Ayyana Halifa
Kamar yadda muka sani cewa; duk wani mai hankali ba zai yiwu ya tafi ya bar gidansa ba, ba tare da mai kula da gidan ba, kodai matarsa ko wani makamancin hakan, kamar yadda hankali yana hukunci da wautar mutumin da yake tafiya ya bar al’ummar da yake shugabanta kara zube ba tare da ya ayyana mata mai kula da ita.
Idan haka al’amarin yake ba yadda za a yi Manzon rahama mai tausayi ga al’ umma wanda ya bayyana mata hatta da hukuncin shiga ban daki da yadda ake fita ya zamanto ya bar wannan al’amari mai girma na tafiyar da al’amuran musulmi ba tare da ya ayyana mai kula da shi ba, alhalin ya san irin al’ummar da ya bari wacce take cike da munafukai da masu son ganin musulunci ya rushe, kuma ga kafiran duniya na daulolin farisa da rumawa sun fara kawo wa daula hari, hada da cewa akwai jahiltar hukunce-hukuncen addini da musulmi kansu suke bukatar wanda zasu cigaba da komawa zuwa gareshi domin dauke kishirwar tambayoyinsu da abubuwa masu yawa da ba sa kirguwa.
Ashe ba jingina kaskanci da wauta ba ne ga mafificin halitta gaba daya, mafi hikimarta, mafi iliminta, wasu musulmi suke yi ba da suke jingina rashin barin halifa ga Manzo (S.A.W) wanda zai tsayu da irin wadannan al’amuran da muka lissafo da ma wasunsu masu yawa.
Idan ya kasance Manzon rahama (S.A.W) ba ya iya barin Madina kodana dan lokaci kankani ba tare da ya ayyana wani mai kula da ita ba, ashe zai yiwu ya san cewa zai bar duniya gaba daya sannan sai ya zamanto bai ayyana wa al’umma wanda zai maye gurbinsa ba! Don haka ne bisa hikimar Allah madaukakin sarki tun farkon kiransa yake shaidawa da cewayana da wasiyyi a wurare masu yawa da suka zo a ruwayoyi gun Ahlul Bait (A.S) da kuma daga ‘yan’uwanmu Ahlussunna, wanda wasu daga cikin wadannan ruwayoyi suna masu kawo sunansa wato imam Ali (A.S).
Don haka ne ma cikin hikimar Allah bayan hajjin bankwana sai ya umarci Manzo da ya karbi bai’ar musulmi ga imam Ali a matsayin halifansa bayansa tun yana raye, domin wannan ya zama hujja a kan musulmi da duniya gaba daya, kuma Allah ya cika haskensa da ni’imarsa garesu da wilayar imam Ali da Ahlul Bait (A.S) bayan Annabin rahama (S.A.W).
Saboda haka sai Manzo (S.A.W) ya umarci atara mutane bayan sun fito daga Makka a lokaci mai zafin rana, kuma ya yi umarni da a dawo da wadanda suka yi gaba; suka yi nisa, kuma a jira wadanda ba su iso ba a wani waje da ake kira KHUM. Game da irin wadannan matakai da ya dauka masu tarihi suna cewa; ya dauke su ne domin muhimmacin al’amarin kuma da hikimar yazama ya wanzu a kwakwalen mutane ne.
Bayan jama’a sun taru ne yasa aka kafa wani mimbari ta yadda kowa zai ji shi, kuma ya gan shi, sannan sai ya hau kan mimbarin ya yi huduba mai tsayi, daga cikin abin da wannan huduba mai tarihi ta kunsa ya zo kamar haka:
Akatara mutane aka yi masa minbari sannan sai annabi (S.A.W) ya hau kansa bayan ya yi salla a cikin wanan taron na musulmi sannan sai ya godewa Allah ya yabe shi, ya fada da sauti madaukaki da duk wanda yake wajan yana jin sa: “Ya ku mutane! Ya kusata a kirani sai in amsa, ni abin tambaya ne, ku ma ababan tambaya ne, me zaku ce? Sukace : Mun shaida ka isar da sako ka yi nasiha, ka yi jihadi, Allah ya saka maka da alheri. Ya ce: Ba kuna shaidawa cewa babu wani ubangiji sai Allah ba, kuma Muhammad bawansa ne kuma manzonsa ne, kuma cewa aljanna gaskiya ce kuma alkiyama mai zuwa ce babu kokwanto a cikinta, kuma Allah yana tayar da wanda suke cikin kaburbura? Sukace : Haka ne mun shaida da hakan. Yace : Ya ubangiji ka shaida. Sannan yace : Ni zan hadu da ku a tafki, kuma ku zaku zo mini a tafkin, wanda fadinsa ya kai tsakanin San’a’a da Busra, a ciki akwai kofuna na azurfa sun kai yawan taurari, ku duba ku gani yaya zaku kusance da alkawura biyu masu nauyi bayana”.
