Kebance-kebancenna biyu Imamamanci a kananan shekaru
Daga cikin abin da ke damfare da imamancin Imam Mahdi (a.s) a wajen Ahlulbaiti (a.s) kudurcewar su da imamanci Imam mahda (a.s) tun yana da karancin shekaru (yana yaro), kuma wadannan kebance-kebance wani lokaci mun kalle su da mahangar musulunci da nufin kafa hujja da ije abin da zai yuyi a ije shi na daga ishkali a addinance, wani lokaci kuma mukan kalla su da mahamgar hakika da bayanin cewa lalle wannan imamancin imamanci ne na gaskiya da ya tattaro dukkanin abubuwan da suka tabbatar masa da nagarta gamsashshiya kuma ba imamanci ba ne na rayawa ko na jeka-na-yi-ka ba.
Kuma Idan muka kalle shi da mahanga ta musulunci zamu ga yazama larura mu tantance mas’alar imamanci tun a farko da cewa shin ita mas’ala ce ta akida?ko kuma mas’alar shari’a ce? Idan ta kasance mas’alar akida kamar yadda Shi’a suka kudurce zamu ga kur’anina bayyana tabbatuwar Annabtar karamin yaro a sari -wacce ita mas’ala ce ta akida- Allah madaukakin sarki ya ce: {ya Yahaya ka riki littafi da karfi kuma mun ba shi hukunci yana dan yaro}[46]
Idan kuma mas’alar ta kasnce ta shar’a to lalleyana daga cikin fayyatattun lamuran musulunci cewa an kange yaro, kuma duk wanda aka kange shi to ya rasa walicci a kan kansa, kenan ta yaya zai iya zama waliyyin waninsa don haka waliccin yaro ba zai tabbata ba kenan.
Hakika musulmai sun yi sabani a cikin wannan mas’alar, ita makarantar mazhabobi hudu ta sanya halifanci da imamanci da shugabanci daga cikin sha’anin shari’a da ayyukan mukallafai, a yayin da makarantar Ahlulbaiti (a.s) ta yi imani da cewa wannan mas’ala ce ta akida kuma tana daga cikin tushen addinin da take daga cikin sha’anin ubangijin talikai, kuma ba ta daga cikin abin da ya kebanci mukallafai kuma ba ta gada cikin abin da ya kebanci ayyukan bayi, don haka makarantar Ahlulbaiti (a.s) ta yi imanin da imamancin yaro na wasu adadi daga Imamai, wanda daga cikinsu akwai Imam Mahdi (a.s), saboda haka akidar ta dace da abin da makarantar Ahlulbaiti (a.s) ta yi imani da shi a wannan mahallin ba wani ishkali da zai zo mata ta bangaren akida mutukar karara kur’ani ya tabbatar da Annabci Annabi Yahaya (a.s) yana yaro, haka ma basu ishkali ta bangaren shari’a mutukar dai a mahangar Ahlulbaiti (a.s) wannan mas’alar ta fita daga iyakar shari’a ta fada shingen akida, kuma hukuncin shari’a na babin kange yaro tana danbbakuwa sannan tana gudana ne kan mukallafai, kuma ba ta dabbakuwa kan Allah Ta'ala, domin ita shari’a dakon Allah Ta'ala ce da ya dora wa mukallafai.
Da haka ne zai bayyana a sarari cewa, da muka kafa hujja da Annabcin Annabi Yahaya (a.s) abin da muke nufi shi ne, mu yi bayanin cewa, Imamanci kamar Annabta yake shi ma mas’ala ce ta Akida kuma lalle ita mas’alar akida ba ta doruwa kan kiyasin (wato ma’aunin) mutane, ballantana ma ba ta doruwa hatta a kan kiyasin shari’ar da ta zo don ta tsara rayuwar mukallafai, don haka be inganta a dabbaka ta a kan ubangijin talikai ba, domin Annabtar Annabi Yahaya (a.s) tana fa’dantar da mu cewa lalle mas’alar Akida ta tsayu ne kan dalili da hujja, idan hujja ta akida ta tsayu kan imamancin yaro karami, babu makawa sai mun yi imani da ita kamar yanda muka yi imani da annabcin yaro karami a yayin da dalili na akida ya tsayu a kanta, a wannan lokaci ba shi da ma’ana a ce kafa hujja da annabcin Annabi Yahaya (a.s) ba shi da mahalli, domin an anbace shi a sarari a cikin kur’ani sabanin mas’alar Imam Mahdi (a.s).
