Haduwa Da Masoyi (Imam Mahdi AJ)
Haduwa Da Masoyi (Imam Mahdi)
Shi'a sun fuskanci wahalhalu a rayuwa sakamakon nisanta da jagoransu Imam Mahadi (a.s) kuma wannan al'amari ya sanya su cikin yanayi mai bakin ciki, koda yake a lokacin boyuwar Imam Mahadi karama Shi'a sun kasance suna masu saduwa da shi ne ta hannun wakilansa na musamman, amma a boyuwarsa babba (mai tsayi) wannan alaka ta katse gaba daya. Kodayake akwai malamai da yawa da suka yi imani da haduwa da shi kuma wannan ya faru ga manyan malamai kamar Allama baharul ulum, Mukaddis Ardabili, Sayyid dan Dawus, da sauransu da suka shahara, da akwai kuma littattafai masu yawa da suka nakalto labarai game da haduwa da shi (a.s) . Sai dai muna iya duba wasu muhimman bayanai game da haduwa da Imam Mahadi (a.s) da suka hada da:
Na farko: Haduwa da Imam Mahadi (a.s) wani lokaci yakan kasance a lokacin matsuwa da takan samu mutum ne, wani lokaci kuma a lokaci ne na al'ada ba tare da wani larura ba.
Akwai labaru masu yawa game da al'amarin da ya shafi damuwar masu mutane da suka bace hanya, kamar mutanen da zasu Makka ziyarar dakin Allah sai suka bace hanyarsu kuma Imam (a.s) ko wani daga yaransa mabiyansa shi ne ya shiryar da su hanya ya fitar da su daga dimuwa, kuma yawancin haduwa da Imam (a.s) ta irin wannan ne. Sai dai game da haduwa da shi a lokacin da ba na larura ba to wannan yana kasancewa ne yayin da shi mai haduwa da shi ya kasance mutum ne ma'abocin dukakaka da matsayi wajen Allah (s.w.t).
Bisa la'akari da abubuwan da muka kawo sama muna iya cewa:
Na daya: Duk wani wanda zai yi da'awar haduwa da Imam (a.s) ba a yarda da maganarsa.
Na biyu: A wannan zamani namu an samu wasu mutane da suka yi da'awar haduwa da Imam Mahadi (a.s) kuma suka kira mutane kan hakan wanda a sakamakon hakan sun batar da mutane masu yawa da kuma karkatar da akidun mutane da batar da su, kuma daga karshe za a samu cewa irin wadannan mutane sukan zo da wasu wurudodi su ba wa mutane wadanda ba su da wani armashi na gaskiya kuma sun saba wa abin da imamai (a.s) suka zo da shi.
Sannan kuma akan samu wasu suna ganin haduwa da Imam Mahadi (a.s) abu ne mai sauki, alhalin wani abu ne wanda ko kokwanto babu a kan cewa; Ubangiji madaukaki ya sanya shi a cikin boyuwa cikakkiya gaba daya kuma idan ka cire mutane kalilan wadanda suka samu ludufin Allah babu wani wanda ya samu nasarar haduwa da shi kai tsaye.
Na uku: Haduwa da shi tana yiwuwa ne yayin da Imam (a.s) ya ga akwai maslahar hakan, don haka ne duk sadda wani mai bege da kauna ya ga ya kasa samun haduwa da shi duk da kuwa ya yi kokari to kada ya yanke kauna daga samun ludufin Allah, kuma ya sani cewa wannan ba yana nufin cewa; shi ba ya cikin ludufin Allah ba ne, kuma ya sani haduwa da Imam (a.s) ba ya nuna alamar kai wa matukar takawa da fifiko da kamala ba ne.
Duk da cewa ganin Imami da magana da shi da kuma haduwa da shi sa'ace mai girma da rabauta mai daukaka, amma mu sani imamai musamman Imam Mahadi (a.s) bai kwadaitar da mu ba wajen kokarin ganinsa kuma bai sanya mana ganin lallai sai mun kai ga ganinsa ba, sai dai akwai maganganu masu yawa daga imamai (a.s) da suka yi umarni da cewa a kodayaushe mu kasance cikin tunawa da shi kuma mu yi addu'a domin bayyanarsa, kuma mu yi aiki domin cimma hadafi mafi girma da dan Adam ya ke sauraro na bayyanarsa domin ya bayyana da gaggawa wannan Duniya, kuma al'ummarta ta amfana daga gareshi kai tsaye.
Imam Mahadi (a.s) da kansa yana cewa: "Ku yawaita addu'ar bayyanata, ku sani wannan ne farin cikinku" .
A nan muna ganin ya dace mu kawo abin da ya faru na haduwarsa mai dadi tare da Alhaji Ali Bagdadi wanda yake daga mutane na gari, domin takaitawa zamu takaita da wadannan bayanai masu muhimmanci:
Shi mutum ne mai takawa wanda kodayaushe yana zuwa Bagadaza yana ziyartar kabairn Imam Musa Kazim da Imam Jawad (a.s), yana cewa: akwia wasu kudin humusi a kain saboda haka sai na tafi Najaf da su, kuma na bayar da toman ishirin ga sheikh Ansari, ishirin ga sheikh Muhammad kazimi, ishiri kuma a Ayatullahi sheikh Muhammad Hasan sharuki, sai kuma na yi niyya cewa toman ishirin kuma idan na koma Bagadaza zan ba wa Ayaltullahi aali yasin.
