Matsayin Ahlul-baiti-2
Matsayi Da Mukamin Ahlulbait (A.S)2 | |||||
Mu'assasar Al-Balagh
Kur'ani Mai Daraja:
"Allah Ya shaida cewa: Lalle ne babu abin bautawa face Shi, kuma Mala'iku da ma'abuta ilmi sun shaida, Yana tsaye da adalci, babu abin bautawa face Shi, Mabuwayi, Mai Hikima". (Surar Aali Imrana, 3: 18) .Matsayi Da Mukamin Ahlulbait (A.S)2
Ta Uku: Ayar Mubahala فَمَنْ حاجَّكَ فيهِ مِنْ بَعْدِ مَا جَاءكَ ك مِنَ الْعِلْمِ فَقُل تَعالَوا نَدْعُ أبْنَاءَنَا وأبْنَاءَكُمْ ونِسَاءَنَا ونِسَاءَكُمْ وأَنْفُسَنَا أنْفُسَكُمْ ثُمَّ نَبْتَهِلْ فَنَجْعَلْ لَعْنَةُ الله عَلى الكَذِبين "To, wanda ya yi musu da kai a cikinsa, a bayan abin da ya zo maka daga ilmi, to ka ce: "Ku zo mu kirayi 'ya'yanmu da 'ya'yanku da matanmu da matanku da kanmu da kanku, sa'an nan kuma mu kankantar da kai, sa'an nan kuma mu sanya la'anar Allah a kan makaryata". (Surar Ali Imrana, 3: 61) Wani abu mai madauwamin tarihi wanda malaman tarihi da tafsiri sun ruwaito shi ya auku, wanda kuma yake nunawa al'umma irin girma da daukakan Ahlulbaitin Manzon Allah (S.A.W), su ne kuwa: Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (A.S) a wajen Allah (S.W.T.) da kuma matsayinsu a cikin wannan al'umma. Wannan abin kuwa kamar yadda su malaman tafsiri da tarihin suka kawo shi ne cewa wata tawaga( ) ta kiristocin Najran ta zo domin ta yi jayayya da Manzon Allah (S.A.W) don a gane waye yake kan gaskiya. Nan take sai Allah Ya umurce shi cikin wannan aya mai albarka da ya kira Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (A.S) ya fita da su zuwa wani kwazazzabo, ya kuma kira Kiristocin da 'ya'yansu da matansu su fito sannan a yi addu'ar Allah Ya saukar da azaba kan makaryata. Zamakhshari a cikin Al-Kashshaf yana cewa: "Yayin da Manzon Allah (S.A.W) ya kiraye su zuwa ga Mubahala( ), sai suka ce: sai mun koma mun yi nazari. Da suka kebanta sai suka ce wa shugabansu; "Ya Abdul Masih! Me ka ke gani? Sai ya ce: "Wallahi, Ya ku jama'ar Nasara, kun sani cewa Muhammadu Annabi ne wanda aka aiko shi kuma hakika ya zo muku da bayani mai rarrabewa game da al'amarin sahibinku. Wallahi babu wata al'umma da ta taba yin mubahala da wani Annabi face babbansu ya halaka, karaminsu kuma ya gagara girma, to idan ko kun aikata hakan to lallai za mu halaka. Idan kun zabi riko da adddininku da zama bisa abin da kuke kansa to ku yi bankwana da mutumin na Larabawa, ku koma garinku. Ko da gari ya waye sai Manzon Allah (S.A.W) ya fito yana mai sammako, yana rungume da Husaini (A.S) yana rike da hannun Imam Hasan (A.S), Fadima (A.S) kuwa tana biye da shi sannan shi kuma Aliyu (A.S) yana bayanta, sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce musu: "Idan na yi addu'a ku ce amin". Ko da Kiristocin nan suka hango Manzon Allah (S.A.W) yana zuwa da tasa tawagar, sai wannan Fadan da ke cikinsu ya ce musu: "Ya jama'ar Nasara! Wallahi ni ina ganin wasu fuskokin da idan Allah Ya so gusar da wani tsauni daga muhallinsa domin alhurmansu sai Ya yi. Don haka (ina shawartarku) da kada ku yi Mubahala da su don za ku halaka ya zamo babu wani kiristan da zai wanzu a bayan kasa har tashin kiyama". To daga nan sai suka ce wa Manzon Allah (S.A.W) cewa: "Ya Abal Kasim! Mun yi shawara ba za mu yi mubahala da kai ba, mu bar ka a kan addininka, mu kuma mu tabbata a bisa addininmu". Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce musu: "Idan kun ki yarda da mubahala, to ku musulunta duk hakkin da musulmai ke da shi kuma kuna da shi, duk kuwa abin da yake kansu yana kanku". Amma sai suka ki, don haka sai ya ce musu: "To ni zan yake ku". Sai suka ce : "Ba mu da karfin yaki da Larabawa, amma za mu yi sulhu da kai cewa ba za ka kai mana hari ba, ba za ka tsoratamu ba, ba za ka fitar da mu daga addininmu ba. Mu kuma za mu kawo riguna dubu biyu duk shekara, dubu daya cikin watan Safar dubu dayan kuwa cikin watan Rajab, da kuma sulken karfe guda talatin". Sai Manzon Allah (S.A.W) ya yi sulhu da su akan hakan, sa'an nan ya ce: "Na rantse da Wanda raina yake HannunSa, hakika halaka ta yi reto kan mutanen Najran, da sun yi mubahala (da mu) da an shafe su an mai da su birrai da aladu, da kuma kwazazzabon nan ya kama da wuta a kansu da kuma Allah Ya tuge Najran da mutanenta har tsuntsayen da ke bisa bishiyoyi, kuma da ba za a shekara ba face Nasara sun hallaka dukkansu". Sannan Zamakhshari ya ci gaba da bayani kan tafsirin Ayar Mubahala da matsayin Ahlulbaiti (a.s) bayan da ya ba da shaidar matsayinsu mai girma da hadisin Ummul Muminina A'isha, ya ce: "(Annabi) Ya gabatar da su (Ahlulbaiti) a kan kansa ne wajen ambato domin ya yi mana tambihi a kan taushin matsayinsu da kusancinsu (ga Allah), don ya nuna cewa su abin gabatarwa ne a kan kai kuma abin fansa da su. Wannan kuwa shi ne mafi karfin dalili a kan falalar Ashabul Kisa'i( ). Tafsirul Kashshaf na Zamakhshari yayin tafsirin Surar Ali Imrana aya ta 61, haka nan kuma ya zo cikin Tafsirin Tha'alabi daga Mujahid da Kalbi( ). Wannan yanayi (na fitowa domin Mubahala) yana nuna mana fitowar rundunar imani ne tana fuskantar rundunar shirka, sannan kuma wadanda suka fito (a sashin imani) su ne 'yan kan gaba wajen karbar shiriya, su ne magabatan al'umma kuma mafi tsarkin cikinsu, rayuka ne wadanda Allah Ya tafiyar da dauda ga barinsu kuma Ya tsarkake su matukar tsarkakewa. Ba a mayar masu da addu'a, ba a kuma karyata wata maganarsu. Daga nan za mu fahimci cewa dukkan abin da ya zo mana daga Ahlulbaiti (a.s) yana gudana ne bisa wannan matsaya (ta tsarki da fifiko) sawa'un wani tunani ne ko shari'a ko ruwaya ko tafsiri ko shiryarwa da fuskantarwa. Domin su ne magaskanta cikin maganarsu da harkar rayuwarsu da kuma tafarkinsu. Da Ahlulbaiti (a.s) ne Alkur'ani ya kalubalanci abokan gaba Musulunci, ya sanya masu jayayya da su su ne makaryata abubuwan bijirowar tsinuwa da azaba; "…sa'an nan kuma mu sanya la'anar Allah a kan makaryata". Shakka babu da ba don an lamunce mana tabbatuwa da kuma gaskiya cikin abin da yake fitowa daga gare su ba, da Allah bai ba su wannan daukaka ba kuma da Alkur'ani bai yi furuci da wannan ba. Fakhrurrazi ya kawo cikin tafsirinsa Alkabir kwaton-kwacin