Bayanin Shianci

Bayanin Shianci

SHEIKH WA'ILI (r)

Godiya ta tabbata ga Allah (s.w.t) Kuma Aminci ya kara tabbata ga bayinsa wadanda ya zaba

Mene ne Shianci?
Da yawa wasu mutane da ake ganin su a matsayin masana addini suka dauki matakin gaba da wata mazhaba saboda bangaranci ko kuma domin sun jahilce ta, mazhabar tafarkin Ahlul-baiti (a.s) ita ce mazhaba ta farko da take fuskantar wannan lamarin na soke-soke. Abin mamaki a irin wannan zamanin da zaka samu yalwatar litattafai da kafofin watsa labarai, da hanyoyin sadarwa, amma irin wadannan kage-kage na karya da yarfe ba su kare ba kan wannan mazhabi. Sai ga shi a irin wannan zamanin an samu wani daga cikin marubuta yana cewa: Lallai Shi'anci ya saba wa hankali, kuma abu ne kullalle. Ya ce: Dan Shi'a bai yarda da hankali ba, don haka ne sai tatsuniya da labarun karya suka yi kamari a gareshi. Saboda irin wadannan kage-kage ne da ake yi wa shi'anci da 'yan shi'a aka rubuta litattafan Shi'a wadanda duk wani mai neman sanin wannan mazhabin yake bukatar koma wa garesu domin sanin shi'anci da bincike kansa.
Shi'anci a lugga yana nufin taimakawa, ko biyayya, ko jibinta lamari, dan Shi'a shi ne mai taimakawa ko biyayya ko jibinta lamari. Don haka ne idan aka ce shi'ar Ali to ana nufin masu biyayya ko taimakawa ko jibita lamarinsu ga imam Ali (a.s). Kalmar shi'anci da wannan ma'anar ba ta kebantu da wasu jama'a ba, sai dai mun samu an kebance ta da mabiya Sayyidi Ali (a.s) har suka shahara da ita. Asalinta shi ne; Shi'ar Ali, amma daga baya sai aka cire Ali sai aka takaita da amfani da kalmar Shi'a. Don haka duk wanda yake biyayya ga tafarkin Imam Ali (a.s) da Alayen Manzon Allah (s.a.w) wadanda dukkaninsu su goma sha biyu (a.s) sun fito daga tsatson manzon Allah (s.a.w) ne, don haka dan Shi'a shi ne mutumin da yake biyayya ga manzon Allah (s.a.w) da halifofinsa daga zuriyarsa su goma sha biyu, wadanda ya yi wasiyya da biyayya garesu bayansa, wadanda na farkonsu shi ne Ali (a.s), na karshensu Mahadi (a.s) wadanda su ne halifofinsa shiryayyu masu shiryarwa.
Muna iya gani game da Kalmar Shi'a cewa: Ya zo a cikin Kur'ani mai girma: "Kuma hakika daga shi'arsa lallai akwai Ibrahim". Saffat: 83.
A wannan aya an siffanta Annabi Ibrahim (a.s) daga cikin masu taimakawa, ko mabiya tafarkin Annabi Nuhu (a.s) na tauhidi, masu ra'ayi da tunani da akidu irin nasa.
Daga cikin abubuwan da ake muhawara da tattaunawa ta ilimi a kai a wannan zamani kan mas'alar mazhabobin musulunci mafi girma wato Shi'a da Sunna, akwai tattaunawar da wasu suke yi a kai wanda yawanci a kan kawo shi ne ta fuskacin suka ga shi'anci (tafarkin biyayya ga) Ahlul-baiti (a.s).
Bayan shekaru masu yawan gaske sarakuna suna bata sunan tsatson gidan annabi (s.a.w) da mabiyansu da yi musu bita da kulli da makirce-makirce iri-iri sai ga canji ya samu a duniyar musulmi, wannan samun canjin zamanin wayewa da saukin hanyoyin isar da sako a duniya ya yi tasiri matuka wurin sanin al'ummar musulmi game da hakikar mazhabin shi'anci. Don haka ne muka ga karin fahimtar wannan mazhabin a duniya baki daya har da kasashen Afrika, da yaduwarsa saboda samun haske kan fahimtar koyarwar alayen manzon Allah (s.a.w).
Wannan lamarin ne ya sanya wasu masu gaba da wannan tafarki suke cewa: Wannan yana nufin rashin gaskiyar Shi'anci ke nan, domin dukkan addinai a karshensu ne suke lalacewa su karkace daga tafarkin gaskiya, saboda haka addinin musulunci ya lalace ne saboda samuwar Rawafidanci (mai suka yana nufin shia'nci, kamar yadda makiya shi'a suke gaya musu).
Sai dai irin wannan sukan ba shi da wani asasi da tushe idan muka yi duba da la'akar da wasu bayanai kamar haka:
Na daya: Idan dai koma wa cikin wani mazhabin ko addini yana nufin wanda ake shiga cikinsa karya ne, to me zaka ce game da kafirai da suke shiga musulunci, shin musulunci karya ne shi ya sa suke shiga cikinsa?! Idan ka ce: haka ne, to ka yarda da kushe musulunci da karyata gaskiyarsa ke nan. Idan kuwa ba haka ba ne, to musulunci da mazhabinsa na shi'anci sun zama gaskiya ke nan.
Na biyu: Fitinar da ta faru a cikin musulmi saboda abin da sarakuna masu kiyayya da mazhabin shi'anci suka yi ne na kashe zuriyar Annabinsu, suka watsa su cikin garuruwa, suka hana su gadonsu, suka zagi sayyidi Ali (a.s) a kan minbarorinsu gaba dayan tsawon lokacin mulkin Umayyawa har zuwa kan Dan Abdul'aziz.
Na uku: Shi'anci bai kasance kamar yadda mai suka yake kawowa ba, domin Shi'a ba su taba barin littafin Allah da Sunnarsa da zuriyar annabinsa ba ko sau daya, mai gani da idon basira ya duba ya gani shin da abin da suka aikata ne addini ya lalace ko da abin da makiyansu suka aiwatar?
Sannan idan aka ce Shi'a ba ana nufin kishiyar Sunna ba kamar yadda wasu suka jahilci hakan, domin kalmar Sunna da ake gaya wa daya bangaren ba ta nufin Sunnar Annabi, sai dai suna ne na daya bangaren da ya samu a tarihi. Mai son karin bayani ya duba litattafan tarihi domin samun dalilin da ya sa aka samu wannan suna na Ahlus-Sunna da dalilin kara kalmar Wal-jama'a a cikinsa a shekara ta arba'in bayan hijira.
