwa, kuma magana ce tsarkakkiya daga Allah, yana furuci da tsarin rayuwa yana kuma ayyana dokokin rayuwar. Duk wani musulmi ya san cewa abin da Alkur'ani ya zo da shi shi ne shari'a da sakon da zai bi a rayuwarsa, sannan kuma an wajabta masa aiki da shi da yin tafiya bisa shiriyarsa. Abin lura kuma shi ne Alkur'anin nan ya yi magana a kan Ahlulbaiti (a.s) da yanayi da tsari kamar haka:
Amfani da sunansu na isdilahi wanda shi Alkur'-anin ya sanya musu. Wani lokaci yakan ambace su da Ahlulbaiti kamar yadda ya zo cikin Ayar Tsarkakewa, wani lokaci kuma yana ambatonsu da al-Kurba kamar yadda ya zo cikin ayat al-Muwadda
(ayar kauna). Ayoyi masu yawa sun sauka da wadannan ma'anoni sannan Sunna ta yi bayaninsu ga al'umma a lokacin da ayoyin suke sauka daga bisani kuma masu fassara da masu ruwaya suka nakalto bayanin cikin littattafansu manya da kanana.
Kiyaye da kuma rubuta dukkan ababen da suka kebanta ga Ahlulbaiti (a.s) bugu da kari kan saukan ayoyi da dama da suke ambaton falalar Ahlulbaiti (a.s), matsayinsu, yabo da fuskantar da al'umma zuwa gare su; wani zubin a ambaci darajojin a hade, kamar yadda ya zo cikin Ayar Mubahala (Surar Ali Imrana, 3: 61) da Ayar Ciyarwa cikin Surar Dahri da sauransu. Wani zubin kuwa a rarrabe kamar yadda ya zo cikin Ayar Wilaya (Surar Ma'ida, 5: 55).
Bari mu bijiro da sashen wadannan ayoyi - suna kuwa da yawa - wadanda suka yi magana a kan Ahlulbaiti (a.s), domin bayani a kan falalarsu da matsayinsu, gami da kuma sharhi: Ta Farko:Ayar Tsarkakewa :
(إنَّما يُريدُ الله لِيُذْهِبَعنْكُمُ الرِّجْسَ أهْلَ البَيْتِ ويُطهِّرَكُمْ تَطْهيراً )
"...Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa". (Surar Ahzabi, 33:33)
Hakika tafsirai da ruwayoyi sun hadu a kan cewa abin da ake nufi da Ahlulbaiti shi ne mutanen gidan Annabi (S.A.W) wadanda kuma su ne, Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (A.S). Bayani ya zo cikin littafin Durrul Mansur na Imam As-Suyudi cewa: (Al-Dabarani ya fitar da hadisi daga Ummu Salma cewa Manzon Allah (S.A.W) ya ce da Nana Fadimatu cewa: "Taho min da mijinki da 'ya'yansa biyu", sai ta taho da su sai Manzon Allah (S.A.W) ya lullube su da wani mayafi, sa'an nan ya sanya hannunsa bisansu ya ce: "Ya Allah! Wadannan su ne Ahlulbaitin Muhammadu (a wani lafazin zuriyar Muhammadu) to Ka sanya tsirarKa da albarkarKa wa zuriyar Muhammadu kamar yadda Ka sanya wa zuriyar Ibrahima, lalle Kai ne Abin godiya, Mai girma".
Sai Ummu Salma ta ce: "Sai na daga mayafin domin in shiga in kasance tare da su, sai Annabi (S.A.W) ya janye shi daga hannuna ya ce: "Lallai ke kina tare da wani alheri "( ).
An ruwaito hadisi daga Ummu Salma, matar Annabi (S.A.W) cewa, Manzon Allah (S.A.W) ya kasance a dakinta bisa wurin kwanciyarsa yana rufe da wani mayafi sakar haibara, sai Fadima ta zo da wata tukunya da abinci a cikinta. Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "Ki kira mijinki da 'ya'yansa Hasan da Husaini". Sai ta kira su. Yayin da suke cin abincin sai aya ta sauko wa Manzon Allah (S.A.W) cewa: "…Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkake-ku tsarkakewa" Sai Annabi (S.A.W) ya kama gefen ragowar sashen mayafinsa ya rufe su da shi, sannan ya fitar da hannunsa daga mayafin ya nuna sama ya ce: "Ya Allah! Wadannan su ne mutanen gidana, make-bantana, to Ka tafiyar da kazamta daga gare su kuma Ka tsarkake su, tsarkakewa".