abin da Zamakhshari ya ruwaito, inda tafsirinsu suka dace da juna a wannan matsayin. Sannan ya yi karin bayani a kan zancen Zamakhshari da cewa: "Ka sani cewa wannan ruwaya daidai take da abin da aka daidaita a kan ingancinsa tsakanin ma'abuta tafsiri da hadisi( )". Allama Tabataba'i ya ce wadanda ake nufi a wannan aya kuma wadanda Allah Ya yi nufin (amfani da su wajen) tsinewa abokan gabarsu, su ne Manzon Allah (S.A.W), Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (A.S). Ga abin da Allama Tabataba'in ya ce: "Malaman hadisi sun hadu a kan ruwaito wannan ruwaya da samun karbuwarta, kuma ma'abuta manyan littattafai kamar su Muslim a cikin Sahihinsa da Tirmidhi a nasa Sahihin, sun tabbatar da wannan ruwaya, sannan malaman tarihi sun karfafa ta. Kana kuma malaman tafsiri sun hadu a kan kawo wannan ruwaya cikin tafsiransu ba tare da wata suka ba, ba kuma kokwanto. Haka nan kuma akwai malaman hadisi da tarihi kamar su Dabari da Abul Fida da Ibn Kathir da Suyudi da sauransu". A cikin wannan aya mai albarka, Allah da ManzonSa Sun yi amfani da Ahlulbaiti (a.s) wajen yin Mubahala da abokan gaban Allah, to hakan kuwa yana sanar da al'umma matsayi da daukakan da suke da shi. Hakika ba don wannan kebantacciyar daukaka da suke da ita a wajen Allah ba, da kuma tsarki na musamman ma ba, da Manzon Allah (S.A.W) bai kira wadannan taurari tsarkaka domin yin barazana ga makiya Allah da saukar da azaba da kuma lamunce amsa addu'arsu ba. A cikin ayar akwai ma'anoni masu zurfi na harshen da aka yi amfani da shi cikin maganar wadanda lallai ne a yi la'akari da su, hakan kuwa shi ne danganta wadannan Taurari (Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini) da Annabi (S.A.W), wato cewan da aka yi "'ya'yanmu" da "matanmu" da "kanmu". Ba don faruwar wannan lamari da fitar da Manzon Allah (S.A.W) ya yi da wadannan Taurari tare da shi ba, da mai yiyuwa zukata su koma ga matan Annabi (S.A.W) wajen kalmar "matanmu", wajen kalmar "'ya'yanmu" kuwa zuwa ga Fadima da sauran 'ya'yan Ma'aiki (S.A.W), sannan wajen kalmar "kanmu" kuwa zuwa ga zatin Annabi (S.A.W) mai tsarki shi kadai. Amma fita da wadannan mutanen hudu da Annabi ya yi tare da shi koma bayan wasunsu, ya fassara mana cewa mafificiyar macen wannan al'umma kuma abin koyi gare ta ita ce Nana Fadima (A.S), zababbun 'ya'yan musulmi kuwa su ne Hasan da Husaini (A.S), don kuwa Alkur'ani ya dangantasu ga Annabi (S.A.W) sai suka zama 'ya'yansa, kamar yadda aya ta nuna. Kana kuma Alkur'ani ya dauki Aliyu (A.S) tamkar ran Manzo (S.A.W). Ta Hudu: Ayar Salati () إنَّ الله ومَلائِكَتَهُ يُصَلُّونَ عَلى النَّبِيّ يأيُّهَا الَّذينَ آمَنُوا صَلُّوا عَلَيْهِ وسَلِّموا تَسليمًا() "Lalle, Allah da Mala'ikunSa suna salati ga Annabi, Ya ku wadanda suka yi imani! Ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama domin amintarwa a gare shi". (Surar Ahzab, 33:56) A cikin ayoyin da suka gabata, Alkur'ani mai girma ya yi magana a kan tsarkin Ahlulbaiti (a.s) da kaunarsu da kuma cewa su ne mutanen gidan Manzon Allah (S.A.W). Masu fassara kuma sun iyakance wadannan mutane da sunayensu cewa su ne Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (A.S). To wannan ayar kuwa ta kawo umurni ne na wajibcin yin salati ga Annabi (S.A.W) da alayensa madaukaka da kuma kebancesu, koma bayan wasunsu da kuma girmama mukaminsu da karamarsu domin al'umma ta san matsayinsu wajen sakon Musulunci a cikin rayuwar al'umma. Fakhrurrazi ya kawo cikin Tafsirinsa abin da aka ruwaito daga Manzon Allah (S.A.W) kan tafsirin wannan aya mai albarka, inda ya ce: "An tambayi Manzon Allah (S.A.W) cewa: "Ya ya za mu yi salati a gare ka Ya Manzon Allah? Sai ya ce: "Ku ce: Ya Allah Ka yi tsira ga Muhammadu da Alayen Muhammadu, kamar yadda Ka yi tsira ga Ibrahim da Alayen Ibrahim, Ka yi albarka ga Muhammadu da Alayen Muhammadu, kamar yadda Ka yi albarka ga Ibrahim da Alayen Ibrahim, lallai Kai Abin godiya ne, Mai girma". Kafin ya kawo wannan nassin, sai da ya bijiro da tafsirin ayar sannan ya ce: "Wannan dalili ne kan mazhabar Shafi'i domin umurnin na wajibci ne( ) saboda haka salati ga Annabi yana wajabta. Kuma salatin ba ya wajaba in ba a tahiya ba, saboda haka yana wajaba ne a cikin tahiya( )". Fakhrurrazi ya karkare da cewa: "Idan Allah da Mala'ikunSa sun yi wa Manzon Allah (S.A.W) salati, to wata bukata kuma yake da shi ga salatinmu? To muna iya cewa yi masa salati ba wai don yana bukatuwa ga salatin ba ne, don kuwa idan ba haka ba ne, to ai babu bukatar salatin Mala'iku bayan salatin Allah a gare shi. Amma ba kome ba ne yasa muke masa salati face bayyana girmamawarmu gare shi, da tausayawarSa gare mu domin Ya saka mana domin salatin. Don haka ne Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "Wanda ya yi mini salati sau guda, Allah Zai masa goma"). A ciki Durrul Mansur na Imam Suyudi, Abdurrazak da Ibn Abi Shaiba da Ahmad da Abd bn Humaid da Bukhari da Muslim da Abu Dauda da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah da Ibn Mardawihi, daga Ka'ab bn Ujrah, ya ce wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah, mun san yadda ake maka sallama, to ya ya ake maka salati? Sai ya ce: "Ka ce: Ya Allah Ka yi tsira a kan Muhammadu da Alayen Muhammadu kamar yadda Ka yi tsira kan Ibrahim da Alayen Ibrahim, lallai Kai ne Abin godiya, Mai girma". Malamin ya kawo hadisai goma sha takwas ban da wannan hadisin dukkan su suna nuni ga tarayyar Alayen Manzon Allah (S.A.W) da shi cikin salati. Ma'abuta littattafan hadisi sun ruwaito su daga sahabbai daban-daban. Ga wasu daga cikinsu: Ibn Abbas da Dalha da Abu Sa'id al-Khudri da Abu Huraira da Abu Mas'ud al-Ansari da Buraida da Ibn Mas'ud da Ka'ab bn Umrah da Ali (A.S). Sannan kuma a cikinsa Imam Ahmad da Tirmizi sun fitar da hadisi daga Hasan bn Ali (A.S) cewa Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "Marowaci shi ne wanda aka ambace ni a gurinsa bai mini salati ba( )". Kamar haka ne malaman fikihu suka ruwaito wajibcin salati ga Annabi Muhammadu da Alayensa (A.S) cikin tahiyar salla( ) da wajibcin kawo ambaton Alayen Muhammadu cikin salla. Duk wanda ya sa ido a kan