Don haka Sunnar annabi abu ce da kowanne Shi'a da Sunna yake ganin shi ya fi biyayya gareta. Amma sanin waye ya fi kusa da ita yana iya bayyana idan duka aka auna su da littafin Allah da sunnar manzonsa ne.
Sai dai kasancewar Shi'a mabiya tsatson manzon Allah (s.a.w) ba su bar wasiyyar manzon Allah (s.a.w) ga wannan al'ummar ta yin biyayya ga alayensa bayansa ba, ba su yarda da kona sunnarsa ba, ba su yarda da rashin rubuta ta ba, ba su yarda da yin ijtihadi da barin Sunna ba, don haka su suka fi cancanta da sunnar manzon Allah (s.a.w).
Sannan bayan wannan bangare biyu masu girma na musulmi wadanda suka yi tarayya a kan cewa su 'yan'uwan juna ne da aka fi sani da Sunna da Shi'a, sai kuma a wadannan karnoni na karshe aka samu kungiya ta uku ta musulmi da aka fi sani da Wahabiyawa masu da'awar cewa su suke da wannan sunan na Ahlus-Sunna wal-jama'a, mai biyayya ga tafarkin Dan Taimiyya da Dan Abdulwahab, wadanda suka kafirta Sunna da Shi'a duka saboda wasu dalilai nasu da suke gani, sakamakon haka ne zamu ga jama'ar musulmi ta kasu gida uku ke nan.
Don haka ne ake kira ga samari masu son yin bincike game da akidojin Shi'a da su yi riko da ka'idar bincike wajan sanin mene ne shi'anci, su koma wa litattafansu na asali da malamansu suka rubuta, da koma wa malamansu don sanin ingantacce a cikin litattafan. Kuma kada su dogara da abin da wani ya fada ko ya rubuta game da Shi'a, wanda ba malami ne da ake la'akari da shi a shi'anci ba. Balle su karba daga malaman da ba Shi'a ba ne su, balle kuma masu gaba da su na wahabiyawa wadanda suke kawo maganganu game da Shi'a ba tare da la'akari da inganci ko rashin inganci ba, sannan na bayansu su zo ba tare da bincike ba su bi sawunsu.
Daga karshe muna rokon Allah ya sa mu dace da yin aiki da littafinsa mai girma, da tafiya a kan tafarkin cikamakon Annabawa Manzo Muhammad (s.a.w), da tsatsonsa alayensa Ahlul-baiti (a.s).
Sakamakon cewa wadanda suka rubuta littafin a inji mai kwakwalwa bayan fassara shi sun rubuta kurakurai masu yawan gaske, wannan ya sanya na dauki matukar lokaci mai yawa wurin gyara, don haka nake kira ga duk wanda ya ga wani kuskure ya gaugauta sanar da mu.

Gabatarwar Bugu Na Biyu
Tsira da amincin Allah su tabbata ga shugbanmu Muhammad da alayensa tsarkaka da sahabbansa da wanda ya bi su da kyautatawa, bayan haka:
Wannan dan littafin ya kasance mai kayatarwa gun masu karatu duk da kuwa ya kasance takaitacce, wannan kuwa ba domin komai ba sai domin irin tsarin da na bi ne wajen rubuta shi ya kasance ya fi littafin kansa kyau, domin idan mun duba zamu ga shi littafin ba shi da wani girma sosai ta yadda zai kasance ya yi wani fice ta wannan fuskacin, sai dai zamu iya ganin sa bai wuce wasu 'yan takardu ba, sai dai an kyautata bayani a cikinsa da kuma kyawun zabin bayanai da lura da abubuwan da suke masu tasiri na musamman a cikin zukata, hada da nau'in tsarin da aka yi masa. Kuma yana daga cikin abin da ya kamata a yi nuni da shi cewa irin yadda nan da nan daga sanya shi kasuwa sai ya kare da wuri ba tare da wani tallata shi da muka yi ba a cikin jaridu ko a wani taro, an kai shi kasuwa ne kawai kamar yadda aka saba, kamar yadda yake a bisa al'ada.
Wannan al'amarin kuwa shi ne ya karfafa mu yin rubutu a cikin irin wannan maudu'i wanda yake mahallin cece-kuce tsakanin bangarorin mazhabobi da darikokin musulmi. Sannan kuma akwai fatan ganin an samu farin cikin muminai a cikin wannan lamari ga wanda da yake neman yardar Allah kuma yake neman ganin an kawar da kiyayya ta hanyar kawo abubuwan da aka yi tarayya a tsakanin musulmi a cikin dukkanin fagagen ci gaban musulunci wanda ya shafi hukucnin shari'a ko akidarmusukunci ko tarihin musulmi, kuma ta yiwu mu kara da cewa yana iya zamantowa cewa birorrukan marubuta masu tsafta suna iya kasancewa hanyar da zata kasance mai rabauta ga hidimar musulmi kuma mafi kyawun hanya domin samun fahimta tsakanin musulmi.
Wannan kuwa hada da cewa wannan hanyar tana iya yanke hannayen hanyoyin nan na 'yan barandan makiya da suke karbar kudade domin ganin sun kawo yamutsi da hura wuta da yada kiyayya tsakanin al'ummar musulmi kamar yadda muna iya ganin haka a wasu wurare lokaci bayan lokaci, wanda wannan al'amari ne da yake ba mu tabbacin cewa lallai akwai wasu hannayen marubuta masu bin 'yan jiya da ba su gushe ba suna irin wannan mummunan aiki a duk lokacin da suka samu dama.
Kuma ina maimamaita abin da ya gabata a cikin bugu na daya cewa idan an samu wani kalami ko wata magana maras dadi a cikin bayanina to ba yana nufin domin gaba ne ko kiyayya ba, ina neman tsarin Allah daga irin wannan fushi da bai kasance domin imani ba ko kuma nuna fushi kan abin da ya shafi hadin kan musulmi ko kuma wani abu da zai nuna halaccin irin wannan usulubi.
To tunda kamala cikakkiya ta kasance ga Allah ne shi kadai, kuma mutum yana da tawaya, don haka ne ma kokarin ganin ya samu dadi a cikin wannan kamalar tasa ya kasance daga al'amuran da ake so, don haka ne ma sai na mike tsaye wajen ganin na gyara wannan rubutu da kuma yin wasu kare-kare da nake ganin zasu kamala wannan Littafi, kuma ina sanar da mai karanta wannan littafin da cewa yana da kyau ya kalli wannan littafin da kallon da yake na nakadi na ilimi, ba irin na iface-ifacen nan na masu son zage-zage ba wadanda suke jifan waninsu da wani abu da suke da shi wanda shi wanda suke jifa din ba shi da shi, sai dai son rai ne ya rufe idanuwansu ya kurumtar da su.