Ya fadi hakan har sau uku. Ummu Salma ta ce: "sai na shigar da kaina cikin mayafin na ce: "Ina tare da ku Ya Manzon Allah? Sai ya ce: "ke kina tare da wani alheri", ya fadi hakan har sau biyu ( ).
Manzon Allah (S.A.W) ya ci gaba da bayyana wa al'ummarsa ma'anar wannan aya mai girma, yana tsarkake fahimtarta ga wannan aya domin al'umma ta haskaka da ita ta kuma rayu a kan shiryuwarta. An ruwaito shi yana cewa:
"Wannan aya ta sauka ne a kan mutane biyar: Ni kaina, Aliyu, Faxima, Hasan da Husaini…."…Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa ( )".
Kamar yadda kuma aka ruwaito daga Ummul Muminina A'isha, tafsirin ayar da bayanin mutanen da ake nufi a ciki, kamar haka: (Manzon Allah (S.A.W) ya fito wata safiya yana sanye da wani mayafi mai zane, wanda aka yi da bakin gashi, sai Hasan dan Ali ya zo, sai Manzon Allah (S.A.W) ya shigar da shi (cikin mayafin), sannan sai Husaini ya zo, ya shigar da shi, sannan Ali ya zo ya shigar da shi, sa'an nan sai ya ce:
A wata ruwayar kuma, Manzon Allah (S.A.W) ya kasance yana wucewa ta kofar Fadima (A.S) yayin da ya fito sallar asuba yana cewa:
"Salla! Ya mutanen babban gida (Ahlulbaiti), salla! "Allah Na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa "( ).
Hakan nan Alkur'ani yake magana a kan Ahlulbaiti (a.s) yana iyakance mutanen da suke ciki, tsarkaka manisanta daga dukkan dauda da sabo da zunubi da kuma son zuciya. Saboda haka halayen su abin koyi ne haka nan su kansu. Alkur'ani bai sanar mana da su irin wannan sanarwa ba, sai domin ya jaddada matsayi da mukaminsu ga al'umma, ya kuma ja hankulanmu zuwa ga koyi da su da komawa gare su domin fahimtar shari'a da karbar hukumce-hukumcenta daga wurinsu. Ta wannan hanyar, Alkur'ani ya ayyana mana mizani na aikace (wato ayyukan Ahlulbaiti) da ma'aunin da za mu koma gare shi yayin da ra'ayoyi suka sassaba, aka kuma sami bambancin fahimta da I'itikadi (wato abin da mutum ya yarda da shi).
Wannan kuwa a sarari yake idan muka duba yadda Alkur'ani ya jaddada cikin ayoyi da yawa ya kuma bijiro da Ahlulbaiti (a.s) a matsayin ja-gorori ga al'umman musulmi bayan Manzon Allah (S.A.W).
Dogewar da Manzon Allah (S.A.W) ya yi, wata da watanni bisa tsayuwa a bakin kofar Aliyu da Fadima (A.S) yana kiransu da asuba zuwa salla, yana kiransu da Ahlulbaiti ba kome ba ne face sanar da al'umma mutanen da ake nufi da Ahlulbaiti, kana kuma yana fassara wa musulmi ayar tsarkakewa, yana sanar da su matsayin Ahlulbaiti (a.s) tare da jan hankulansu zuwa gare su da kuma wajabta musu kaunarsu da yi musu biyayya da jibinta al'amari gare su. Dabarani ya ruwaito daga Abu Hamra' cewa:
"Na ga Manzon Allah (S.A.W) yana zuwa kofar Aliyu da Fadima tsawon wata shida yana cewa: "Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa( )".
Fakhru al-Razi ya ambata a cikin tafsirinsa, Tafsir al Kabir, cewa bayan saukar ayar: "Kuma ka umurci iyalanka da salla, kuma ka yi hakuri a kanta", (Surar Daha, 20: 132), Manzon Allah (S.A.W) ya kan je (kofar) Aliyu da Fadima kowace safiya yana mai cewa: (lokacin) salla (ya yi), ya aikata hakan har na tsawon watanni.
Sannan kuma ya kawo hadisin Hammad bn Salma, daga Aliyu bn Zaid daga Anas cewa: "Annabi (S.A.W) ya kasance yana wucewa ta dakin Fadima koyaushe ya fito zuwa ga salla har na tsawon wata shida, yana mai cewa: "Salla! Ahlulbaiti! "Allah Na
nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa( )".