wannan aya zai fahimci cewa manufar shar'anta salatin da lizimtar da shi shi ne girmama Alayen Manzon Allah (S.A.W), wadanda Allah Ya tafiyar da dauda daga gare su kuma Ya tsarkake su matukar tsarkakewa, domin al'umma ta yi koyi da su, ta bi tafarkinsu, kuma ta fake a gare su lokacin fitinu da sassabawa. To wadannan da salla ba ta inganta sai gami da an masu salati, su ne Shuwagabannin al'umma, su ne a ka yi nuni da su kuma aka lamunce a yi koyi da su. Ba don tabbata da lamuncewar tsayuwarsu da kubutar abin da ya fito daga gare su ba, da Allah bai umurci musulmi a dukkan zamunna da su rataya da su da yi musu salati cikin kowace salla ba. Hakika cikin wannan maimaitawa - maimaita salati ga Annabi da Alayensa, da kuma farlanta hakan a kowace salla - akwai jaddadawa da jan hankulan musulmi cikin kowace salla saboda muhimmanci Ahlulbaiti (a.s) da matsayinsu, da kuma koyi da su da rayuwa bisa tafarki da hanyarsu. Ta Biyar: Surar Insan "Hakika mutane na gari suna sha daga wani kofin (giya) da mahadinta ya kasance mai kamshin kafur ne. Akwai abubuwa guda biyar a cikin ko wane daya daga cikinsu da suka kasance wajibai, su ne kuwa: zama gwargwadon tahiya, yin shahadojin nan guda biyu da salati ga Annabi da Alayensa (A.S). Dubi Shara'ii Islam, juzu'i na 1, babin salla. (Shi kafur din) wani marmaro ne da bayin Allah suke sha daga gare shi suna bubbugo shi bubbugowa ta hakika. (Don ko) suna cika alkawari na bakance suna kuma tsoron ranar da sharrinta ya kasance mai tartsatsi ne. Suna kuma ciyar da abinci tare da kuma suna son sa; ga miskini da maraya da kuma ribatacce a yaki. (Suna cewa): "Mu kawai muna ciyar da ku ne saboda Allah, ba ma nufin sakamako ko godiya daga wurinku. Hakika mu muna jin tsoron rana mai sa daure fuska matsananciya daga Ubangijinmu". Sai Allah Ya kare su (daga) sharrin wannan ranar Ya kuma hada su da haske da kuma farin ciki. Ya kuma saka musu da Aljanna da alhariri saboda hakurin da suka yi. Suna masu kishingida a cikinta a kan gadaje ba sa samun zafin rana ko sanyi a cikinta. Inuwowinta suna kusa da su, an kuma yiwo kasa-kasa da 'ya'yan itacenta kasa sosai. Ana kuma kai-ka-wo da korai na azurfa da kofuna wadanda suka kasance na karau. Karau din na azurfa ne, sun auna su, aunawa daidai da bukata. Ana kuma shayar da su wata giya a cikinta wadda mahadinta ya kasnce mai kanshin zanjabilu ne (watau citta mai yatsu). (Shi zanjabilu) wani marmaro ne a cikinta da ake kiran sa Salsabilu. Samarin hadimai dawwamammu da ba sa tsufa kuma suna kai-ka-wo tsakaninsu, idan ka gan su sai ka yi tsammanin su wani lu'u-lu'u ne wanda aka baza. Idan kuma ka yi kallo a canza ka ga ni'ima da kuma mulki kasaitacce. A samansu akwai tufafi sakar alhariri koraye da kuma abawarsa, aka kuma yi musu ado da warawarai na azurfa, Ubangijinsu kuma Ya shayar da su abin sha mai tsafta. Hakika wannan ya kasance sakamako ne a gare ku, kuma aikinku ya kasance abin godewa. A cikin wadannan ayoyi masu albarka, Alkur'ani ya yi zancen Ahlulbaiti (a.s) ya kuma sanya su su ne koluluwar masu gabatar da