Abin da aka fada ga me da wani mutum kwarai ya kayatar da ake cewa da shi me ya sa kuke canza "K" da "G", kuma kuke canza "Dh" da "Z" (wato suna canza Ğ da Ò su kuma canza Ş da Û) sai ya ce: "äÍä áÇäÛæá Òáß"
Daga karshe ina neman wanda ya karanta wannan littafin ya fadakar da ni idan ya ga wani aibi ko wata zamiyar kafafu, domin mumini madubin mumini ne. Allah ya shiryar da mu ga abin da yake so kuma yake yarda da shi, kuma muna godewa Allah tun farko har zuwa karshe.
Mawallafi

Gabatarwa bugu na farko
Da Sunan Allah mai rahama mai jin kai
Akwai abubuwan da mai karatu ba zai iya wadatuwa da su ba kafin ya shiga cikin ainihin maudu'in da muke magana a kai, domin wadannan abubuwan zasu kunshi amsa ne na abubuwan da zasu iya zowa mai karatu na daga tambayoyi yayin karanta littafin, kamar yadda haka nan kuma zasu iya sanya mai karatu ya fahimci abin da ake magana a kansa tun farko domin kada ya samu fahimtar akasin abin da littafin yake son bayani kansa. Kuma muna iya kawo wadannan abubuwa a takaice kamar haka:
1- Zai iya yiwuwa mai karatu saboda ya ga Sunan littafin "Hakikar Shi'anci" ya dauka cewa wannan littafin zai yi magana ne kan dukkan abin da ya shafi Shi'anci ne tun daga sama har kasa. Domin kada ya fahimci hakan; Ina son in jawo hankalinsa ya fahimci cewa ni a wannan littafin ban kawo dukkan abin da ya shafi Shi'anci ba na daga bayanai da suke siffanta shi ko kuma suke magana a kan hakikaninsa ne, sai dai ni na kawo wasu abubuwa ne da zasu iya isa domin bayanin hakikanin Shi'anci kuma a lokaci guda akwai bayanin abubuwan da ake da sabani tsakanin bangarorin musulmi a cikinsa musamman wanda ya shafi sabani tsakanin wani bangare na musulmi da kuma Shi'a, kuma suka kasance har yanzu akwai jayayya da sabanin a tsakaninsu duk da kuwa irin rubuce-rubuce da aka yi a kansu tun da dadewa har zuwa wannan lokaci namu kuma suka shafi wani bayani game da Shi'anci ta fuskancin bangaren al'umma da bangaren fikirarsa.
2- Kuma a bisa hakika akwai mutane masu yawa tun da can da suka rubuta litattafai masu yawa masu zurfi fiye da wannan kuma masu tsayi da kayatarwa fiye da haka a game da 'yan Shi'a da Shi'anci, sai dai ni ina ganin na gyara wasu abubuwan da suka kunsa ta hanyar rubutu da wani sabon usulubi da ya saba da na sauran, kuma amma ba ina cewa wannan usulubin da na zaba ya fi sauran ba ne, sai dai ina da tabbacin cewa wannan zai fi saurin kai mai karatu zuwa ga abin da yake son samu na natija a cikin karatunsa, domin kuwa ba ni ne farkon wanda ya yi kokari ya kuma yi kuskure ba, kuma irin wadannan mutane suna da yawa a tarihi.
3- Mai karatu yana iya cin karo da wasu matsalolin da miyagun asakaloli da yakoki da sa-in-sa suka haifar a cikin tarihin musulmi kamar yadda dukkan wanda ya taba lekawa tarihi zai iya ganin irin wadannan miyagun munanan abubuwan da aka haifar da su a tsawon tarihin musulmi, kuma wadanann abubuwa ne da suke sun faro bisa yanayin dabi'ar rayuwar musulmi duka da kuwa jure wa jin su yana yi wa mutane wahala, amma duk wanda ya saba da rubutu a irin wadannan fagage ya san irin girman ciwon da ake ji kuma da irin juriya da ake bukata wajen hakan. Amma wani babban abin takaici sai ga da yawa daga marubuta sun gajiya sun karkatar da alkalamin rubutunsu yana bin son zuciya da kuma bangaranci da muhimmancin wannan al'amari da yake wucewa yau da gobe da kuma irin tunkudar hadari da bala'in da yake zuwa lokaci lokaci, da kuma mutanen da suke kawo shubuhohi wadanda su ba su yi nesa da shubuhohin ba, kuma wannan turnuki zai ci gaba a wannan yanayi mai duhu kuma yana ci gaba a wannan lokaci namu muna ganinsa ba tare da mun yi wani kokarin mun tsaftace shi ba, mun fito da komai fili mun kuma ta ce shi tacewa cikakkiya domin mukai ga wani ra'ayi da wani sakamako. Kuma ina iya maimaitawa cewa mu sani wannan juriyar ba wani abu ne mai sauki ba a bisa hakika domin mutun ya fi bin son zuciyarsa fiye da hankalinsa sai wanda kyawawan halayensa suka yi wa dabaibayi kuma addini yake tsarkake shi, kuma Allah ne muke roko ya sanya mu daga cikinsu.
4- Haka nan kuma wani yana iya cewa duk da abin da ka ambata dazu haka ne, to mene ne amfanin wannan littafin a cikin irin wadannan al'amuran? Sau da yawa mukan samu abin mamaki na dagewa da nacewa a kan jefa irin wadannan mas'alolin kamar hakan, kai ka ce ba a yi magana game da wannan al'amari ba, kuma ba a yawaita tambaya da amsa a kan hakan ba a wurare masu yawa. Suka ce; wannan al'amari shi ne kusan abin da yake sanya mutum yana samun nutsuwa da cewa wadannan al'amura da ake ta magna a kan su ba zasu samu wani warwara ba kuma ga lokacin mai tsada da ake ta batawa a kansu a irin wannan al'amarin.