Ranar alhamis sai na koma Bagadaza da farko sai na je kazimain kuma na ziyarci imamai biyun, sannan sai na nufi gidan Ayatullahi aali yasin na ba shi bangaren (wani kaso na) kudin da ya rage da suke a kaina, kuma na nemi izinin a wajensa cewa zan bayar da sauran a hankali, sai ya yarda, kuma ya dage in zauna wajensa, amma sai na bayar da uzuri na yi bankwana da shi na koma Bagadaza.
Na cimma daya cikin uku na tafiyata sai na ga wani Sayyid (sharifi) da koren rawani, kuma a goshisa akwai wani bakin tabo bayyananne, kuma zai tafi kazimaini don ziyara. Sai ya yi kusa da ni ya yi mini sallama kuma ya rungume nei ya rabani da kirjinsa kuma ya yi maraba ya ce: ya yi kyau ina zaka tafi?
Sai na ce: na yi ziyara ne kuma yanzu zan tafi Bagadaza ne. sai ya ce; daren juma'a ne ka koma kazimain ka tsaya a can! Sai na ce, ba zan iya ba. Sai ya ce: zaka iya koma domin in bayar da sheda cewa; kana daga masoya kakana Imam Ali kuma kana daga masoyanmu, kuma shi ma sheikh ya bayar da sheda akan hakan. Ubangiji yana cewa: "ku sanya shedu biyu" .
Haji Ali ya ce: Ni da ma can na nema daga Ayatullahi aali yasin ya rubuta mini sheda cewa ni ina daga cikin Shi'a kuma masoya Ahlul Baiti (a.s) domin in sanya ta a cikin likkafanina. Sai na tambayi wannan Sayyid din: yaya ka san ni? Sai ya ce: yaya kuwa wanda yake bayar da hakkinmu cikakke ba zamu san shi ba? Sai na ce: wane hakkin? Sai ya ce: hakkokin da ka ba wa wakilaina. Sai na ce: wane ne wailinka? Sai ya ce: sheikh Muhammad Hasan! Na ce: shin shi wakilinka ne? sai ya ce: na'am.
Daga manganar da ya yi sai na yi makaki mai tsanani, sannan sai na ga kamar dai akwai sanayya sabuwa da ni da shi ne wacce na manta, saoba da farko ya kira ni da sunana, sai na yi zaton akwai wani hakki na zuriyar Manzon Allah ne da yake son in ba shi saboda yana cikinsu ne. sai na ce: haka ne akwai hakkokinku 'ya'yan Manzon Allah amma na karbi damar sarrafa shi. Sai ya yi murmushi ya ce; haka ne akwai wani hakkinmu da ka ba wa wakilanmu a Najaf. Sai na tambaya shin aikina kuwa yardajje ne a wurin Allah? Sai ya ce: haka ne.
A zuciyata na ce: yaya wannan Sayyid yake cewa game da malaman zamanin nan a matsayin wakilansa? Amma dai sai na gafala, na manta da wannan al'amarin.
Sai na ce: shugabana shin da gaske ne da ake cewa kowane dare na juma'a idan muutm ya ziyarci Imam husai (a.s) zai dawwama cikin aminci. sai ya ce: haka ne! sai a lokacin na ga hawaye sun cika masa idanuwa, babu wata jimawa sai na ganmu a haramin kazimain (a.s) ba tare da wuce hanyoyi ba, sai ga mu a harami.
Sai muka tsaya a gefen hanyar shiga. Sai ya ce: karanta ziyara! Sai na ce: shugabana ban iya ba. Sai ya ce: idan na karanta kai ma zaka karanta? Sai na ce: na'am!
Sai ya fara ya yi sallama ga Manzon Allah da imamai daya bayan daya, sannan bayan ambaton sunan Imam Askari (a.s) sai ya fuskanto ni ya ce: ka san imaminka? Sai na ce: yaya kuwa ba zan san shi ba? Sai ya ce: to ka isar masa da sallamarka. Sai na ce: Assalamu alaika ya hujjatul lahi! ya sahibaz zaman! yab nal Hasan! Sai ya yi murmushi ya ce: Alaikas salam warahmatullahi wa barakatuhu.
Sai na shiga harami na sumbanci kabari, sai ya ce: Karanta ziyara. Sai na ce: ba zan iya ba shugabana. Sai ya ce; in karanta maka? sai na ce: na'am! Sai ya karanta ziyarar nan mash'huriya ta "Aminullah" sannan sai ya ce: shin zaka ziyarci kakana Imam Husain (a.s)? sai na ce: haka ne, yau daren juma'a ne kuma daren ziyarar Imam Husain ne. sai ya karanta ziyarar nan mash'huriya ta Imam Husain (a.s). yayin sallar magariba sai ya ce: ka yi sallar jam'i. Bayan salla sai ya bace min daga ganina, kuma duk yadda na yi bincike ban iya gano shi ba.
Sai a lokacin na fahimci cewa na tuna wannan sayyid da ya kira sunana, kuma ya nemi in koma kazimain duk da ba na son komawa. Kuma ya ce damanyan malaman zamaninsa wakilansa ne, daga karshe kuma ya bace bagatatan, sai tunani ya zo mini cewa wannan shi ne Imam Mahadi (a.s). Kaicona da sai tun daga baya na gane shi ne !
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center for Islamic Propagation