wani bisa kansu wajen ciyarwa da kuma takawa. Alku'ani ya sanya su misali da ja-gora ga dan'Adam, domin sauran mutane su yi koyi da su da kuma rayuwa bisa tafarkinsu. Abin da ya faru har ya sa aka saukar da wadannan ayoyi dominsa yana nuni ne da matsayin Ahlulbaiti (a.s) da kaiwarsu matuka wajen aikatawa da lizimtar shari'a da kuma fuskantar Allah cikakkiya. Kuma su ne mutanen kirkin da aka yi musu albishir da aljanna, to duk wanda ya yi koyi da su, ya yi tafiya a kan tafarkinsu, to za a tashe shi tare da su. Zamakhshari ya kawo bayani kan wannan aya cikin tafsirinsa. Ga abin da ya ce: (Daga Ibn Abbas (r.a.): Wata rana Hasan da Husaini (A.S) sun yi rashin lafiya, sai Manzon Allah (S.A.W) tare da wasu mutane suka ziyarce su don gai da su, sai ya ce wa Imam Ali (A.S): Ya Abal Hasan, da dai ka yi bakance kan rashin lafiyar 'ya'yanka. Sai Aliyu da Fadima da baiwarsu Fiddha suka ce idan suka sami sauki daga wannan ciwo nasu, za su yi azumin kwanaki uku. Sai kuwa suka warke, alhalin kuwa a wannan gida mai albarka babu wani abu na daga abinci. Sai Aliyu (A.S) ya yi bashin sa'i uku na Sha'ir daga wani Bayahude mai suna Sham'un Alkhaibari, daga nan sai Fadima ta nika sa'i guda ta yi gurasa biyar, adadin mutanen gidan. Sai ta sanya gurasar a gabansu domin su yi buda baki, bayan lokacin shan ruwa ya yi. Sun shirya za su ci kenan sai ga wani almajiri ya tsaya a kofa ya ce: Assalamu Alaikum, mutanen gidan Muhammadu (S.A.W), ni miskini ne daga miskinan musulmi, ku ciyar da ni, Allah Ya ciyar da ku daga abincin aljanna. Sai suka fifita shi (wajen cin abincin) wato suka dauka suka ba shi, su kuwa suka kwana ba su dandani kome ba, sai ruwa, sannan kuma suka wayi gari da azumi a bakinsu. Da suka kai maraice, suka sake shirya abincin buda baki, sai ga wani maraya ya tsaya a kofa ya yi bara, nan take suka dauki abincin suka ba shi, suka kwana haka. A rana ta uku ma suka ci gaba da azumi, shi ma da lokacin buda baki ya yi suka shirya dan abin da ya sawwaka, a nan ma sai ga wani kamamme ya zo shi ma yana neman abin da zai ci. Sai suka dauki abin da suka tanada suka ba shi. Da suka wayi gari sai Aliyu (r.a.) ya kama hannun Hasan da Husaini suka nufi gurin Manzon Allah (S.A.W). Yayin da Annabi (S.A.W) ya gansu suna karkarwa kamar 'ya'yan tsaki saboda tsananin yunwa, sai ya ce: "Babu abin da zai bakanta mini rai fiye da halin da na ganku a ciki". Sai ya tashi ya tafi tare da su sai ya ga Fadima (A.S) tana wurin sallarta alhali bayanta ya mannu da cikinta, idanunta sun fada. Ganinta cikin irin wannan hali ya bakanta wa Manzon Allah (S.A.W) rai, sai ga Jibrilu (A.S) ya sauko ya ce: "Karbi ya Muhammadu, Allah Na tayaka murna batun Ahlulbaitinka", sai ya karanta masa wannan surar( ). Ta Shida: Hakika ayoyin Alkur'ani masu yawa sun sauka da batun Imam Aliyu bn Abi Talib (A.S) wanda aka yi tarbiyyarsa cikin gidan Manzon Allah (S.A.W) tun yana karami( ). Ya tashi karkashin kiyayewarsa (S.A.W) don haka ya kwaikwayi halayensa. Ya yi imani da shi, gaskanta shi da kuma binsa tun yana dan shekara