Idan muna son amsa a kan haka muna iya cewa masu ganin cewa kofa a toshe take to suna son ke nan mu sallama kuma mu yi saranda ga wadannan kalubale da suke fuskantar mu, alhalin ba mu da wani abu da zai iya ba mu mafita sai fuskantar duk wani kalubale. Kuma babu wani lokaci da babu masu bincike kan gaskiya kuma duk wadanda shubuhohi suka rinjaya suna demaucewa ne a cikinta kuma suna da yawa, kuma yin kunnen shegu da bukatun irin wadannan nau'i biyu na mutane ba tare da an taimaka musu ba abu ne wanda masanin sakon karshe na wannan addini da ya zo domin daukaka rayuwa zuwa ga mafi alherin al'amari ba zai iya jure shi ba. Kuma barin wadannan marubuta masu rudarwa su yi wasa da kwakwalen musulmi shi ma wata bayar da gudummuwa ce ga masu kawo rudu. Mu masu kira ne domin share irin wannan alekakai daga tafarkin musulmi har sai hanya ta kasance shararriya a gabansu. Kuma dukkan sakamakon da za a samu a wannan fage yana kasancewa ya yi daidai da kiran nan na da'awar musulunci da kuma yin daidai da jihadi da alkalami da tunani, kuma ba ya daga cikin hankali mu kyale mai rashin lafiya ba tare da mun ba shi koda kwankwada daya ta ruwa ba, alhalin muna da iko a kan hakan kamar yadda muke gani.
Sau da yawa mutun ya rayu tsawon zamani cikin son rai da gajiyawa sannan sai ya koma zuwa ga gaskiya sakamakon alkaluman marubuta masu tsafta da suka gyara masa tunaninsa musamman ma idan wadannan alkaluma suka iya daukar bisa hanya mai sauki kuma suka kasance daga zuciya tsarkakkiya, kuma suka dora rayuwarsa a kan tsarin musulunci mai tsarki.
5- Wani abin da yake iya saukake magana game da abin da yake faruwa na sabani tsakanin bangarorin musulmi tun da ta faru, ba ta kai zuwa ga asasi ba, tana matsayin fagen rassa ne kawai duk da da yawa daga mutane suna son su isar da ita zuwa asasi ta hanyar ba ta wani suna daban da kuma kokarin shigar da wasu abubuwan ta bayan fage. Sai dai idan mun lura sosai zamu ga ta faro ne daga asasi zuwa ga rassa, kuma matukar muna son gaskiyar lamari dole ne mu fara maganin wadannan al'amura. Kuma matukar hankula suna da sabani wajen riska da fahimta kuma fahimta ta sha bamban to abu na hankali shi ne mu ce; sabanin da yake cikin mas'alolin tunani abu ne na tunani da hankali kawai abin da yake jawo mantuwa ga irin wannan shi ne kuntata tunani da kuma son rai.
6- Tun da mas'alolin wannan littafin suna da yawa don haka ne mai karatu ba zai samu maudu'i daya ba kuma saboda haka yanayin da zai samukansa game da hakan zai sassaba. Tare da cewa idrakinmu ga wannan mas'alolin da wannan maudu'i na akida ya tattaro su, sai dai rassan wannan maudu'i mabambanta ne, kuma mu muna idrakin cewa akwai dan musamaha a cikin abin da ake kira akida, domin tana iya yiwuwa ba ya daga abin da mutm yake imani da shi wani lokaci, sai ya kasance wani shi'ari ne kwai da yake da maslaha a cikinsa ko kuma al'adarsa take doruwa a kansa. Kuma wannan sirri ne da ya sanya zamu ga wasu mutane wani lokaci suna riko da wasu tunani da sun san batacce ne. Sai dai yin aiki da tunanin da mutum yake da shi yana daga dalilai mabambanta ne, kuma wannan yana daga musibarmu da bala'in da ya same mu a yau.
7- Ni dai duk abin da nake nema wajen mai karatu shi ne kada ya dauka cewa kiran da muke na barin bangaranci da kada ya dauka mu ma mun zo da bangaranci ne wanda ya zama ke nan kamar mun yi gudu mun komo inda muka bari. Wannan kuwa domin sanya takobi gaban takobi ba koda yaushe ne yake nufin kira zuwa ga yaki ba, kai yana iya zama ma kira ga barinsa ne, kuma bayar da magani mai daci ba don kiyayya ba ne koda kuwa maganin ya fi ciwon daci. Don haka ne ma sau da yawa hadafofi kodayaushe sukan samukansu gaban wasu abubwan da suke yi musu kalubale, kuma matukar hadafi yana girma to da sannu zai nemi wasu hanyoyi a lokuta masu yawa kamar yadda hankali yake doruwa kan hakan, kuma gaskiya take yin halinta a kan hakan.
8- Bayan haka dukkan wannan, kasancewa ta mabiyin tafarkin Ahlul-baiti (a.s) ina kira ga dukkan mai karatu da ya duba abubuwan da suka same su a tarihi da yanayin da suka dade suna samun kansu a kai domin ya kasance masa ma'auni da yake gabansa da zai fassara yanayin tunani da na zamantakewa da ya samu Shi'a, kuma da wannan ne zai nisanci karkacewa daga nau'in hukunci da zai yi musu. Idan ya gan su suna tsanantawa a kan tunanin takiyya to ya sani domin ba su fita daga yanayin hakikanin gaskiyar abin da yake faruwa ba ne kuma ba su saba wa shari'a ba, idan ya ga wasu ayyuka da wasu matakai gun wasunsu to kada ya manta mataki ne na hankali kuma bai kamata ba wani ya auna kansa da ayyukan da wani yake gudanarwa a kansa.
9- Ina takaita dukkan wannan takardu da na rubutu da kiran dukkan bangarorin musulmi da su karanta abin da ya shafi junansu da hankali a aikace, kuma su nisanci sukan juna da bata Sunan wanda ya jawo yayyaga da rusa sahun hadin kan musulmi, sannan kuma su tsaya su karanta sakamakon karanta abin da ya shafi junansu domin samun sakamako mai kyau na wannan yanayi, sannan kuma muna kira duka da hakan ga dukkan musulmi da su sanya tarihi a fagen tuhuma domin mu hukunta shi mu huta da dukkan wannan abubuwan takaici da bakin ciki da ya haifar da muke rayuwa cikinsu, mu sani tarihi yana nan yana aiki a kanmu koda kuwa zamani ya yi nisa tsakaninmu da abin da ya faru a cikinsa. Muna rokon Allah taimakon a kan tafiyarmu gidan rayuwarmu mai tsauri, da kuma haskaka tafarkinmu da haskensa, kuma godiya ta tabbataga Allah a tun farko da kuma karshe.