Sai wani ya daga muryayana mai tambaya; ya Manzon Allah (S.A.W) menene alkuwura biyu masu nauyi? Manzon Allah ya ce: Alkawari mafi girma shi ne Littafin Allah, gefensa a hannun Allah daya gefen a hannunku, ku yi riko da shi kada ku bata, dayan kuma mafi karanta su ne Ahlina (Ahlul Bait). Hakika (Ubangiji) mai tausayi mai sanin komai ya bani labari cewa; ba zasu taba rabuwa ba har sai sun riske ne a tafki, kumana roka wa abububwan nan biyu wannan a wajan ubangijina.Kada ku shiga gabansu sai ku halaka, kuma kada ku takaita gabarinsu sai ku halaka”.
Sannan sai ya yi riko da hannun Ali dan Abu Talib (A.S) har sai da aka ga farin hammatarsu, mutane suka san sugaba daya. Sai Manzo yace : “Ya ku mutane wanene ya fi cancantar biyayyar muminai fiye da kawukansu? Sukace : Allah da Manzonsa su ne mafi sani. Yace : Ubangiji shugabana ne, kuma ni ne shugaban muminai, kuma ni na fi cancanta da biyayyar muminai fiye da kawukansu, to duk wanda nake shugabansa wannan Ali shugabansa ne”, yana maimaita wannan har sau uku.
Sannan sai yace : “Ya ubangiji! Ka jibanci lamarinwanda ya bi shi, ka ki wanda ya ki shi, ka so wanda ya so shi, ka kyamaci wanda ya kyamace shi, ka taimaki wanda ya taimake shi, ka tabar da wanda ya bar shi, ka juya gaskiya tare da shi duk inda ya juya, ku sani wanda ya halarta ya isar wa wanda bai halarta ba”.
Sannan jama’a ba ta watse ba har sai da Jibrilu ya sauka da wahayin Allah da fadinsa: “Yau ne na kammala addininku gareku, kuma na cika ni’imata a gareku, kuma na yarda da musulunci addini gareku”[ 12] .
San Manzon Allah (S.A.W) yace : “Allah mai girma a kan kammala addini da cikar ni’ima da yardar ubangiji da manzancina da shugabanci ga Ali (A.S) bayana”.
Sannan sai ya yi umarni aka kafa hema ga Ali (A.S) kuma musulmi su shiga wajansa jama’a-jama’a suna yi masa sallama da bai’a akan shugabancin muminai, sai duk mutane suka yi hakan, ya umumarci matansa da sauran matan muminai da suke tare da shi su ma suka yi bai’a.
Daga cikinna gaba wajan yi masa murna da bai’a akwai Abubakar da Umar dan Khaddabi, kowannensu yana cewa: Farin ciki ya tabbata gareka ya dan Abu Talib, ka wayi gari, ka yi yammaci shugabana kuma shugaban dukkan mumini da mumina[13] .
Manzon Allah ya kasance babu wani abu da yake raba shi da Ali a karshen rayuwarsa, yana mai yi masa wasiyya da karfafa shi kuma da shirya shi domin daukar nauyi mai girma da zai hau kansa, ya kasnce mai lizimtar dakin Imam Ali (A.S), kuma ya kasnce yana dafa shi domin tafiya yayin da rashin lafiyarsa ya tsananta har ya yi wafati a hannunsa kuma dakin wasiyyinsa imam Ali (A.S) kamar yadda imam Ali ya fada a daya dagahudubobinsa[ 14] .
Bawanda yake tare da Manzon Allah a lokacin wafatinsa sai imam Ali (A.S) da ‘yarsa (A.S) da wasu daga Banu Hashim da iyalansa. Yayin da mutane suka samu labarin wafatinsa Madinagaba dayanta ta hau kuka da bakin ciki mai tsanani, Umar dan Khaddabi ya daga takobi ya hana mutane cewa Manzo ya rasu har sai da Abubakar ya zo. Sannan Abubakar da Umar dan Khaddabi da wasu daga abokansu suka gaggauta zuwa Kangon Banu Sa’ida (Sakifa) suka tarar da wani tarona Ansar a can da suke neman zabar halifa daga cikinsu, wannan al’amarin ya kai ga jayayya mai tsanani da kuma ganganta manta bai’ar da aka yi wa Ali (A.S).
A daya bangaren imam Ali da Ahlin gidansa sun shagaltu da shirya Manzo (S.A.W) da bizne shi, Ali ya wanke shi ba tare da ya cire rigarsa ba, Abbas da dansa Fadl suka taimaka masa da zuba ruwa, ya kasance yana cewa: Ina fansar ranka da babana da babata, kanshinka ya girmama kana rayayye da kana fakakke[15] .
