Har zuwa karshen karni na bakwai malamai sun hadu a kan wannan al’amari cewa tafiya domin aiwatar da wani aiki na mustahabbi koda ba ta zama mustahabbi ba to alal akalla ta halasta. Amma a farkon karni na takwas, Sai Ibn Taimiyya ya yi riko da hadisin Manzo wanda Abu Huraira ya ruwaito ta yadda ya saba wa dukkan malamai da suka hadu a kan wannan al’amari. Wannan ruwaya kuwa da Ibn taimiyya ya yi mafani da ita, an ruwaito ta ne ta fuska guda uku, amma abin da yake iya tabbatar wa Ibn taimiyya da manufarsa ya zo da fuska biyu ne kamar haka:
1- Kada a yi nufin tafiya sai zuwa masallatai guda uku: Wannan masallaci nawa, masallacin ka’aba da Masallacin Kudus.[52]
2- Ana yin tafiya ne kawai zuwa ga masallatai guda uku[53], Ibn taimiyya ya yi riko ne da zahirin wannan hadisi domin tabbatar da manufarsa, ta yadda ya yi da’awar cewa domin aiwatar da ayyukan ibada masallatai uku ne kawai mutum zai iya zuwa domin yin hakan. Saboda haka ziyarar Manzo wanda yake matsayin ibada ba ya daya daga cikin wadannan abubuwa guda uku. Wannan kafa hujja ta Ibn Taimiyya kuwa idan muka lura da kyau zamu iya gane rashin ingancinsa, domin kuwa ba shi da kafafu masu karfi.
Domin kuwa mun san cewa jumlar da take kebewa tana ginuwa daga sassa guda biyu kamar haka:
1-Jumlar da ake kebewa daga gareta: "Ba wanda ya zo wurina".
2- Jumlar da a ka kebance "Sai Ali"
Hadisin da ya gabata ya ginu ne ta hanyar jumloli biyu ne:
1-jumla ta farko jumlar da aka kebance daga gare ta "Kada ku yi tafiya. "
2-Jumla ta biyu kuwa, wadda aka kebance: "Sai masallatai uku".
A jumlar ta farko abin da aka kebance bai fito ba a fili, bisa la’akari da ka’idar larabci a nan dole mu kaddara wata jumla, wadda zata iya zama daya daga cikin wadannan jumloli guda biyu kamar haka:
1-Mai yiwuwa ka iya cewa "masallaci" ne. (wato kada ka yi tafiya zuwa kowane masallaci sai masallatai guda uku)
2-Mai yiwuwa ana nufin "wuri" ne (kada ka yi tafiya zuwa wani wuri sai masallatai guda uku) Saboda haka bisa ga tsammani na farko, zai zama ma’anar jumla zai zama haka, wato kada ka yi tafiya zuwa kowane masallaci sai masallatai guda uku da aka ambata.
Saboda haka idan muka dauki wannan ma’ana zai zama cewa Manzo yana magana ne a kan masallatai, wato don mutum ya yi salla kada ya yi wahala don tafiya kowane masallaci sai masallatai guda uku da aka ambata. Saboda haka a nan ziyarar Manzo ba ta cikin abin da aka hana a cikin wannan hadisi domin ba a kansa ake Magana ba. Sannan dalilin da ya sa aka yi hani tafiya wani masallaci domin yin salla domin sauran masallatai hukunci guda garesu babu wani wanda ya fi wani daraja daga cikinsu, saboda haka yayin da mutum yake da damar yin salla a daya daga cikin masallatai me zai sanya ya sha wahala domin ya tafi waninsa.
Misali kamar idan akwai masallacin jumma’a a wani gari me zai sanya mutum ya tafi wani gari domin ya yi sallar jumma’a a can, domin kuwa ladar da zai samu a wancan masallacin ba ta dara wadda zai samu ba a wannan na garinsu.
Amma dangane da wadancan masallatai uku abin ba haka yake ba, domin salla a cikin daya daga cikinsu ya fi salla a cikin sauran masallatai, saboda haka tare da kula da cewa a cikin wannan hadisi an yi magana ne kawai a kana masallatai, don haka tafiya zuwa wasu wurare bai shafi wannan hani na hadisi ba, saboda haka ba ya magana a kan halasci ko haramcin yin hakan.
Amma idan muka dauki ma’ana ta biyu ma’anar wannan hadisi zata kasance kamar haka: kada ka yi tafiya sai zuwa wurare guda uku (masallatai guda uku da muka ambata).
Idan muka dauki wannan ma’ana dogaron Ibn Taimiyya yana iya zama dai-dai. Amma tare da lura da yadda tarihin musulmai ya tafi a kan mustahabbacin tafiya zuwa kabarin Manzo (S.A.W), domin ziyara tana nuna mana rashin ingancin wannan hadisi.
Na farko kamar yadda muka gani a cikin hadisin da ya gabata, ana iya tsammanin wata ma’ana daban, sakamakon wannan ma’ana kuwa ba za a samu wani fito na fito ba a hadisai da ayoyi da kuma tarihin musulmi da suke nuni a kan halascin ziyarar Manzo. Kuma tare da daukar ma’anar farko musamman kasantuwar mu dauki cewa kalmar da zamu iya kaddarawa ita ce masallaci, domin kasantuwar dacewarta da abin da ya zo a cikin jumlar, kuma shi ne abin da ya fi dacewa ya kuma fi karfi. Saboda haka wannan hukunci wanda Ibn Taimiyya ya dauka zai zama sam ba shi da ma’ana a nan.
Haka nan idan muka dauki ma’ana ta biyu wato muka dauka cewa ai a nan ana nufin "wuri" wato bai halitta ba mutum ya tafi wani wuri sai wadannan wurare guda uku, wannann kuwa zai bayar da ma’anar da ba ta dace ba, sannan fitowar wannan kalma daga mai hikima musamman Manzo ba zai yiwu ba. Wato ya zama an hana zuwa kowane wuri sai wadannan wurare guda uku (Masallacin ka’aba, Kudus da Masallacin Manzo). alhalin musulunci ya halatta wasu tafiye-tafiye da dama a cikin musulunci wasu daga cikinsu ma mustahabbi ne. Misali kamar tafiya domin neman ilimi, ko tafiya domin kasuwanci ko tafiya don sada zumunci, tafiya don yawon bude ido, tafiya domin jihadi da dai sauran tafiye-tafiye da suke halas wadansu ma mustahabbi a musulunci.
Saboda haka a nan dole ne mu dauki ma’ana ta farko wato masallaci, cewa kada mutum ya yi tafiya domin ya je wani masallaci sai masallatai guda uku, domin kuwa su ne su kafi sauran masallatai matsayi. Da wannan ne zamu fitar da batun tafiya domin ziyarar Manzo domin ba ita ake magana ba a cikin wannan hadisi.
Bayan dangane da ingancin wannan hadisi koda an dauki ma’ana ta farko, akwai shakku a cikinsa. Domin kuwa yana nufin wannan magana ta fito daga bakin Manzo inda take nuni da cewa tafiya zuwa kowane masallaci ba ta inganta sai masallatai guda uku. Alhali kuwa ruwayoyi sun zo a kan cewa Manzo (S.A.W). Wasu ranakun Asabar yakan tafi kasa, wata sa’a bisa abin hawa domin ya je masallacin "Kuba?" domin ya yi salla raka’a biyu a wajen. Wannan masallaci a zamanin da Manzo yake a raye yana da tazarar kilo mita 12 tsakaninsa da Madina.[54]