Shimfida
Ma'anar Kalmar Shi'anci a Lugga
Kalmar Shi'anci a lugga tana nufin biyayyya da taimakekeniya da jibintar al'amuran juna. Don haka kalmar 'yan Shi'a a lugga tana nufin mataimaka ko mabiya kuma wannan Sunan yawanci ana gaya wa mabiya Imam Ali (a.s) shi, har sai yakebanta da su ya zama su ake gaya wa.
Kuma da wannan ma'anar lugga ne Kur'ani ya yi amfani da kalmar Shi'a kamar a cikin fadin Ubangiji madaukaki "Hakika daga cikin Shi'arsa akwai Ibrahim" aya 83 saffat. Haka nan fadinsa madaukaki "Wannan yana daga Shi'arsa wannan kuma yana daga makiyansa" 15 kasas.
Shi'anci a Isdilahi
Shi'anci da wannan ma'anar ta isdihalhi yana nufin imani da wasu akidu na musamman. Sannan kuma masu bincike sun yi sabani kan wannan akidu game da yawansu ko karancinsu al'amarin da zamu yi bayaninsa nan gaba dalla-dalla, kuma wannan ma'anar ta fi tafarko fadada. Don haka ne zamu bincike game da ma'anar Shi'anci a ma'ana ta biyu saboda ya shafi kowanne daga cikinsu.
Kasancewar Shi'anci imani ne da akidu na musamman don haka ne ma malamai da masu bincike suka yi bayanin ma'anarsa da sassabawa game da bayanin ma'anarsa, ga wasu nan daga cikin wadannan bayanai:
1- Shahidi na biyu a cikin littafin sharhin Lum'a ya ce: "Shi'a su ne wadanda suke biyayya ga sayyidina Ali koda kuwa bai yarda da jagorancin sauran imamai ba, don haka ya hada da Imamiyya da jarudiyya, da zaidiyya da isma'iliyya banda wadanda suke masu wuce gona da iri daga cikinsu kamar wakifiyya da fadahiyya".
2- shaihul Mufid a littafin mausu'a kamar yadda mawallafi ya cirato daga gareshi ya ce: "Shi'a su ne mabiya Ali masu gabatar da shi da fifita kan sauran sahabban manzon Allah (s.a.w), wadanda suka yi imani da cewa shi ne jagora bayan manzon Allah (s.a.w) da wasiyya daga manzon Allah (s.a.w) ko da nufin Allah da izininsa a bisa nassin shari'a kamar yadda Shi'a imamiyya suke ganin shi, ko kuma da siffantawa kamar yadda Jarudiyya suke gani".
Kuma haka nan an nakalto wannan ma'anar ta Shi'anci daga Mustapha Asshaibi a littafinsa na "Sila".
3- Shahristani a cikin "Milal wan Nahal" ya ce: "Shi'a su ne wadanda suka bi bayan Ali (a.s) kuma suka yi furuci da jagorancinsa da halifancinsa a nassi da wasiyya ko bayayyananne ko boyayye kuma suka yi imani da cewa jagoranci ba ya fita daga 'ya'yansa, idan kuwa ya fita daga hannunsu to sai dai da ta hanyar zaluntarsu da waninsu ya yi ko kuma da takiyya daga garesu".
4- Nubkhati a littafinsa na firak ya ce: "Shi'a su ne jama'ar Ali (a.s) da ake ce musu Shi'ar Ali a zamanin Annabi (s.a.w) da kuma duk wanda ya tafi a kan son Ali (a.s).
5- Muhammad Farid Wajdi a littafinsa na "Da'iratul Ma'ariful Karnil Ishrin" ya ce: Shi'a su ne wadanda suka yi biyayya ga Ali a game da jagorancinsa kuma suka yi imani da cewa jagoranci na 'ya'yansa ne kuma ba ya fita daga hannunsu kuma suka ce su imaman ma'asumai ne daga manya da kanana zunubbai kuma suka yi furuci da wilaya (son Ali da jibinta lamari gareshi) da barranta (kin azzalumi da gaba da makiyan Allah da Manzo da imamai) a zance da aiki sai dai alokacin takiyya yayin da suka ji tsoron riko da kamun azzalumi".
Wadannan su ne misalai na bayani da zamu gabatar domin ka san mene ne Shi'anci a ra'ayin malamai masana masu bincike, kuma da wannan muna iya ganin wasu sun hada:
Cewa Shi'a suna gabatar da Imam Ali da fifita shi a kan wanisa na sahabbai saboda samun nassin shari'a a kan hakan ko kuma samun wata siffa da ya kebanta da ita kuma babu ita ga waninsa, kuma a fili yake cewa Shi'anci shi ne lizimtar fadin imamancin (jagorancin) Imam Ali da zuriyarsa da kuma fifita ta a kan waninta saboda nassin shari'a da Shi'a suke da shi a kan hakan, kuma muna iya fahimtar abubuwa biyu game da hakan:
Na farko: Imamanci jagoranci ne na nassin shari'a, kuma Imamai (a.s) sun ci gaba da isar da sakon Annabi (s.a.w) ne kuma duk abin da annabta take da shi na hakki kamar biyayya da isma in banda wahayi to yana tare da imamanci.
Na biyu: Imamanci ba ya yiwuwa da zabe domin Allah ne yake ayyana wanda ya so, kuma an yi nassi ta hanyar Annabi (s.a.w) da biyayya ga jagorancin Imam Ali (a.s) bayansa, kuma ya zabe shi da siffofi da yake da su da babu wani mai su.
Amma dadi a kan abin da muka fada wanda ya zo a cikin wadannan bayanai da muka kawo wadanda ana samun su a cikin wasu llitattafai da nassi wanda muna iya cewa ya hada da asasin mazhaba ne ko na musulunci kamar yadda zaka gani a bayanai da zasu zo nan gaba, kuma hadafin yin wannan bayanai shi ne domin mu yi karin haske kan abin da malamai masana suka kawo ne game da Shi'a da akidojinsu.
Irin wadannan ra'ayoyi da zamukawo suna neman su sanya alaka tsakanin Shi'anci da yahudanci ko kiristanci ko zindikanci da kokarin jingina Shi'anci da wasu jama'a daban. Wadannan masu kawo irin wadannan ba komai suke nufi da wannan ba sai kokarin nuna cewa Shi'anci bai samu tofuwa ba kamar yadda sauran mazhabobi suka tofo. Kuma zamu yi maka bayanin wadannan ra'ayoyi da suke nuna Shi'anci da wata ma'ana maras inganci domin bata Sunan Shi'anci. Sannan kuma bayan kawo wadannan ra'ayoyi na masu gaba da Shi'anci sai in yi nawa bayani a kai.