A cikin wannan akwai bayani da kuma nuni zuwa ga muhimmancin da Manzon Allah (S.A.W) ya riki Ahlulbaiti (a.s) da shi, da kuma karfafawarsa wa musulmi cewa su (Aliyu, Fadima da 'ya'yansu) su ne mutanen gidansa (Ahlulbaiti), wadanda Allah Ya tafiyar da dukkan dauda ga barinsu, Ya kuma tsarkake su tsarkakewa. Wannan muhimmancin an nuna shi ne bayan Allah Ya yi magana da ManzonSa cewa: "Kuma ka umurci iyalanka da salla, kuma ka yi hakuri a kanta".
Sannan a sarari yake cewa daga abin da ayar: "Allah Na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa", take nuni da shi da kuma amfani da lafazin maza ba lafazin mata ba da aka yi, wato (عنكم) da kuma (يطهِّركم), akwai nuni zuwa ga wadanda ake nufi, su ne wadannan mutane biyar din. Bayani ya zo a cikin Tafsirai cewa da Allah Yana nufin matan Annabi (s.a.w.) ne da Yayi amfani da kalmar (عنكنّ) da ta (يطهِّركنّ) da magana irin wacce ake yi wa mata.
A baya mun riga da mun ga Hadisin Mayafi lokacin da aka saukar da wannan aya ta tsarkakewa yayin da Ummu Salama taso shiga cikin wannan mayafi amma Manzon Allah (S.A.W) ya ce mata ke dai kina a matsayinka, kuma kina a kan alheri.
Hakan yana nuna mana rashin shigar matayen Annabi (S.A.W) cikin wannan aya ta tsarkakewa, kana kuma babu daya daga cikinsu da ta yi ikirarin saukar wannan aya a kansu, duk kuwa da cewa ayar ta falaloli da kuma matsayi mai girma ce. Wannan ayar ta fitar da wata hanya wacce abin da take nuni da shi da abin da ta tattara suna da yalwar gaske. Tana jan hankulanmu zuwa ga batutuwa na asasi a rayuwar Musulunci domin kada mu sami rikitarwar fahimta balle ma manufofin Littafin Allah na gaskiya su tawaya. Allah Ya yi nufin gina al'umma bisa ginshikin tsarki da nisantar dauda da abin kunya sai Ya sanya Ahlulbaiti (a.s) a matsayin wani tushe abin dogara da kuma haske mai haskakawa. Lalle babu wani mutum da Alkur'ani mai girma ya siffanta shi da wannan siffa daga cikin musulmi, babu kuma wanda Manzon Allah (S.A.W) ya siffanta shi da wannan siffar (siffar tsarki maras iyaka) face Ahlulbaiti (a.s).
Ta Biyu: Ayar Soyayya
(قُلْ لا أَسْألُكُم عَلَيْهِ أجْراً إلاّ المَوَدَّةَ في القُربى ومنْ يَقْتَرِفْ حسنةَ نزِدْ لهُ فيهَا حسْنًا إنّالله غفورٌ شَكُور)
"Ka ce: "Ba ni tambayar ku wani lada a kansa face dai soyayya ga makusanta. Kuma wanda ya aikata wani abu mai kyau, za Mu kara masa kyau a cikinsa, lallae Allah Mai gafara ne, Mai godiya". (Surar Shura, 42:23)
Hakika Manzon Allah (S.A.W) ya bayyana ko wane ne ake nufi da wannan aya mai albarka, kuma ko su waye kaunarsu da biyayya gare su da rayuwa bisa tafarkinsu ya wajabta ga musulmi. Malaman tafsiri da hadisi da tarihi sun ruwaito cewa Makusantar Annabi" wadanda ake nufi a wannan ayar su ne Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (A.S).
Zamakhshari ya fada a cikin tafsirinsa al-Kashshaf cewa: "An ruwaito cewa mushrikai sun taru a wurin taronsu sai sashinsu ya ce wa sashi: "shin kuna ganin Muhammadu zai nemi wani lada a kan abin da yake kira gare shi? Sai aya ta sauka cewa: "Ka ce: "Ba ni tambaya ku wani lada a kansa face dai soyayya ga makusanta( )".
Sai Zamakhshari ya ce: "Kuma an ruwaito cewa yayin da wannan aya ta sauka sahabbai sun tambayi Manzon Allah (S.A.W) cewa: "Ya Manzon Allah su waye danginka wadanda sonsu ya wajabta a kanmu". Sai ya ce: "Aliyu da Fadima da 'ya'yansu biyu".
