Siffar Imam 2
WALLAFAR: JA'AFAR SUBHANI
Sifofin Imam Mahadi
Ku yi mana bayanin siffofin Imam Mahadi (a.s) a dunkule a takaice? Sannan ku fada mana marhalolin rayuwarsa har karshen duniya?
Siffofin Imam Mahadi (a.s) da dama sun zo a ruwayoyi daga Manzon Allah da Ahlul Baiti (a.s) wadanda zamu yi nuni da wadansunsu a nan:
Fuskarsa ta samari ce, goshinsa yana da tsayi kuma mai haske ne, girarsa kamar jinjirin wata, idanuwansa bakake ne kuma masu girma, hancinsa madaukaki ne kuma mai kyau, hakoransa masu haske ne, a tsakanin habarsa akwai wata alama kamar alamar Annabi, jikinsa madaidaici ne.
A wata ruwaya ta zo da siffofinsa kamar haka; Shi mai ibada ne, mai raya dare, mai hakuri da adalci da kyayawan ayyuka, …shi ne ma'abocin tashi da gwagwarmaya da jihadi, shugaban Duniya, mai tseratarwa, mai gyara mai girma, shi samuwa ne mai haske daga zuriyar Manzon Allah (s.a.w) daga kuma 'ya'yan fadima (A.S, kuma na tara daga zuriyar Imam Husaini (a.s) wanda a lokacin bayyanarsa zai dogara a jikin ka'aba ne, ya kuma rike tutar Manzon Allah (s.a.w), kuma da gwagwarmayarsa ne zai raya addinin Allah (s.w.t) ya kuma aiwatar da hukuncin Allah a duk fadin Duniya, ya kuma cika Duniya da tausayi da adalci bayan an cikata da zalunci .
Sannan rayuwarsa tana da marhaloli uku da suka hada da:
1- Zamanin boyewa; Rayuwa a boye da ta fara daga lokacin haihuwarsa zuwa lokacin shahadar babansa Imam Hasan Askari (a.s).
2- Zamanin boyuwa; da ya fara daga lokacin shahadar babansa Imami na sha daya (a.s) zuwa lokacin da zai bayyana da nufin Allah da umarninsa.
3- Zamanin bayyanarsa: bayan tsawon lokaci yana mai boyuwa zai bayyana da nufin Allah (s.w.t) zai cika dukkan Duniya da kyawawan abubuwa da kuma ado da kawa. Babu wani wanda ya san lokacin bayyanarsa kuma an rawaito daga gareshi cewa wadannan da suke ayyana lokacin bayyana makaryata ne .
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center for Islamic Propagation