Tasowar Shi'anci da Asalinsa
1- Dakta Abdul'aziz Adduri ya kawo asalin Shi'anci da kasa shi kamar haka ne cewa akwai na akida wanda ya fara daga lokacin Annabi (a.s) ne. da kuma na siyasa da ya fara bayan kashe Imam Ali (a.s). Kuma ya kafa dalili a kan haka da cewa ma'anar Shi'anci an yi amfani da ita ne a lokacin "Tahkim" -wato hukunci tsakanin jama'ar Imam Ali (a.s) da ta Mu'awiya dan Abusufyan- wanda a cikin aka ambaci jama'arsu da shi'ar Ali (a.s) da kuma shi'ar Mu'awiya, abin da yake nufin mabiya Ali (a.s) da kuma mabiya Mu'awiya ba tare da kawo wasu abubuwan da suka shafi siyasa ba bayan hakan.
2- Muhammad Farid Wajdi a "Da'iratul ma'arif" ya ce: "Shi'a su ne wadanda suka goya wa Ali (a.s) baya a cikin jagorancinsa kuma suka yi imani da cewa jagoranci ba ya fita daga 'ya'yansa, kuma suka yi imani da ismar imamai daga zunubbai manya da kanana, da kuma yin imani da wilaya da bara'a (wato kauna da biyayya da kuma barranta) a zance da aiki, sai dai a lokacin takiyya idan sun ji tsoron azzalumi kuma sun kasu kashi biyar; 'Kaisaniyya, Zaidiyya, Imamiyya, Gullat, da Isma'iliyya' kuma wasunsu suna karkata zuwa ga Mu'utazilanci wasu kuma zuwa ga Sunna, wasu kuma zuwa ga Tashbihi".
wannan bayani na Farid Wajdi ya rigaya cewa na kawo wani bangare nasa a bayanin ma'anar Shi'anci kuma na kawo wannan ne domin in kawo shi gaba daya, domin bayanin abin da ake fada kan Shi'anci tun farkonsa har zuwa yau, domin mu sani cewa wadannan kalmomi ba a rana daya ba ne aka shigar da su cikin ma'anar Shi'anci, sannan kuma mu iya gani afili cewa Farid Wajdi ya hada wani cakude kawai ya sanya abin da ba Shi'anci ba cikin Shi'anci kuma ya jingina wa Shi'a abin da su sun barranta daga gareshi, kuma ni ba na son in gaggauta raddi ne gare shi sai ya kasance tun yanzu mun shagaltu da irin wadannan jawabai da raddinsu a wurin da ya dace da su a wannan littafin.
3- Dakata Kamil Mustapha a littafinsa na "Assila" ya ce: "Bayan haka yana bayyana garemu cewa Shi'anci ya faro tun farkon musulunci a matsayinsa na kashin bayansa, kuma ya bayyana kamar wata kungiya ta siyasa bayan Mu'awiya ya yi gaba da Imam Ali (a.s) a game da jagorancin al'amuran musulmi, sai ya bayyana bayan haka a matsayin wani motsin gwagwarmaya mai karfi karkashin Sunan Shi'anci bayan kashe Imam Husain (a.s) kai tsaye, don haka muna iya cewa Shi'anci wani abu ne da ya bayyana tun lokacin Annabi amma ya karfafa a mtasyin siyasa bayan kashe Usman dan Affan sannan sai ya kasance kalma ce da ake amfani da ita a isdilahinta bayan kashe Imam Husaini (a.s). kuma wannan yana nufin ya bi marhaloli daban-daban domin ya samukamalarsa kamar yadda Dakta Kamil yake cewa.
4- Dakta Ahmad Amin ya ce: "Shi'anci ya fara tun farko da ma'ana mai sauki wato cewa Ali (a.s) shi ne ya fi waninsa ta fuska biyu: Shi kansa da kuma kusancinsa da Annabi (s.a.w). Sai dai wannan Shi'anci ya dauki wata sabuwar sura da sabon salo da aka shigar da wasu sababbin abubuwa a cikin addinin musulunci wadanda suka hada da yahudanci da kiristanci da majusanci. Kuma tunda mafi girman abin da aka shigar a musulunci daga Farisawa ne, to don haka ne ma suke da gudummuwa mafi yawa a tasiri kan Shi'anci.
A fili yake cewa daga abin da Ahmad Amin ya fada muna iya cewa shi a ra'ayinsa ke nan Shi'anci ya samu daukaka da ci gaba ne ba don wani abu da ya tofo daga cikinsa ba, sai dai saboda kare-kare da aka yi wa addinin musulunci da akidojin wasu addinai da aka sanya akidojinsu a musulunci, sannan kuma sai Shi'anci ya zabe su daga musulunci ya kuma karbe su suka zamanto wani bangare nasa, har sai da ya kasance yadda yake. Kuma yana ganin cewa Farisawa sun yi tasiri ke nan kan wannan mazhaba fiye da waninsu kamar yadda shi Ahmad Amin yake son nunawa. Kuma wannan ra'ayi ne da Ahmad Amin ya samu daga waninsa kuma shi ma waninsa ya samu daga wani ne har dai a kai ga mutum na karshe na farko da ya fara yin wannan maganar kage kan Shi'a, har dai wannan maganar ta kusan zama wani dalili gun wasu masu bincike masana. Kuma in Allah ya so nan gaba kadan zan nuna maka karyar wannan kage da kuma hadafin da ake son cimma da wadannan maganganu na damfara Shi'anci da Farisanci.
5- Dakta Ahmad Mahmud Subhi ya ce:
"Bayan ya kawo abubuwan da aka fada kan Shi'anci da kuma kawo cewa dangantakar Shi'anci ga Shi'a kamar zuhudu ne lokacin manzon Allah (s.a.w) da halifofin farko, da kuma bambancinsa da sufanci da ya wakana a lokacin ganusiyya da kuma tasirantuwarsa da wasu fikirori da akidu masu sabawa da juna kamar yadda aka sani gun muhyiddin Ibn Arabi da kuma Sahrawardi a misali".