A cikin Musnad na Imam Ahmad bin Hambal - da isnadinsa ambatacce -, daga Sa'id bn Jubair daga Ibn Abbas (r.a.) ya ce: "Yayin da zance Allah Ta'ala cewa: "Ka ce: "Ba ni tambayar ku wani lada a kansa face dai soyayya ga makusanta", ya sauka, sai mutane suka tambayi Manzon Allah (S.A.W) cewa: "Ya Rasulallah! Su waye danginka wadanda sonsu ya wajaba a kanmu? Sai ya ce: "Aliyu da Fadima da 'yayansu biyu( )".
Fakhrurrazi ya tabbatar da wannan zancen cikin Tafsirul Kabir bayan ya ambaci maganar Zamakhshari dangane da Alu Muhammad (dangin Muhammadu). Ga abin da yake cewa: "Ni ina cewa dangin Muhammadu su ne wadanda al'amuransu suke tare da na shi (Annabi), to kuma duk wadanda kusancinsu yafi kusa da shi da kuma cika, to su ne aalu (dangin Annabi). Babu shakka cewa Fadima da Ali da Hasan da Husaini suna da mafi tsananin alaka da Manzon Allah (S.A.W), wannan kuwa an nakalto ta hanyoyi daban. A saboda haka ya wajaba su kasance su ne Aalu". Har ila yau an sassaba a kan ma'anar aalu, wasu sun ce su ne danginsa, wasu kuma sun ce su ne al'ummarsa. To idan mun dauke shi da ma'anar dangi, to su din dai su ne aalu din, idan kuma muka dauke shi da ma'anar al'umma( )wadanda suka karbi kiransa to nan ma dai su ne aalu din. Don haka a bisa dukkan yanayi dai su aalu din ne dai.
To amma shigar waninsu cikin kalmar aal, a nan kan an samu sabani kan hakan. Marubucin al-Kashshaf ya ruwaito cewa yayin da wannan aya ta sauka, mutane sun ce: "Ya Manzon Allah su waye danginka wadanda kaunarsu ta wajaba a kanmu? Sai ya ce: "Aliyu, Fadima da 'ya'yansu biyu", sai ya tabbatar da cewa wadannan hudun su ne dangin Annabi (S.A.W), to idan kuwa hakan ya tabbata to ya wajaba su zama abin kebancewa da karin girmamawa. Ana iya tabbatar da hakan ta fuskoki kamar haka:
Fadin Allah (S.W.T) cewa: "face dai soyayya ga makusanta", kuma fuskar kafa hujja da ayar ya gabata.
Babu shakka cewa Annabi (S.A.W) ya kasance yana kaunar Fadima. An ruwaito shi yana cewa: "Fadima yanki ne daga gare ni, abin da yake cutar da ita yana cutar da ni ". Kamar yadda ingantaccen hadisi ya tabbatar cewa Annabi Muhammadu (S.A.W) ya kasance yana kaunar Aliyu, Hasan da Husaini (A.S). To idan wannan ya tabbata, lallai kaunarsu ta zama wajibi a kan dukkan al'umma domin fadin Allah (S.W.T.) cewa: "Ka ce: Idan kun kasance kuna son Allah, to ku bi ni, Allah Ya so ku...". (Surar Ali Imrana, 3:31)
"...ku bi shi, don ku shiryu". (Surar A'arafi, 7: 158)
Da kuma fadinSa cewa: "...to, wadanda suke sabawa umurninSa, su kiyayi abkuwar wata fitina....". (Surar Nur, 24: 63)
"Lalle abin koyi mai kyau ya kasance gare ku daga Manzon Allah...." (Surar Ahzabi, 33: 21)
Addu'a ga dangin Manzo tana da wani matsayi mai girma, domin haka ne aka sanya wannan addu'ar ta zama cikamakin tahiya a cikin salla, wato: "Ya Allah! Ka yi tsira ga Muhammadu da Alayen Muhammadu, kuma Ka yi jin kai ga Muhammadu da Alayen Muhammadu"( ). Ba a samun wannan girmamawa ga wani wanda ba su dangin ba. To duk wannan yana nuni da cewa kaunar alayen Muhammadu wajiba ce. Imam Shafi'i yana cewa:
Ya kai mahayi tsaya a wannan kwari na Mina,
Ka kira mazaunin al-Nahidhi.
Da daddare yayin da alhazai suka wuce zuwa Mina,
Tamkar kogin Furatu mai yalwa da yawan ruwa.
Idan Rafdhu(1) shi ne son Zuriyar Muhammadu,
To mutane da aljannu su shaida ni Rafidhi ne( ).