Sannan imam Ali (A.S) yadora Manzo akan wani gado ya yi masa salla kuma ya umarci musulmi da su shiga su yi masa salla ba tare da jam’i ba, suna shiga jama’a-jama’a suna yi masa salla, imam Ali (A.S) ya kasance yana cewa: “Aminci ya tabbata gareka ya kai wannan annabi da rahamar Allah da albarkarsa.Ya ubangiji mu muna shaidawa cewa hakika ya isar da sakon da ka saukar masa, ya yi nasiha ga al’umma, ya yi jihadi a tafarkin Allah, har Allah ya daukaka addininsa, ya cika kalmarsa, ya ubangiji ka sanya mu cikin masu bin abin da ka saukar gareshi, ka tabbatar da mu bayansa, ka hada tsakaninmu da shi. Sai mutane suce : Amin.Har maza da mata da yara suka yi salla gareshi, tsira da amincin Allah su tabbata gareshi da alayensa.
Ya binne Manzo adakin da ya yi wafati, ya sanya shi cikin kabari, ya yaye fuskarsa, kuma ya daidaita kumatunsa mai tsarki a kan turbaya, sannan sai ya zuba kasa. Amma musulmin da suke a Sakifa domin nada halifa bisa jayayya mai tsanani babu wani daga cikinsu da ya samu damar zuwa wajan janazar Manzoko yi masa salla ko bizne shi. Aminci ya tabbata gareka ya Manzon Allah!ranar da aka haife ka, da ranar da ka yi wafati, da ranar da za a tashe ka rayayye.
Allah madauki yana cewa: “Saboda (kai) rahama ce daga Allah ka yi sanyin hali a garesu, kuma da ka kasance mai kaushi mai kaurin zuciya da sun watse daga gefenka”[ 16] .
Haika Manzon rahama (S.A.W) ya kasance mai kyawawan dabi’u marasa misali, don haka duk abin da alkalami yake rubutawa to yagaza ya kawo hakikaninsu, amma zamu yi nuni da wasu kadan daga ciki.
Ya kasance mai kaskantar da kai, kuma rayuwarsa madaidaiciya ce, ta yadda idan bako daga larabawan kauye ya zo mazauninsa yakan tambaya wanene Muhammad acikinku[ 17] ?. Duniya ba ta rude shi ba, ya kasance yana kallonta da idanun takawa da tsentseni, kuma bai fada a tarkontaba[ 18] . Ya kasance ba ya yaudara, yana cika alkawuransa, yana sadar da zumuncinsa, ba ya bayar da dama ga wani ya yi magana a kan wani, domin yana son ya bar mutane yana mai kubutacciya zuciya; wato ba ya kallonsu da waniabu[ 19] .
Ya kasance misali ne a yalwar kirji da hakuri da rangwame. Anas yana cewa: Manzo (S.A.W) ya kasance yana da wani abin sha na sahur, kuma da na shan ruwa da yamma, wani lokaci guda daya ne ma, wani lokaci madara ce, wani lokaci kuma gurasa ce da ake taunawa a tsotse, wata rana na yi tanadinta, sai ya jima bai dawo ba, sai na yi tsammanin ya sha ruwa a wajan wani daga sahabbansa ne, sai na shanye, sai ya zo bayan sallar isha da awa daya, sai na tambayi wadanda suke tare da shi cewa; shin Manzo ya sha ruwa a wani waje ko kuma wani ya gayyace shi? Sai sukace : A’a. Ya ce: Sai ya kwana ya wayi gari da azumi bai ci komai ba, kuma bai tambaye ni ba, bai kuma taba maganarta ba haryau[ 20] .
Ya kasanceyana son salla da yawa, idan mutane suka zo sai ya dakatar da salla ya saurare su, idan suka tafi sai ya cigaba.
Yana girmama kowa, kuma ma’aunin daraja a wajansa shi ne imani da aiki… ba ya ganin kima don dukiya do matsayi ko alfarma, ya kasance mai tausayi ga abokin tafiyarsa mai himmantuwa da sha’aninsu dabukatunsu[ 21] .
Ba ya daga cikin dabi’ar Manzo (S.A.W) daukar fansa akan wanda ya munana masa, yana mai rangwame ne ga masu keta iyakarsa, kuma yana fuskantar munanawarsu da hakuri da juriya da afuwa da rangwame. Duk da irin wahala da cutarwa da ya fuskanta daga Kuraishawa a farkon kiransa amma bayan Fathu Makka sai ya yafe musugaba daya.Kamar yadda ya yafewa Wahashi makashin amminsa Hamza da kuma Abu Sufyan da matarsa Hindu.
