Muassasar alhasanain (a.s)

Makalolin Halaye

Hakkokin Sauran Mutane

Hakkokin Sauran Mutane

Amma hakkin mai bin ka bashi da yake neman ka biya, to idan kana da yalwa sai ka ba shi, ka isar masa da ita ka wadata shi, kada ka hana shi ka yi taurin bashi. Domn Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Taurin bashin mawadaci zalunci ne". Idan ka

Bayanai

Hakkokin Makusanta

Hakkokin Makusanta "Kuma hakkin wacce kake kula da ita da mallakar aure shi ne ka san cewa Allah ya sanya ta mazauni, wurin hutu, wurin nutsuwa gareka, da kariya, kuma haka nan ya wajabta wa kowannenku gode w

Bayanai

Hakkokin Al'umma

Hakkokin Al'umma "Amma hakkin jama'ar da kake jagoranta shi ne ka sani cewa sun zama jama'arka ce saboda karfinka a kansu, kuma ba komai ba ne ya sanya ka mahallin matsayin mai kula da su sai rauninsu da kaskantuwarsu. Babu wani abu da ya cancanci wanda rauninsa da kaskancinsa ya mayar da shi jama'arka,

Bayanai

Hakkokin Jagorori

Hakkokin Jagorori "Amma hakkin jagora shi ne ka san cewa shi jarrabawa ce gareka, kuma shi abin jarrabawa ne game da kai saboda abin da aka sanya a hannunsa a kanka na iko, kuma ka tsarkake masa nasiha, kada ka yi gogayya da shi, ka ga ke nan ka sanya shi ya sanya hannunsa a kanka sai ka kasance dalilin halakarka da halakarsa.

Bayanai

Hakkin Dan'uwa

Hakkin Dan'uwa "Kuma hakkin dan'uwanka shi ne ka sani cewa shi ne hannunka da kake shimfidawa, kuma bayanka da ake jingina da shi, kuma daukakarka da kake dogaro da ita, kuma karfinka da kake ijewa da shi, don haka kada ka rike shi makami a kan sabon Allah, ko ka sanya shi tanadi domin zaluntar halittar Allah, kuma kada ka bar taimakonsa,

Bayanai

Hakkin Da

Hakkin Da "Kuma hakkin danka shi ne ka san cewa shi daga gareka yake kuma abin rabawa zuwa gareka a wannan duniya da alheirnsa da sharrinsa, kuma kai abin tambaya ne kan abin da ka koya masa na kyakkyawan ladabi da shiryarwa ga ubangijinsa mai girma da buwaya, da kuma taimaka masa kan biyayyarsa, sai ka yi aiki cikin umarninsa da aikin wanda ya san za a saka masa da kyautata masa, wanda kuma za a yi wa azaba kan musguna masa".

Bayanai

Hakkin Uba

Hakkin Uba "Kuma hakkin babanka ka sani shi ne asalinka kuma ba don shi ba, da babu kai, kuma duk wani abu da kake gani gareka da yake kayatar da kai, to ka sani babanka ne mafarin wannan ni'imar gareka, sai ka gode wa Allah, ka gode masa gwargwadon wannan. Babu karfi sai da Allah".

Bayanai

Hakkin Uwa

Hakkin Uwa "Ka sani hakkin babarka cewa; Ta dauki cikinka a inda babu wani mutum mai iya daukar wani, ta ciyar da kai daga cikin zuciyarta da abin da babu wani mutum mai ciyar da irinsa ga wani, ta zama lokacinka da jinta da ganinta, hannunta da kafarta, gashinta da fuskarta, da dukkan gabobinta, tana mai murna da farin ciki.

Bayanai

Hakkin Bawa

Hakkin Bawa "Kuma hakkin wanda kake mallaka shi ne ka sani cewa shi halittar ubangijinka ne, kuma dan uwanka ne na uba da uwa, kuma tsokarka da jininka ne, ba ka mallake shi ba domin kai ne ka halicce shi ba Allah ba!, kuma ba ka halicci wani abu na daga gabobinsa ba, ba ka fitar masa da wani arziki ba.