Daganan ne ibni Hajar Askalani Al-haisami shi da makamancisa suka kalubalanci imamancin Imam Mahdi (a.s) da cewa ba ta da asasi kwata-kwata. A yayin da ya rubuta hakan da salon be dace ba,yana mai cewa: “sannan abin da ya tabbata a shari’a mai tsarki lalle waliccin yaro baya inganta, ta yaya ya yiyu ga wadannan wawayen su yi da’awar imamancin dan shekara biyar ......”[47]
Hakika ya bayyana cewa wannan ba ya daga cikin abin da shari’a ta tabbatar kadaidai yana daga cikin abin da fikihun su ya tabbatar wanda be inganta su lazimta mana shi ba.(Wato su hukunta mu da shi ba).
Kuma idan muka kalli lamarin ta bangaren Tarihiza mu samu cewa lalle Mahdi (a.s) ya gaji babansa a shugabancin musulmai yana dan shekara biyar, kuma wannan yana nufin lalle ya kasance Imami da dukkanin abin da imamanci ya tattaro na tunani da ruhi tun da wurwuri a cikin rayuwarsa madaukakiya.
Sayyid shahid Assadr yana fadi a kan wannan lamarin imamanci a kananan shekaru kanana a sarari lamarin da da dama daga cikin mahaifan Imaman Ahlulbaiti (a.s) suka rigaye shi a kai, ka ga Imam Muhammad dan Ali Al-jawad, ya hau imamanci yana dan shekara takwas a rayuwarsa[48] , kuma Imam Ali dan Muhammad Al-hadi (a.s) ya karbi imamanci yana dan shekara tara[49] a rayuwarsa, kuma Imam abu Muhammad Hasan Al-askari (a.s)[50] mahaifinimam Mahdi (a.s), ya karbi jagoranci yan adan shekara ashirin da biyu, idan an lura za a ga cewa rike mukamin imamanci da karancin shekaru ya kai kokoluwarsa da matuka a cikin Imam Mahdi (a.s) da Imam Jawad (a.s), kuma mun ambace ta da mabayyanin abu wato abu na sarari wanda da aka saba gani saboda idan aka danganta ta da wani adadi na mahaifan Imam Mahdi (a.s) tana tabbatar mana da wani abu na sarari na ilimi da musulmai suka rayu da shi, kuma suka kiyaye shi a cikin gogayyar rayuwa tare da Imami da wannan yanayin ko wancen. Kuma ba zai yiyu a nemi mu tabbatar da wani abuna sarari ba wanda yake mafi bayyana kuma mafi karfi fiye da gogayyar al’umma ba,[51] kuma da sannu zamu bayyana haka bisa jeri mai zuwa.
Imamanci Imami daga Ahlulbaiti (a.s) be zamo wani bangare daga bangarorin hukuma ba, kuma be zama irin iko ko mulkin da ke ciratuwa daga mahaifi zuwa da ba, irin wanda tsarin mulki ke ba shi kariya, kamar imamancin halifofin fadimawa da halifancin abbasawa ba, kadai (irin wannan ikon) ya kasance yana tabbata ta hanyar samun biyayya daga mutane ta hanyar wakilansa da mutane masu yawa ke bi tahanyar yin tasiri a zukatan mutane da da gamsar da tunaninsu a kan wannan tsarin da nuna sun cancanci shugabancin musulunci da jagorancin sa ta bangaren ruhi da tunani.
Hakika wannan tsarin wakilcin da mutane ke bi tun a farkon musulunici aka gina shi, sannan ya girmama ya yadu a lokacin Imam Bakir da Sadik (a.s), kuma makarantar da wadannan Imamai biyu suka kafa ta wayi gari a cikin wannan tsarin a tana dauke da wani tunanu faffada wanda ya yadu a cikin a duniyar musulmai, kuma wannan tsari ya tattaro darurawan fakihai da malaman Kalam da na tafsiri da ma malamai a cikin fagagen lilmi Musulnci da na Dan’adam din da aka sani a waccen zamanin, har sai da Hasan dan Aliyyul Washa ya ce: hakika na shiga masallacin kufa sai na ga shehunnai[52] dari tara dukkaninsu suna cewa Ja'afar dan Muhammad (a.s) ya zantar da mu.