Duk da haka bai taba yarda da ketare iyakar Allah ba, kuma ba ya jin tsoron zargin mai zargi game da addinin Allah, shi ya sa ma yayin da Almakhzumiyya ta yi sata bai karbi shiga tsakiyar Usama dan Zaid ba, yanacewa[ 22] : Abin da ya halakar da wadanda suke gabaninku shi ne sun kasance idan mai girma ya yi sata a cikinsu sai su bar shi, idan mai rauni ya yi sata sai su tsayar da haddi a kansa.
Ya kasance yana kiyaye jikinsa da tufafinsa a kan tsafta koda yaushe, yana amfani da mafi kyawun turare, imam sadik (A.S) yana cewa: “Yana kashe kudi a kan turare fiye da yadda yake kashewa a kan abinci”[ 23] . Duk inda ya wuce kanshin turareyana tashi, ya kasance yana kallon mudubi yana taje gashinsa, wani lokacin yana kallon ruwa ne ya gyara gashinsa, ya kasance yana ado ga sahabbansa ballanta matansa. Yana cewa: “Allah yana son idan bawansa zai fita wajan ‘yan’uwansa ya yi shiri ya yi ado”[ 24] .
Manzon Allah (S.A.W) ya kasance mai yawan shagaltuwa da salla, an rawaito daga Abu Abdullah (A.S) yana cewa: Ya kasance idan Manzon Allah ya yi sallar isha sai ya yi umarni da a kawo masa ruwan alwala da asuwakinsa, a ajiye turba a gun kansa, sai ya yi bacci kadan sannan sai ya tashi ya yi asuwaki ya yi alawala ya yi salla raka’a hudu, sannan sai ya yi bacci kadan sai ya tashi ya yi asuwaki ya yi alwala ya yi salla, yana asuwaki duk sadda ya tashi daga baccinsa[25] .
Ya kasance yana tsawaita kaskantar da kai ga Allah da tsayuwa gabansa har sai da kafafunsa sukakumbura[ 26] . Ya kasance mai yawan tunani game da abin da yake gewaye da shina halittar sama da kasa da rana da makamancinsu, saudayawa yakan yi tunani game da girman mahalicci. Amma game da zuhudunsa ya isa girman zuhudunsa cewa kyale-kyalin duniya ba su taba fitinarsa ba, kuma ba su tabajan hankalinsa ba.
____________________
[1] Surar Kalami: 3 – 4.
[2] - Tafsirul mizan: 4/151.
[3] - majma’azzawa’id: 6/26.
[4] - Siratul mustapha: 42. A’alamul hidaya: 1/25.
[5] - Assiratul muhammadiyya: 41.
[6] - Sahih Muslim: 7/134. Sahih buhari: 5/39.
[7] - Injilar Yohana: Assihah 14. Wato John: Genesis 14.
[8] - Almizan: 20/327.
[9] - Biharul anwar: 18/207-208.
[10] - Mausu’atut Tarih: 1/405. Mausu’atul mustapha wal itra: 1/108.
[11] - I’ilamul hidaya: 1/94.
[12] - Ma’ida: 3.
[13] - Tarihin yakubi: 3/112. Masnad Ahmad: 4/281. Albidaya wannihaya: 5/213. Mausu’atul gadir: 1/43, 165, 196, 215, 23, 238.11/131.
[14] - Nahjul balaga: huduba; 197.
[15] - Assiran nabawiyya ta ibn kasir: 4/518.
[16] - Ali imrana: 159.
[17] - Biharul anwar: 16/220-229.
[18] - Biharul anwar: 16/220-229
[19] - Biharul anwar: 16/232.
[20] - Kahlul basar: 67-68.
[21] - Biharul anwar: 16/228.
[22] - Irshadus sari: 9/456.
[23] - Wasa’ilus Shi'a’:1/443.
[24] - Wasa’ilus Shi'a’: 3/344.
[25] - Wasa’ilus Shi'a: 1/356.
[26] - Kahlul basar: 78.
Abin Da Littafi Ya Kunsa
Shimfida 3
Jazirar Larabawa Kafin Musulunci 4
Wane ne Muhammad (S.A.W) 6
Kasuwancinsa 7
Aurensa 8
Albishir Da Zuwan Manzo (S.A.W) 9
Wahayi 10
Wahayi Ga Manzon Rahama (S.A.W) 11
Saukar Wahayi 12
Kira A Boye 14
Kiran Danginsa 15
Kiran Mutane A Bayyane 17
Annabi (S.A.W) A Madina 19
Yakokin Manzo (S.A.W) 20
Hajjin Bankwana 21
Hudubar Hajjin Bankwana 22
Ayyana Halifa 23
Karshen Rayuwar Manzo Da Wafatinsa 25
Daga Kyawawan Dabi’un Annabi 26
Rangwamensa Da Afuwarsa 27
Tsarkinsa Da Tsaftarsa 28
Ibadarsa Da Zuhudunsa 29