Bayan duk wadannan misalai da maganganun da suka zo daga wasu litttattafai da suka kawo bambancin Shi'anci a farkon musulunci da kuma zamunan da suka biyo baya sai ya rufe magana da wadannan bayanai masu zuwa da cewa:
1- Adadin mas'alolin tunani na Shi'a suna dada yawa fiye da yadda suke a zamanin farko babu wani kokwanto, wanan kuma ba domin daduwar asalin asasin fikirar Shi'anci ba ne, sai dai domin yawaitar karin bayanai dalla-dalla da sharhin dunkulallun bayanansa, ba wai dadi ba ne kan asasin abin da ya kafu a kansa, sai dai bayanin asalin Shi'anci ne, kuma wadannan bayanai suna bayyana dalla-dalla a tsawon zamuna da suka gabata har zuwa yau.
A bisa misalin ruwayoyin da suka zo game da nunin fifikon Ali (a.s) daga Manzon Allah (s.a.w) shin suna bayani ne ta yadda zai wajabta a kan musulumi su yi riko da imamancinsa ta fuskancin wasiyya gareshi da halifanci, kuma idan haka ne; shin wannan jagorancin ya tsaya ne gun abubuwan da suka shafi jagoranci ko kuma dole ne Imami (a.s) ya kasance yana da fifiko a komai kamar ya kasance shi ne mafi ilimin mutane, mafi karfinsu, mafi adalcin mutane, haka nan ma abin da ya shafi isma da sauransu.
To dukkan wannan al'amuran suna shiga cikin lamarin jagoranci halifancin Annabi, ba wasu al'amura ba ne da suka dadu a kan asalin wannan lamarin, sai dai sun bubbugo ne daga ci gaban tunani da kuma daduwar yawan masu karbar mazhabar, da yawan mas'aloli da tambayoyi da ake tayarwa kan lamarin imamanci wato halifancin Annabi (s.a.w).
2- Irin wannan ci gaban kamar irin ci gaban zamani ne, don haka ne ma musulunci ya samu ci gabansa tare da samun tofuwa da bullar wasu mazhabobi. Musulmi tun farkon samuwarsu sun yi imani da Allah da samuwarsa da kadaitakarsa, da siffantuwarsa da siffofin kamala da tsarkakarsa daga siffofin tawaya, kuma amma duk wannan a dukkule ne. Amma yayin da fagen tunani ya fadada, kuma duniyar musulmi ta bude wa al'umma da al'adu mabambanta, sai ga mas'aloli suna kunno kai, sai musulmi suka koma wa abin da suka yi imani da shi a dunkule suna masu gini a kan dunkulallun bayanansa a takaice, suna fasa su dalla-dalla al'amarin da ya haifar da fikirori daban-daban, kuma wannan ya faru game da imaninsu ga mahaliccin komai: Aka samu jayayya game da sabuban halitta a game da siffar halittawa, wanda a ganin wasu wannan yana iya kai wa ga kididdigar mahalicci, ko kuma wannan yana rushe kadaitakar Allah a matsayinsa na mahallicci: Domin Allah madaukaki yana da tasirin da halittu ba su da shi, kuma dukkan abin da yake ga ababan halitta ta wata fuska ne, kuma wannan ba ya rusa cewa Allah madaukaki shi ne mafificin masu halittawa. Sai wannan mas'ala ta haifar da mas'alar ayyukan bayi, da kuma alkanta wannan da mas'alar zabi ko tilasci a cikin ayyukan bayi.
Wani misalin shi ne: Imanin da musulmi suke da shi tun lokacin da suka samu hujjar da suke da ita ta ayoyin Kur'ani mai girma, sai wannan ya sanya su jayayya game da zahirin wasu daga ayoyin Kur'ani domin wannan yana nufin jingina abin da bai inganta ba zuwa ga Allah madaukaki, wannan irin mas'alar ta hada da irin fadin Allah madaukaki cewa: "Wasu fusaku a wannan rana masu haske ne, suna masu duba zuwa ga Ubangijinsu". Alkiyama: 22. Yayin da Ahlus-sunna suka tafi a kan cewa zai yiwu a ga Allah madaukaki a ranar kiyama da idanuwa kuru-kuru, dogaro da zahirin aya, su kuma malaman imamiyya (Shi'a) suka tafi a kan cewa mustahili ne a ga Allah domin wannan yana nufin yiwuwar jiki ga Allah (s.w.t), daga karshe kuma a samu hauhawar sassa ga Allah sannan sai kuma bukatuwa, sai faruwa gareshi, daga karshe ke nan sai a kore wa Allah Ubangijintaka, don haka ne ma suka tafi a kan cewa fassara kalmar "Nazar" a wannan aya tana nufin sauraron rahama, ba ganin Ubangiji ba. Kamar yadda ake yin amfani da ita a harshen Larabci da wannan ma'ana yayin da wani zai ce da wani ina sauraronka, kuma Kur'ani ya sauka ne da harshen Larabci kamar yadda suke magana a cikin muhawarorinsu.
Wannan ke nan hada da cewa Ubangiji madaukaki ya danganta wannan kalma zuwa ga fusaku da cewa su ne aka jinginawa kalmar nan ta "Nazar" alhalin su ba sa cikin gabobin gani. Kamar dai fadinsa madaukaki: "Ba sa sauraron komai sai tsawa daya da take rikon su, sai ga su suna masu husuma" . Yasin: 49, da ya yi amfani da kalmar "Nazar".
Haka nan wani misali da zan iya kawowa shi ne na yawaitar al'amuran musulunci fiye da yadda yake a zamanin farko, musulmi sun yi imani da cewa Allah ba ya aikata wasa kuma zahirin ayoyin Kur'ani sun zo suna karfafa hakan, ya zo a cikin fadinsa madaukaki: "Wannan da ya halicci mutuwa da rayuwa domin ya jarrabe ku" surar Malik: 2. Ya zo da fadinsa cewa: "Ba mu halicci sammai da kasa da abin da yake tsakaninsu suna masu wasa ba" Dukhan: 38. Amma duk da hakan musulmi sun yi jayayya bayan hakan a kan cewa shin ayyukan Allah suna da hadafi wanan kuma yana nufin tawaya ga Allah (s.w.t) domin dukkan mai aikin da yake da hadafi to yana bukatar mai samarwa, ko kuma ayyukansa ba su da hadafi, wannan kuma yana lizimtar cewa ayyukansa wasanni ne, Allah (s.w.t) kuwa ya barranta daga hakan. Sai Ahlus-sunna suka tafi a kan cewa ayyukansa ba su da hadafi, sai imamiyya suka tafi a kan cewa suna da hadafi ba tare da wannan ya lizimta wa Allah wani mai samarwa gareshi ba, wannan kuwa domin amfanin yana komawa ne zuwa ga bayi kansu, don haka zai yiwu a hada tsakanin wadannan al'amura biyu ke nan, sai ya kasance amfanin bayi da kuma kasancewar Allah ba ya wasa, kuma ba ya bukatuwa zuwa ga komai. Duk da wadannan abubwan da muka fada ba zai yiwu ba a ce; akidun musulmi sun fi yawa fiye da yadda suke a da can farkon musulunci, abin da ya faru shi ne musulmi sun dada yalwatawa cikin sharhin al'amura a dunkule yayin da suka bukaci hakan sakamakon haduwar su da sauran al'adu da fikirori iri-iri.