Hakika sharadan da wannan makarantar ta doru a kan su ita da abin da yake kamantata na daga wakilcin mutane a cikin marayar al’ummar musulmi, sun yi imani da su kuma suna kayyadantuwa da abin da suka kunsa wajen ayyana Imamai da sanin cancantarsa a matsayin Imami, an gindaya sharadai masu tsanani, domin sun yi imani da cewa Imami ba zai taba zama Imami ba sai ya zama ya fi kowa ilimi a zamaninsa.[53]
Hakika wannan makarantar ita da jagorancinta na jama’a ta kasance tana gabatar da babbar fansar da kai (mabiyanta sun sadaukar da kansu sun bada jini da tsoka) a hanyar ta ta ganin ta tabbata kan akidarta ta imamanci; saboda ta kasance babar barazana a mahangar hukumar da take ci, ko da kuwa ta bangaren tunani ne kawai, al’amarin da ya sa hukumar wancen lokacin ta ci gaba da kai musu hari na kar a bar iri, sai aka kashe wanda aka kashe aka daure wanda aka daure kuma daruruwa suka mutu a cikin duhun kurkuku, kuma wannan na nufin imaninsu da imamancin Ahlulbaiti (a.s) yana jawo musu musiba,[54] kuma ba shi da wani abu da yake da shi wanda ake samun karawa ( ta wani abin duniya ) da shi face abin da mai akidantuwa da shi yake ji ko yake tsammani na kusanci da Allah Ta'ala da kuma samun matsayi a wajensa.
Hakika Imamin da wannan (tsarin na wakilcin) gugun al’umma ya tabbatar da imamancinsu, ba su kasance sun kebance kansu daga jama’ar ba, kuma ba su kai kansu can tsororruwar matsayi a cikin manyan gidaje kamar dai yadda sarakuna suke yi wa jama’arsu ba, kuma (imamai) ba su taba yarda an sa shamaki tsakanin su da jama’a (mabiyansu) ba, sai dai in hukumar da ke mulki ce ta shiga tsakanin su (da mabiya) ta hanyar jefa su (imaman) kurkuku ko nisantasu, kuma wannan abu ne da muka sani ta hanya adadi masu yawa na marawaita da masana hadisi game da ko wane daya daga cikin Imamai goma sha daya, da ma ta hanyar abin da aka cirato na daga wasikun da suka kasance tsakanin Imam da wadanda suka yi zamani da shi, da kuma tafiye-tafiyen da Imam yake yi ta wani bangaren, da kuma abin da ya kasance yana yadawa ta hanyar wakilansa a mabanbanta sasannin Duniyar musulunci da wani bangaren daban, da ma kuma abin da Shi’a suka yi sabo da shi a kansa na bibiyar yanayin da imamansu suke ciki da kai musu ziyara a madina mai haske yayin da suke dafifi zuwa gidaje masu tsarki don gudanar da faralin hajji.[55] Dukkanin wadannan a sarari sosai suna tabbatar da kaikawo mai cigaba tsakanin Imam (s.a) da wakilansa da suka yadu cikin fadin sassan duniyar musulunci bisa mabanbantan matsayinsu na daga malamai da wasunsu.
Hakika masarautar da ke ci wacce ta yi zamani da Imamai ta kasance ta na kallon su kuma tana kallon wannan shuganacin na su na ruhi a matsayin babban hadari kan samuwarsu da ikonsu, bisa wannan ne suka zage dantsensu wajen ganin sun yi kaca-kaca da wannan shugabancin kuma suka yi ta aikata munanna abubuwa saboda haka wani lokaci ma sukan nuna kekashewar zuciya da dagawa idan haka ya zame musu larura wajen kare kujerarsu ta mulki, kuma dauri da kora sun kasance abubuwan yau da gobe da su kansu Imamai[56] suka yi ta fama da su, duk da abin da hakan ke sabbabawa na jin damuwa da kyamar da masulmai da mutanen mabiya - Ahlulbaiti (a.s) - ke bayyanawa a bisa mabanbantan matsayinsu.
Idan muka kalli wadanna nukududin guda shida da idon basira wadannan suke tabbatatun abubuwa ne na tarihi, da ba shakka a cikinsu zai iya yiyuwa mu fita da sakamako kamar haka: Tabbas samuwar imamanci na wuri lamari ne a fili wanda yake da tabbacin samuwa, kuma be kasance wahami da wahamomi ba, domin imamin da ya bayyana a fage aiki yana karamin yaro ya kuma shelamta kansa a matsayin Imam na ruhi da tunani ga musulmai ba ki daya, kuma dukkanin wadannan tarin jama’ar suka zama suna yi masa biyayya a matsayin Imami, babu makawa sai ya kasance yana da wani matsayi bayyananne abin la’alari kuma ya zama yana da matsayi a ilimi da sani mai fadi sasanni kuma ya zama yana da kwarewa a fikihu da tafsiri da akida domin idan har be zama haka ba, da ba zai yiyu wannnan gungun jama’ar su yarda da imamancinsa ba, tare da cewa Imamai sun kasance a wajen da zai yiyu ga mabiyansu su su yi ma’amala tare da su kuma a yanayoyi mabanbanta zasu iya yin tasiri a rayuwarsu da ma ma’aunin mutuntakarsu. Shin kana ganin zai yiyu wani dan karamin yaro ya yi kira zuwa imamancinsa, kuma ya dora kansa a matsayin alamin musulunci - ta hanyar imamamnci - alhali yana kan ido da majiyar mutanen da suke yi masa biyayya, sai su yi imani da shi sannan su sadaukar da abu mai kima a kansa na daga abincinsu da rayuwarsu ba tare da sun kallafawa kansu gano hakikanin sha’aninsa ba, kuma ba tare yanayin imamancinsa na yarinta ya girgiza su ba, don su sami masaniya kan hakikanin matsayinsa ta hanyar gudanar da gwaji da jarraba wannan yaron Imami ba? Kuma ka kaddara cewa mutane ba su motsa wajen sanin yanayinsa ba, shin zai yiyu matsalar ta shude tsawon kwanaki da watanni ba tare da hakika ta bayyana gare su ba, dun da kai kawo da alaka ta dabi’a mai cigaba tsakanin wannan yaron da sausan mutane? Kuma shin hankali zai karbi cewa ga shi yaro ne a tunaninsa da aikinsa da gaske amma kuma hakan be tabbata akansa ta hanyar doguwar alaka ta yau da gobe ba?