Ibn Munzir da ibn Abi Hatam da ibn Mardawihi da Dabarani cikin Mu'ujamul Kabir daga Ibn Abbas sun ce: "Yayin da ayar: "Ka ce: "Ba ni tambayar ku wani lada a kansa face dai soyayya ga makusanta", ta sauka sai mutane suka ce: "Ya Manzon Allah su wane ne makusantanka wadanda kaunarsu ta wajaba a kanmu? Sai ya ce: "Aliyu da Fadima da 'ya'yansu biyu ( )".
A cikin Mu'ujam din dai ya inganta daga Imam Hasan dan Ali (A.S) cewa wata rana yayin da yake huduba wa mutane ya ce: "Ni ina daga cikin Ahlulbaitin da Allah Ya farlanta kaunarsu a kan kowane musulmi, inda Ya ce: "Ka ce: "Ba ni tambayar ku wani lada a kansa face dai soyayya ga makusanta".
(Ibn Abi Hatam ya fitar daga Ibn Abbas cewa: (lokacin da aka karanta wannan aya): (….ومن يقترفْ حسنة) "…kuma wanda ya aikata wani abu mai kyau…) (Surar Shura, 42: 23), sai ya ce: "(hakan) shi ne kaunar Ahlulbaiti ( )".
Alkur'ani mai girma ya tabbatar da tsarkin Ahlulbaiti (a.s) da ayar tsarkakewa
kuma ya fahimtar da al'umma matsayinsu da rawar da suka taka dangane da daukaka sakon Musulunci a cikin rayuwar al'umma. Da wannan ne kuma suka cancanci soyayya da riko zuciya daya wanda Alkur'ani ya yi umurni da shi a wannan ayar.
Abin da Alkur'ani yake nufi da wannan soyayya ba wai bege da doki da soyayya ta zuci kawai ba ne, domin babu wata fa'ida ga soyayya da kaunar da take cikin rai da zuciya, amma ba ta da wata bayyana a waje (a fili). Lallai tabbatar kauna da soyayya ga makusantan Manzon Allah (S.A.W) yana samuwa wajen koyi da su da kuma rayuwa bisa turbarsu da lizimtar mazhabarsu da abin da ya fito daga gare su, da kuma daukar matsayinsu a al'umma matsayin shugaba kuma ja-gora.
Yayin da Alkur'ani yake sanya wannan ayar a bisa harshen Manzon Allah (S.A.W) kuma Yake umurtansa da cewa ya sanar da al'ummarsa da mutane bai daya cewa ba ya nufin samun wani lada ko sakayya daga gare su domin isar da sako da jure wahalhalun kira zuwa ga Allah da kuma shiryar da su, face soyayya ga makusantansa (S.A.W) da tsarkake zuciya gare su da rayuwa bisa tafarkinsu, abin da kurum Alkur'ani yake
nufi shi ne kiyaye tafarkin al'umma da tsare hanyarta ta akida da shari'a, domin al'umma ta fuskanci Ahlulbaiti bayan da Alkur'ani ya fuskantar da ita zuwa gare su.
Ba don lamuncewar da ake samu daga Ahlulbaiti (a.s) ba, da kuma ikon ja-gorancin al'umma a kan hanyar shiriya da lamunce hakan ba, da Alkur'ani bai saukar da soyayyar ba, kuma da ba a umurci Manzon Allah (S.A.W) da ya sanya hakkinsa (ladansa) a kan al'umma shi ne kaunar Ahlulbaiti (a.s) ba.
Wannan tarin bayanai da muka kawo na maganganun malaman tafsiri da hadisi sun nakalto mana fassarar da Manzon Allah (S.A.W) ya yi wa wannan aya mai albarka, da sanya kaunar Ahlulbaiti (a.s) cikin zukata kuma ya sanya kaunar ta hakika ce mai tabbata cikin zuciyar ko wane musulmi, tana bayyana a cikin halayensa, tunaninsa da kuma begensa. Soyayyar nan tana kuma ayyana matsayarsa a kan Ahlulbaiti (a.s) da makiyansu da masoyansu da kuma bin tafarki da kuma abin da ya tabbata daga gare su na hadisi, fikihu, tafsiri, tunani, akida, shari'a da kuma tsarin aiki na jagoranci da siyasa.
Wannan lambar girma da daukaka tana da manufa da abin da take nuni da shi a kebance, wanda ya kamata musulmi su kiyaye shi kuma su riski zurfinsa.