Musulmi a farkon musulunci da musulmi a wannan zamanin namu dukkansu suna da madogara daya ne wato; Littafi da Sunna, samma abin da ya gabata a dunkule ne sai aka bukaci bayani dalla-dalla saboda samuwar bukatuwa zuwa ga hakan alhalin da can babu ita a farkon musulunci, don haka ci gaban da shi'anci ya samu irin wannan ne da ya faru a cikin musuluncin kansa, kuma shi a bisa hakika da wannan ma'anar ba shi da wata jayayya a kai.
Amma faruwar sababbin ra'ayoyi wadanda suke nesa da musulunci babu wannan a cikin shi'anci, domin duk wani abu da musulunci yake kin sa, to bisa tabbas Shi'anci yana kin sa, hakika dukkan abin da ya faru a musulunci kamar yadda muka fada din nan babu wani tawaya da yake haifarwa ga akidun jama'un musulmi, kuma idan abin da ya faru a Shi'anci na ci gaba kamar abin da ya faru ne a musulunci to mene ne yake haifar da wata matsala a akida kuma ya kawo wasu matsaloli da ba su da wata madafa, har ake jifan Shi'a da su?.
3- Idan ma mun sauko mun kaddara shigar wani abu a cikin Shi'anci kamar yadda wasu suke son tabbatarwa haka nan babu wani dalili to irin wannan kaddarawar tunanin Shi'anci yana kin sa idan ya kasance ba ya daidai da abin da yake cikin littafin Allah da sunnar annabinsa (s.a.w) da kuma tsarin musulunci gaba daya, irin wannan kaddarawar ra'ayi ne da yake komawa kan mai shi, kuma duk abin da ba cikin musulunci yake ba to babu shi a Shi'anci da tabbacin cewa Shi'anci fikira ce da ta zo daga Ahlul-baiti (a.s) kuma su ne daidai da Kur'ani kuma su kamar jirgin Nuhu (a.s) ne, don haka ne wanda yake danganta wani abu mummuna ga Shi'anci ya samu cakude ne tsakanin Shi'anci da kuma 'yan Shi'a, kuma da yawa wanda ake cewa da shi dan Shi'a amma shi'ancin yana kin sa a bisa tsarinsa wanda abu ne da zamukawo shi nan gaba, sha'anin wannan shi ne kamar sha'anin sunnanci ne wanda yake kore wasu masu rabuwa da shi wadanda karkacewarsu ta tabbata daga tsarin tafarkin musulunci, kuma samuwar irinsu ba ya cutar da Ahlus-sunna, kuma wannan ba ya hana a kira su da Sunan da ake gaya wa Ahlus-sunna gaba daya.
A mafi munin kaddarawa idan an samu wasu karin mas'aloli a cikin kowace irin wace mazhaba ce, kuma ya kasance dadi a kan asalinsa kamar yadda yake an kaddara kuma an dauka haka ne, to hakan ba ya iya haifar da wani musun abubuwan da suke laruri na addini ga mai wannan akida, kuma ba ya kaiwa ga ridda ko karkacewa. Sannan irin wannan ba ya sanya jifa da kalmar fita daga addini da fita daga musulunci ga wanda yake da wannan da kuma damfara shi da yahudanci da kiristanci da makamancin hakan na daga dangantakar da babu wani musulmi mai dabi'a da halaye na gari masu dogaro da koyarwar musulunci da yake gaya wa dan'uwansa irin wannan.
Yaushe ne fadin wasiyya ga Ali (a.s) a bisa misali da cewa kowane Annabi (a.s) yana da wasiyyi, kuma wasiyyai (a.s) dole su kasance ma'asumai ne domin a samu tabbatar hadafin kafa su jagorori ga al'umma su tabbata da kuma imani da cewa Imam Mahadi (a.s) rayayye ne, da makamancin wannan na daga akidoji, yaushe ya kasance fita daga addini kuma ya kai ga hari da jifa da kalmomi munana maras dalili wanda mutanen zamaninmu na yau ba su gushe ba suna bin marigayansu ba tare da sanin asalin wannan sukan ya bayyana ba, kuma ba a yi tattaunawa a kai ba domin warware mas'alar.
Amfani da dukkan karfi a fagen soki burutsu ba shi da wani amafani ko kadan, hada da cewa zai iya yiwuwa a yi amfani da wannan karfin a wajan da ya dace domin kawo hadin kai da kuma kawar da duk wani abu da ya gurbata lamarin musulmi, da kuma tsaftace yanayin musulunci daga gaba da kiyayya da mugun kuduri da kulli wanda ba ya amfanar da kowa sai makiya musulunci. Kuma duk wadanda suke iza wutar kawo rarraba da gaba tsakanin musulmi to mutane ne da suke nesa da musulunci kuma ba su da nisa da shubuhohi da rudu, musamman irin wadannan al'amuran yana zama wajibi ne su kasance sun takaita da malamai ne kawai, kada ta sauko a tsaka-tsakin mutane balle taci barkatai din su.
Wannan kuwa domin malamai suna da wata kariya da take hana su nisanta daga kallon hadarin kaji, da harara, da kuma gabar jahiliyya, kamar yadda muke iya gani cewa kumajin kabilanci da bangaranci a tunanina ya fi hadari a kan dan Adam fiye da makamin kare dangi. Haka nan kuma a tarihin musulmi an samu sabani da ya kasance kuma har yanzu yana nan yana shake da bakin ciki a bakin duk wani mumini mai imani da Allah (s.w.t) da addininsa da dukkan hadafin sakon sama na Ubangiji madaukaki wanda yake yana daga hadafinsa shi ne sanya ruhin mutumtaka da 'yan'adamtaka a cikin dukkan wani loko na rayuwar dan Adam.
Cibiyar Haidar don Yada Musulunci
www.hikima.org
hfazah@yahoo.com
Hafiz Muhammad Sa'id
Monday, December 10, 2012