Idan kuma muka kaddara cewa lalle tsayin al’ummakan imamancin Ahlulbaiti (a.s) bai bada dama su gane hakikanni lamari ba to don me ya sa masarauta mai ci ta yi shiru ba ta yi kokarin bayyana hakika ba idan har tana da riba kan hakan? Ya tsananin saukin yin hakan ga masarauta mai ci da ace Imami yaro, yaro ne shi a tunani da wayewa kamar yanda aka san yara, ya isa ya zama mafi cin nasarar hanya idan aka gabatar da wannan yaron ga Shi’arsa da wadanda ma ba Shi’arsa ba kan hakikar yadda yake, kuma ta tabbada da dalili kan rashin cancantar sa ga imamanci da shugabancin mutane a ruhi da tunani, idan har ya zama yana da wahala a kasa tabbatar da rashin cancantar mutumin da yake dan shekara arba’in ko dan shekara hamsin saboda ya kewaye sani da wani babban gwargwado a wayewar zamaninsa kan yanda ake darewa kujerar imamacni, ke nan babu wata wahala wajen tabbatar da rashin cancantar yaro na al’ada duk yanda ya kasance mai kaifin basira da hazaka kan imamanci da ma’anarsa kamar yadda Shi’a imamiyya[57] suka san shi, kuma da hakan ya kasance mafi saukin hanya (wajen kawo karshen Shi’a ) fiye da bin hanya mai murdiya da bin tafarkin yin kof daya da ta’anatin da masarautar wancen lokacin ta zaba kuma ta yi ta bi (don ta kawo karshen shi’anci).
Kadai fassarar da za a bayar kan yin shirun hukumar wancen lokaci ga barin yin wasa da lamarin[58] ita cecewa ta riski cewa imamanci tare da karancin shekaru lamari ne na gaskiya ba abu ne da aka kirkira ba.
Kuma bisa hakika hukuma ta gane haka a aikace bayan da ta yi kokarin yin wasan kura da wannan lamarin na imamanci sai ya zamana ta gaza yin komai a kai, kuma tarihi sheda ne kan wadannan kokarce-kokarcen da kuma gazawarsu[59] a daidai lokacin da ko sau daya ba a taba ba mu labarin girgizar matsayan imamancin yaro ba ko kuma aka ce Imami mai karancin shekaru ya fuskanci wani yanayi na tsanani da ya fi karfinsa ko ya sa amincin mutane da shi ya yi rauni ba.
Wannan muke nufi a lokacin da muke cewa hakika imamancin karamin yaro lamari nena hakika a rayuwar Ahlulbaiti (a.s) ba kawai rayawa ba ne kamar yadda wannan lamarin yana da tushensa da yanayoyinsa masu kamanceceniya a cikin kundin abin da aka saukar da sama wanda ya shude tsahon tarihin manzanci da shugabancin da Allah Ta'ala yake nadawa.
Kuma Yahaya (a.s) ya isa misalikan tabbacin lamarin imamancin yaro daga Ahlulbaiti (a.s) a cikin taskar ubangiji, yayin da Allah Ta'ala yake cewa: {ya Yahaya ka riki littafi da karfi kuma mun ba shi hukunci yana dan karamin yaro}[60]
A lokacin da ya tabbata cewa imamancin wanda ke da karancin shekaru lamari ne na hakika kuma ya tabbata a aikace a cikin rayuwar Ahlulbaiti (a.s) ba wata ja-in-ja da zata yi saura kan lamarin imam mahdi (a.s), da halifancin sa ga babansa a lokacin yana dan yaro[61] “[62] .