goma. Sannan kuma Imam Ali (A.S) ya kasance mai daukar tutar Manzon Allah (S.A.W) kuma shi ne jarumin sojansa wanda ya kere kowa a dukkan yake-yakensa, da suka hada da Badar, Uhud, Hunain, Ahzab, Khaibar, Zatu Silasil da dai sauransu. A saboda irin jaruntar da ya nuna a irin wadannan yakuna, ya sa Manzon Allah (S.A.W) da kansa ya jinjina masa da bayyanar da wasu kalmomi dawwamammu da suka kasance ado ga littatta-fan tarihi sannan kuma abin koyi na koli cikin sadaukar-wa da kuma jihadi. Idan muka yi bincike kan asbabun Nuzul (dalilan saukar ayoyi), za mu samu cewa abin da ya sauka dangane da Amirul Muminina, Aliyu bn Abi Talib (A.S) ban da abin da muka ambata na Ahlulbaiti (a.s) -suna bayani ne: Kan jaruntar Aliyu (A.S) gwarzontaka da kuma sadaukarwarsa a kan tafarkin Allah kan hakurinsa bisa cutarwa da izgili. Kan gudun duniya, takawa ilimi da kuma kaunarsa ga muminai.Bari mu ambato wasu misalai kamar haka: Ayar Wilayah: إنَّما وليُّكُمُ اللهُ ورَسولُهُ والَّذينَ آمَنوا الَّذينَ يُقيمونَ الصَّلاةَ ويُؤتُونَ الزَّكاةَ وهُمْ راكِعونَ # ومَنْ يَتَوَلَّ اللهَ ورَسُولَهُ والَّذينَ آمَنُوا فإنَّ حِزْبَ اللهِ هُمُ الغالِبُونَ "Abin sani kawai, majibincinku Allah ne da ManzonSa da wadanda suka yi imani, wadanda suke tsayar da salla, kuma suna bayar da zakka alhali suna masu ruku'i. Kuma wanda ya jibinci Allah da ManzonSa da wadanda suka yi imani, to, kungiyar Allah su ne masu rinjaye". (Surar Ma'ida, 5: 55-56) Zamakhshari cikin tafsirinsa ya bayyana cewa: "Wannan aya ta sauka ne dangane da Aliyu (Allah Ya karrama fuskarsa) lokacin da wani ya roke shi alhali yana cikin ruku'in salla, sai ya sake masa zobensa wanda yake loko-loko a dan kuriyarsa, wanda cire shi baya bukatar aiki mai yawa da ka iya bata salla. Idan ka ce ta ya ya za a ce da Ali ake alhali lafazin na jam'i ne? sai in ce maka: An zo da shi akan lafazin jam'i ne ko da yake dalilin saukar ayar a kan mutum guda ne domin a kwadaitar da mutane wajen yin tamkar aikinsa, sai su sami tamkar ladansa. Domin kuma tambihi cewa halayen muminai wajibi ne su kasance da wannan koluwa wajen kwadayin aikin alheri da bibiyar lamarin mabukata ta yadda idan wani abin da ba ya son jinkiri ya lizimce su suna cikin salla, ba sa jinkirta shi sai an idar da sallar( )". Al-Wahidi ya ambata cewa al-Kalbi ya fadi cikin dalilin saukar wannan aya, cewa: "Lalle karshen wannan aya a kan Aliyu dan Abi Talib (r.a.) take domin ya ba da zobensa ga wani mai bara alhali yana cikin ruku'un salla( )". Littattafan tafsiri da hadisi masu yawa sun ambato cewa wannan aya mai albarka ta sauka ne dangane da Imam Ali (A.S). Akwai cikakken bayani kan hakan cikin wadannan littattafa ga mai karin bayani( ). Ayar Tabligh (Isar da Sako): يا أيُّهَا الرَّسُولُ بَلِّغْ مَآ أُنْزِلَ إلَيْكَ مِنْ رَبِّكَ وَإنْ لمْ تَفْعَلْ فَمَا بَلَّغْتَ رِسَالَتَهُ واللهُ بَعْصِمُكَ مِنَ النَّاسِ. "Ya kai Manzo! Ka iyar da abin da aka saukar maka daga Ubagijinka. Kuma idan baka aikata ba, to, ba ka iyar da sakonSa ba kenan, kuma Allah Zai tsare ka daga mutane...( )" (Surar Ma'ida: 5:67). |