Bayanai

Hakkin Jama'ar Kasa Na Ilimi

Hakkin Jama'ar Kasa Na Ilimi Amma hakkin jama'arka na ilimi shi ne; Ka san cewa Allah ya sanya ka mai kula da taskar abin da ya ba ka na ilimi, kuma ya jibinta maka shi na kula da taskar hikima, to idan ka kyautata cikin abin da ya ba na wannan kuma ka tsaya da shi a matsayin mai yi musu jiransa mai tausayi da nasiha irin na ubangida ga bawansa,

Bayanai

Hakkin Jamaar Kasa

Hakkin Jamaar Kasa "Amma hakkin jama'ar kasa da kake jagoranta shi ne ka sani cewa sun zama jama'arka ce saboda rauninsu da kuma karfinka, don haka wajibi ne ka yi adalci a cikinsu, ka zama garesu tamkar uba mai tausayi ne, ka yafe musu jahilcinsu, kada ka gaggauta musu da ukuba, kuma ka gode wa Allah a kan abin da ya ba ka na karfi kansu".

Bayanai

Hakkin Mai Bawa

Hakkin Mai Bawa Amma hakkin mai mulki da kai yana kama da mai mulki a kai a jagoranci, sai dai wannan -jagora- ba ya mallakar abin da wancan -mai bawa- yake mallaka. Don haka haka biyayyarsa ta zama wajibi a kanka a cikin komai karami da babba,

Bayanai

Hakkin Ilimi

Hakkin Ilimi "Kuma hakkin mai tarbiyyantar da kai da ilimi -mai ilmantar da kai-, shi ne ka girmama shi, ka kuma karrama majalisinsa, da kyautata sauraronsa, da fuskantowa zuwa gareshi, kuma kada ka daga sautinka, kuma kada ka amsa wa wani mutum wani abu da yake amsa masa sai dai ya kasance shi ne wanda yake amsawa, kada ka yi wa wani magana a majalisinsa, kada ka yi gibarsa,

Bayanai

Hakkin Sarki

Hakkin Sarki "Amma hakkin jagora shi ne ka san cewa shi jarrabawa ce gareka, kuma shi abin jarrabawa ne game da kai saboda abin da aka sanya a hannunsa a kanka na iko, kuma ka tsarkake masa nasiha,

Bayanai

Hakkin Hajji

Hakkin Hajji Kuma haqqin hajji shi ne ka san cewa shi zuwa ne ga ubangijinka, kuma gudu ne daga zunubanka, kuma da shi ne za a karvi tubanka, da sauke nauyin wajibi da Allah ya wajabata maka shi a kanka".

Bayanai

Hakkin Salla

Hakkin Salla "Kuma hakkin salla shi ne ka san cewa ita halartowa ce zuwa ga Allah madaukaki, idan ka san hakan, sai ka tsaya matsayin bawa mai kaskanci, kaskantacce, mai kwadayi, mai tsoro, mai kauna, mai jin tsoro, miskini, mai kaskan da kai, ga wanda yake tsayawa gabansa da nutsuwa da dumanina

Bayanai

Hakkin Kafa

Hakkin Kafa "Amma kuma hakkin kafafuwanka, shi ne kada ka yi tafiya da su inda ba ya halatta gareka, a kansu ne zaka tsaya kan siradi, ka duba domin kada su zamar da kai sai ka halaka cikin wuta".

Bayanai

Hakkin Ji

Hakkin Ji "Amma hakkin ji shi ne a tsarkake shi daga giba -yi da wani-, da jin abin da bai halatta a ji ba, da tsarkake shi daga sanya shi hanyar zuwa ga zuciya, sai dai idan wata magana ce mai kima da zata farar da wani alheri a cikin zuciyarka, ko kuma zaka samu wata dabi'a

Bayanai

Hakkin Harshe

Hakkin Harshe Imam Zainul-abidin (a.s) yana cewa: "Kuma amma hakkin harshe; shi ne ka kare shi daga mummunar Magana ta alfahasha -da batsa-, da saba masa alheri, da barin maganar da ba ta da wani amfani, da kyautata wa mutane, da kyautata zance game da su, da siffanta shi da ladubba

Bayanai

Hakkin Hannu

Hakkin Hannu Hakkin Hannu Imam Zainul-abidin (a.s) yana cewa: "Amma hakkin hannunka shi ne kada ka shimfida ta kan abin da bai halatta gareka ba, sai ka samu azabar Allah a gobe -kiyama- da wannan shimfidawar da ka yi, ka kuma samu zargi daga mutane a gidan yau -duniya

Bayanai

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)